Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hutu ya kwonta kyakyawa tace"johnne wai lfy inata magana kayi shiru? . "
Numfashin ta ne ya kusan d'aukewa sakamokon ganin k'yakyawar fuska wada kyan ta ya razana ta ita da johnne da gard din da suke wurin.

.

Itako Kamrina da yake tana da dakakiyar zuciya ko gezo bata yi ba ,saima goshin ta da ya fashe Yake zubar jini, da gwiwar hanun ta, dakyar yarinyar ta Samu addou'a tayi sanan ta kama Kamrina tasa ta a mota, privet asibiti nasu sukayi da ita, Yar budurwar duk tsoro ya kama ta, mursmushi Kamrina tayi da taga yanayin yarinyar cike da tsoro tace cikin voice dinta mai dadin sauraro tace"kwontar da hankalin ki ni mutum ce ba kamar yanda kuke tunani ba. "
Nauyayar ajiyar zuciya ,wanan budurwar tayi har asibiti aka kaita doctor yayi mata komai duk da a tsorace yake yin abun, dan kyan yarinyar tsoro Yake basa.


Haka yarinyar suka d'auke ta ,a cikin motar suka tafi da Kamrina, wai wacece wanan budurwar, ba kowa bace ila *Suraya*
Yar tsohon shugaban kasa, kawar Princess tifa ada, juyowa tace" ni sunana Surraya, ke kuma fΓ£ ."

Murmushi Kamrina tayi tace "sunan ki akoi dadi ni sunana Kamrina."
Waw Nice Name."
Kalon ta Kamrina tayi dan bata san abinda tace ba, can Suraya tace "gaskiya kanwata Ban taba ganin mai kyau irin ki ba fΓ£. "
Dariya kawai Kamrina tayi.
"ehee kanwata ina ne gidan ku saΓ­ sanan Kamrina ta nisa, tace banida gida. "
"ban gane ba"
Cewar Suraya.

Nan Kamrina ta fada ma Suraya duka tarihin ta, sosai Suraya ta tausaya mata, tace "sis ki d'auke ni a matsayin yar uwar ki ta jini zaki CI gaba da Rayuwa da Family na, daga yau ki dauke ni yayar ki.

Murmushi Kamrina tayi tana godiya , ita ko Suraya ta rungume ta, tana mai jin kaunar ta a ranta kamar yar uwar ta...........✍






Aci gaba da gashiπŸ‡
Maimou LoveπŸ˜˜πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
*WACECE NI KAMRINA*
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€






*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*πŸ’‹




✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
πŸ’«
*🌟🌟TAURARI WRITERS ASSOCIATION*............✍
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨







*PAGE 9-10*






A haka su kamrina suka isa wani tsalelen gida,fΓ£dar tsaruwar sa bata lokaci ne, gidan ya hadu ba kadan ba, ko da wasa Suraya batayi gigin nuna Kamrina ga Momyn ta ba, domin ita mata ce da batada kirki, sanan gata da jin haushin Ace dan wani yafi danta halita mai kyau da dai sauran su, sam ita bata ma son talaka ne, hakan yasa Suraya tabi da Kamrina ta kofar baya, inda daga nan har dakin ta, dan tasan matsawar tabi da ita ta falo to Momyn ta zata ganta.


Tana kaita daikin ta ya tsaru, komai coulour pink ne, saboda ta kasance mace mai son kalar, ko fadar haduwar tsarin dakin ta kauyanci ne, b'angaren ta kamar na amarya, falo da ciki, tunda suka shigo Kamrina ta kali gidan sau daya bata kara ba, anma kuma abun mamaki, babu wani nuna kauyanci da tayi.


Ita kanta Suraya tayi mamakin ta, domin a yanda ta bata labarin ta ai ya kamata har gidan nasu ya ma bata tsoro, anma mamakin shine har suka shiga d'akin ta ba alamun kauyanci, ta dai yi dan kale kalen ta, sanan tace "d'akin ki yana da kyau sosai 😍


"Allah ko cewar Suraya sanan tace nagode. Nan Suraya ta shigo da abinci da sauran kaya motsa baki, sam bata bar yan aiki sun sigo Dakin ba, daga falo tace su aje. ....... .
Kamrina kam taci abinci sosai dan bata taba cin irin SΓ‘ ba......




Wani gaye ne kyakyawa, wanda fadar kyan SΓ‘ hum sai wanda ya gani, kwonce yake bisa tsalelen gadon SΓ‘ da yasha ado hum daga kaga wanan saurayi ya tara abu hudu, kyau mulki , hutu, kudi ,fari ne dogo mai matukar kyau, da cikar halita ,,,,,, ,,,,, , ,,,,,,
Namiji har na miji wato Prince kumar kenan, Umar ne ya dan doke SΓ‘ yace "kai wai lfy ina maka magana ka shiga tunani."

"hum wly bari aboki na, wai kasan cewa Princess tifa muna daΓ­ tare ne da sunan soyaya, anma ba ko daya cikin zuciya na, a yanda ake cewa soyaya ni ba hakan nake ji a zuciya na ba, nasan daΓ­ tana burge ni, yanda ta iya d'aukan wanka da kyan ta, sai kuma shakuwar da mukayi anma bayan haka bana jin komai, ga wasu halaye ga Princess sam bata mutunta ni, wai daga an fara magana ko zolayar ta nake, saΓ­ tace wai ita tafi karfin wulakanci, kuma in na rabu da ita ni keda asara ba ita ba, dan wanda suka fini kyau da komai suna son ta, anma ni bazan taba samun wanda ya fita kyau ba,,,,,,,,,,,,,,,,,,
Ko kadan bata d'auke ni a matsayin wanda zai aure ta ba nan da yan watani, gashi batada lokaci na, kulum, itadai barta da kwoliya , kulum cikin zuwa inda za'a gyara fatar ta take, sanan kasan wani abu hum, wai ranar muna tadi nake ce mata ni mutum ne mai son yaya, ba kamar su fito daga kyakyawar matata Princess.


Hum wai saΓ­ ta bata rai wai na bar maganar nan dan ita fa in munyi aure ba da wuri zata haihu ba kuma in ma ta haihun da daya ya ishe ta, shima saΓ­ nan da shekaru goma, dan ko tayi aure bazata bar gasar kyau ba, dan haka bata bar jikin ta haka kawai ta tsufa ba kaji ko gashi yanzu al'ada familyn mu dole in zaka aure to zaka fara da mace biyu nΓ©, ma'ana ka auri mace biyu a lokaci guda,niko.Allah na gani bana son wada bata kai Princess kyau ba, kuma nasan bazan mΓ‘ samu ba, shi yasa itama take min gori kulum, gashi kulum saΓ­ naje nayi mΓ‘ mai martaba magiya akan ya bari na auri Princess kadai anma ya kiya, yace dole na nemo cikon ta biyu ko kuma su su zaba min
........ .......


Wani zazafan huci ya furzar yayin da ya gama maganar.



Tabas shima umar ya tausaya halin abokin nasa, yayin da sam ya tsani wanan banzar akidar ta abokin nasa, baisan cewa ba ,kyau bashi ne abinda ya kamata ya aje burin SΓ‘ akai ba, ya kamata yayi fatan samun mace ta gari ba wai kyau kadai ba......



Hakuri daΓ­ yaci gaba da basa tare da shawarwari .



B'angaren
Princess tifa kam a yanzu kyanta ya kara karuwa, yayin da kulum take cikin gyara jikin ta, Ga gasar su ta kusa nan da wata biyu wanan gasar tafi yin shiri a kanta, d'aukan kai da wulakanci kam saΓ­ abinda ya karu, kuyanga guda cΓͺ amintatar ta wato rabi, rabi ta kasance kulum saΓ­ ta zuga Princess tifa tare da yi mata kirari mai SΓ‘ ta kara jin kanta ita wata ce, ga rabi tasan yanda zata tsara Princess ,ita ke zuwa wurin wani mugun boka ta amso mΓ‘ princess maganin farin jini da kuma kara kyau a idanun al'ouma, duk wani sirrin princess Rabi ta sani.



Bayan sati daya zuwa yanzu Kamrina ta koyi abubuwa diyawa game da Suraya, komai nuna mata Suraya take, kasancewar wani buri da taci, gashi Kamrina akoi saurin d'aukan Abu.


Sam Suraya bata kai Kamrina salon ba, dan tsoron kar taje ta bata plan dinta, tana da wata yar aiki wada ta amince mata, ita mΓ‘ ta d'auke ta aikin, ita ta kama mata suke gyaran Kamrina, a yayin da taje ta hado mata kayan gyaran jiki masu kyau sosai da mayuka masu matukar kyau da tsada, lokacin da suka warware gashin Kamrina dake kumshe cikin wani abu mai kama da hula, zhara mai aikin cikin wani mahaukacin gudu tabar d'akin, dan an mΓ‘ yi SΓ‘'a bata suma ba kamar wacan lokacin da suraya ta gabatar mata da Kamrina,nan take ta suma, saida aka zuba mata ruwa tana tashi ta fara zabga kuka wai tayi gamo, dakyar Suraya ta fahimtar da ita, anma duk da haka ba wai dan ta yarda Kamrina mutum ce ba πŸ’― ba.

Gashi kuma yanzu gashin ai ya tabata aljana ce ,dan in ba aljana ba ita bata taba ganin irin wanan gashin ba, shigar ta b'andaki sau uku tana zawo, shima dakyar Suraya ta shawo kanta.


Dan ko ita kanta Suraya ta tsorata da gashin Kamrina.....







Wai fans na gaji wly,


Comment sharhi shi ke kara mana karfin gwiwa.





Aci gaba da gashiπŸ‡
Maimou LoveπŸ˜˜πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
*WACECE NI KAMRINA*
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€







*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*πŸ’‹






```Dan Allah masu bina ta privet cewa na basu daga farko dan Allah kuyi hakuri, wly akoi wahala mutum yayi typing kuma ya dawo yana turawa, daga nayi typing kulum sai na tura duk groupe din da nake, so ku kuma yan groupe ya kamata ku tausaya in mutum ya tambayi novel daga farko ku basa, dan nasan wasun ku suna da shi , sharewa kawai suke dan Allah ku dinga tausaya wa kuna ba masu nema``` πŸ™






*PAGE 11-12*







Sati daya kenan da gyaran Kamrina wanda har tanzu ba'a bar gyaran ba, kulum saΓ­ anyi mata gyaran, sanan za'a dinga sata wata mashine mai dumama jiki, in kaga Kamrina saΓ­ ka fita hayacin ka tsananin kyau da d'aukar ido, da gashi.

Zhara ce ke jera abinci a table na falon Saraya, kasancewar Momyn Suraya dama ba zama take ba kulum tana kasashe dan bisiness din ta, a wata bai huci tayi zaman sati a gida ba, sam babu ruwan ta da sama yaran ta ido duk abinda suke so shi suke yi, dan mΓ‘ Allah ya bata shiryayun yaya masu kamun kai badan haka ba in wasu diyan ne aida yanzu sun tambade, Daddyn su shima baya zama kulum suna wanan gari suna wancan gari, saboda harkar siyasa su.


Sadaf sadaf zhara ta lalaba ta leko d'akin da su Kamrina da Suraya suke dan har ga Allah yanzu tsoron su duka take, gani take Suraya ma ta zama Aljana ,tana rawar kafufu dan gaskiya kyan Kamrina abin tsoro ne, tana kakarwar kafafu tana i ina tace "ranki ya dade an jera abinci, tana gama fadar hakan ta juya zata arta a guje ganin Kamrina ta juyo, ji tayi an cabko ta,sululu tayi zata some ganin wada ta riko ta, nan fa zhara ta fara wa'inahu suleymanu wa'innahu bismillah, ta rimtse idanun ta gam πŸ˜–.....

Murmushi Kamrina tayi sanan ta fara magana cikin sanyi da zazakar muryar ta mai rikita mace ma to ina ga namiji in yaji, tace "zhara bude idanun ki ina sΓ³ ki natsu ki fahimce ni na miki magana, dan nima mutum ce kamar kowa, kamar yanda kike ba Aljana bace ni kaina ina tsoron Aljanun nan, dan da na gansu zan iya artawa a guje yanzu, dan na fiki bala'in tsoron su, ta fadi haka tare da kyalkya cewa da dariya, a hankali zhara ta fara bud'e idanu, ta sauke su bisa kan Kamrina dake rike da ita.





Sosai Kamrina tayi ta nusar da da Zhara har ta sake kuma ta yarda ganin Kamrina ta fara kuka, nan fa zhara ta yarda cewa ba Aljana bace, tare da ita suka ci abincin dan sam Suraya bata d'auki yan aiki a matsayin bayin ta ba.......



. "Kaga Malam dakata, kar kaga dan zan aure ka shi zai baka damar yi min abinda ka ga dama ba, dan haka dole ko nayi aure naci gaba da gasa ta in ba haka ba fine zaka iya neman wata, sanin kanka ne bazaka taba samun kamata ba, Dan yanzu shekaru goma tunda na taso ni kecin gasar nan, kofin diamond da zinari kulum a gidan yake kuma bazai taba gusawa ba,cewar Princess tifa."


Tunda ta fara masifar ta yake kalon ta, takaici ma ya hana SΓ‘ magana, saΓ­ wani madacin miyau da ya hada, yace "to naji, kinsan Al'adar gidan mu da mata biyu ake farawa,."

"Hum wanan matsalar ku ce kaje ka nemo ta biyun anma nasan sam bazata kai ni ba ko kadan, dan haka ban damu ba, kaje ina jiran kishiyar tawa,dan nasan ba komai ce a waje na ba ila baiwa ta, kaga banida time dan lokacin gasar mu yana matsowa kulum nake gyaran jiki na sai anjima. "


Nan tabar Kumar da Matsanan cin takaici, wanan wulakancin nata yasa sam baya son yazo wurin ta, sam shifa ba wani jin sonta yake ba, zai daΓ­ aure ta ne dan ya kece raini cikin abokai anma ba komai zaici gaba da hakuri, matsalar SΓ‘ daya ce ina zai Samu dayar matar ko bata kai Princess Tifa ba ya aura.


*bayan wata guda*.


Mai karatu in kaga Kamrina tofa tsoro gareka ya zama wajibi, idan ka tuna ada ma da bata gyara kyan ta ya ruda ni da duk wanda ya ganta, anma yanzu da tasha gyara ,ga kamshi da kamrina take, ta iya tafiya da yanga da takalmi mai tsini, kaya ko duk yanda tasa saΓ­ kirar ta ta fito, itadai Allah ya bata, saide tayi fatan kyan Aljanna.

B'angaren Princess ma abin saΓ­ wanda aka gani, rigar da zata SΓ‘ ranar gasa wajen wata daya akayi ana aikin ta, yayin da kulum Rabi saΓ­ ta amso mata wani tsumi tasha wurin boka........


Niko nace to fa abin mai yi ne, dan abin Princess tifa akoi tsoro kam.. ....



Momyn Suraya ce ta shigo d'akin Suraya tana fada, wai mai ke sata zaman d'aki, wani uban burki taja tayi turuss, sakamokon abinda idanun ta sukayi arba dashi, cikin matsanancin tsoro da rawar kafafu, dan tuni fitsari ya fara zubo mata, dΓ‘ hanu ta fara nuna wani gefe tana Alja,,,,,,,,,,,,,
Bata karasa ba ta fadi suuuuu a some.
.
.
.hankali a tashe sukayi kanta.......... ✍







Aci gaba da gashi πŸ‡
Maimou love πŸ˜˜πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
. *WACECE NI KAMRINA*
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€







*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*πŸ’‹







πŸ’«
*🌟🌟TAURARI WRITERS ASSOCIATION*...............✍









*PAGE 13-14*







Kamrina ce ta debo ruwa ta zuba ma Momy, can Momy tayi ajiyar zuciya, a hankali ta fara bud'e idanu saΓ­ akan Kamrina kara somewa tayi, hankalin su in yayi dubu to ya tashi,
Kara daΓ­ yayafa mata ruwa sukayi, nan ta kara fardado wa, anma bata koma ba, nan ta fara magiya dan Allah in ma Aljanna ce tayi hakuri.

Dakyar Suraya tasha kanta sanan tayi shiru.

Gaban Suraya ne ya fadi hankalin ta ya tashi tabas tasan cewar karshen zaman Kamrina yazo, cikin bacin rai Momy ta tashi taje bisa kugera, har yanzu zuciyar ta bugawa take. Kure Kamrina tayi tana kalon ta, yayin da ita ko Kamrina kanta ke kasa....

Bayan yan mituntuna Momy ta kai duban ta ga Suraya ranta a bace tace "Suraya mai kika d'auke ni, ina so karki boye min komai ki fada min yanda kika samu wanan yarinyar, boye min wani abu a gareta shi zaisa ki ja mata har ke ma...."

Share hawaye Suraya Tayi tabas tasan zaman Kamrina ya kare a gidan nan, anma ba komai uwa uwa ce, dole zata fada mata.

Nan Suraya ta fada ma Momy komai game da Rayuwar da Kamrina tayi, sanan ta dora da nasiha, tace "Momy ina so ki sani ke mahaifiya ta ce, kin fini sanin daidai, wanan yarinyar marainiya ce gaba daya ta taso batada gata a rayuwar ta, plz Momy ki taimaka ma rayuwar ta, watarana kema Allah zai biya ki da gidan Ajanna."

Sosai jikin Momy yayi sanyi, idanu suka mata jawur, nan ta yafuto Kamrina tace "zo nan ya ta, a hankali Kamrina ta tako nan Momy ta rungume ta tana hawaye, ita kanta Suraya sakin baki tayi tana kalon ikon Allah ,dan tunda take bata taba ganin hakan daga Mahaifiyar ta ba, Momy tace "cikin dariya bayan ta sumbaci goshin Kamrina tace "Masha Allah Ashe daΓ­ akoi diyata ta mace ta biyu ban sani ba aka boye min ita, Momy ta fadi hakan yayin dΓ‘ ta kaima Suraya hararan wasa, dariya sukayi duka, sanan tace "Kamrina insha Allah na d'auki Alkawari matsawar ina raye to Nice mahaifiyar ki, ina fatan kema zaki d'auke ni a matsayin mahaifiya ko?
Hawaye Kamrina tayi ta Kara rungume Momy tana godiya, itama Momy rungume ta tayi dan har ga Allah taji kaunar Kamrina kamar ita ta haife ta .
Momy ta kali Suraya sanan tace "ya kamata diya ta ta shiga gasar kyau din nan kodan inyi maganin pitsarara yarinyar nan Princess."

Tsale Suraya tayi tace "yauwa Momy nima plan dina kenan saide bansan diyar ki ko ta yarda ba. "ta fadi haka tare da marairaice fuska ta kali Kamrina, dariya kamrina tayi ta noke kafada tace "ni ban yarda ba saΓ­ abinda Momy na tace. "
Dariya sukayi duka, sanan Momy tace "diyata aΓ­ ni na yarda kuma yanzu Za'a kara gyara ki, babu wanda zai san

Dake.
Insha Allah zanje ayi duk wani shiri na d'aukan ki.

Suraya tace "gaskiya Momy ni bazan yarda ba kar dan kinga wanan ta kwoce min ke. "

Dariya suka SΓ‘ duka, Momy tace"ke bikin ki ya kusa dole abar min auta ta, ga yayan ki nan shima in kunyi aure aΓ­ saΓ­ na ganku kawai,... Akasa dariya, sanan Momy tace Suraya zo ki amshi akoi wasu less da shadodi da atamfofi sai Ki kira telan ki yazo gida ya auna ta. Godiya sukayi duka.......
Momy ta fita ta rasa mai yasa take jin son Kamrina, tayi farin ciki sosai. Tana zuwa d'akin ta d'auki waya indiya tayi kira nan kamfanin ta na sahari da sauran kaya, tana tsakar maganar ne Suraya tazo saida suka gama maganar sanan Momy ta Kali Suraya tace "ja'ira kawai kije kanyan suna d'aki na, In anjima zanje nasa sunan ta ccikin masu gasar sanan nan da kwona uku ku shirya a indiya Za'ayi sauran gyaran ta da kuma kamfani na na can Za'a mata kayan da zata SΓ‘, harda gyara ke Za'a miki na amare na jiki da sauran su, itama Za'a mata na jiki........





Tsalo Suraya tayi tana godiya, Suraya aure Za'a matΓ‘ ita da yayan ta rana guda bayan an gama gasar su Princess, Umar sanda zai auri princess laila kanwar Jabir, yayin da jabir zai Auri Suraya..........

Wanan kenan, Bayan Suraya tayi godiya ne ta koma wurin Kamrina, tace " baby Momy tace "Momy tace mu shirya nan da kwona uku zamuje indiya, sunyi murna nan suka ci gaba da fira.


Tun daga lokacin Momy taje wurin d'auka kuma an D'auki Kamrina,,,,,,,,,,

Ko Umar sanda bai san da Zaman Kamrina a gidan ba ..


.bayan kwona uku suka daga saΓ­ indiya, Kamrina kam saida zata shiga jirgi ta dan daga nikaf dinta saboda sojawan, dan Momy tace tasa Nikaf, su kansu sojawan saida suka tsorata gani kyanta. Ana shiga jirgi ta maida nikaf din ta.


Wuri guda suka zauna sunata fira, jirgi ya daga saΓ­ baban birnin Mumbai dake kasar indiya............






Aci gaba da gashi πŸ‡
Maimou Love πŸ˜˜πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
*WACECE NI KAMRINA*
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€






*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*πŸ’‹




✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
πŸ’«
*🌟🌟TAURARI WRITERS ASSOCIATION*...............✍
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Wattpad: Maimounasaniissa









*PAGE 15-16*






Da zuwan su indiya, suka sauka a wace unguwa inda keda wani dan gida madaidaici, mai kyau, gidan Momy ne ,da take sauka in tazo duba kamfanin ta.......



Suka shiga, Momy tace"yauwa kunga gidan izak kan, wani yaron ta dake mata gyaran gida ba'indiye ne, tace "kunga mΓ‘ ya gyara, kuje ga daki can ku kwonta ku dan huta, kar a jima sai muci abinci sanan mu tafi kamfani. "



Haka ko akayu zuwa sukayi suka kwonta, suka huta, can bayan sun huta, suka ci abinci sanan suka je kamfanin, kamfani ne baba, wanda akoi wurin da ake buga sahri da kaya irin wanan na indiya, da akoy b'angaren takalma, da riguna masu class.......


Wani Office suka je wurin managan, nan fΓ£ Momy suka juya harshe sai indiyanci suke, kamrina kam sakin baki tayi tana kalon su, duk da har yanzu da Nikaf take, dan matsawar aka bar fuskar ta bud'e to fa sai ta ruda mutane.....


Bayan su Momy sun gama maganar, suka shiga ita da kanta tayi zanan da yanda take so a buga doguwar rigar, bata son wada tarkace zasuyi yawa, saide daΓ­ daΓ­ wadeda, tana so ta fido Kamrina komai simple, kuma class, designe din da Momy ta nuna wanda take so ayo ma Kamrina gaskiya ya



Burge kowa, nan aka shiga da Kamrina aka auno ta, yanda rigar zata kama ta ta mata kyau, in kaga dirin ta tamkar na wata yar 20years dan Kamrina diri kam kugu da da boobs akoi su sosai.


Ana auna ta, akayi wajen takalma, suma na ita kadai Za'a tsara musu shi mΓ‘ su .

Sarka ma haka, kai haka daΓ­ sukayi ta zagaya wa duk wani abu na bukata sun hada sa, nan da kwonaki goma, suna fita sukaje wata salon na gyaran jiki ne ,Suraya nata b'angare daban na gyaran jikin ta, za'a mata gyaran da har wata uku bazai bace ba, yayin da itama Kamrina Za'a mata makamancin SΓ‘ .kulum saΓ­ sunzo, Momy ta barsu ta shiga gari wajen harkar bisiness din ta, sai dare zata tafi dasu, sanan ta kawo su shida na safe .....




Yarima Kumar ne gaban mahaifan sa zaune, sarki yace " Prince kana tune da sauran kaunakin da na baka ko, duka duka kwona goma muka baka, ka kawo matar ka ta biyu idan kuma ba haka ba mu zamu maka zabi, tashi kaje. "



Cikin damuwa Prince Kumar yabar wurin mahaifin SΓ‘, wurin mahaifiyar sa ya huce ,koda yaje yayi salama kuyangin suna mata tausa, kayan marmari ne a gaban ta kala kala nan ta salame su ganin Danta cikin damuwa, zuwa yayi ya kwonta saman kujera ta Alfarma dake shimfide a falon, tashi fulani tayi tazo ta dafa sa tace "son lfy daΓ­ ya nagan ka a wanan yanayi. "

"Mom wai baza'a bar wanan Al'ada ta mata biyu ba, gaskiya Mom ni banga wace zan hada da Princess ba, saboda kaf mata sune kasan ta a kyau."
"Haba son yanzu soboda Allah tun farko ga Suraya nan yar gidan hajiya saratu Aminiya ta, Suraya diyar ta, yarinyar tana da hankali kuma tana da kyau anma kaki, gata yar asali, yanzu gashi har zata auri wani anma ka tsaya ruwan ido, sanin kanka ne bazaka taba samun wada takai kyan Princess Tifa ba, saboda kana ga shekaru nawa Princess ke cinye gasar, to yanzu dai ba wanan ba karka damu zan kira Hajiya Saratu muyi shawara duk da yanzu tana indiya in ta dawo kaji duk yanda mukayi, tunda ita tafi ni yawace yawace zata fini sanin masu kyau, idan kuma hakan baiyi ba, sai asa gasa duk budurwa mai kyau saΓ­ tazo nan kawai kayi zabe a yan matan.....


Shidai Kumar baice komai ba, yana nan yana tunani.......





Satin uku na cika, bayan Momyn Suraya sun

Please Login or Register in order to submit comment