Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Princesse suke ba, dan yawancin su tantama suke anya Kamrina ba Aljanna bace.



Prince Kumar kam har yanzu tsaye yake, idanun sa sun kasa manta abinda suka gani, yayin da suke muradin sake tozali da halitar da ta rikita su, gangar jikin sa tayi bulaguro, yayin da zuciya ke bugawa, baki ya kasa furta komai, idanun sa kyam akan inda Kamrina ta tsaya,Fulani ko dariya tayi dan tasan Γ  rina, yayin da ita kanta dauriya take dan a yau kyan Kamrina ya kara ruda ta da bata tsoro ,tana kwonkon to anya kawar ta ba tq boye mata wani abu ba, saurin kawar da zargin tayi, da ta tuna Momy tace mata yarinyar da uwar ta tayi kama....



Ruwa aka yayafa ma Princesse tifa, firgit ta farka, ta kali mahaifiyar ta, sanan ta fara zare idanu, "ina wly karya ne babu wada ta isa taci gasar nan sai ni kowa yasan cewa nice mai kyau, wly ko aljanna Ce wanan wada n'a gani nafi karfin ta, ni Princesse Tifa babu wada ta isa ta kwoce k'ofin zinari da na Diamond daga hanu na. "duk tabi ta zare, Kamrina kam n'a gamawa ta koma da tafiyar. Ta nutsuwa, tana shigowa d'akin da aka basu kafin alkalai su gama rubuce rubucen su su yanke hukunci, Suraya ta Rumgume ta sosai, tana murna tace "wayo dadi kanwata yau kin gama min komai wly, kin kawo k'arshen takama da d'aukan kai. "


Kamrina tace" wai dan Allah anty wane irin kyau ne dani da mutane ke somewa suna sufanta ni da Aljana.?

Murmushi Suraya tayi, sanan ta talabo habar Kamrina tace" kanwata kinada baiwar komai Allah ya baki, babu Inda ya rage Γ  jikin ki, kyan ki duk yanda mutum ya kure kalon ki dan ya hango wata makusa bazaka samu ba ki godewa Allah, mai maganar nan ne ya katse musu fira, yayin da ya bukaci duk wanda suka zo gasar su fito dukan su,kamar farko haka suka jero suka taho har kan Princesse wada dakyar mahaifiyar ta da rabi suka lalabo ta ta taho....
Daga ita sai kamrina Princesse ta jima tana kalon Kamrina cike da bakin ciki da takaicin wanda ya barta ta zauna masu gari, ba karya ko makiyin Allah yayi kadan ya kushe Kamrina, ashe ita batada ma kyau ga Inda kyau yake, anya ba Aljana bace kuwaπŸ€”tana wanan tunani Kamrina ta karaso kusa da ita, dayawa mutane har kara gwole idanu suke sudai su kara kalon Kamrina, yayin da matasa har magidan ta yayan masu kudi da masu kudi, kai harda sarakuna ke burin malakar Kamrina, babu wanda ya kara bin takan Kamrina kowa burin sa Kamrina ta zama tasa .....


Mai gabatar da taro ne ya fara magana, yana masha Allah "Γ  gaskiya yau munsha mamaki, kusan shekaru goma Princesse fatima ita keci anma yau abin yazo da sauyi, yan mata ko wace ta rufe Ido masu addou'a nayi,masu tsafi nayi, nan yace "Alkalai sun yanke hukunci, dan haka gworzuwar wanan shekara ba kowa bace ila Kamrina. "

Wanan karon kam Princesse tifa ya tayi hauka, yayin da wuri ya kaure da ihu, yan matan da suka zo gasar ko basuyi wani bakin ciki sosai ba sauran cikin su ma murna sukayi n'a ganin k'ofi ya fito daga hanun Princesse ba, dan karamin hauka Princesse tayi ba tabar wurin dan ko tsayawa gamawa ba'ayi ba dayawan maza dariya suke mata dan sunsha kai rokon soyayar ta tana masu wulakanci, da gudu taje ta shiga mota tabar wurin Γ  haukace yayin da Momyn ta ta bita da kuyangi, mai martaba ma ta maza yayi dan kar ace yayi shirme ko yabi bayan yar sa, anma da yaje ya lalabi yar tilon Yar sa .

Kumar kam bai ma san Princesse ta bar wurin ba, K'ofin aka ba Kamrina, ta daga akayi photos, sanan aka Bata millions ashrin, tare da kyaututuka, mayan masu kudi da matasa, sarakuna duk sunzo sun mika mata kyaututu ka, yawanci su kudi ne, Γ  takaice dai ko nan ta tashi da million talatin, Γ  yayin da akayita pic , anyi ta neman Princesse Γ  bata nata don tazo ta biyu tanada naira millions goma, sai dan kofin azurfa nata, aka ba yan yan uwan ta su tafi mata dashi, su kansu Alkalai sun sha pic da Kamrina, yayin da Fulani taja hanun Prince kumar wanda ya zama kamar sakarai, Momy ma Jan Umar sanda tayi sukace to muje muma mu bada tamu gudunmuwar, sai Γ  sanan Prince Kumar ya samu bakin magana yace "Fulani mu kuma meye hadin mu da ita ? cewar Kumar

Murmushi Fulani tayi tace " ai kanwar ku Ce wada taci gasar ya ga aminiya ta kuma kanwa ga abokin ka Umar.
Wata irin firgita kumar yayi ya kali Umar Anma ya kasa magana bakin sa na rawa.

Murmushi Umar yayi yace "magana mai tsawo muje In aka gama zan fada maka komai. "


Haka nan Umar yaja kumar kamar soko sukaje wurin,dan su fulani har sun karasa, Fulani kyautar one million tayi ma Kamrina, Momy kam kyautar sarkar gold tayi ma Kamrina, ,,,,,,,,,,,,,,,,,,,
Prince Kumar na zuwa gap da Kamrina numfashin sa ya kusan d'aukewa, zuba mata ido yayi ko kyaftawa babu, Kamrina n'a ganin sa ta gane sa, ta basar dan har yau tana jin haushin abinda ya mata
......





Princesse tifa ikon Allah kawai ya kaita gida, dan wani mahaukacin gudu ta dinga yi,tana zuwa gida motar ma ko rufewa batayi ba, ta fito tabar key Γ  motar. Da gudu tayi d'akin ta, ta rufe komai ta samu jefar wa take Γ  kasa, tazama ya mahaukaciya,,,,,
Maman ta ma da rabi suka karaso bugun duniya Princesse taki budewa, dak'yar Rabi tasha kanta da kalaman ta na zuga da munafurci........



Tana budewa Rabi ta shigo da Maman ta, kaf ta farfashe kayan d'akin ta hargitsa d'akin, idanun ta duk sunyi ja ta fita daga hayacin ta.

Rabi tace "haba uwar d'aki na, meye na ki tada hankalin ki keda kowa yasan shekara da shekaru kina cin gasar meye Dan wata aljana tayi tsubun ta taci, dama kinsan boka yace wanan karon akoi matsala kije anma baki Je ba, nasan wanan aljana ce dan mutum ai karya ne yayi karo dake. "


Sai yanzu zuciyar Princesse ta dan sauko nan ko suka ci gaba da tusa mata mugayen sharwarwari Γ  kanta....


Maman ta tace "to Princesse yanzu abinda ya kamata muyi ayi kowa ya huta tun kafin shima ya juya baya wato Prince Kumar, kinsan irin wulakancin da kika sha masa yanzu lalaba sa zakiyi ayi auren daga nan sai mu fara gudanar da plan din mu, ki shirya, in anjima ke rabi sai muje gabadaya wurin boka domin abin sai anyi sa da zafi zafi, dan dole sai mun kai Kumar wurin boka domin ya kama mana shi.........







Aci gaba da gashiπŸ‡
Maimou LoveπŸ˜˜πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
*WACECE NI KAMRINA*
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€










*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*πŸ’‹










✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
πŸ’«
*🌟🌟TAURARI WRITERS ASSOCIATION*.................✍
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨








_To fans naji batun ku kuma na aminta da yardar Allah In ba wani baban Uzuri ne dani ba to zan dinga yi muku kulum nagode, inajin dadin comment din ku😍_










*PAGE 25-26*







Sosai kamrina ta samu k'yaututuka, Fulani kam jirgi suka bi, suka koma kasar su,yayin da Prince Kumar yaki tafiya, Γ  cewar sa sai ya lalaba Princesse Tifa anma ba hakan ba ne Γ  zuciyar sa..


Momy da Kamrina tare akaje gida cike da farin ciki ,yayin da wasu sukayi ta neman su sumu kebewa da Kamrina, Anma basu samu wanan dama ba, saide dayawa wasu sunbi su Kamrina har gidan dan susan Inda take, yayin da wasu suka aika yaran su dan suga gidan..... ........ .......

Bayan su Kamrina anje gida kowa yaje yayi sallah magarib harda Prince da Umar dan ya matsu yaji meye alakar su da wanan kyakyawar halitar.

Kamrina suna Salah sai bayan isha'i Suraya tace "Sis In kin gama kizo diner muci abinci. "kada kai kawai Kamrina tayi ta shiga tsoilette, tayi wanka ta dawo tasa wata doguwar riga marar nauhi sam ta kasa kama gashin dan ya kara santsi da sulbi ga yawa ko kadan ta kasa tufke sa, ga Suraya Bata nan, sakin sa tayi, har yana taba cinyoyin ta, fuska Γ  shagwobe ta fito, tayo falon su Momy suna jiran ta a diner kowa ya taru anma banda Dady dan yabar kasar,Kumar ma yana zaune cikin su ana dan fira, Momy tace "Suraya kije ki kara kiran Kamrina, tazo muci abinci, ana ta jiran ta kar aje gajiya ta hana ta Momy bata gama zancan ba sai ga Kamrina tana turo baki irin n'a shagwaba nan gashin a sake dan in har ta Dan duka to zai iya tabo kasa. tunda tayi Salama Kumar ya ganta yayi mutuwar zaune sake da baki, gabadaya ya fido idanuwan sa, acikin zuciyar sa addou'a yake dan neman tsari dan wanan yarinya Aljana tayi kama bada mutum ba, Momy ce ta dawo dashi daga tunani sa tace auta meye ya same min ke.? Ta tambayi Kamrina duk ta dan nuna damuwa har ga Allah ba karamin Son Kamrina take ba,,,,,,, zuwa Kamrina tayi ta aza kanta bisa kafadar Momy,


Momy ta dan shafa kan Kamrina tace "Auta meye ?
Dan haka Momy ke kiran Kamrina.
"uhum Momy nidai a fida min gashi nan ya ishe ni gaskiya yanzu gashi na kasa tufke sa πŸ˜”"

Ido Kumar ya kara fidowa, cikin ransa yace wai da gaske dama gashin ta ne,wanan shagwobar da ta kara narkar da zuciyar kumar, har yaji dama Γ  jikin sa take wanan shagwobar, dan bakin ta yaji kamar yaje ya tsotse sa, dakyar kumar ya iya cin abincin.

Momy tace "auta yi hakuri zauna muci abinci sai mu tufke miki."zama tayi kowa Suraya zuba masa sanan aka fara ci, Kumar ko sai satar kalon Kamrina yake dan cin abincin ta ma burge shi yake ,kawai ita yake kalo, su kansu Momy sun lura har abokin sa Umar.....


Bayan an gama cin abinci, umar yace "autar Mama congratulation. "


"Ni nayi fushi yaya πŸ˜™"


Umar ya fido ido yace "lala kanwata me nayi ?

To yaya Ai banga naka kyautar ba. "

Dariya aka d'auka Momy tace "kworai aba auta ta.


Dariya yayi yace "kanwata karki damu tawa kyautar tana bisa hanya ."


"nagode Yaya cewar Kamrina.


Dakyar Umar yaja Kumar daga faFalon lon suka koma d'akin Umar, Kumar yace " dan Allah ka fada min alakar ka da wanan yarinyar mai kyau, dan naga sai wani ja min aji kake, kai ba mace ba. "




Su Mama duhu nayi taja rabi da Princesse tifa sukayi wurin boka, suna zuwa ya kece da dariya nasan za'a rina saida nace tazo aikin sai tazo anma ta kawo taurin kai, yarinya mu a aikin mu ba'a tsalake maganar mu in ko aka tsalake to tabas sai an samu matsala. "



Wani haushin sa Princess taji, zata masa rashin mutumci mahaifiyar ta ta girgiza mata kai ,shiru tayi anma zuciyar ta na tafarfasa, boka yace yanzu mai kuke bukata, ?


Maman tace "boka so muke shi wanan yaron dan sarkin kasar Rajugur,, muna so akara sa masa Son Princess yanda bazai so wata ya mace ba sama da diya ta. "


Wata muguwar dariya boka ya kece da ita yace an gama. Anan dai yayi yan surkulan sa yace su tafi aiki ya kamala.......
Washe gari

Momy ce ke waya ita da Fulani, tace "saratu nifa n'a fada ma mai martaba, dan na samo ma da na mata ta biyu kuma har n'a fada ma mai martaba kuma ya yarda ,cikin matukar farin ciki Momy
Tace "wacece wanan. "

Murmushi Fulani tayi tace " ya ta Kamrina mana.........



Kuyi hakuri yau bana jin dadin jiki na shi yasa zaku ga typing kadan.

















Aci gaba da GashiπŸ‡
Maimou LoveπŸ˜˜πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
*WACECE NI KAMRINA*
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€










*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*πŸ’‹










✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
πŸ’«
*🌟🌟TAURARI WRITERS ASSOCIATION*.................✍
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨








_haba dan Allah gaskiya Allah na gaji, dan ina typing ina turowa kulum, anma mutum bai karantawa sai daga baya ana biyo ni ta pc ace daga farko saboda Allah wanan ai da wahala, wly wly Γ  rana zan tura ma mutum sama da talatin kuma kulum sai an tambaye ni, saboda Allah da wane zanji da rubutun, ko da turawa kulum ta pc, akoi mutane diyawa masu shi ta groupe me yasa in an tambaya bazaku turo ba, Γ  gaskiya n'a gaji in aka ci gaba da matsa min zan daina typing din gaba daya n'a huta ma raina, wani in zaice ma ka basa da gadara zai tambaye ka, sai kace shi ke saya maka data turowa, saboda Allah mutum n'a Son abu bazai tambaye ka cikin karamci da mutumci saidai kiji Γ nce turo min kaza daga farko, wata ba ma salama, tabas ina Son masoya na anma gaskiya zan iya hakura dayin rubutun ma baki daya na huta, kuyi hakuri in kunga Ban tura ba dan Ni kadai nasan wahalar da nake sha, sanan kuyi hakuri in na Bata muku πŸ™_





Alhamdulillah jiki na da sauki sosai yanzu kam, nagode da Addou'a kuπŸ˜πŸ™













*PAGE 27-28*







Sosai Momy taji dadin wanan batun, murmushi ta Wanda ya fito har cikin wayar da suke sanan Momy tace Alhamdullilah, Allah abin godiya gaskiya nayi farin ciki da wanan maganar insha Allah ba matsala Allah tabatar mana da Alherie.

Ameen Fulani tace suka dan Tatauna daga bisani sukayi salama.


Numfasawa Momy tayi saide fargabar ta daya kar Γ  gano abinda suke boyo game da Kamrina.....


Anma in bayan haka sosai take murna da wanan hadin.......


Bayan Umar ya gama fada ma Prince kumar cewa yar uwar sa ce kamrina kamar yanda
Momy tace ya fada duk wanda ya tambaye sa alakar sa da Kamrina cewar yar uwar sa ce .




Nisawa Kumar yayi, yayin da yake tuna yanayin yanda take shagwaba
Ta gashin ta ya tuna so yake ya samu yanda da zaiyi ya taba gashin nan ya tabatar tukon. Dan har yanzu bai yarda da wanan uban gashin da ya gani ba.



Sake sake ya fara, yayin da zuciyar sa take jin wani bakon Al'amari game da Kamrina.......


Dadare, Umar baya nan ya tafi wurin budurwar sa da ta kawo ma antyn ta ziyara, yayin da Yazeed yazo hira gun Suraya suna falon baki suna tadi, wata dubara ta fado ma kumar, dan haka ya d'auki waya dake d'akin yayi kiran Momy, tana zaune tana harkar computer n'a harkar kasuwancin ta taga kiran wayar kumar, ta d'auka, tace "Son ya akayi ne me kake bukata,?
Dan sosa kai Kumar yayi kamar yana gaban Momy tana ganin sa, yace "Momy tea nake so wly. "


"OK to bari n'a turo auta ta kawo maka, tunda Suraya Bata kusa.

,

Wani mugun dadi Kumar yaji ya ziyarce sa,yace"thanks Mom .


"ok bye cewar Momy ta aje waya ta kira kamrina tace takaima yayan ta tea.

Ko kadan Kamrina Bata kawo komai ba tace to .dan Γ  tunanin ta Umar ne.....


Cikin kayan barcin ta riga da wondo, masu kauri ne, dan basu nuna tsiraici ba, saide sunyi bala'in yi mata kyau, kanta ta tufke shi da ribom ja, wanda anmi ne suka tufke mata shi, yayin aka sake sa daga baya yana reto, Γ  haka dan ta saba bata sa dankwoli ba Momy har ta gaji da fada, to ta saba, cewa take in tasa zafi take ji, haka ko ta fito da tea bisa plat, ta nufi b'angaren Su Umar da Salama ta shiga falon ba kowa, hucewa d'akin tayi, da salama ta shiga gogan na dana wayar sa kansa Γ  duke yayi kamar bai jita ba, itako ganin sa taji wani kutu ya turnike ta, k'wofa tayi ta aje tea din saman table din , cikin ko in kula kamar mai ciwon baki tace "ga tea din Yaya nan"
Ajewa tayi zata juya taji ance"ke"
Gaban ta ya fadi taji sarai da ita yake taki waiwayo wa, ganin yayi bazata tsaya ba hakan yasa yayi wani kukan kura ya cakumo ta, saida ta tsorata, gashin ta ya ruko dama abinda yake so kenan, ya hade ta da bango, yace "ke kin raina ni ko, tun dazu nake ganin take taken ki. "


Cikin bacin rai Kamrina ta kale sa tace "Kai malam lfy me na maka, nasan ka ne, ko ko dole sai na kula ka ne, meye hadi na dakai. "


Sosai Kumar yaji takaicin zancan ta, kuma yaji haushin kansa, meye nasa na wani matsa yarinyar mutane, meye hadin sa da ita, wanan ai salon ya jama kansa raini ne, gashin ta ya kara damkowa, duk da sulbin dake jan hanun sa, ya tabatar tabas gashin nata ne,aje mamakin sa yayi Γ  gefe. Yace " kin isa naso maganar ki ne, ke din banza, mai zan so anan, ko dan kina ganin kinci gasa,to nayi haka ne ganin hararan da kike min, meye tsakani n'a dake kamar ni ki nemi raina min hankali.


Tsawa ta daka masa dan zuwa yanzu ranta ya gama baci sosai, cikin masifa ta fara masa bala'i, "kai malam wai meye hadi na dakai zaka takurawa rayuwΓ  ta fada sosai take, anma sam Kumar ya tafi wata duniya yanda yaga tana motsa karamin bakin ta, ga wani kamshi da bakin keyi daga ciki
Kasa d'aurewa yayi baisan lokacin da ya hade bakin su wuri daya , take Kamrina ta fara yawo da idanu gashi ya ririke ta, sosai yake aika mata wani mayunwacin kiss mai tafiyar da ita, ya fita hayacin sa, wani karfi ne yazo mata, ta tura sa, da gudu tabar d'akin, ranta yayi mugun baci, gata ba mai saurin kuka ba, da ta samu kukan to da taji dadi........


Shiko Kumar wani kayatacen murmushi yayi, ransa fes ko ba komai ya bata mata ,anma wani irin yanayi yake ji game da ita, gashi jikin sa ya mutu ranar haka ya kwona ya rasa farin ciki yake ko akasin hakan.........


Yayin da Kamrina ta kwona cikin kunci da kara tsanar Kumar '...
........




Da safe, wajen k'arfe goma n'a safe, motar Princess tifa ce ta shigo gidan, yau ita kadai ke tukin sai murmushi, take dan wanan zuwan n'a musanman ne tayi ma Kumar ,Bata taba iske sa ba saide shi ya Je Inda take.........

Cikin kasaita ta fito, sanye da doguwar riga ta shada ja, tasa alkaiba, tayi kyau sosai, an zubo gashi baya.....


Direct cikin baban falo tayo duka suna zaune Momy kadai ce bata nan dan ta fita. Su uku ne Suraya Kumar Umar, yayin da Kamrina take D'akin Momy tana gyara mata d'aki.


Cikin takun kasaita ta shigo falon tana taunar shuingwom tana wani yauki, Suraya ta fara ganin ta anma bata mata magana ba, "Hi Princess tace dasu, Umar ne yayi dan murmushi yace "Γ  amaryar mu yau kece Γ  gidan mu, lalai yau sai anyi ruwa da kankara Γ  gidan nan . "

Dago da kai Kumar yayi jin wada ta shigo, ita kuma Princesse daidai ta fida katon bakin gilashin da tasa Γ  idanun ta, ta sauke idanun ta cikin n'a kumar, sukayi ido hudu, wani abu ne ya shiga idanun sa, wanda shi kadai yagani gani........... Take wani irin mahaukacin Sonta ya kara shigar sa daidai saukowar Kamrina, da idanun ta suka canza kala jin ana shirin yin cuta, wani abu kamar wuta wuta ya fara fitowa daga idanun ta








Aci gaba da gashi πŸ‡
Maimou LoveπŸ˜˜πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
*WACECE NI KAMRINA*
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€










*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAHI AM*πŸ’‹










✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
πŸ’«
*🌟🌟TAURARI WRITERS ASSOCIATION*.................✍
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨












*PAGE 29-30*







Γ€ hankali Kamrina take takowa, da duk tsigar jikin ta ke tashi, Kumar kam tuni Son Princess ya kara mamaye sa.

Ganin tayi nasara yasa tayi murmushi ta maida katon gilashin ta, ta juya zata fita, suka hada ido da Kamrina, ita kadai taga wutar dake fitowa daga idanun Kamrina, "ke"Princess ta nuna ta yayin da bakin ta ke i ina, wata dariya Kamrina tayi, sanan ta shake wuyan Princesse tace ina wuri kikayi cuta, ke kin isa, sosai Kamrina ta shake ta, yayin da Kumar da Umar suka taso agaji, Suraya kam dariya take dan Kamrina tayi mata daidai........

Wani wawan mari ne Kumar ya zabga ma Kamrina wanda saida taga stars, take ta dawo hayacin ta ta saki Princesse takai duban ta ga Kumar, ta kale sa rai a matukar bace, tace "kai kai ka mare ni, kai dan gidan uban waye, wa ya baka incin Mari na, saboda wanan munafukar zaka mare ni, to kaje na barka da ita tayi maka duk abinda zatayi, ke kuma ta juya kalon ta ga Princesse da idanun ta suka rikide, sukayi ja na wahala tana murza wuya, sanan Kamrina taci gaba da cewa, kika kuskura kika nemi cutar da Family dina wly ko mahaifin ki bai isa ya ceceki ba, dan haka kije duk abinda zaki ma wanan ta nuna Kumar, ki masa, ki kama hanya kibar gidan nan ko ki jasa ku tafi .."
Ran Kumar yayi matukar baci, na ganin Kamrina na masu wulakanci shida abar sonshi, anma dan uwan ta ya kasa magana ga zagin da ta masa wanda tunda uwar sa ta haife sa ba'a taba masa irin wanan zagin ba,tsanar ta ya sake maimaye sa a dukan zuciyar sa ....

Jan Princesse Kumar yayi wani mugun kalo Kumar ya jefa ma Umar yace "anma wly ka bani mamaki, ace kana ganin Yar uwar ka zata ilata min mata to bari kuji wly babu wanda ya isa ya taba min mata matsawar ina raye

."


Yana gama fadar haka ya ja Princesse suka bar gidan baki daya.


Umar ransa Γ  bace ya juyo kan Kamrina yace "auta me yasa kikayi haka me ta miki. "


Zumburo baki Kamrina tayi tace "yaya ku bakun ga abinda n'a gani ba, nifa rainon Apou ce nakan ji ajiki na In har za'ayi cuta, dan haka wanan matar abinda tazo kenan anma na gode Allah da baku tazo cuta ba. ... Tana gama fadar haka ta koma b'angaren su.


Ajiyar zuciya Suraya da Umar sukayi, Umar yace da Surayae"anya wanan yarinyar batada Aljanu ko ?


Dariya Suraya tayi tace " to yaya wa ya sani............. "



Tunda Princesse suka Je Gidan su ita da Kumar lalaba ta yake yana bata hakuri tare da lalaba ta da kalamai masu dadi.


Tabas Princesse

Please Login or Register in order to submit comment