Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mahaifiyarki da hannunki ai asara tabbata a gare😭)*

Alhaji Mansur kuwa sai da ya gaji dan kansa sannan ya zube a k'asa yana huci, Aunty Murja ta zauna kusa dashi tana cewa "Yayana wai meyake faruwa ne?" Kallonta yayi sannan ya shiga bata labarin duk abin da yake faruwa, hankalinta yayi matuk'ar tashi ta ce "daman nan gidan matsafa ta kawo mu ta ce wai bikin 'yar k'anwarta za'ayi" Alhaji Mansur dai bai k'ara cewa komai ba ya tashi ya fara sauka daga benen ita ma Aunty Murja bin bayansa tayi, suka bar Hajiya Asiya a kwance jini ne kawai yake ambaliya a jikinta.

*Wannan kenan😉karku manta fa yanzu aka fara kuma comments da sharhinku shi yake k'ara min k'warin guiwar yi muku typing more comments more typing*

*'BANGAREN SAFWAN DA SAFNA😩😢*

"Ruhina dan Allah ka tsaya ka saurareni wallahi ban yi haka dan in b'ata maka rai sai dan.............." D'aga mata hannu Safwan yayi fuskar nan ta sa babu alamar murmushi "Dakata nace ki dakata min Safna ina son ki bud'e kunnuwanki da kyau dan ki ji abin da zan fad'a miki daga yau karki k'ara kirana da wani ruhinki dan ni ba ruhinki ba ne, Shashasha kawai" Yana gama fad'ar haka ya fita daga falon da sauri zuciyarsa cike da tausayin Safna dan ya san maganar da ya fad'a mataa gaskiya za ta yi mata ciwo sosai, motarsa ya shiga tare da kallon kofar falon yana jin son Safna yana ratsa masa zuciya dan yasan duk saboda shi ne, ta ke yin haka "Ina sonki sosai Ruhina ya zama dole nayi miki haka domin ba na son ki dinga nunawa Hafsa k'iyayya, ba na son ya zama kanku a rabe ya ke, ina son ku zama tsintsiya d'aya mad'aurinki d'aya, ko dan saboda yaranmu ka da su taso su ga kanku a rabe su ma ya zama kansu ba a had'e yake ba, na san ba zan sami matsala daga gurin Hafsa ba, ke ce zaki ba ni matsala kuma na san hakan da nayi shi zai sa ki sauko daga masifaffan kishin da kika dorawa kan ki".

Yana gama fad'ar haka ya ja motar mai gadi ya bud'e masa gate d'in gidan da gudu ya ja motar ya nufi ma'aikatarsu, Safna kuwa Safwan yana fita ta zube a kan kujera tana kuka, "meyasa ruhina za ka min haka saboda wata banza, haba ruhina kasan ina tsananin sonka sosai kuma dole nayi kishi a kanka" Haka tai-tayin surutai barkatai tana kuka tamkar ranta zai fita, kamar wacce aka tsikara ta tashi ta shige d'akin Safwan ba san me tayi a d'akin ba amman ta d'auki kusan mintina biyar a d'akin sannan na ganta ta fito ta shige na ta d'akin hmm ni kuwa nace Safna ki dai bi a hankali kishi ba hauka ba ne, daga nan na tarkata d'an komatsena na nufi gidan Hajiya Mama wajen Aliyu dan na ji ya zata kasance.

*'BANGAREN ALIYU😭❤️🗝️*

Da sassafe wajen k'arfe shida ya fito daga d'akinsa ya nemi kujera ya zauna tare da zabga tagumi idanuwansa suna kan k'ofar falo dan ba shi da wani buri a yanzu irin ya ga hasken idanuwansa Khadijatullahi, saboda ba zai tab'a iya jure rashin ganinta da bayayi ba, yana nan zaune sauro duk sun isheshi da kuka a kunne sai gani yayi ana kok'arin bud'e kofar falon nan ya shiga Addu'ar Allah yasa Khadijatullahi ce, ai kuwa ya yi babbar sa'a Khadijatullahi ta fito rik'e da Affan a hannunta shi kuma sai tsala kuka yake, Aliyu ya tashi ya nufi gurin da take fuskarsa d'auke da murmushin jin dad'in ganinta "ba ni shi na rik'e miki" Aliyu yayi magana yana mik'a hannunsa, had'e fuska Khadijatullahi tayi tare da kawar da kanta jefe tana jan tsaki.

"Malam ka matsa min daga hanya zan huce" Tayi maganar cikin tsawa, "Haba Dija ta wai ni menene laifina, wallahi ni da gaske nake ina sonki kuma auren........." Saukar marin da ya ji ne yasa shi yin shuru bai k'arasa maganar ba, ya dafe gurin yana kallonta cike da mamaki, "Idan baka fita a harka ta ba, to wallahi kad'an ma ka gani, kuma idan ka cigaba da dorawa kanka soyayyata to tabbas za ka mutu ko kuma nace lokacin mutuwarka yayi, dan ni ba zan tab'a sonka ba na tsaneka kai ba ma kai kad'ai ba gaba d'aya mazan duniyar nan na tsanesu" Tana gama fad'ar haka ta wuce fuuuu ta shige falon saukar bak'i.

Aliyu kuwa wasu zafafan hawaye ne suka shiga zubo masa ya d'auki kusan mintina talatin a tsaye har sai da ya ji k'afafuwansa suna rawa sannan ya samu ya lallab'a ya koma d'akinsa zuciyarsa kamar zata fashe ga wani irin zafi da ya ji zuciyar ta sa take yi masa, sai bugawa ta ke yi da k'arfi.

Kwanciya yayi a kan gadonsa tare da runtse ido hawaye na cigaba da zuba daga idanuwansa babu abin da yake maimaitawa sai innalillahi wa inna ilaihi raju'un a haka har ya fara jin sauk'i a cikin zuciyarsa, wani irin bacci mai nauyi yayi awan gaba dashi, Allah sarki Aliyu ka ba ni tausayi Allah ya kawo maka sauk'i.

*'BANGAREN JABIR😂*

Tun da su Abba suka fita hankalinsa ya k'i kwanciya dan kuwa a kan idonsa suka fita gashi Abba yayi masa gargad'i a kan kar ya biyosu, wannan dalilin ne yasa bai bi bayansu ba, yana nan zaune a falo jugum yana jiran ganin Abba dan kuwa Jabir ya d'auki alk'awarin duk wanda ya sake ya sha jinin mahaifinsa to tabbas sai ya tabbatar ya kashe shi koma d'an gidan uban waye, Shigowar su Abba da Aunty Murja ne yasa Jabir mik'ewa da sauri yana sakin wata aijiyar zuciya tare da yin murmushi "Abbana kun dawo kai amman na ji dad'i sosai hankalina ya kasa kwanciya, dan ban san halin da ku ke ciki ba" Abba yayi murmushi tare da cewa "muna lafiya ya kamata ka je ka kwanta dare ya yi" Jabir ya ce "to Abba" Sannan ya shige d'akinsa Aunty Murja ta bi bayansa da kallon dan kuwa wani irin haushin Jabir d'in ta ke ji,duk san ta ganshi sai abin da yayi wa Khadijatullahi ya fad'o mata a rai, Alhaji Mansur ya kama hannunta suka shige d'aki, ni kuwa dijartyy nace ba sai na shiga d'akin ba, dan babu kyau shiga hurumin da ba na ka ba😂

Jabir yana shiga d'akinsa Teemarh ta rumgumeshi tare da kissing d'insa a kunci tana cewa "Darling shi ne ka tafi ka bar ni a d'aki" Tayi maganar cike da shagwab'a, Jabir ya ce "Ki yi hak'uri darling kin ji ki min uzuri yau d'in ne na shiga tension" Teemarh ta ce "Allah sarki darling sannu" Abin da ta ce kenan a kan kujera suka zauna Teemarh ta kwanrar da kanta a kan k'irjinsa tare da lumshe idonta shi kuma Jabir abin nema ya samu babu a kan haka ya shiga kissing d'inta har sai da ta kai su sun koma kan gado, ni kuma ina ganin sun nufi kan gado nayi saurin fitowa daga d'akin na koma gidan Hajiya Mama wajen Khadijatullahi.

*'BANGAREN KHADIJATULLAHI🤔*

Tana shiga d'akin ta ci karo da Amatullahi tana tsaye ranta ya gaba b'aci da lamarin Khadijatullahi nan ta shiga zazzaga mata masifa ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba "Wallahi kin ba ni mamaki k'warai da gaske yanzu har za ki iya d'aukar hannu ki mari Aliyu saboda kawai ya ce yana sonki, to insha Allahu wallahi tallahi zan je nayi magana da Aliyu ba zai sake tun kararki da maganar soyayya ba kuma sai na fad'awa Aunty Murja duk abubuwan da kike aikatawa, saboda anan kin ga Hajiya Mama da Shahida suna kyaleki shine har kika samu damar marin Aliyu wai me kike tak'ama dashi ne, kin tsani maza ko, to da ke da tsanar sai na had'a ku na zazzageku wanne ai wulk'anci ne da rashin sanin darajar d'an adam" Amatullahi ta k'arasa maganar tare da zama a kan kujera sai huci ta ke yi.

Ita kuwa Khadijatullahi hawaye ne ya shiga zubo mata saboda maganganun Amatullahi sun yi matuk'ar tsaya mata a rai kuma sun bata haushi sosai ashe akwai ranar da za ta zo Amatullahi tayi mata irin wannan rashin mutuncin zaunawa tayi a k'asa tare da rumgume Affan tana kuka tare da cewa.
"Besty meyasa ki ka yi min haka, saboda..........." Cikin masifa Amatullahi ta dakatar da ita da cewa "Ba na son ki ce min komai saboda ni ba na mu'amala da wacce ba ta san darajar d'an adam ba, kuma tabbas sai na tabbatar na fad'awa Aunty Murja duk abin da ki ke yi" Tayi maganar ba tare da ta kalli Khadijatullahi ba, "Dan Allah ki yi hak'uri ki fad'a min abin da zan yi dan na gyara kuskurena karki yi fushi da ni amman ni na yarda ki fad'awa Aunty Murja tayi min duk hukuncin da ya dace da ni amman dan Allah karki ce za ki dai na min magana dan hakan zai saka zuciyata cikin tsananin damuwa" Ta k'arasa maganar tana had'e hannayenta guri d'aya alamar rok'o tana cigaba da yin kukan.

"To idan kina so kar inyi fushi da ke, ki je ki ba wa Yaya Aliyu hak'uri kuma ki karb'i soyayyarsa idan kuma ki ka k'i to babu ni babu ke har abada" Amatullahi tayi maganar fuskar nan ta ta a d'aure, Khadijatullahi cikin rawar murya ta ce "zan yadda ki ke so" Amatullahi ba ta k'ara ce mata komai ba ta d'auki Affan wanda ya ke kan cinyar Khadijatullahi ta shige bedroom ta bar Amatullahi zaune tana kuka, duk da cewar ta tsani Aliyu amman ya zame mata dole ta je ta nuna masa ta amince da soyayyarsa kuma ta bashi hak'uri saboda Amatullahi kar ta yi fushi da ita, dan haka ta barshi a zuwan idan gari ya waye sai ta je har d'akinsa suyi magana.

Shahida duk abin da suke fad'a duk tana ji dan bata wani jima da tashi ba, tayi farin ciki sosai duk da cewar ita Khadijatullahi ba'a son ranta zata karb'i soyayyar Aliyu ba, amman ta san hakan zai faranta ran d'an uwan na ta kuma daga wannan lokacin Khadijatullahi za ta san ba duka maza ne suka taru suka zama d'aya ba kuma halin Jabir da Aliyu sam ba d'aya yake ba, shi Aliyu yana da kyakkyawar zuciya kuma ita gaskiya tunda suke dashi bai tab'a yin wata budurwa ba, dan 'yan mata ba sa gabanshi, a haka dai wani sabon baccin ya kwasheta wanda yake cike da mafarkai kala-kala a kan Khadijatullahi da Aliyu.

Misalin k'arfe 7:30am na safe Khadijatullahi ta gama had'a musu breakfast ta shirya cikin wata shadda pink ta saka hijabinta har k'asa ta d'auki abincin Aliyu ta nufi d'akinsa a bakin kofar ta tsaya tare da kwankwasawa, Aliyu wanda yayi shirinsa na zuwa office amman saboda irin damuwar da yake ciki, ji yake duniyar tayi masa zafi dan a halin yanzu gaba d'aya baya cikin nutsuwarsa, jin ana kwankwasa kofar ne yasa ya zauna a kan kujera tare da cewa "Shigo" Dan shi a tunaninsa Shahida ce ta zo kawo masa breakfast d'insa.

Khadijatullahi ta shiga d'auke da sallama a bakinta, da sauri Aliyu ya mik'e jin muryar zab'in zuciyarsa dan kuwa ko a mafarki ya ji wannan daddad'ar muryar to tabbas sai ya farka daga baccin nasa, "Dija ta" Aliyu ya fad'a tare da kafeta da manyan idanuwansa yana murmushi hawaye na kok'arin zubo masa, Khadijatullahi ba ta amsa ba har sai da ta ajiye masa abincin a kan table d'in da yake tsakiyar d'akin sannan ta dawo gurin da yake tsaye tasa guiwoyinta a k'asa tana cewa "Dan Allah Yaya Aliyu ka yi hak'uri da abin da nayi maka d'azu, ba zan sake ba" Wani irin farin ciki ne ya shiga ratsa zuciyar Aliyu ya k'ara fad'ad'a murmushinsa, shima ya tsugunna suna kallon juna ido cikin ido da sauri Khadijatullahi ta kawar da kanta dan jin wani irin abu da ya tsarga mata zuciya saboda Aliyu yana da matuk'ar kwarjini ba za ta iya jurewa su yi kallon ido cikin ido ba.

"My Heartbeat yau ke ce da kanki ki ka zo ki ba ni hak'uri gaskiya na ji matuk'ar dad'i fiye da tunaninki ina sonki sosai dan haka tun lokacin da abin ya faru na mance dashi na d'aukeshi tamkar mafarki na yi muku na farka fatana shi ne ki karb'i soyayyata" Murmushin yak'e Khadijatullahi tayi "nagode sosai ni zan tafi besty tana jirana zamu tafi makaranta" Aliyu ya ce "to ai nima Office zan je, ai sai na sauke ku a makarantar","to shikenan" Abin da kawai Khadijatullahi ta fad'a sannan ta tashi tayi masa sallama ta fita.

Aliyu kuwa ya rasa inda zai tsoma ransa ji yake tamkar anyi masa albishir da gidan Aljanna haka ya zauna ya bud'e abincin soyayyan dankalin turawa ne sai kuma kwai da aka soya shi daban ya ci sosai dan ji yayi kamar kar ya daina ci, "gaskiya matata ta iya girki" Yayi maganar a fili yana murmushi, jakarsa ya rataya a kafad'arsa sannan ya fita zuwa d'akin Hajiya Mama.

A zazzaune ya tarar dasu sun gama shirin su da alama shi suke jira Shahida ta ce "kai Yaya Aliyu Haidar shi ne ka shanyamu sai mun yi lating" Harara ya wurga mata sannan ya k'arasa gaba Hajiya Mama ya tsugunna ya gaisheta ta amsa tana sakar masa murmushi sannan ya mik'e tare da juyawa nan suka had'a ido da Khadijatullahi tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa murmushi yayi tare da cewa "to muje ko darling sisters karku makara" Sai da su ka yi wa Hajiya Mama sallama sannan suka fita Aliyu yana biye da su a baya, suna zuwa motar Amatullahi da Shahida suka shige bayan motar Khadijatullahi za ta shiga Amatullahi ta ce ta shiga gaban motar ranta ya b'aci sosai wato wulak'ancin da za su yi mata kenan Aliyu ne ya bud'e mata kofar gaban motar babu musu ta shiga ya rufe ya za ga ya mazaunin driver ya zauna sai da ya kalli Khadijatullahi sannan ya ja motar ya nufi makarantarsu Khadijatullahi sai da ya sauke su sannan ya kai Shahida gurin aikinta shima ya huce na shi gurin aikin.

*Wannan kenan💃🏽*

*'BANGAREN SALIS DA NIHAL🌹💍*

Salis da Nihal wata iriyar sabuwar soyayya su ke nunawa junansu kamar su had'iye juna, kullum suna manne da juna kamar cingum, zuwa aiki ne kawai yake raba ta dashi nan ma idan zai tafi ta dinga yi masa kuka kenan ya tafi da ita, yau ma hakan take yayi shirinsa kyaf na zuwa aiki Nihal ita ma ta shirya ta saka hijabi har k'asa tana rataye da jakarsa a kafad'arta suna tafiya suna yin hirarsu ta masoya har suka iso gurin motar Salis Nihal tayi saurin shigewa gaban motar ta rufe, Salis ya saki murmushi dan kuwa ya fahimci kwana biyun nan wata iriyar sabuwar shagwab'a Nihal d'in ta ke ji.

Bud'e motar yayi ya zura kansa yana kallonta ita kuma sai turo masa baki take idanuwanta sun cicciko da kwalla za ta yi kuka ta ce "Yau ma ba za ka je da ni ba ko?" Tayi maganar hawaye na gangarowa daga idanuwanta, hannunsa yasa yana goge mata hawayen fuskarsa ta chanza zuwa yanayin damuwa ya ce "Am sorry Babyna na saka ki kuka, kin san ina sonki da yawa ba na son kowane banza ya dinga kalle min fuskar kyakkyawar matata, ina matuk'ar kishinki sosai kin ga Ma'aikatarmu gaba d'ayanmu maza ne, babu mata wannan shine dalilin" Nihal ta ce "to na ji zan zauna a mota" Salis ya shiga motar dan kuwa yasan daman idan Nihal tayi irin wannan rigimar sai yayi da gaske yake shawo kanta "Ta ya ya zan bar gimbiyata a cikin mota ni kuma na tafi office kina tunanin zan iya barinki a cikin mota, to Wallahi Nafisa ba zan tab'a tafi na barki a cikin mota ko da kuma na minti d'aya ne barantana na awanni.

Murmushi Nihal tayi jin ya fad'i sunata na gaskiya dan ba ta tab'a jin ya fad'a ba sai yau, irin yadda ya fad'i sunan nata cikin wani irin salo yayi matuk'ar sakata nishad'i kuma ta ji tana matuk'ar k'aunar sunan na ta, "to amman ni ina jin tsoron in zauna ni kad'ai a gidan nan" Murmushi yayi ya ce "to sai na ka na kai ki gidan Mama idan na dawo sai na biya na d'auke ki","Yawwa to shikenan" Fita Salis yayi ya koma mazaunin driver ya ja motar ya nufi gidan mahaifiyarsa, suna isa suka fita a tare suka shiga gidan, Mama tayi matuk'ar yin farin cikin ganinsu tare nan suka gaisheta sannan Salis ya tashi ya fita dan yayi lating ya shiga motarsa ya ja ya nufi ma'aikatarsu.

*'BANGAREN HAJIYA ASIYA👹*

Kwance take a gadon asibiti Alhaji Mukhtar wanda suke tare dashi a k'ungiyar matsafa yana zaune a kan kujera ya zabga tagumi yana kallonta, Alhaji Mukhtar jiya ya makara bai je gidan da wuri ba har bayan da Abba da Aunty Murja suka tafi sannan ya iso gidan yana shiga ya tarar da Hajiya Asiya kwance male-male cikin jini, bai tsaya yin wani tunani ba shine ya d'auketa ya sakata a mota ya kawota asibiti, wani irin sonta ne yake ji yana ratsa masa cikin jini daman ya dad'e yana son ya nuna mata yana tsananin sonta amman ya rasa yadda zai yi ya sanar da ita, amman abin da ya shige masa duhu shine meyafaru da gidan matsafan nasu ko da wani ne yayi musu lek'en asiri yayi musu shunan 'yan sanda? Amman bashi da me basa amsa dan haka ya watsar da tambayoyi ya shiga yin tunani a kan soyayyar da za su yi da Hajiya Asiya da zarar ta amince masa, shi kuma a shirye yake da yayi komai saboda ita.

Haka dai har wajen k'arfe biyar babu alamar Hajiya Asiya zata farfad'o ko da yake daman likitan ya ce masa zata jima sosai kafin ta farfad'o dan kuma ba k'aramin duka a ka yi mata ba, dan da ba'a kawota asibitin da wuri ba da zata iya rasa ranta, Alhaji Mukhtar ya tashi ya fita domin ya samarwa kansa abin da zai saka a bakinsa wani babban shago ya shiga yayi musu siyayya kusan leda biyar manya-manyan ledoji ne kuma gaba d'aya kayan ciye-ciye ne, ya dawo d'akin da aka kwantar da Hajiya Asiya ya zauna yana jiran farfad'owarta.

*POLY🏛️💕*

Tafiya suka suna hirarsu ta k'awaye suna dariya har suka iso gurin da suke zama, kowaccen su ta samu guri ta zauna Hafsa ta kalli Khadijatullahi ta ce "Amaryar Yaya Aliyu ina gaisuwa" Harararta Khadijatullahi tayi kawai ba tare da ta ce komai ba, sai jijjiga Affan ta ke yi Amatullahi ta ce "Lallai kuwa dai gwanda kema ki fad'a mata ta gyara halinta, dan kuwa duk wanda ya ce yana sonka ai ya gama yi maka komai","Wannan haka yake besty tabbas Yaya Aliyu yana matuk'ar son Khadijatullahi amman ita ta tsaya yi masa shakara (yanga)" Dariya Amatullahi tayi ta ce "Ai kuwa gwanda ta dai na dan kuma Aliyu d'aya ne tamkar da dubu, ba irinsa ake yi wa yanga ba","tabbas"Hafsa tayi maganar tana kallon Khadijatullahi.

Khadijatullahi ta ce " besty wai ba na ce miki shikenan ba"Tayi maganar cikin muryar kuka idanuwanta a kan Amatullahi, kallonta Amatullahi tayi ta ce "Ohh ni yau na ga abin da yafi k'arfina, ce miki nayi ki yi kuka" Khadijatullahi ta goge hawayen da suka zubo mata tare da sauke ajiyar zuciya, Hafsa ta dafata tana cewa "Besty wallahi Yaya Aliyu ba halinsu d'aya da wannan d'an iska kema iya zaman da ku ka yi dashi ya kamata ki fahimci hakan" Khadijatullahi ta kalli Hafsa ta ce "To shikenan Besty" Anan aka koma Aji suka tashi suka nufi ajin na su.

*'BANGAREN TALATU😂*

Lokacin da aka sanar da ita cewa Salis da Nihal sun koma gidansu kuma sun cigaba da yin rayuwarsu ta ma'aurata fad'uwa tayi ta suma har sai da aka kai ta asibiti haka tai-tayin zage-zage a asibitin nan da aka turasu asibitin mahaukata saboda irin yadda take dukan duk wanda ya matso kusa da ita, domin a cewarsu Talatun tana da matsala a kwakwalwarta.

*'BANGAREN ALIYU💔💍*

Da wuri ya dawo daga Office saboda ya d'auko su Khadijatullahi, ko gida bai je ba ya huce gurin da Shahida ta ke yin aiki ya kirata a waya ta ce masa yanzu zata fito ya jirata ta gama komai, ko minti d'aya ba'a yi ba sai ga Shahida ta fito gaban motar ta bud'e ta shiga, Aliyu ya ja motar ya huce makarantar su Khadijatullahi, ai kuwa yayi sa'a yana isa makarantar ana tashin su Khadijatullahi fitowa su ka yi daga motar suka jinjina a jikin motar, Khadijatullahi wacce tun fitowarta ta ga shigowar motar Aliyu gabanta yayi muguwae fad'uwa haka kawai ta ke jin wani irin abu a cikin zuciyarta, Amatullahi da Hafsa kuwa ba su gansu ba, sai da su ka zo daf dasu sannan Amatullahi ta gansu murmushi tayi tare da kallon Khadijatullahi "Besty ga mijinki ya zo d'aukarmu" Kallonta Khadijatullahi ta ce "Yaya Aliyu ai na ganshi tunda mu ka fito" Tayi maganar cikin wani irin yanayi dan ba ta son ran bestyn na ta ya b'aci.

K'arasawa gurin da suke tsaya su ka yi Hafsa ta rumgume Shahida tana cewa "Oyoyo sister ina Sister Nafisa" Shahida tayi murmushi ta ce "Nihal tana chan gidanta, ta koma yau satinta uku kenan da komawa" Hafsa ta ce "Allah sarki zan kirata kuwa" Sai kuma ta kalli Aliyu ta ce "Yaya Aliyu ina yini" Murmushi yayi sannan ya ce "Lafiya alhamdulillahi, ya karatu?",mun gode Allah" Hafsa ta fad'a tana kallon motar Yaya Safwan wacce ya kunno hancin motar cikin makarantar yayi parking sannan ya fito ya nufo gurin da su Hafsa suke dan ya gansu tun shigowarsa, hannu ya mik'awa Aliyu su ka yi musafaha Hafsa ta ce "Yaya Safwan wannan shine Yaya Aliyun da nake baka labarin cewar shi zai auri bestyna Khadijatullahi" Murmushi Safwan yayi ya ce "Ai na sanshi Aliyu Mansur Jikamshi"Aliyu ya ce "Wato Hafsyy har kin ba shi wannan labarin kenan" Yayi maganar cike da jin dad'in maganar Hafsa sannan ya dora da cewar "Ai mun san juna ni da Safwan sosai" Hafsa ta ce "Au to ai shikenan ma" Haka su ka yi d'an hira da bata huce minti biyu ba, Hafsa tayi musu sallama suka jera ita da Safwan suka shiga mota Hafsa tana d'agowa su Khadijatullahi hannu har suka fita daga makarantar.

Aliyu ya bud'ewa Khadijatullahi gaban motar ta shiga dan su Shahida tunda motar su Hafsa ta fita daga makarantar suka bud'e bayan motar suka shiga, suka bar Khadijatullahi a tsaye ita da Aliyu, shima zagayawa yayi ya zauna mazaunin driver ya ja motar suka nufi gida, Aliyu yana tuki yana satar kallon Khadijatullahi ita kuwa tana lura dashi dan tana kallonsa ta jefen idonta amman ta nuna kamar ba ta san abin da ya ke yi ba.

Suna isa gidan Aliyu yayi parking sannan ya fito daga cikin motar cikin takunsa na isa da tak'ama ya zagayo ya bud'ewa Khadijatullahi motar ta fito su Shahida ma suka fito suka shige cikin gidan, Aliyu ya kalli Khadijatullahi ya ce "My heartbeat idan kin shiga gida kin huta ki zo falon bak'i ina son ganinki keda yarona","To Yaya Aliyu" Tayi maganar a sanyaye tare da nufar hanyar shiga gidan, shima ya bi bayanta zuciyarsa cike da farin ciki, ta huce zuwa falo, shi kuma Aliyu ya shige d'akinsa.

Wajen k'arfe 8:00pm na dare sai ga Khadijatullah ta nufi falon bak'i tana rumgume da Affan a k'irjinta, ta shiga falon bakinta d'auke da sallama "Assalamu alaikum" Ido biyu ta yi da Aliyu yana zaune yana kallon bbc hausa "Wa'alaikissalam Matata" Ya amsa mata sallamar ciki muryarsa me jan hankalin mutane da kuma rud'a 'yammata.

Khadijatullah ta shiga ta zauna a kan kujera tare da kwantar da Affan Wanda yake shan baccinsa hankalinsa kwance, Aliyu ya tashi daga gurin da yake ya koma kujerar da Khadijatullah take zaune, ya zauna da yake kujerar ta zaman mutum uku ce, Affan ya d'auka tare da sumbatarsa a kuncinsa, kallon Khadijatullah yayi ya ce "My wife to be, ya gajiya","ba gajiya" Ta ce a takaice.

"Khadijatullah wallahi ina sonki sosai, Dan Allah ki karb'i soyayyata, nayi miki Alk'awarin ba zan tab'a

Please Login or Register in order to submit comment