Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bari ki tozarta ba, Kuma ba zan yi miki irin abin da Yaya Jabir yayi miki ba, saboda ni da shi ba halinmu d'aya dashi ba, zaki iya gwada ni ta kowacce hanya domin ki tabbatar da abin da nake fad'a miki".

"Yaya Aliyu Ina tsoro kada.............." Sai ta fashe da kuka mai cin rai,hankalin Aliyu ya tashi "Final choice meyafaru?Dan Allah ki daina kukan nan haka" Shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya ta ce "Yaya Aliyu kayi min Alk'awarin ba za ka tab'a cutar da ni ba, kuma idan munyi aure za ka rik'eni da amana" Murmushi yayi ya ce "Indai wannan ne matsalarki Matata kada ki damu, Kuma nayi miki Alk'awarin ba zan tab'a cutar da ke ba","To na amince da soyayyarka Yaya Aliyu".

"Da gaske babyna" Khadijatullah ta gyad'a masa kai alamar eh, anan fa Aliyu ya shiga zuba mata kalaman soyayya, sai wajen k'arfe 8:45pm sannan Aliyu ya rakata har bakin kofar falo ya mik'a mata Affan sannan su ka yi sallama ya koma d'akinsa ita kuma ta shige falon, kai tsaye bedroom ta nufa ta kwanta, bacci Mai nauyi yayi awon gaba da ita.

*'BANGAREN TEEMARH DA JABIR😂*

Zaune suke a kan kujera suna kallon *so k'addarar zuciya* Arewa 24 Jabir ya janyo Teemarh jikinsa tana shafata, Yana sumbatar kuncinta kallonsa Teemarh tayi tare da cewa "Dan Allah darling ka bari mu gama yin kallon nan, sai mu yi abin da ya dace","A'a darling yanzu nake so please ki tafi mu kwanta".

"Ya salam darling Dan Allah........." Toshe bakinta yayi sannan ya d'auketa cak ya kai ta kan gado, kayan jikinta ya shiga kok'arin cire Mata, Teemarh ta saka kuka tana cewa "Darling Wai meyasa ba ka son, farin cikina kawai Kai burinka ka samu abin da daga gareni" Jabir Wanda yake kok'arin zame Mata riga jin abin da Teemarh take fad'a yasa ya tashi daga kanta, kayansa ya mayar jikinsa ya fita daga d'akin a fusace, Teemarh ta saka kuka, ita ma ta mayar da kayanta ta bi bayansa da sauri, Amman Bata ga koda k'eyar Jabir ba, barantana shi, durk'ushewa tayi a k'asa tana kuka, ji tayi an d'agota da sauri ta juya tare da tashi tsaye tana ci gaba da yin kukan, Aunty Murja ta kalleta sosai sannan ta ce "Fatima meyafaru ki ke kuka?","Bakomai Mummy" Teemarh tayi maganar cikin shash-shekar kuka, "ba za ki iya fad'a min damuwarki ba Fatima" Kukan Teemarh ya tsananta ta ce "Darling ne" Tayi maganar tana goge hawayen fuskarta.

Aunty Murja ta ce "koma Mai yayi miki bai kamata ace kin zo kina yin kuka ba, ya kamata ki zauna ki nutsu ki kirasa, sai ku tattauna a kan matsalarku, ta haka ne za ku fuskanci juna" Teemarh tayi murmushi ta ce "Nagode Mummy zan yi amfani da shawararki insha Allahu" Daga nan kowannan su ya koma d'akinsa, Teemarh ta d'auki wayarta ta shiga kiran layin Jabir Amman a kashe wayar take Dan haka ta zauna ta cigaba da yin kallonta Amman zuciyarta tana gurin Jabir.

*'BANGAREN SAFNA😔👏🏽*

Safna ta fito da gudu daga d'akinta tana murmushi suka had'a ido da Safwan ta matso kusa dashi zata rumgumeshi, yayi saurin tureta yana cewa "karki matso kusa da ni" Yayi maganar fuskarsa a d'aure, Safna ta ce "Ruhina ka yi hak'uri na tuba ba zan k'ara ba, Amman Dan Allah karka hukunta ta wannan hanyar ka yi min duk abin da ya dace da ni ka ji Ruhina" Kallonta yayi kamar ba zai yi magana ba sai Kuma ya ce "Akwai sharad'ai guda uku da zan fad'a miki, idan har ki ka amince dasu to shikenan komai zai huce" Safna ta ce "wad'anne sharad'ai ne?" Zama Safwan yayi ita kuma ta tsaya tana son jin wane sharad'i ne wannan "sharad'i na farko shine karki sa ke yin kishi a kan Hafsa ina son ki d'auketa tamkar Zahra k'anwarki wacce ku ka fito ciki d'aya, Sharad'i na biyu kuma karki sa ke yi min zancen yaushe Khalid zai dawo saboda ni nasan gurin da na kai shi babu abin da za'ayi masa na kuntatawa Sharad'i na uku kuma karki sa ke yi min maganar Hafsa idan muna tare da ke, idan kin yarda da su za ki iya zuwa" Safwan yayi maganar tare da bud'e hannayensa alamar Safnan ta zo jikinsa.

Hawaye ne suka shiga gangaro mata a hankali ta fara tafiya kamar mai sand'a, ta fad'a jikinsa tare da rushewa da wani irin kuka, tana tsananin jin kewar yaronta amman kuma anyi mata katangar k'arfe dashi, tana ji tana gani ba ta da damar da za ta tambayi yaronta, sai ya zama laifi, "na amince da sharad'anka ruhina amman dan Allah ka kawo min yarona koda sau d'aya ne na ganshi, idan na ganshi ba zan sake cewa a kawo min shi ba nayi maka alk'awari" Tausayinta ya kamashi amman ya zama dole yayi haka, domin ya k'ara saka son Hafsa a cikin zuciyar Safna "to shikenan zan kawo miki shi gobe insha Allahu","to nagode" Safna ta fad'a cikin rawar murya, daga nan suka dora soyayyarsu daga inda suka tsaya.

*Team Khadijatullahi where you😂😂yau fa ta gwangwaje ku da kalamai masu dad'i*

*'BANGAREN HAJIYA ASIYA DA ALHAJI MUKHTAR🤔*

Sai da Hajiya Asiya ta kwana biyu sannan ta farfad'o wajen k'arfe 8:00am na safe Alhaji Mukhtar yana zaune kusa da ita ya zuba mata ido yana kallonta cike da so da k'aunarta, a hankali ta fara bud'e idanuwanta ta zuba su a saman d'akin abubuwan da suka faru suka shiga fad'o mata hawaye na zuba daga idanuwanta, yanzu shikenan ta san gurin wad'annan wahalallun iyayen nata zata koma ta ci gaba da shan wahala, Alhaji Mukhtar ya saki murmushi tare da kiran sunanta "Asiya" A hankali ta juya ta kalli mai kiran na ta ganin Alhaji Mukhtar yayi matuk'ar ba ta mamaki tare da jefo masa tambayoyi "Ina ne nan? Me na zo yi nan? Waya kawo ni? Ina yarana? Ina Abban Jabir" Murmushi yayi mai cin rai jin ta ambaci sunan mijinta amman ya danne ya fara ba ta amsoshinta "kina asibiti ne, na je gidan tsafi ne na tarar da ke kwance cikin jini shine ya d'aukoki na kawoki, kuma tun da na kawoki babu wanda ya zo gurinki amman gaskiya nayi mamaki sosai yaranki ko mijinki babu wanda ya nemeki kenan hakan na nufin basa buk'atarki a rayuwarsu, ko kuma basu damu da ke ba?".

Hawaye Hajiya Asiya tashi zubarwa tana cewa "A'a yarana suna sona sosai ba za su iya juya min baya ba kuma"............"To gashi sun juya miki kuwa tunda yau kusan kwananki goma babu wanda ya zo asibitin nan kuma har gidan na je amman su ka yi min rashin mutunci suka ce basa sonki a rayuwarsu" Alhaji Muhktar ya fad'a cikin yanayin damuwa dan kuwa ya fad'i haka ne kawai dan Hajiya Asiya ta ji haushi kar ta ce zata koma gidan mijin na ta, dan kuwa shi bai ma san ina ne gidan Hajiya Asiyan ba, kuma bai san waye mijin na ta ba.

"Yanzu haka su Jabir za su yi min ban yi tunanin haka daga garesu ba kuma nima insha Allahu zan fita a rayuwarsu kamar yadda nima suka fita a rayuwata" Hajiya Asiya tayi magana tare da goge hawayen fuskarta, Alhaji Mukhtar kuwa murmushi yayi ganin cikin k'ank'anin lokaci yayi nasarar raba tsakanin Hajiya Asiya da mijinta da kuma yaranta yanzu shikenan dole yasan shi za ta bi ya kai ta gidansa ya samu ya biya buk'atarsa da ita dan a iya zaman da su ka yi da ita ya fuskanci cewar Hajiya Asiya macece mai shegen son kud'in tsiya, dan haka ya san da zarar yana sakar mata kud'i to bashi da wata damuwa,haka dai yayi ta rarrashinta tare da cusa mata tsanar yaranta da kuma mijinta.

*'BANGAREN INNA LARAI DA LADO😂😣*

Tun ranar da Inna Larai ta dawo gida, yaronta da iyayenta suka d'auki karan tsana suka dora mata domin sun ji labarin irin abin da ta aikata domin a cewarsu kaf danginsu babu mazinaci, dan haka suka cireta daga cikinsu wani d'an k'aramin d'aki suka ba ta wanda ake kiwon kaji a cikinsa, kaji ne gaba d'aya a cikin d'akin dan su kansu kajin ma d'akin yayi musu kad'an, a haka amman Inna Larai take rab'awa take zama duk a takure, ga shi sunyi mata gargad'in kar su sake su ga k'afarta a waje idan har ba su suka bata izinin ta fito ba, ba'a ba ta aminci sai kowa ya ci ragowar da aka rage shi za'a gefa mata a jikinta ya zube kajin su yo kanta su yi ta caccakarta sun cin abincin, wata ran kuwa ba za su bata ba haka zata wuni da kwana ba ta ci abinci ba.

Lado kuwa duk irin abin da ake yi wa mahaifiyarsa ko a jikinsa dan wani abun ma shi yake tsara yadda za'ayi mata kuma shine ya hana a dinga bata abinci sai dai ragowar da aka ci aka rage, saboda a cewarsa wai ta haka za'a horata idan wani ya nemeta da niyyar yayi zina da ita ba za ta yarda ba, Yau kamar kullum Zaituna 'yar k'anwar Inna Larai Hafsatu ta d'auki kwanon abincin da aka tarkatawa Inna Larai abincin a aka ci aka rage ta nufi d'akin kajin "Ke! Ke Zaituna tsaya" Lado wanda ya fito daga d'akinsa ya dakatar da Zaituna daga shiga d'akin, juyowa tayi tare da cewa "Na'am Yaya" Karb'ar kwanon abincin yayi daga hannun Zaituna ya k'arasa d'akin kajin ta window ya jefawa Inna Larai abincin ai kuwa kaji suka yo kanta suna caccakarta suna cin abinci Lado ya saki dariya tare da cewa "Kaii wannan abin yana saka ni nishad'i sosai" Sai ya juya ya shige d'akinsa dan daman abin da ya fito dashi kenan.

Zaituna kuwa hawaye ne suka shiga gangaro mata tana matuk'ar jin tausayin Inna Larai sosai kuma tana son ta taimaka mata amman bata da halin da za ta yi hakan dan kuwa ko ta ce zata taimaka mata Lado ba zai tab'a barin tayi ba, nan wata dabara ta fad'o mata tayi murmushi "Inna insha Allahu zan yi kok'arin na taimaka miki ta wannan hanyar, ba zan bari ki wulak'anta ba ai k'addara tana kan kowa" Tayi maganar a zuciyarta daga nan ta juya ta koma d'akinta.

Inna Larai kuwa kuka take kamar ranta zai fita takaici da bak'in ciki had'e da nadama sun gama kasheta yanzu da bata biyewa D'an Ladi ba da tuni tana chan gidanta babu wanda ya isa yayi mata wannan wulak'anci, anan ta fara tunanin yadda za ta yi domin ta tsaratar da kanta daga wannan uk'ubar da ake yi mata amman ta rasa mafita tayi kuka har ta godewa Allah.

Wajen k'arfe 9:00pm na dare bayan kowa ya kwanta Zaituna ta fito rik'e da kwanon abinci tana sand'a a haka har ta isa d'akin kajin ta shiga chan ta hango Inna Larai ta takure a jikin bango, k'arasawa tayi kusa da ita tare da kiran sunanta "Inna" Da sauri Inna Larai ta d'ago tare da cewa "Na'am Zaituna ke ce?","Eh Inna ni ce" Tayi maganar tare da zama kusa da ita ta bud'e mata kwanon da ta zo dashi Shinkafa da miya ce wacce ta ji kifi "Ga shi Inna ki ci, kuma Insha Allahu kullum da daddare bayan kowa yayi bacci zan dinga kawo miki abinci kina ci" Murmushi Inna Larai tayi hawaye suna bin kuncinta ta ce "Nagode sosai yarinyata, kowa ya guje ni amman kuma ke baki gujeni ba, nagode da kulawarki","bakomai Inna ki yi sauri ki cinye abincin kar wani ya fito" Haka Inna Larai ta karb'i kwanon ta dinga zabga loma daman wata iriyar bak'ar yunwa ta ke ji, gaba d'aya ta cinye abincin, sannan ta mik'awa Zaituna kwanon tare da cewa "nagode" Zaituna ta fita daga d'akin ta nufi na ta d'akin tana sand'a har ta shige ta ja kofar ta kulle, ta ajiye kwanon sannan ta koma kan gado ta kwanta tana jin wani irin dad'i a zuciyarta da ta samu ta taimakawa Inna Larai.

*'BANGAREN ABBA DA AUNTY MURJA🥰💃🏽*

Yau Aunty Murja ta tashi da rashin lafiya komai ta ci sai ta amayo shi, hankalin Abba ya tashi haka ya shiryata suka je asibiti likita yayi mata gwaje-gwaje anan ya gano cewar tana d'auke da d'an k'aramin ciki ne sati hud'u, farin ciki gurin Abba ba'a magana, haka ya rik'e Aunty Murja suka fito daga asibitin suka nufi gida, Aunty Murja gaba d'aya kunyar Abba ta ke ji kamar ta nitse a k'asa, Abba shima ya fuskanci haka, kuma ya ji ya k'ara jin son Aunty Murja a cikin zuciyarsa, suna isa gida ta fito ya zagaya ya bud'ewa Aunty Murja murfin motar ta fito kanta a k'asa tana shirin wucewa ta barshi ya rik'e hannunta "Menene haka kuma Murjanatu? Ba na so ki daina kinji" Kai ta gyad'a masa alamar eh "Yauwa ko kefa kin ga babu inda kika tab'a ganin ance wai mata tana jin kunyar mijinta, ko saboda kina da ciki yanzu shine zaki sauya min ki daina kula dani kamar yadda ki ke yi?","A'a ba zan sauya maka ba" Tayi maganar kanta a k'asa "To d'ago ki kalleni","ba zan iya ba, dan Allah kar ka ce dole sai na kalleka kuma karka yi fushi dani" Abba ya b'ata fuska sannan ya ce "Wato ban isa na ce ki yi abu ba ki yi ko?" Hawaye suka shiga zubo mata dan kuwa ba za ta iya kallonsa ba, gaba d'aya wata iriyar muguwar kunyarsa ta ke ji tun da likita ya sanar masu cewar tana da ciki "Kayi hak'uri dan Allah ba haka ba ne" Tayi maganar cikin muryar kuka.

Abba zuciyarsa tayi matuk'ar shiga bak'in ciki saboda ganin zubar hawayen Aunty Murja amman kuma duk da haka dole ya san yadda zai yi ya cire mata wannan sabuwar kunyar da ta tsiro da ita yau, hannunta ya saki sannan ya nufi hanyar da zata sadashi da babban falon, Aunty Murja ta bi bayanshi tana kuka babu kowa a falon ko da yake babu kowa daman a gidan Teemarh ce sai Jabir shi kuma Jabir ba ya zama a gidan Teemarh kuma ba ko yaushe take fitowa babban falon ba kullum tana d'akinta, Suna shiga d'akin Aunty Murja ta sha gabansa tana kuka kuma har lokacin kanta na k'asa kok'arin tureta Abba yake amman ta rumgumeshi tare da k'ank'ameshi sosai tana kuka "Kayi hak'uri dan Allah zan kalleka wallahi da gaske na ke yi zan kalleka" D'agota Abba yayi yana murmushi "To kalleni" Yayi maganar tare da kafeta da ido, d'agowa tayi ta zuba idanuwanta a cikin na sa tana hawaye "Yauwa ko kefa Matata" Yayi maganar yana goge mata hawaye murmushi Aunty Murja tayi tare da cewa "ka hak'ura kenan Yaya?" Kai ya gyad'a mata alamar eh ta rumgumeshi ya kamata suka zauna a kan kujera yana fad'a mata kalamai masu dad'i.

*Ni kuwa nace to Abba asha soyayya lafiya, amman ku yi a hankali karku kone nayi gidansu Safwan ni kam😂*

*'BANGAREN SAFWAN DA SAFNA🤗❤️🌹*

Kamar yadda yayi mata alk'awarin cewar zai kawo mata Khalid, haka kuwa a ka yi washe gari bayan ya dawo daga office ya biya gidansu Hafsa ya d'auki Khalid bayan ya cewa Hafsan gobe zai dawo dashi suka nufo gida tare dashi, Safna tana zauna tana kallo ta saka t.v a gaba kai sai kayi tunanim cewar kallon film d'in da ake yi ta ke yi saboda yadda ta kaf t.v da ido amman kwata-kwata hankalinta ma baya kan t.v yana kan yaronta da kuma mijinta dan ganin yau Safwan d'in ya dad'e ta san gurin Hafsa ya tafi kuma ga shi bata da damar tambaya sai ya ce tayi masa laifi.

Ta share guntun hawayen da ya zubo mata, ji tayi an dafata tayi saurin d'agowa anan idanuwanta su ka yi tozali da yaronta Khalid cikin tsananin murna ta jawo shi jikinta tana cewa "Yarona kai ne","Eh Mommy ni ne nayi kewarki sosai" Safna ta ce "nima haka darling nayi kewarka sosai i miss you more" Safwan wanda ya hard'e hannuwansa a k'irji yana kallonsu ya had'a hannuwansa guri d'aya tare da yin tafi, da sauri Safna ta kalli gurin da yake sam tama manta dashi kallon Khalid tayi sannan ta ce "je ka d'akinka ka huta ko? Na san ka kwaso gajiya","Eh mommy bacci ma zanyi"Khalid ya ce tare da nufar d'akinsa bai jira jin abin da Safna za ta ce ba.

Kallonta ta maida gurin Safwan wanda ya d'aure fuska kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa, tashi tayi ta matsa kusa dashi tana murmushi "Ruhina ka yi hak'uri kasan nayi missing d'in Khalid sosai, kuma"..........
D'aga mata hannu yayi tare da cewa "yi shuru wannan shine dalilin da yasa nace zan bar yaron chan gurin Hafsa saboda ke kwata-kwata ida yana kusa da ke bakya damuwa da ni ko kuma menene damuwata bakya yin hira da ni gaba d'aya lokacinki yana k'arewa ne a gurin dan haka yanzun nan zan mayar dashi dan ba zai zo ya hana ni jin dad'ina ba"

Safna ta kalleshi ta ce.

*Eid Mubarak 💞✨ Fans Ina yi muku barka da sallah da fatan an ci nama lafiya, aci nama dai a hankali kar azo a dinga ce min Dijartyy a kawo filajin😂*

"Ruhina wallahi ba haka ba ne kai ma kasan ka na da matuk'ar muhimmanci gurina ina sonka ina tsananin k'aunarka Amman tunda ka ce haka insha Allahu zan dinga ajiye duk abin da nake ina kula da kai" Safwan ya ce "To shikenan tunda kin ce haka Ruhina Ina sonki nima fiye da yadda ki ke sona" Murmushi Safna tayi sannan ta ce "To yanzu ka huce ko Ruhina" Kai ya gyad'a alamar eh, tayi kissing d'insa a kunci tare da cewa "Shiyasa nake sonka mijina, to yanzu tashi muje ka yi wanka" Harararta yayi ya ce "Kiyi min wanka dai" Safna ta ce "to shikenan tashi muje nayi maka wanka" Tashi yayi suka shiga d'akin Safwan d'in, toilet suka shiga tare su ka yi wanka sannan suka fito kayan bacci suka saka sannan suka kwanta bacci.

_Yau fa kuyi hak'uri ba zan yi typing mai tsayi ba saboda zan je na ci naman sallah🤣_

*'BANGAREN KHADIJATULLAH DA ALIYU💔💃*

Yau an tashi da ruwan saman tun asuba ake yi sai wajen k'arfe 11:00am na safe aka tsaya Khadijatullah ta fito tsakar gida ta tsaya bata da wani buri irin ta ga Aliyu ya fito ta kalleshi ta ji dad'i a zuciyarta, Amatullahi ce ta fito daga d'aki tana kallon Khadijatullah fuskarta kunshe da murmushi dafa Khadijatullah tayi ta ce "Dijan Yaya Aliyu meya faru?","Bakomai Bestyna me ki ka gani kike tambayata?" Amatullahi ta ce "Kawai dai na ga Mata ta fito tana jiran mijinta ya fito" Harararta Khadijatullah tayi sannan ta shige falon Dan ta San indai ta tsaya to Amatullahi sai ta k'ureta, Amatullahi ta bi bayanta tana yin dariya ciki².

Aliyu kuwa bacci yayi tayi dan sai wajen 11:45am ya tashi ya shiga wanka ya shirya cikin wani yadi mai tsada green colour, ya fito ya nufi falo domin ya gaishe da Hajiya Mama kuma ya ga sahibarsa, Yana shiga ya tarar da Hajiya Mama zaune a kan kujera tana kallon labarai ita kad'ai ce "Assalamu alaikum" Hajiya Mama ta d'ago tana murmushi tare da amsa masa sallamar ta sa "Wa'alaikassalam" Zama yayi a k'asa wajen k'afafuwanta "Ina kwana Hajiyata","Lafiya k'alau d'an albarka ka tashi lafiya" Aliyu ya ce "Lafiya alhamdulillah Ina su Amatullahi ko sun tafi makaranta ne?" Hajiya Mama ta ce "A'a yau ai lahadi ba su je ba suna cikin d'akinsu" Aliyu ya ce "Ohh haka ne fa" Daga nan suka zaune suna yin hirarsu irin ta jika da Kaka.

Khadijatullah wacce tunda Aliyu yayi sallama take son ta fito Amman ganin idanuwan Amatullahi a kanta yasa ta share rumgume take da Affan a hannunta gaba d'aya hankalinta Yana wajen Aliyu, mik'ewa tayi ta nufi hanyar da zata sadata da falon taji muryar Amatullahi tana cewa "Ina za ki je kuma bayan muna hira","Zan je gurin Hajiya Mama" Ba ta jira abin da za ta ce ba ta fita da sauri.

Shahida tayi murmushi ta ce "Sister kin ga Allah ya amshi addu'armu sister ta fara son Yaya Aliyu Haidar" Amatullahi ta ce "Hakane kam dan d'azu ma jiransa ta fita yi a waje shine na je na fatattakota" Dariya Shahida tayi sosai sannan ta ce "Kaii Sister ki barta su soye abin su mana ke kuwa" ita ma dariyar tayi ta ce "To na barsu Sister Shahida" Daga nan suka cigaba da yin hirarsu ta duniya.

Khadijatullah tana fita su ka yi ido biyu da Aliyu murmushi ya sakar mata, nan ta ji wani irin dad'i ya tsarga mata cikin jijiyoyin jikinta, zuciyarta kuwa ta cika da farin ciki, Zama tayi a kan kujera tare da sunkuyar da kanta "Sannu da hutawa Hajiya" Ta fad'a kanta a sunkuye "Yawwa Khadijatullah ya babana har yanzu bacci ya ke yi?","A'a ya tashi idonsa biyu" Hajiya Mama ta tashi tare da zuwa gurin da Khadijatullah take zaune ta karb'i Affan d'in sannan ta shige bedroom d'inta, Shuru falon ya d'auka na tsawon mintina 10 babu Wanda yayi magana a cikin su Aliyu ya kafeta da kyawawan idanuwansa Yana k'ara jin k'aunarta na shiga zuciyarsa, Khadijatullah ta ce "Ina kwana" Murmushi yayi sannan ya amsa "Lafiya alhamdulillah Gimbiyar Mata yau Kuma rowar kyakkyawar fuskar nan ake min ba'a d'ago a kalleni ba","A'a ba rowa nake maka ba" Tayi maganar cike da jin kunyarsa, Amatullahi da Shahida ne suka fito tare da zama kusa da Khadijatullah "Muma ba za'ayi ba mu ba, mun zo a koya mana soyayya" Amatullahi tayi maganar tana kallon Khadijatullah.

Aliyu ya ce "Kun zo dai kawai ku takura mana, muna cikin soyayyarmu, idan soyayya ku ke son koya kowaccenku tayi zuciya ta samo saurayi mana gauraye kawai bamashinshini" Yayi maganar Yana dariya, Shahida ta ce "Laaa Yaya Aliyu Haidar mu ne gaurayen? Gaskiya ka taro match" Amatullahi ta ce "Fad'a masa dai dan kuwa ya taro babban match" Aliyu ya ce "Ahh abin na d'an sauk'i ni da nake da messi, please ku tashi ki bamu waje kun ji darling sisters" Tashi su ka yi Amatullahi ta ce"To zamu ba ku guri ku zanta Amman fa ba mu hak'ura ba" Aliyu ya ce "To na ji" Fita su ka yi tsakar gida suka zauna a kan taburma, Khadijatullah suna fita ta d'ago kai ta kalli Aliyu sannan ta ce "Kaii Yaya Aliyu Amatullahi rigimarta tayi yawa na san ita ta giggib'o Sister suka fito" Dariya yayi sosai sannan ya ce "Bar ni da su ai na fuskanci takura mana suke son su fara yi" Murmushi tayi ba tare da ta ce masa komai ba, nan Aliyu ya shiga kashe Khadijatullah da kalaman soyayya masu ratsa zuciya da jinin jiki.

_Ni kuma na ce Bari na bar ku haka Masoya na rankaya gidan Nihal da Salis iyayen soyayya🤣💃_

*'BANGAREN SALIS DA NIHAL💕💖*

Kwance take a jikinsa tana ta zuba masa shagwab'a iri-iri, shi kuma sai lallab'ata ya ke yi kamar wata kwai "Babyna ni gaskiya ba zan yarda ba, sai mun je tare Allah ba za ka bar ni a gida ba idan kuwa ka fita wallahi kuka zan tayi Kuma har ka dawo ba zan daina ba" Salis ya ce "Haba babyna so kike zuciyata ta buga, tunda haka ne to ni na hak'ura da fitar ma tunda daman yamma tayi" Murmushi Nihal tayi tare da cewa "Da gaske ka ke babyna" Salis ya ce "Eh mana Baby Nafisa kuma Baby Nihal Kuma Babyn baby" Dariya tayi sosai ta ce "Sweetheart duk ni kad'ai wannan sunan, to nagode sosai Babyn baby, can't love you less" D'aukarta yayi kamar wata jaririya suka shige bedroom suka rufe kofa.

_ni kuma er sa ido na ce sai na bi su na ga me za su yi Amman kuma sun kulle kofar da key🤣sai na yanke shawarar kawai nayi gidan Teemarh da Jabir😂_

*'BANGAREN TEEMARH DA JABIR😂💖*

Teemarh tana kwance tana jiran dawowar Jabir ganin har k'arfe 12pm na dare bai dawo ba, ta kifa kanta da guiyoyinta tana kuka kamar ranta zai fita, dan ta san Jabir yana chan yana shek'e ayarsa da yammata dan kuma hausawa sun ce Mai hali baya fasa halinsa, ji tayi an dafata da sauri ta d'ago rinannun idanuwanta ta zubawa

Please Login or Register in order to submit comment