Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

labour and she has* *suffered Γ  great deal, the delivery drip usually pushes down the Baby for easy delivery.it does not necessarily* *mean that she has another aliment,,if she's left to herself without the help of delivery drip, she may lose the Baby In the process*



*Well done Kamrina*,
*Thank you*


Adaidai wanan lokacin Kumar dake tsaye yazo hucewa ta wurin Window, din class Din zai huce yaji wanan zazakar muryar mai cik'e da gardi, kuma murya mace daya ke da ita wato Kamrina, juyawa da sauri yakai duban sa cikin ajin aiko take yaga abinda ya firgita sa ya birkita tunanin sa, k'amewa yayi wuri daya sake da baki, da rudani, sakamokon Kamrina da yaga ita ke wanan magana, Kamrina n'a yatsine fuska domin ta fara bayani bata gama ba an tsayar da ita, ba hakan taso ba, taso Malamin ya barta ta gama jawabin ta .


Da k'yar Prince Kumar ya samu ya tataro nutsuwar sa waje daya, bakin sa na motsi yana kalon mamaki cik'e da fuskar sa da k'yar ya samu yace "ikon Allah wanan shine Allah daya, gari banban ,wanan mai zak'ak'an muryar abin da ya banbanta ta da Kamrina, shine ilimi da wayewa da kuma gogewa ,ita kuma wacan yar k'auye ce ba turanci toma wa zai kawo ta singapore, dan ko jiya yayi waya gida mtsss. "



Anma duk wanan zancan zucin da yake idanun sa na kan Kamrina, à haka bai san iya tsawon lokacin da ya dau ba a tsaye har su Kamrina suka tashi.kowa ya fito sai Kamrina da ta tsaya tana ida rubutun da aka musu, domin ita saida lecturer nasu ya gama yayi masu explication sanan ta fara rubutu saida ta gane komai, ganin ba kowa aiko Kumar ya shigo kafe ta yayi da idanu, yana ayanawa dama ace wanan wayayar mai aji da tsari itace matar sa ba wacan ba wada ko zo n'a kashe ka da turanci Bata sani ba, da ya caba, sosai ya shagala yana kalon ta, yayin da yake jin wani abu na tsirgawa daga k'afafun sa har cikin zuciyar sa, yanayin sa na canzawa, Kamrina da ta gama rubutun ta ta maida komai cikin jakar ta, ta d'auko, tashin da zatayi ta juyo, waro ido tayi 😱alamun taji tsoro anma à zuciyar ta ba wanan tsoron bane à fili ta nuna masa tsoro ya bata, anma à zuciyar ta tsoro firgici ne suka tarar mata, anma ko kadan bata nuna masa ba.


Basarwa tayi alamun ma bata taba ganin sa ba, tace "Excuse me you"πŸ€” tayi masa alamar shi waye ?.
D'auke numfashi yayi, take yaji wani abu ya tsarga zuciyar sa, dak'yar ya dawo daidai, yace mata "sanu ko"
Domin yaga kamar ta baci da Kamrina sosai har ya fara wasiwasi, ya kara ce mata "sanu dai"

Wani kalo ta masa alamun bata san mai yake cewa ba, tace "what is it sanu dai ?



"tab Kumar yace domin yanzu ya fida wasi wasi cewar ba Kamrina bace ba kama kawai ce, anma Allah yayi kama anan dama yasan Kamrina jahila ya Za'a hada ta da wanan wayayar.


"Hi"

Ya kara ce mata, daidai tazo hucewa kusa dashi tace masa "Hi"


Ta huce, ai kusan sumewa yayi Γ  wurin jin kamshin jikin ta tare da kamshin bakin sa da tace masa Hi, wani kamshin dadi n'a sweet ya isko hancin sa




Kusan sankarewa yayi.



Kamrina ko tana fita sauri sauri gudu ta shiga wani lungu, ta fake, wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke har wata yar zufa take, taga alamun bai gane ta ba.


Anma fa Ba karamin kokari tayi ba na nuna masa da tayi ita Bata ma san mai yake fada mata ba.



Ruwa ta fido tasha, sanan taci gaba da tafiya.



Kumar tsaye ya an dasa sa.







Aci gaba da gashiπŸ‡
Maimou Love😘
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
*WACECE NI KAMRINA*
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€






*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAHI AM*πŸ’‹





*PAGE 57-58*






Dak'yar Kumar ya samu ya daga k'afafun sa dan sun masa nauhi, tafiya yake yana waige waige ta ina zai kara ganin ta ko ya kara jin sanyi a ransa.


Anma bai ganta haka kafafun sa keta jansa lungu da sako anma bai ganta ba hΓ‘kan yasa ya hakura ya koma class, ko can ma ya kasa barkata komai, saΓ­ tunanin mai kama da Kamrina yake har aka gama aka tashi anma bai gane komai ba.


Tunda Kamrina ta koma d'akin su take ta zuwa da dawowa ,tana tunanin ta fada ma Rukaya ko kuwa, a a kar ta fada mata, zama tayi ta kira gida suka gaisa da Fulani har mai martaba sun gaisa ya kara mata Nasiha, sukayi salama, ta kira wurin su Momy da dady sun gaisa suka sha fira, har Suraya ta kira da ya Umar .


Koda Rukaya tazo Kamrina bata ce da ita komai ba sukaci gaba da sha'anin su.



Tun daga wanan rana Kumar ya maida k'ofar class din su Kamrina wurin zuwan SΓ‘ In baida lecture.

Anma ita Kamrina ko inda yake bata kalo in ta tashi, In ya mata magana bata amsawa, yayi ta bibiyar ta.

Anma duk da haka har yanzu baisan d'akin da take ba, shi kansa yana mamakin kansa da yaki yin zuciya ya barta, saΓ­ ma kara nace mata yake, ko yayi kokarin barin ta sai zuciyar Sa taki amince masa.



Kilishi tunda taji labarin Kamrina bata nan tayi kokarin kara. Maimaita mugun nufin ta gun Fulani, ranar dadare bayan tayi nasarar sama Fulani maganin barci a abun sha, ba'a kuna karatu ba, daidai fatima Aljanar Kamrina ta kawo ziyara gidan dan kwona biyu bata zo ba anan tasan cewa kawar ta ta tafi neman ilimi, taji dadi sosai dama abinda take son ji kenan, tace Bari ta dubo kilishi, cikin iska ta tafi yanayin yanda ranta ke baci tasan kilishi zatayi wani mugun abun, aiko wanan karon a cikin d'aki kilishi da jan zani d'aure tana ta surutun ta, cikin wata rikitatar murya fatima tazo anma bata bayana ba, tace "Wato ke baki hakura ba ko, nayi miki warning anma kinyi kunan uwar shegu kin watsar,"
A rikice Kilishi ta fara magana tana rokon ta da Allah tayi hakuri bazata kara ba. Kilishi harda fitsari, Fatima taso maida mΓ‘ kilishi cutar da taso aika mΓ‘ Fulani anma ta fasa saboda Tuna maganar Kamrina, a wata muguwar sufa Fatima ta fito, kilishi suma ne kawai batayi ba, fatima tace na kara barin ki anma ki sani karon mu na karshe bazai miki kyau ba."


Mari biyar masu zafi akayi mΓ‘ kilishi, fatima ta bace, cikin bargo kilishi ta boye.

Washe gari da ta tashi fuska tayi suntum.




Duk wanda ya tambaye ta sai tace sanyi ne.

Anma fa kudirin ta na saΓ­ ta dau fansa akan Kamrina yana nan.


Kumar ne zaune yau Princess ma na gida, tazo saΓ­ karairaya take ta zauna bisa Jikin Kumar tana shafa sa, tana kashe masa ido daya, wurgar da ita yayi ya nuna ta da dan yatsa ransa a matukar bace yace "ni iskancin ki ya ishe ni, ki kama hanya kibar kasar nan ba tare da izini na ba, kin maida ni wani soko ya ke kika auro ni, sai in kina bukata ta kizo kina shafa ni, daga na biya miki zaki tashi ki barni, in ni keda bukata saide na mutu ke ba wani dadi ba ki gyara kanki in kina gyarawa mtssss."



"Dan har ka samu ina kawo kaina to rike abun ka ka jika kasha dan nima aΓ­ ba dadin naka nake ji ba mtssss. "


Tana gama fadar haka ta koma d'akin ta robar 🍌 ta d'auka tasa kasan ta tana amfani da ita, tana dan ihun ta.



Shiko Kumar taikaicin ta ya ishe SΓ‘, gashi wani iri yake jin kansa yana matukar bukatar mace kusa dashi, kulum cikin azumi yake.

A wanan yanayi ya gama shekarar sa daya da ta rage masa, kuma ya Samu kyalyawan sakamoko .


A lokacin kuma Kamrina nada shekara biyu da zuwan makarantar, suna hawa na biyu a bene, Kamrina ta kara gogewa ta waye, idan tana magana da turanci bazaka taba tunanin ta iya hausa ba, dan ko magana suke da mutane to da turanci suke, in kaga tayi magana da hausa to suna tare da Rukaya a daki, itama Rukaya saura shekara daya ta gama, dan ita shekaru uku dama zatayi, Kamrina ce zatayi shekara bakwoy 7.yanzu saura mata shekara biyar, kuma har yau bata je hutu ba a cewar ta saΓ­ ta gama.

Yau Kumar ke shirin tafiya hakan yasa ya yanke shawarar fada ma Kamrina a cewar SΓ‘ yana son ta, domin a zaman da yayi ya yarda ya kamu da matsanan cin son ta ba na wasa ba.


Yau su Kamrina sun fito daga aji, a waje mutane duk sun firfito, kumar yana ganin ta da sauri yaje ya duka, kusan ta, ya fido wani zobe na damond mai kyau, saida ya fara mata kalamai masu zafi, yace yana son ta, zata aure SΓ‘, irin na christa daΓ­, ya gama tsara ta, Kamrina ta dubi dumbin jama'a dake guri, kowa abun ya burge sa Kumar ko dadi yake ji yasan zata yarda, saida Kamrina ta kare masa kalo tace "you love me"


"yes I love you. "


Kumar ya fada da karfi.


Fuska Kamrina tayi, tace "I hate you"


Kowa gurin saida ya dan girgiza da kalaman ta, sanan taci gaba da masa magana da turanci cewar "baka cikin tsarin mazajen da nake so, baka taba burge ni ba, karkaga ka waye, wly katon jahili na d'auke ka, bana sonka bana son ka na tsane ka. "

Subahanilillah wanan kalamai ba karamin girgiza Kumar yayi ba, ya taba zuciyar SΓ‘, fiya da tunanin ku, yayin da zuciyar sa ke barazanar bugawa, ya shiga rudu, ya kaskantar da kansa a gaban mutane ita kuma ta masa wulakanci shi Prince Kumar mace ta masa haka.


Kamrina na gama magana tabar gurin, da gudu tayi d'akin su tana zuwa ta zube bisa gado tana kuka, dan ita ko kadan bata iya wulakanci ba tayi haka ne dan ta rama, yaji mi ake ji In an wulakanta mutum a cikin mutane, duk da wai har yanzu bata jin son Kumar ko kadan.



Dayawa mutanen da suke wurin sun tausaya ma Kumar, wasu kuma yan matan dadi sukaji, suna Allah kara.



A ranar Kumar ya tisa keyar Princess dake kumbure kumbure suka bar kasar, zuciyar SΓ‘ na masa barazana kamar zata tarwatse. Ba karya duk wanan wulakancin da ta masa ko kadan baiji son ta ya ragu ba. .


Ashe haka ake ji idan anyima mutum wulakanci, a gaban mutane, saΓ­ yanzu yake da na sanin abinda yayi mΓ‘ Kamrina, Princess kam haushi take ji an raba ta da kawayen ta.




Kumar an tura Masu motocin da zasu tarbosu, jirgi na sauka aka d'auke su sai gida.







Aci gaba da gashi πŸ‡
Maimou LoveπŸ˜˜πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
*WACECE NI KAMRINA*
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€


.


*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAHI AM*πŸ’‹





_Sorry fans ina nan lfy lau wly, oga ne yazo banida kaina shi yasa, yau ma dan na dan samu sarari ne zan muku, karku ji shurun yayi yawa, nagode sosai da Kulawar ku Allah saka da Alherie_







*PAGE 59-60*












Sam Princesse ta kasa gane kan Kumar, har suka isa gida, harda mai Martaba Γ  masu tarbe da Hafsa da kilishi ,suna isowa aka tarbo su, ko wanen su murmushi d'auke Γ  fuskar sa,Kumar na fitowa ya rungume mahaifin sa, mai Martaba yace "Welcom son."


"Thanks dad"



Cewar Kumar, yaje ya rumgume Mahaifiyar sa ya gaida Kilishi da sauran mutanen, itama Princesse duk ta gagaishe su, yayin da kowa ke fairin ciki ana musu sanu da zuwa.



Direct b'angaren su aka musu da kayan su, bayan an shiga falo anyi gaishe gaishe, aka baje masu abinci kala kala Γ  saman dogon table din, kowa ya zauna nan kowa ya zauna harda su kilishi, da Hafsat da mai martaba ,tebur din mutum ishrin zai iya cin abinci Γ  sama, nan aka zauna ana ta ciye ciye cikin murna, Kumar duk ya raba hankalin sa biyu sai waige waige yake so yake yaga inda Kamrina zata bulo, me yasa ita bata zo cin abincin ba ,dan duk an taru, wata kila tana d'akin ta.

Zuciyar sa ke fada masa hakan .

Γ€ dadafe ya gama cin abincin, Dan ya matsu ya ganta, saboda ji yake yanzu zai zauna da ita ,tunda bai samu wacan ba .wani nishadi yake ji zaiga Kamrina sa, Dan Γ  yanzu zai nuna mata so.

Γ€ haka ya gama yace "Momy dad zanje na Dan huta."


" OK son"

Itama Princess bayan sa tabi.


.

Haka cikin tamaka yake takawa, har ya isa b'angaren su komai na nan ,saide yan gyare gyare da akayi, komai sabo Aka sa an kashe dukiya, domin komai da aka sa masu mugun tsada ne. Tunda ya shiga baiyi wata wata ba yayi b'angaren Kamrina anma saide mai b'angaren Γ  kule yake, mamaki ne ya kama sa, to ina ta tafi, ko ta fita ne, nan take ransa yayi mugun baci, ya ayana kawai fita ne Kamrina tayi ba tare da izinin sa ba, wani kishi ne yake jin yana taso masa, rai bace ya koma b'angaren sa ko takan Princesse baibi ba, domin haushin ta ma yake ji.

B'angaren Princess ma bata kula sa ba dan itama kanta hayaki yake.



Wasa wasa sai ga Prince yana Zagaye tsakanin d'akin sa da na Kamrina, Sam ya kasa samun nutsuwa, haka har dare, Γ  lokacin yasa kayan barcin sa masu sulbi, wondo dogo da doguwar riga, yayi matukar kyau duk wata kira tasa ta maza ta bayana ,kalo daya zaka masa ka tabatar da cikak'en namiji ne ,ya kara wani sihirin kyau, zuwa yanzu ya hasala rai ya baci, yana ayana rashin mutuncin da zai mata In ta dawo ,Γ  hankali ya huce b'angaren su Fulani, Γ  d'akin ta yayi salama fulani n'a waya saida ta gama tace "son lfy dai na ganka hakan ?


"wai Momy ina matata taje ne?

"Mata wace mata ?
Cewar Fulani.


"Mom Kamrina fa"

Ya fada a shagwabe .


"Mtsss, au ashe kanada wata mata ko, kaga ko na ma manta,


Tana can wajan dangin Baban ta ta tafi gurin su"
Cewar Fulani


😳waro idanu yayi yace "Mom da izinin wa taje nidai nasan ban bata izini ba, haka kawai abar yarinya ta tafi wani wuri ba tare da izini n'a ba, gaskiya à fada min garin da ta tafi naje n'a d'auko ta. "


Sake da baki Fulani tayi, sanan daga bisani tace "wly Son bakada kumya ko kadan, ni kake fada ma wanan maganganun, kake wani ce min matar ka, da kanada mata ne, ni ai Γ  iya sani n'a Fatima kadai ce matar ka, kuma matar so, tunda ka tafi ka taba kira kaji lfyr ta ne, ka taba mata aike ne, ka taba tambayar lfy ta, sai yanzu kazo kana ma mutane zancan banza ,kuma zancan cewa wai zakaje ka d'auko ta ban lamunce ba, kai bara kaji duk ranar da ka kara min Zancan dawowar ta sai n'a tsine ma dan haka zatayi iya zaman ta har lokacin da take so ta dawo Dan kanta. ,da baka san kanada mata ba sai yau."




. Ba karamin girgiza Kumar yayi ba da kalaman Mahaifiyar sa,kusan duk wani sasa n'a jikin sa daina aiki yayi n'a dan wucin gadi,


Anya Γ  yanzu zai iya rayuwa ba Kamrina, wayo Allah Fulani zata kashe sa.


Sosai ya jima zaune cikin wanan hali sai daga bisani ya tashi ya tafi jiki Γ  mace.

Fulani tayi tsaki tace "shasha kawai..




Γ€ ranar haka Kumar ya kwona yana sake sake Γ  ransa.....




Kamrina tunda Kumar ya tafi sai taji kuma ba dadi, anma ana kowna biyu ta warware taci gaba da harkokin ta maida hankali akan karatun ta.





*bayan shekaru biyar*



Γ€ yau ne su Kamrina aka rantsar dasu, sun zama kworaru, doctor, wanda kuma ake ji dasu Γ  kasar, ayau akayi taron yayin da Fulani da Momy suka halaci taron, Kamrina kaf cikin class dinsu itace ta farko tafi kowa sakomoko mai kyau, yayin da k'asar taso ta rike ta, ta dinga masu aiki tace Γ 'a kasar ta zata koma, domin ko lokacin tana karatu asibiti daban akan kira ta, in abun ya shige masu duhu, da ikon Allah sai aci nasara, hakan yasa tayi suna fiye da zaton ku. Anyi taro, mutane Sun halarta sosai, aka ba su Kamrina diplΓ΄me dinsu, cike da Murna Kamrina take takon ta mai d'aukan hankali idan kukaga yanda Kamrina ta koma zakuyi zaton bata taba furta kalmar hausa Γ  bakin ta ba

Fatar ta tayi wani bala'in yin fresh, ta kara haske, yayin da boobs dinta suka kara cika pum ya zasu futo cikin rigar, hips kam ba'a magana, Dan ya kara cikowa sosai, in tana tafiya ya tana juya su, yanda suke rawa ta kara tsawo, uwa uba waye wa ilimi kam ko baturen sai ta kure.


Γ€ haka ta iso ta rungume Momy, da Fulani, tana murnar ganin su, daga Momy har Fulani sakin baki sukayi suna kalon halitar Allah.


Γ€ hankali cikin muryar ta mai dadi tace "Momy shine ba'a zo min da Dana ba Abdoul Malik, dan wajen Suraya ne da ta haifa, tunda Aka haife sa ya fara wayo ko yaushe sai sunyi vidΓ©o cal da Kamrina yana mata gworancin sa kasancewar ta mai matukar Son yara sosai sai ta biye masa, kulum sai yace mata Anty yaushe zaki zo tace ina nan zuwa mai boy.



Sun shaku sosai.

Momy tace "auta kece kika koma haka, saida mukayi da gaske kafin mu gane ki."

Dariya Kamrina tayi ta kali Fulani tace "wai Mama."


Murmushi Fulani tayi tace " kyale ta diya ta, nikam komin sakewar bazan kasa gane ya ta ba ai."

Dariya sukayi duka, to mu tafi dan gobe in Allah ya kaimu zamu dunguma sai gida ,jikin Kamrina ya Dan yi sanyi anma ba yanda ta iya.


Γ€ haka taje tayi salama da yan class din su da sauran mutane abokan arziki, kowa yaji ba dadi.

Washe gari k'arfe takwos su Kamrina n'a filin jirgin Singapore, yayin da Fulani ke waya da mai Martaba take shaida masa zasu taso, ya masu fatan Allah kawo su lfy.



Kumar ne ya shigo fada, duk ya rame ya lalace,saide kyan sa na nan, Γ  zuwa yanzu Son matar sa Kamrina ke wahalar dashi, yasha kwonciya asibiti, Γ  yanzu haka yanada hawan Jini.

Gaida Sarki yayi, mai martaba ya amsa Γ§ikin kulawa, yace "ya jikin naka,wai Son mai ke damun ka ne ?


"Dad matata nake so Γ  maido min ka taimaka kasa baki Mom ta maido min mata ta ,wly in ba ita zan iya mutuwa."


. " Subahani lillah cewar Mai Martaba, karka damu son ka shirya k'arfe daya kuje ku d'auko Mahaifiyar ka da baki, insha Allah zan mata magana kuma matar ka zata dawo kaji ."


Wani farin ciki ne ya mamaye zuciyar Kumar Wanda ya jima baiyi ba.







Kuyi hakuri da typing Eror








Aci Gaga da gashi πŸ‡
Maimou Love πŸ˜˜πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
*WACECE NI KAMRINA*
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€






*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*πŸ’‹






*yar daki na my Fatima Kelu ,ke din ta daban ce wly banida bakin yi miki godiya saide nace Allah bar zumunci, ya barmin ke yar Daki na, dan Haka wanan page din baki dayan sa naki ne kiyi yanda kike so dashi*😍😍😍😍😘






*Ina kike my Halissa (Lissa) hakika kinyi kokari, ina mai matukar tayaki murnar kamala litafin ki Haneefa, ubangiji Allah yasa muyi aiki da darasin dake ciki ke kuma Allah biya ki, kuskuren dake ciki Allah yafe miki up up litafi yayi ba karya wly Allah kara suburbudo basira*....








*PAGE 61-62*







Tunda mai Martaba yace ma Kumar cewar Matar sa zata dawo yake cikin farin ciki, take yasa Γ  gyara masa gidan sa da ya gina katoton gidan ne na gani n'a fada, anma ba cikin fada yake ba.


Koda Prince Kumar yayi b'angaren sa a farin ciki yake, Princesse ce zaune Γ  falo, duk tayi kiba ta zama wata katuwa da ita, sai ya zamana wanan kyau da take da duk ya tafi, ko kadan kibar bata mata kyau ba, yayin da shi kuma Kumar yaji duk ya tsani wanan kibar da tayi, Dan gaskiya Γ  yanzu har kumyar Γ ce matar sa ce yake .
Gashi ta raina sa sosai.

Haihuwa yake so anma Sam Ita Princess bata so Dan haka
Ne ma take shan maganin hana d'aukan ciki .
Γ€ cewar ta bata so ta tsufa, niko nace Princesse ai ko yanzu ma sai Γ  slow irin wanan kiba haka Hum.

Gashi har yanzu maneji kawai yake da ita baya wani jin dadin ta, yayin da ita kuma sam ta kasa ganewa ta gyara kanta, hakanan take salaba ta.


Da salama ya shigo falon nata fuska d'auke da murmushi ,ya zauna kusa da ita yace "Madame sanu da hutu. "


Mamakin farin cikin sa Princess take yi anma kuma sai ta bazar dan yanzu ko kadan basa shiri, yanzu zasu fara maganar arziki sai ta juye ta zama ta tsiya.



Nan dai suka zauna kamar kurame, shiko Kumar daga ya tuno maganar Mahaifin sa sai yayi murmushi ,itadai kalon sa kawai take.
Yana yi yana duba agogo dan ya matsu Mahaifiyar sa tazo Γ  tafi Γ  kawo masa matar sa.
Da sauran awa daya ya tashi yayi wanka ya shirya cikin manyan kaya,na wani danyan yadi fari mai kyau da tsada dinkin yayi bala'in yi masa kyau yasa wani mayan agogo, sumar kansa ta kwonta luf kamar wani balarabe, ya gaira sajen sa,kai gaskiya ya hadu iya haduwa, ya fesa turaren sa mai sanyin dadi. Ya fito cikin takon sa mai kayatar wa, Γ  lokacin Princesse ta tashi, daga gurin da take ta shiga d'akin ta, yana fitowa yama gard dinsa signe, suka fido motoci guda takwos ,hudu farare jip manya, hudu bakake suma manya masu tsada.
. Haka suka jera yayin da fara ke gaba baka na bi mata haka aka tsara motocin, kana ganin su kasan motoci sun hadu iya haduwa.a ta tsaka Kumar ya shiga Γ  lokacin saura minti goma sha biyar jirgi ya sauka.



Suna isa jirgi da minti biyar ya sauka Prince n'a mota yana jira yana duba agogo, yayin da yake jin gaban sa na faduwa.

Ana haka jirgi ya iso Γ  kan idon Kumar kur yayi yana kalon jirgin har ya sauka Γ  hankali.


Yana gama sauka kumar ya iso ya tsaya yayin da ya maida hanuwan sa bayan sa .

Γ€ hankali k'ofar jirgi ya bud'e mutane suka fara fitowa, duk akan idon Kumar sai ga Fulani da kuma Momy suma sun fito

Please Login or Register in order to submit comment