Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zo,to fa sai ka yi da gaske zaka iya fita" Teemarh ta ce "Gaskiya kam ga Aliyu ma ya k'i dawowa" Teemarh ta kalli su Khadijatullahi ta ce " Sannunku 'yan uwa ya ku ke" Murmushi su ka yi "Lafiya alhamdullahi" Suka amsa a tare "Wai Aunty Fati ina Yaya Jabir" Teemarh ta ce "Yana gida wallahi", "Wannan ita ce matar Jabir" Amatullahi ta yi tambayar tare da kafe Teemarh da ido, ita ma Teemarh jiyowa ta yi tana kallon Amatullahi tana murmushi, Shahida ta ce "Eh mana ita ce, sunanta Aunty Fatima" Amatullahi ta ce "Ohhh lallai kam, kin cika 'yar kasada" Ta yi maganar ciki-ciki, Teemarh ta ce "Sistoo magana ki ke yi ne?" Amatullahi ta yi murmushin yak'e tare da cewa "A'a fa, lazimi na ke yi" Khadijatullahi dariya ce ta kwace mata dan ta ji abin da Amatullahi ta ce, kuma ga maganar da ta fad'awa Teemarh "Tabbas Lazimi kike bestyna" Amatullahi ta kalleta tana murmushi "Bestyna abin k'aunata,me ya baki dariya kuma?" Khadijatullahi ta ce "No! Bakomai, kawai dai lazimin ki ne ya ba ni dariya, ya kamata ki nutsu sosai" Hararar wasa Amatullahi ta hurga mata, tare da d'auko wata hirar ta daban dan ta san indai ta biyewa Khadijatullahi to Teeamarh zata iya fahimtar inda zancensu ya nufa.

Har wajen k'arfe 10pm na dare Teemarh tana gidan Hajiya Mama, Hajiya Mama da ta ga ba ta da niyyar tafiya ta ce "Yau Fatima kwana za ki yi ne?" Teemarh wacce take kwance a kan doguwar kujera ta ce "A'a Hajiya yau zan tafi" Hajiya Mama ta ce "To ikon Allah yaushe za ki tafi kenan, kin san k'arfe nawa yanzu kuwa?" Dariya Teemarh ta yi ta ce "Hajiya Mama na sani mana k'arfe goma har da 'yan mintina, ai Yaya Jabir ne ya ce zai zo ya d'auke ni" Tana rufe bakinta sai ga Jabir ya yi sallama ya shigo falon "Assalamu alaikum" Karaf su ka yi ido biyu da Khadijatullahi, duk da irin yadda ta chanza masa, amman ba zan tab'a mantawa da wannan fuskar ba "Khadijatullahi" Ya kira sunanta a gigice gumi yana k'aryo masa, Yaron da ke kan cinyar Khadijatullahi ya k'urawa ido, shima Affan kallonsa yake yana dariyarsu irin ta yara, yana gwarancinsa don yanzu watan Affan biyar "Kenan wannan yaron nawa ne" Yayi maganar a zuciyarsa, Teemarh ta mik'e ta k'araso gurin da yake tsaya ta ce "Darling lafiya kuwa? Ka santa ne?" Bai kalli inda Teemarh take ba, dan har lokacin idanuwansa suna kan Khadijatullahi da Affan, Amatullahi ta ce "Fatima kina son jin irin rashin mutuncin da mijinki yayi wa 'yar uwata ne?" Da sauri Teemarh ta juya tana kallon Amatullahi ta ce "Meya faru ni na rasa gane kan wannan abin" Amatullahi tayi gajeren murmushi tare da cewa "To yanzu zan warware miki komai, wannan shaid'anin mijin na ki ya auri 'yar uwata, bayan ya gama biyan buk'atarsa da ita ya saketa a cikin daren nan, bai tausaya mata ba, kuma wannan yaron da yake kan cinyarta, d'an wannan shaid'anin mijin na ki ne" Teemarh ta zaro ido domin ta san Jabir ya tab'a yin aure, amman ba ta tab'a yin tunanin ta tambayesa ina matarsa ba, "kina nufin Dijah matar Jabir ce" Cikin muryar b'acin rai Khadijatullahi ta ce "Karki k'ara ce min matarsa domin ni, ba matarsa ba ce Allah ubangiji ya kiyayeni na auri wannan tak'adirin d'an iskan, wancan lokacin da na aureshi akan babu yadda na iya ne" Jabir dai bai iya yin koda motsi daga inda yake ba, barantana har ya iya magana, Hajiya Mama wacce take zaune ta zuba musu idanuwa tana kallonsu ta ce "Kai Jabir shigowa za ka yi ne, ko kuma tsayuwar za ka yi ta yi ne kamar wani gunki" Dakyar Jabir ya fara tafiya gaba d'aya jikinsa a sanyaye yake, Zama ya yi kan kujera nadamar abin da ya yi wa Khadijatullahi ta shiga zuciyarsa, wani irin zafi yake ji a cikin zuciyarsa wanda bai san dalilin jin sa ba, "Hajiya Mama Dan Allah"...... Hajiya Mama ta yi saurin dakatar dashi da cewa "Jabir yanzu dare ya yi ka d'auki matarka ku tafi gida, gobe idan Allah ya kaimu sai mu yi magana" Jabir bai musa mata ba ya amsa mata da "to" Sannan ya mik'e ya nufi hanyar fita daga d'akin, ya juyo ya kalli gurin da Khadijatullahi take, sannan ya fita daga falon, Teemarh ta d'auki Jakarta da mayafinta ta bi bayansa, ita ma jikinta a sanyaye ya ke.


Jabir yana zuwa wajen motar ya bud'e ya shiga, Teemarh ta shiga motar tare da kallonsa zuciyarta a cunkushe "Darling" Ta kira sunanshi muryarta a sanyaye, juyowa ya yi yana kallonta ba tare da ya ce komai ba, sai hawaye da yake zubowa daga cikin idanuwansa zuwa kan kuncinsa, hannunta ta saka tana goge masa hawayen tana yi masa murmushin yak'e "Ka daina kuka ka ji darling insha Allahu komai zai yi dai-dai" Jabir ya sauke ajiyar zuciya "Darling na san nayi wa Khadijatullahi abubuwan da basu dace ba, ban kyauta mata ba sam, idan har ba ta yake min ba tabbas ba zan tab'a yafewa kai na ba" Teemarh ta ce "Karka ce haka darling insha Allahu Dija zata yafe maka ka ji, yanzu tana cikin b'acin rai shiyasa,amman ka barta zuwa d'an wani lokaci kafin nan ta sauko" Murmushin jin dad'i ya yi tare da rumgume Teemarh "Nagode darling nagode sosai, da fatan zaki taimaka min wajen ganin Khadijatullahi ta yafe min","Insha Allahu" Teemarh tayi maganar tana murmushi, haka Jabir ya ja motar duk da cewar ba ya jin dad'in zuciyarsa, amman haka ya daure domin baya son ganin Teemarh cikin damuwa.

*'BANGAREN HAJIYA ASIYA*

Hajiya Asiya ta sha matuk'ar wahala a hannun Alhaji Mukhtar tun da ya samu abin da yake so daga gareta, ya ke nuna mata tsantsar tsana kullum cikin dukanta yake, gashi matarsa ma haka zatai mata rashin mutunci kuma ta sakata wankin kayanta dana yaranta, duk rashin mutuncin Hajiya Asiya sai da bakinta ya mutu, nadamar abin da tayi wa iyayenta da mijinta ta shiga zuciyarta, tunani ta shiga yi yadda zata samu ta rabu da auren Alhaji Mukhtar ta koma gurin mijinta ta nemi gafarsa kuma ta je gurin iyayenta duk da cewa ta san ba lallai su yafe mata ba, domin tayi masu rashin mutunci kala-kala, hawaye ne ya shiga zubo mata "Allah na tuba, Allah ya ubangiji ka yafe min kasa su Innata su yafe min, nasan na zalince su kuma abin da nayi musu ne yake bibiyata, tabbas hausawa sunyi gaskiya da suka ce abin da ka shuka shi zaka girba, yau gashi ina girban abin da na shuka" Ta k'arasa maganar tana kuka mai tab'a zuciya, ta d'auki kusan mintina talatin tana kukan nadamar abin da tayi daga k'arshe ta tashi ta shiga toilet, wanka tayi sannan ta dora alwala ta dawo falon ta shimfid'a dadduma tayi sallah raka'a biyu, ta dad'e tana rok'on Allah ya yafe mata, ta mik'e ta koma kan gado ta zabga tagumi.

"Ke Asiya! Asiya dan ubanki kina ina ne?" A firgice Hajiya Asiya ta mik'e jikinta na rawa ta nufi kofar zata bud'e kamar ance ta lek'a ta window anan ta ga Alhaji Mukhtar ta wata sandar shan jini, gabanta ne ya fad'i, ta ja da baya, idanuwanta ne suka sauka akan wata 'yar k'aramar kofa da zata iya sadata da gate d'in da zata fita daga gidan, da sauri ta nufi wata drower ta d'auko key d'in kofar ta k'arasa gurin kofar ta bud'e ta fara gudu, Allah ya taimaketa gate d'in gidan a bud'e yake, tana fita ta ga wani mai adaidaita zai huce, ta tsayar dashi ta shiga tare da cewa masa "Ka yi sauri ka bar nan dan Allah zai kasheni" Mai adaidaitan ya ja da gudu sunyi nisa sosai, ya juyo yake tambayarta "Hajiya ina muka nufa?" Anan tayi masa kwatancen inda zai kai ta, suna k'arasowa, ta fita tare da ce masa "Ina zuwa yanzu zan shiga gidan, mai gadi zai kawo maka kud'inka" Mai adaidaitan ya ce "To shikenan babu damuwa" Juyawar da za ta yi suka had'a ido da Alhaji Mansur yana tsaye a bakin motarsa, da sauri ta k'arasa gurinshi tana kuka "Dan Allah Abban Jabir"........ "Ya isa Asiya ki yi min shuru, ba na buk'atar sake ganinki a rayuwata, tunda ke butulu ce baki san darajar d'an adam ba" Durk'ushewa tayi akan guiyoyinta tana kuka "Duk abin da ka fad'a min na san na chanchanci fiye da haka ma, zaka iya kirana da abin da ya fi butulu ma, Amman dan girman Allah Abban Jabir koda ace zaka yanke alak'ar da take tsakaninmu, ina rok'onka ka yafe min, na san nayi maka butulci ban kyauta maka ba, ka yafe min dan Manzon Allah" Alhaji Mansur jikinsa ne ya yi sanyi sosai, dan shi a rayuwarsa baya so ya ga matarsa tana kuk saboda shi "To na ji, ta shi tsaye" Mik'ewa tayi tana jin jiriri yana kok'arin kayar da ita, muryar Alhaji Mansur ta ji yana tambayarta "Wanchan fa, meya tsaya yi" Ya yi maganar yana nuna man adaidaita "Shi ya kawoni, kud'insa zan biya sa" Ta basa amsa kanta a sunkuye.

Zuwa ya yi gurin da mai adaidaitan yake tsaye ya d'auko naira dubu biyar ya mik'a masa, nan fa ya shiga godiya ya ja adaidaitarsa ya yi gaba, shi kuma Alhaji Mansur ya dawo gurin da Hajiya Asiya take tsaya ya ce "Yanzu ai kin ga abin da son zuciyarki ya janyo miki, ni dai yanzu na yafe miki Allah ubangiji ya yafe mana gaba d'ayanmu" Godiya Hajiya Asiya ta shiga yi masa tana kuka, ya dakatar da ita da cewa "Ya isa haka, ni yanzu ina da gurin zuwa zaki iya yin tafiyarki" Hajiya Asiya ta ce "To zan tafi amman dan Allah ina neman wata alfarma a gurinka, ina so ka zo muje tare na nemi yafiyar su Innata dan na san indai na je ni kad'ai ba za su saurareni ba" Alhaji Mansur bai mu sa mata ba ya ce ta shiga mota su je, ta shiga gurin mai zaman banza ta rufe, shi kuma Alhaji Mansur ya ja motar ya nufi gidan su Asiya.

To fa k'ak'ak'ara k'ak'a shin iyayen Hajiya Asiya zasu ya fe mata kuwa, ku biyoni dan jin yadda labarin zai kasance💃🏽.

Suna isa gidan Hajiya Asiya ta ga gaba d'aya ya chanza mata ya koma irin na manyan masu kud'i ta san ko ba'a fad'a ba, Alhaji Mansur ne ya gyara gidan ya zama abin ban sha'awa, ta bud'e murfin motar ta fita amman me sai ta kasa motsawa daga gurin da take, wasu zafafan hawaye suna zubowa daga cikin idanuwanta yanzu da wane idon zata kalli iyayenata wanda rabon da ta saka su a idonta tun ranar aurenta da ta fita ta koma gidan k'awarta Aisha, Alhaji Mansur wanda har ya yi nisa ya juyo yana kallon Asiya, tabbas yasan tafi nadama amman ya kamata ya koya mata hankali sosai "Me ki ka tsaya yi anan? Kin kawo ni ne dan ki tsaya kina kuka" Tafiya ta fara yi inda Alhaji Mansur yayi gaba tana bin sa a baya, wani babban falo suka shiga inda nan take tayi ido biyu da iyayen nata, kuka ta saka tare da k'arasawa gabansu ta zube, magana take son yi amman ta kasa saboda irin kukan da ya ci k'arfinta, su kuwa Malam Kalla ido kawai suka zuba mata, "Dan Allah Inna da baffa ku yafe min abin da nayi muku, na san ban kyauta muku ba idan har baku yafe min ba, to tabbas haka rayuwata zata cigaba da tafiya cikin bak'in ciki da k'unci, ba zan tab'a ganin dai-dai ba, dan Allah ku yafe min na tuba" Alhaji Mansur ya ce "Baffa ku yi hak'uri ku yafewa Asiya tabbas tayi nadamar abin da tayi a baya, dan Allah ku yafe mata" Inna ta sauke ajiyar zuciya tare da cewa "Bakomai Mansur na yafe mata" Malam Kalla ya ce "Tabbas Asiya kin ci darajar Mansur yau da ke kad'ai ki ka zo gidan nan sai na b'alb'allaki, amman bakomai na yafe miki Allah ubangiji ya shiryeki" Nan Alhaji Mansur yayi musu godiya sannan ya mik'e tare da yi musu sallama, ya fita daga falon.

Inna ta cewa Hajiya Asiya "Tashi na nuna miki d'akinki","To" Tayi maganar tare da mik'ewa ta bi bayan Innar, suna shiga d'akin Hajiya Asiya ta ce "Innata ina 'yan uwana","Gaba d'ayansu sun yi aure, amman Hajara tun tafiyarki da 'yan kwanaki aka nemeta aka rasa har yau ba'a ganta ba" Zaro ido Hajiya Asiya tayi ta ce "Inna na shiga uku ina Hajara ta je?" Inna ta ce "Wallahi bamu sani ba, ni na rasa ma ya zan yi"Ta k'arasa maganar tare da fashewa da kuka "Kiyi hak'uri Innata ai na dawo zan je zan nemo duk inda 'yar uwata ta je, zan dawo da ita gida" Hajiya Asiya tayi maganar tare da rumgume Innar tana rarrashinta, har tayi shuru haka dai Innar tayi ta ba wa Asiya labarin irin neman da su ka yi wajen neman Hajara amman ba su sameta ba, kuma basu ji labarin komai a kanta ba "Ina tunanin wani ne ya bata labarinta, shiyasa ta gudu" Hajiya Asiya ta juyo cike da rashin fahimtar inda maganar Innar ta nufa "Inna ban gane ba, labarinta kuma, wane irin labari ne?" Inna ta gyara zama tare da cewa "Hajara ba 'yarmu ba ce tsintota Baffanku ya yi, mun b'oye muku ne saboda ba ma son ku nuna mata wani abu da zai sa ta fahimci ba iyayenku d'aya ba, musamman ke dan nasan indai kika san hakan za ki yi mata gori ne" Hawaye ne ya shiga zubowa Asiya "Innata insha Allah zan nemota, duk inda taje ai bai kamata tayi mana haka ba, ko da ace wani ne ya fad'a mata asalinta ya kamata,ta fad'a muku domin mu ta ya ta nemo iyayenta, bai kamata ta gudu ba" Haka dai Hajiya Asiya tayi ta kwantarwa da mahaifiyar hankali abin gwanin ban sha'awa, ni kam 'yar mutan zazzau nace Hajiya Asiya ko ke fa🤣.

*BAYAN WATA 'DAYA DA SATI BIYU🌼*

Jabir hankalinsa ya gama tashi ko bacci ba ya iya yi saboda tunanin Khadijatullahi, zuwansa gidan Hajiya Mama yafi sau ashirin dan ya samu ya ga Khadijatullahi ya nemi yafiyarta amman kullum yaje baya samun damar ganinta, zaune yake a cikin office d'insa kasancewa Abba ya bashi jagorancin ma'aikatarsa wacce ake yin shainkafa, ya zabga tagumi wayarsa ce ta shiga ruri ya kalli wayar wacce take ajiye a kan taburin office d'in *Bro Aliyu* shine ya bayyana a kan screen d'in wayar, Jabir cike da jin haushin Aliyu gami da wani a zababban kishi da ya taso masa, ya katse kiran Aliyun tare da sakashi a blacklist dan Shahida ta bashi labarin Aliyu ne yake son Khadijatullahi dan har an kusa saka ranar aurensu, tarin takaddu ne a gabansa wad'anda ake jira ya saka hannu, amman ya kasa duba koda guda d'aya baren tana ya saka hannun.

Mik'ewa ya yi da sauri ya d'auki wayarsa tare da mukullin motarsa, ya fita daga office d'in bayan ya kulleshi motarsa ya shiga yana tuk'i amman gaba d'aya hankalinsa baya kan titin ya lula tunanin Khadijatullahi da kuma yaronsa Affan, Jabir bai yi aune ba sai ji yayi ya daki wata k'atuwar mota, wanda haka ya yi sanadiyar motarsa ta fad'a cikin wani babban rami ta kama da wuta gaba d'aya motar ta cinye, Innalillahi wa inna'ilaihiraju'un mutanan gurin suke ta faman fad'a koda suka lek'a ramin basu ga alamar akwai mutum ba, dan kuwa komai a cikin motar ya k'one kurmus, da yake wasu a gurin sun san motar Jabir nan aka samu wanda yake da number wayar Alhaji Mansur nan suke fad'a masa Jabir ya yi hatsari kuma gaba d'aya motar ta k'one kuma yana cikin motar, Alhaji Mansur ana fad'a masa haka ya zube a k'asa tare da rushewa da kuka, Aunty Murja ta k'araso tana tambayarsa menene, ya kwashe duk abin aka fad'a masa ya fad'a mata yana kuka "Shikenan yanzu yarona ya mutu, ina tsananin son Jabir kamar raina amman yanzu ya mutu ya bar ni" Aunty Murja gaba d'aya hankalinta ya tashi, haka dai tai-ta rarrashin Alhaji Mansur har ya yi shuru, nan ya d'auki wayarsa ya kira Aliyu, Aliyu wanda yake zaune a falon Hajiya Mama suna hira ya ji wayarsa ta d'auki ruri ya yi tunanin Jabir ne, amman da ya kalli screen d'in wayar ya ga number Abba, ya d'aga jin muryar Abba a chan k'asa k'asa yasa Aliyu ya saka wayar a speaker don ya ji abin da Abban zai ce masa "Aliyu kazo yanzu, Allah ya yi wa d'an uwanka rasuwa a hanyarsa ta dawowa gida ya yi hatsari motar gaba d'aya ta k'one kuma yana cikin motar" Mik'ewa Aliyu ya yi jikinsa na rawa hawaye suka shiga zubo masa, nan da nan gumi ya dinga keto masa ya jik'ashi shark'af "A'a Abba d'an uwana bai mutu ba, yana raye ba zan yarda ba wallahi ba zan yarda ba" Aliyu ya yi maganar tare da yin jifa da wayar, Shahida kuwa hannu ta d'ora akai tare da kurma wani uban ihu "Mun shiga uku yayanmu ya mutu, innalillahi wa'inna ilaihi raju'un" Aliyu kuwa fita ya yi da sauri ya shiga motarsa ya nufi gurin da Jabir d'in ya yi hatsari.

Ya na zuwa gurin nan ya nufi gurin rumin gadan-gadan, da yake akwai hanyar da ake bi a shiga cikin ramin Aliyu yana shiga ramin ya nufi gurin motar Jabir da ta k'one, yana kuka jikinsa ya yi sanyi domin ganin irin yadda motar ta k'one tabbas ya san ya rasa d'an uwansa dan gaba d'aya motar ta zama toka, nishin da ya ji a bayansa ne yasa ya juya da sauri, Aliyu ya mik'e ganin Jabir a kwance cikin jini rumgumeshi ya yi yana jin wani irin farin ciki yana shiga zuciyarsa, d'aukarsa ya yi cak suka fita daga cikin ramin a mota ya sakashi ya nufi asibitin Abbansu, suna isa asibitin Aliyu ya fito daga cikin motar, wasu nurses guda goma suka nufo shi suna tura gadon da ake d'aukar mara lafiya idan an kawoshi, Aliyu ya fito da Jabir ya d'ora shi a kan gadon, nurses d'in suka tura gadon Aliyu yana bin bayansu har aka shiga da Jabir emergency room, Sai a lokacin Aliyu ya dawo cikin hayyacinsa ya zaro 'yar k'aramar wayarsa ya kira Abba ya fad'a masa Jabir bai mutu ba yanzu ma suna asibiti dashi, sannan ya kira Shahida ita ma ya fad'a mata, ko minti goma ba'ayi ba sai ga su Hajiya Mama da Abba sun shigo cikin asibitin suka yo kan Aliyu suna tambayarsa "Ina Jabir d'in" Nan yake nuna musu d'akin da aka shiga da Jabir "Alhamdulillahi Allah mun gode maka, ya ubangiji ka tashi kafad'un wannan bawan na ka" Hajiya Mama ta yi maganar tana kuka, dukansu suka amsa da "Amin" Khadijatullahi ta ce "Yaya Aliyu ka tabbatar Jabir bai mutu ba" Ta yi maganar cikin yanayin damuwa "Eh Dija Mijinki bai mutu ba" Khadijatullahi ta kalli Aliyu cike da mamaki amman ba ta iya cewa komai ba, Teemarh ce ta rumgume Khadijatullahi tana kuka "Dan Allah Khadija ki taimakawa mijina ki yafe masa, ina da tabbacin sanadiyar tunaninki ne yasa ya yi hatsarin nan" Khadijatullahi gaba d'aya ta rud'e ta ma kasa magana, sai bin mutune da ta ke yi da ido, haka dai suka nemi guri kowa ya zauna, kowannansu ka kalli fuskarsa zaka ga tarin damuwa da tashin hankali mara misaltuwa.

*'BANGAREN LADO DA INNA LARAI💃🏽💞*

Durk'ushe yake a gaba mahaifiyar ta sa yana kuka yana neman gafararta "Dan Allah Innata ki yi hak'uri da duk abubuwan da nayi miki ki yafe min na san tabbas ban kyauta miki ba, na zalince ki ni ba d'a na gari ba ne" Inna Larai tayi murmushi ta ce "Bakomai Lado na yafe maka, abin da na shuka ne nake girbarsa" Lado ya ce "Nagode Innata Allah ya saka miki da alkhairi, ki tashi muje d'akina ni zan koma d'akinsu Lawal" Inna Larai ta mik'e Lado tana gaba Lado yana bin ta a baya, ta shiga d'akin Lado, kayansa ya shiga tattarawa yana kaiwa d'akinsu Lawal har ya gama ya zauna suka d'an yi hira da Innar ta sa, daga k'arshe ya yi mata sallama ya fita.

Yana fita su ka yi kicibus da Zaituna, kallonsa tayi cike da girmamawa tana sakar masa murmushi "Yaya dan Allah kayi hak'uri ka yafe min, ban yi maka rashin kunya dan"............. "Yi shuru Zaituna meyasa ki ke ba ni hak'uri, ai gaskiya kika fad'a min kuma nagode da kika dawo da ni hanya madaidaiciya, kuma insha Allahu zan gyara kuskuren da nayi a baya" Murmushi Zaituna tayi ta ce "Indai kayi hakan ni kuma na amince zan aureka, domin kuwa kasan Ina tsananin son Inna" Zaituna tayi maganar tana rufe fuskarta, Lado ya ji matuk'ar dad'in kalaman Zaituna wani farin ciki ya shiga tsarga masa, ita kuma Zaituna ganin kallon da Ladon ya ke yi mata yasa ta shige d'akin da Inna Larai take da gudu tana dariya, shima ya nufi d'akin su Lawal yana jin dad'i a cikin zuciyarsa.

*BAYAN KWANA BIYU✌🏽*

Aka saka ranar auren Zaituna da Lado wata d'aya farin ciki gurin wad'annan masoyan ba'a magana, nan suka shiga nunawa junansu wata iriyar sabuwar k'auna kamar su cinye junansu, kullum suna tare Lado yana zuba mara ruwan kalaman soyayya, ni kuwa er mutan zazzau nace Lado ya za ka yi mana haka Amatullahi fa😅Karka manta ita ce tsohuwar zuma🤣.

*BAYAN AWANNI GOMA SHA BIYAR🤧*

Da taimakon Allah Likitoci su ka yi nasarar, ceto rayuwar Jabir bayan gwagwarmayar da suka sha, kafin su yi nasarar ceto rayuwarsa dan gaba d'aya likitocin jikinsu ya yi sanyi ganin irin yadda jini yake zuba kamar famfo daga jikin Jabir, dakyar suka samu suka yi masa aiki har jinin ya tsaya, Doctor Isham ne ya fito daga d'akin yana gyara rigar jikinsa da sauri Alhaji Mansur ya taresa yana tambayarsa "Ya jikin Jabir" Murmushi Doctor Isham yayi ya ce "Alhamdullahi da taimakon ubangiji mun yi nasarar ceto rayuwar Jabir, yanzu dai mun yi masa allurai nan da awa d'aya zai iya farfad'owa" Kowannansu ya shiga furta "Alhamdulillahi" Doctor Isham ya nufi office d'insa, Nihal ce ta shigo asibitin da gudu tana kuka dan Shahida ta kirata ta fad'a mata Jabir ya yi hatsari "Abbanmu ina Yaya Jabir d'in yake" Abba ya ce "Ki kwantar da hankalinki yana nan lafiya" Shiga d'akin su ka yi gaba d'ayansu, zama su ka yi a kan kujerun dake d'akin suna kallon yadda Jabir d'in ya ji raunika a jikinsa, masu kuka nayi masu tagumi da jimami nayi.

Bayan awa d'aya Jabir ya fara motsi da 'yan yatsun hannunsa tare da kiran sunan Khadijatullahi, ras gaban Khadijatullahi ya yi mummunan bugu, duk da irin yadda ta tsani Jabir yanzu kam wani irin tausayinsa take ji saboda ganin irin yadda gaba d'aya kamanninsa suka chanza "Na'am" Ta amsa tana zubar da wasu zafafan hawaye, hannun Teemarh ta kama suka k'arasa gurin gadon zama su ka yi a kan gadon, Jabir a hankali ya bud'e idanuwansa ya dorasu a kan Teemarh "Zahra" Ya kira sunanta a hankali, duk da irin yadda Teemarh take cikin tashin hankali sai da tayi mamakin a ina Jabir yasan sunan da danginta ne kawai suke fad'a mata "Na'am" Cikin wata iriyar wahalalliyar murya ya ce "Ina Khadijatullahi?" Khadijatullahi ta ce "Gani nan" Ya juya a hankali dan Khadijatullahi ta zauna ta wajen kansa ita kuma Teemarh ta wajen k'afafuwansa, hannuwanta ya kama yana kok'arin fashewa da kuka "Dan Allah ki yafe min, nasan ban kyauta miki ba kuma"......... "Na yafe maka tuntuni Allah ya yafe mana ga baki d'aya" Khadijatullahi ta k'atseshi daga k'arasa maganar da zai yi "Nagode sosai, ina yarona?" Khadijatullahi ta karb'i Affan daga hannun Amatullahi ta ajiyeshi kusa da Jabir tana cewa "Gashi nan" Hannun Affan ya rik'e yana murmushi, gaba d'aya su Abba sun ji matuk'ar dad'in yadda Khadijatullahi tayi wa Jabir kuma sun san nan da 'yan lokaci kad'an burinsu zai cika, wasu kawar da k'iyayyar da Khadijatullahi ta ke yi

Please Login or Register in order to submit comment