Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Jabir gata nan ko yau kake so a d'aura aure zan baka goyon baya d'ari bisa d'ari, wani irin shu'umin murmushi yayi sannan ya kalleni muka had'a ido ya kanne min ido d'aya, su Kawu Sani suka fita amman shi Jabir bai fita ba sai wani irin kallo da yake min wanda kana ganinsa zaka san na cikakkun 'yan bariki ne matsowa ya yi daf dani yana kok'arin kama min hannu nayi saurin komawa bayan Aunty Murja murmushi ya yi sannan ya ce dijarh kenan son kud'in wad'annan matsiyatan Kawun naki yayi yawa dan haka ki sani yanzu ina zuwa na sakar musu kud'i nace a yanzu nake son a d'aura mana aure da gudu zasu yarda kuma karki wani damu indai hannunki ne nan da sati d'aya zan yi duk abin da nake so a jikinki nasan dai kin san abin da nake nufi zan d'and'ani zumarki duk da cewa Auren wucin gadi zamu yi yana gama fad'ar haka ya fita daga gidan na rik'e Aunty Murja ina kuka sosai kamar raina zai fita, zaunar da ni tayi tare da rumgumeni a jikinta cikin muryar kuka nake ce mata Aunty Murja na shiga uku dan Allah ki yi duk yadda zaki yi kar in auri wannan d'an iskan, ita ma cikin kuka ta ce ba za ta iya hana auren nan ba saboda indai tayi yunkurin rama auren hakan zai iya jawo mana babbar matsala muna cikin wannan yanayin sai ga Amatullahi ta shigo nan na zai yana masa komai ita ma ta shiga yin kuka, haka dai muka kasance cikin tashin hankali har sati ya zagayo, da misalin k'arfe 10 na dare sai ga su Kawu Sani da Jabir kamar dai yadda suka zo ranar farko da yake lokacin zafi ne mun yi shimfid'a a tsakar gida muna shirin kwanciya da sauri na tashi ta koma bayan Aunty Murja jikina na rawa, Kawu Sani ya ce to kamar yadda muka zo muka sanar da ku satin da ya wuce za'a d'aura auren Khadijatullahi da Jabir to yau an d'aura kuma yanzu yazo tafiya da matar sa ne, kuka na saka mai had'e da ihu Amman haka Kawu Sani ya finciko ni daga bayan Aunty Murja ya tura ni gurin Jabir kamar jira yake ya kama hannuna ya rik'eshi sosai sannan ya nufi kofar fita, haka muka fita daga gidan ina tirjewa har muka isa gurin motarsa ya bud'e ya turani ya rufe motar ya koma mazaunin driver ya shiga ya ja motar mun yi tafiyar kusan awa biyu har muka isa wani babban gida gate mai gadi ya bud'e gidan a wajen da aka tana da dan yin parking yayi parking d'in motar ya bud'e motar ya fito ya zagayo inda nake a bayan motar ya bud'e ya jayo ni, yana jana ina tirjewa har muka isa wata kofa wacce ta sadamu da wani tafkeken falo kai tsaye wani babban bedroom ya nufa dani ya wurgani kan gadon sannan ya cire kayan jikinshi ya rage daga shi sai gajeran wando dakyar na iya tashi saboda yadda ya wurgani kan gadon sai da na bugu da bakin gadon haka Jabir yayo kai na ganin haka yasa na shiga kok'arin kare kai na ina d'aukar duk abin da yazo min hannuna ina wuraga mishi, tsayawa Jabir yayi cak ganin haka yasa na dena jifanshi ina nuna shi da yatsa ina cewa karka matso kusa dani, murmushi yayi tare da fad'awa kan gadon ya bage yana kallona, juyawar da zan yi in mayar da kwalbar da na d'auka kawai naji Jabir ya jawo ni na fad'a kan gado ya hau kai na yana murmushin mugunta yana cewa kinga ai kin shigo hannuna sai yadda nayi dake zan ci in more sosai yayi maganar yana kanne min ido, tureshi na shiga kok'arin yi ina kuka amman ina Jabir ya riga da ya sakar min nauyinsa gaba d'aya, Jabir bai d'aga ni ba har sai da ya rabani da budurcina, haka ya tashi ya shiga toilet yayi kusan mintune goma sannan ya fito d'aure da towel har sai da ya gama shiryawa sannan ya nufo gurin da nake kwance ya miko min wata farar takarda yana murmushi, zaki iya tafiya gidan ubanki, tashi nayi dakyar hawaye na bin kuncina na bud'e takardar _Ni Jabir Mansur jikamshi na sake ki saki uku_ abin da aka rubuta a takardar kenan wani irin kuka na saki ina kallonsa haka na saka kayana kamar jira yake in gama saka kayana ya dinga ja na har sai da muka fito farfajiyar gidan sannan ya ce bari in turo miki 'yan rakiya domin su rakaki har gida ko, ya zagaya bayan gida sai gashi da wasu karnuka sun kai guda biyar manya manya sai haushi suke nan karnukan nan suka nufo inda nake da mike dakyar domin tsiratar da kai na na shiga guda mai gadi ya bud'e min kofa da sauri na fita haka ina gudu karnukan nan suna bi na gashi dare yayi kowanne gida na huce a rufe ya ke babu kowa a unguwar daga ni sai wad'annan karnukan,har Allah ya kawo min wani mutum yazo wucewa a mashin ganin yadda nake gudu karnuka na bi na ya ce in hau mashin d'in haka na hau mashin d'in dakyar ya ja mashin d'in da gudu sai da muka yi nisa sannan yake tambayata daga ina nake? Ina kuka na sanar dashi komai ya tausaya min sosai dan haka sai da ya kai ni har kofar gida nayi masa godiya na k'arasa gidan, ina tura kofar na tarar a bud'e take na shiga gidan a inda muka bar Aunty Murja a nan na same ta na fad'a kanta ina kuka nan ta d'ago ni tana tambayata meyafaru cikin daren nan yanzu kusan k'arfe 2 kika dawo? na fad'a mata duk abin da Jabir yayi min ta rumgume ni tana kuka tana cewa ashe Auren wucin gadin da ya ce zaku yi wannan yake nufi Allah ya isa tsakaninmu dashi".

Khadijatullahi ta kalli Hafsa wacce fuskarta tayi sharkaf da hawaye ta ce "Hafsa wannan shine labarin abin da Jabir yayi min, wanda ba zan tab'a mantawa dashi ba har abada" Hafsa cikin kuka ta ce "lallai Jabir ya cika zazzalumi,mugu,macuci kuma insha Allahu, Allah sai ya saka miki abin da suka yi shi da su Kawu Sani" Amatullahi wacce take kusa da Khadijatullahi tana kuka ta ce "Ai su Kawu Sani tun ranar da suka zo suka gama yin rashin mutunci Jabir ya tafi da Khadijatullahi suna fita suka had'u da 'yan fashi a hanya suka harbesu babu wanda ya rayu a cikinsu" Hafsa ta ce "Ai daman duk wanda ya zalinci wani Allah ba zai tab'a barin shi ba" sun jima suna zaune kowannan su zuciyarsa fal da bakin ciki had'i da tsanar duk wani namiji, a haka Aunty Murja tayi sallama ta shigo d'akin suka amsa mata Hafsa ta gaisheta "Ina wuni Aunty Murja" ta amsa mata cikin sakin fuska "Lafiya k'alau Hafsa ko?" Hafsa tayi murmushi ta ce "Eh" zama tayi a bakin gadon d'akin tana kallonsu "Hafsa wato saka ki suka yi a gaba suna kukan nasu da suka saba kenan" Murmushin yak'e kawai Hafsa tayi, kiran Mommy ya shigo wayarta tayi sallama Mommy ta amsa sannan ta ce "ga driver nan na turo shi zai zo gidansu Khadijatullahi ya d'auke ki" Hafsa ta ce "to Mommy" Daga nan suka kashe wayar wajen k'arfe 8:00 na dare driver ya aiko a kira Hafsa tayi wa Aunty Murja sallama su Khadijatullahi suka rakata wajen motar sannan suka dawo Amatullahi ita ma tayi wa Aunty Murja Sallama Khadijatullahi ta tashi zata rakata ta hanata ta ce "Haba besty bakomai kawai ki zauna ki huta" daga nan ta fita zuwa gida.

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

*'BANGAREN GIDANSU JABIR*

Kwance yake a kan gadonsa yana ta juyi abin duniya ya taru yayi masa yawa yasan Abba sare baya tab'a yin magana biyu, anan take wata dabara ta fad'o masa, wani irin tsalle yayi tare da sakin wani irin shu'umin murmushi "tabbas wannan dabarar tayi kuma ita kad'ai ce zan yi nak'i auren Teemarh". Komawa yayi ya kwanta wani irin bacci mai dadi ya tafi dashi.

*Washe gari🌸⚜️*

Inna Larai ce zaune ita da Lado sun gama had'awa Amatullahi mak'irci gurin mahaifinta Malam Shu'aibu a kan cewa tana fita yawo kuma idan ta tafi makaranta ba ta dawowa sai chan dare wajen k'arfe goma za'a zo ayi parking d'in mota a sauketa a kofar gida, hankalin Malam Shu'aibu ya tashi dan haka ya buga sammako da dawo gidansa, ko da ya dawo ya tambaya ina Amatullahi suka ce tana cikin d'akinta, ya nufi d'akin yana kwad'a mata kira da sauri ta fito cikin wata doguwar rigar abaya plum colour ta yafa mayafin abayar rik'e da jakarta ta zuwa makaranta tayi kyau sosai sai kamshi take yi murmushi tayi ta tsugunna har k'asa ta gaisar da Abbanta, abin da ya bawa su Innah Larai mamaki sai suka ga Malam Shu'aibu yayi murmushi ya amsa gaisuwar da tayi yayi mata umarni da ta tashi tsaye ta mik'e, anan ya shiga tambayarta "Mamana meyasa idan kin je makaranta bakya dawowa da wuri sai goma na dare kuma ajiye ki ake yi a mota, kuma kika watsa Larai mai a fuska ita da Lado" cikin mamaki ta ce "Abbana ni kuma wallahi Abba kullum da wuri nake dawowa kuma ni da Khadijatullahi muke dawowa a adaidaita, kasan dai ba na kula kowane saurayi kai ma shaidata ne bare har in shiga motarsa wallahi zan iya dafa al'kur'ani ban tab'a shiga motar kowa ba kuma ban tab'a kai wa goma na dare a waje ba kuma Innah Larai da Lado sune suka ja duk abin da nayi musu anan ta fad'a masa duk abin da ya faru" ta k'arasa maganar tana kuka, anan Malam Shu'aibu ya shiga rarrashin 'yar tasa har tayi shuru ya kama hannunta suka yi hanyar waje, Amatullahi idanuwanta a kan su Inna Larai da fuskokinsu suka chanza saboda basu yi nasarar had'a uba da 'yar ba tasan tabbas sune suka had'a mata mak'ircin nan kuma wallahi ba za ta kyalesu ba sai ta rama (ni kuwa 'yar mutanan zazzau na ce su inna larai an taro match🤣) haka suka fita daga gidan mahaifinta na rik'e da hannunta a kofar gida suka tsaya mahaifina ta ya kalleta cike da so da k'auna "Mamana kiyi hak'uri nasan kina hak'uri zama dasu Larai daman nasan ni ba halinki ba ne, amman nasan yadda zan shawo kan abin" hannu ya zura a aljihu ta d'auko 2k (dubu biyu) ya mik'a mata sannan ya cigaba da magana "gashi nan kiyi amfani dashi dan ba lallai ki dawo ki same ni ba, zan koma chan companyn namu yanzu ma jirana ake yi" Amatullahi ta karb'a tare da yi masa godiya, ta nufi gidansu Khadijatullahi zuciyarta fal farin ciki domin kuwa taji dad'i da Abbana ta ya ce zai koma wannan zai bata damar had'a musu nata mak'irci amman kuma ita ba k'arya zata musu ba, a kan abin da suke aikatawa a gidan zata yi musu basu san dawa suke zancen ba ne, da wannan tunanin ta k'arasa gidansu Khadijatullahi ta tarar ita ma har ta gama shiryawa doguwar rigar abayar tasa komai iri d'aya haka suka yi wa Aunty Murja sallama suka nufi hanyar fita daga gidan.

Suna fitowa suka yi sa'a ga wani mai adaidaita zai fita daga layin suka tsayar dashi suka shiga Amatullahi ta ce "Baba poly zaka kai mu ta gadon k'aya" kasancewar mai adaidaitar tsoho ne, shiyasa ta ce masa Baba, ya amsa mata da "to" suna isa Khadijatullahi ta bud'e jakarta ta d'auko naira d'ari biyar wacce ita kenan da ita zata mik'awa mai adaidatan Amatullahi ta dakatar da ita da cewa "to Hajiyata ai sai ki bari in biya ko?" ta fad'a tana mik'awa mai adaidatan naira d'ari biyar tunda daman a haka ake kawo su makarantar, suka shiga makarantar suna zuwa suka tarar da Hafsa har tazo abin da ya basu mamaki shine abayar da Hafsa ta saka komai iri d'aya da tasu babu abin da ya bambanta k'arasawa gurinta suka yi Amatullahi ta ce "Besty Hafseyy yau fa kinsa mun shiga mamaki sosai" murmushi tayi ta ce "Saboda kayan da nasa irin naku ko?" Khadijatullahi ta ce "Wallahi kuwa komai irin d'aya" Hafsa ta ce "ba abin mamaki ba ne ai, saboda tun jiya da muka je gidanku na ga abayar Khadijatullahi a kan gado kawai naji jikina ya bani ita zaku saka yau sai na k'are mata kallo Allah yasa naga kwalliyar jikin abayar duk da cewa ba duk na gani ba, shine muna tafiya na tsaya na saya a wani super market, murmushi suka yi gaba d'ayansu sannan suka nufi hanyar ajinsu domin an kusan fara lecture, basu dad'e da shiga ba Malam ya shigo suka fara lectures.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••

*'BANGAREN GIDANSU JABIR*

Jabir ne tsaye a gaban madubi yana kallon kansa ya gama shirinsa tsaf cikin wasu kaya gajeren wando ne wanda ko guiwarsa bai kai ba sai wata farar riga wanda a bayanta an rubuta *JABIR D'AN TUWA* da manyan harafai gashin kansa ya kwanta luf sai shek'i yake yi, haka ya fito babban falo, babu kowa a falon dan haka ya nufi kofar fita daga falon, Jabir yana bud'e kofar falon Aliyu na fitowa daga d'akinsa kallo d'aya yayi masa ya d'auke kansa domin kuwa wani irin haushin Jabir d'in yake ji, shi kuwa Jabir bai ga Aliyu ba saboda ya riga ya fita daga falon, motarsa ya nufa ya shiga ya jaa ta da gudu mai gadi yayi saurin bud'e masa gate ya fita daga gidan wak'ar babban mawak'in yahudawa ya saka Ojoro wanda Omale yayi ya k'ure kid'an yana bin wak'ar a hankali, Club ya nufa yana isa farfagiyar club d'in ya tarar da wasu 'yammata su biyu a tsaye, fita yayi daga cikin motar ya nufi inda wad'annan 'yanmatan suke kai masha Allahu kyawawa ne ajin farko, sanye suke da wasu d'ammun riga da wando sun yafa wani d'an k'aramin mayafi, k'are musu kallo yayi bai tab'a ganinsu a club d'in ba "Yau akwai chilling kenan, wad'annan daga ganinsu sababbin hannu ne" ya fad'a a zuciyarsa a fili kuma ya ce "Hi bebs" cikin wata iriyar muryarsa ta shu'uman 'yan bariki, murmushi suka sannan suka ce Jabir d'an tuwa, bai yi mamakin jin sun fad'i sunansa ba domin kuwa Jabir yayi k'aurin suna gurin iskanci da shaye-shaye, murmushi yayi sannan ya ce "Sannunku bebs ya kamata ku fad'a min sunayenku domin nima nasani" d'aya daga ciki ta ce "sunana zulaihat amman zaka iya kirana da Zuly baby, sai ta nuna d'ayar ta ce wannan kuma sunanta Ummita" Jabir yayi kayatatcen murmushi sannan ya kama hannayensu yayi cikin hotel d'akinsa ya nufa ya bud'e sannan suka shiga gaba d'ayansu suka bage hajarsu a kan gado Jabir yana kwance a kan gadon su kuma sun kwanta a jikinsa suna shafa shi tare da kissing d'in jikinsa (tofa jama'a Jabir bai saduda ba, Allah dai ya kyauta) haka sukai ta aikata bad'ala har sai wajen k'arfen biyar da rabi sannan Jabir ya tashi daga kan su Zuly yayi wanka ya dawo ya fara kok'arin shiryawa Zuly da Ummita suka matso kusa dashi suka shiga shiryashi Jabir kuwa wani irin farin ciki ne ya kamashi tabbas wad'annan 'yammatan sun iya soyayya sai da suka gama tsaf sannan ya tashi ya bashi rabar 'yan dubu dubu ya fita daga d'akin Zuly da Ummita murna fal ciki dan tunda suke harkar bariki babu wanda ya tab'a basu dubu ashirin ma barantana har a basu rabar 'yan dubu dubu, shi kuwa Jabir ko cikin club d'in bai shiga ba ya shiga mota ya nufi layinsu Khadijatullahi.

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

*Poly🔱🏨*

Wajen k'arfe shida dai-dai aka tashi daga makarantar, su Khadijatullahi suka fito daga aji Hafsa ta hango Yaya Safwan a jikin motarsa ya hard'e hannunsa a k'irjinsa yana ta baza idanuwana ya ga inda zai hango Hafsa gefensa wani kyakkyawan yaro ne wanda shekarunsa ba zai huce 6 ba,kamanninsa d'aya da yaron, Hafsa cike da mamaki had'i da bak'in ciki take nunawa su Amatullahi gurin da Yaya Safwan d'in yake ta ce "kun ga wanchan tsohon azzalumin yazo tare da d'ansa" Kallonsa suka yi sannan Amatullahi ta ce "gurinki ina ga ya zo" tsaki Hafsa ta ja sannan ta ce "wannan kuma shi ya sani" Yaya Safwan ya hango Hafsa tare da wasu yammata su biyu da sauri ya kamata hannun Khalid suka nufi gurin da suke, Hafsa ce a tsakiyarsu dan haka yana isa gurin yayi musu sallama "Assalamu alaikum" Khadijatullahi da Amatullahi ne suka amsa masa sallamar "Wa'alaikumussalam" suka yi gaba domin su basu damar yin magana, Hafsa ganin haka ita ma ta bi su da sauri Khalid ya kama hannun Hafsan yana cewa "Mommy ki tsaya Abbana zai yi magana dake dan Allah" kallon yaron tayi kamar ta ture yaron sai kuma ta tsaya Safwan ya k'araso inda suke ya dafa kan Khalid tare da cewa "Nagode yarona" Safwan ya bud'e baki zai yi mata magana ta dakatar dashi da cewa "yanzu ina tare da bestyna ka bari ka zo gida muyi magana" tayi maganar ba tare da ta kalleshi ba, tafiya ta fara yi Khalid yana biye da ita tsayawa tayi tana kallonsa ta bud'e baki zata yi masa magana Khalid ya rigata da cewa "Mommy zan biki dan Allah karki ce A'a" Hafsa ta ce "Ka tambayi Abbanka idan ya bar ka sai mu tafi" Safwan ya ce "Haba babyna ai kema Khalid kamar 'dan ki ne dan haka zaki iya tafiya dashi zan zo in d'aukeshi daga nan sai muyi maganar" kama hannu Khalid d'in tayi sannan ta nufi inda su Khadijatullahi suke d'an har sun fita daga cikin makarantar tana zuwa gurin da su Amatullahi suke ta watsa musu harara sannan ta ce "Shine zaku wani tafi ku bar ni" Murmushi Amatullahi tayi sannan ta ce "Ahh mun tsaya ai dole mu baku guri domin a ji dad'in bawa flower ruwa sosai".

Khadijatullahi tayi dariya ganin irin yadda Hafsan take hararar Amatullahi fuskarta a murtuke, drivern Hafsa ne ya zo suka nufi motar gaba d'aya, haka suka nufi layin gidansu Khadijatullahi suna isa, tun kafin su fito daga motar Khadijatullahi take bin wata mota mai numfashi da ta gani a kofar gidansu mamaki ya cika zuciyarta, haka suka fito daga motar bayan sunyi sallama da Hafsa, Amatullahi ta kalli Khadijatullahi ta ce "besty yau bazan shiga gida ba ki cewa Aunty Murja zuwa anjima zan dawo akwai abu mai muhimmancin da zan yi ne" Khadijatullahi ta ce "to shikenan besty" Amatullahi ta nufi hanyar gidansu domin kuwa yau su Inna Larai sai ta tabbatar ta koya musu hankali, Khadijatullahi haka ta nufi kofar gidansu zuciyarta na buguwa, Jabir kuwa yana ganin Khadijatullahi ya bud'e motar ya fito idanuwansu suka had'u Jabir yana mata wannan Shu'umin murmushin nasa, Khadijatullahi tayi baya zuciyarta na bugawa idanuwanta suka firfito jikinta ya maka rawa tana nuna sa da yatsa tana kok'arin kiran sunan "jaa.....ja....jabir".
Jabir ya nufi inda Khadijatullah take tsaye idanuwansa a kan cikinta "naji ance wai kina da ciki" sai Kuma yayi wani irin murmushin mugunta tare da ya mutse fuska sannan ya ce "Wayyo ni Jabir ina da k'arfin jini ace daga kwanci da mace sau d'aya har ta harbu ciki ya bayyana" cikin dakewa Khadijatullah ta fara magana "kaii tsinanne kayi gaggawar barin kofar gidan kafin na saka an jagaliya suyi min yaga-yaga da naman jikinka, shege d'an gidan shegiya" tayi maganar cikin zafin nama domin kuwa yau zata koyawa Jabir hankali zai san ita ma bawai k'anwar lasa ba ce Jabir ya kalleta sosai ya ga irin hucin da take kamar tsohuwar zakanya ya shek'e da wata iriyar dariya sannan ya ce "duk ki gama zagina karki ga nazo nan kofar wannan matsayacin gidan naku ki ce zaki yi min rashin mutunci ai kin san waye Jabir kuma kin san ba k'aramin aikina ba me wallahi yanzu a gaban kucakan 'yan layin naku nayi miki abin da ya faru ranar Asabar 26 ga wata march k'arfe 1 zuwa 2 na dare" wani irin a zababben mari ta wanke shi dashi hagu da dama sai da ta jera Masa sau biyar sannan fara magana "Eh tabbas nasan waye kai, Kai d'in ba kowa ba me in Banda dabba, Kuma ka sani idan a wanchan ranar kayi min ba yadda zan yi to yanzu baka Isa ba Jabir nima d'in nan da ka ke ganina ba k'aramar tantiriyar mara mutunci ba ce, wallahi Jabir na tsane ka na tsani duk wani Abu da ya dangance ka, Jabir idan baka bar nan kofar gidan ba zan iya kashe ka" magana take cikin wani irin yanayin bak'in ciki muryarta duk a shshshak'e, Jabir yaji matuk'ar jin zafin Marin da Khadijatullah tayi Masa domin kuwa tunda yake babu Wanda ya tab'a Marin shi, cikin zafin nama yake nuna Khadijatullah da yatsa Yana cewa "ba ni kika mara ba, wallahi ki jira zaki ga abin da zai biyo baya Kuma ki rubuta ki ajiye ni Jabir zan k'ara aurenki a Karo na biyu Kuma sai nayi miki abin da yafi Wanda nayi miki a baya" Yana fad'ar haka ya nufi motarsa ya bud'e zai shiga ya ji maganar Khadijatullah "Lallai Jabir sai yau na tabbatar Kai ka fi dabba ma, wa zaka aura?to Ina Mai tabbatar maka ni Khadijatullah na fi k'arfin ka, sai dai ka auri wannan shashashar uwar ta ka domin ita ce dai-dai kai, banza a jawo dak'ik'i Kuma insha Allahu sai kayi mutuwar da sai ana tattaro naman jikinka sai kayi mutuwar da ba za'a iya gane gawarka ba, na tsane ka na tsane shege Mai hali timakai" tana gama fad'ar haka ta shiga gida da gudu tana kuka, Jabir kuwa murmushi yayi domin kuwa yasan Yana zuwa gurin wad'annan kawun nata ya basu kud'i dole ko tana so ko Bata so a d'aura auren (ni kuwa 'yar mutanan zazzau nace Jabir ka makaro😂)

Ya shiga motarsa ya ja ya nufi gidansu kawun Khadijatullah, ko da ya je ya ga gidannasu gaba d'aya an ruguje shi, Nan ya tambayi wani saurayi a kan meya faru aka ruguje gidan Kuma Ina mutanan gidan, nan saurayin ya fad'a Masa duk abin da ya faru sannan ya d'ora da cewa "yaran gidan Kuma tun ranar da aka kawo gawarsu Kawu Sani suka tattara suka bar garin babu Wanda yasan inda suka je" Yana gama sanar dashi ya juya yayi gaba Jabir ya daki motarsa yanzu shikenan sai ya auri Teemarh damar abin da yaso shine ya samu a mayar da aurensa da Khadijatullah hakan ne zai saka ba zai auri Teemarh ba, gashi duk Shirin da yayi Yana nema ya ruguje, haka ya shiga motarsa ya nufi gida zuciyarsa cike da tashin hankali, Yana zuwa gidan ya tarar gaba d'ayansu suna falo Abba sai zagaye yake a falon kallo d'aya zaka yi masa ka tabbatar Yana cikin fushi ga Hajiya Asiya a gefe sai kuka take yi ita da Nihal saboda yau Alhaji Mansur tunda ya tashi ya tambaya Ina Jabir? Aliyu yace ya ganshi ya fita nan ya saka Hajiya Asiya a gaba yana Mata bala'i a kan ita ta saka shi a kan wannan tarbiyyar, Kuma yake shaida musu cewa Aure zai k'ara domin ya samarwa 'ya'yansa uwa ta gari shine fa suke ta kuka ita da Nihal, (ni kuwa nace wallahi Alhaji Mansur ka min dai-dai👏😂) Shahida da Aliyu basu ji haushi ko bakin ciki ba domin kuwa sun San tabbas Abbansu Yana buk'atar macen da zata kula dashi saboda Mami Sam Bata damu da ta kula dashi ba ita dai kawai tana zaune dashi ne saboda Yana da kud'i.

Jabir

Please Login or Register in order to submit comment