Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaku so kuji shin a ina Aliyu yaji ta'asar da Jabir ya yi wa Khadijatullahi, ba'a gurin kowa ya ji ba Shahida ce ta fad'a masa komai, domin lokacin da ya shigo gidan ya tarar da ita tana kuka da sauri ya k'arasa kusa da ita yana tambayarta menene, anan take ta zai yana masa komai da komai ta dora da cewa "Yaya Aliyu ina tsoron abin da Yaya Jabir ya yi wa Khadijatullahi ya faru a kai na ko Nihal saboda kasan ance duk abin da ka yi wa d'an wani to kai ma sai an yi wa naka, Yaya Aliyu kuma abin takaicin Mami da sanin ta Yaya Jabir yake yin komai amman bata tab'a hanashi duk abin da yake yi ganin dai-dai take yi masa" kuka yake yi sosai amman haka ya dake ya shiga rarrashin k'anwar tasa da kalamai masu dad'i sannan ya nufi d'akin Jabir d'in.


Jabir kuwa da ya ga Aliyu bashi da niyyar bud'e kofar ya koma nashi d'akin, ya zauna wayarsa ya zaro a aljihu ya kira number Teemarh kamar jiransa take ya kirawo ko ringing wayar bata yi ba Teemarh ta d'aga tare da cewa "Hello baby" Jabir cikin yanayin damuwa ya ce "Ina son kizo gida yanzun nan" ya fad'a tare da kashe wayar, murmushi Teemarh tayi sannan ta shiga wanka ta fito d'aure da d'an k'aramin towel ta shirya cikin wata 'yar yaloluwar rigar bacci wacce iya karta rabin cinyarta gaba d'aya rabin k'irjinta duk a bud'e yake shara-shara ce wacce ana iya ganin bra da pant d'in da ta saka wannan riga dai zan iya cewa da ita gwara babu, ko d'an kwali bata saka, ta baza gashin dokin da ta saka a kanta ya sauka har gadon bayanta, ta d'auki wata 'yar k'aramar jaka.

Haka ta fito tana taku d'ay-d'ay ta nufi baki titi ta tari mai adaidaita tayi masa kwatancen gidansu Jabir suka d'auki hanya, suna isa ta sauka ta biya mai adaidaita kud'insa ta nufi gate d'in gidan ta shiga kwan'kwasawa mai gadi ya bud'e mata kofar 'yar k'aramar gate d'in dan daman Jabir ya sanar dashi zai yi bak'uwa, haka ta shiga gidan tana wani rangaji daman gidan ba yau ta saba zuwansa ba dan haka ta san ko ina a gidan, Babban falo ta shiga ta tarar babu kowa kai tsaye d'akin Jabir ta nufa tana tura kofar ta ga a bud'e take dan haka ta shiga tana girgiza ko ina na jikinta, a kan gado ta tarar dashi a kwance, ta nufi gadon tana zuwa ta hau kanshi tana sumbatarsa, duk da irin yadda yake cikin bak'in ciki sai da yaji zuciyarsa tayi wasai sabida yasan Teemarh zata bashi jin dadi, haka ya murgina Teemarh ta koma k'asa shi kuma ya hau kanta ya shiga kissing d'inta tare da zame rigar jikinta, ya shiga tsotsar ko ina na jikinta (ni kuma 'yar mutanan zazzau nace Allah ya kyauta Jabir anji kunya anyi asarar rayuwa) haka dai sukai ta shek'e ayar su.

*****************************************************

*'BANGARENSU AMATULLAHI DA KHADIJATULLAHI*

Kasancewar yau suka fara lecture basu wani dad'e a makarantar ba aka tashi wajen k'arfe 11:00am Amatullahi da Khadijatullahi suka fito daga ajin suna tafiya, Hafsa ce 'yar ajinsu ta nufosu da gudu tana cewa "Sisters! Sisters!! Sisters!!!" kasancewar bata san sunansu ba shiyasa ta kirasu da haka, gaba d'ayansu suka juya tare da tsayawa Hafsa ta k'araso tana murmushi ta mik'awa Amatullahi glass d'inta tare da cewa "kin yi mantuwa" murmushi Amatullahj tayi tare da cewa "nagode sosai" Hafsa ta ce "bakomai wallahi, amman meye sunan 'yan uwan nawa" Amatullahi ta ce "Ni dai sunana Amatullahi Shu'aibu mudassir" ta nuna Khadijatullahi ta ce "wannan kuma sunanta Khadijatullahi Abbakar mai yak'i" Murmushi Hafsa tayi tare da cewa "Am glad to meet you sisters (nayi farin cikin had'uwata da ku 'yan uwana)" Khadijatullahi wacce tun da suka fara magana ba ta ce komai ba sai yanzu saboda ta fuskanci Hafsa babu ruwanta tana da faran-faran "Mu ma munyi farin cikin had'uwa da ke, amman ke baki fad'a mana sunanki ba" Hafsa ta ce "Sunana Hafsa Alk'asim mai fata, amman idan babu damuwa zan iya zama k'awarku wallahi kawai ina ganinku naga kun shiga raina sosai", "ba damuwa" Amatullahi ta fad'a a takaice, haka suka nufi bakin gate d'in su uku Hafsa suna fita sai ga drivernta yazo d'aukanta, kallonsu tayi tare da cewa "Sisters kuzo mu rage mu rage muku hanya" babu musu suka nufi motar tare,domin kuwa sun san ko sun k'i yadda suka ga babu masu adaidaita a ta wajen dole sai anyi tafiya sosai kuma ga Khadijatullahi ba wata isasshiyar lafiya ce da ita ba, ba za ta iya tafiyar ba, Amatullahi ta ce tayi musu kwatancen unguwarta su har kofar gida, aka kai su suka sauka tare da yiwa Hafsa godiya Hafsa ta ce "Haba sisters menene na godiya ai mun zama d'aya" Amatullahi ta ce "Haka ne kam, sai mun had'u gobe" Hafsa ta ce "to shikenan" daga nan driver yayi wa motar key suka nufi gida, Amatullahi ta k'arb'i jakar Khadijatullahi suka nufi cikin gida, kai tsaye d'aki suka shiga bakinsu d'auke da sallama, Aunty Murja wacce take kan gado a kwance tana karanta wani littafi na *Na Hafsa Zubairu Sambo* me suna *Ikhlas* tashi tayi tana yi mush sannu da zuwa "Barkanku da dawowa 'yan k'annena" murmushi suka yi gaba d'aya Amatullahi ta zauna tana bawa Aunty Murja labarin Hafsa da kuma irin k'irkinta Aunty Murja ta ce "Ahhh gaskiya tana da kirki sosai Allah ya saka mata da mafificin alkhairi" suka amsa da "Amin" Khadijatullahi ta samu guri ta zauna a kan yaloluwar taburmar da take bage a d'akin wacce duk ta gama jin jiki ta yayyage, Aunty Murja ta shiga basu labarin littafin da take karantawa irin yadda Hilal yake wulak'anta Ikhlas wacce ta kasance tana mutuwar son shi kamar ranta, Amatullahi cike da jin haushi ta ce "Ai ni wallahi Aunty Murja babu ni babu maza shiyasa ni babu ruwana da saurayi namiji hmmm namiji kenan" Amatullahi ta k'arasa maganar cikin wani irin yanayi

Khadijatullahi dai sun sosa mata inda yake mata ciwo hawaye suka shiga zubo mata shar-shar da sauri Amatullahi ta zo tana goge mata tana bata hak'uri "ki yi hak'uri besty kin ji komai zai wuce kuma insha Allahu Jabir sai yayi mummunar k'arshe" Khadijatullahi ta ce "Allah ya yarda ya ubangiji ka saka min" tayi maganar tare da k'ank'ame Amatullahi tana kuka ita ma Amatullahi kukan ta fashe dashi, Aunty Murja ce ta sauko daga kan gado tana rarrashinsu, har suka yi shuru abinci ta zubo musu suka d'an tab'ashi kad'an suka tureshi, rufe musu abincin tayi "gashi nan idan kun gama k'uncin tunda ku baku san k'addara ba sai ku ci" ta fad'a tare da juyawa ta koma kan gadon zuciyarta cike da tausayin k'anwar ta ta.

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

*'BANGAREN GIDANSU JABIR*

Karfe biyar dai-dai goma dai-dai na dare girjin su Abba ya sauka a kano, Aliyu ya kira ya sheda masa ya sauka yana Airport haka Aliyu ya d'auki mukullin motarsa ya nufi Airport d'in ya d'auko Abba, a motar Aliyu ya shiga bawa Abba labarin duk abin da Jabir da mahaifiyarsu tare da Nihal suke aikatawa, kuma ya kwashe duk abin da Shahida ta fad'a masa a kan irin yadda Jabir d'in ya lalata rayuwar Khadijatullahi ya sana'ar dashi babu abin da ya boye masa, hankalin Abba ya tashi ransa kuma ya b'aci wato a gidansa za'a dinga yin irin wannan lalatar lallai zai d'auki mummunar mataki a kan Jabir, Nihal da mahaifiyarta su.

A haka suka isa gidan kowan nan su zuciyarsa a jagule, Aliyu yayi parking a gurin da aka tanada dan ajiye motoci, Abbah ya fita daga motar ya nufi kofar da zata sadashi da babban falon gidan Aliyu na biye dashi, Abba yana tura kansa cikin falon ya hango wata yarinya daga ita sai wata arniyar riga wacce da ita da babu duk d'aya Jabir yana rumgume da ita yana shafa ko ina na jikinta ga Hajiya Asiya a zaune a falon tana kallonsu tana murmushi, gabansa yayi wani irin fad'uwa zuciyarsa ta fara kaiwa da komowa, cikin kakkausar murya Abba ya kira sunan Hajiya Asiya da k'arfi.
"Asiya"
Hajiya Asiya ta mik'e tsaye jikinta har rawa yake "shikenan yau ta faru ta k'are kashinta ya bushe" ta fad'a a zuciyarta Jabir kuwa da sauri ya ture Teemarh daga jikinshi jikinsa na b'ari, ita kuwa Teemarh ko a jikinta sai ma gyara jikinta da take yi, Abba kuwa yana zuwa ya d'auke Hajiya Asiya da wani wawan mari hagu da dama ji kake tas! tas!! tas!!! Sai da ya yi mata mari yafi goma sannan ya kama wuyanta ya shak'e shi sosai dan har ta fara kok'arin shid'ewa, Alhaji Mansur bashi da saurin fushi amman idan har ka sake yayi fushi to ka shiga uku domin bai iya fushi ba, Jabir cikin rawar murya ya ce "Abba karka kasheta Mami ce fa" ai bai san sanda yayi wurgi da Hajiya Asiya ba taje ta bugu da hannun kujera ta fad'i kasa sumammiya, Alhaji Mansur ya koma kan Jabir ya shiga dukanshi ta ko ina komai ya d'auka maka masa yake, Shahida ce ta fito daga d'akinta da gudu dan jin hayaniya a falon ganin Mami a k'asa Abba kuma yana d'aukar komai yazo masa a hannu yana makawa Jabir yasa ta kwalla wani irin ihu dai-dai lokacin Nihal ta shigo gidan cikin shigarta wacce sai ka rantse ba musulma ba ce, ai kuwa Aliyu yayi kanta da duka tana ihu ya gwara kanta a jikin bangon d'akin ta fad'i kasa kanta yana fitar da jini amman Aliyu bai kyaleta ba haka yayi ta dukanta kamar Allah ya aikoshi, Shahida ta rasa ya ya zata yi da ranta duk ta bi ta rud'e ruwa ta d'auko a fridge mai sanyi ta shek'awa Mami, ta farka a jijice tana kuka, Shahida ta koma gurin Abba tana rokonshi da ya dena dukan Jabir domin kuwa duk ya farfasa masa jiki ko ina na jikinsa jini yake fitarwa, da kyar ta samu Abba ya bar Jabir ta rik'eshi tana bashi hak'uri, Teemarh da taga gidan ya hargitse ta nufi hanyar fita da sauri domin kuwa tana tsoron kar kuma su juyo kanta, Abba cikin kakkausar murya ya tsayar da ita "Ke tsaya anan" tsayawa Teemarh tayi jikinta na rawa domin kuwa ta ji tsoron irin dukan da ya yiwa Jabir d'in, Shahida kuwa gurin Aliyu ta nufa "Yaya Aliyu dan Allah kayi hak'uri ka kyaleta please darling brother" tayi maganar cikin kuka, Aliyu ya je ya nufi kan kujera ya zauna zuciyarsa cike da bak'in ciki, da kyar Shahida ta iya d'aga Nihal dan kuwa Nihal ta gama galabaita bata iya tsotsi da jikinta numfashin ma dakyar take iya fitarwa, kusa da Mami ta zaunar da ita, ita ma ta zauna Abba kuwa yana tsaye cikin muryar da take nunawa yana tsantsar bakin cikin ya fara magana "nagode da irin yadda kuka mayar min da gida, gidan karuwai, amman ku sani daga yau ba zaku sake yin gangancin mayar min da gida na karuwai ba, ya nuna Jabir da yatsa sannan ya ce "nayi nadamar haihuwarka kuma nasan duk irin tarbiyyar da kake kai a yanzu uwarka ce ta dora ka a kai, dan haka nan da wata d'aya za'a d'aura aurenka da wannan yarinyar" ya nuna Teemarh da yatsa, wani irin farin ciki ne ya lillib'e Teemarh Jabir d'inta zai zama mallakinta, Jabir kuwa gabansa ne yayi mugun fad'uwar cikin muryar tashin hankali ya ce "Abbah dan Allah dan manzon Allah kayi hak'uri Teemarh ce fa, wallahi ba zan iya aurenta ba karuwa ce ta gama zubar da mutuncinta, duk wani d'an iska na garin nan babu wanda bai santa a mace ba, ni na yarda ka aura min duk wadda kaga dama amman dan Allah ban da Teemarh".

Teemarh ta kalli Jabir tana cike da mamakin kalamansa yau Jabir ne yake kiranta karuwa kuma yake cewa ba zai aureta ba, bayan shine mutum na farko da ya fara saninta a 'ya mace cikin muryar kuka ta fara magana "Lallai Jabir tabbas na yarda da cewa kai d'in macuci ne mayaudari ne kai har kana da bakin da zaka kirani da karuwa bayan kai ne ka fara lalata min rayuwa Jabir wallahi kai ba mutum bane kai shad'an ne, ko shad'an ba zai tab'a aika irin wannan abin ba" cikin tsawa Abba ya dakatar da ita "Ke ya isa haka, kai kuma d'an uwarka aure kamar anyi an gama". Fita Teemarh tayi daga gidan tana kuka mai ban tausayi, Jabir ya nufi d'akinsa zuciyarsa cike da tashin hankali tabbas zai bi ko wacce iriyar hanya domin ya ga bai auri Teemarh ba, Abba ya juyo kan Nihal yana nunata da yatsa "kema d'an uwarki ki shirya aure zan miki domin ba zaki jawo min magana ba shegiya 'yar gidan gantalalliya" yana gama fad'ar haka ya juya ya nufi d'akinsa Aliyu da Shahida ma kowannan su ya koma d'akinsa aka bar Mami da Nihal, Nihal ta rumgume Mami tana kuka tana son tayi magana amman ta kasa, haka dai suka zauna su kad'ai a falon kowannan su cike yake da tsantsar damuwa da tashin hankali a cikin zuciyar.

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

*'BANGAREN KHADIJATULLAHI DA AMATULLAHI*

Hankalin Khadijatullahi ya fara kwanciya kuma ta fara rage damuwa da tunanin da take yi, kullum a makaranta zaka gansu su uku ko a aji ma su uku suke zama a banci Hafsa tana matuk'ar jii dasu Khadijatullahi yau ma kamar kullum suna zaune a kujerun roba farfagiyar makarantar a k'asan wata bushiya, Hafsa ta kalli kayan jikinsu Khadijatullahi wanda ya kasance iri d'aya ta ce "Gaskiya fa bana jin dad'in abin da kuke min kuna ware ni a cikin ku" Amatullahi ta kalleta fuskarta d'auke da mamakin abin da Hafsa ta fad'a ta ce "Haba hafsiyy ya za'a yi mu ware ki a cikinmu bayan komai tare kuke yi da ke", Khadijatullahi ta ce "wai ma tsaya me muka yi miki da kika fad'i haka" Hafsa ta ce "gashi nan kuwa komai na ku tare kuke yi kama daga kaya, mayafi, hijabi, d'inki , takalmi, amman ni sai dai ku barni ni kad'ai kayana daban" murmushi suka yi gaba d'aya, Amatullahi ta bud'e baki zata yi magana wayar Hafsa ta hau ruri, Hafsa ta duba screen d'in wayar lokaci d'aya yanayin ta ya sauya hawaye suka fara ambaliya a fuskarta,l m hankalinsu Khadijatullahi yayi matuk'ar tashi cikin rawar murya Khadijatullahi ta ce "Hafsa me yafaru?" kallonsu tayi cikin tashin hankali ta fara magana "ina cikin tashin hankali sisters sabida irin muguwar yaudarar da namiji yayi min" Khadijatullahi da Amatullahi suka had'a ido gabansu yana fad'uwa, Amatullahi ta ce "Hafsa kenan kema kina nufin kin had'u da bakin cikin d'a namiji", Hafsa ta yi murmushi mai ciwo tare da cewa "Amatullahi kedai bari kawai", Khadijatullahi cikin sanyi murya ta ce "ke kuma me namiji yayi miki Hafsa" Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa "Kamar yadda na fad'a muku sunana Hafsa Alk'asim mai fata kasancewar ni kad'ai ce a gurin iyayena suka d'auki son duniya suka d'ora min, na taso cikin gata babu abin da nake nema na rasa a lokacin da na kai shekara goma sha takwas, Yaya Safwan d'an k'anwar Abbana ya fara nunawa yana sona amman ni kuma ina basarwa, a hankali a hankali soyayyar Yaya Safwan ta ginu a cikin zuciyata har ina jin idan babu shi bazan tab'a iya rayuwa ba ko wuni nayi ban ganshi ba hankalina sai ya tashi inyi ta kuka har sai yazo na ganshi sannan zan sami nutsuwa, ganin irin tsantsar soyayyar da muke nunawa junanmu yasa su Abbana suka saka ranar aurenmu, kwatsam wata rana, ranar da bazan tab'a mantawa da ita a tarihin rayuwa ba Yaya Safwan yazo har gida ya sami Abbana ya fad'a masa wai bazai iya aurena ba, saboda ya gano cewa ni karuwa ce ina bin maza, kuma shi gaskiya bazai iya auren karuwa, lokacin da Abbana yazo ya fad'a mana abin da Yaya Safwan ya ce masa ban yarda ba hara sai da naje na sameshi har gida ya maimaita min irin abin da ya fad'awa Abbana, yayi min zagin cin mutunci nayi kuka nayi kuka har nagodewa Allah haka na kwaso k'afafuwana dakyar na dawo gida, Ummie mahaifiyar Yaya Safwan ta sako shi a gaba suka zo har gida amman Yaya Safwan ya ce shi ba zai tab'a aurena ba, amman in har aka tilasta masa ya aureni to tabbas a ranar da aka kai ni suzo su d'auki gawa ta dan wallahi kasheni zai yi, haka Ummie tayi ta kuka tana bani hak'uri Abbana ya ce mata babu komai suka tashi suka tafi, in takaice muku sisters har kwanciya nayi a asibiti ba na iya gane kowa,Allah ubangiji yasa dai akwai sauran kwana na a gaba, muka dawo gida Mommyna ta cigaba da rarrashina, ranar wata asabar sai ga mai gadin gidanmu ya shigo hannunsa rik'e da invitation card ya mik'awa Mommyna ya ce Yaya Safwan ne ya bada a kawo min nan da kwana uku masu zuwa za'a d'aura aurensa nayi kuka Mommyna tayi ta rarrashina, haka na k'arbi katin na yayyagashi nayi watsi dashi, na tashi na shige d'akina, bayan Auren Yaya Safwan da kusan wata hud'u shine aka samar min admission anan makarantar ana sauran kwana uku in fara zuwa makaranta ina zaune a cikin d'akina wayata ta shiga ruri ko dana duba sai naga number ce babu suna, na d'aga tare da yin sallama daga chan b'angaren ya amsa sallamar tare da kiran sunana gabana ne ya fad'i jin muryar Yaya Safwan da sauri na kashe wayar nayi wurgi da ita, na cigaba da yin harkokina a ranar sai ga Yaya Safwan yazo har gida, muna zaune a falo dani da Mommyna da Abbana muna hira yana zuwa gaban Abbana ya tsugunna yana kuka yana fad'ar wai ayi hak'uri da abin da yayi sharrin shaid'an ne, yasan yayi min sharri amman wallahi yana tsananin sona, takaici da bakin ciki ya lillib'e ni, ban san sanda na tashi nace ya tashi ya fitar mana daga gida, ya tashi zai k'araso gurin da nake na shiga d'akina da gudu tun daga ranar shine kullum sai ya kirani ni kuma bana d'agawa yanzu ma shine ya kirani" Hafsa ta k'arasa maganar tana kuka mai tsima zuciyar mai sauraro.


Amatullahi ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ita dai lamarin maza yana bata tsoro, kwata-kwata babu tausayi ko imani a zuciyarsu tashi tayi ta matsa kusa da Hafsa tana goge mata hawayen fuskarta tana rarrashinta, Khadijatullahi wacce fuskarta tayi sharkaf da hawaye ta ce "wai meyasa maza zazzalumai ne, gaba d'ayansu basu da imani macuta ne" tayi maganar tana sharce hawayen da suke ambaliya a fuskarta, Amatullahi ta ce "Hafsa ki yi hak'uri tabbas Yaya Safwan ya yaudareki kuma yayi miki k'azafi amman da zaki ji abin da Jabir ya yi wa Khadijatullahi zaki san abin da Yaya Safwan yayi miki ba komai ba ne" Hafsa cike da k'aguwar son jin abin da Jabir yayi wa Khadijatullahi ta ce "Sister Khadijatullahi kema kenan kin had'u da bak'in cikin namiji? Amman ke meya faru dake?"

wani irin murmushin mai ciwo tayi sannan ta ce
"Kamar yadda kika sani sunana Khadijatullahi Abbakar Mai yak'i iyayenmu mu biyu suka haifa daga ni sai Aunty Murja wacce ta kasance yayata kuma mahaifiyata, Mahaifina Abbakar mai yak'i yana da rufin asirinsa dai-dai gwargwado domin yana tafiye tafiye zuwa wasu garuruwar ya saro shanuwa ya dawo ya siyar dasu anan garin kano, wannan abin ne yasa gaba d'aya 'yan uwansa suka tsaneshi duk da cewa ciki d'aya suka fito da su, suke nuna mana tsana sosai har ya kasance bama zuwa gurinsu, mahaifiyar babbana da mahaifinsa sun rasu tun kafin babbana ya yi aure sakamakon gobarar da suka yi a gidan cikin dare gaba d'aya suka k'one, ranar wata lahadi ranar da bazan tab'a mantawa da ita babbana ya yi tafiya zuwa zaria domin saro shanuwa, sai gawarsa aka kawo mana ya rasu sakamakon hatsarin da suka yi motar da su babbana suke ciki wata gingimari ta daki motar babu wanda ya rayu dan har driver mutuwa ya yi, lokacin da innarmu ta ga gawar babbana ta yanke jiki ta fad'i ko da muka kai ta asibiti aka shiga da ita emergency room muna nan zaune sai aka fito da ita fuskarta a lillib'e da sauri na k'arasa gurin likitan jikina na rawa nake tambayarsa meyasa suka rufewa innata fuska, ku yi hak'uri domin Allah ya karb'i abinsa abin da likitan suka ce mana kenan, nan Aunty Murja ta fasa ihu ta zube a k'asa tana rusa kuka, nima naje kusa da ita na k'ank'ameta ina kuka, haka muka dawo gida mak'obtanmu suka shigo aka yiwa inna da babba wanka aka kai su makwancinsu na gaskiya, haka rayuwarmu ta cigaba da tafiya muna zaune a gidanmu daga ni sai Aunty Murja duk duniyar tayi mana zafi" A dai-dai nan Khadijatullahi ta tsaya saboda jin k'arar kad'ai k'ararrawar komawa aji "to bari in tsaya anan idan mun fito lokaci bai k'ure ba sai in cigaba idan kuma lokaci ya k'ure gobe idan Allah ya kaimu sai in k'arasa miki" Khadijatullahi tayi maganar cikin muryar kuka.

Hafsa ta ce "Ko lokaci ya k'ure ma sai in bi ku har gida dan yau sai naji labarinki gaba d'aya sannan zan tafi gida" tayi maganar ita ma hawaye na kok'arin zubo mata share hawayen tayi sannan ta matsa kusa da Khadijatullahi ta kama hannunta ita da Amatullahi suka tashi suka nufi ajin zuciyoyinsu cike da bakin ciki.

Wajen k'arfe shida suka tashi daga makarantar suka fito bakin gate Hafsa ta kirawo Mommy a waya ta ce mata yau ba zata samu dawowa da wuri da zata biya gidansu Khadijatullahi da yake Mommy ta san labarin su Khadijatullahi dan haka ta ce to shikenan bakomai, mai adaidaita suka tara ya kai su har kofar gida Hafsa ta biya kud'in, suka shiga gidansu Khadijatullahi amman abin mamaki basu tarar da Aunty Murja ba, Khadijatullahi ta ce "To ina Auntyna taje" Amatullahi ta ce "haba besty kila taje wani gurin ne" haka suka zazzauna a kan taburmar Hafsa ta ce "wallahi har na k'agu in k'arasa jin labarinki" wani murmushi mai ciwo Khadijatullahi tayi sannan ta ce "Yanzu kuwa zaki ji labarina gaba d'aya" Khadijatullahi ta fad'a cikin wani irin yanayi sannan ta fara magana.

"ranar wata jumma'a muna zaune a tsakar gida ni da Aunty Murja lokacin kwanan su babbana hamsin da mutuwa sai ga Kawu Sani ya shigo gidan ko sallama babu mun yi mamaki sosai da ganinsa domin tunda su babbana suka mutu babu wanda yazo daga cikin 'yan uwansa wani matashin saurayi ne wanda kana kallonsa zaka san naira ta zauna wasu k'ananun kaya ne a jikinsa wanda ni a ganina dasu gwara babu, yake biye dashi a baya su Kawu lawan da Kawu Sanusi suna biye dashi a baya mik'ewa muka yi tsaye muna musu sannu da zuwa babu wanda ya amsa mana daga cikinsu sai ma kallon k'ask'anci da suke bin mu dashi, gaba d'aya na tsargu da irin kallon da wannan saurayin yake min, Aunty Murja ta nufi d'aki da niyyar d'auko taburma ta shimfid'a musu Kawu Sani ya dakatar da ita da cewa Ke Murja ina zaki je Aunty Murja ta ce taburma zan d'auko muku cikin tsawa ya ce ba zama ne ya kawo mu ba, mun zo ne mu sanar da ku cewar mun yiwa Khadijatullahi miji nan da sati d'aya za'a d'aura auren kuma ba kowane mijin ba sai wannan ya nuna wannan saurayi tare da cewa sunanshi Jabir ya ga Khadijatullahi yazo har gurinmu ya nuna yana son ya aureta, wani irin ihu na kwalla tare da cewa dan Allah Kawu kayi min rai wallahi bana son shi baka ganshi ba kalli kayan da ya saka fa, wani irin zafaffan mari Kawu Lawan ya wanke ni dashi wanda har sai da na rasa ganina na 'yan mintinue, da sauri Aunty Murja ta jawoni ta rumgumeni tare da dafe kan kuncina inda Kawu Lawan ya mareni, dan ubanki bakin ciki zaki yi mana shagiya mai mugun hali irin na ubanta, kai

Please Login or Register in order to submit comment