Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba,.

Shi kuma Kumar d'aukan Princess yayi saΓ­ d'akin Sa....

Direct bisa gado ya aje ta, yayin da ita kuma take ta chagwaba, bata rai tayi tace "ango na dama wanan Aljanar itace matar ka kaki sanar daniπŸ˜’"

"Hum wly Princess yanda kika ganta yau nima haka na ganta, anma ai ni bana ganin kyan ta, ke kadai nake gani, sosai Princess taji dadin maganar, tace "shine kake mata dariya,kana wani kama ta. "


" Hum Princess kishi ko, to nayi haka ne kar asamu dan gulmar da zaije ya fada ma Fulani ,cewar bana kula ta, wanan shine dalili. "


Sauke ajiyar Zuciya Princess tayi najin zargin ta ba gaskiya bane ,kuma ta kara godewa boka.....


"Uhum my Princess tashi ki rage wanan kayan naki, nima bari naje nayi wanka ,shiga yayi yayi wanka yayin da itama bayan ya fito itama tayi wanka.....

Kayan barcin sa yasa, ya feshe jikin SΓ‘ da turare, yayin da itama ta fito daga wanka ta shafe jikin ta da mayuka, tasa kayan
Barci, yace tasa hijab ,ya Umarce ta sukayi sallah raka'a biyu, ya dafa kanta ya mata addou'a,sosai ,sanan daga k'arshe ya d'auko kaza guda wajen biyar, da yaghour nan ya fara bata tana basa suna CI, har suka koshi, ya tatare kayan yakai kitcin, itama tazo tayi brush, shima yayi, bisa gado Princess ta hau, ta fida hijabin ta, yar rigar ta figigiya ta barci ta bayana .


Bayan ya fito daga toilette shima lfy gado yabi ,ya jawota, a hanakali ya fara shafar ta, yana aika mata sakwoni masu tsaya wa a rai ,wanda suka fara fida ta a hayacin ta ,rigar ta ya fida gaba daya, nan take yan kananun boobs dinta suka bayana, baki yakai ya fara tsotsa, saΓ­ wani nishi suke saki, sosai ya jagula ta, sun d'auki tsawon lokaci ji tayi yana addou'a saduwa da iyali, nan yake gaban ta ya fadi, dan boka ko ranar da za 'a kaita a daren ranar da yace ta dawo zaiyi wani rubutun malaka a jikin ta saida ya kara saduwa da ita, ya bata duk wani shirin da aka mata ya shanye romon.


Wanan abu shi ya kara fadar mata da gaba, anma da ta tuno da wani hayaki da boka yace tayi, kafin mijin ta ya kusance ta dan matsawar tayi hakan mijin ta bazai taba gane wa ita ba budurwa bace. sai taji dan dadi, tashi zatayi, Kumar da ya gama fita hayacin SΓ‘ ya maida ta, dan duk a tunanin SΓ‘ tsoro ne irin na rashin sabo, ci gaba da wasani yayi a jikin ta, gaba-daya ya kashe masa jiki, Addou'a saduwa daΓ­ ya kuma yi ya shige ta a hankali, duk a tunanin SΓ‘ budurwa ce zaibi da ita a sanu, anma saΓ­ me duk da akoi matsi sawa daya yayi ya tabatar da ba budurwa bace, wani irin abu yaji ya tokare masa zuciya, idanun SΓ‘ suka canza launi........







Aci gaba da gashi πŸ‡
Maimou LoveπŸ˜˜πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
*WACECE NI KAMRINA*
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€










*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAHI AM*πŸ’‹












✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
πŸ’«
*🌟🌟TAURARI WRITERS ASSOCIATION*.................✍
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨













*PAGE 39-40*







Kara tura abar SΓ‘ yayi yaji ko abinda Yake zargi ko ba gaskiya ne ba .ji dai yayi ta kara hucewa, gaba-daya yaji sha'awar sa ta gudu ta barsa, cikin zafin rai da zafin nama ya zare abar sa, ya tashi tsaye kikam, shako wuyan Princess yayi ,ya tado ta zindir daga ita har shi ba kaya, tuni hankalin Princess ya tashi Dan tunda take ba'a taba mata makamancin wanan abun ba, "dan Uban ki wa kika kai ma budurcin ki?


Ya shake wuyan Princess idanu duk sun firfito hanun sa ta kama ta fara d'auke numfashi, saida yaga tana shirin shekawa ya jefar da ita ya fara zabga mata maruruka , yace "wato ashe duk kyan ki na dan maciji kikayi, ashe kin ba wasu banza budurcin ki ,wly Allah ya isa bazan taba yafe miki ba, mari yake gwora mata baji ba gani, sai can kuma yaji wani irin abu kamar ya Soki kansa, rike kansa yayi da hanu biyu, yakai minti uku zuwa biyar, yayin da Princess ta kasa koda motsi, dan ya mata liss batada wani katabus.



Waro idanu Kumar yayi ganin yanayin da Princess take, saurin rungumo ta yayi cikin rudu yace My Princess waye ya miki haka?



Waro ido😳 Princess tayi jin maganar SÑ ta rainin hankali, duban SÑ tayi,dakyau taga da gaske yake tambayar ta yake ba, murmushi tayi, dan tasan wanan aikin boka ne, ko ba komai yau ya mata rana ,Kukan munafurci ta fara tace "cikin marairaicewa ba kaine ba kaki bina a sanu gashi yanzu duk kasa na saí zogi yake min."



Kansa ya duba, yagan sa suntur, yayin da ya duba ta itama haka, hakan yasa ya yarda da abinda tace. "




Ashe wanan lokacin boka ne ya tashi, dan dama yasan ga wanan lokacin
Kumar zai kusanci Princess, dan Aljanun da yake aiki dasu sun fada masa, hakan yasa ya tura aljani mantau, ya shiga kan Kumar ya mantar dashi yanayin da Kumar ya samu Princess....



Duk da Prince yana jin wani kunci a ransa kadan kadan anma bai san na meye ba hakuri ya dinga bata, yayin da ya d'auke ta saΓ­ b'andaki yasa ta a ruwan dumi, itako saΓ­ kukan karya take,tana wani kara lafewa, tare da murmushin mugunta, duk da tana
Jin zafin marurukan da
Ya mata anma bata damu ba tunda shi ya manta....


Duk abin nan da ake yi Kamrina najin yanayin, kuma tasan sarai iska ya shigo idan suke har wani b'angare daban.. Abun ne ya zame mata biyu biyu, b'angare daya iskan da aka turo yama Princess aiki ne, daya kuma daga cikin b'angare na gidan ,Kuma tabas wanda yake daga wajen gidan yafi mugunta,take idanun ta sukayi jawur ,hankalin ta ya tashi ranta ya bace, da kayan barci ta fito,kalon b'angaren su Kumar tayi wata wuta wuta ta fito daga idanun ta, sanan kuma ko mai ta tuna tayi wata yar dariya ta juya tayi tafiyar ta , tafiya take har ta bud'e falo ta fito, tafiya ta fara yi mai nisa, tana tafe ranta na kara baci, a haka takai minti talatin tana tafiya domin gidan da b'angaren da tayi akoi tazara....
A hankali tabi wani lungu na bayan wani tsareran d'aki, ta kara shiga wani lungun, tana zuwa daidai bayan d'aki taga mace d'aure da zani jΓ‘ d'aure tayi d'auri kirji. ,kaskon wuta a kanta daya kuma na hanun ta, saΓ­ tika rawa take ya yar bori, tana wasu surutai yayin da take fadin abinda wanan mugun Aljanin zaiyi
A daya b'angaren, duk da ita bata ganin SΓ‘, wanan macan ta fara magana bayan tayi yan surkulan ta tace "shekara da shekaru kenan muna neman wanan damar anma bamu samu ba, saΓ­ yau da akayi wanan sabgar, kuma yau an tabatar min bata cikin tsarki, sanan batayi addou'a yayin da zata kwonta ba, domin ni na bata lemun da tasha yasa ta barci, ba Tare da tayi wata Addou'a ba, gashi bata SΓ‘ karatun kulum ba da yake hana mun aikin mu ba, dan haka kaje kaje, ka saukar mata da cutar da baza'a taba samun maganin ta ba, kaje kaje. "

Wanan kalamai su suke fitowa daga bakin wanan matar mai d'aure kirji.


.


Hanu Kamrina ta maida a kirjin ta sanan ta kara bata rai duk abin nan wanan matar bata lura ba, domin hankalin ta ya tafi ga abinda take shirin aikawa, shikam Aljanin da ake magana dashi tuni tsoro ya mamaye SΓ‘, sakamokon wada yayi arba da ita....


Saide In bana gidan nan za'ayi cuta, anma matsawar ina wanan gidan baku isa ku cika burin ku ba,.😑"
Kamrina ce ke wanan Kalamai, cak wanan mata ta tsaya da aikin ta, yayin da tsoro firgici rudu, ya shige ta, tuni kaskon wutar duka suka fado .



Fitsari ne ke barazanar fitowa daga jikin matar, karkarwa ne ta fara ,murmushi Kamrina tayi ,yayin da take kara nufo wanan matar, ita kuma matar tana jΓ‘ da baya...........





Fans kuyi hakuri da wanan ba yawa.





Aci gaba da gashi πŸ‡
Maimou loveπŸ˜˜πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
*WACECE NI KAMRINA*
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€










*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*πŸ’‹










✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
πŸ’«
*🌟🌟TAURARI WRITERS ASSOCIATION*.................✍
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨















*PAGE 41-42*











Saida Matar nan takai gab da katanga, Kamrina ta karaso, daf da ita yanzu kam suka gane junan su, Kilishi saΓ― karkarwa take, dama tun da aka kawo Kamrina kyanta ya tsorata ta tace Aljana ce, ashe Kam gaskiya ne.


"Hum dama tunda nazo Gidan nan nasan cewa kune matsala da ke da yar ki da kuma yar rikon ki, to ki rubuta ki aje duk wani mugun abu da kike kulawa na sani idan na kara Jin wani abu ko ganin sa ya faru Γ  Gidan nan, to ki sani Γ  kanki zai koma.



Kilishi kam fitsari ne ya
Kufce mata a wondo ba shiri ,tace "wly bazan kara ba kiyi min rai,na tuba. "


Dariya Kamrina tayi tace "n'a barki wanan karon anma nan gaba in ma kinyi zaki hadu da fushi na."


Tana gama fadar haka tayi tafiyar ta.

Kilishi ko cikin wani mahaukacin sauri har tana faduwa tabar wurin.


Kamrina bata tsaya ko ina ba sai b'angaren ta, tana zuwa d'akin ta ta rufe.


Zuwa tayi ta zauna, saman gadon ta, ta tankwoshe k'afafu wuri daya.


'Assalamu Aleykum. "


Taji anyi wata kyakyawar matashiyar budurwa ce ta fito daga jikin bango. "



Wa 'aleykum Salam Kamrina ta amsa mata, fuskar ta d'auke da Kayatacen murmushi
.

Karasowa wanan budurwa tayi cikin kayan ta farare, idan ka ganta batada maraba da mutum zama tayi kusa da Kamrina...wada take turo baki alamun tayi Fushi. Sanan Kamrina tace 'Fatima nayi fushi, saboda Allah yaushe rabon ki da ni, tun daya dacin gasa ta ko aure na baki zo ba,duk da ba son auren nake ba ."


Wada aka kira da Fatima tayi murmushi sanan ta kama hanuwan Kamrina, tayi murmushi tace "Yi hakuri Kawa ta, wly wani baban Uzuri ne baba na ya aika ni nayi, kinsa harkar taimako ne ."


"uhum haka ne ba komai. "cewar Kamrina.

Dariya Kamrina tayi tace " wai kinga wanan matar kuwa, Inajin harda fitsari tayi.



Nan fa suka ci gaba da labari...


*Wacece wanan Fatima*


Fatima ba kowa bace ila yar sarkin Aljanun musulmai.
Dalilin haduwar tasu shine.
Watarana Apou wanda ya rike Kamrina Γ  lokacin,Kamrina nada shekaru tara Γ  duniya, watarana Apou ya fito farauta, duk da ya kasance mafarauci, kuma Mahalbi ba kowace daba yake harbi, wani mahalbi ya hango ya saita wata daba, ya harbe ta, anma wanan maharbi yana ganin wanan dabar ya harbe ta ya neme ta sama ko kasa bai ganta ba.

Apou ne yana tsakar fucewa yaga mace Γ  Kwonce cikin jini da gudu bai Wani tsaya tunanin ba ya d'auke ta da yake ba nisa da bukar sa, anan ne shida Kamrina suka taimaka ma wanan matar da magani,saida tayi kwona hudu suna mata magani, sanan ta samu lfy.



Anan ne take fada ma apou cewar ita sunan ta fatima, kuma ita aljana ce, musulma, Wani mahalbi ne ya harbe ta ya aza daba ce, anma ba komai ta masa uzuri tunda bai Sani ba.

Nan tayi ma Apou godiya, tare da d'aukan Alkawarin kula dashi da kuma Kamrina.


Wanan ne dalilin haduwar Fatima da Kamrina, tun rasuwar Apou ita ke zuwa ta kama ma Kamrina fira, takan shiga jikin takan shiga jikin ta in taga za'ayi mugunta, ko za'a cutar da ita dan ita sam bata Son zalunci. Yan mata ce Shekarun ta dari hudu, Anma sai take zuwa Γ  yar budurwa dai-dai Kamrina suke kiran junan su da Kawa.


Wanan kenan



Sai yau ne t'a dawo hankalin ta a tashe jin yanayin za'ayi cuta kuma muguwa Γ  gidan Kamrina.



Fira suka sha sosai, kamar yanda suka saba, sanan can Fatima ta numfasa, tace "kiyi hakuri Kawa ta, nasan zaki fuskanci matsaloli Γ  rayuwar auren ki, anma kiyi hakuri, bazan taba shiga tsakanin ki da mijin ki ba, domin Allah shi ke tsara rayuwar bayin sa, sanan bazan iya raba ki da kadarar ki ba, sanan ko wace mace da irin jarabawar da take fuskanta Γ  Gidan auren ta....
Dan haka ni bazan shiga
Tsakanin miji da mata ba, kuma ki Dinga hakuri Γ  duk rayuwar da kika tsinci kanki.
Sanan daga karshe ina mai baki shawara cewar ki nemi ilimi saboda shine babar matsalar farko da zaki fuskanta.. "




Sam Kamrina bata d'auki abun da wani mahinmanci ba, ita ba wani ilimin da zata nema, Fatima ce ta katse mata tunani tace "ita wanan matar zan dinga kewayo ta akai akai, domin muguwa ce kuma Mai taurin kai."

Wato kilishi. Sosai jikin Kamrina yayi sanyi, jin fatima zata tafi, sunyi fira sosai, nan Fatima ta bata wani zobe, tace "idan kina bukatar gani na ki murza wanan zobe zaki ganin....

Da wanan sukayi bankwona..

Aje zoban Kamrina tayi kasan filo din ta.



Ta kwonta.


Washe gari, Prince da Prince tare
Sukayi wanka, shida Princess sai shagwobe masa take..



Wasu abokan sa dake kasar waje, jar fata ne, dan haka wajen su goma suka hada ma Kumar Yar party, suma duka da matan su, basujin komai sai turanci, ko wane da matar sa ,shima Kuma prince da matan sa sukace yaje....


Tunda ya tashi sukayi sallah suka yi breakfast dashi da Princesse suke kunkume d'aki suna ta zaban abinda ya kamata susa yau, domin party ne za'ayi n'a girma, kowane bature yana ji da kudi, da kuma ilimi ga gayu, haka suma matan nasu hakan ne.....

Wasu kaya Kumar ya fido ma Princesse riga da wondo, rigar tana da dan tsawo tasha adon wani adon duwatsu ja ce, an rubuta Princess Γ  baya,,,
Haka shima Kumar kusan kalar kayan, shima an rubuta Prince Kumar rigunan sunyi bala'in kyau, k'arfe biyar za'a fara,

Wajen k'arfe hudu da rabi, Kumar, ya aika kuyangi su shirya Kamrina, kuyangin na zuwa Kamrina na zaune ita da bakin ta wanda suka kawo ta suna mata Salama zasu tafi bayan sun kara mata nasiha Fulani ta cika su da abun Alherie, Kamrina tayi kuka sosai kafin ta barsu..

Kuyangi suka fada mata bata yi musu ba, dan tana matukar jin kumyar Fulani kar ta kara zuwa irin na jiya....


Kuyangin na b'angaren ta ne, duk sun girme ta, da asiya da hafsa.


Cikin ruwan turare Kamrina tayi wanka, tana fitowa suka kama mata aka shirya ta cikin wani sari riga da Wondo irin na indiya, jajaye ne, sun mata matukar kyau, dirin ta da kuma kyanta ya kara fitowa.



Gashin ta aka sakar mata shi, ta d'aura dankwolin sa, gashin ya fito daga tsakiya, da mayafin su bayan ansa mata sarkar gold da yan kune, mayafin aka yafa mata a daidai wuya..

Da takalma masu tsini tayi matukar bala'in kyau..

Aka mata yar make up simple, k'arfe biyar, suka fido ta, Prince ma tare da Princesse suka fito sunyi kyau sosai suma. ....


Ganin Princesse sun kusan sankarewa.

Γ€ tarΓ© suka tafi, kadan kadan sai ya kali Kamrina...

Princesse kam abin ya cika ta, wani irin kishin Kumar yake taso mata...


Suna isa wuri yayi wuri ya hadu matuka kowa ya halara, nan aka tarbo su Kumar ana ta yaba kyan su, ana cewa yayi sa'a Anma duk Γ  cikin turanci, daga su sai wani mutu shima dj su kadai kejin hausa
....



Nan fa suka zauna Kumar ke tskiya yayin da matan nashi suka sashi tsakiya.


An fara gabatarwa, akace Kumar yazo ya nuna farin Γ§ikin sa, aiko yazo da turanci ya nuna farin cikin sa tare da godiya akayi masa tafi.. .
Nan dj yace saura bayanin uwar gida gwiwa Γ  sace dan taga kowa ita yake kalo, Γ  hankali, ta tashi ta fara da hausa dj yace da turanci ranki ya dade zakiyi bayani, domin nan duk basa jin hausa."

Zufa ce ta karyo ma Kamrina, Dan ko uwarka bata sani da turanci ba....

Nan tace ma dj suyi hakuri bazata iya ba domin Bata iya turanci ba...

Aiko dj ya fada.


Nan fa aka fara kananan maganganu, ashe kyan ne ba ilimi.

Kowa da irin maganar da yake.


Wanan abu ba karamin Kona ran Kumar yayi ba, dan wani irin tsanar ta yake ji, wani irin bakin cikin ta yake ji, yau ranar farko da aka taba Cisga sa, aka ci mutuncin sa, aka yada masa aji, cikin jama'a wani irin haushin ta da tsanar ta yake ji tasowa yayi sai Γ  inda take, kama abun maganar yayi, yaba mutanen hakuri, sanan yace sunsan yanda yake bazai taba auran jahila ba iyayen sa ne suka laka masa ita, shi ga zabin sa can, ya nuna Princesse dake zaune ....


Wani dadi taji,tana wage baki, cikin yanga ta taso tayi nata turancin aka yaba mata, shiko gogan sai wani washe hakora yake Princesse ta fida sa kumya, wulakanci sosai Kumar yayi ma Kamrina gaban Mutane, Ko ba'a fada ma Kamrina ba tasan cewa Kumar wulakanci yayi mata ganin mutane sai kalon ta suke. Γ€ hankali Γ  kunyace taje wurin dj d'akyar ta roke sa, ya fada mata duk abinda Kumar yace Γ  kanta, goge,hawayen da suka zo mata tayi, tayi masa Godiya, waje ta fita tasa dreba ya maida ta, ko kadan su Kumar basu ga fitar ta ba.









Aci gaba da gashiπŸ‡
Maimou loveπŸ˜˜πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€
*WACECE NI KAMRINA*
πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€πŸ€¦β€β™€






*NA*✍
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAHI AM*πŸ’‹






*PAGE 43-44*






Tunda Kamrina ta Shiga mota kuka ne take wanda bashida sauti, hata dreba ya tausaya mata, yana bata hakuri har ya kaita gida.


Suna zuwa gida a b'angaren Fulani tace ya aje ta.

Ya ko aje ta,yana aje ta ya juya, Fulani zaune bisa kayatatun kujerun ta irin na sarauta, falon sai wani sihirtacen kamshi ke Tashi ,sanye take da doguwar rigar shada ta alfarma, idan ka ganta sam bazaka yi tunanin cewar Kumar daga tsatson ta ya fito ba,tasha ado, gefen ta ko kuyangi ne zaune sunata bata labari .

Salama Kamrina tayi, da fara'a Fulani ta amsa ta tarbi Kamrina, tace" a'a yata barka da zuwa, "

Har kasa Kamrina ta duka ta gaisar da Fulani, sanan ta tashi taje kusan ta, ita kam Kamrina har ga Allah jin Fulani take ya mahaifiyar ta, yayin da b'angaren Fulani ma hakan take jin Kamrina.
Salamar Kuyangin Fulani tayi, bayan Sun tafi Fulani ta sake duban Kamrina suka kara gaisawa ta tambayi lfy ta, sanan ta dora da Nasiha

"yata, nasan daga ke har Kumar ba wai dan kuna son junan ku kuka yi aure ba, zabin iyaye kuka bi, anma abinda nake so daku shine kusa ma zuciyar ku hakuri, ku zauna da junan ku ,ku rike junan ku bisa gaskiya ,nasan Kumar yanada zafi sosai, anma idan kika gane masa yanada saukin kai ki zauna da abokiyar zaman ki bisa amana, insha Allah zan hada ku baki daya na muku Nasiha. , wani mataki kika Kai b'angaren adinin musulmci da kuma Boko.?


Shiru Kamrina tayi dan har ga Allah bata san abin cewa ba, can ta nisa a hankali tace "banyi ko daya ba. "


Jim Fulani tayi jin abinda tace, anma bata ga laifin ta ba, dan Kawar ta tace mata a kauye sukayi rayuwa ita da oyayen ta. Nisawa tayi, cikin ranta tace dankari, ashe kam akoi rikici, idan Kumar yasan hakan, domin tasan akidar danta ciki da waje..


Niko nace ai tuni ya Sani, an huce wurin.


A fili ko Fulani cewa tayi OK insha Allah za'a san abin yi, fira sosai Kamrina ta saki jiki sukayi, Aciki ko Fulani take Kara nuna mata dubaru na zamantakewa.


Sai gab da magariba Kamrina ta koma b'angaren su.


Tana zuwa akayi kiran salah tayi alwala tayi Sallah. Zaune tayi bayan ta gama sallah, tana tunanin wulakancin da Kumar ya mata, Ashe dama ya kaita ne dan yaci mutuncin ta, Ashe dama haka yake,,, wata irin tsanar Sa ta Kara dursuwa a zuciyar ta. Bum taji an banko k'ofa, dan saida ta zabura.

Kumar ne ya shigo shida matar Sa Princess, sai huci yake ya mayuwacin zaki.
Zuwa yayi baiyi wata wata ba ya gwora ma Kamrina mari har guda biyu, ya nuna ta da yatsa, yace "ba'a taba ci min mutuncin a bainar jama'a ba sai yau kuma a kanki, Ashe dama ke katuwar jahila Ce ban Sani ba kika bari aka d'aura aure na dake, to Bari kiji wly bakin cikin da kika kunsa min you kema sai jikin ki ya fada miki, belt din wondon Sa ya zage nan ya Fara laptawa Kamrina ita, Princess na Kara zuga Sa, Kamrina ko da taurin rai, ko gezo batayi ba, domin itafa a yanda take jin zuciyar ta saide ya kashe ta, anma bazai taba ganin gazawar ta ba, duk inda Kumar ya buga a jikin ta sai yayi ja wurin ya tashi, wani wurin ko har fata ke tashi.


Sam Kumar idanun Sa Sun rufe zuciyar Sa sai tunzura Sa take kara Yi, ganin Kamrina ta nuna Taurin Kai taki tashi ta agaji kanta hakan ba karamin Kara tunzura Sa yayi ba, saida ya mata liss Princess taga yarinyar mutane na shirin shidewa sanan ta dakatar da Kumar, baiwar Allah Kamrina zuwa yanzu akowonce take a gun, komai Nata ya Saki,idanun ta sunyi jawur, kukan m'a yaki zuwar mata, bata iya ko kwokwaran motsi, numfashin ta sama sama yake fita.



Yar da belt din hanunsa Kumar yayi yace "why na tsane ki, bansan laifin da nayi ma iyaye na suka hada ni dake ba, why why ko hanyar da na bi na ganki sai na zama ajalin ki, wawuya jaka jahila, ke a tunanin ki kyan ki zai rudar dani ne, daba kawai, gwora tun wuri kar in zama ajalin ki ki fada ma Wanda suka hada mu su warware auren nan, in ba haka ba nine ajalin ki. "

"My Prince muje dan Allah iya hakan ma ai ya isa

Please Login or Register in order to submit comment