Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunda yayi musu kallo d'aya ya watsar haka ya nufi d'akinsa yana cika yana batsewa kamar zai fashe, Abba ya k'are masa kallo daga sama har k'asa wai ace wannan d'ansa ne yake irin wannan shigar ya fita waje sai kace tsohon shaid'ani (ni kuwa nace Abba ai Jabir wallahi yafi shaid'an🤣) cikin zafin nama ya nufeshi gadan gadan ya jawoshi ya kifa masa mari wanda har sai da ya rasa ganinsa na tsawon dak'ik'a guda ya fad'a kan kujerar da take kusa da kujerar da Aliyu yake zaune, Abba ya ce "dan ubanka ina ka je tun safe sai yanzu ka dawo" Jabir ya d'ago ya kalli mahaifinnasa da rinannun idanuwansa ya ce "Club naje kuma......" Ai jin wani sabon marin da ya ji a fuskarsa yasa yayi shuru da maganar da zai k'arasa, haka Alhaji Mansur ya rufeshi, Aliyu ya tashi ya rik'e Abban yana bashi hak'uri shi kuwa Jabir tashi yayi sai da ya kusan shiga d'akinsa ya juyo ya kalli mahaifinnasa ya ja tsaki tare da tofar da yahu, nan fa Alhaji Mansur ya fusata yana kok'arin fusge rikon da Aliyu yayi masa, amman Aliyu ya riga ya rik'eshi sosai Jabir ya shiga d'akinsa ya saka mukulli, Abbah ya ce "to wallahi ka shirya goben nan za'a d'aura maka aure da wannan k'aruwar yarinyar shege gantalallan banza d'an iska mara kunya mara tarbiyya" Jabir duk yaji abin da mahaifinnasa ya ce dan da k'arfi yake magana, kwanciya yayi a kan gado yana tuna maganganun da Khadijatullahi ta fad'a masa "na tsaneka insha Allah sai kayi mutuwar sai ana tattaro naman jikinka sai kayi mutuwar da ba za'a iya gane gawarka ba" bai san meyasa ba wannan maganar ta tsaye masa a rai kuma ya ji son cikin da Khadijatullahi take dashi a zuciyarsa, tsaki ya ja tare da cewa "aikin banza" haka ya cigaba da sake-sake a cikin zuciyarsa.

Abbah kuwa dakyar Aliyu da Shahida suka lallab'ashi ya shiga d'akinsa su ma suka shiga nasu d'akin, Mami da Nihal kuma abin duniya duk ya ishe su, haka dai suma suka nufi nash d'akin kowannan su zuciyarsa cike da bakin ciki da tashin hankali.


••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••

*'BANGAREN KHADIJATULLAHI*

Tana shiga gidan da gudu tayi gurin da Aunty Murja take zaune tana tankad'an garin tuwo ta fad'a jikinta tana kuka cikin jijicewa Aunty Murja ta ce "Khadijatullahi meyafaru? Wani abun aka yi miki?" cikin kuka mai tsima zuciyar me sauraro ta fara magana "Aunty Jabir Jabir ne" zaro ido Aunty Murja tayi tare da cewa "A'uzubillahi minashshed'anir rajim Allah kayi mana tsari dashi, a ina kika ganshi" anan ta kwashe labarin duk yadda suka yi dashi ta fad'a mata, Aunty Murja ta ce "to aniyyarsa ta bi sa wallahi mun fi k'arfinsa, ki daina damuwa kin ji k'anwata ina tare dake ba zan tab'a bari ki wulak'anta ba" haka Khadijatullahi ta kwanta a jikin Aunty Murja, dakyar Aunty Murja ta iya k'arasa tankad'an sannan ta tureshi gefe d'aya, domin ji tayi ma ba za ta iya yin tuwon ba, daman akwai ragowar garin kwaki da sugar suka jik'a suka sha shi, suka shiga d'aki domin yin bacci haka suka kwanta kowanna su da abin da yake sak'awa a cikin ranshi.

```'BANGAREN HAFSA🥴```

Tunda ta shiga gida duk inda tayi Khalid yana biye da ita kamar jela, haka tai ta jiran Yaya Safwan domin ya zo ya d'auki Khalid su tafi gida amman har wajen k'arfe 10:30pm na dare babu alamar zuwan Yaya Safwan,ta kama hannunsa suka nufi b'angarenta domin suyi bacci, a kan k'aton gadonta suka kwanta Khalid ya rumgumeta sosai, yana tayi mata labarin makarantarsu "Mommyna kin ga a class d'inmu na fi kowa kok'ari, Abbana har keke ya siya min da nazo ta d'aya" Hafsa ta ce "Kai masha Allah yaron k'irki gaskiya dole Abbanka ya siya maka keke" murmushi Khalid yayi sannan ya ce "Mommy kinga an kusan fara exams idan nazo ta d'aya ke me zaki siya min?" Hafsa ta ce "Me kake so na siya maka?" Khalid ya ce "Ina son ki siya min waya na dinga yin games" Hafsa ta ce "to karka damu insha Allahu zan siya maka waya" cike da jin dad'i Khalid ya ce "da gaske Mommy" Hafsa ta ce "Eh mana, amman Khalid meyasa ka ke ce min Mommy?" Khalid ya ce "Abbana ne ya ce in dinga ce miki Mommy saboda kema Mommyna ce" shuru Hafsa tayi tana kallon yaron, "Lallai wato kitumurmurar da Yaya safwan yayi mata kenan, hmm Allah ya kyauta" tayi maganar a zuciyarta haka suka cigaba da yin hira har bacci ya kwashe su.


*******************************************************

*'BANGAREN AMATULLAHI😂*

Fans dole in dara anzo wajen fa🤣🤣Amatullahi iyayen bala'i bari muji yau da me zata jewa su Inna larai😂😂

Haka Amatullahi ta shiga gidan ta tura kai zata shiga tsakar gidan sai jin Inna Larai tayi tana cewa Lado "wannan yarinyar ba zamu tab'a barinta ba wallahi dole ne, mu kulla mata wata kitumurmurar da zata saka ubanta ya tsaneta" Lado ya ce "kamar me kenan?" Inna Larai ta shek'e da wata iriyar mahaukaciyar dariya sannan ta ce "za ka nuna cewa kana sonta zaka aureta, sai mu sanar da mahaifinta daga nan sai in fad'a maka shirinmu na gaba" Lado ya ce "Inna kin tabbatar wannan shirin naki zai saka mu rabasu" Inna Larai ta ce "rabuwa ta har abada kuwa". Amatullahi tayi wani gajeren murmushi sannan ta shiga gida da sallama sam bata nuna musu cewa taji abin da suka fad'a ba haka ta nufi d'akinta ta kwanta tana murmushi "Lado da Inna Larai kenan wallahi ni Amatullahi na fiku shaid'anci ina nan ina jiran ka furta ka na sona na yarda da soyayyarka daga nan wasan zai fara"

Wayyo ni 'yar mutanan zazzau😂🤣😂Amatullahi da Lado za'a fara soyayya🤣🤣🤣ba zan iya daina dariya ba wayyo cicina😂😂😂Ummu Juwairiyya kina jin wata drama ko😅😅

*'BANGAREN GIDANSU JABIR*

*WASHE GARI⚜️🔱*

Misalin k'arfe sha d'aya na safe Abba ya fito daga d'akinsa ya shirya tsaf cikin wata tsadaddiyar shaddarsa teal blue ko minti biyu Abba bai yi da fitowa ba Aliyu ya fito daga d'akinsa shima shadda ya sa royal blue, Abbah ya ce "Aliyu yi da sauri mun makara fa, suna ta jiranmu" Aliyu ya amsa "to Abba" fita suka yi daga falon suka nufi wajen da aka tanada dan ajiye motoci, suka shiga kai tsaye suka nufi masallaci domin d'aura auren Jabir da Teemarh, masu karatu nasan zaku ce yaya aka yi Abba ya gano iyayen Teemarh har ya je musu da maganar d'aura auren yau, tun jiya da Abba ya shiga d'aki ya k'uduri aniyar d'aura auren Jabir gobe,Aliyu yana zaune Abba ya kirashi a waya ya ce "ya gano masa a ina yarinyar take? kuma su waye iyayenta?" Aliyu bai gane wace yarinyar Abba yake nufi ba sai da yayi masa bayani, sannan ya gane a daren Aliyu ya yi bincike suka yi sa'a kuwa gidansu Teemarh ba wani 'boyayyan gida ba ne, wani abokinsa mai suna Jafar da yake a layin yake shi ya nuna musu gidan, Aliyu ya kirasa a waya domin ya taimaka masa da binciken, da yake Jafar yana ganin Jabir yana zuwa kofar gidansu Teemarh anan yake sanar da Aliyu ai yasan yarinyar dan yana ganin Jabir d'in a gurinta kullum, a daren Abba da Aliyu suka je gurin Jafar ya rakasu har kofar gidansu Teemarh ko da mahaifin Teemarh ya fito Abba ya sanar dashi abin da ya kawosu Mahaifin Teemarh Alhaji Lamid'o yayi matuk'ar farin ciki domin daman bashi da wani buri a yanzu irin ya ga ya aurar da Teemarh domin wannan Harkar barikin da take yi yana matuk'ar kuntata zuciyarsa, haka suka yi sallama ya shiga gidan yake sanar musu Teemarh kuwa tayi farin ciki matuk'a kuma nan da kudiri niyyar sai ta kuntatawa Jabir sai ta gigita rayuwarsa zai san ita ya cewa karuwa haka tayi ta saka irin wahalar da zata bashi da kuma rashin mutuncin da zata dinga yi masa, wannan kenan.

Taro yayi taro an d'aura auren Jabir da Teemarh a kan sadaki naira dubu d'ari haka su Abba suka biya ta gidan su Teemarh domin da ita zasu koma gidan, suna zuwa aka suka tarar har an shirya Teemarh cikin wani tsadaddan lace wanda Alhaji Mansur ne ya saka aka kawo mata kayan lefe akwati goma sha biyu, fuskarta a lillib'e da mayafi aka saka ta mota Aliyu wanda shi yake driving d'in ya ja motar suka nufi gida, suna isa mai gadi ya bud'e musu gate d'in tafkeken gidan suka shiga Aliyu yayi parking, Aliyu ya fito ya bud'ewa Teemarh motar ta fito fuskarta har lokacin a lillib'e take Abba na gaba suna fiye dashi a baya har suka shiga cikin babban falon gaba d'aya suna falon suna kallo Jabir ya dora k'afarsa a kan center table d'in falon, "Assalamu alaikum" suka yi sallama suka shigo, Shahida ce kad'ai ta amsa sallamar tare da yiwa musu sannu da zuwa, suka amsa mata da yawwa Jabir ya kallesu gaba d'aya sannan ya bi yarinyar da fuskarta take lillib'e da mayafi da kallon mamaki zuciyarsa cike da tambayoyi gabansa yana fad'uwa tsoro da firgici suka shigeshi mikewa tsaye yayi yana cigaba da kallon yarinyar, Mami ta kallesu sannan ta fara magana fuskarta kunshe da mamakin wacece wannan "Abban Jabir wacece wannan?" Wani irin kallo ya wurga mata domin gaba d'aya haushinta yake ji kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Matar Jabir ce Fatima" Jabir da ke tsaye cike da razana ya ce "Abba wace Fatima kake nufi, ba dai Teemarh kake son ka ce min ba" Abba yayi murmushi sannan ya kalli Teemarh ya ce " 'yata bud'e fuskarki domin su ganki" Teemarh kamar jira take ta yaye mayafin idanuwanta a kan Jabir tana yi masa wani irin kallon zaka gane kurinka, Jabir yayi baya jikinsa na rawa ashe daman jiya da Abba ya ce yau za'a d'aura auren da gaske yake shi gaba d'aya ya yi tunanin kawai fad'a yake yi, "Abba karka min haka dan la'ilaha illallahu ka ce min wasa ka ke min, Abba ba zan iya zama da karuwa ba" magana yake cikin yana yin tashin hankali, Abba bai bi ta k'ansa ba ya juya ya shige d'akinsa.

Nihal kuwa gabanta ya shiga dukan uku uku domin kuwa tasan Abba zai waiwayo kanta dan baya tab'a furta magana ba tare da ya aikata ta ba, hawaye suka shiga zuba daga idanuwanta, ta k'ank'ame Shahida da ke kusa da ita tana cigaba da kuka, hankalin Shahida ya tashi ta shiga rarrashin 'yar uwar ta ta haka ta kama hannunta suka shige d'akin Nihal d'in, Mami ma jikinta a salub'e ta nufi d'akinta, Falon ya rage daga Aliyu sai Jabir sai kuma Amarya Teemarh.

Aliyu ya kalli Teemarh tare da cewa "Aunty Fatima nikam zan huce Allah ya bada zaman lafiya, ina nan ina jiran babies da yawa nan da 'yan shekaru" murmushi Teemarh tayi sannan ta ce "To nagode Aliyu haidar" haka Aliyu ya huce yana kallon Jabir yana murmushin jin dad'i domin kuwa hakan ne ya kamace shi.

Teemarh ta kalli Jabir sannan ta fara matsawa kusa dashi tana magana tana hurga masa harara ta had'e fuskarta kamar ba ita ce ta gama murmushi ba "Jabir d'an tuwa, kai k'aramin k'waro ne kuma zaka san nii Fatima Lamid'o ka cewa karuwa sai na gigita maka rayuwarka kai baka ji ma kunyar kirana da karuwa ba to kasan ni kai ne ka fara lalata ni dan haka dole ka zauna dani a matsayin matarka, kuma ina k'ara fad'a maka da babbar murya cewa idan ka k'ara kirana da karuwa to a wannan ranar zan nuna maka nii cikakkiyar karuwa ce zan bar maka mugun tab'o a rayuwarka" tana gama maganar ta shige d'akin Jabir d'in haka Jabir ya zauna dab'as a k'asa tabbas Abba ya auro masa masifa da bala'i amman kuma dole ya san matakin da zai d'auka dan ba zai tab'a zama da yarinyar da ya gama da ita ba, babu abin da bai sani ba a jikinta, haka dai ya d'auki key d'in motarsa ya fita daga gidan zuciyarsa cike da ba'kin ciki.

*'BANGAREN KHADIJATULLAHI DA AMATULLAHI*

Amatullahi ce ta fito daga d'akinta sanye da hijabi har k'asa kasancewar yau lahadi ne babu makaranta ta nufi hanyar fita Lado da ke zaune a tsakar gida shi kad'ai yana jiran fitowarta ya nufeta da sauri yana murmushi ya sha gabanta "K'anwata tun d'azu nake ta jiran ki fito, saboda akwai magana mai muhimmancin da nake so muyi da ke", "Lallai Lado anzo dai-dai gab'ar da nake so azo" ta yi maganar a zuciyarta a fili kuma ta d'an nuna alamun mamakia fuskarta kafin ta ce "Lado yau kuma da me ka zo?" Murmushi Lado yayi sannan ya ce "K'anwata babu da abin da nazo dashi sai alkhairi, domin a gaskiya ba zan iya b'oye miki ba tun ranar da kika gama secondary school d'inki naji soyayyarki ta shiga zuciyata amman ina tsoron in fitar miki dan karki k'i amincewa Amatullahi ina sonki sosai" Amatullahk tayi wani gajeren murmushi sannan ta ce "kana tunanin zan yarda da cewa kana sona? Bayan irin abubuwan da kake min hmmm Lado kenan" Lado ji yayi kamar ya kwad'a mata mari amman sai ya tuno indai yayi hakan shirinsu zai rushe dan haka sai ya da ke tare da cewa "Haba sweety da gaske nake yi ina sonki, idan kuma kina tunanin k'arya nake yi zan je in fad'awa Inna sai ta fad'awa Abba, ina ga hakan ne zai tabbatar miki da cewa da gaske na ke yi" Amatullahi ta ce "A'a ba sai ka yi hakan ba, zan je gidansu Khadijatullahi idan na dawo zamu yi magana" Lado ya ce "To shikenan, bari in taka miki" haka suka jera suna tafiya har sai da suka kusan zuwa gidansu Khadijatullahi sannan Lado ya koma gida zuciyarsa fal da farin ciki burinsu zai cika shi da Inna Larai, Amatullahi kuwa juyawa tayi tana kallon Lado tayi wata iriyar malalaciyar dariya sannan ta ce "Lado kenan ka ri ga ka fad'a tarkon Amatullahi, daga kai har uwar taka dai-dai nake da ku, d'an iska har da wani cewa sweety" ta ja wani tsaki tare da shiga gidansu Khadijatullahi, da sallama ta shiga d'akin "Assalamu alaikum" Hafsa da Khadijatullahi ta gani zaune a kan yaloluwar taburmar d'akin suka amsa mata sallamar a tare "Wa'alaikissalam" guri ta samu kusa da Khadijatullahi ta zauna tana tambayarsu "Ina Aunty Murja" Khadijatullahi ta ce "taje gidan Hajiya Mama" Amatullahi ta ce "Allah sarki Aunty Murjarmu tana kok'ari sosai wallahi" Hafsa ta ce "Wallahi kuwa sosai ma" Amatullahi ta ce "Besty ke kuma yaushe kika zo, ko kin yi tunanin yau akwai school" Hafsa ta ce "A'a wallahi besty kawai dai ba zan iya jira har sai gobe mu had'u ba shiyasa na zo" Murmushi Amatullahi tayi ta ce "Allah sarki besty mun ji dad'i kuwa" Khadijatullahi ta kallesu tana cewa "Ban baku labari ba jiya sai ga wannan d'an barikin Jabir ya zo gidan nan" Amatullahi ta wani daki bango tare da zaginsa sannan ta ce "uban me ya kawo shi gidan nan kuma shege dan gidan tambad'add'iya" Khadijatullahi ta kwashe duk yadda suka yi ta fad'a musu, Amatullahi ta ce "ai kuwa aniyarsa ta bi sa shege ai na gaba yayi gaba, wallahi da ace ban tafi ba had'u dashi sai na saka wallahi anyi mishi dukan tsiya na saka yara suyi ta jifanshi, nima ina nan muna shirya wata babbar drama a gidanmu" Hafsa ta ce "Wace iriyar drama kuma?" Nan Amatullahi ta kwashe duk komai ta fad'a musu bata b'oye komai ba ta d'ora da cewa "Sun yi tunanin zan iya fad'awa tarkonsu ne, ai yanzu wasan ya fara" Khadijatullahi da Hafsa ban da dariya babu abin da suke yi "Kai besty wallahi ke 'yar drama ce wato tsiyar da kika tafkawa Inna Larai shiyasa ranar kika ce wai na ganta amman ban gane ita ba ce" Khadijatullahi tayi maganar tana cigaba da dariya, Hafsa ta ce "Allah ya shiryeki besty kina zuba kamshi fa" Amatullahi ta ce "Wallahi ku tsaya ku ga yadda za'a buga wannan babban game d'in" Hafsa ta ce "besty muna biye da ke wallahi" Amatullahi ta ce "ya labarin yaya safwan kuwa?" Hafsa ta tab'a baki sannan ta ce "bai zo ba ya bar min yaronsa yau kuma da sassafe ya aiko masa da kayansa a akwati" Dariya suka saka sannan a tare suka ce "Mommy Hafsa" harararsu tayi sannan ta chanza hirar zuwa ta makaranta, sai wajen k'arfe 2pm na rana driver Hafsa ya zo ya d'auketa suka tafi gida, ko minti biyar Hafsa bata yi da tafiya ba sai ga Aunty Murja ta dawo suka yi mata sannu da zuwa ta zauna ta ajiye kwanon silban a k'asa sannan ta bud'e shi jollof d'in taliya ce da macaroni ga nama da yawa haka suka had'u suka cinye abinci, hira suka zauna suna yi abin gwanin ban sha'awa.

*'BANGAREN JABIR ANGO DA AMARYARSA TEEMARH*

Jabir kwata-kwata duk yadda yake tunanin Teemarh ta huce hakan domin gaba d'aya ta chanza masa, sam yanzu bata nuna masa soyayya kalaman soyayyar da take yi masa da yanzu bata yi idan ya shigo d'akin sai dai ta bi sa da wata muguwar harara kuma abin da yake bawa Jabir haushi shine Teemarh ta daina barin sa ya kwanta a kan gado sai dai a kan kujera ya ke kwana abinci kuwa idan an raba an basu bata ajiye masa sai dai ta ci iya cinta sauran ta kaiwa mai gadi, tana zaune a kan gado ta mik'e k'afa Jabir ya banko kofa ya shigo yana ta faman huci, Teemarh tayi masa wani wulak'antatcen kallo tare da cewa "Kai meye haka zaka shigo min d'aki kana wani huci kamar tsohon mahaukaci" Jabir ya gama fusata gaba d'aya jikinsa rawa yake yi ya ce.

"Teemarh sai yau na tabbatar baki da mutunci, ashe ana baki abincina shine kike kai wa su wad'anchan matsiyatan, to wallahi baki isa ba tunda ba ubanki ne yake siyo abincin ba, shashasha 'yar gidan matsiyata" Jabir yayi magana yana cigaba da huci, Teemarh ta ce "To ai kai ne babban matsiyacin dan kuwa sun fika komai da komai wallahi, kuma da kake cewa ba mahaifina ne ya siya ba, na ji daman nace Abbana ne ya siya kuma haka nayi niyya su nake son na bawa abincin dan haka banga wanda ya isa ya hanani bawa su baba mai gadi abinci ba, kuma da kake ce min shashasha 'yar gidan matsiyata to sannu mai kud'i dan gidan k'aruna", Teemarh ta k'arasa maganar tana harararsa, Jabir ya gama fusata ya gama kaiwa k'arshe cikin zafin nama ya jayota yayi wurgi da ita kan kujera har sai da ta bugu da hannun kujerar goshinta ya fara zubar da jini, Jabir ya nufi kanta gadan-gadan Teemarh tayi saurin tashi tana nuna shi da yatsa "Jabir wallahi zaka san ni ka wurga kan kujera kuma...." bata k'arasa yin magana ba taji ya zabga mata mari har sau biyu hagu da dama ita ma kuwa tana d'agowa ta rama marin sai da ta jera masa sau hud'u sannan ta nufi hanyar fita da gudu tana kuka domin kuwa yau sai tayi wa Jabir sharrin da bazai tab'a mantawa da ita ba.

A babban falo ta tarar da mutanan gidan gaba d'aya ta je gaban Abba ta zub'e tana k'ara saka sabon kukan, Abba ya kalleta ya ce "Fatima meya faru" cikin kuka ta ce "Abba na shiga uku Jabir zai kashe ni, wai kawai yana shigowa d'akin ya fara dukana ya gwara min kai na a bango" Jabir da ke tsaye yana jin duk abin da ta fad'a dan Teemarh tana fitowa shima ya biyo bayanta "Wallahi Abba k'arya take yi wai fa dan......"wani irin mari Abba ya d'aukeshi dashi yana fad'ar "Ok k'arya take yi wannan jinin da yake zuba daga goshinta fa, shima k'aryar ne ko kana nufin ita da kanta zata jiwa kanta ciwo" ya rasa abin cewa domin kuwa Teemarh tayi amfani da wannan ciwon wajen yi masa sharri, haka ya juya jikinsa a sanyaye ya nufi d'akinsa, Abba ya kalli inda Teemarh take durkushe ya ce "ki yi hak'uri kin ji Fateema, Aliyu kira doctor ya zo ya dubata" Aliyu ya Amsa da "to" haka ko minti d'aya Aliyu bai yi da kiran doctor d'in ba sai gashi yayi sallama ya shigo da yake a unguwar yake, bandegi ya saka ya had'e mata goshin sannan ya rubuta musu magungunan da zata dinga sha, yayi musu sallama ya koma gidan shi, Teemarh ta ce "Nagode Abba Allah ya saka da Alkhairi" Abba ya ce "Amin ya Allah" haka ta tashi ta bi bayan Jabir zaune ta tarar dashi a kan kujera ya zabga tagumi, Teemarh ta shek'e da wata iriyar mahaukaciyar dariya tare da tafa hannu tana cewa "Jabir kenan ai yanzu wasan ya fara tagumi yanzu ka fara yin shi, ai wallahi sai ka gane kurinka, banza kawai" Jabir yayi murmushi tare da cewa "Teemarh kenan nii Jabir d'an tuwa kika yi wa wannan abin ko? To wallahi zan nuna miki cewa nii babban d'an iska ne, karki ga wai ina tagumi kiyi tunanin wai tsoron ki nake ji, to wallahi ba'ayi macen da zan ji tsoronta ko kuma ta takura min ba, Teemarh ki rubuta ki ajiye Jabir yana nan sai ya rugu rayuwarki gaba d'aya" Teemarh ta zauna a kan kujera tana murmushi tare da cewa "Me kake cewa maimaita inyi hadda" tsaki ya ja ya fita daga d'akin kai tsaye gurin da aka tanada dan ajiye motoci ya nufa ya ja motar da gudu har yana kok'arin kwarfe mai gadin da motar Allah ya taimaka ya kauce masa (ni kuwa 'yar mutanan zazzau nace wai Jabir an had'u da k'arfen k'afa ko nace gaba da gabanta Aljani ya taka wuta😂).

~*BAYAN WATA DAYA*~

Cikin Khadijatullahi yana k'ara girma dan yanzu watansa hud'u, duk da cewa yanzu ta rage yawan damuwa sai dai idan abin da Jabir yayi mata ya fad'o mata ta shige b'and'aki tayi kukanta mai isarta ta wanke fuskarta ta fito, ga laulayi ya sakata a gaba duk abin da ta ci sai ya dawo shiyasa kwana biyu basa zuwa makaranta ita da Amatullahi saboda Amatullahi ba za ta tab'a iya zuwa makarantar ba tare da Khadijatullahi ba, Hafsa kuwa tayi matuk'ar damuwar rashin zuwa makarantar da basa yi, shiyasa ita ma ta daina zuwa ya zamana kullum ita da Khalid suna gidansu Khadijatullahi, Aunty Murja da ta ga abin nasu ba na k'are ba ne, ranar wata Asabar bayan sun zo suna ta hira ta zauna tare da fara yi musu fad'a "Gaskiya mun ba ni mamaki sosai, yanzu ace kun daina zuwa makaranta saboda Khadijatullahi bata da lafiya bata zuwa, to insha Allahu gobe kowannan ku ya shirya zaku koma makaranta dan na gaji da zaman da kuke kullum kuka kullum cikin damuwa kuke ba za ku iya d'aukar k'addara ba kenan" Amatullahi ta kalli Aunty Murja cikin yanayin damuwa ta ce "Aunty Murja ba zamu iya zuwa makaranta ba tare da Khadijatullahi ba" Hafsa ta ce "Wallahi Aunty Murja gaskiya Amatullahi ta fad'a ba zamu iya zuwa makaranta ba tare da besty ba" Aunty Murja ta ce "Ai shine nace ku shirya gobe har Khadijatullahi dukkanku makaranta zaku tafi" suka amsa da "to shikenan Aunty Murja".

Haka kuwa aka yi washe gari kowannen su ya shirya suka fito su uku, kayansu iri d'aya motar Hafsa suka shiga drivernta ya ja su suka nufi makarantar, a makarantar ma haka Khadijatullahi tai-tayin Amai dan da har zasu dawo gida Khadijatullahi ta ce ba za ta koma gida ba har sai an tashi haka suka kyaleta har sai da aka tashi drivern Hafsa ya zo ya kai su har kofar gidan sannan ya nufi gidansu Hafsa, Amatullahi ta kama Khadijatullahi dan wani irin jiri take ji yana neman fad'ar da ita, suka shiga gidan kai tsaye d'aki suka nufa suka tarar da Aunty Murja tana share d'akin Amatullahi ta taimakawa Khadijatullahi ta kwanta a kan gadon, Amatullahi tayi

Please Login or Register in order to submit comment