Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin, "To Momy zan taho, kuma ba zan faɗiwa kowa ba In Sha Allah!" Daga haka ta sake yin shiru kafin ta sake furta, "To Momy zan yi duk yadda ki ka ce." Daga haka ta sauke wayar a kunni wasu sabbin hawaye na shatata daga idanunta.Hukuncin da Momy ta yanke akan tabi flight ta koma KD ya yi mata tsauri, amma ta san Momy ba zata faɗi abinda zai zamo aibu ba sai abinda zai sama mata fita daga wulaƙancin AD Dukku.Wanda ya gama fahimtar ta gama matowa a kansa, shiyasa yake taka ta da wulaƙantata son ransa.Ta ɗauki waya da sauri don sayen ticket ɗin jirgin da zata bi a yau zuwa KD ɗin idan zata samu.Cikin sa a ta sayi ticket ɗin jirgin da zai tashi a yau ɗin da misalin 3pm na yamma. Ta aje wayar lokacin da ta kammala da komi tana ji zuciyarta na mata nauyi matuƙa, sai ta tashi ta nufi bathroom tayo wanka ta fito.Cikin wasu riga da wando masu faɗi marasa nauyi ta shirya kanta, ta ɗaure gashinta da band tana fitowa zuwa downstairs domin cin abinci.Ita ma tea ɗin da ragowar bread ɗin da ya rage ta ci, tana mamakin yadda yau ta karya da wuri cikin jin matsananciyar yunwa.Sai dai tunawa da tayi ba ita kaɗai bace a yanzu sai mamakin hakan ya ragu a zuciyarta, ta kammala da cin abincin tana mai komawa zuwa upstairs ta nufi ɗakin baccinsa.Da kayan da ya cire ya barsu zube a tsakar ɗakin ta fara cin karo, sai ta nufi tsakiyar ɗakin hancinta na cika da ƙamshinsa da ya kama ko'ina da komi nasa.Kayan ta kwashe takai inda suka kamata,kafin ta fara gyaran ɗakin tana yi hawaye na zuba mata na tsananin kewar ganinsa da zata yi.Ta zauna daga kan sofa tana sharan hawayen da suka kasa tsaya mata,zuciyarta na cigaba da tunanin miye ne aibunta da AD Dukku ya kasa ƙaunarta? Me ta rasa da har yau ta kasa samun zuciyarsa bare kulawa da nuna mata tarairaya irin wanda ta sha mafarkin samu daga mijin aurenta? A hankali wani ƙaramin kuka ya ƙwace mata mara sauti sosai.Tayi mai isarta kafin ta rarrashi kanta, tana bai wa kanta ƙwarin guiwar tafiya ta barsa kamar yadda uwarsa ta ce.Hakan kaɗai ne mafita a gareta matuƙar tana son cikin jikinta da ita kanta su tsira daga fuskantar fushi da wulaƙancinsa.Bata baro ɗakin nasa ba sai da ta gyare ko'ina cikin dakiya da ƙarfin hali,domin ba za ta iya fita ta bar ɗakin a haka ba alhali tayi sabo ita ce mai gyara masa ko'ina ɗin.Diana ɗakunanta kawai take gyarawa, amma bata gyaran ɗakinsa wannan aikinta ne da take ganin ita kaɗai ta cancanta ta yisa.Kaya ta haɗa cikin madaidaicin akwati, wanda ya ɗaukar mata kaya masu ɗan yawa da duk wani abun buƙata.Kamar ta ɗaga waya ta kira Yayarta Anty Laurah ta sanar da ita komi, sai gargaɗin Momy na cewa karta sanar da Hajiyarta ko Anty Laurah ɗin ya faɗo ranta.Ta aje wayar tana ji damuwar duniya na rufar mata.Kanta ya fara ciwo babu ƙaƙƙautawa, hakan ya sanya ta tuna bata sha magungunanta ba.Sai ta ɗakkosu ta sha tana mai zuba su cikin tsadaddiyar hand bag ɗinta na BVLGARI,wanda ta shirya duk wasu ƙananun abubuwan da xata buƙata a ciki.Hatta da maganin da ya saya daban a pharmacy ɗin da suka tsaya, sai da ta saka su cikin bag ɗin, ta zuge jakar tana tunanin yadda zata isa gaban Momy ta nanata mata zancen zubda cikin da AD ɗin ke so ayi. Wayarta ta janyo ta tura masa saƙon cewa zata bi jirgin 3pm zuwa KD bisa umurnin Momy. Daga ƙarshen saƙon tayi amfani da kalamai na soyayya da ban haƙuri, tana sake jaddada masa irin soyayyarsa dana abinda take ɗauke dashi da ke bin jininta.Don haka ba za ta iya zaɓan ɗaya ta bar ɗaya ba, dukkaninsu take so ta kuma zaɓa. Lokacin da saƙon ya nuna ya tafi, komawa tayi ta zame kwance bisa sofa tana hawaye sosai.Idanunta a lumshe suke amma hawaye ne ke biyo fuskarta a guje, sabida tsananin zafi da wani irin karyewa da zuciyarta ke yi akan zazzafar ƙaunar da take masa.Ta miƙa hannu ta shafo lafaffan cikinta, tana jin wani irin feeling mai zafi na tsananin ƙaunar cikin da ke manne a haifarta na ratsata.Sosai ta hana kanta sukuni da kutsawa duniyar tunanuka kala daban-daban, har zuwa sanda ta ji ƙarar shigowar saƙo cikin wayarta.Hannunta har rawa yake lokacin da ta ga sunansa ne akan saƙon, alamun reply ya yo mata na text ɗin da ta tura masa ɗin. Koda ta buɗe saƙon wani irin zafi taji zuciyarta nayi,sakamakon baƙaƙen maganganun da ya gasa mata na cewa tafi ruwa gudu.Sannan ya sake jaddada mata cewa matuƙar tana son cigaba da zaman aurensa,to tabbas ta rabu da cikin jikinta don bai shirya haihuwa a yanzu ba. Jifa tayi da wayar lokacin da ta kammala karanta ɗatatan kalamansa, masu nuni da cewa ko kaɗan bata gabansa,bai kuma damu da maganar tafiyar da zata yi ɗinba kamar yadda Momyn nasa ta buƙata.Ta jima a kwance tana kuka har sai da wata uwar yunwar ta sakaɗota, sannan ta tashi tana sake janyo waya ta kira Diana.Tana ɗaga kiran ta furta, "Ki dafo min noodles, amma ya yi yaji sosai,ya kuma ya yi ruwa-ruwa." Ta kashe wayar tana ji duk ta ƙosa ta ga noodles ɗin a gabanta, ya kuma yi irin yadda take so ɗin. Koda Diana ta kawo mata shi har ɗakin baccinta, jikinta har rawa yake ta amsa plate ɗin tana sauke idanunta akan dahuwar noodle ɗin da ya yi mugun kyau, sai tashin ƙamshin pepe da mixed spices yake yi.Ta tsaida Diana tana sanar da ita zancen tafiyarta arewa a yau ɗin, tana mai bata umurnin haɗa kayanta don dole ita ma ta bar gidan a yau tunda anan cikin Port Harcourt ɗin take aka samo mata ita.Ko kaɗan Diana bata so wannan tafiya ta gaggawa da ta tasowa Madam Hannah ɗin kamar yadda suke kiranta da sunan ba, don tana jin daɗin aiki a ƙarƙashinta sabida bata da faɗa da hayaniya.Sannan tana kyautata musu sosai ita da duka ma'aikatan gidan, shiyasa suma suke bata girma da ƙaunarta sosai. Tana gama cin noodles ɗin wani bacci mai daɗi ya fara fisgarta, sai tayi kwanciyarta bisa sofa ɗin ba tare da ta hau bed ba.Bata tashi farkawa ba sai wajen 1:30pm, hakan yasa a gaggauce ta nufi toilet ta ɗauro alwala ta zo ta gabatar da sallah.Tana idarwa wanka ta sake yowa ta shirya cikin wani simple gown na swiss lace mai shegiyar tsada, ko kaɗan kayan basu da nauyi gashi ɗinkin ya amshi jikinta sosai.Kana kallonta za ka gano irin fresh ɗin da tayi gunin sha'awa, ga wani irin glowing da fatarta ke yi na samun hutu da kuma yanayin weather ɗin kudu mai kyau da ya taɓa fatar.Babu komi akan face ɗinta sai asalin natural face ɗinta, idanunta kaɗai ta iya sanyawa kwalli sabida kukan da ta sha idanun sun koɗe matuƙa.Sassanyar ƙamshin turarenta na LADY MILLION by PACO RABANNE ke tashi, duk ya buɗe ko'ina na ɗakin da sassanyar ƙamshi.Ta kammala shirin komi tare da aje bag da gyalenta bisa sofa,ta shiga neman layin driver ɗin da ya aje don fita da ita idan zata saloon ko mall.Sai da ta kira kusan sau uku sannan Bola ya ɗauka, wanda yake bayareban lagos ne zama ya kawo shi port harcourt ɗin. Allah ya haɗa shi da Adnan Dukku har ya ɗaikesa aikin driving ɗin da a sati bai fi su fita sau 2 ko 3 ba.Sabida Hannah bata san kan garin ba, kamar yadda bata saba da kowa ba har yau da take da watanni biyu da wasu kwankin a garin.Sanar dashi tayi ya taho zasu wuce airport, tafiya ta kamata zuwa gida arewa kamar yadda suke faɗi idan sun ji mutum zai irin garuruwan su Kaduna da sauran garuruwan da ke arewacin nigeria.

Ƙarfe 2:30pm suka isa airport ɗin, ta gama duk abinda zata yi kafin ta jira lokacin da aka fara kiran passingers.Bola bai baro airport ɗin ba sai da ya tabbatar da tashin jirginsu,sannan ya juya don komawa gida ya aje motar. Tuni Diana dama ta riga Hannah barin gidan, bayan ta sallameta da kuɗi enough!Ta kuma bata tabbacin ba za ta jima ba zata dawo..........✍🏻



*Pay 500 in to this account number👇🏻*
*0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank*
*OR*
*PAY IN TO DIS ANOTHER ACCOUNT* 👇🏻
*8167768704 AISHA* *DANSABO IBRAHIM*
*ACCOUNT NAME:OPAY*
*Evidence of payment to this number:08167768704*


🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻*
*MTN*
*GLO*
*AIRTEL*
*9MOBILE*
*MONTHLY VADILITY 💃🏻*

*DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻



#Lovestory#
#Najma#
#Aysha Ɗansabo Lemu🥰
[3/12, 9:39 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!🤲🏻* *Arewabooks@ayshadansabo*

*Paid book:500*

*Chapter 16*

_Free page_


*Kaduna.*

Najma da Momy ne a kitchen suna hiransu tana taya Momyn aikin yankan su carrot da zata saka a filling ɗin samosa.Momyn ta kan amsa call akai-akai tana cigaba da yin sheet ɗin samosanta,gefe guda kuma zuciyarta sam babu daɗi da abinda surukarta ta sanar da ita tun safiyar yau ɗin.Ƙarfin hali kawai take yi tana dannewa, don bata so a fahimci halin da zuciyarta ke ciki akan irin baƙin cikin da Adnan ke cusa mata, tun kafin auren har aka yisa.Najma ta aje bowl ɗin da ta gama goge carrot ɗin a ciki tana duban Momy ta ce, "Momy na gama, sai kuma me zan kama miki?"
Momy ta dubi Najma tare da kallon yadda ta yi komi tsaf cikin nutsuwa, ta saki murmushi mai faɗi tana faɗin, "Najma kin iya aiki a nutse gunin sha'awwa,da Nasreen ce da yanzu kinga ko'ina ya ɓaci.Babu abinda zaki yi yanzu sai ki nutsu ki ga yadda ake haɗa feeling ɗin da naɗesa a sheet ɗin." Najma ta jinjina kai cike da murnar yabon da ta samu daga Momy ta ce, "To Momy, bari in nutsu ɗin kuwa don ina so inga na iya irin waɗannan abubuwan zamanin." Daga haka ta dinga bin yadda Momy ke komi cike da ƙwarewa har suka kammala.Najma ɗin ta koyawa yadda ake naɗe samosan,cikin sa a kuma ta iya yinsa tsaf! Ita Momy ta barwa suyan ta fice daga kitchen ɗin lokacin da agogo ke buga 2:30pm na rana.Najma na aikin suyan tana yaba kirkin Momy da yadda take janta a jiki, tana nuna mata ƙaunar da bata yi zato ba.Tun shigowarta da safe bayan tafiyar Nasreen school, Momyn ta hanata komawa ɓangaren Gwaggo,suka yini suna hira da yin ƴan wasu aikace-aikacen a kitchen.Don yau ɗin ta kula sosai Momy ke jin motsa jiki da yin ayyukan kitchen kala da kala, hakan kuma sai ya yiwa Najma daɗi don ita indai a fannin son koyan girki ne bata da damuwa. Nabeela ita ma tun rana ta fita zuwa saloon da wankin ƙafa ,daga can kuma ta ji tana sanarwa Momyn zata biya gidan wata friend ɗinta.

Tana kammala suyan samosan ta kashe gas ɗin tare da kintsa komi a mazaunin da ya dace,ta bar samosan a colander ya ɗige kafin a kwashe shi a mazubin da ya dace.Ta baro kitchen ɗin tana jin wani irin nishaɗi a zuciyarta,domin gani take yi ko yanzu aka kwaɓa mata dough ɗin samosan zata iya yinsa ya fita tsaf! In Sha Allah! A nan falo ta zauna don tun 1 suka yi sallah suka yi lunch tare da Momy a dining.Don haka bata jin yunwa ko gajiya tunda tayi sabo da aikin wahala a ƙauye,shiyasa take ganin ba komi tayi yau ɗin ba.Musamman da ya kasance a cikin lafiyayyen kitchen ɗin ƴan gayunnan suka yi aikin, suna yi sanyi AC na ratsa ko'ina a jikinsu. Wayar ta janyo daga lungun kujera inda ta aje sa, ta kunna data tana hawa online.Ganin Nasreen a online ya sanya tayi mata magana tana tambayarta ta kusa dawowa ko da sauran time? Nasreen tayo mata reply ta voice note tana sanar da ita sai 4 zata dawo kamar yadda ta faɗi da safe.Suka ɗan taɓa hiransu kafin Najma ta kashe datan tana kiran layin Inna Karima don tayi magana da mutanenta su Hanne.Bugu uku Hanne da wayar ke hannunta ta ɗaga, jin muryar Najma ce ya sanyata sakin ihun murna kafin su fara gaisawa Najma na tambayar ina Lubcy? Hanne ta bata amsa da cewa an aiketa ne,sai suka dasa hira tamkar ba credit ake janyewa ba.Sun jima sosai suna magana har Lubah ta dawo aiken da aka mata ta amsa wayar ita ma suka dasa hira.Daga ƙarshe Najma ta gaisa da Inna Karima sukai sallama da juna akan cewa nan da kwana biyu zasu iso giwa ɗin kamar yadda Daddy ya faɗi. Tana aje wayar fuskarta cike da murmushi,Momy ta fito daga ɗaki ta sauya shiga cikin wata boubou mai kyau na atamfar batik.Ta yafa babban gyale mai tsananin kyau da ya haska da kayan jikinta,fuskarta ɗauke da murmushi take duban Najma ta ce, "Naj! Tashi muje ɓangaren su Gwaggo ki ɗauki mayafi zaki rakani unguwa mu dawo, tunda gidan mu kaɗai ne karki zauna babu abokin hira gara mu riƙa zaga gari kina ganin ko'ina ko?" Najma ta gyaɗa kai ƙaunar Momy na sake zama a zuciyarta,ta miƙe tsaye tana faɗin, "To Momy, aiko dai zan zauna shiru babu Nabeelah babu Nasreen ta ce sai 4 zata dawo." Momy tayi murmushi tana duban Najma da kulawa ta ce, "Kema tare da Nabeela zaku shiga jami'a In Sha Allah! Don ita ma kin ga jamb kawai take jira a fara sayarwa ta zana, kinga sai a siya muku tare tunda kin ce takaddunki na waec da neco sunyi kyau ko?" Najma ta jinjina kai ta ce, "Hakane Momy sun yi kyau." Suka fito zuwa sashin Gwaggon kaduna suna hiransu cike da nishaɗi. Bayan Momy sun sake gaisawa da su Inna Mairo ne ta sanar da Gwaggo cewa Najma zata rakata unguwa su dawo.Gwaggo da Inna Mairo suka yi musu a dawo lafiya, Najma ta isa ɗaki ta sanyo veil mara girma sosai don bata da hijab sai na sallarta kawai.Lokacin da aka je yi musu siyayya taso ta ce tana son a ɗinka mata su, don su ta saba sawa a giwa bata iya sanya gyaleba,amma kunya ya hanata faɗin tana so ɗin.

Tayi kyau sosai da cream and silver colour ɗin veil da ta yano kanta dashi.Momy tayi mata duba ɗaya tana yaba tsantsar kyawun Najma da kyawun surarta, domin a yanzu kaɗai da suka samu kwanaki huɗu a garin har wani kyau ta ƙaro sabida hutu da kwana a cikin AC. Ga kuma lafiyayyan cima da suke ci suna wanka da sabulai masu tsada da kyawu,hakan ya sanya fatarta fara gogewa asalin black beauty colour ɗinta na wani irin haskawa. Sannu a hankali suka isa zuwa parking space na gidan,inda motoci uku suka rage a fake.Mommy ta aiki driver ɗinta can wani waje da motarta, hakan yasa dole a ɗaya daga cikin motocin Daddy biyu da suka rage zasu fita.Front seat ta buɗewa Najma ta shige, tana jinta a can sama cikin irin dalla-dallan manyan motocin da bata taɓa hasashen hawansu nan kurkusa ba.Motar ta birgeta matuƙa sai faman yaba kyawun ciki da wajen motar take yi a zuciyarta, amma a zahiri a kame take bata nuna ƙauyancinta afili sam! Momy dake mazaunin driver ta tashi motar suka dumfari bakin gate. Mai gadi ya buɗe musu gate yana yiwa Momy a dawo lafiya, suka fice tana ɗaga masa hannu fuskarta a sake kamar yadda ta saba. Sai da suka ɗauki hanya sosai Momy ta dubi Najma tana tana sanar da ita cewa airport suka nufa,domin ɗakko matar babban ɗanta da suke Port Harcourt.Ta cigaba da cewa, "Na aiki Lukman gashi kuma ta kira suna dab da sauka, dole yasa na fito don na ɗakkota da kaina Najma.Ban gayawa Gwaggo bane don zata yi surutu, ni kuna bana son ɓata lokaci don babu daɗi mutum ya sauka flight yana faman jiran azo a ɗauke sa.Don haka ko mun koma gida bana so ki sanar da ita ni ce na ɗakko Hannatun koda ta ganta,tunda muna isa direct wajena zamu wuce kinji ko?" Najma ta jinjina kai ta ce, "Bakomi Momy ba zan faɗi ba, ai ba a haka, daga ɗaukata rakiya kuma sai naje ina faɗin abinda ba a tambayeni ba.Ko tambayata aka yi ma cewa zan yi bansani ba gaskiya." Momy tayi dariyar yadda Najma tayi maganar bilhakki cikin sassanyar muryarta mai daɗin amo,ta tsaida dariyar tana faɗin, "Das my gal! Allah ya yi muku albarka Najma." Najma ta amsa da cewa, "Ameen." Daga haka Momy ta cigaba da shara gudu a lafa-lafan titunan kaduna, waɗanda suka samu gyara na musamman daga ƙwararran gwamnar jihar mai shegiyar fasaha da fikrah.

Sun isa airport ɗin dake mando daidai da saukar jirgin da ya ɗakko su Hannah daga jihar rivers.Lokacin da ta fito ta tadda Momy ce da kanta ta zo ɗaukarta sai jikinta ya sake yin sanyi, ƙaunar Momy da soyayyar da take wa aurensu da AD na sake kama zuciyarta.Cikin nutsuwa da sanyin jiki take ƙarisowa jaye da luggage da hand bag ɗinta, sai da ta kusa ƙarisowa Najma ta fice da sauri tana amsar luggage ɗin ta cigaba da jansa har wajen motar.Momy ta fito tana wa Hannah bar da isowa lafiya, tana mai duban tsakiyar idanun Hannah da ruwan hawaye ke taruwa a cikinsu.Murya cike da kulawa ta dubeta tana faɗin, "Hannah shige muje, bana son sanya damuwa a rai please! Kin dai san wace ce Gwaggo a wajen Adnan,don haka bana so ta gane rauninki a wannan karon don Allah!" Momy ta yiwa Hannah maganar cike da roƙo, don sam bata so Gwaggo ta samu kafar dagula lamuran, duk da cewa ta san komin ɗaurewa ƙarya gindi akan lamuran AD ɗin da ta saba,a wannan karon ba za ta yi hakan ba don ita ma ba za ta so a cire cikin shalelenta ba.Hannah ta gyaɗawa Momy kai, kafin tayi magana cikin sanyin murya ta ce, "In Sha Allah Momy!" Daga haka Najma ta gama sanya luggage ɗin a bayan boot,ta isa ga back seat ta shige don baƙuwar Momy a gaba ta kame.Momy ta ja motar suna cigaba da magana da Hannah, ita dai Najma na jinsu amma bata gane inda maganganunsu suka dosa ba.Koda ta gaida Hannah waiwayowa tayi ta amsata cike da fara'a, tana mai maida dubanta kan Momy ta ce,"Ina kuma kika samo wannan black beauty ɗin?" Momy ta saki murmushi tana bai wa Hannah amsa da faɗin, "Hannatu kenan, ƴar ƙanwar Daddy ne fa.A garin giwa suke da zama but yanzu sun dawo wajen mu zamu rayu tare In Sha Allah, so she's ur husband cousine Sis, ina fata zaki ɗauke ta tamkar su Nasreen?" Hannah da sam bata da wani damuwa, gyaɗa kai tayi tana faɗin, "In Sha Allah Momy! Amma gaskiy she's very black beauty and suna matuƙar kama da Anty Jiddah kuma."
.Momy ta saki murmushi tana faɗin, "Tafi Jiddah kyau ai Hannatu, ita wannan photocopy ɗin Innarta ce sak! Sai dai ita Innar fara ce ita kuma sai ta fito a black beauty." Najma dai blushing take tayi tana sauraran yadda su Momy ke ta faman yaba kyawunta da black skin ɗinta. Sun iso gida daidai da shigowar motar Nasreen ta dawo daga skull, suka faka motocin kusan a tare suna mai ɓalle murafen motocin suka fito.Nasreen ita ce ta fara isowa wajen motar da Momy ta faka don ta hango fuskar wata kamar Anty Hannah ɗinsu.Tana ko isowa ta ga ita ɗince ta saki ƙaramin ihun murna tana rungumeta ta ce, "Welcome Anty Hannah! Ke kaɗai kika taho ina Yaya AD?" Hannah ta sake rungume Nasreen cike da fara'a da danne dukkanin ƙuncin zuciya ta bata amsa da faɗin, "Ni kaɗaice Nasreeny, AD zai zo may be a weekend." Najma Nasreen ta duba dake tsaye tana dubansu da murmushi akan fuskarta, sai ta saki Hannah tana faɗin, "Alright! Allah ya kaimu weekend ɗin lafiya, gwarama da ba tare kuke ɗinba ai." Hannah ta saki murmushi tana mamakin yadda su Nasreen ɗin ke tsoransa da rashin damuwa da lamarinsa, sabida ya iya musu faɗansa da baya ƙarewa.Sosai suke shakkarsa basa sakewa idan yana waje sam,don abu kaɗan zai rufesu da masifa ko ya mammakesu. Nasreen tana duban Najma ta ce, "Najma kice ke ce ƴar rakiyar Momy yanzu, so ya garin kinyi missing ɗina yauma ko kuwa waya ki kai tasha da mutanen giwar taku?" Najma ta saki murmushi tana ɗan narke face ta ce, "Nayi amma kaɗan, waya kam mun sha shi in gaya miki.Suna gaida ku da kyau ke da Nabeelah da duk nake ta basu labarin kirkinku." Nasreen ta sanya dariya suna yin gaba don tuni Hannah da Momy sun yi gaba zuwa ciki.

A ɗaya bedroom ɗin Momy Hannah ta yada zango tana jinta a gajiye kamar wacce ta baro wata ƙasa zuwa KD ɗin.Wanka tayo da ruwa mai ɗumi, ta fito ɗaure da towel ta nufi bakin bed ta zauna tare da janyo luggage ɗinta.Doguwar rigar shan iska mara nauyi ta zaro ta saka, tana fesa turarenta mai daɗin ƙamshi da sanyi.Hijab ta nema ta saka ta tada sallah, tana idarwa ta fara jin dukkanin jikinta na ɗaukar rawar jin yunwa tamkar wata mai ulcer.Hakan ya sanya ta miƙewa da sauri ta nufi falo don neman abinci, tun kafin a kai ga gabatar mata dashi.Babu kowa a falon don Momy ta shiga yin sallar la'asar da ya riskesu a hanya,ita ma Najma sun ƙule a ɗakin Nasreen.Don haka kai tsaye ɓangaren dining da ba baƙonta bane ta nufa, don kuwa tun bata auri AD ba suna zuwa gidan su yini. Lafiyayyiyar fried rice da salad ta zuba ta fara ci, tana ci tana korawa da orange juice mai matsakaicin sanyi.Sai da yunwar cikinta ta fara gushewa,kafin ta ɗebo cinyoyin pepechicken ta ɗaura akan soyayyiyar shinkafar da ta ji veggies da hanta tana cigaba da zirawa cikinta. Momy ce ta fito daga ɗaki ta hangota kame a dining ɗin tayi nisa cikin cin abincinta, ta ƙarisa wajen dining ɗin fuskarta ɗauke da murmushi tana faɗin, "Sorry Hannatu! Ba a fara gabatar miki da abinci ba first, na ɗauka sai kin huta zaki buƙaci abincin sorry!" Hannah duk sai kunyar duniya ya rufeta, ta rasa bakin magana sai sunkuyar da kanta da tayi kawai.Momy dake dubanta tana gano dukkanin alamun mace mai juna biyu a tattare da ita, sai ta sake sakin murmushi tana faɗin, "Shi babyn mai ci ne kenan,tunda ya urunta min daughter!" Wani bahagon kunya ya sake rufarwa Hannah, ta sake ƙasa da kanta tana blushing cike da jin nauyin Momy.Momy ta baro wajen don bata damar kammala cin abincinta a nutse, zuciyarta na cigaba da kisima rashin mutuncin da Adnan zai zo ya tadda a gareta.Don tasha alwashin saɓa masa fiye da duk yadda zai yi zato, sabida ta ga rashin arziƙin nasa gaba yake yi maimakon ya yi baya.

Koda Hannah ta kammala cin abincin sai kunya ya hanata tasowa daga dining zuwa cikin falo.Momy ce ta gane kunya ce ta hanata tasowa, sai ta ɗaga murya ta kirawo sunanta, "Hannatu!" Hannah ta amsa tana mai tasowa a kunyace ta iso cikin falon.Nesa da kujeran da Momy ke zaune ta zauna, tana sake sunkuyar da ƙanta ƙasa sabida tana jin idanun Momyn na yawo a kanta. Kamar saukar aradu ta ji Momy ta jefo mata tambaya tana cewa, "Hala sai da kika gaya masa na ce ki taho ɗin kamar yadda ya furta idan kin zaɓi cikin ki baro masa gidansa ko?" Hannah ta daburce da rasa abin faɗi, sai ta gyaɗa kanta kawai zuciyarta na karyewa da rauni mai yawa. Momy ta jinjina kai tana sake jefa mata

Please Login or Register in order to submit comment