Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gadonta hawaye yana zuba daga cikin idanuwanta ita dai lamarin Salis yana bata tsoro kullum idan ya kusanceta kafin ya gama sai ta suma kusan uku ko biyu, kuma gashi baya kusantarta sau d'aya sai dai sau uku safe, rana da kuma dare ko da kuwa ace yana d'akin uwar gidansa sai ya zo gurinta.

Sallamar da aka yi ne ya dawo da ita daga dogon tunanin da ta shiga, a zabure ta mik'e jikinta ya fara rawa hawaye suka fara zuba daga idanuwanta "Dan Allah Yaya Salis yayi hak'uri wallahi ba na jin dad'i yau" murmushi yayi sannan ya ce "Menene na kuka babyna haba dan Allah ki daina kin ji" ba ta ce mata komai ba sai kukan da take yi, hawa kan gadon yayi sannan ta kai hannunsa wuyanta yana cewa "Me ke damunki zazzab'i ko kuma me?" Cikin rawam murya ta ce "Zazzab'i", "Wayyo Allah babyna sorry bari in d'auko miki magani ki sha, ko kuma tashi mu tafi asibiti" mik'ewa tayi da sauri ta d'auki mayafinta ta yafa, Salis ya tashi kenan sai suka ji a turo kofar da sauri Talatu ce tare da yaronta, fuskarta d'auke da fushi.

"Munafikin Allah ta'ala shi ne kace min kana zuwa yanzu zaka dawo ashe gurin wannan shafaffiyar ka zo, bayan kuma kasan yau ba'a d'akinta ka ke ba", murmushi yayi sannan ya ce "Talatu kenan, to ai gurin matata na zo dan haka ba wani abu mugun abu na aikata ba", harara Talatu ta shiga wurga musu ji take kamar ta shak'e Nihal domin wani irin haushinta take ji, domin tun da ya aureta Salis ya rage yin sex da ita, wani lokacin ma ba'a son ransa yake kusantarta ba wanda a da ba haka yake mata ba, amman ta san maganinta zasu had'u da ita tana nan tana tara ta, Salis ta kalla sannan ta ce masa "Ka zo mu tafi to" Nihal ta kallesa sannan ta ce "Yaya Salis ka je kawai na ji sauk'i zan sha magani" ta fad'a sannan ta koma ta zauna a kan gadon, Salis ya fita daga d'akin tare da Talatu, Nihal tayi saurin zuwa ta kulle kofar ta saka key ta sauke ajiyar zuciya, tare da godewa Allah.

Haka ta koma kan gadon farin ciki fal zuciyarta ji take kamar ta zuba ruwa a k'asa ta sha, yau dai ta huta da wannan jarababben namijin (ni kuwa nace nihal daga baya kenan wai anyi sadaka da karuwa🤣😂).

*'BANGAREN ABBA*

Tunda ya d'ora idanuwanshi a kan Aunty Murja ya ji gaba d'aya hankalinsa ya kwanta da yarinyar domin kuwa tana da saurin shiga ran mutane, yau kwana uku kenan amman kullum da tunaninta yake wuni a zuciyarsa, shiryawa yayi kyaf domin kuwa yau zai je ya fad'awa Hajiya Mama abin da ke cikin zuciyarsa ga me da Aunty Murja, motarsa ya shiga mai gadi ya bud'e masa gate d'in gidan ya fita daga gidan ya nufi gidan Hajiya Mama.

Alhaji Mansur yana isa gidan Hajiya Mama yayi parking d'in motarsa ya shiga gidan bakinsa d'auke da sallama "Assalamu alaikum" babu kowa a tsakar gidan dan haka ya nufi d'akin Hajiya Mama ya shiga d'akin da sallama Aunty Murja ya gani zaune tana karatun wani littafi mai suna *Magajin masarauta* wanda *Murjanatu bintu Al'amin ce ta rubutashi* da sauri ta d'ago kanta suka had'a ido da ita zuciyar Alhaji Mansur ta shiga bugawa da k'arfi gaba d'aya ya shagala da kallo Aunty Murja ita kuma ganin irin kallon da yake mata duk gaba d'aya ta rikice ta kasa amsa sallamar da yayi sunkuyar da kanta k'asa tayi tana wasa da littafin da yake hannunta, Hajiya Mama ce ta fito daga bedroom d'inta ta tsaya tana kallon irin yadda d'an nata yake kallon Aunty Murja yana murmushi ko kifta idanuwansa ba ya yi, wani irin murmushin su na manya tayi tare da godewa Allah daman tana son ace d'an nata ya ga Aunty Murja ya ce yana sonta, kuma daman tana son ta yi masa magana a kan ya aureta, domin kuwa ta san zai more da mata kuma 'ya'yansa zasu taso cikin tarbiyya.

Gyaran murya tayi Alhaji Mansur ya d'ago yana sosa kai tare da cewa "Hajiya ashe daman kina nan nayi tunanin ai bakya nan" harara ta watsa masa tare da cewa "To yau kuma da sabon salon da ka zo kenan, ka tab'a ganin ka zo gidan nan ba ka same ni ba" murmushi yayi tare da neman guri ya zauna yana cewa "A'a Hajiya ai nayi tunanin ko suna ki ka je", "A'a dambe na je ba suna ba" wannan maganar da Hajiya Mama ta yi ba k'aramar ba wa Aunty Murja dariya ta yi ba har ta kasa b'oye dariyar sai da ta yi ta a fili, Alhaji Mansur ya kalli yadda Aunty Murjan take dariya, ya k'ara jin ta shiga ransa domin ita kanta dariyar ta ta abin tsayawa a kalla ce "Murjanatu kema maganar Hajiya ta baki dariya kenan" ya fad'a yana kallonta, Aunty Murja ta yi mamaki domin jin Alhaji Mansur ya fad'i sunanta "to a ina yasan sunana?" ta fad'a a zuciyarta.

Alhaji Mansur ranar da ya fara ganin Aunty Murja, ya ji Hajiya Mama ta kira ta da Murjanatu shikenan shima ya rik'e sunan, Kallonsa Aunty Murja ta yi sannan ta ce "Eh".

Hajiya Mama ta samu guri ta zauna tana cewa "to ai sai kuyi ta dariyar, idan kun zare na kai ku dawanau" dariya Alhaji Mansur ya yi sannan ya ce "To mun dena Hajiya. yau fa zuwan nawa na musamman ne, na zo neman wani abu mai muhimmanci ne ban sani ba ko zan dace na same shi ya zama mallakina".

Hajiya Mama duk da cewa ta san inda zancen sa ya dosa, amman sai ta nuna masa ba ta gane ma yake nufi ba ta ce "Wane irin abu ne wannan mai muhimmanci?"

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalli gurin da Aunty Murja take zaune suka had'a ido a karo na biyu, gabanta ne ta ji ya fad'i gaba d'aya ta ji zuciyarta tana bugawa da sauri, tashi ta yi sannan ta ce "Hajiya bari inje tsakar gida na k'arasa tankad'en na san yanzu ruwan ya tafasa" Hajiya ta ce "to shikenan" fita tayi da sauri ta zauna a tsakar gidan tana tankad'en, Alhaji Mansur kuwa Aunty Murja tana fita ya juyo yana kallon Hajiya Mama yana cewa "Hajiya Mama kin san dai irin zaman da nake da Asiya, gaba d'aya ta lalata min tarbiyyar yara Shahida da Aliyu ne kad'ai suka fita zakka, kuma uwa uba Asiya sam bata k'aunar 'yan uwana,Hajiya Mama ina buk'atar na k'ara aure tunda dai ina da halin da zan iya rik'e mace sama da d'aya, kuma ina son na auri Murjanatu idan ba'ayi mata miji ba domin na yaba da halayenta"

Murmushi Hajiya Mama ta yi sannan ta ce "Alhamdulillahi daman ina da burin na ga ance yau kai ne zaka auri Murjanatu domin yarinyar tana da hankali sosai, kuma gaskiya ba na tunanin anyi mata miji saboda a yadda ta ba ni labari iyayensu sun mutu kuma ita kad'ai ce take kula da 'yan uwanta ita suke kallo a matsayin uwa kuma yayarsu" Alhaji Mansur ya ji matuk'ar dad'i ya ce "to yanzu Hajiya ya ya za'ai ina son nan da sati uku masu zuwa a d'aura auren saboda ba na son a ja wani dogon lokaci" Hajiya Mama ta ce "to ai sai ka bari muji ta bakinta ko?" Alhaji Mansur ya ce "Hakane kam Hajiya Mama" Hajiya Mama ta kira sunan Aunty Murja, ta amsa tare da ajiye tankad'en ta shigo d'akin har lokacin zuciyarta bata dena bugawa ba, zama ta yi a kujerar da ta tashi tare da sunkuyar da kanta tana cewa "Gani Hajiya" Hajiya Mama ta ce "Mansur ne ya zo min da wata magana wacce ta saka ni cikin tsananin farin ciki, da ina da dama da tun kafin ya rufe bakinsa zan basa abin da ya ke buk'ata amman ban da wannan damar shiyasa na ce bari in kirawo ki domin muji ta bakinki, Mansur yana so ya aureki kuma baya so a ja lokaci mai tsayi" Aunty Murja ta d'ago da sauri suka had'a ido da Alhaji Mansur wata iriyar kunya duk ta lillib'eta ta saka kanta a kan cinyarta tare da jan hijabinta ya rufe mata fuska, Hajiya da Alhaji Mansur murmushi kawai suka yi, Hajiya ta mik'e ta shiga bedroom domin ta basu guri su yi magana.

Alhaji Mansur ya ce "Murjanatu ki d'ago domin ki ba ni amsa, kina sona? kuma zaki aure ni?" bata d'ago ba domin gaba d'aya ji ta yi kamar ta nitse a gurin saboda kunya "Dan Allah ki d'ago ki ba ni amsa kinji ki cire kunya domin in san in da na dosa" d'agowa ta yi kanta a k'asa dan ba za ta iya had'a ido da shi ba, murmushi yayi sannan ya ce "yawwa gimbiyata yanzu fad'a min na ji ra'ayinki" , "Eh zan iya auranka" abin da ta ce kenan sannan ta fita da sauri gidansu ta nufa wani irin farin ciki duk ya cika zuciyarta, Alhaji Mansur kuw murmushi yayi sannan ya shiga bedroom d'in Hajiya Mama yana cewa "to Hajiya Amaryata fa ta tafi, nima tafiya zan yi" ya fad'a yana zama kusa da ita.

Hajiya Mama ta ce "Lallai Murjanatu wato tafiya babu sallama" Dariya sosai Alhaji Mansur yayi "haba Hajiya kiyi mata uzuri yau dan kuwa kunya ce ta sa ta tafi ba sallama" tashi yayi sannan ya ce "Hajiya nima zan huce", "to shikenan sai ka dawo". Fita yayi daga gidan ya shiga mota ya ja zuciyarsa cike da farin ciki, kai tsaye ma'aikatarsa ya huce.

*'BANGAREN NIHAL*

Zaune take a kan kujera tana chatting da Shahida tana mata korafin tunda ta zo gidan Salis d'in bata tab'a zuwa ba ko ta daina sonta ne?, Shahida ta shiga bata hak'uri da kawo mata uzurin yanzu tana zuwa aiki ne kuma bata dawowa da wuri shiyasa bata zo ba, amman zata kawo mata ziya nan zuwa wani satin insha Allahu

Salis ne ya shigo ya ganta tana zaune tana chatting a bayanta ya tsaya, tare da rumgumota ta baya, a zabure ta mik'e ganin shi ne yasa ta sauke ajiyar zuciya, "kai Yaya Salis ka ba ni tsoro wallahi" murmushi yayi tare da cewa "Sorry baby nayi sallama ne na ji baki amsa ba, kin shagala da chatting", "Eh wallahi da Shahida na ke chatting shiyasa ban ji sallamar ba" matsawa kusa da ita yayi yana kok'arin jawo ta jikinshi, cikin muryar d take nuna alamar za ta yi kuka ta fara magana "Dan Allah Yaya Salis yau ka bar ni, dan manzon Allah", Kallonta yake ido cikin ido ya ce "wai me yasa kullum idan na zo gurinki domin ki biya min buk'ata ta sai kin wulak'anta ni" kuka ta fashe dashi tare da durkushewa tabbas tasan wannan duk alhakin Khadijatullahi ne yake bibiyarta Allah ya had'ata da Jarababben namiji, tsugunnawa yayi kusa da ita ya d'auketa cak be za me da ita ko ina ba sai kan gado, ya kwantar da ita domin shi ba zai iya jira wai ya bi ta ta lallami ba, haka ya fara tsotsar ko ina na jikinta ita kuma tana kuka, tabbas ta yarda alhak'i k'uikuyo ne gashi sun d'auki al'hakin baiwar Allah tun yanzu ita ta fara ganin sakamakon abin da Yayansu Jabir ya aikatawa baiwar Allah, haka Salis ya yi abin da ya kawosa ya d'agata ya shiga toilet ya yi wanka, ya fito d'aure da towel yana kallon inda Nihal d'in take sai wani irin nishi take ta yi matuk'ar ba sa tausayi, ta nufi inda take kwance ya d'agata ya d'auke ya kai ta toilet ya saka ta a cikin ruwan zafin da ya tara, ta kurma wani irin ihu tana kok'arin tashi zata fita daga cikin bahon wanka amman Salis ya rik'eta sosai kuma ya dannata cikin ruwan ta yadda ko ina na jikinta zai gasu sosai.

Sai da Salis ya tabbatar ruwan zafin ya zama ruwan sanyi sannan ya fito da ita, a kan gado ya kwantar da ita yana mata murmushi, shiryawa ya yi cikin shadda kalar sararin samaniya sannan ya feshe jikinsa da turare ya yi mata sallam ya nufi ma'aikatarsu, Nihal kuwa ta ji dad'in ruwan zafin da Salis ya sakata domin yanzu ta ji jikinta yayi mata dad'i, doguwar riga kawai ta saka ta koma ta kwanta a kan gadon, ji tayi an banko kofar d'akin da sauri ta mik'e da kyar tana kallon wacce ta banko kofar Talatu ce ta shigo ,rik'e da wuk'a a hannunta sai shek'i take yi, Nihal ta tsorata sosai da ganin yadda Talatu ta shigo d'akin kuma da wuk'a, cikin rawar murya Nihal ta ce "Talatu mai za ki yi da wuk'a", "kashe ki zan yi kowa ya huta" Nihal jikinta ya kama rawa Talatu kuwa ta nufota Nihal ganin haka ya sa ta d'irgo daga kan gadon ta nufi kofar fita amman ta murd'a kofar ta k'i bud'uwa, wani irin ihu ta saka saboda yankan da Talatu tayi mata a baya har sai da doguwar rigar ta yage jini ya fara zuba kamar da bakin kwarya, a dai-dai lokacin Salis ya dawo saboda manta wata takadda da yayi yana shigowa ya ji ihun Nihal ya nufi d'akin da sauri sai jin muryar Talatu yayi tana cewa "wallahi yau ba zan bar ki ba sai na kashe ki" ya murd'a kofar ya ji a rufe take ya laluba jikinsa sosai yana da mukullin d'akin ya d'auko ya bud'e d'akin ya ga Talatu ta d'aga wannan wuk'ar tana kok'arin dab'awa Nihal da sauri ya finciko Talatu ta fad'i k'asa abin ka da mai k'iba sai ta fasa ihu,wani irin mahaukacin mari ya d'auketa dashi tare da janta ya fita da ita daga d'aki huci yake cike da jin haushinta ya fara magana "ki je gidanku domin ni ba zan iya zama da makashiya ba, na sake ki saki d'aya" Kuka Talatu ta fashe dashi, shi kuwa Salis ya juya d'akin Nihal, ya matsa kusa da ita yana kiran sunanta ba ta motsi sai yanzu ya ga irin yanka da Talatu tayi mata a hannunta da wuyanta d'aukanta yayi cak ya nufi motarsa da ita ya sakata a bayan mota ya kwantar da ita, ya ja motar mai gadi ya bud'e masa gate d'in gidan.

Gudu yake a kan titin kamar zai tashi sama har ya isa wani katafaran asibitin Alhaji Mansur an rubuta *MANSUR SPEACIAL HOSPITAL* da manyan bak'i yana fitowa wasu nurses guda hud'u suka suka nufosa da gadon da ake d'aukar mara lafiya, ya bud'e bayan motar ya d'auko Nihal ya d'ora ta a kan gadon, nurses d'in suka tura gadon Salis yana biye da su a baya, Emergency room suka nufa da ita, Salis ya sami kujera ya zauna tare da zabga tagumi.

*'BANGAREN HAFSA❤️*

Hafsa zaune a kan gado tana shirya Khalid zai tafi makaranta, kallon yaron ta yi sosai tare da cewa "Wow sweetheart you look so cute" murmushi Khalid ya yi tare da cewa "Thanks Mommy i really appreciate" Hafsa ta ce "To yanzu mu je karka yi lating ko?" ta kama hannunsa suka fito falo, Mama suka tarar a zaune a falon tana breakfast suka gaisheta gaba d'ayansu, ta amsa cike da fara'a a fuskarta, zama suka yi domin yin breakfast, sai da suka gama sannan Hafsa ta kama hannun Khalid suka fita Ado driver ya bud'ewa Khalid d'in mota ya rufe ya shiga mazaunin driver ya ja motar, ita kuma ta koma falon ta zauna tana chatting kasancewar yau ba da wuri zasu shiga lectures ba.

*'BANGAREN JABIR DA TEEMARH😹*

Yau Jabir ya kudurce a zuciyar sai ya kwanta da Teemarh ko da kuma za ta mutu, duk da cewa yana zuwa club yana shek'e ayarsa da 'yanmatansa, zaune yake a kan kujera yana kallo ya kalli in da Teemarh take kwance saboda yau ta tashi da zazzab'i mai zafi tunda tayi sallar Asuba ta kwanta ba ta iya tashi ba, Jabir ya mik'e ya zo ya kwanta a kusa da ita idanuwanta a lumshe suke shiyasa ba ta san ya zo kusa da ita ba, hannunsa ya saka a kan wuyanta ya ji zafi rau kamar wuta ya kalleta tare da cewa.
"Teemarh baki da lafiya ne?" Kai kawai ta gyad'a masa alamar "eh" dan ba za ta iya magana ba, murmushi Jabir yayi tare da cewa "wow abu yayi dad'i" Kayanta ya shiga cire mata, Teemarh kuwa dan k'arfin hali a haka ta shiga kok'arin tashi, amman inaaa ba za ta iya tashi da dan jikinta gaba d'aya babu kwari, tureshi ta shiga yi, amman Jabir ya hau kanta ya sakar mata nauyinsa gaba d'aya, a haka ya shiga tsotsarta har sai da burinsa ya cika a kan Teemarh sannan ya tashi ya shiga toilet domin yayi wanka, Teemarh kuwa kuka take yi mara sauti, tabbas sai yau ta sake yarda Jabir d'an akuya ne, bata da lafiyan ma ba zai kyaleta ba (ni kuwa nace amman Jabir ka cika mara imani, amman akwai ranar k'in dillanci).

Haka Jabir ya fita ya kalli gurin da Teemarh take kwance tana kuka, ya saki wata iriyar mahaukaciyar dariya sannan ya nufi drower ya d'auko wata rigar ball da wani wando gajere ya saka sannan ya dawo gurin da Teemarh wanka ya shiga yayi mata da ruwan zafi sannan ya dawo ya shiryata cikin wata rigar bacci a kan gadon ya kwantar da ita ya kara bakinsa a dai-dai saitin kunnanta yana cewa "Teemarh 'yar gidan talakawa, sai ki je wannan matsiyacin uban naki ya kai ki, asibiti dan ni Jabir ba zan kai ki ba, dan an aura min ke ne domin na ji dad'ina, kuma kin ga wannan kurarin naki ya zama na banza kenan tunda gashi na kwanta da ke, wallahi ba zan tab'a kwantawa da kai ba, da na kwanta da kai gwanda na kwanta da kare" yayi maganar tare da fashewa da dariya, tashi yayi ya fita yana cigaba da dariya, Teemarh kuwa kuka ta fara yi, zuciyarta cike da bak'in ciki, wayarta ta samu ta lalubata ta ji ta a kusa da ita ta bud'e ido da kyar ta shiga kiran number Shahida.

Sai da ta kirata kusan sau biyu amman taba d'auka ba, sai ana ukun ne, Shahida ta d'auka tare da yin sallama "Assalamu alaikum Aunty Fatima", "Shahida ki zo d'akina yanzu" abin da Teemarh ta iya cewa kenan dakyar, ko minti biyu ba'a yi ba sai ga Shahida ta shigo d'akin da Sallama d'auke a bakinta, ganin irin yanayin da Teemarh take ciki ne yasa tayi saurin fita falo gaba d'ayansu suna zaune suna hira har da Jabir, "Wayyo Mami Aunty Fatima bata da lafiya sai wani irin abu take yi" tsaki Mami ta ja tare da cewa "Shi ne ki ka taho duk a firgice kin razana ni kamar wacce aka yi mata mutuwa, to menene had'ina da ita, ta mutu mana ni ina ruwana" Abba ya bi Hajiya Asiya da wani irin mugun kallo ba tare da ya ce mata komai ba, sannan ya kalli Shahida tare da cewa "zaki iya kamata ki fito da ita" Shahida ta bud'e baki zata yi magana Jabir ya ce "Haba Abba wannan yarinyar fa munafika ce babu wani rashin lafiyan da take yi" Abba cikin fusata ya ce "Uwar ka ce munafikar, banza mara tausayi kawai" Shahida dai komawa d'akin Teemarh ta yi ta taimaka mata ta chanza kayan jikinta zuwa doguwar rigar atamfa, haka Shahida ta kamata suka fito falon

Aliyu ne ya tashi domin ya kai su asibiti, Jabir ya bi Teemarh da kallo tabbas ta zame masa k'arfen k'afa amman dole ya rabu da ita dan ba zai iya zaman aure da k'aruwa ba, Shahida kuwa motar Aliyu suka nufa daman Aliyu ya ri ga ya bud'e musu murfin motar tun kafin su k'arasa dan haka duka shiga bayan motar gaba d'ayansu shi kuma ya shiga mazaunin driver ya ja su zuwa asibitin Abbansu, suna zuwa nurses suka zo da gadon d'aukar mara lafiya aka dora Teemarh suka shiga Emergency room da ita, Salis ne ya hango Aliyu da sauri ya nufeshi domin yanzu yake shirin kiran Abba ya sanar dashi abin da yake faruwa, Salis yana isa ya mik'awa Aliyu hannu suka yi musafaha, Shahida cikin jin dad'i take tambayar Salis d'in "Ango kasha kamshi, ina Amaryar take duk da cewa ni mai laifi ce a gurinta".

Salis ya d'an yi murmushin ya ke sannan ya ce "Nihal ita ma tana nan asibitin" zaro ido Shahida tayi tare da cewa "Meya faru da Other half" anan ya basu labarin iya abin da ya sani, ya d'ora da cewa "yanzu nake shirin kiran Abba na sanar dashi sai ga ku kun zo" Hankalinsu ya tashi sosai Shahida ta shiga kuka tare da nufa inda Salis d'in ya nuna mata yake anan aka kwantar da Nihal, ta window d'akin ta lek'a nan ta hango likitoci kusan goma a kan ta suna kok'arin ceto rayuwarta, nan ta zub'e a k'asa tana fad'in "Meyasa za ki min haka Talatu ba ki kyauta min ba, me Other half tayi miki da zaki yi kok'arin kasheta".

Aliyu ne ya k'araso inda take tare da d'aga ta yana rarrashinta da kalamai masu dad'i, Shi ma Salis d'in hak'uri yake bata haka dai tayi shuru, suka zazzauna a kan kujera Shahida ta d'auki wayarta zata kira Mami Aliyu ya ce karta kirata ta barta idan Nihal d'in ta farfad'o sai a kirasu a sanar dasu komai, kowannan su tagumi ya zabga zuciyoyinsu cike da damuwa.

*'BANGAREN AMATULLAHI🤸🏽‍♀️😂*

Inna Larai na dawowa daga gidan Baffa Usmanu ta tarar da Lado a kofar gida, ya ja ya tsaya sai huci yake yi kamar zai fashe, kallonsa tayi tana murmushi tare da cewa "jarumin d'ana ashe kana nan" Wani irin mugun kallo yayi mata tare da cewa "dole ki ce min jarumi tunda kina cuta ta, ai yanzu nasan komai kuma wallahi karki ga ke Innata ce sai kin biya ni, domin kuwa ban ga wanda zai ci min kud'i ya zauna lafiya ba" Inna Larai tayi masa kallon rashin fahimta tare da cewa "me ka ke fad'a ne, ban gane ba yi min bayanin yadda zan fahimta" Lado cikin hargagi da masifa ya ce "ina nufin kajin da kike zuwa kina siyar min, kina ce min mutuwa suke yi, to yanzu na san asalin gaskiyar" gaban Inna Larai neya fad'i "wa ya fad'awa Lado wannan maganar" ta fad'a a zuciyarta ba ta san maganar ta fito fili ba sai ji tayi ya ce "Amatullahi ce, ita ta fad'a min" Inna Larai ta kai kololuwa wajen k'ara tsanar Amatullahi "wato ita ce ta had'ata da gudan jininta, ai kuwa wallahi sai ta koya mata hankali" tayi maganar a zuciyarta.

Huce Lado tayi ta shiga gida dan har mutane sun fara taru suna son jin ba'asin meya had'a 'da da uwar, shima Lado bin bayanta yayi da sauri yana cigaba da yin bala'i tun daga zaure Inna Larai take kwad'awa Amatullahi kira da sauri Amatullahi ta fito tana cewa "Waye wannan yake min wannan kiran mafarautan?", "Uban ki ne shegiya".

Amatullahi ta mayar da fuskarta ta masu tausayi tare da cewa "Inna me nayi?" Inna Larai ta d'aga hannunta da niyyar marin Amatullahi, Lado yayi sauri ya rik'e hannunnata Yana cewa "Saboda ta fad'a min gaskiya shine zaki mareta, to wallahi karki kuskura" Amatullahi ta saka kuka tare da yin d'akinta tana shiga ta fashe da dariya "Kai Allah Mai yadda ya so, kad'an ma ku ka gani" hijabinta ta saka ta fito tsakar gida Babu kowa dan haka ta huce, ta fita daga gidan ta nufi gidansu Khadijatullah.

Tana shiga ta tarar da Aunty Murja ta zabga tagumi tana ta murmushi, abin ya ba wa Amatullahi mamaki sosai, tayi sallama kusan sau biyar, Amman Aunty Murja ba ta ma san tana yi ba.

K'arasawa tayi kusa da Khadijatullah wacce take zaune ita ma tana kallon Aunty Murja zuciyarta cike da tambayoyi domin ta ga kwana biyu Aunty Murja tana cikin farin ciki Amman da ta tambayeta sai ce Mata tayi bakomai, zama Amatullahi tayi kusa da ita suna kallon juna ta ce "bestyna meya faru da Aunty

Please Login or Register in order to submit comment