Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taji tsoron Kamrina ba kadan ba, dan yanzu ta kara tabatar wa da cewa kamrina ba
Mutum bace aljana ce. ..................


Bayan kwona biyu, Su Alhaji ne dadyn Suraya suka sauka à Rajugur domin wani taro da akayi shi yasa mai martaba ya sauke su shida abokin sa a fada anan suka kwona, washe gari dasafe, sarki daga shi sai dady da abokin sa ana yar hira mai martaba yace "Alhaji naji wata magana ranar ga Fulani, shine nace mai zai hana ayi auren yanzu tunda yaron nan yau zai dawo kuma ni gaskiya à yanda naji fulani tace na tabatar yarinyar tana da hankali da natsuwa, sam bana Son yaron nan ya kawo min wata tunda ga ita yar sarkin bagadur ita saï ayi daga baya ya kake gani ."...... ..


Nisawa Dady yayi yace "Eh Saratu ta fada min kuma na yarda da wanan batun dan haka ba matsala, nan take Dady ya kira Momy ya fada mata, yayin da mai martaba ma ya sanar da Fulani kuma ta aminta da zancan......

À take aka kawo goro Dady ya zama wakilin Kamrina yayin da Kanin mahaifin Kumar ya wakilci Kumar, nan fa aka d'aura auren Kumar da Kamrina, kowa yayi farin cikin abun yayin Da Fulani da Momy suka Fi kowa jin dadin abun, fargabar Momy da daddy guda kar asalin Kamrina ya tonu, anma insha Allah, Allah na taré da mai taimako, shi zaici gaba da rufa masu sirin su.



Momy ce take waya da wata mata mai gyara, ana haka Suraya tazo, bayan Momy t'a gama waya ta aje.

Duban ta takai ga Suraya tace "Suraya "
"Na'am Momy, An daura auren Kamrina da Kumar. "

Dum Suraya taji gaban ta ya amsa abun banbara koi, tace "Momy dagaske 😳


" Kworai yau Dadyn ki da na Kumar suka d'aura auren, fargaba ta daya, ta yanda Kamrina zata d'auki zancan. "


Nisawa Suraya tayi tace" Momy gaskiya wani b'angaren naji dadin hakan, wani b'angare kuma fargabar ita Kamrina."

Momy tace "je kira min ita ai gata muka mata. "


Tashi Suraya tayi jiki à sanyaye tayi b'angaren su Kamrina n'a kalon TV tace "sis Momy na kiran ki, tana fadar haka tashige d'aki,dan bazata iya jurar damuwar da zata gani à idanun yar uwar ta ba yayin da taji abinda aka aikata mata.



À hankali Kamrina ta tashi tayi wurin Momy gaban ta na faduwa, tana zuwa Momy ta tarbo ta ta Rumgume ta, sanan ta aza kanta saman cinyar ta, ta fara shafa sumar kanta, tace "auta zan miki wata magana, kuma ina so ki fahimci manufa ta ,bazamu taba cutar ki ba, yanda muke ji ga yayan cikin mu haka muke jin ki, bazamu taba kaiki Inda Za'a cuce ki ba, Kamrina a yau aka d'aura Auren ki da dan sarkin Rajugur ,wato yayan ki Kumar abonkin kumar ai kin gansa. "


Wata irin zabura zumbure Kamrina tayi ta mike idanun ta suka canza launi ,jijiyoyin kanta suka tatashi, sai yau kadai ta samu hawaye sun zubo mata, tace" a'a ya zakumin haka, ya zaku min haka mai n'a muku, dan kawai ina gidan ku mai yasa zakumin aure nace ina so ne. "



Da gudu tabar falon, kanta har wani juyawa yake, yayin da ta bar Momy da mutuwar zaune, fargaba, Rudani, tashin hankali tsoro, duk lokaci guda sukayi ma Momy dirar makiya, zufa ce ke keto mata duk da sanyin AC din dake cikin falon, ya zatayi ne, ya Za'ayi dama ta buga gaba da Dan daba nata ba, ashe kuskure ta tafka bata sani ba............







Tofa ana wata sai ga wata, shin ya zata kasance ?


Kamrina zata yarda da auren ko zata bar musu gidan ?

Ya zata kasance da Momy da à yanzu ta fara dana sanin aminta da tayi da Kamrina ?


Hum ya uban gaya zaiji yayin da yaji abinda ya faru wato kumar ?


Ya Princesse Tifa zata ji🤦‍♀






To nima dai nace aci gaba da gashi 🍇
Maimou Love😘



Aci gaba da gashi🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
*WACECE NI KAMRINA*
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀










*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAHI AM*💋










✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💫
*🌟🌟TAURARI WRITERS ASSOCIATION*.................✍
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨















*PAGE 31-32*






Suraya na kwonce saman gado tana nazari, Kamrina tazo ta haye saman jikin ta tana kuka kamar ranta zai fita, bata taba kuka ba a rayuwar ta sai lokacin da Apou ya rasu, sai yau, lalai abin ya girmama, rungume ta Suraya tayi yayin da gaban ta ke kara tsananta wajen faduwa. ...


Sosai Kamrina tasha kukan ta ta koshi, sanan ta daga jajayen idanuwan ta tace "Anty banyi ma Momy adalci ba, tayi bugun gaba dani tayi min aure, tayi min gata, ta d'auke ni à matsayin yar ta, kun tsince ni à titi kun so ni, yayin da kowa ya guje ni, ana min kalo, kun bani gurbi à matsayin yar cikin ku yar uwa, kanwar ku. Anma yau ni na muku butulci, n'a fada ma Wada ta d'auke ni yar cikin ta, ta aminta zuri'a ta ta d'auke ni à matsayin yar uwa, ta bani abinda ban taba samu ba, wato gurbin uwa ,anma ni yau Kamrina nike fada ma mahaifiya kuma uwa ta wanan kalamai marar dadin ji, wayo Anty nikam meye amfani na ."😭😭😭



Momy da ta biyo ta duk taji abinda Kamrina ta fada da sauri tazo ta rungume Kamrina daga baya tana dadaba ta, alamun rarashi, da sauri Kamrina ta juyo tana ganin Momy ta rungume ta rungume ta itama, sanan cikin kuka tace "ki yafe min Momy wly ko cikin wuta kika ce n'a shiga zan shiga, insha Allah zan kasance mai miki biyaya har karshen numfashi na , ki yafe min😭."




Dago ta Momy tayi ta share mata hawaye , ta girgiza mata kai tace" auta kar ki kara kuka kinji, nagode da kika fahimce ni, insha Allah wanan zabi da muka miki alherie ne, kiyi shiru ki maida lamuran ki ga Allah kinji babyn Momy."

Dariya Kamrina tayi, Suraya taja hanci Kamrina tace "Hum uwa da ya har an shirya, dariya Kamrina tayi ta kali Momy tace "Momy ai bamu bata ba dama ko, kada kai Momy tayi tace "kworai kuwa dota. "


Akayi dariya duka.


Momy tace dota kinga kudin ki nan fa, naira millions hamsin da biyar, sai kuma sarkar gold guda bakoy, sai ta zinari guda biyar,dan haka sai à bude miki acount azuba miki kudin. "

Waro ido Kamrina tayi tace Momy wanan kudi da yauwa gaskiya, ku d'auka kuma. "

"Haba dota me zamuyi da kudin ki, wly ki d'auka ki aje kayan ki, rikici ne ya kaure tsakanin Momy da Kamrina,Momy tace bazata d'auka ba, ita ma Kamrina tace bata yarda ba, saida Kamrina ta fara kuka sanan Momy tace to sun d'auki millions goma ita da daddy, nan ma Kamrina bori ta tayar tace saide Momy da dady su d'auki millions ashrin 20 dakyar Momy ta yarda, sanan Kamrina ta d'auki millions biyar biyar taba taba Suraya kuma tace aba Umar biyar.



Wanan kam Momy bata hana ba domin cewa tayi yan uwan ta ne bazata shiga tsakani ba, Suraya kam tasha godiya, cikin sarkar gold ma da ta zinari biyu biyu taba su Momy itama saida ta fara kuka suka amsa.





Nan fa sukayi ta fira har yama ta fara sanan Momy ta fita, Suraya ta kama hanun Kamrina tace "Autar mama kin fa yi sa'a miji, koda yake shi yayi sa'a."
Turo baki Kamrina tayi tace "anty ni ki daina min zancan wanan mugun plz. "


Dariya Suraya tayi tace "Hum watarana ke da kanki zaki dinga Son a miki maganar sa."


Itadai Kamrina Bata ce komai ba, domin ranta mugun baci yake In ta tuna cewa yanzu ita malakin wanan mutumin ne, wato Kumar...........

Momy musaman ta kira mai gyaran jiki daya indiya, daya sudan, daya kuma nan take kasar bagadur, kworaru ,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,

Gyara sosai ake ma su Kamrina da Suraya, domin rana daya zasu tare ita da Princesse tifa, saide ita à ranar za'a d'aura auren, har Suraya duk rana daya ne , nan da wata daya..



B'angaren Kumar bayan yaje gida ya huta, Mai Martaba ya kira sa yake fada masa cewar ina matar da akace ya kawo ta biyu i'ina ya fara sanan yace "ranka ya dade ban samu ba,dan Allh à barni da Princesse ta ishe ni. "

"zancan banza kenan, to ni dama n'a riga da na maka mata, sai kayi shiri domin ita dayar ma har n'a riga n'a d'aura maka aure da ita, nasan fargabar ka, domin ita tafi wada kake Son kyau ka tashi ka tafi, Allah maka Albarka. "

Shidai Kumar, duk da yaji abinda mai martaba yace bai damu ba ko kadan ba ,domin shi yasan mace daya zai Aura kuma Princesse Ce, pakat, duk wasu abokan sa ya gayata, kuma duk wanda zai tambaye Sa to mata daya yake cewa zai Aura...

Kamrina tun rada taci gasa kulum saï masu kudi sunzo neman ta, wai suna Son ta da aure, saide ace tayi aure.....



*Bayan wata daya*

Àka d'aura auren Kumar da Princesse tifa, yayin da aka d'aura n'a Suraya itama da Yazeed.
Ranar kam anyi mutane kasashe daban daban.

Farin ciki à gidaje uku baya faduwa.


Yayin da Prince da Princesse basu san cewar Kamrina itace matar sa ta farko ba, yace" mata an masa aure anma baisan wacece ba, bata damu ba dan tasan Prince nata ita kadai

Yau boka yace "lalai Princesse tazo ita da Rabi domin yau za'ayi aikin da Za'a yima Prince asirin da ko uwar sa bata isa tasa sa yayi ba, matsawar ba princesse tace ba.

Wanan batu boka ke ma Princess domin tun gasar da ta fadi bata ci ba take yarda da aikin bokan, komai yi take ba sabawa, kuma tun aikin da taga yayi ma Kumar ta kara yarda dashi.....
Boka yace "wanan karon Aljani yana Son ki biya sa da budurcin ki, domin wanan aikin bazai yiwu ba sai kin bada budurcin ki."


Wata irin zabura princesse tayi.









Aci gaba da gashi🍇
Maimou Love😘🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
*WACECE NI KAMRINA*
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀










*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAHI AM*💋










✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💫
*🌟🌟TAURARI WRITERS ASSOCIATION*.................✍
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

















*PAGE 35-36*







Sam Kamrina kin kwoliya tayi, har lokacin zuwa diner yayi yayin da Princess tasha shiri cikin doguwar riga ta wani farin less mai matukar kyau fari da d'aukan hankali, tayi kyau sosai, rigar ta matse ta,tasha nadin gwogworo tasa wasu dogayen takalma, nan aka mata jagora wajen motar da ango Yake ,aka sata ciki, duk mutane sun tafi saí Mota uku wada zata kai ango da amare,a hankali Princess ta shiga, wani lumshe ido Prince kumar yayi, yayin da yayi wani mahaukacin kyau ,shada fara ce yasa da tasha wani irin dinki mai matukar kyau irin na maza, kuma akayi dinki sarakuna da ita, sanye yake da farin agogo na gold, yayin da fuskar Sá tasha kyau ainahin kyan Sá ya fito, kai ango yasha kyau har ya gaji, rike hanuwan Amarya yayi, yayin da ya kwonto da kanta saman kafadar Sá, a hankali cikin voice nashi mai dadin sauraro yace" Amarya ta kinga kyan da kikayi, kuwa na manta dama da amarya ta kyakyawa ce. "
Nan yaba dreba umarni cewa ya kuna motar su tafi..

Wani dadi Princess taji jin bada wacan matar za'a tafi ba, a hankali tace "Prince nawa ina wacan matar taka bada ita za'aje ba?


Bata rai Prince yayi yace "ni banda wata mata bayan ke, kuma dan Allah karki kara min zancan wata bayan ke plz,dan ni a iya sani na mata daya na aura ba biyu ba. "

Wani dadi ne ya kama Princess jin Prince ita kadai yake muradi .......


Ta Kara lafewa a jikin Sá kamar mage shi kuma saí shafa ta yake........




A haka aka tada mota suka tafi....

Fulani ce mai kwoliya ta iske ta cewar Kamrina taki ayi mata....

Da sauri Fulani tazo, har Dakin Kamrina, nan fa tayi ta lalashin ta, anan aka yima Kamrina kwoliya, duk da tace kar a cika mata fuska, tayi kyau matuka, kun dai san mutuniyar wajen kyau ,wata doguwar riga itama aka Sá mata, ta mata kyau matuka, yayin da ta fido surar ta sosai In kaga kirar ta ya ta masu shekaru 20,ita kanta Fulani tasbihi take da wanan suruka da ta samu ,,,,,,,,,,,,,,



Ita kanta kusan komai iri daya da na Princess anan ne na gane da cewa kenan iri daya fulani tasa a dinka masu, wani farin mayafi mai kyau sara sara ta yafa mata, bakin ta yasha jan baki, abu ga farin mutum. Tayi bala'in kyau, kawayen wata cousin din Kumar da sukayi anko na wani tissu bleu mai kyau, doguwar riga su shida, dama tunda Fulani taji kumar ya tafi da matar sa ita kuma ta tsaida su Rukaya cousin din Kumar da kawayen ta, motoci shida Fulani tasa abokan Kumar saura su zo da su, shi Kumar bai má sani ba, nan Rukaya taja Kamrina da take zuba kamshi ,a wurin party na yan mata da samari ne, saí kuma couple wanda sukayi aure, duk matasa ne, babu manya, matasa masu ji da Naira, wasu da matan su suke zuwa wasu kuma da yan matan su, wasu kuma samari su kadai wasu kuma yan mata su kadai....


Baban fili ne, da yasha decoration fari da já.


Ango da Amare kujerar ango ke tsaka, yayin da kujerar amaren ko wace ke gefen sa....


A haka ga dj saí sakin sauti Yake, zuwan amarya da ango ne aka saki wani sauti Mai dadi, nan fã aka tashi kowa saí kalon su ake, yayin da ake bin Kumar da Princess da wasu fulawa já, kuma ana feshe su da wani farin turare mai kunfa da kamshi, Kumar rike da hanun Princess saí murmushi yake zubawa ko ina tafi ake, ana ga amarya da ango nan sun zo, kowa ya tashi.


A haka suka karaso suka zauna mazaunin su..

Suna zama aka fara gabatar da party, Rukaya
Ce cikin mota fara da ita da wata kawar ta suka Sá Kamrina tsakiya har sun Sabá da Kamrina dan firar da suke saí kayi tunanin sun jima da sabawa ,a haka har suka iso halt din, katon wuri ne Mai kama da falo anan ake partyn, wani abokin ango ne yazo ya rada má dj wani abu a kune, nan dije ya dakatar da kida yace "ku saurara kowa ya baje kunuwa yana sauraro, yace "yanzu aka sanar dani cewa Uwar gida ran gida matá ta farko a gurin Prince ta karaso. "

Wani tari ne ya sarke Kumar jin ance wai uwar gidan Sá, to uban wa yace tazo bayan In tazo yasan ba wata mai kyau bace zata bata masa taro gashi shi yazo da kyakyawar matar sa da shidai gaskiya an cuce sá.



Gaban Kamrina ne ya fadi lokacin da Rukaya tace mata sun iso, a hanakali yan matan dake tare da Rukaya suka jera, suna watsa jar fulawa wasu kuma turare suke fesawa ,a hankali Kamrina ta fido kyakyawar k'afar ta.







Aci gaba da gashi 🍇
Maimou Love😘🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀
*WACECE NI KAMRINA*
🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀🤦‍♀










*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAHI AM*💋










✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
💫
*🌟🌟TAURARI WRITERS ASSOCIATION*.................✍
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨










_Wly groupe Maimouna Novels kuna burge ni saboda comments din ku, sharhi kam kuna zuba Sá, dan haka wanan shafin naku ne_









*PAGE 37-38*







Gaba-daya ta fido kafafun ta, ta fito waje baki daya, Rukaya ce ta kamo hanun ta yayin da kawayen Rukaya suka jera suna zuba fulawa já dá kuma turaren feshe, dai-dai hanyar ficewar ta.

A hankali Kamrina ke takowa ,yayin da dj ya saka wani sauti mai kayatarwa, Mai sanyaya zuciya , duk mahalukin dake halt din ya zuba ido yaga Uwar gida, yayin da ango ya rumtse ido gam, domin yasan dariya ce kawai za'a masa ,ita ko Princess idanun ta a bud'e suke, kar, so take taga wacece wanan uwargidan nata, haha itadai tasan tunda ta riga da ta mamaye son ta ga zuciyar mijin ta ba wada yake so saí ita.....


A hankali su Kamrina Suka shigo halt din dake cike dankam da mutane, tana sanyo kafa ciki taji mutane diyawa daga ciki wasu suna addou'a neman tsari daga Aljanu, wasu kuma tasbihi ne suke tare da kure Kamrina da kalo, domin kyan Kamrina kowa ya sani, ba saina bata baki wajen zayane muku rudun da mutane suka shiga ba, har da masu cewa Prince yanada mata kamar haka ya tashi ya kwoso Princess, wasu suce gaskiya Prince yayi dace, ya zabe yan matan masu kyau ya aure, wasu suce ai sam má Princess bata dace da Prince ba, da uwargida kadai ya kamata ya zauna.........


Jin wanan abubuwan yasa Prince bud'e idanu a hankali ya sauke su akan Uwargidan tasa a cewar sa ,a hankali ya ware shanyayin idanun sa masu haukata yan mata dai-dai isowar Kamrina, ya sauke su kanta, dum yaji wata irin faduwar gaba ne ya dirar má Kumar yayin da yayi wani irin zabura ya tashi tsaye ya kura ma Kamrina idanu, ita ko a jikin ta zuwa tayi inda Rukaya tasa ta zauna ta zauna, wani sihirtacen kamshi ne ya shako su lokacin da ta zauna, yayin da daya b'angare Princess tayi suman zaune kwakwolwar ta ta tsaya cak ta daina aiki, gangar jikin ta sam baya motsi, tsoro, fargaba, Al'ajabi tare da Mamaki duk suka bi suka mamaye zuciyar ta, wai ashe dama wanan Aljanar itace kishiyar ta, wayo Allah itako wani irin sakaci tayi wanan Aljana ta aure mata miji...........


Hanu ta aza bisa kai, 🙆‍♀,sanan tayi saurin d'aukewa idanun ta sun kada sunyi jawur ,ta rasa mai ke mata dadi.....



Kumar duk da yana jin haushin Abinda yarinyar nan tayi má Princess, anma yaji dadi sosai da iyayen Sá suka aura masa ita ko bai son ta ai shi kam ya huce raini wly, saurin basarwa yayi, ko kadan bai lura da yanayin Princess ba, ya sakar má Kamrina murmushi kamar gaske, sanan ya zauna tsakiyar su.


Dj ne fã da ya rude ya fara koda Uwar gida, shima duk yabi ya zauce, wanan abu ba karamin kara Sá wutar tsana da rudu a zuciyar Princess yayi ba , ganin da tayi kowa yabar ta tata, kowa ta Kamrina Yake, ko masu d'aukan photo hankalin su ya koma kan Kamrina, shiko Kumar saí wani kara shishige ma Kamrina yake, yana wage baki ya gonar auduga.

Har kakama ta yake, itadai Kamrina kar take kalon sa, sam bata son hakan dan yana cikin jama'a ne da yaga tijara.


Dan wani irin

haushin Sá take ji daga shi har matar sa.......
Sosai aka fara gabatar da abinda yakawo su, nan fa aka umarci ango da matan Sá su fito su taka, Kamrina badan taso ba haka Rukaya tasa ta tashi, nan Kumar ya kama hanun matan Sá Biyu, suka zo filin rawa,, tsab Kumar ya taka rawar Sá yayin da Kamrina duk da son rawar ta ko girgizawa bata yi ba, ita kanta Princess bakin cikin da take ciki ya hana ta taka rawa. Like kam sun shasa, ango má yasha lika ma matan Sá dolar,anyi watsin dala kamar ba gobe ba kamar Kamrina yafi zuba mata, kai Princess kam tasha takaici a wanan pharty, matasa da mata sunsha rawa, komawa mazaunan su sukayi wato Prince da matan Sá, nan akace su yanka cake 🎂,ango ne ya yanka, akace Uwargida za'a fara ba sanan amarya, wanan abun ma yaci ran Princess, Haka Prince ya debo yayi bakin Kamrina fuskar ta adan sake ta bud'e baki ya Sá mata, akayi tafi raf raf, itama dakyar ta iya yanka katoto ta zungura masa a baki, mutane diyawa ta burge su, dj yace wanan yana nufin Uwar gida zata kula mana da mijin ta, Kamrina taji takaici da tasan haka ne da karami ta basa ,Prince ya juya ya yanko yakai bakin Primcess itama ya bata, ta dan ci kadan, itama wuka tasa ta yanko zabgege wanda yafi na Kamrina, zata kai bakin Kumar, ya waro idanu😳 ganin abinda take shirin yi ,ita kam Kamrina abin dariya ya bata ganin haukan kishi irin na Princess ,tasan saboda ita ne tayi hakan, anma ita tayi haka ne dan keta, anma ita kuma wanan mahaukaciyar ta aza ko tana son mijin ta ne, mtssss.


Kumar yayi kuri kuri da idanu yayin da Princess take faman kai masa wanan zabgegen cake din a baki, dj yace "tofa yau ake shirin yinta...


"Amarya ma tace baza'a barta a baya ba, takalmi Kamrina mai tsini ta daidaici k'afar Kumar daidai tsinin ta taka k'afar Sá dakyau, ba shiri Kumar ya bud'e baki zaiyi saki kuwa domin zafin ya mantar dashi inda Yake kamar hadin baki Princess ta tura masa wanan katon cake a baki, rumtse ido Kumar yayi jin zogi da radadi da k'afar Sá keyi, ga katon cake da ya girmi bakin Sá baisan yanda zaiyi dashi.

A hankali yasa hanu ya fido wanan cake ya gutsiri kadan yaci, idanun Sá sunyi jawur dan tsabar wuya da yaci, take ya kara jin tsanar Kamrina, yayin da ita kuma take sune kai tana dan Murmushi na mugunta.....

Masha Allah diner kam ya kayatar, sanan ya bada kala, anyi partyn da ba'a taba yi ba...


Wajen misalin k'arfe sha biyu na dare aka gama.

Wani abokin ango shi ya d'auki ango da amaren Sá Biyu suka sashi a tsakiya,kasancewar duk manyan abokan nasa Umar Sanda da Yazeed abokan Kumar suma suna can yau ake kai musu nasu amaren, a cikin ,k'afar Kumar tayi kumbri tayi suntum, wani mugun kalo ya aika má Kamrina, ta gansa sarai anma ta share, rungume Princess yayi, ita kuma ganin haka abin ya mata dadi ta kara lafewa a jikin Sá, Kamrina ko a kwolar rigar ta, yayin da Prince keta fada ma Princess kalamai na soyaya, yana nuna mata komai kyan mace a bakar jaka yake kalon ta, tauraruwar ta kadai ke haskawa a birnin Zuciyar sa, tabas idan Kamrina tace bata ji zafin maganar sa ba tayi karya, domin ya ambace ta da bakar jaka.....


A haka daí suka isa gida, har b'angaren Prince aka aje su.

Direct Kamrina
Ta bud'e mota tayi b'angaren ta, ko kara kalon su Kumar bata yi

Please Login or Register in order to submit comment