Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta gani tare da Malam d'an ladi mai guga sun fito daga d'akin Inna Larai wani irin ihu ta fasa tare da fita waje ta tsaya dai-dai kofar gidan tana cigaba da kurma ihu, ai kuwa mutane su ka yi kanta suna tambayarta meya faru? "Inna Larai da Malam d'an Ladi mai guga na gani sun fito daga d'aki" Ta yi maganar tana kuka, ai kuwa nan jama'a su ka shiga gidan suka tarar da su Inna Larai da Malam d'an Ladi a tsaye duk sun rud'e dan sun san yau asirinsu ya gama tonuwa, dukan Malam d'an Ladi suka shiga yi ba ji ba gani, Inna Larai ta shige d'aki tare da kulle kofar tana kuka.

Amatullahi kuwa wayar wani Adamu ta ara ta kira Mahaifinta ba fad'a masa komai ba bu abin da ta b'oye masa, hankalinsa ya tashi anan take ya ce ta ba wa Inna Larai ta ce ai ta shiga d'aki ta kulle ya ce to ki ce mata ta gaggauta fitar min daga gida na saketa saki uku, ba na buk'atar sa ke ganinta, a rayuwata yana gama fad'ar haka ya kashe wayar zuciyarsa na yi masa zafi, Adamu ta ba wa wayarsa tare da shiga gidan dan kuwa ba za ta bar Inna Larai ta k'ara ko da minti biyar ba a gidan, d'akinta ta nufa ta d'auko wani k'arfe mai tsini sannan ta nufi d'akin Inna Larai tana buga kofar d'akin da k'arfi tare da cewa "to tsinanniya tsohuwar 'yar bariki ki bud'e kofar nan ki bar mana gida dan Babana ya sake ki saki uku, sai ki je ki cigaba da yin karuwancin na ki a chan wani gurin amman ba'a gidan nan ba" Tana magana tana buga kofar kuma irin bugun da ta ke yi wa kofar ba na wasa ba ne, Inna Larai jin abin da Amatullahi ta ce ta fashe da kuka tare da saka kayanta a buhu ta bud'e kofar dan ta san halin Amatullahi ba ta k'i ta k'arya kofar ba kuma ta yi mata rashin mutunci.

Hanyar fita daga gidan Inna Larai ta nufa tana jin kunyar kanta saboda irin mugayen maganganun da 'yan unguwar ta su suke fad'a mata Amatullahi ta bi ta a baya tana zungurarta da k'arfen tana cewa "Allah ya ra ka taki gona, sai a bi wani sarkin ba dai Yarima ba" Jama'a Unguwar kuwa bayan sun gama yi wa Malam d'an Ladi duka suka cukumeshi sau police station, Amatullahi ta ja kofar gidan ta mukulle da mukulli sannan ta nufi gidan Hajiya Mama ranta fas, dan kuma a rana d'aya ta jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya.

*'BANGAREN HAFSA, SAFWAN DA SAFNA😉*

A yau aka saka ranar Safwan da Hafsa wata hud'u aka saka, ta kira Shahida ta fad'a mata sannan ta ce ta fad'awa su bestynta, Shahida ta yi mata murna tare da yi mata Allah ya sanya Alkhairin Hafsa ta amsa da Amin, daga nan suka kashe wayar, tana ajiye wayar ko minti biyar ba'a yi ba wayar ta shiga ruri da sauri ta d'auki wayar tare da kallom screen d'in wayar Hayatee ta gani murmushi tayi tare da d'aga wayar ta kara a kunne tare da cewa "Assalamu alaikum Yayana" Daga chan b'angaren Safwan wanda yake cikin office d'in ya ce "Wa'alaikumussalam Amaryata" Rufe fuskarta Hafsa ta yi kamar yana ganinta ba tare da ta ce komai ba, Safwan yayi ta tsokanarta, amman Hafsa yau kam ba ta biye masa ba, dan wata iriyar kunyarsa take ji dan har ba ta so ya zo dan ba za ta iya fita ba, a haka dai suka d'an d'auki d'an lokaci suna waya daga nan suka kashe wayar.

A b'angaren Safna kuwa tun da safe take aikin kuka dan kuwa ta san rabuwarta da Safwan ta zo, saboda a cewarta idan ya auri Hafsa ya zama ba na ta ba, sai da ta ji kanta ya fara yi mata ciwo sannan ta kwanta a kan doguwar kujera wani irin bacci ne mai nauyi ya kwasheta dan kuwa daman rabonta da bacci tun shekarar jiya dan jiya yadda ta ga rana haka ta ga dare, sai wajen k'arfe 5:00pm na yamma ta farka wanka ta yi sannan ta saka wata doguwar riga pink wacce aka yi wa gaban rigar kwalliya da duwatsu manya manya, dawowa tayi ta kwanta dan kuwa bacci ne a idanuwanta baccin ne ya kwasheta.

Safwan ne ya shigo falon da sallama, idanuwansa suka sauka a kan Safna wacce take bacci fuskarta ya k'urawa ido yana jin tausayin matarta sa ganin yadda fuskarta ta kumbura fuskarta tayi jajawur, k'arasa yayi kusa da ita tare da shafar fuskarta a hankali "Ruhina" Ya kira sunanta a hankali jin ba ta farka ba yasa ya d'auketa cak ya kai ta kan gado ya kwanta da ita, toilet ya shiga shi ma yayi wanka ya dawo ya kwanta a kusa da ita yana cigaba da shafata a haka shi ma bacci ya kwashe shi.

*'BANGAREN SALIS🤗*

Kamar yadda Abba ya ce zai kai Nihal Asibitin haka kuwa a ka yi da ya je yayi wa Hajiya Mama bayani ba ta k'i ba, dan kuwa yanzu ta san Mama ta yi nadamar abin da tayi wa Nihal d'in, haka Nihal su ka yi sallama da su Khadijatullahi, ta bi bayan Abba suka bar gidan tana jin kewar 'yan uwan na ta a cikin zuciyarta, su na isa asibitin Abba ya fito daga motar ita ma ta fito Abba ya huce gaba tana bin sa a baya har suka isa cikin d'akin, Baffa da Mama duk suna d'akin Nihal ta tsugunna har k'asa ta gaisar da su, sannan ta sami wajen kusa da Mama ta zauna, Mama da Abba suka gaisa da Abba cikin mutunta juna Abba yayi musu ya me jiki su ka amsa masa da cewa "Da sauk'i" Suka d'an tab'a hira daga nan Abba yayi musu sallama ya nufi hanyar fita daga asibitin Baffa sai da ya taka masa har gaban motarsa sannan ya dawo, ya tarar da Mama ta rumgume Nihal tana kuka tana ba ta hak'uri.

Murmushi Nihal yayi tare da cewa "Haba Mama ai ke d'in kamar mahaifiyata ce dan haka, wallahi ni ban ji haushin abin da ki ka yi min ba, kuma ki daina ba ni hak'uri, dan ba na so kin ji Mamana" Ita ma murmushin ta yi sannan ta d'ago Nihal d'in tana murmushi tare da cewa "Nagode sosai yarinyata" Fita Mama da Baffa su ka yi daga d'akin dan su ba wa Nihal d'in damar ganin Mijin na ta, ai kuwa abin Mamaki Mama su na fita Salis ya mik'e zaune tare da kashewa Nihal ido yana murmushi "Babyn baby ya kika ga wannan drama" Zaro ido Nihal tayi tana k'arewa Salis d'in kallo zuciyarta fal mamaki "kenan Salis k'aryar rashin lafiya yayi dan ta dawo" Nihal dariya tayi tare da cewa "Gaskiya babyna wannan drama tana da abin burgewa amman kuma sauran kad'an zuciyata ta buga" Dirowa yayi daga kan gadon ya tako har gurin da take yana cewa "Ai kuwa gwanda da ba ta buga ba, domin babynki yana lafiya ya ji sauk'i fiye da yadda kike tunani kawai wannan wani wasan kwaikwayo na yi tare da taimakon su Dr Maryam dan ki dawo gareni" Janyo shi tayi tare da kissing d'insa a goshi tana cewa "gaskiya Baby ina sonka da yawa ba ka ji dad'in da na ji ba, da muka k'ara kasancewa tare da juna dan har na fitar da ran sake zama da kai darling" Ta k'arasa maganar hawaye na zuba daga idanuwanta.

Goge mata ya shiga yi tare da gaya mata kalamai masu dad'i da kwanta da zuciya har ta yi shuru sai kuma ta kallesa tana murmushi ta ce "yanzu baby meye abu na gaba da za mu yi, dan gaskiya ya kamata ka warke haka" Tayi maganar tana dariya, dariyar yayi mishi sannan ya ce "zuwa gobe zan warke daga d'aya kuma za'a sallame mu kamar yadda mu ka tsara da su Dr Maryam, "Allah ya kaimu babyna" Ya amsa da "Amin" daga nan suka cigaba da hirar soyayyar su zuciyoyinsu cike da farin ciki.

*'BANGAREN JABIR😂*

Tun da wannan yaron ya ba shi takaddar ya saka a aljihu, bai sake tunawa da ita ba sai da ya gama shek'e ayarsa ya nufi hanyar gidan yana yin parking ya bud'e kofar zai fita sai ya tuna da takaddar da sauri ya saka hannunsa a aljihun ya zaro takaddar ya fara warwareta a hankali idanuwansa ya dora a kan takaddar ya fara karanta abin da aka rubuta a cikin takaddar a fili.
"Kai daman baka chanchanci ayi maka sallama dan kuwa ba na saka ka a sahun mutane sai dai dabbobi, na rubuta maka wannan sak'on ne saboda na sanar da kai cewar nii Amatullahi sai na tabbatar na tarwatse rayuwarka, sai na saka ka yi nadamar haihuwarka da wannan tambad'add'iyar uwar ta ka ta yi, dabba kawai" Abin da aka rubuta a takaddar kenan, Jabir kuwa yana gama karantawa ya fashe da dariya tare da cewa "ke kuma irin na ki salon kenan, to koma wacece ina jin na ga ta inda za'a tarwatsa min rayuwar" Yana gama fad'ar haka ya fita daga motar ya nufi cikin hanyar da zata sadashi da babban falon yana cigaba da dariya kamar wani zararre takaddar tana hannunsa, sai da ya zo daf da kofar babban falon sannan ya gefar da takaddar a cikin bola, ya tusa kansa falon ba tare da yayi sallama ba, har ya nufi d'akinsa zai shiga sai kuma ya juya ya nufi d'akin Hajiya Asiya, ya kama hannun kofar kenan zai murd'a sai ya ji muryar Hajiya Asiya tana cewa "A gaskiya ni dai ba zan iya ba da mijina asha jininsa ba, da dai kun tsaya a kan wannan shashashar ne to, zan san yadda zan yi na kawo muku ita mu sha jininta tunda daman ban da wani burin irin na ga bayanta, Jabir kuma A'a gaskiya shima ba zan iya ba" Gaban Jabir ne ya buga yayi saurin ja da baya, jikinsa sai rawa yake yi, "me hakan ke nufi? Kenan Mami ta shiga k'ungiyar matsafa, suke son su sha jinin Abba, shine tak'i yarda suka dawo kai na, Lallai kuwa wallahi Mami baku isa ba chabb baki ma san da wa kike zancen ba" Wad'annan maganganun da Jabir ke yi duk a fili ya ke yi, kuma a kan kunnan Alhaji Mansur wanda fitowarsa kenan daga d'akinsa ya ji Jabir d'in yana magana, da sauri ya k'araso gurin da Jabir yake tsaye ya kama hannunsa su ka fita daga babban falon.

Motar Alhaji Mansur suka shiga Jabir ya kalli mahaifin nasa tare da cewa "Abba wallahi ba zan tab'a yarda ba, babu wanda ya isa ya sha jinina, kashe su zan yi gaba d'ayansu kawai kowa ya huta" Dafasa Alhaji Mansur yayi yana d'an k'ak'alo murmushin yak'e ya ce "Jabir mu godewa Allah tunda Allah yasa ka ji mugun abin da mahaifiyarku take b'oyewa daman ni gaskiya ban yarda da ita ba, saboda irin abin da ta tsira idan ta fita daga gida da yamma sai da safe take dawowa, kuma na sha tambayarta ina take zuwa sai ta shiga yi min kuka, wata ran kuma ta ce min wai biki ta je, yanzu dai abin da na ke so da kai ka ja bakinka ka yi shuru karka fad'awa kowa game da abin da ka ji saboda idan ka fad'a har ya koma kunnanta komai zai lalace.

Kallonsa Jabir yayi cike da tausayawa yau ne karo na farko da ya ji so da k'aunar mahaifin nasa suna ratsa cikin zuciyarsa "Abbana jininka fa suke son su sha kai da Step mother, kuma nima suna so su dawo kai na, ta ya zaka ce nayi shuru wallahi kashe su zan yi gaba d'ayansu kafin su, su kashemu","Jabir karka yi haka ka ji d'ana, a yau d'innan zamu shawo kan abin ba zan bari komai ya same mu ba" Ajiyar zuciya Jabir ya sauke sannan ya ce "to shikenan Abba, wallahi Abba ban tab'a jin tsanar Mami a cikin zuciyata ba sai yau wallahi na tsaneta sosai" Kallonsa kawai Alhaji Mansur yayi domin kuwa shi ma wata iriyar tsanar Asiya ce ta cika masa zuciya lokaci d'aya.

Fita su ka yi daga cikin motar suka koma cikin gidan kowannansu ya shige d'akinsa zuciyarsu fal bak'in ciki, Jabir yana shiga ya tarar da Teemarh tana kwance idanuwanta a lumshe, kujerar da take fuskantarta ya zauna tare da zabga tagumi, Teemarh ta bud'e idonta ta zuba a kan Jabir tana nazarin yanayin da yake ciki tabbas ta san ba k'aramin abu ba ne zai saka Jabir cikin damuwa ba, dan kuwa da wuya ka ganshi yana cikin damuwa, ko da kuwa abin ya dameshi ba zai tab'a bari har ya nuna a fuskarsa ba, sai dai ya barshi a iya zuciyarsa.

Tashi tayi ta k'arasa gurin da yake ta zauna tana cigaba da kallonsa "meke damunka?" Ta tambayesa tana kallonsa, d'agowa yayi yana kallonta sannan ya d'an sakar mata murmushi ya ce "ai ke ce damuwata, kin k'i yarda da soyayyata, Teemarh me zan miki ki yarda cewa ina sonki" Murmushi Teemarh tayi sannan ta ce "A kan wannan shine ka damu kan ka, to dan Allah ka dai na damun kan ka dan nima ina sonka, kuma kai kanka kasan da hakan" Jabir kawai murmushi yayi dan yanzu baya cikin yanayin da zai iya kula kowa dan gaba d'aya haushin duniyar ya ke ji, Teemarh ta kama hannunsa tana cewa "Darling anya kuma ba akwai abin da ka ke b'oye min ba?" Kallonta yayi sannan ya ce "Kina tunanin da akwai abin da zai iya b'oye miki karki manta fa ke d'in matata ce" Murmushin jin dad'i Teemarh tayi tare da kwantawa a kan k'irjinsa, Jabir ya jinjina da bayan kujerar ya lumshe idonsa yana jin wani irin zafi a cikin zuciyarsa.

*'BANGAREN KHADIJATULLAHI♥️😢*

Shahida da Amatullahi ne su kad'ai suna hirarsu ta duniya Shahida ta kalli Amatullahi tare da cewa "Sister ina son mu yi wata magana da ke dan nasan ke kad'aice za ki iya taimakon Yaya Aliyu Haidar" Amatullahi tayi shuru dan tunda Shahida ta kirawo sunan Aliyu ta san abin da zata ce mata "Ina jinki sister" Amatullahi ta fad'a tana kallon Shahida, Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tare da cewa "Yaya Aliyu Haidar ne yake son Khadijatullahi, Sister nayi matuk'ar tausayawa Yayanmu dan nasan ba zan tab'a samun abin da yake so a gurin Khadijatullahi ba dan ta tsanesa sosai, duk da cewa ba shi ne ya aikata mata laifin ba, ya riga ya narku cikin soyayyarta yana tsananin buk'atar taimakonmu wanda ni kuma ban da halin taimaka masa","Inaaa wallahi ni ba zan tab'a sonshi ba, ina baki shawarar ki yi gaggawar basa shawarar ya daina sona, dan kuwa da nayi soyayya dashi gwanda na mutu, na tsaneshi saboda gaba d'aya maza halinsu d'aya ne" Khadijatullahi tayi maganar cikin zafin rai dan kuwa ta ji duk maganganun da Shahida ta ke yi wa Amatullahi.

Hawaye Shahida ta shiga zubarwa ta tashi ta fita daga d'akin, falon saukar bak'i ta shiga ta zauna tana cigaba da rera kuka "Ya Allah kayayewa Yayana wannan masifar da take son tunkaroshi, tun kafin abin ya zo yafi k'arfinshi, Ya Allah ka taimaka masa kasan Yaya Aliyi Haidar yana da kyakkyawar zuciya karka dora masa abin da ba zai iya ba" Tana kuka take yin maganar abin gwanin ban tausayi.

Aliyu ne ya shigo falon ya k'urawa k'anwar ta shi ido, shima hawayen ne suke zubo masa, "Darling Sister ki daina kuka na san wannan jarabawa ce Allah ya dora min ita kuma insha Allahu zan yi kok'ari na cinye Jarabawar da izinin Allah","Allah ya sa Yayana" Shahida ta fad'a tana goge hawayen idonta dan ba ta son ganin Yayan na ta cikin damuwa, zama yayi kusa da ita su ka yi jugum-jugum kamar masu zaman makoki.


*(Allah sarki Aliyu Haidar ka had'u da babbar Jarabawa Allah ubangiji ka bamu ikon cinye ta mu jarabawar Amin👏🏽❤️)*

*B'ANGAREN ABBA DA AUNTY MURJA💕*

Zaune yake a kan kujera ya zabga uban tagumi hankalinsa gaba d'aya a tashe yake tunaninsa d'aya ya ya za'ayi ya shawo kan matsalar nan da ta kunno masa kai cikin gida daman ya gama yanke shawarar ba zai sake zama da ita ba dan yana gama warware wannan matsalar zai saketa takoma gidan ubanta, dan ya gaji da abubuwan da ta ke yi masa dan ya fuskanci wata ran idan har ya barta to tabbas sai gidansa ya kama da wuta, wata dabara ce ta fad'o masa a rai nan ya sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da furta "Alhamdulillahi" a fili.

Aunty Murja wacce ta ke zaune kusa dashi ta ce "Yayana wai me yake faruwa ne" Murmushi yayi ya ce "Wata matsala ce ta kunno min, amman yanzu na samu mafita, amman matata ina so ki dage da addu'a kuma karki dinga zama ba alwala kin ji, duk da nasan ke d'in ba daga nan ba indai wajen nan ne, amman ki cigaba da yi karki gaji" Murmushi ita tayi sannan ta ce "insha Allahu zan dage, kuma na ji dad'i da ka samu mafitar da zata fitar min da mijina daga cikin damuwa Alhamdulilah" Tayi maganar tana dora kanta a kan kafad'arsa, nan ya shiga shafa mata gashin kanta a hankali, yana zuba mata kalaman soyayya da kuma nuna mata irin yadda take da matuk'ar muhimmanci a gurinsa.

(to ni 'yar mutanan zazzau nace Abba asha soyayya lafiya😂💕 nayi gidan su malam salis romeo🤣)

*Washe gari☄️*

Da sassafe Dr Sadiya ta ba wa su Salis sallama suka nufi gidansa kai tsaye, Mama da Baffa suna zuwa gidan ba su dad'e suka fito Tanimu driver ya bud'e musu motar suka shiga, ya shiga mazaunin driver ya ja motar sai da ya kai su har kofar gida, sannan ya nufi gidan.

Salis kuwa su Mama na fita ya mike daga langwabewar da yayi ya jawo Nihal jikinsa yana cewa "Baby nayi matuk'ar missing d'inki haka na dawo tamkar wani mahaukaci saboda soyayyarki ta riga da ta samu babban gurbi a cikin zuciyata" Sai da tayi kissing d'insa a gefen kuncinsa sannan ta ce "nima haka Babyn baby, dan kuma sauran kad'an akai ni dawanau" Dariya yayi sosai sannan ya ce "to ai kuwa gwanda da ba'a kai ki ba dan kuwa da an kai ki nima da yanzu ina chan"."Yanzu dai ki tashi mu je mu kwanta kin san fa, na gaji ina buk'atar in huta tare da matata" Nihal ta ce "Na sani babyna tashi muje" Tayi maganar tare da tashi shima mik'ewa yayi suka shige bedroom ni kuwa 'yar mutan zazzau nace Malam Salis romeo wannan abin yafi k'arfi na nayi gidan Hajiya Mama dan naji yadda zata kasance da Aliyu.

*'BANGAREN ALIYU😭♥️*

Kullum soyayyar Khadijatullahi k'ara dad'uwa take a cikin zuciyar Aliyu gashi yanzu Khadijatullahi ba ta barin su had'u dashi kullum tana d'aki, wannan abin ba k'aramin tayarwa da Aliyu hankali yayi ba, yau gidan babu kowa daga Aliyu sai Hajiya Mama dan Amatullahi da Khadijatullahi sun koma makaranta yau sun shiga second semister Shahida kuma tana gurin aikinta, Aliyu yana zaune kusa da Hajiya Mama ya zabga tagumi Hajiya Mama sai magana ta ke yi masa amman shuru babu alamar zai amsa mata, tab'a shi tayi yayi wata iriyar zabura, Hajiya Mama ta ce "Wai meyake faruwa da kai ne Aliyu na ga kwana biyu, ka na cikin damuwa sosai" Nan ya k'ak'alo murmushi tare da cewa "babu komai Hajiya bari na koma d'akina akwai aikin da zan yi" Ya fad'a tare da tashi ya koma d'akinsa kwanciya yayi yana jin zuciyarsa nayi masa zafi "Allah na rokeka ka kawo min sassaucin wannan zazzafar soyayyar da na ke yi wa Khadijatullahi" Ya fad'a a fili.

Wayarsa ya ji ta shiga ruri ya zura hannunsa ya d'aukota a cikin drower Big bro sunan da ta ga ya bayyana a kan screen d'in wayar kamar ba zai d'aga ba sai kuma ya d'aga tare da cewa "Assalamu alaikum" Jabir bai amsa ba ya fara zaiya na masa abin da ya sa ya kirawosa "Bro kasan me? Wallahi akwai gagarumar tashin hankali, gidannan yana kok'arin kamawa da wuta ga shi Mami ta zama matsafiya" Tashi Aliyu yayi zaune yana cewa "Ban gane Mami ta zama matsafiya ba? Kuma me zai saka gidan ya kama da wuta?" Anan ya kwashe duk abin da ya ji Asiya ta fad'a da kuma yadda su ka yi da Abba ya dora da cewa "Yanzu dai wallahi idan Abba bai d'auki mataki ba ni zan d'auka dan wallahi kashe su zan yi gaba d'ayansu" Hankalin Aliyu ya kuma tashi zuciyarsa kuma kamar zata fashe daman ga shi yana fama da ciwon son Khadijatullahi to ga shi kuma Maminsa ta zama matsafiya, Aliyu ya ce "to ita Mami tana ina?","hmmm d'akinta mana" Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke tare da cewa "Insha Allahu burinsu ba zai tab'a cika ba, karka damu bro ka ji karka ce zaka kashe su ka barsu tunda Abba ya ce zai samu mafita na san zai samu a yau d'in nan","Allah ya sa" Aliyu ya amsa da "Amin" daga nan suka ajiye wayar, Aliyu ya komaya kwanta yana mamakin wannan lamarin.

Kamar yadda suka saba kullum da yamma su ke tafiya gurin tsafinsu kuma a yau ake son Hajiya Asiya ta kai su Abba da Aunty Murja, Asiya ta ci kwalliya sosai kamar mai zuwa gidan biki tana fitowa ta tarar da Aunty Murja da Abba sun shirya cikin wata iriyar shadda kala d'aya Hajiya Asiya tayi murmushi tare da cewa "mu je ko?" Fita su ka yi suka shiga mota suka bar gidan Motar Hajiya Asiya ce a gaba sai ta Abba a baya.

Na san masu karatu zaku ce to ya haka kuma?

Hajiya Asiya ta had'awa su Aunty Murja k'aryar cewa yau ne ake dinner bikin 'yar k'anwarta Hajara da daddare tana son su je gurin tare wannan shine dalilin da yasa suka shirya domin zuwa dinner.
Suna isa gidan matsafan Hajiya Asiya ta fito tare da nufo motarsu Alhaji Mansur cikin tafiyarta ta isa da k'asaita, bud'e motar su ka yi tare da fitowa Aunty Murja dai mamaki da tsoro ne suka kamata, amman ganin tana tare da Habibinta Alhaji Mansur yasa ta shiga b'oye tsoronta hannunta Alhaji Mansur ya kama tare da sakar mata wani lallausan murmushi, suka nufi cikin gidan.

Suna zuwa kofar da za su shiga d'akin tsafin Hajiya Asiya ta juyo tana kallon Alhaji Mansur duk da cewa ita ba ta tab'a sonshi ba kawai tana zaune dashi ne saboda yana da kud'i amman ita kanta ta san yayi mata halacci ya nuna mata soyayya, murmushi tayi sannan ta komarda dubanta kan Aunty Murja "To ina so mu yi sallama da ku anan dan idan mu ka shiga wannan d'akin babu damar yin haka, idan kuma da wata wasiyya da ku ke so ku fad'a min ni kuma nayi muku alk'awarin zan isar muku da ita" Wani irin zafafan mari Alhaji Mansur ya shiga jera mata hagu da dama har sai da ta kai k'asa haka ya shiga tattakata yana ball da ita ya d'ago kanta ya gwara da gini har sai da kan nata ya fashe, amman Alhaji Mansur bai dai na gwara mata kai da gini ba har sai da Hajiya Asiya ta dena motsi, Aunty Murja ta shiga kok'arin janye Abba tana kuka, amman sam bai ma san tana yi ba dan idanuwansa sun gama rufewa.

'Yan sanda ne suka fito daga d'akin tsafin tare da su Hajiya Suhaima gaba d'ayansu an saka musu ankwa a hannunsu, Aunty Murja ta bi su da kallo ita gaba d'aya kanta ya gama d'aurewa, haka aka tisa k'eyar su Hajiya Suhaima 'yan sanda suka saka su a cikin motarsu aka nufi police station da su, suna isa police station aka saka su Hajiya Suhaima a cikin sell dukansu aka shiga yi ba ji ba gani har wasu daga cikinsu suka dai na motsi, Hajiya Suhaima kuwa duk ta gama jigata dan kuwa ta sha duka ba na wasa ba, har ba ta iya gane kowa idanuwanta suka shiga zubar da jini.

*(ni kuwa nace ai kad'an ma ki ka gani Hajiya Suhaima, tunda har ki ka kashe

Please Login or Register in order to submit comment