Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wajen k'arfe uku, ya bud'e idanuwansa ya dorasu a kan wasu kyawawan yammata guda uku kowaccensu sanye take cikin kananun kaya riga da wando, wani kayatatcen murmushi yayi tare da kirawo sunansu "Leemsha, summy,Ammi" kowaccen su ta amsa da "Na'am sweety". Jawo su yayi jikinsa yana shafasu suma suna mai dar masa martani (Ni kuwa 'yar mutanan zazzau nace na shiga uku Jabir sai kace bursuru🙆🏼‍♀️),"Leemsha wacce ta kwanta a kan k'irjinsa tana tana kissing d'in lips d'insa ta ce "Sweetheart meyafaru da kai ne, dan naga kabar kofa a bud'e kuma nasan indai kazo kabar kofa a bud'e kana cikin damuwa ne"

Cikin wata iriyar murya mai wani irin salo mai d'aukar hankali ya ce "Wallahi wata tsohuwar banza ce ta b'ata min rai", Leemsha kuwa bata k'ara cewa komai ba, suka shiga yin bad'alarsu.

*'BANGAREN KHADIJATULLAHI*

Yanzu Khadijatullahi ta fara sakin jikinta kuma ta rage yin koke-kokenta Amman kuma kullum ne babu ranar banza sai tayi wa Jabir mugayen addu'o'i tare da tsine masa, Amatullahi kuwa tunda ta koma gida taga babu kowa tayi wata shegiyar dariya tare da cewa "Yau asibiti yayi d'iba kenan, ai Inna Larai kad'an kika gani indai zaki dinga zagin iyayena zan cigaba da baki wahala wallahi".

Yau kamar kullum suna zaune Amatullahi ta ce"Aunty Murja ya kamata mu fara shirye-shiryen makaranta domin nan da Sati d'aya insha Allahu zamu fara lecture" Khadijatullahi ta kalli Amatullahi domin kuwa ita har ta manta da sun sami admision ta ce "Amatullahi ni na hak'ura da zuwa makarantar kawai ke ki tafi" nan da nan hawaye ya fara zuba daga idon Amatullahi cikin muryar kuka ta fara magana da cewa "kina tunanin zan iya zuwa makaranta ba tare da ke ba, tun muna yara muke tare komai namu tare muke yinsa tun daga primary har zuwa yau babu abin da nake iyawa ba tare da ke ba yanzu kuma ina murna zamu fara zuwa makaranta zamu cigaba da kasancewa tare shine rana tsaka zaki ce min ba zaki je ba ai shikenan nagode sosai" tana gama fad'ar haka ta tashj ta fita daga gidan da saurinta tana kuka, hankalin Khadijatullahi ya tashi mik'ewa tayi ta d'auki hijabi ta saka duk sa cewa bata jin dad'in jikinnata haka ta bi Amatullahi domin ta bata hak'uri, Aunty Murja ta bisu da kallo tabbas k'awancen nasu yana matuk'ar burgeta "Allah ubangiji ya barku tare har abada". Ta fad'a a fili tana murmushi.
Haka Khadijatullah ta bi bayan Amatullah tana kiran sunanta Amman Amatullah ta k'i tsayawa har sai da suka kusan isa gidansu Amatullah, Khadijatullah ta tsaya tana sauke numfashi domin cikin nata Yana tsananin bata wahala, wannan tafiyar ma da tayi ji take tamkar k'afafuwanta zasu fita daga jikinta, ganin Amatullahi tana kok'arin shigewa gidan yasa Khadijatullah ta fara tafiya a daddafe har ta Isa gidansu Amatullah, shiga gidan tayi bakinta d'auke da sallama, "Assalamu alaikum" jin ba'a amsa Mata ba tayi tunanin Babu kowa a gidan Amman tana shiga tsakar gidan ta ga Lado da wata Mata fuskarta nannad'e da band'egi, ta tsugunna ta gaisar da wannan matar Amman Bata amsa Mata ba, sai ma jan tsaki da taji matar tayi, Lado kuwa cike da jin haushi ya ce "to munafuka zaki tashi ki bar nan wajen ko sai na kwarfeki" Khadijatullah ba tare da ta cewa Lado komai ba ta tashi ta nufi d'akin Amatullahi, tayi sallama ta shiga d'akin zaune ta tarar da Amatullahi tana kuka a kan d'an k'aramin gadon d'akin nata, Tsugunnawa Khadijatullah tayi a gabanta ta rik'e hannunta ita ma tana kukan "ki yi hak'uri k'awata nasan nayi miki laifi Amman Dan Allah ki yafe min, na amince zan je makarantar in dai hakan zai saka ki cikin farin ciki, Dan Allah ki daina kukan nan haka ya isa, zan je wallahi da gaske nake" Amatullahi ta juyo fuskarta d'auke da murmushi ta ce "da gaske kike besty" Kai Khadijatullah ta gyad'a Mata alamar "Eh" Amatullah ta d'agota ta taimaka Mata ta zauna a kan gadon kusa da Amatullahi hannayensu suna had'e da juna, Amatullahi ta ce"kin ga yanzu kaya iri d'aya zamu dinga sakawa, kuma ya kamata muje kasuwa domin muyi siyayyar makarantar" Murmushin yake kawai Khadijatullah take yi dimples d'inta suna lotsawa,ba tare da ta ce komai ba.

Haka Amatullahi tayi ta tsara musu yadda zasu dinga yin shiga idan zasu je makarantar ita dai Khadijatullah "Eh", "A'a shine kawai abin da take cewa, har wajen k'arfe 8:00am na dare Khadijatullah ta tashi ta ce "To besty zan tafi gida" Mik'ewa Amatullahi tayi tana cewa "Lallai kam yau Maman baby ta dad'e a gidan nan tun 5:00 na rana gashi yanzu karfe takwas na dare" harararta Khadijatullah tayi sannan ta ce"wacece Maman babyn?" Amatullahi ta saka duka hannuwanta a kunnuwanta alamun bada hak'uri ta ce "Am so sorry besty, ai nice Maman baby kin ga idan kika haihu ni zaki bawa babyn" Khadijatullah ta ce "Ai gwanda da kika gyara zancenki dan ni bazan tab'a son cikin nan ba" Amatullahi Bata ce komai ba suka gera suka fita daga cikin d'akin a tare, nufar kofar gida suka yi Khadijatullah ta juyo ta kalli Amatullahi dai-dai lokacin da ta saka k'afafuwanta zata fita daga gidan tare da cewa "Yau ban ga Inna ba ko Bata nan" Amatullahi cikin dariyar mugunta ta ce "kin ganta mana kamanninta ne suka chanza miki shiyasa baki ganeta ba" shuru Khadijatullah tayi Bata ce komai ba Amman zuciyarta ta cika da mamakin abin da Amatullahi ta fad'a, ta juya ta cigaba da tafiya ita ma Amatullahi ta bi ta a baya sai da suka kusan isa gidan sannan suka yi sallama da juna, Amatullahi ta koma gida ita Kuma Khadijatullah ta k'arasa gidan, tana zuwa ta tarar har Aunty Murja ta kwanta bacci ita ma ta kwanta a bayanta duk da cewa ba baccin take ji ba Amman ta lumshe idonta ta kusan awa a kwance bacci Mai nauyi yayi awon gaba da ita.

*'BANGAREN GIDANSU JABIR*

Hajiya Asiya ta gama rikicewa saboda rashin ganin d'an nata Aliyu har zazzab'i tayi ta kira Abbansu domin taji ko suna tare ya ce "basa tare" haka dai ta b'oye Masa Bata fad'a masa komai ba, saboda ta san in har ta fad'a masa to ta shiga uku a gurin Alhaji Mansur, gashi Shima Jabir tun ranar da ba'a ga Aliyu ba ya fita yau kwana uku Bata saka shi a idanuwanta ba, Amman shi Bata damu ba domin ta san ba zai huce yana club da yammatan shi ba, haka dai zata zauna tayi ta sam batunta duk da irin tsananin son da take yiwa Jabir Amman ranta yana matuk'ar k'aunar Aliyu, zaune suke ita da Shahida domin Nihal tun jiya da saurayinta yazo ya d'auketa suka fita bata dawo gidan ba, Hajiya Asiya ta zabga tagumi tana kuka Shahida ce ta matso kusa da ita tana ta rarrashinta, Jabir ne ya shigo falon daman bai shi bai san wata sallama ba, dan haka ya shigo falon ko sallama bai yi ba yana fi to, wani irin kallon yabi mahaifiyar tasa da 'yar uwarta dashi na rashin mutunci sannan yayi shigewarsa d'aki babu sannu da gida ba gaisuwa, (ni kuwa 'yar mutanan zazzau nace yau Jabir har Hajiya Asiyan baka kyale ba, lallai abin naka ya huce tunanina😂), Abin mamaki maimakon Hajiya Asiya ta damu da irin yadda d'annata yayi Mata, Amman ko kad'an Bata damu ba sai ma tashi da tayi ta bi sa 'bangarensa ta tarar dashi a falo ya bage a kan kujera ya d'ora 'kafarsa d'aya a kan center table d'in da ke falon yana jijjigata, k'arasawa kujerar da yake tayi tana yi Masa sannu da zuwa "My son sannu da zuwa" Kallon kan ki ake ji ya bita dashi sannan ya tab'e Baki tare da cewa "Ai nayi tunanin ba zaki zo kiyi min sannu da zuwa ba, sai wani kuka kike tun ranar da ba'a ga Aliyu ba, Amman ni kwanana uku bana gidan nan Amman ko ki kirani ki ji lafiya" Mami ta zauna a kusa dashi tare da cewa "My Son ai kai nasan kana club ne, shiyasa ban kira ka ba, saboda nasan baka son takura, Amman shi Aliyu bai dawo ba har yanzu kuma na kira Abbanku ya ce basa tare" ta k'arasa maganar tana kuka, duk da irin yadda Jabir yake jin haushin Mamin a kan rashin kiransa da ba tayi ba sai da yaji tausayinta kuma ya ji hankalinsa ya tashi,"Mami kina nufin har yanzu Aliyu bai dawo ba" kai ta gyad'a masa alamar "eh", Jabir ya bud'e kenan zai yi magana sai ga Aliyu ya shigo falon bakinsa d'auke da sallama "Assalamu alaikum" yayi sallamar cikin sanyayayyiyar muryarsa mai d'aukar hankalin mutane, babu wanda ya amsa sallamar gaba d'aya sukai gurin da yake tsaye a bakin kofar falon, rumgumeshi Mami tayi tana fad'ar "Yarona ina ka tafi ka bar ni, nasan ban kyauta maka ba amman bai kamata kayi tafiyarka ba,kasan ina sonka sosai" zame jikinsa yayi daga rumgumar da Mami tayi masa ya k'arasa gurin Jabir suna kallon kallo sunyi kusan minti biyar suna kallon juna Jabir da ya gaji ya ce "Menene kake wani kallona kamar wanda yayi maka wani mugun abu", Wani irin murmushi mai ciwo Aliyu yayi tare da cewa "ina kallonka ne saboda kayi abin da ya kamata a kalleka kuma a kiraka da mara tausayi mara imani, Jabir wallahi kaii ba mutum bane dabba ne" Mami tayi saurin zuwa gaban Aliyu tana cewa "Aliyu baka da hankali d'an uwan naka kake cewa dabba" kallon takaici ya bi Mami dashi daba dan ita d'in mahaifiyarsa ce ba da yau yayi mata abin da ba za ta tab'a mantawa dashi ba, amman kash! ta ci dajarar ita mahaifiyarsa ce, cikin muryar da take nuna alamu yana cikin tsantsar bakin ciki da jin haushinsu ya fara magana "Mami banyi tunanin haka daga gurinki ba, ta yaya zaki bada goyon baya aka zalinci baiwar Allah marainiya to ku sani duk abin da kuke b'oyewa yanzu nasan komai kuma zan fad'awa Abba, shiyasa kace wai Auren wucin gadi kuka yi da yarinya to kasani duk abin da kayi sai an yiwa k'anwarka ko kuma 'ya'yanka kuma idan an tashi yi musu sai anyi musu ninkin abin da kayi banza,dabba,dak'ik'i" yana gama fad'ar haka ya fita ya koma b'angarensa zuciyarsa cike da bak'in ciki, Jabir kuwa ransa ya gama b'aci sai huci yake kamar wank tsohon mayun wacin zaki, Mami ta kamashi suka je suka koma ta shiga rarrashinsa cikin hassala ya ce "dalla ni ki kyaleni kina kallon wannan yaron har ni zai zo gaba na ya ce min ni dabba, dak'ik'i, banza" ya mik'e ya fara zagaye d'akin Mami ta tashi zata matsa kusa dashi ya d'aga mata hannu cikin tsawa ya ce "Mami karki matso kusani ki fice min a d'aki kafin na sauke fushi na a kan ki" fita Mami tayi ba tare da ta ce masa komai ba, 'bangaren Aliyu taje tayi ta bubbuga kofar d'akin nasa amman yayi banza da ita sai da ta gaji dan kanta, ta koma b'angarenta bedroom d'inta ta nufa taje ta kwanta tana sake-sake a cikin ranta maganar Aliyu ce ta fad'o mata da yake cewa sai ya fad'awa Abbansu sauke nannauyan ajiyar zuciya tayi tare da cewa "duk yadda zanyi, zanyi Aliyu ba zan tab'a barin ka ka fad'awa Abbanku komai gamai da Auren wucin gadin da Jabir yayi ba" ta saka wannan ta saka wannan har bacci ya d'auketa.

*B'ANGAREN AMATULLAHI DA KHADIJATULLAHI*

Yau Lado ya shirya tsaf zai d'aukarwa mahaifiyarsa fansar abin da Amatullahi tayi mata, wajen k'arfe 9:00pm na dare Lado ya d'auki ruwan zafin da ya tafasa shi ya nufi d'akin Amatullahi dashi, yayi sa'a kuwa kofar d'akin a bud'e take dan haka ya kutsa kansa a kwance ya tarar da ita tayi lanfa dan ta ji shigowar Ladon Amman tayi kamar bacci take yi, "Lado kenan idan kasan wata ai baka san wata ba daman nasan duk daran dad'ewa zaka zo d'aukarwa mahaifiyarka fansar abin da nayi mata shiyasa kullum cike nake da shirin zuwanka" Zabagegiyar wuk'ar da take gafenta kasancewar Amatullahi ta kashe wutar d'akin shiyasa Lado bai ga wuk'ar ba idonsa ya riga da ya rufe kawai burinsa ya watsawa Amatullahi ruwan zafin a fuska, ya d'aga d'an k'aramin bokitin da ya d'ebo ruwan zafin zai shek'a mata ai kuwa sai jin saukar wuk'ar yayi a hannunsa ya saki bokitin a kasa ruwan zafin ya zuba a k'afafuwansa ya kwala wani irin jijitatcen ihuuuuuuuu.......

Anan zan tsaya sai ku dakace ni a gobe idan Allah ya kaimu domin jin yaya zata kasance tsakanin Lado da Amatullahi shin Aliyu zai fad'awa Abba tak'adirancin da yake yi ko kuma Mami zata hanashi yaya rayuwar Jabir zata kasance anan gaba dashi da mahaifiyarsa da kuma k'anwarsa Nihal ku cigaba da biyo ni 'yar mutanan zazzau domin jin yadda zata kasance.
Da gudu Lado ya fita daga d'akin Amatullahi yana zabga ihu kamar zai zauce, Amatullahi wacce take tsaye a kan gadonta ta shek'e da wata irinyar dariya tare da cewa "An gaya maka ni d'in ta wasa ce, da ka tsaya hannunnaka zan cire gaba d'aya d'an iskan banza". A tsakar gida Lado ya tarar da Inna larai tana jiran fitowarsa zuciyarta cike da farin cikin d'annata zai d'aukar mata fansa, jin ihun Lado da tayi ne yasa hankalinta ya tashi gashi kuma tana tsoron shiga d'akin Amatullahi saboda tana tsoron abin da zai biyo baya gashi daman bata gama jinyar fuskarta ba, da gudu Lado ya k'araso gabanta har yana ban gaje ta yana fad'ar "inna 'yar ta'adda ce Amatullahi 'yar daba ce" ya fad'a a rud'e hannunsa yana fitar da jini kamar da bakin k'warya, Inna a gigice ta ce "me tayi maka Lado?" Lado ya ce "Inna ta sare ni a hannuna, kalli ki gani" da kyar Inna ta iya bud'e idonta domin tun ranar da Amatullahi ta dannata a cikin kaskon mai ta dena gani sosai, kuka Inna larai ta saka tana magana cikin sarkewar murya "gaskiya yarinyar nan ta cika tantiriya,bari ubanta yazo wallahi bazan iya zama da ita ba, ko ni ko ita wallahi" ta k'arasa maganar tare da shigewa d'akinta tana kuka shi kuma Lado ya fita zuwa *BUBA SPEACIAL HOSPITAL* domin a duba shi.

*Wace ce Amatullahi?*

Mahaifin Amatullahi Malam Shu'aibu d'an asalin garin kano ne yana da rufin asirinsa dai-dai gwargwado mahaifiyar Amatullahi Asma'u 'yar abokin Malam Shu'aibu ce wanda shima ya kasance yana da rufin asirinsa, Malam Shu'aibu ya dad'e yana tsananin son Asma'u amman ya kasa fad'awa mahaifinta Malam Abbakar saboda a ganinsa kar ayi mata dole dan ya san indai ya fad'awa Malam Abbakar to zai amince ne kuma shi sam baya son ya auri Asma'u ba'a son ranta ba, haka dai ya cigaba da dakon soyayyar Asma'u a cikin zuciyarsa, ranar da bazai tab'a mantawa da ita ba domin a ranar ne burinsa ya cika na auran Asma'u, Malam Abbakar ne ya aiko har gida a kan yana nemansa a gidansa, cike da tashin hankali Malam Shu'aibu ya nufi gidan aminin nasa saboda shi a tunaninsa kodai wani abun ne ya faru a gidan, yana zuwa aka yi masa iso har cikin falon gidan da sallama ya k'arasa ya shiga falon, lokaci d'aya kuma ya shiga cikin matsanancin mamaki ganin gaba d'aya 'yan gidan a falon gidan ga kuma Malam liman da kuma mai unguwa Malam Tanko, bayan sun gaisa ne Malam Shu'aibu ya zauna a kan kujera, Malam Abbakar bayan yayi sallama tare da yin wasu addu'o'i sannan ya fara koro bayanin abin da yasa ya tara su gaba d'ayansu, "Malam liman da ranka ya dad'e mai unguwa abin da yasa na tara ku anan dan ku zame mana shaida nii Abubakar na bawa Abokina kuma aminina Malam Shu'aibu auren Asma'u, kuma ina so a yanzu ba sai anjima ba a d'aura musu aure, kuma nayi wannan shawarar ne tare da amincewar Asma'u ba wai dole nayi mata ba" wani irin farin ciki ne ya lullub'e Malam Shu'aibu ya dinga tunanin wai mafarki yake yi ne ko kuwa da idonsa biyu ashe akwai ranar da burina zai cika na auren muradina Asma'ul Husna, yana cikin tunanin ne ya ji muryar Malam liman yana yi masa Allah ya sanya alkhairi daga nan suka tashi shi da mai unguwa suka fita nan, Malam Abbakar ya tashi daga gurin da yake da dawo kusa da aminin nasa "Ina yi muku addu'ar Allah ya baku zaman lafiya ya ba ku zuri'a d'ayyiba, na san zaki yi mamakin abin da yasa na had'a auranka da Asma'u nayi hakane ba dan komai ba saboda bana son irin yadda kake zaune babu wacce zata dinga kula da kai, ina yi muku fatan Alkhairi zata iya d'aukar matarka ka tafi da ita domin ta ri ga da ta shirya", kallonsa Malam Shu'aibu yake cike da tsantsar son Malam Abbakar ya ce "ban san ma da wasu irin kalmomi zan yi amfani dasu ba wajen gode maka nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi". Haka suka d'an tab'a hira Malam Shu'aibu ya tashi da niyyar tafi gida Malam Abbakar ya cewa Asma'u da ta tashi ta bishi, haka ta tashi tana kukan rabu da 'yan uwanta ta bi mijinta Malam Shu'aibu mahaifiyarta tana biye da ita da k'aton akwatin kayanta Allah sarki, motar Malam Abbakar suka shiga aka saka akwatin a boot driver ya ja su zuwa gidansu Malam Shu'aibu, suna zuwa driver ya shigar musu da akwatin sannan sukai sallama suka shiga gidan tare Asma'u ta rufe fuskarta da mayafi, suna shiga Inna Labara mahaifiyar Malam Shu'aibu ta tare su fuskarta d'auke da mamaki "Shu'aibu kai da wace?" cike da jin kunya ya ce "Inna Asma'u ce 'yar gidan Abbakar, nan Inna ta shiga fara'a ta ja Asma'u suka je suka zauna a kan taburma, shima ya d'auko taburma ya ajiye a kusa dasu Malam Shu'aibu ya fad'awa Inna duk abin da ya faru, wata iriyar gud'a inna tayi sannan ta shiga sakawa Malam Abbakar Albarka tashi tayi ta gyara musu wani d'an k'aramin ta d'auki akwatin Asma'u ta kai d'akin, abinci ta zubowa Asma'u ta ci sosai, tun daga ranar Malam Shu'aibu ya cigaba da nunawa Asma'u soyayya da tsantsar k'auna har Allah ya bata ciki wanda ba'a gane shi ba har sai da cikin ya kai wata hud'u murna gurin Malam Shu'aibu ba'a magana, haka ya cigaba da bata kyakkyawan kulawa ta musamman har Allah ya sauketa lafiya ta haifi 'yarta mace a gida a wata ranar litinin, ranar suna aka sakawa yarinya suna Amatullahi haka gidan ya cika damk'am da 'yan uwa da abokan arzik'i sai wajen k'arfe 10:00pm na dare sannan aka watse aka bar Asma'u daga ita sai Inna da yarinyarta Amatullahi, Amatullahi ta taso cikin gata saboda Malam Shu'aibu ya d'auki son duniya ya dorawa Amatullahi hatta yaye shi ya yayeta duk inda zai je da ita yake zuwa, Asma'u kuma bata k'ara samun ciki ba har sai da Amatullahi ta kai shekara 14 a duniya wannan cikin yazo mata da laulayi har yayi sanadiyar mutuwarta Allah sarki Malam Shu'aibu yayi kukan rashin matarsa mai ladabi da sanin ya kamata bashi kad'ai ba har Inna ma tayi kukan rashin Asma'u Malam Abbakar ne ya shiga rarrashin Malam Shu'aibu tare da yi masa nasiha mai ratsa zuciya, a ranar da Asma'u ta cika shekara d'aya da rasuwa, Inna Laraba Mahaifiyar Malam Shu'aibu ta koma ga Allah, tashin hankali ya k'ara aurar Malam Shu'aibu daman gashi bai gama fita daga cikin damuwar rashin matarsa ba, ya rasa abin da yake yi masa dad'i haka ya cigaba da rayuwa daga shi sai Amatullahi a gidan duk inda zashi tana nanik'e dashi, ranar da Inna tayi arba'in Malam Abbakar yazo masa da maganar auren wata bazawara 'yar abokinsa Larai, Malam Shu'aibu ya amince saboda daman yana buk'atar wacce zata dinga kular masa da Amatullahi, haka Malam Abbakar ya shige gaba aka d'aura auren Malam Shu'aibu da Larai, ya gyara gidan da suke zaune aka k'ara d'akuna, ka kawo Amarya Larai d'akinta tare da yaronta Lado, tun da Larai ta ga irin son da Malam Shu'aibu yake yiwa Amatullahi ta d'auki tsanar duniya ita da d'anta suka dorawa Amatullahi suka fara takura mata amman sai suka ga abin yafi k'arfin su saboda Amatullahi ba k'aramar 'yar bala'i ba ce dan komai sukai mata sai ta rama bata tab'a barinsu, Allah ya had'a Amatullahi da wata 'yar layin su Khadijatullahi suka kulla aminci kullum Amatullahi tana gidansu Khadijatullahi idan Khadijatullahi ta ga lokacin zuwa Amatullahi yayi bata zo ba haka zata d'auki hijabi taje gidan ta ga lafiya haka suka cigaba da rayuwa cikin so da k'aunar junansu, Inna Larai kuwa bakin ciki kamar zata yi hauka ganin tayi shekara biyar a gidan Malam Shu'aibu amman ko b'ari bata tab'a yi ba kuma tana tsananin jin bakin cikin irin yadda Malam Shu'aibu yake nuna damuwarsa a kan 'yar tasa kuma kullum cikin yi mata siyayyar tsire yake mata, shiyasa kullum ita ma take k'ara jin tsanar Amatullahi da kuma bakin cikin rashin samun cikin da bata yi ba.

*Wannan shine takaitatcen tarihin Amatullahi, yanzu zan dora labarinmu*

Yau ya kama su Amatullahi zasu fara zuwa makaranta, Amatullahi ta tattaro kayan da zata saka tazo gidan su Khadijatullahi domin ta shirya a gidan, kayan iri d'aya suka saka komai nasu iri d'aya sun yi kyau sosai, haka suka fita daga gidan zuciyoyinsu cike da farin ciki, Khadijatullahi ta tsinci kanta cikin wani irin farin ciki sosai mara misaltuwa, haka suka yiwa Aunty Murja sallama tayi musu addu'o'i ta samun nasara, suka kama hanyarsu ta zuwa poly, 'bangare d'aya suka cike gaba d'ayansu wato law, suna isa cikin makarantar suka tarar ana shirin shiga lecture bayan sun tambayi ina ne ajinsu aka nuna musu suka nufi ajin cikin farin ciki da annashuwa, suka shiga ajin bakinsu d'auke da sallama wasu daga cikin 'yan ajin suka amsa musu, suka nemi guri a gaba suka zauna suna yin hirarsu har Malami ya shigo kowa yayi shuru aka shiga lecture.
*'BANGAREN GIDANSU JABIR*
Jabir kuwa fitowa yayi daga d'akinsa a fusace ya nufi d'akin Aliyu ya shiga bugawa da k'arfinsa yana huci, Aliyu wanda yake kwance a kan d'aya daga cikin kujerun falon nasa yana ji yayi banza sai ma kunna t.v da yayi ya kai tashar Arewa 24 inda ya tarar suna film d'in *Rud'in zuciya* duk da kasancewar shi ba ma'abocin kallon indian film ba ne amman yau dan ya musgunawa Jabir ya k'unna, kiran layin Abba ya shiga yii ringing d'aya biyu Abba ya d'aga "Assalamu alaikum aminci Allah ya k'ara tabbata a gareka yarona" wani irin murmushi yayi wanda yake d'auke da tsantsar jin dadi "Wa'alakumussalam Abbana kai ma haka, ya dubai d'in Abba yaushe zaka dawo ina son yin magana da kai kuma gaskiya maganar ba zai yiyu muyi ta waya ba" ya k'arasa magana cikin wani irin yanayi na bakin ciki, Abba tunda ya ji Aliyu ya ce akwai maganar da zasu yi yasan maganar tana da matuk'ar muhimmanci dan haka bai yi niyyar dawowa kwanan nan ba amman ya cewa Aliyu "Insha Allahu zuwa jibi zan dawo, amman kowa lafiya dai ko" Aliyu ya kasa d'aurewa hawaye ne ya shiga zubo masa ya share da hannunsa cikin muryar kuka ya ce "Abba Jabir ne, Jabir yana zubar mana da mutunci Abba Jabir ya lalata rayuwar marainiyar Allah yarinyar da bata ji ba bata gani ba saboda son zuciyarsa shi da Mami, Abba labarin yana da tsayi Abba dan Allah ka dawo gobe gidan nan yana shirin tarwatsewa, Mami, Nihal da Jabir gaba d'aya sun had'u sun lalata rayuwar yarinya, Abba in takaice maka Nihal yanzu yau kwananta uku bata gidan nan wai saurayinta ne yazo ya d'auketa suka fita" ya k'arasa magana yana kuka mai tsima zuciyar mai sauraro, Abba kuwa sakin wayar yayi bayan ya gama jin duk bayanin Aliyu yanzu haka Asiya ta mayar masa da gida, ai kuwa babu shiri yasa aka yi masa visa zai biyo jirgin k'arfe biyar na yamma dan bazai ma bari ya kwana ba, Aliyu ya katse kiran sannan ya shiga kok'arin goge hawayensa.

Masu karatu na san

Please Login or Register in order to submit comment