Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na d'auke ku ne, tamkar 'yan uwana, dan haka komai nayi muku ku daina gode min dan Allah" Khadijatullahi ce ta rarrafo kusa da k'awar ta ta dakyar sannan ta kama hannayenta duka biyun tana kuka "nagode miki sosai, tabbas nasan kina sona sosai nagode sosai kuma....." aman da ya taho mata ne yasa ta kasa k'arasa maganar ta juya da niyyar ta shiga band'aki amman ina juyawarta kenan ta fara shek'a amai Aunty Murja da Amatullahi suka rik'eta, sai da ta gama shek'a aman sannan suka wanke mata jikinta inda ta b'ata suka kai ta kan gado ta kwanta, Amatullahi ta dawo ta gyara gurin da Khadijatullahin tayi aman sannan ta dawo ta zauna tana tambayar Aunty Murja "Aunty Murja bata da lafiya ne" Girgiza kai Aunty Murja tayi da alamun damuwa a kan fuskarta ta ce "Wallahi Amatullahi ban sani ba, dan bata ce min bata da lafiya ba" anan Amatullahi ta ce "to Aunty Murja mu tashi muje asibiti" da sauri Aunty Murja ta kalleta ta ce "haba Amatullahi ina nake da kud'in kai ta asibiti", "karki damu ni zan bada kud'in a dubata" haka suka samu suka d'aga ta da kyar akai sa'a kuwa suna fita suka sami mai adaidaita suka shiga sai asibitin nasarawa dake nan cikin garin kano, suna zuwa aka shigar da Khadijatullahi emargency domin duba lafiyarta sun d'auki kusan minti 40 suna jiran a fito a sanar dasu halin da Khadijatullah d'in take ciki, jin alamar da suka yi ana kok'arin bud'e kofar emargency room d'in ne yasa sukai saurin zuwa bakin kofar, doctor Halima ce ta fito tana ganinsu ta shiga sakar musu murmushi tare da cewa "ina tsananin taya ku murna, 'yar uwarku tana d'auke da ciki har tsawon wata biyu, kuma tana nan lafiya kalau dan yanzu na barta zaune tana hutawa, a yanzu ma zaku iya tafiya gida dan laulayi ne yasa tashiga cikin........" k'arar da suka ji an kwala ne ya katse doctor Halima k'arasa maganar da zata yi, juyawa sukai Khadijatullahi ce ta fad'i ta suma domin taji abinda doctor Halima ta fad'a Hankalinsu a tashe sukai kanta suna kiran sunanta

"Khadijatullahi! Khadijatullahi!! Khadijatullahi"

Amman ina bata ko motsi, haka doctor Halima ta shiga kiran nurses, suka zo da sauri suka ciccib'eta suka maida ita Emargency, Aunty Murja da Amatullahi suka koma gefe suka zabga tagumi fuskokinsu d'auke da tashin hankali mara misatuwa.
Tun k'arfe hud'u da aka shigar da Khadijatullah Emargency room har k'arfe 8pm na dare, Babu Wanda ya fito daga Emargency d'in daga nurses d'in har doctor Halima,hakan yasa Aunty Murja da Amatullahi suka shiga cikin matsanancin tashin hankali suna tunanin kodai Khadijatullahi ta mutu ne.

A b'angaren doctor Halima kuwa tunda suka shiga da Khadijatullahi suka shiga kok'arin ceto rayuwarta da ta d'an dake cikinta, yanayin Khadijatullahi ya tsananta domin numfashinta sai kok'arin d'aukewa yake yi, ga bugun zuciyarta sai bugawa yake da k'arfi tamkar ganga ake bugawa, gashi sai wata irin jijjiga take yi, sai da nurses kusan biyar suka rirrik'eta,hankalin doctor Halima ya tashi domin har ta fitar da ran rayuwar baiwar Allah, Anan take ta fara zubar da hawaye domin taga tashin hankali k'arara a fuskokin 'yan uwannata da suka kawota, yanzu idan aka ce ta mutu, ta san zasu shiga cikin mugun yanayi, anan take wani tunani yazo mata da sauri ta fita ta kofar baya office d'inta ta shiga taje ta had'o allurai ta dawo Emargency room d'in tayi mata, cikin ikon ubanjigi tana mata ko minti biyar ba'ayi ba, ta samu bacci, wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya doctor Halima tayi tare da cewa "Alhamdulillahi Allah na gode maka" fita tayi domin ta koma office d'inta amman wannan karan ta kofar gaba ta fita, ai kuwa su Aunty Murja na ganinta sukai wajenta tare da wurga mata tambayoyi "doctor ya Khadijatullahi? Kodai ta mutu ne? Dan Allah ki sanar damu idan ta mutu" kamar had'in baki tambayoyin nasu suka zo dai-dai, "ku biyo ni office" tayi maganar a takaice, tare da yin gaba suka rufa mata baya da sauri, suna shiga doctor Halima ta huce kujerarta ta zauna, su kuma suka zauna a kujerar da ake ganin likita, bayan doctor Halima tayi d'an rubuce-rubucenta sannan ta d'ago tana yi musu bayani "A gaskiya 'yar uwarku tana cikin halin damuwa da kuma tsantsar tashin hankali, wanda a binciken da nayi na gano cewa ta dad'e a cikin wannan yanayin, kuma uwa uba wannan k'arar da ta suma ya k'ara sakata a cikin razana wanda har zuciyarta tana kok'arin bugawa, amman yanzu Allah ya taimaka mun shawo kan matsalar ta ta, amman in har zata cigaba da saka abu a ranta wanda har zai sakata ta dinga shiga damuwa to zata iya kamuwa da babbar matsala a zuciyarta kuma babyn cikinta zai iya samun matsala shima".

Wata iriyar wahalalliyar ajiyar zuciya suka sauke, doin tunda doctor Halima ta fara magana suka kafeta da idanu sai da ta gama bayanin, Aunty Murja ce ta ce "to doctor mun gode sosai,Allah ya saka da alkhairi, kuma insha Allahu zamu yi iya bakin kok'arinmu ganin mun fitar da ita daga cikin halin damuwar da take ciki".
Wata gajeriyar takadda ta mik'a musu Aunty Murja ta k'arb'a, doctor Halima ta ce "gashi nan magungunan da za'a siyo ne domin idan ta tashi sai a bata d'an ruwan tea ta sha ya d'an ratsata, sai ta sha maganin".
Godiya suka k'ara yi mata sosai sannan suka tashi suka fita, Emargency room d'in suka nufa domin ganin yaya jikin Khadijatullah d'in, d'akin da aka kwantar da ita suka tambaya wata nurse ta nuna musu, suka shiga da sauri Amatullahi ta k'arasa kusa da ita ta kama hannuwanta sai ta fashe da kuka tana magana ciki tashin hankali mara misaltu "dan Allah Khadija ki tashi kin barni a cikin matsananci hali, Allah ya isa tsakanina da Jabir bazan taba yafe maka ba, kai ka jawo mana duk irin halin da muke ciki yanzu da muna cikin kwanciyar hankali amman yanzu ka tsarwatsa mana farin cikinmu insha Allah sai kayi mummunan k'arshe sai kayi mutuwar da ba za'a iya gane gawarka ba shege,d'an iska, azzalumi mara tausayi, mara imani" duk tana kuka take yin wad'annan maganganu, dafata Aunty Murja tayi ita ma tana hawayen "haba Amatullahi ki daina irin wad'annan furucin a kan Jabir, tabbas mun san ya zalinceta amman haka Allah ya riga ya k'addara mana kuma kin san komai muk'addari ne, kuma kowane bawa akwai irin tashi k'addarar ki yi hak'uri kinji k'anwata" ta k'arasa maganar tana bubbuga bayanta, Amatullahi kuwa ta riga ta gama kaiwa k'arshe tabbas da ace Jabir zai bayyana a yanzu zata iya k'asheshi domin ta ramawa k'awarta abin da yayi mata, kallon takardar hannun Aunty Murja tayi wacce doctor Halima ta bata ta magunguna "Aunty bani takardar nan zan siyo magungunan kafin Khadijatullah ta tashi tunda ance tana tashi a bata tea sai a bata maganin" babu musu Aunty Murja ta mik'a mata domin daman ta ba san indai zata samu kud'in siyo magungunan ba, tana kan tunanin ko taje ta ari kud'i sai kuma Amatullah ta ce ta bata zata siyo, tashi tayi daman hijabi ne har k'asa a jikinta ta ce "Aunty Murja sai na dawo" kafin Aunty Murjan ta bata amsa ta fita da sauri.

Amatullahi kuwa tana fita bata zame ko ina ba sai bakin titi ta tari mai adaidaita tayi masa kwatancen inda zai kai ta, sun kai a kalla mintina 10 suna tafiya kafin su isa wani tafkeken gida, ta sauka ta biya mai adaidaitan kud'insa sannan ta d'auki wani k'aton dutse ta nufi gate d'in gidan cikin zafin nama take buga gate d'in gidan, cikin hanzari mai gadi ya nufo gate d'in yana jaraba yana bud'ewa Amatullahi ta bangajeshi ta shiga cikin gidan nan mai gadi ya biyota yana mata bala'i "ke baki da hankali ne kin shigo gidan mutanan kiyi maza ki fita ki yanzun nan nayi miki shegen duka" cikin zafin nama Amatullahi ta juyo ta d'auke mai gadin da wani wawan mari sannan ta cigaba da tafiya, duk da cewa bata san kan gidan ba, amman hakan bai bata damar tsayawa ba tayi tafiyar kusan mintuna 40 sannan ta hango wata kofar glass wacce da alama ita ce kofar shiga falon gidan nufar kofar tayi a kayi sa'a a bud'e take tana zuwa bakin kofar, ta bud'e da kanta, ta shiga ko sallama bata yi ba, hangosu tayi a chan falo gaba d'ayansu sun zauna suna kallon wani indian film, kawai taje ta tsaya a gurin tana yi musu wani irin wulak'antatcen kallo, su Mami da suke falo dukansu suka mik'e suna kallonta "ke kuma daga ina? Uban waye ya baki izinin shigowa har falon nan?" Nihal tayi maganar cikin jin tsiwa "Ubanki ne dan Uwanki" Amatullahi ta fad'a cikin zafin rai, sai kuma ta juya gurin Jabir "Dan ubanka, dan uwarka yarinyar sa ka wulak'anta ka tozarta yanzu tana da ciki dan haka ina fad'a maka da babbar murya kasan inda dare yayi maka domin kuma dole ka d'auki dawainiyarta" cikin mamaki da zafin jin zagin da tayi mata Jabir ya ce "ke kuma daga ina da har zaki zo har ciki gidanmu kina ci mana mutunci", "daga gurin uwarka" ta fad'a jikinta har rawa yake saboda bala'i Nihal ta nufota cikin tsiwa ta cakumeta, ai kuwa Amatullah ta cakumeta ita ma ta had'ata da bango, ta saki wata iriyar gigitatciyar k'ara, a rud'e Mami ta matso kusa da ita da niyyar ta cakumeta Aliyu ya rik'eta, sannan ya matsa kusa da Amatullahi wacce ta shak'e wuyan Nihal sai ihu take ya ce "ki yi hak'uri ki saketa muyi magana" sakinta tayi ta fad'i a k'asa tana rik'e da wuyanta, "ki zauna" Aliyu ya fad'a a takaice "ni ba zama ya kawo ni ba" ta bashi amsa fuskarta a murtuke, "na sani amman ki zauna domin muyi magana" zama tayi tare da hard'e hannayenta, Mami ta ce "kai Aliyu tayi mana irin wannan cin mutuncin amman ka dinga wani lallab'ata kamar kana jin tsoronta", "Mami dan Allah ki zauna, bai kamata ba hakan" yayi magana cikin sigar rarrashi zama suka yi gaba d'aya cike suke da jin haushin Aliyu, shima ya koma ya zauna sannan ya fara magana "baiwar Allah bai kamata ki shigo mana gida babu sanarwa kuma......." hannu Amatullahi ta d'aga masa tare da cewa "a fuskata kaga alamar nazo gidannan da niyyar mutunci, ai 'yan mutunci sune ake sanar dasu tun kafin azo gidansu, kuma wallahi ka ganni nan ba mutunci ne gareni ba, d'an uwanku ne ya sakani nazo har gidannan idan ba haka ba me zanzo nayi a wannan banzan gidan da har wani za'a ce sai na sanar, ina matuk'ar ganin mutuncinka da sai nayi maka abin da ba zaka tab'a mantawa dani ba", wani kayatatcen Murmushi Aliyu yayi ya ce "ki yi hak'uri amman ni ban gane me kike nufi ba, kin ce dan uwanmu ne ya saka ki, ki ka zo anan gidan me yayi miki haka", Amatullahi tayi masa wani matsiyacin kallo sannan ta ce"Ka tambayi d'an uwanka wannan Jabir d'in mai zumin shegu" ta fad'a tana nuna Jabir da yatsa, cikin rashin fahimta Aliyu ya ce "Bro me ya faru ne" domin shi Aliyu bai san Jabir yayi aure ba dan babu wanda ya fad'a masa, Jabir yayi wani gejeran murmushi sannan ya ce "ni da ban fahimci mai ya kawo ta gidannan ba, amman yanzu na fahimta wata yarinya ce wallahi da muka tab'a yin auren wucen gadi da ita a kan ta take magana", Amatullahi za ta yi magana Aliyu ya dakatar da ita ta hanyar cewa "dan Allah ki yi hak'uri duk da cewa ban san me ya faru a tsakaninku da Jabir ba, ina mai baki hak'uri ina zuwa" yayi maganar tare da tashi ya shiga d'akinsa bandir d'in kud'i ya d'auko tare da dawowa falon ya mik'a mata tare da cewa "gashi nan kuje kuyi amfani dashi", tashi tayi ta d'auki takardar da ta zurgawa Jabir a k'asa ta nufi kofar fita ko godiya ba tayi masa ba, haka tayi tafiya mai tsayi sannan ta kai bakin kofar gate d'in ta fita tayi sa'a kuwa tana fita sai ga mai adaidaita yana sauke wasu mata ta tsayar dashi ta shiga ta ce masa "Asibitin nasarawa zaka kai ni" mai adaidaita ya amsa mata da "to hajiya".

A b'angaren Jabir kuwa Amatullahi na fita ya kalli Aliyu cikin jin haushinsa ya ce "Amman wallahi baka da hankali wato har da d'aukar kud'i ka bata" sai kuma ya ja tsaki, Mami kuwa mikewa tayi ta zabgawa Aliyu mari hagu da dama har sai da tayi masa sau bakwai sannan ta rufe shi da bala'i "Amman ban tab'a tunanin zaka iya yarda ayi wa 'yar uwarka rashin mutunci kana kallo ba tare da ka d'auki mataki ba kuma kana jii shashashar yarinyar nan har ni sai da ta zageni amman shine ka goyi da bayanta" Aliyu kuwa cikin jin haushin marin da Mamin tayi masa ya shige d'akinsa a fusace ba tare da ya ce komai ba, haka Mami ta matsa kusa da Nihal ta d'aga ta tare da cewa Shahida "Shahida dan Allah kamata ki kai ta d'akinta" ta ce "to Mami" haka ita ma Mami ta juya ta nufi d'akinta a ka bar Jabir shi kad'ai yana ta sake-sake a cikin zuciyarsa.


Amatullahi kuwa suna isa Asibitin ta sallami mai adaidaita sannan ta nufi gurin da ake siyar da magunguna ta basu takardar suka mata total d'in kud'in magungunan gaba d'ayansu dubu ashirin 20k ta arga ta basu sannan ta nufi d'akin da aka kwantar da Khadijatullahi tana shiga ta tarar har ta tashi tana zaune, tayi sallama ta shiga, Aunty Murja ta amsa mata ta k'arasa ta zauna a bakin gadon tana yiwa Khadijatullahi sannu "sannu besty ya jikin naki" cikin muryar rad'a ta amsa mata "da sauk'i" Amatullahi ta bawa Aunty Murja ledar magungunan tare da ragowar kud'in, cike da mamaki Aunty Murja take kallo Amatullahi tare da wurga mata tambaya, "Amatullahi a ina kika samu wad'annan kud'ad'en masu yawa haka.

Amatullahi ta ce.
"Aunty Murja gidansu Jabir naje domin kuwa in sheda musu da cikin da ke jikin Khadijatullahi ba zai yi ace ga mari ga kuma tsinka jaka ba, dole su d'auki dawainiyyar babyn har ta haihu, anan ta fad'a musu duk yadda suka yi daga farko har k'arshe", Aunty Murja tayi shuru kawai tana kallon Amatullahi har ta gama yi musu bayani, sannan ta nisa ta ce "A gaskiya ban san da wane irin baki zan gode miki ba, ke d'in ta daban ce, amman daga yanzu karki k'ara zuwa gidan saboda kin san halin Jabir tantirin d'an iska ne, dan Allah kinji k'anwata k'arki k'ara zuwa tunda dai kin riga kin je kin sheda musu hakan ma yayi".

"To Aunty Murja,ba zan sake zuwa gidan ba" tayi maganar cikin ladabi. kama hannun Khadijatullahi wacce hawaye sai ambaliya suke a fuskarta, ta shiga goge mata cikin muryar rarrashi ta fara magana "ki yi hak'uri kinji besty, bai kamata ki damu kan ki a kan wannan cikin ba, tunda dai ta hanyar aure kika same shi, nasan dai dole ki ji zafi da bak'in cikin samin cikin saboda irin abin da a kai miki A daren Aurenki". Da kallo kawai Khadijatullahi ta bi ta ba tare da ta ce mata komai ba, zamewa tayi ta kwanta a kan gadon ta rufe idonta zuciyarta na cigaba da k'una, Amatullahi ta kafeta da ido cike da tausayawa, har hawaye na kok'arin zubo mata, amman tayi saurin share hawayen dan kar Aunty Murja ta gani, jin Muryar Aunty Murja tayi tana cewa "Amatullahi ya kamata ki tafi gida tunda kin ga dare yayi k'arfe 9pm yanzu, in yaso gobe sai ki dawo" girgiza kai Amatullahi tayi tana cewa "A'a sam Aunty Murja ba zan iya tafiya gida ba, anan zan kwana dan Allah karki ce in tafi ko na tafi ba zan tab'a samun kwanciyar hankali ba", dafata Aunty Murja tayi cikin so da k'aunar yarinyar ta ce "Haba Amatullahi kina gani fa mun taho dake asibiti ba tare da kin je kin sanar a gida ba, kin ga bai kamata a ce kin kwana ba, kar hankalin iyayenki ya tashi basu san inda kike ba", "girgiza kai tayi a karo na biyu ta ce "waye zan damu idan bai ganni ba, Abbana ne kawai kuma baya gari yayi tafi ba yanzu zai dawo ba, kin san dai irin zaman da nake da step mother tunda Mamana ta mutu, ni yanzu ban da kowa daga Abbana sai kuma ku da nake ganinku tamkar 'yan uwana" ta k'arasa maganar cikin muryar kuka.

Babu yadda Aunty Murja ta iya dole ta kyale Amatullahi domin ta kwana a gurinsu, Amatullahi ta zame ta kwanta, kanta na kusa da k'afafuwan Khadijatullahi ita kuma Aunty Murja daman tana zaune a kan kujerar roba dan haka ta k'ara gyara zamanta domin ta ji dad'in baccin, har sukai bacci idan Khadijatullahi biyu domin kuwa ita ba bacci take ba kawai rufe idonta tayi, tashi tayi zaune tare da d'aga hannayenta biyu sama hawaye na zuba daga idanuwanta ta fara jerowa Jabir mugayen Addu'o'i "ya Allah kaga abin da azzalumin bawanka yayi min, ya Allah na rok'eka kayi min muguwar sakayya, ya Allah kasa Jabir yayi mutuwar wulak'anci, ya Allah ka tarwatsa masa duk wani farin cikinsa ka maye gurin binsa da bakin ciki, bakin cikin da zai dauwama a cikinsa har izuwa ranar tashin alk'ima, ya Allah na rok'eka kafin Jabir ya mutu ka d'ora masa cutar da kowa zai dinga gurinsa ya zama abin k'yamata ga jama'a" sai kuma ta fashe da kuka mara sauti tare k'ank'ame jikinta guri d'aya, ta d'auki kusan mintina goma tana kuka bacci mai nauyi yayi awan gaba da ita.

*B'ANGAREN GIDANSU JABIR*

Kwance yayi a kan tafkeken gadonsa wanda mutane goma sha biyar ma zasu iya kwanciya ba tare da yayi musu kad'an ba, maganar da Amatullahi tayi masa ne ta tsaya masa take ta yawo a kunnansa "yarinyar da ka wulak'anka ka tozarta yanzu tana da ciki" bai san meyasa duk a maganganun da Amatullahi tayi masa ba wannan ta tsaye masa a rai, duk da cewa ba wai Khadijatullahi ce kawai ya tab'awa ciki ba, mata da yawa yayi musu ciki wad'anda ma bazai tab'a arga adadin su ba, amman wasu daga cikin matan su suke kawo kansu wasu kuma ta k'arfi yake yi musu, amman bai tab'a damuwa ba, amman gashi yau a kan cikin Khadijatullahi yayi matuk'ar damuwa har ya kasa yin bacci, wani dogon tsaki ya ja tare da cewa "koma dai menene bazan tab'a yarda cikina ne ba, domin ni bazan had'a zuri'a da 'yar gidan matsiyata ba" a haka dai ya rufe idanuwansa yana cigaba da saka abubuwa da yawa a ransa har bacci b'arawo yayi awan gaba dashi.

*Wanene Jabir?*

Jabir babban d'a ne ga Alhaji Mansur jikamshi wanda ya kasance shine minister mai fetur na k'asa nigeria, mahaifiyarsa hajiya Asiya 'yar wani malami ce wanda ya kasance yana koyar da almajirai karatu sun had'u ne ta sanadiyar mahaifinnata Malam kalla domin Alhaji Mansur idan ya samu lokaci yana shigowa unguwar tasu ya yiwa Malam kalla alheri da kuma almajiran da yake koyarwa, ranar nan yazo gurin Malam kalla sai ga Asiya ta fito daga cikin gidan sanye take da d'an k'aramin mayafi tsugunna har k'asa ta gaishesa cikin fara'a da sakin fuska ya amsa mata sannan ta fita zuwa aike da mahaifiyar ta tayi mata, haka ya tashi ya tafi gida tun daga ranar ya nemi nutsuwarsa ya rasa domin kuwa ya kamu da tsananin son Asiya da ya ga yana neman cutuwa dai haka ya shirya ya nufi unguwarsu Asiya domin ya sami babanta Malam kalla ya sheda masa abin da yake faruwa ya ji ko anyi mata miji.

Yana isa kofar gidan Malam Kalla ya fito daga cikin motar kamar yadda ya saba yaje har cikin rumfar da Malam Kalla yake koyar da Almajirai karatu ya zauna bayan sun gaisa ne.

Alhaji Mansur ya fara magana da cewa "daman Malam na ga 'yar wajen ka ce nace to bari in zo naji ko anyi mata miji ne, dan ni har ga Allah ina sonta da Aure ne a yanzu idan har ba'ayi mata miji ba ma zuwa nan da wata biyu ma nake son ayi biki" Alhaji Mansur yayi maganar cike da girmamawa, wani irin farin ciki ne ya kama Malam Kalla tabbas yayi matuk'ar farin cikin jin wannan furucin daga gurin Alhaji Mansur d'in domin kuwa Alhaji mansur mutum ne da kowane uba zai so ace 'yarsa ta aure sa" dan haka Malam Kalla ya fara magana cikin tsananin farin ciki "Alhamdulillahi Allah na gode maka a gaskiya Alhaji ba zan iya bayyana irin farin cikin da nake ciki ba domjn kuwa nasan kai d'in mutum ne na gari amman ban san wa ka gani ka ke so daga cikin yaran nawa ba?".
Cikin jin dad'in yabon da Malam Kalla yayi masa ya ce "Wacce ta fito ranar da muke zaune ta gaisar da ni ta fita da mayafi", "Ohhhh Asiya kenan" Malam Kalla ya fad'a domin kuwa yasan kaf cikin 'ya'yansa ita kad'ai ce take saka mayafi sauran duka hijabi suke sakawa.
"Eh ita nake nufi" Alhaji Mansur ya ce cikin Murmushin jin dad'i, Malam Kalla ya ce "A gaskiya Asiya ba'ayi mata miji ba, amman dai ban sani ba ko ita akwai wanda take so, ina son ka bani lokaci zuwa gobe domin in zauna da ita duk yadsa mukai da ita zaka ji insha Allahu". "To Malam insha Allahu goben zan dawo kamar dai-dai wannan lokacin", "To Allah ya kaimu" Malam Kalla ya fad'a da murmushi a kan fuskarsa, Alhaji Mansur bayan sun d'an yi hira sannan ya tashi ya ajiyewa Malam Kalla band'ir d'in kud'i ya rabawa almajirai kud'i sukai masa godiya ya tafi zuwa gidansa.
Malam Kalla tunda Alhaji ya tafi ya zauna yayi shuru tabbas yayi matuk'ar farin ciki da har Alhaji Mansur ya ga d'iyarsa ya nuna yana sonta, Amman yaso ace daga d'aya daga cikin 'yan uwan Asiya ya gani ya ce yana so ba Asiya ba, domin Asiya sam bata dace da Alhaji Mansur ba, Macece mai girman kai da nuna isa bata ganin kowa da mutunci hatta shi da yake mahaifinta bata ganinsa da mutunci gashi uwa uba bata da kamun kai kwata-kwata, amman bazai so ace shi da kanshi ya aibata 'yarsa ta cikinsa ba, shiyasa bai nunawa Alhaji Mansur komai ba, kila idan Allah yayi ta sanadiyar Auren da zata yi ta shiryu ta dena duk abin da take yii, a haka dai ya yi ta tunane-tunanansa har a kai sallar magriba ya tashi ya nufi masallaci, anan idarwa ya dawo gida kai tsaye d'akin mahaifiyar Asiya ya nufa, zaune ya tarar da Asiya a kan 'yar yaloluwar taburmar d'akin tana taunar cingum tana danna waya, sallama yayi ya shiga d'akin amman Asiya ko d'agowa ta k'allesa ba tayi ba, baran tana ta amsa sallamar, sai mahaifiyar Asiyar ce wacce take tankad'an garin masara ta amsa sallamar tare da yi masa sannu da zuwa, ya amsa da yawwa sannan ya samu guri ya zauna, ya fara koro bayani.

"Alhamdulillahi! Alhaji Mansur wanda yake zuwa gurina shine yau yazo min da maganar da ta sakani cikin farin ciki", cikin murna da farin ciki Inna ta ce "Wace magana ce wannan malam", "Wace yayi yana son Asiya zai aureta" ai kafin Malam Kalla ya k'arasa maganar Asiya ta mik'e tsaye cike da farin ciki, daman ta dad'e tana fatan Allah ubangiji ya mallaka mata Alhaji Mansur a matsayin mijinta domin kuwa tunda taga yana zuwa takanas yana yiwa mahaifinta alheri ta san ba k'aramin Attajiri bane shiyasa duk inda ta ganshi take tsugunawa har k'asa ta gaishe sa, gaba d'aya taji ta fara kyankyamin d'akin nasu ta fara magana cikin rashin girmamawa "Ai daman nasan zance yana sona domin na had'a dukkan abubuwan da ko shugaban k'asa ne ya ganni sai ya ce yana sona, daman na sha fad'a muku ni ba matar talakawa bace ai yanzu kun fara ganin gaskiyar al'amarin, kuma wannan gidan bai dace ace nii Asiya irin yadda nake da

Please Login or Register in order to submit comment