Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

SAFNA👨‍👩‍👦*

Zaune suke a farfagiyar gidan suna hirarsu ta masoya Hafsa ta kalli Safwan ta ce "Ruhina" Tayi maganar cike da tsokanarsa, zaro Ido yayi tare da cewa "Lallai na ga alamar so kike Ruhina ta Zane ki, kin satar Mata suna" Dariya tayi sosai sannan ta ce "A'a fa Allah ya huci zuciyar Ruhin Ruhi" Shima dariyar yayi sannan ya ce "Awww haka ne kam fad'i ki k'ara fad'a, ke Kuma zuciyata ba","A'a nima Ruhinka ce na barwa Aunty Safna nawa Nima nasan zata bar min na ta" Tayi maganar cike da Shagwab'a.

"Hakane kam" Safwan ya fad'a tare cigaba da kallonta, suka cigaba da yin hirarsu sai wajen k'arfe 4pm ya bar gidansu Hafsa ya nufi gidansa, da sallama ya shiga falon Amman abin da ya bashi mamaki bai ga Safna ba, domin ya Saba Yana shigowa da ita yake fara cin karo zata rumgumeshi tayi Masa sannu da zuwa.

D'akinta ya shiga ya tarar da ita ta kifa kanta a kan guiyoyinta sai shash-shekar kukanta ka ke ji yana tashi da sauri ya k'arasa kusa da ita Yana cewa "Subhanallahi Ruhina me ya faru Baki da lafiya ne?" Yayi maganar Yana d'ago Mata kanta kallonsa take shima ita yake kallo cikin muryar kuka ta ce "Lafiya k'alau nake","to meya sa ki kuka?","bakomai" Safna ta yi maganar tare da fashewa da sabon kuka.

Hankalin Safwan ya gama tashi ya jawo Safna gaba d'ayanta zuwa jikinsa Yana kissing d'inta har sai da ta yi shuru sannan ya cigaba da tambayarta "menene Ruhina?","bakomai Ruhina" Ta fad'a tana sauke ajiyar zuciya mai nauyi "ban kai matsayin da zan san damuwarki ba? Wato baki d'auke ni a matsayin Wanda zaki dinga fad'awa damuwarki ba ko?","A'a ba haka ba ne Ruhina kai d'in kana da matuk'ar muhimmanci a wajena"."To fad'a min me ya ke damunki?" D'agowa tayi tana kallonsa ta ce "Ruhina da gaske gobe za'a saka ranar aurenka?" Tayi maganar hawaye na kok'arin zubo Mata.

Shuru yayi Yana kallonta na tsawon mintina sannan ya ce "haka ne" Hawayen da suke kok'arin zubo tana mayar dasu suka samu damar silalowa zuwa kan kuncinta, hannunsa ya saka Yana goge Mata hawayen fuskarsa ta nuna tsantsar damuwa Amman haka ya shiga b'oye damuwarsa Yana murmushi ya ce "Ruhina saboda haka shine kike yi min asarar hawayenki, to ba na son na k'ara ganin wannan kyakkyawar fuskar tana kuka, saboda tana da matuk'ar tsada da muhimmanci gurina, kin san ko da na auri Hafsa ba zan tab'a wulak'anta ki ba, karki manta fa ke ce Ruhina" haka dai Safwan yayi ta tsara Mata kalamai har ya samu ta sauko ta dena kuka, hirar soyayya suka shiga yi da nunawa junansu irin yadda suka damu da juna.

*'BANGAREN TEEMARH DA JABIR😂*

"Darling! Darling!! Darling!!!" Jabir ya shigo d'akin yana zabgawa Teemarh Kira, Teemarh kuwa tana jinsa tayi banza dashi sai ma tsaki da ta ja ta koma kan gado tayi kamar wacce take yin bacci, Jabir kuwa ya ga sanda Teemarh ta kwanta dan haka ya nufi kan gadon gadan-gadan yana yin wani shu'umin murmushi.

Kwanta yayi kusa da ita tare da jan ta jikinsa da sauri ta tashi tana zabga Masa harara sauka tayi daga kan gado ta nufi kujerun d'akin ta zauna, biyota yayi ya zauna kusa da ita "darling wai me nayi miki ne, wallahi Ina sonki sosai sweetheart","to Jabir na ji Kuma nagode Amman Dan Allah ka kyaleni ba na sonka ni" duk da cewa ya ji haushin kalamanta, Amman Kuma ya zamar Masa dole ya kwantar da kansa ya samu abin da yake so gurin Teemarh.

"To na ji Darling bakya sona kuma na san duk abin da kika yi min zuciyata ce ta jawo min tunda ta kasa dai na sonki" Yana gama fad'ar haka ya tashi ya futa daga d'akin, Teemarh ta bi bayansa da kallo sai kuma ta ji ba ta ji dad'in abin da tayi masa ba, zuciyarta ta k'arye ji take kamar ta bi sa ta ce masa ta hak'ura kuma tana sonshi amman kuma ta san Jabir farin sa ni ta ya ya zata yarda cewa ba yaudararta zai yi ba, kuma da gaske yana sonta, dole sai ta tabbatar da cewa yana sonta ba yaudararta zai yi ba sannan zata yarda dashi.

Da wannan tunanin ta tattara ta koma kan gado ba'a fi minti d'aya da kwanciyarta ba wani irin bacci mai nauyi yayi awan gaba da ita.

*'BANGAREN ABBA DA AUNTY MURJA*

Tunda ya fito daga d'akin Hajiya Asiya ya shiga d'akin Aunty Murja kwance ya tarar da ita tana karatun littafi tana ganinsa ta ajiye littafin ta tashi ta zauna tana kallonsa fuskarsa ta nuna mata cewa yana cikin damuwa dan haka ita ma lokaci d'aya ta shiga tsananin damuwa, zama yayi kusa da ita tare da zabga tagumi, hannu ta saka ta cire masa tagumin tare da girgiza masa kai alamar "A'a" sannan ta ce "Yaya hankalina ya tashi zuciyata ta shiga tsananin damuwa saboda, sarkin da yake mulkarta yana cikin damuwa, shin ya zan yi da raina".

Murmushi yayi sannan ya ce "to matata ki kwantar da hankalinki ina cikin koshin lafiya kawai dai lamarin Asiya ne yake ba ni tsoro kullum abin ta cigaba yake yi, kwata-kwata bata ba ni matsayina na mijinta" Ajiyar zuciya Aunty Murja tayi sannan ta ce "Addu'a ya kamata mu dinga yi mata, insha Allahu wata rana zata fahimci cewa kuskure take aikatawa kuma ina mai tabbatar maka da cewa zata gyara duk kuskurenta ka ji dan Allah karka saka wannan a ranka".

Wani irin farin ciki ne ya kamasa tabbas yana matuk'ar alfahari da Murjanatu domin kuwa duk sanda ta ganshi cikin damuwa hankalinta ba ya kwanciya har sai ta ganshi yana cikin farin ciki, "Allah yayi miki albarka matata","Amin mijina" Ta fad'a tare da sakar mata murmushi, daga nan suka koma kan gado suka fad'a duniyar soyayya.

*'BANGAREN SALIS*

Mama hankalinta ya tashi matuk'ar tashi tun ranar da ta je gidan Hajiya Mama take ta faman jiran ganin Nihal amman gashi yau sati biyu babu Nihal babu alamarta, Salis kuwa jikin na shi kullum k'ara tsananta yake yayi bak'i ya rame sosai, Baffa mahaifin Salis ne ya shigo d'akin bakinsa d'auke da sallama da sauri Mama ta k'arasa gurinshi tare da fashewa da kuka tana cewa "Malam ka taimaka min ka je ka dawo masa da matarsa kar ya mutu dan Allah ba ni da wani d'a shi kad'ai ne gareni ina matuk'ar sonshi sosai dan Allah ka taimaka min Malam" Mama ta k'arasa maganar tare da had'e hannuwanta guri d'aya alamun rok'o.

Murmushi Baffa yayi sannan ya ce "Sai yanzu kenan kika sauko kin ga yaronki yana kok'arin mutuwa ko? To ba da ni ba wannan abin kunyar gwanda............'' ,"Dan Allah Malam karka min haka ka taimaka min wallahi sharrin shaid'an ne da kuma matarsa Talatu da tazo ta fad'a min k'arya da gaskiya a kan Nihal ni kuma na zauna a kai, amman yanzu na gane gaskiya wallahi ba zan sake ba" Mama ta k'atse Baffa da maganar da yake son yi, Baffa ya ji tausayinta matuk'a dan haka ya kalleta sosai sannan ya ce "Zan je na bada hak'uri kuma zan yi kok'ari na ga na dawo da Nihal k'afata k'afarta amman sai kin yi min alk'awarin duk wanda ya sake kawo miki wata magana a kan Nihal k'arki ji ta, kuma ki yi masa kaca-kaca","Wallahi nayi maka alk'awarin zan doshe kunnuwana daga jin maganganun Talatu a kan Nihal".

Jinjina kai yayi sannan ya ce "to shikenan zan je na dawo da ita zuwa gobe","Allah ya kaimu" Mama ta fad'a cike da farin ciki "Amin ya rabbil'almin"Baffa ya fad'a sannan ya mik'e saboda jin kiran sallar da yayi ya ce "bari na je nayi sallah","to a dawo Lafiya" Mama ta fad'a Baffa ya fita da sauri ya nufi masallaci.

*'BANGAREN ALIYU❤️*

Kwance yake a kan tafkeken gadon da ke d'akin nasa idanuwansa suna kallon saman d'akin gaba d'aya hankalinsa da tunaninsa suna kan Khadijatullahi wani irin abu yake ji duk sanda ya dora idanuwansa a kanta, ko da ace yana cikin bak'in ciki ne idan ya dora idonsa a kanta sai ya ji wani irin farin ciki yana ratsa zuciyarsa, idan kuwa ya wuni bai ganta ba baya tab'a samun nutsuwa har sai ya dawo yayi arba da kyakkyawar fuskarta, a hankali ya furta "Dija ta" tare da sakin wani irin murmushi wanda yake nuna tsantsar farin cikin da yake ciki "wai daman ashe haka so yake? ban tab'a tunanin haka so yake da dad'i ba sai da na fad'a sonki wanda ni kai na ban san lokacin da na fad'a cikin kogin soyayyarki ba sai ganina na yi a cikinsa Dija ta" Yayi maganar a fili tare da juyawa jikinsa "Dija ta na san cewa kin tsani maza sosai, amman insha Allahu ni zan cire miki wannan tsanar da ki kai wa maza, zan tabbatar nasa kin fahimci cewa ba duka maza ne suke da hali irin na Jabir ba ina sonki babyna".

Khadijatullahi ta sauko daga iriyar muguwar k'iyayyar da take yiwa Affan har tana jin son yaron a cikin zuciyarta, Amatullahi kullum Affan yana gurinta ba ta ba wa Khadijatullahi shi har sai idan yana kuka alamar yana jin yunwa tana gama shayar dashi za ta karb'eshi tayi ta lallab'a yaron kamar wani kwai, Affan yafi sabawa da Amatullahi a kan Khadijatullahi, Nihal da Shahida kuwa ba'a magana dan kuwa kullum tare suke kwana dashi suna jin d'uminsa, ko kuka suka ga yana yi hankalinsu ya tashi har sai sun ga ya daina.

Zaune suke a tsakar gida kamar yadda suka saba kullum da yamma zasu shimfid'a taburma su yi ta hirarsu ta duniya, Aliyu ne ya fito daga d'akinsa sanye yake cikin wani yadi tsadadde brown yayi kyau sosai tafiya yake a hankali kamar wani mai sand'a har ya k'araso inda suke ya tsugunna har k'asa yana gaisar da Hajiya Mama "Ina yini Hajiya","Lafiya alhamdulillahi" Hajiya Mama ta fad'a tana sakar masa murmushi, guri ya samu ya zauna yana satar kallon Khadijatullahi wacce tun zuwansa ta had'e fuska kamar wacce ba ta tab'a yin dariya ba, Nihal ta kalli Aliyu tana murmushi ta ce "Yaya Haidar wai kwana biyun nan na ga ka na d'aukar wanka da yamma, ko dai an samo mana Aunty ne" Harara ya wurga mata sannan cikin muryarsa mai jan hankali ya ce "To ke kuma uwar 'yan sa ido, meye ruwanki da ni ko kuma so kike ki ganni kace-kace kamar wata ke" Zaro ido Nihal tayi tare da dafe k'irji kamar wacce tai gano ta ce "na shiga uku Yaya Haidar ni ce 'yar sa ido, kuma k'azama" Tayi maganar cikin muryar shagwab'a.

Shahida ta ce "Ai Other half wallahi Yaya Aliyu Haidar ya fad'a mai zurfin baki ga kwana biyun nan ba sai ki ga yana ta wani smiling shi kad'ai" Dariya su ka yi gaba d'ayansu amman ban da Khadijatullahi wacce har lokacin fuskarta babu alamar murmushi "Awww har da ke ko darling sister"Aliyu yayi maganar tare da satar kallon Khadijatullahi "Eh mana Yaya Aliyu Haidar ai ina kula da kai sosai yanzu fad'a mana wannan wace mai sa'a ce tayi sa'a sace zuciyar Yayanmu, zuciyar da take da matuk'ar tsada 'yan mata da yawa suna son su ga cewa wannan kyakkyawar zuciyar ta so su","hmmm! Shahida kenan kawai ku ta ya ni da addu'a kun ji, dan ina tsananin buk'atar haka a halin da nake ciki yanzu" Nihal ta kalli Aliyu sosai, ta fuskanci yana cikin tsananin damuwa "To Yaya Allah Ubangiji ya fitar da kai" Nihal ta fad'a tana cigaba da kallon d'an uwan na ta, Shahida ta ce "Amin ya rabbi".

Amatullahi da ta fuskanci inda maganar Aliyu ta dosa dan ta fahimci cewa Aliyu yana tsananin son Khadijatullahi, saboda irin yadda yake nuna kulawarsa a kan ta, da kuma yadda yake sadaukar da abubuwa da yawa a kan ta, amman kuma tana tausaya masa saboda ta san cewa Khadijatullahi ba lallai ta yarda ta so shi ba, kuma ko da zata yarda gaskiya sai an kai ruwa rana "Yaya Aliyu Allah ya fitar da kai ya dora ka a kan wacce ka ke so, tayi maka son da ba ka tab'a tunani ba, ta so ka da dukkanin zuciyarta" Murmushin jin dad'in Addu'ar da Amatullahi tayi masa yayi sannan ya ce "Amin Allah ya sa sister nagode sosai","Amin" Suka amsa gaba d'ayansu.

Hajiya Mama tana jefe tana jin su ita dai ba ta ce musu komai ba dan kuwa ita ma tuntuni ta fahimci cewar Aliyu yana son Khadijatullahi, ta ji dad'i sosai amman kuma ta wani b'angare na zuciyarta tana tausayawa Aliyun saboda Khadijatullahi ba lallai ta so shi ba, ta tsani maza bayan haka kuma ta tsani Jabir wanda hakan ya shafi Aliyu shi ma ta tsane shi, Aliyu ya tashi daman ya zo ne ya ga Khadijatullahi ya kalli Hajiya Mama tare da cewa "Hajiya zan je gidan Musaddik ba zan dad'e ba zan dawo","to A dawo lafiya" Aliyu ya ce "Allah yasa'' Sannan ya fita daga gidan motarsa ya shiga ya d'auki hanyarsa zuwa gidan Abokinsa Musaddik.

Hajiya Mama suka cigaba da yin hirarsu har sai da aka kira sallar magriba sannan suka tashi kowannansu ya doro alwala suka gabatar da sallar magriba, ko da suka gama suka yi addu'o'in da ake yi bayan anyi sallah sannan suka dora hirarsu daga inda suka tsaya.

*'BANGAREN TEEMARH DA JABIR💕🥀*

Sanye take da wata doguwar riga tana share d'akin rigar tayi matuk'ar kamata sosai, ji tayi an bud'e kofar d'akin da sauri ta d'ago kai suka had'a ido da Jabir wanda yake tsaye a bakin kofar ya hard'e hannuwansa a k'irjinsa yana kallonta yana murmushi, a hankali kuma ya tako zuwa inda take "Love d'inta sannunki da aiki" Kallonsa tayi kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ce "yawwa sannunka" Sannan ta cigaba da yin sharar sai da ta gama share d'akin gaba d'aya sannan ta zauna a ksn kujera ta kunna t.v, tashar Arewa 24 ta kai ta tarar ana yin episode d'in *k'addarar rayuwa* wani irin murmushi tayi dan tana bala'in son film d'in, Jabir yana kallonta dan yana tsaye a gurin da ta huce ta barshi ya k'i motsawa.


Sai da aka gama episode d'in ta juya dan ta ga inda Jabir d'in yayi dan ta ga yau bai takura mata ba, dan tayi tunanin ma ko ya fita daga d'akin ne, mamaki ya kamata ganinshi a tsaye kamar wani soja a gurin da ta huce shi kuma idanuwansa yana kanta, abin har ya so ya ba ta dariya amman ta shanye tare da cewa "menene ka ke yi a tsaye ko dai soja ka dawo ne ban sani ba?" Zuwa yayi ya zauna kusa da ita "ba dole na zama sojan k'arfi da yaji ba Love d'ita tana fushi da ni, kuma na rasa yadda zan yi nasa ta fahimci cewa ina sonta, amman ita ta fifita kallon film fiye da mijinta" Murmushi tayi sannan ta ce "hmmm Jabir kenan yaudararka wacece ban sani ba kai kan ka kasani na sanka sosai fiye da yadda baka tunani, na san wannan nacin da kake min akwai buk'atar da kake so ka cimma a kai na, dan haka wallahi ni ba zan tab'a yarda da kai ba".

Wata iriyar muguwar ajiyar zuciya ya sauke tabbas shi kansa yasan Teemarh ta san halinsa sosai, kuma yasan dole sai ya samu wannan k'alubalan wajen shawo kanta amman kuma dole sai ya tabbatar ya sa ta yarda da cewa yana sonta dan ya samu buk'atarsa a gurin Teemarh "Teemarh, nasan cewa ba za ki tab'a yarda da ni ba saboda irin abubuwan da nayi miki amman dan Allah ina so ki ba ni dama dan na tabbatar miki da cewa ina sonki","ko kuma kana son jikina ko?" Teemarh ta fad'a tana kallonsa ido cikin ido, Jabir ya rasa me zai ce mata kawai sai ya tashi ya fita wai shi a dole ya nuna mata yayi fushi, ita kuma Teemarh tab'e baki tayi sannan ta kwanta a kan kujera tana chatting, a haka har bacci ya kwasheta.

*'BANGAREN BAFFAN SALIS🚴🏽‍♀️💕*

Washe gari kamar yadda yayi wa Mama alk'awari da misalin k'arfe 2:00pm na yamma bayan yayi sallar azahar ya nufi gidan Alhaji Mansur, yana isa mai gadi yayi masa iso Alhaji Mansur ya cewa mai gadin ya kai shi falon bak'i gashi nan zuwa, haka ya fita ya shiga da Baffa falon bak'i, ba'a fi minti d'aya ba sai ga Alhaji Mansur ya shigo falon bakinsa d'auke da sallama "Assalamu alaikum" Da sauri Baffa ya tashi tsaye tare da amsa masa sallama "Wa'aikumussalam ranka ya dad'e" D'aure fuska Alhaji Mansur yayi tare da cewa "Amman ka ba ni mamaki sosai, ta ya za'ai ka na zaune ina shigowa ka tashi tsaye, raina yayi matuk'ar b'aci sosai" Baffa cikin girmamawa ya ce "Allah ya huci zuciyarka insha Allahu zan kiyaye gaba" Murmushi Alhaji Mansur yayi sannan ya ce "Allah ya sa, zaka iya zama" Ya fad'a yana nuna masa kujera".

Zama yayi sannan suka gaisa Baffa ya fara fad'a masa abin da ya kawo shi "da farko dai Alhaji ina mai ba ku hak'uri a kan irin abin da Mahaifiyar Salis tayi muku na sa ni bata kyauta ba kuma na ji matuk'ar kunyarka saboda na san anyi muku ba dai-dai ba, amman ina mai neman alfarmar da Nihal ta dawo d'akinta" Alhaji Mansur ya gyara zamansa sannan ya ce "Haba dan Allah sirikina saboda haka ne daman ka zo har nan, ai na ga Salis ba sakinta yayi ba dan haka insha Allahu gobe zan dawo da ita har asibitin kuma dan Allah kayi wa Salis d'in ya jiki kafin na zo" Baffa yayi wa Abba godiya sosai sannan ya tashi ya tafi shima Abba ya koma d'akin Hajiya Asiya dan yau anan yake.


*'BANGAREN ALIYU💃🏽💕*

Dawowarsa kenan daga gidan Musaddik sai ga Nihal da Shahida sun shigo d'akin sun zauna kusa dashi, kallonsu yayi tare da sakar musu murmushi ya ce " 'yan biyu meya faru?" Nihal ta ce "Yaya Haidar gurinka muka zo" Kallonsu yayi sannan ya ce "To gani nan 'yan k'annai na" Shahida ta ce "Yaya Aliyu Haidar wa ka ke so?" Kallonta yayi kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Khadijatullahi" Waro ido Nihal tayi tare da fashewa da kukan tausayin d'an uwana ta tabbas daman ta so ta fahimci haka saboda irin yadda yake yi mata, amman ta ya ya Khadijatullahi zata karb'i soyayyarsa bayan ta tsani kowane namiji kuma tana ganin irin yadda Khadijatullahi take nuna tsantsar k'iyayyarta a kan Yayan na su.

"Haba darling sister idan kina kukan nan sai zuciyata ta k'arye ai" Aliyu yayi maganar zuciyarsa nayi masa zafi, Shahida ta ce "Yaya Aliyu Haidar ai dole tayi kuka, kai ma kasan dai Khadijatullahi irin yadda ta tsaneka sosai ta ya za'a ta so ka, Yaya Aliyu Haidar wallahi ni............" Sai kuma ita ma ta saka kuka, hankalinsa yayi matuk'ar tashi shima yasan ya d'aukowa kan sa babban aiki amman kuma ba laifinsa ba ne laifin zuciyarsa ne, rarrashinsu ya shiga yi sannan ya samu su ka yi shiru, nan da suka d'aukar masa alk'awarin zasu taimaka masa har sai Khadijatullahi ta so shi, suka shiga kwantar masa da hankali ganin irin yadda ya damu sosai, Aliyu cikin raunanniyar muryarsa ya ce "Nagode muku sosai darling sisters, na san kun damu da ni kuma na san na d'aukowa kai na babban aiki, shiyasa na ce muku ku ta ya ni da addu'a","Insha Allah zamu ta ya ka kuma zamu taimaka maka wajen ganin Khadijatullahi ta so ka" Nan dai suka yi masa alk'awari kala-kala a kan Khadijatullahi sai sun san yadda su ka yi ta so shi.

*'BANGAREN ASIYA👹*

Yau ya kasance za'a fad'i wanda zai kawo musu wanda za'a sha jininshi bayan sun gama tsaface-tsafacensu Wannan saurayin da har yau ban san sunansa ba ya mik'e ya gama zagaye su sannan ya zo gaban Hajiya Asiya ya tsaya tare da mik'a mata wata laya ta karb'a sannan ya ce "me za ki kawo mana kishiyarki da kuma mijinki dan muna buk'atar shan jininsu" Hajiya Asiya tayi tare da cewa.
"Alhaji kuma? Gaskiya ba zan iya ba da mijina ba" Ta yi maganar tana kallonshi ido cikin ido, ransa yayi matuk'ar b'aci cikin muryar da ta ke bayyanar da tsantsar b'acin rai ta ce "To idan kuwa ba za ki kawo shi mu sha jininsa ba to ki tabbatar da cewa lokacin mutuwarki yayiii dan kuwa za mu sha jininki, gobe da daddare mu ke buk'atar ki kawo su idan kuwa ba ki kawo su gaba d'aya ba to tabbas zan kasheki ne" Ya k'arasa maganar yana dora mata wata iriyar zagegiyar wuk'a a wuyanta, gabanta ne ya shiga fad'uwa, haka dai suka gama kowa ya fito dan tafiya gidansa, Hajiya Suhaima ce ta biyo bayan Hajiya Asiya wacce har ta bud'e motarta zata shiga kiran sunanta tayi da k'arfi "Asiya" Juyawa Hajiya Asiya tayi ranta a b'ace a halin yanzu wata iryar muguwar tsanar Hajiya Suhaima ta ke ji, domin kuwa ita ta ja mata ta kawota nan gidan, ita tayi tunanin ai gurin wani boka za su je ya gama musu da Aunty Murja.

"Menene?" Ta yi maganar tana wurga mata wani irin kallo, wata iriyar dariya Hajiya Suhaima ta fashe da ita tana cewa "Ke daman kina tunanin cewa zaki sha jinin iyayen wasu, mazajen wasu, da kuma 'yaya da k'annan wasu ki ce wai ke ba za'a sha na mijinki ba, to wallahi ba ki isa ba, dole sai mun sha jinin mijinki, kuma ni ba haka na so ba, na so ace jinin wannan tambad'adden d'an naki a ka ce, amman mu je zuwa na san wata rana dole sai mun sha jinin d'an tsinanniya" Wani irin mahaukacin mari Hajiya Asiya ta zabgawa Suhaima hagu da dama sai da ta jera mata kusan sau biyar, sannan ta ce "To wawiya dabba ki sa ni burinki ba zai tab'a cika ba, dan kuwa ko Abban Jabir ba za ku sha jininsa ba ballantana yarona Jabir, ke ce tsohuwar mahaukaciya da har zaki iya ba da mahaifiyarki tabbas asara da tab'ewa su tabbata a gareki shashasha jaka mara tunani" Tana gama fad'ar haka ta shige motarta ta ja da k'arfi ta nufi gidanta.

Wannan saurayin ya saki murmushi ya ce "Asiya kenan kina wasa da Jafar uban matsafa amman Allah ya kaimu gobe za ki ga aiki da cikawa, kar Allah ya sa ki kawo su ki ga abin da zai faru da ke" Yana gama fad'ar haka shi ma ya tafi gidansa, Hajiya Suhaima kuwa nan ta kuduri niyyar sai ta lalata Ahalin Asiya gaba d'aya, ta jima tana sake-sake sannan ta nufi motarta ta ja ta bar gurin, zuciyarta fal bak'in ciki.

*'BANGAREN AMATULLAHI👰🏼‍♀*

Tafiya ta ke yi cikin nutsuwa da kuma aji, a haka har ta isa club d'in da Jabir ya ke zuwa, nesa da club d'in ta tsaya,daga gurin da take ana iya hango cikin club d'in ta jima tana raba ido ta ga ta ina zata hango Jabir amman babu alamar Jabir a gurin ta shafe kusan awa d'aya tana tsaye sai chan ta hango Jabir ya fito daga hotel yana rumgume da wata budurwa da alama ta sha ta bugu sosai "Shege d'an gidan mahaukaciya, wallahi na juyo gareka sai ka gommace kid'a da karatu" Wani yaro ne ya zo hucewa ta yi saurin kiransa "kai yaro dan Allah zo" Zuwa yaron yayi tare da cewa "ga ni" Wata takadda ta ba shi, sannan ta nuna masa Jabir tare da cewa "Wanchan za ka kaiwa wannan takaddar dan Allah" karb'a yayi tare da cewa "to zan ba shi" Yaron ya nufi gurin da Jabir yake sai da Amatullahi ta tabbatar yaron ya ba wa Jabir wannan takaddar sannan ta juya ta nufi gidansu dan ta ga halin da 'yan gidan su ke.

Amatullahi irin yadda take bibiyar Jabir ko mahaifiyarsa Hajiya Asiya ba ta yi masa, dan kuwa duk guraren da ya ke zuwa sai da ta bincikosu kuma duk motsin da yake yi tana sane dashi dan kuwa ya d'auki aniyyar d'aukarwa Khadijatullahi fansar abin da yayi mata sai ta tabbatar da wulak'antasa ta hana shi sukuni, tana shiga gidan ta tarar da abin da ya bata tsoro Inna Larai

Please Login or Register in order to submit comment