Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Wanda ya dafatan Jabir ne da sauri ta ture hannunsa tare da juyar da fuskarta jefe ta cigaba da yin kukanta, Jabir kuwa duk da cewar baya son Teemarh Amman sai da ya ji hankalinsa ya tashi Dan ya San dalilin kukan na ta ba zai huce na rashin dawowarsa da wuri ba.

Zama yayi kusa da ita tare da kok'arin jiyo da fuskarta, Amman tak'i yarda sai tureshi ta ke yi da ya gaji ya mik'e tsaye tare da d'aukarta cak sannan ya koma ya zauna a kan kujerar Yana rumgume da ita a jikinsa, Teemarh tai-tayi ta kwace Amman ta kasa tana kuka ta fara magana "Tunda ka nuna min ba ka k'aunata kuma ka tsaneni kawai ka rabu da ni ka sakeni na koma gidanmu" Tayi maganar tana cigaba da tureshi, Jabir ya k'ara k'ank'ameta sosai a jikinsa yana cewa "Haba Darling wane dak'ik'in ne ya fad'a miki na tsaneki kuma ba na sonki da har ki ke cewa na sakeki ai darling ni da ke mutukaraba babu mai rabamu dan ko mutuwa ma tare da za mutu da ke please ki tsaya ki saurareni kin ji","Me zan saurara daga bakinka na san club ka je gurin yammatanka ka fad'a min me na rageka dashi ko kuma me suka fini dashi, kyau ko kuma surar jikin ko Kuma......" Bakinta ya toshe mata "Ba su fiki da komai ba darling kuma wallahi ba Wai na je club Dan"........"Dakata Jabir ba na son jin komai daga bakinka".

Da k'arfi ta fisge jikinta daga na shi ta fad'a kan gado tare da rushewa da wani irin kuka Mai cin rai, Jabir ya tashi ya koma kan gado Yana cewa "Darling ki daina kukan nan haka Dan Allah kinji babyn Jabir"

Cikin zafin nama Teemarh ta mik'e daga kwancen da take tana cewa.
"Karka k'ara cemin wani babyn Jabir dan ni ba babynka ba ce, babu ni babu kai ka ji na fad'a maka ka fita idona" Tayi maganar cikin kunar zuci, murmushi Jabir yayi ya ce "Ok am so sorry dear na dena, amman dan Allah ki daure ki saurareni ko da sau d'aya ne kinji baby boo" Teemarh tayi masa wani irin kallo "Ba ni da lokacin da zan saurareka, ka matsa daga kusa da ni dan manzon Allah","Hmmm!" Abin da Jabir ya iya cewa kenan sannan ya koma kan kujera ya zabga tagumi yana kallonta ta cigaba da kukan, wani irin haushin kansa ya fara ji saboda ya san Teemarh tana son shi sosai bai kamata yana yi mata abin da zuciyarta zata k'untata ba, kwantawa yayi a kan kujera a hankali bacci mai nauyi yayi awon gaba da shi, ita kuwa Teemarh sai da tayi kukanta mai isarta bacci 'barawo ya sace ta.


~*BAYAN WATA BIYU✨*~

A yau aka d'aura auren Alhaji Mukhtar da Hajiya Asiya bayan rigingimun da suka faru a tsakaninsu, dan da aka sallameta daga asibitin gidanta ya kai ta inda matarsa ta nuna ba za ta iya zama da ita ba tunda ba matarsa ba ce ta ya ya zai d'auko macen da ba muharramarsa ya kawo ta gidansa, nan suka huce suka bar ta tana ta 'ba'batu ya kai ta d'akinsa, kullum ya zamana ya na gurin Hajiya Asiya a cikin d'akin domin so ya ke ya shawo kanta ya gama da ita amman sam ta k'i yarda ta ce masa ita ba za ta yarda tayi zina ba sai dai ya aureta haka ya amince ba dan yaso ba, wannan shine dalilin da yasa a ka daura auren Hajiya Asiya.

*Ya ku ke ganin wannan drama fans Alhaji Mukhtar ya auri Asiya domin ya cika burinsa a kan ta akwai cakwakiyoyi sosai🤣✨*

Haka Alhaji Mukhtar ya dawo gida jikinsa na rawa dan yau burinsa zai cika, dole Asiya ta amince dashi yanzu ko ta k'i ko ta so, kai tsaye d'akinsa ya nufa inda ya tarar da Hajiya Asiya tana kwance a kan makeken gadon d'akin, hannunta rik'e da waya tana daddannawa, da kallo ta bi Alhaji Mukhtar har ya k'araso kusa da ita ya washe baki tare da cewa "Hajiyata an d'aura fa" Hajiya Asiya ta ya tsine fuska "To yayi" Tayi maganar tare da cigaba da danna wayar "To yanzu dai ai zancen 'boye-'boye babu shi, tunda kin zama mallakina" Ya k'arasa maganar tare da fad'awa kan gadon, a gigice Hajiya Asiya ta mik'e tana kallonsa tare da dafe k'irji tana cewa "Me zan gani, me ka ke shirin yi min, to karka so ma ka ji na fad'a maka ban shirya ba" Wani irin kallon kin raina min hankali Alhaji Mukhtar ya ke bin Asiya dashi "Lallai ma Asiya ba ki san ma wanene Mukhtar Sa'id Baba ba, ki je ki tambayi Sadiya za ta fad'a miki wanene ni, indai ina son abu to dole fa sai na same shi ko ta wane irin hali ne, wallahi Asiya tunda aka d'aura mana aure to a yanzun nan sai na samu abin da na ke so gwanda ki shafawa kan ki ruwan sanyi, ki amince tun kafin ki ga ba dai-dai ba" Wata iriyar mahaukaciyar dariya Hajiya Asiya tayi tare da cewa "Ka na tunanin zai amince ka kusance ni ne, to idan mafarki ka ke gwanda ka farka don kuwa ni Asiya wallahi na fi k'arfinka, ba zan iya amincewa d'an mafiya ya kusance ni ba, ko kuma nace matsafi" Ai tana k'arasa maganar ta ji ya d'auketa da wasu zafafan mari tun ina argawa har sai da na gaji na daina na ce Allah ya k'ara wallahi🤣.

Har sai da ta fad'a kan gadon sannan ya cire kayan jikinsa ya kama doguwar rigar jikinta ya yaga ta "Yanzu za ki fahimci wanene ni ke har kin isa ki ce min matsafi to wallahi sai kinyi danasanin haihuwarki da uwarki tayi yau d'in nan" Tun Hajiya Asiya tana iya tureshi har ta fara gazawa haka tana ji tana gani Alhaji Mukhtar ya samu abin da ya ke so, ya tashi ya shiga toilet yayi wanka ya dawo ya shirya cikin tsadaddiyar shadda ya fita daga gidan.

Hajiya Asiya kuwa tashi tayi ta shiga wanka zuciyarta babu alamar nadama wanka ita ma tayi sannan ta dawo ta shirya cikin atamfa blue colour doguwar riga ce, kwanciya tayi a kan gadon tare da lumshe idonta, har bacci ya fara d'aukarta ta ji saukar duka a jikinta, ta yunk'ura da niyyar tashi amman ta kasa sakamakon d'aure hannuwanta da k'afafuwanta da aka yi da sauri ta d'aga kai Alhaji Mukhtar ta gani a kan ta rik'e da wata dorina mai kauri, ta bud'e baki za ta yi magana ta ji saukar wata bulalar haka yayi ta jimgarta tun tana ihu har sai da ya zama ta kasa yin ihun sai dai hawaye da ya ke bin fuskarta, sai da ya gaji dan kansa sannan ya durgar da bulalar ya fita a fusace, kuka Hajiya Asiya ta ke yi mai tsima zuciya gaba d'aya jikinta rad'ad'i ya ke yi mata, fatar jikinta duk ta yi ja, tayi rud'u-rud'u.

*'BANGAREN HAFSA✨*

Yau sauran wata d'aya a d'aura auren Hafsa da Safwan wata iriyar soyayya suke nunawa junansu kamar su cinye juna kullum suna tare, yana zaune kusa da Safna ya d'auki wayarsa ya kira Hafsa ringing d'aya biyu Hafsa ta d'aga wayar tare da yin sallama "Assalamu alaikum Sweetheart" Murmushi Safwan yayi ya ce "Wa'alaikumussalam Ga ruhina za ku gaisa da ita" Yayi maganar tare da sakawa Safna wayar a kunne, Safna idanuwanta suka cicciko da k'alla tana kallonsa a hankali hawaye suka fara gangarowa, Safwan ya d'aure fuska tare da kawar da fuskarsa da kallonta ya fara kok'arin tashi ya bar ta, ganin haka yasa Safna dai-daita kanta "Assalamu alaikum Amarya" Hafsa tayi murmushi dan da taji shuru ta d'auka Safna ba za ta yi mata magana ba "Wa'alaikumussalam Aunty Safna ina yini" Safna ta ce "Lafiya alhamdullahi Ya shirye-shiryen biki","Alhamdullahi Aunty Safna" Safna ta ce "To Allah ya kaimu lokacin sai anjima" Bata jira mai Hafsa za ta ce ba ta ajiye wayar ta nufi d'akinta da gudu tana kuka.

Safwan ya d'auki wayar su kayi sallama da Hafsa, ya bi bayan Safna yana shiga d'akin ya ganta kwance a kan gado tana kuka, ji ta ke zuciyarta kamar za ta fashe (Ni kam nace Safna kin yi namijin kok'ari wallahi ba za iya ba🤣) d'aukarta yayi gaba d'aya ya zauna a kan gado sannan ya dora a jikinsa yana rarrashinta dan kuwa yau Safna ta burgesa sosai ya san saboda kar yayi fushi da ita tayi haka "Ruhina ki yi shuru dan Allah ba na son ki na yin wannan kukan kin ji sarauniyata" Murmushi tayi mai ciwo ta ce "Ruhina dole nayi kuka, dan Allah ka bar ni idan nayi kukan zan ji dad'i a zuciyata, ina jin zuciyata kamar za ta fashe" Ta k'arasa maganar tana kuka, tausayinta ya kamasa "Babyna nasan kina tsananin kishina, amman za ki iya yi min wani alk'awari?" Safna ta d'ago idanuwanta tana kallonsa tare da cewa "Eh zan yi maka" Wayarsa ce ta hau ruri yayi sauri zarota daga aljihu tare da d'agawa yayi sallama ban ji mai wancan d'in ya ce ba sai ji nai ya ce "To insha Allahu ranka ya dad'e gani nan zuwa" Ya fad'a tare da kashe wayar kallon Safna yayi "Ruhin ki yi min afwa mai gidana yana kirana akwai lissafin da za mu yi dashi mun fara to ba mu k'arasa ba kuma uzuri ya kama shi, idan na dawo zamu kin ji Sarauniyata dan Allah ki yi min alk'awari ba za ki daina wannan kukan, zuciyata tana raya min cewar ni mara adalci ne indai na ganki ki na kuka" Yayi maganar cikin yanayin damuwa, murmushi tayi ta ce "Allah sarki ruhina kai ba mara adalci ba ne, kuma zan dai na kuka ka ji ka tafi kawai karka damu","Kinyi min alk'awarin za ki dai na kuka?" Kai ta d'aga masa alamar eh, haka ya tashi ya shirya Safna ta rakashi har gaban mota ya shiga, Safwan ya kafeta da ido yana kallonta ta ce "Allah ya dawo min da kai lafiya","Amin" Har ta juya ta fara tafiya Safwan ya kirawota "Ruhina" Da sauri ta juyo tana kallonsa tana murmushi "Na'am" Shima murmushin yayi mata sannan ya ce "Ina sonki sosai" Yana gama fad'ar haka ya rufe murfin motar ya ja mai gadi ya bud'e masa gate d'in gidan ya fita ya nufi hanyar ma'aikatarsu, Safna kuwa murmushi tai-tayi har ta koma cikin falon ta kwanta tare da kunna kallo.

Sai wajen k'arfe 9:00pm na dare Safwan ya dawo da sauri Safna ta tashi daga kwanciyar da tayi tunda ya tafi tana yi masa sannu da zuwa murmushi yayi tayi zuciyarsa fas, rumgumeta yayi tare da cewa "Da fatan kin cika min alk'awarina ko?" Safna ta ce "Eh na cika ban yi kuka ba" Safwan ya ce "Yawwa er aljanna" Zama su ka yi a kan kujerar da ta tashi sannan ya ce "To yanzu za mu yi maganar alk'awarin da na ke so ki yi min" Safna ba ta ce komai ba sai dai gaba d'aya ta tattara hankalinta a kan sa da jin wane alk'awari kuma ya ke son tayi masa "Ina son ki yi min alk'awarin ba za ki sake yin kuka a kan auren nan da zan yi ba, dan idan na ganki ki na yin kuka ba na jin dad'i a cikin zuciyata dan Allah ruhina ki daure ki yi min alk'awarin nan ko na ji dad'i dan Allah ki daina yawan kukan nan kin ji dan Allah" Safna dai shuru tayi hawaye suna shirin zubowa, amman sai ta daure ta mayar dasu tana kallonsa "Yaya Safwan duk alk'awarin da ake cewa nayi maka, ina yi indai na ji bai fi k'arfina ba amman wannan ba zan iya ba dan ni kai na wani lokacin ban san lokacin da kukan ya ke zuwar min ba sai dai kawai na ji ina yi" Tayi maganar cikin muryar kuka, rumgumeta yayi sosai yana bubbuga bayanta tare da yi kalamai masu dad'i, daga nan suka tashi suka shiga d'aki.

*'BANGAREN INNA LARAI🤦🏽‍♀️😩*

Kullum Zaituna sai ta kawo mata abinci da daddare bayan kowa ya kwanta kuma babu wanda ya tab'a kamata, Zaune take a tsakar gida wajen k'arfe 5:00pm na yamma tana daka yaji sai ga Lado ya shigo ko sallama bai yi ba, Kallo d'aya Zaituna tayi masa ta kawar da kanta dan tunda ta ga irin wulak'anci da ya ke yi wa mahaifiyarsa ta ji ta tsaneshi kwata-kwata, shi kuma Lado yana ganin Zaituna ya saki murmushi tare da k'arasowa gurin da take, wata 'yar k'aramar kujerar k'arfe ya ja ya zauna tare da kiran sunanta "Zaituna" Bata amsa masa ba sai ma cigaba da aikinta da tayi, shi kuma bai damu ba ya cigaba da yin magana "Shine jiya na aiko a kira ki, ki ka k'i zuwa ko?","A'a ni babu wanda ya zo ya kira ni" Tayi maganar ba tare da ta kalleshi ba "kina nufi Idi bai zo ya kira ki ba?","Idi ya zo amman kuma ni bai ce min kirana ake yi ba" Nan Lado ya shiga zabgawa Idi kira "Idi kai idi kana ina?" Da sauri Idi ya fito daga d'akinsu tare da zuwa ya tsugunna kusa da Lado "Ga ni Yaya" Lado ya d'aure fuska tare da cewa "Jiya da nace ka je ka kira min Zaituna ashe da ka je ba ka kirata ba, ka zo ka ce min ka kirata ta ce tana zuwa" Idi ya zaro ido ya ce "Wallahi Yaya na kirata ai gata nan ka tambayeta na san Aunty Zaituna ba ta k'arya za ta fad'a maka gaskiya" Zaituna ta ce "Eh ya kirana ni kawai bai yi niyyar zuwa ba ne" Lado ya kalleta sororo kamar wanda aka dasa shi dai a saninsa Zaituna ba ta da rashin kunya amman yau gashi ta kalli cikin kwayar idonsa tana gaya masa magana mara dad'i ji yayi kamarya d'auketa da mari amman kuma da ya tuna cewar yana sonta sosai kuma hakan zai iya jawowa a k'i bashi aurenta ya sa ya fasa, ya fara magana cikin tsawa.
"Ke Zaituna yaushe ki ka koyi raina na gaba da ke, wato wuyanki ya yi kaurin da har zan aika ki zo ina son ganinki ki k'i zuwa amman"........ "Ka ga Lado dan Allah dan annabi ka bar ni na sha iska, meye ruwanka da ni ko akwai abin da na tsare maka ne da har za ka ke fad'a min maganar da ka ga dama, ni ba zan tab'a yiwa wanda bai san darajar mahaifiyarsa biyayya ba, saboda haka zaka iya b'ace min da gani" Zaituna ta yi maganar cikin tsiwa tare da hurga masa harara, Lado ya tsaya sororo yana kallonta cike da mamaki, tunda suke da ita ba ta tab'a kallon cikin idonsa ta gaya masa maganar mara dad'i ba sai yau, kuma ba ta tab'a kiran sunansa ba sai dai ta ce masa Yaya amman yau gashi tana kiransa da asalin sunansa, "Zaituna ni ki ke gayawa wad'annan maganganun, kuma ki ke kirana da Lado" Ya yi maganar tare da tsare ta da ido zuciyarsa tana bugawa da k'arfi, wani irin kallon ta yi masa tare da cewa "Yo to menene sunanka idan ba Lado ba, kuma kai wanene da ba zan gaya maka gaskiya ba, ka je kayi wa mahaifiyarka biyayya ka bata hak'uri tun kafin dare ya yi maka" Tana gama fad'ar haka ta shige d'akinta da sauri tare da rufe kofa, shi kuwa Lado jikinsa a sanyaye ya mik'e ya nufa d'akinshi, zuciyarsa cike da bak'in ciki yana shiga d'akin ya zauna tare da zabga tagumi yana tunanin maganganun da Zaituna ta fad'a masa, ya d'auki kusan mintina talatin yana tunanin daga k'arshe ya kwanta a kan gadonsa tare da lumshe idanuwansa.

*'BANGAREN JABIR DA TEEMARH☹️*

Yau kusan kwana bakwai Jabir bai fito ko da falo ba, kullum yana d'aki yana kok'arin shawo kan Teemarh amman abin ya gagareshi, Teemarh ba ta da aiki sai dai ta zauna tai-ta yin kuka, fuskarta gaba d'aya ta kumbura tayi jajahur idanuwanta kuwa da kyar take iya bud'e su, saboda irin kukan da ta ke yi yasa su ka yi ciki-ciki, "Haba Daring ya kamata ki tsaya ki saurareni, wallahi akwai dalilin da yasa na je club ranar plss My Teemarh ki saurareni ba na son kina yin wannan koke-koken" Jabir wanda ya ke kusa da Teemarh a kan gado ya yi maganar fuskarsa tana nuna alamun damuwa, "Jabir na san baka so na dan Allah ka kyaleni" Teemarh wacce take kwance a kan gadon tana faman rera kuka tayi maganar cikin muryar kuka, "Wai wa ya ce miki ba na sonki, wallahi Teemarh ina sonki sosai dan Allah ki daina kukan nan, ki fad'a min abin da ki ke son nayi miki da zai saka ki yarda ina sonki" Teemarh ta d'ago fuskarta tare da zuba masa idanuwanta "Ka tabbatar duk abin da na fad'a maka za kai min" Jabir ya gyad'a kai tare da cewa "Indai hakan zai saka ki farin ciki, zan yi miki ko ma menene".

"Darling ina son ka daina zuwa club, duk abin da ka ke so ni zan yi maka shi koma menene,amman dan Allah ka daina zuwa club ba dan ni ba, dan Allah na rok'eka da girman Allah" Jabir ya yi shuru kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "Na amince darling indai hakan zai sa ki yarda cewar ina sonki" Teemarh ta yi murmushi "Da gaske ka ke Darling" Jabir ya yi murmushi "Eh mana, da gaske na ke, babyn Jabir" Ajiyar zuciya Teemarh ta sauke tare da cewa "To darling na yarda kuma na san ba za ka k'arya min alk'awarina ba, yawwah Darling dan Allah ina son na je gidan Hajiya Mama yau na dad'e ban je ba" Jabir ya jawo Teemarh jikinsa yana shafata "To darling da yaushe za ki je","Ni ko yanzu ma" Jabir ya ce "Nop ba yanzu ba dai sai anjima" Teemarh ta ce "Allah ya kaimu" Jabir ya ce "Amin ya Allah" Nan ya shiga shafe jikin daga nan suka tsunduma duniyar soyayya.

_Habibaties ku yi min addu'a ba ni da lafiya cikina ke ciwo😭👏🏽_

*'BANGAREN AMATULLAHI🤣💃🏽*

Amatullahi ta je gurin club d'in su Jabir amman abin mamakin har ta gaji da tsayuwa amman ba ta ga jibtawar Jabir ba, anan take tambayar wani mai shago Jabir ya daina zuwa ne?, da yake kaf unguwar babu wanda bai san shi ba, saboda irin shaharar da ya yi wajen lalata yaran mutane, ya ba ta amsa da cewa yau kusan sati guda Jabir bai zo club d'in nan ba, kuma gaskiya na ji labarin cewar matarsa ce take son ta hana shi zuwa, Amatullahi tayi masa godiya ta nufi gidan Hajiya Mama zuciyarta cike da mamakin wace 'yar kasada ce ta auri Jabir, kuma da wad'anne irin kalmai ta ja ra'ayin d'an iskan nan ya daina zuwa club, k'wafa ta yi tare da cewa "Koma wacece ita ta ga za ta iya" A haka ta k'arasa gidan Hajiya Mama, Falon saukar bak'i ta shiga tare da zama ta kunna t.v tashar arewa 24 ta kai anan ta tarar ana yin wani film d'in hausa, film d'in ya yi matuk'ar jan ra'ayinta sosai, gaba d'aya ta maida hankalinta wajen kallon film d'in.

"Besty! Besty!! Besty!!!" Ta ji muryar Khadijatullahi tana kiranta, mik'ewa ta yi da sauri ta fita daga falon "Na'am Bestyna" Amatullahi ta yi maganar tana k'arasawa kusa da ita "Ina ki ka je? Tun d'azu ina ta faman nemanki" Murmushi Amatullahi ta yi "Yau Babana ya dawo ne, shine na je gurinshi" Khadijatullahi ta kafeta da ido, tabbas ta san Amatullahi ba gaskiya ta ke fad'a mata ba, dan tun suna k'anana indai Amatullahi ta yi magana tana iya gane cewar k'arya take fad'a ko kuma gaskiya "Yau kuma k'arya za ki yi min bestyna, ban yi tunanin za ki iya k'in fad'a min halin da ki ke ciki ba, na san ba gaskiya ki ke fad'a ba Baba bai dawo ba, dan in ya dawo zaki ce min na zo muje mu gaishe dashi" Da sauri Amatullahi ta kalli Khadijatullahi daman ta san zata iya gane cewar k'arya ta ke yi mata "Besty dan Allah ki fahimceni" Khadijatullahi ta ce "Ba na son ki ce min komai domin ba na gana da mak'aryaciya" Khadijatullahi tana gama fad'ar haka ta shige babban falon ta zauna a kan kujera tana kallon Aliyu tana sakar masa murmushi "Yaya Aliyu na bar ka kana ta jira na ko, dan Allah ka yi hak'uri" Aliyu ya bud'e baki zai yi magana Amatullahi ta shigo falon tare da zuwa gurin da Khadijatullahi ta ke zaune ta tsugunna "Haba besty kin san ban tab'a yi miki k'arya ba, wallahi bestyna gurin"....... Khadijatullahi ta dakatar da ita da hannu fuskarta a murtuk'e "Dan Allah ki tafi kawai ba na son ganinki".

Hawaye ne suka shiga zubowa Amatullahi, ta mik'e tana goge hawayen na ta da gefen hijabinta "Ke Amatullahi dawo ki zauna" Aliyu ya yi maganar lokacin da Amatullahi take shirin fita daga falon, juyowa ta yi ta koma ta zauna dan ita sam ba ta ma kula da Aliyu yana falon ba, "Meya had'aku?" Ya yi maganar yana kallon Khadijatullahi wacce ita ma shi take kallo "Hmmm!" Abin da Khadijatullahi ta ce kenan "Yaya Aliyu ni ban tab'a yi mata k'arya ba, wallahi da gaske na ke yi maka" Amatullahi ta yi maganar tana kuka "Ai yau kuma kin yi min, kuma ni ba na mu'amala da mak'aryaci" Khadijatullhi ta yi maganar tana hararar Amatullahi, Aliyi ya ce "To ya isa haka, Amatullahi me ki ka yi mata?" Amatullahi ta ce "Ni Yaya Aliyu gurin Jabir na je" Wata iriyar zabura Khadijatullahi ta yi "Me ki ka je yi gurin wannan shegen d'an iskan" Nan Amatullahi ta bata labarin duk abin da take shirin yi wa Jabir d'in domin d'aukar mata fansa ta dora da cewa "Kuma duk zuwan da na ke yi sau d'aya na samu na fara isar masa da sakona, yau kuma da na je shine me shagon ya ke ce min ya daina zuwa club d'in saboda matarsa" Khadijatullahi ta matso kusa da Amatullahi ta rumgumeta tana kuka "Besty meyasa baki fad'a min ba, ki ka yi min shuru kin san wannan d'an iskan, kuma kin san halinsa, bai kamata kina saka kanki a tsari saboda ni ba, dan Allah ki daina saboda idan wani abu ya sameki ba zan tab'a iya yafewa kaina ba" Amatullahi ta d'agota tana goge mata hawayen fuskarta "Ki daina kuka ya isa haka, ka da kanki ya yi ciwo" Murmushi Khadijatullahi ta yi "To na dena dan Allah ki yi hak'uri da"..... Rufe mata baki Amatullahi ta yi "Dan Allah ki manta da komai ai ya wuce, bari na baku wajen ko kuna hirarku na katse ku, Yaya Aliyu a sha soyayya lafiya" Ta yi maganar tana dariya tare da fita daga falon.

_Masu son daren aurena daga farko zuwa inda aka tsaya ya yi min magana ta wannan number 08122188717_

"My Heartbeat wallahi kun burgeni sosai, tunda na ke ban tab'a ganin k'awaye irin ku ba, kuna son junanku kuna tsananin k'aunar junanku, Allah ubangiji ya bar ku tare" Aliyu ya yi maganar yana murmushi "Amin Yayana" Khadijatullahi ta yi maganar ita ma tana sakar masa murmushi, nan suka shiga yin hirarsu irin ta masoya sun kai kusan rabin awa suna hira daga nan su ka yi sallama, Aliyu ya tafi gidan abokinsa musaddik.

⏰5pm

K'arfe biyar na yamma dai-dai Teemarh ta isa gidan Hajiya Mama "Assalamu alaikum" Ta yi sallama tare da shiga cikin gidan, su ka yi ido biyu da Shahida "Laaa Aunty Fatima ke ce" Murmushi Teemarh ta yi tare da k'arasawa gurin da Hajiya Mama ta ke zaune ta tsugunna har k'asa tana gaisheta "Ina wuni Hajiya","Lafiya lau ina d'an duniyar mijin na ki?" Teemarh ta sunkuyar da kai tare da cewa " Yana gida" Tashi ta yi ta koma kusa da Shahida tana cewa "Hmm! Ai babu abin da za ki ce min" Dariya Shahida ta yi ta ce "Ki yi hak'uri Aunty Fatima akasi aka samu, kuma kin san gidan Hajiya Mama idan ka

Please Login or Register in order to submit comment