Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana nufan bed kai tsaye don kwanciya. Ya lumshe idanunsa lokacin da kansa ke warwarewa daga caji da ta ɗauka, feeling ɗin da yake ji na tsananin son kusantar mace na sake ratsashi.Ya sake lumshe idanunsa yana ayyanawa a zuciyarsa da Hannah na nan da yanzu tana cikin jikinsa, don amfaninta kenan a garesa da zaran ya shigo a irin wannan yanayin da yake ciki.Tashi ya yi ya nufi side drawer ɗinsa yana ciro kwalin wani magani da ya jima bai yi amfani dashi ba, tun bayan fara sanin Hannah da ya yi a mace.Ya ɓalli biyu ya jefa a baki yana takowa inda ya aje ragowar table water ɗin ya ɗauka ya kora ruwan maganin suka wuce,ya aje goran yana sauke numfashi tamkar wanda yaci babu.Da ƙyar ya iya rintsawa a ƙarishen daren,yana mai yankewa kansa cewa dole zuwa jibi friday ya wuce KD don tinkaran koma miye akan cikin jikinta.

**********
*Kaduna.*

Washegary da wuri Najma ta wuce zuwa kitchen ɗin Gwaggo,suka haɗu da Tabawa don haɗa abincin breakfast.Lafiyayyan ƙosai da kunun tsamiya suka dama, sai aka soya egg da irish tare da dafa ruwan shayin da yaji kayan ƙamshi a dahuwar.Sosai ƙosan da Najma ta soya ɗin ya yi kyau da taushi, gashi ganin akwai wadatan kayan gayu na girki sai ta yi karanbanin yanka green pepe da wadatacciyar albasa a cikin ƙullun,ta saka curry kafin a soya.Sai ƙosan ya bada kala da flavour mai daɗi don green pepe akwai shi da daɗi a cikin wasu soya-soyen ga duk wacce ta ganewa sirrin.Ƙarfe tara suka kammala da komi Tabawa na faman yaba ƙoƙarin Najma da son aikinta,don tana da zafin nama da himma matuƙa da gaske. Najma ɗakinsu ta wuce don yin wanka ta shirya kafin Gwaggo ta fito, su haɗu suyi breakfast ɗin tare.Ta samu Inna Mairo a zaune tana sauraran karatu a cikin wayarta, ta gaidata tana mai wucewa bathroom ta yo wanka ta fito.A tsanake ta shirya cikin wata free gown na atamfa, wanda ɗinkin ya yi mata kyau a jiki sosai tare da fidda kyawunta.Bata shafawa fuskarta komi ba sai man leɓe data gogawa lips ɗinta,fuskarta sai ya yi fayau da asalin natural black beauty face ɗinta.Sassanyar ƙamshin turaren MISS DIOR da Nasreen ta bata ke tashi a jikinta,kamar yadda dukkanin ɗakin ma ya buɗe da ƙamshin mai sanyi.Inna Mairo ta ɗaga ido ta dubi Najma tana faɗin, "Najma kinga yadda ki ke ta sauyawa kuwa? Anya zuwa nan gaba ba zaki dinga yawo da dogon hijab har da niƙab ba? Ina tsoron kyawun mace ya cika bayyana Najma, domin ya kan zamewa wasu ƴan matan mummunan bazarana ga rayuwarsu.Nasihata a gareki kullum shi ne ki zama mai matuƙar kamun kai da takatsantsan wajen kare mutuncinki ta ɗiya mace,sannan ki nisanci sanya tufafin da zasu dinga bayyana surarki domin hakan ba wayewa bace.Ko kaɗan kada ki bari ruɗin duniya da zaman bariki su sanya ki watsar da tarbiyar da muka ginaki akai, domin daga ni har Malam burin mu ki zama nutsatstsiya mai tayamu kare mutuncinki da namu.A kowani mataki na rayuwa ki riƙa tuna cewa mutuncinki dana addininki shi ne abinda zaki fara karewa sama da komi a duniya.Sannan ki ji tsoran Allah wajen kiyaye kanki daga mazan da ba muharramanki ba, karki ruɗu da kalar rayuwar wasu ki ce kema zaki koyi dasu a abinda zai taɓa mutunci ko tarbiyarki mai nagarta.Don Allah Najma karki sauya akan kyawawan ɗabi'u da halayen da aka sanki dasu, sannan karki dinga manta asali da tushenki duk yadda rayuwa zata zo miki da sauyi.Ki dinga tuna cewa ke ɗin ba kowa bace ba kuma ƴar wani bace, face ƴar ƙauyen garin giwa." Inna Mairo ta ɗan dakata da maganar tana duban yadda Najma ta nutsu tana saurarenta.Ta ɗaura da cigaba da faɗin, "Ba ina miki wannan nasihar da wata manuface Najma, sai don ina tsoron sharrin zuciya da ruɗin duniya.waɗanda suke saurin sauya tunanin ɗan adam farat ɗaya! Dole sai ana yi ana taro ku tare da yi muku nasiha,don duniyar dukkaninta babu tabbas a cikinta.Ki riƙe gaskiya da amana, duk rintse karki yarda mutanen da suka aminta dake, suke nuna miki ƙauna tsakani da Allah su sameki da rashin gaskiya ko cin amana.Ki taimakeni ki tayani kyautata musu da yi musu biyayya, sannan ki guji shiga cikin lamarin da ba a sanya ki ciki ba.Ki nisanci ƙarya da ha'inci,duk da cewa ba halayyarki bace,amma ina so kiyi matuƙar takatsantsan Najma domin zama a ƙarƙashin wasu abu ne mai matuƙar wahala.Ki ninka haƙurinki domin dole za a saɓa miki kamar yadda kema zaki saɓa musu cikin rashin sani koda gangan,ina fata zaki kiyaye ki kuma nisanci son abin hannunsu.Dukkanin abinda aka ɗakko aka baki kiyi godia, wanda ba a baki ba ko ya shiga ranki ki kauda da kai karki yadda ki taɓa abinda ba a baki ba.Na sani baki da kwaɗayi, amma ina miki matashiya da ki ninka akan kyawawan ɗabi'unki da na sanki dashi, hakan zaisa na cigaba da alfahari da ke Najma kin ji ko?" Najma da dukkanin jikinta ya yi sanyi da nasihun Inna Mairo, sai ta gyaɗa kai murya a sanyaye ta ce, "Naji Inna, kuma In Sha Allah zan kiyaye dukkanin nasihunki.Allah ya barmu tare har mutuwa mu je mu tadda Malam a aljanna cikin aminci." Inna Mairo ta yi murmushi wani abu na motsa zuciyarta.Cikin sanyin murya ta furta,"Ameen Najma! Allah ya cigaba da haskaka makwancinsu,tashi muje kada Gwaggo tayi ta jiran mu." Suka fito daga ɗakin jere da juna,zukatansu na tuno musu da rayuwarsu a garin giwa tare da mutanen arziƙinsu Iyalan gidan Hakimi. Sun tadda Gwaggo har ta fito tana zaune wajen da suka saba cin abinci ta fara serving kanta.Suka zauna suna gaida Gwaggo a tare,ta ɗaga ido tayi musu duba ɗaya tana yaba kyawun da dukkaninsu suka yi cikin suturu masu kyau da ke jikinsu.Idanunta akan Najma ta furta, "Jikata ya gajiyan suya?" Najma ta saki wide smile tana faɗin, "Babu gajiya Gwaggo, Allah dai ya sanya ya yi miki daɗi,don nayi miki karambanin ƙara wani abin a ciki."

Gwaggo ta kai hannu tana buɗe kulolin har ta buɗo wanda ƙosan ke ciki, wani ƙamshi ya cika wajen mai daɗi.Ta ɗakko ɗaya ta kai baki tana faɗin, "To bari na ji wani karanbani ne kuma aka yi a cikin ƙosan." Ta tauna tattausan ƙosan da ke tashin ƙamshin green pepe da albasa tare da ƴar curry kaɗan da aka buga ƙullun dashi,wani irin daɗi ya ratsa harshenta zuwa kwanyarta.Ta lumshe ido tana buɗesu akan Najma ta ce, "Wayyo daɗi! Inji Yaro, gaskiya Najma kin iya ƙosai tamkar wata tsohuwar mace da hannunta ya nuna a iya tuya.Gaskiya dole Kabeeru ya yaba miki, aini ban taɓa sanin kin iya har hakan ba da kusan kullum dashi zan dinga karin safe,don ni Kabeeru ya gado a son karin safe da ƙosai ko waina da kunu." Daga Inna Mairo har Najma suka saki ƙaramin dariya, Najma na duban yadda Gwaggo ta sake jefa ƙosan a baki har da wani kanne ido.Ta sake sakin smile tana faɗin, "Allah sarki Gwaggo! Ai nima bansan kina so ba kuwa, da yake sana'arsa muke yi a ƙauye muke samun na rufin asiri lokacin." Gwaggo ta jinjina kai tana jin ciwon su dinga tuno rayuwar wahalar da sukai a baya,cikin kulawa da son kawar da maganar ta ce, "Gaskiya ni dai ke ce zaki dinga mana ƙosai ko idan watan azumi ya kamane, wannan irin ƙosai mai shegiyar daɗi haka." Najma suka sake sanya dariya,kafin tayi serving ɗinsu ita da Inna Mairo suka fara nasu karin.

Suna dab da kammalawa Nasreen da Hannah suka shigo cikin falon Gwaggon.Hannah ke gaba Nasreen na bayanta cikin shirin fita skull,suka zauna suna gaida su Gwaggo cike da ladabi.Najma ta gaida Hannah ta amsa da fara'a tana faɗin, "U look so fresh and beautiful Najma! Gaskiya na jima banga black beauty da skin mai kyau irin naki ba." Najma ta saki murmushi tana duban Nasreen da ta tsareta da ido ta ce, "Sis wannan kallon kuma fa?" Nasreen ta saki smile tana cewa, "Kyau kika min ba kaɗan ba Najma, anya nan gaba ba goslow zaki dinga haɗa mana a layi ba?" Najma ta jefa mata harara tana faɗin, "Kai Nasreen, wallahi kin cika neman magana." Hannah ta taya su yin dariyar idanunta na sauka akan ƙosan da Gwaggo ke ci baji ba gani.Gwaggo ta ɗago suka haɗa ido da Hannah, sai tayi saurin faɗin, "Hannatu ko zaki ci ƙosai a zubo miki, ko kema ƴar gayunce irin mijinki da sai abincin turawa yake karyawa dashi?" Hannah tayi ƙasa da kai tana faɗin, "Gwaggo ni kam babu ruwana ina ci sosai ma, musamman wannan ɗin da nake ganin kyawunsa tun a ido." Gwaggo ta zuba mata plate ta miƙa mata tana faɗin, "Maza sakko kici tunda zafinsa, ga kunu nan ki zuba shi ma idan kina so." Hannah da dama ƙosan ta biyo, don tunda akai zancensa jiya ta ji shi kaɗai take son ci.Shiyasa Nasreen na shiryawa ta ce zata yo nan ɗin ita ma tace da Momy zata zo ta gaida su Gwaggon,suka fito suka yo nan ba tare da ta tsaya yin breakfast a can ba.Sosai ta ci ƙosan tana yaba daɗinsa da ƙwarewar Najma a iya sarrafashi, Gwaggo ta cigaba da kwarzanta daɗinsa suna kwasan dariya.Nasreen ce ta yiwa Najma magana cewar zata wuce skull, idan ta dawo kuma zata rakata wata unguwa.Ta raka Nasreen ɗin har wajen motarta ta wuce skull, ita kuma ta juyo zuwa side Gwaggon.Tana shigowa Hannah na fitowa zata koma side ɗin Momy, ta yiwa Najma kallo ɗaya da murmushi akan fuskarta ta ce, "Najma naci ƙosai mai daɗi da yawa, gaskiya kin sama ladana thank u beauty!" Najma ta sakar mata smile tana faɗin, "Laah! Bakomi Anty, na gode nima da yabawa." Daga haka Hannah ta wuce ita kuma Najma ta shige daga ciki.Sai wajen sha ɗaya suka fito daga side ɗin Gwaggo zuwa na Momy don gaidata.Sun sameta tare da Nabeelah da Hannah zaune suna hiransu, suka gaisa a mutunce idanun Momy akan Najma ta furta, "Idon ki kenan daughter? Na fito jiya kawai sai na tadda Gwaggo ta tasa ƙeyarki kun koma can ɗin,ai gobe dai Daddy idan ya dawo zai yi mata magana da kansa cewa nan zaki dawo da zama dai." Najma da haka kawai bata son hakan a ranta sai ta saki murmushin yaƙe ba tare da ta yi magana ba, sai Inna Mairo ce ta ce, "Ai dama kun barta kawai a can ɗin, indai Najma ce ba za ta iya zaman waje ɗaya alhali tasan ina cikin gidan." Momy tayi dariya tana faɗin, "Aiko hakanan zata dawo nan ɗin, gara ta zauna cikin ƴan uwanta su riƙa yin komi tare hakan zai sake haifar da shaƙuwa a tsakaninsu......✍🏻




*Pay 500 in to this account number👇🏻*
*0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank*
*OR*
*PAY IN TO DIS ANOTHER ACCOUNT* 👇🏻
*8167768704 AISHA* *DANSABO IBRAHIM*
*ACCOUNT NAME:OPAY*
*Evidence of payment to this number:08167768704*


🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻*
*MTN*
*GLO*
*AIRTEL*
*9MOBILE*
*MONTHLY VADILITY 💃🏻*

*DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻



#Lovestory#
#Najma#
#Aysha Ɗansabo Lemu🥰
[3/20, 5:14 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!*🤲🏻 *Arewabooks@ayshadansabo*

*Paid book:500*

*Chapter 18*

_Free page_

Hira sosai suka sha a tsakanin junansu kafin Momy ta wuce kitchen,don fara shirya abinda zata tarbi Daddy dashi.Wanda a yau ɗin friday zai dawo weekend daga Abuja.

Najma Momy ta kira bayan Inna Mairo ta koma ɓangaren Gwaggo domin taya Tabawa ɗaura girki.A hankali Najma ke taya Momy ayyukan da ta bata,don ta fahimci tana da son koyan girkin da gaske.Bayan sun kammala Najman ce dai Momy ta saka ta dinga kwasan warmers ɗin zuwa ɓangaren Daddy tana shiryawa akan dining.Cikin tsari da nutsuwarta na halitta take gudanar da komi nata,abinda ke sake birge Momy kenan don tana son mace ta kasance nutsatstsiya ba mai rawar kai ba.

Hannah ɗaki ta shige tana chart da kuma karance-karancen novel da ta fara koya, don zaman kaɗaicin da take yi a port harcourt ɗin idan AD ya fita oficce, ya sanya ta fara koyan karatun novels da ake turawa a wani group da Anty Laurah ta sanya ta a ciki.Wani book ɗin Mamuhgee take karantawa mai suna IDON NERA,sosai ɗin book yake tafiya da zuciyarta take kuma jin daɗin karatun.Ta lunshe idanunta tana tunanin AD Dukku da son zuwansa a gobe ko yau ɗin, don da gaske kewar ganinsa take yi tsakanin jiya da yau da bata sanya shi a idanunta ko jin motsi ko muryarsa da ke kasheta ba. Momy ce ta kira wayarta time ɗin da ta idar da sallar zuhur da ta tashi ta gabatar da ƙyar, sabida kasalar da take ji.Ta ɗaga wayar tana sauraren Momy da ke bata umurnin fitowa tayi lunch tare dasu a dining.Ta aje wayar tana miƙewa ta canza rigar jikinta daga dogon shimi zuwa doguwar riga mai ƙaramin hannu.Rigar na wani haɗaɗɗan Indian material ne da yaji ɗinkin embroidery, wanda aka yisa tun daga wuyar rigar zuwa ƙasansa.Sosai tayi kyau da fresh irin na masu ciki, waɗanda hutu ya ratsa fatarsu babu wahala sam a tare dasu. Tare da Najma da Momy suka haɗu sukai lunch ɗin,bayan sun kammala Momy ta sanya Najma raka Hannah zuwa part ɗinsu da su Rabi suka kammala goge ko'ina.Sosai Najma ta yaba da tsaruwar part ɗin,wanda yafi na Gwaggon kaduna girma.Sannan tsarin ginin ma yafi haɗuwa, ga kuma rantsatstsun kayan ɗaki dana kitchen da aka yiwa Hannah irin na ƴaƴan gata,waɗanda iyayensu suka tada kai da naira.Don mahaifinta Alhaji Surajo ba ƙaramin mai kuɗi bane,don ma ya ɗan samu karayan arziƙin da har Daddy ya keresa,amma a baya ko Daddy ba zai nuna masa arziƙi ba.Ƴan asalin jihar kano ne su,aiki ne ya maida Alhaji Suraj ɗin Abuja da iyalinsa baki ɗaya.Sai dai yana da gida a kaduna da suke yawan hutu nan,daga nan su wuce kano a wasu lokutan.A hakane kuma ta hanyar yawan zuwa Kd da suke yi,suna ziyartan gidan Daddy da kuma yadda Adnan ɗin ke yawan ziyartan Alhaji Suraj ɗin idan ya shiga Abuja, Hannah ta ƙyalla ido ta gansa ta kuma maƙale masa.Babu kalar samarin da bata yi ba tsakanin Abuja da mahaifarta kano,amma ta watsar da kowa ta kama ɗan mutan Dukku.Wanda shi kuma zuciyarsa bata taɓa ƙaunarta ba, kawai auren nasu yazo a NUFIN ALLAH ne kawai.Wanda idan ya yi NUFIN abu ya kasance sai ya kasance ɗin,koda ace babu yarda da amincewar kowa ne.

Duk yadda Hannah ta so Najma ta jira yi dawowar Nasreen daga skull anan side ɗinta ƙi tayi, ta matsa zata wajen Innarta ne ta dawo ne.Hakanan Hannah ta ƙyaleta ta wuce,tana jinjina rashin saurin sakin jikin Najma da mutane sosai.Gashi kuma ita Allah ya ɗaura mata son Najma a ranta tun ganin farko, sabida yadda kyawunta da sanyinta ya tafi da zuciyarta.Sannan yawan murmushin da baya rabo da fuskar Najmar abin na sake birgeta, yana kuma ƙarawa Najmar kwarjini da kyawu matuƙa.

Najma na baro side ɗin Hannah ta wuce ɓangaren Gwaggo.A nan falo ta samesu suna hira,Gwaggo kuma na daga kishingiɗe tana amsa waya.Ta nema waje ta zauna tana sauraran yadda Gwaggo ke amsa wayar cike da ɗaga murya,wanda hakan ya zame mata jiki sam bata iya magana a hankali a waya ba.Bayan ta kammala wayar ne Najma tayi mata sannu da hutawa,ta amsa da fara'a tana faɗin, "Najmatu gobe fa sai garin giwa,tafiya babu fashi In Sha Allah! Don haka Nasreen na dawowa zaku je ku yo siyayyar tsaraban da za a wuce musu dashi.Duk dai na kammala tanadan abinda ya dace,amma su ƴan matan ƙawayen naki kece zaki san abinda zai fi birgesu." Najma godiya ta dinga wa Gwaggo bayan ta dasa aya a maganarta.Gwaggo ta nuna babu komi yiwa kaine, daga nan kuma sai ta sanya Najma zuwa kitchen ɗinta ta ɗakko mata kwanon nono da fura a fridge ɗinta.

Nasreen sai ƙarfe biyu da rabi ta shigo gidan a gajiye, direct ɗakinta ta wuce tayo wanka ta saka riga mara nauyi.Dining ta fito ta nemi abinci don da yunwa ta shigo gidan,sabida bata ci komi a skull ɗin ba yau ɗin.

Momy ce ta sanar da ita cewa Hannah na part ɗinta,hakan ya sanya Nasreen na kammala cin abincin suka nufi wajen Anty Hannah ita da Nabeela da tun rana ke ɗaki tana karatun books na skull don ita mayyar karatu ce. Daga can wajen Anty Hannah side ɗin Gwaggo Nasreen ta wuce wajen Najma.Ta samu Gwaggo da Inna Mairo tare da Tabawa a falo suna zantawa,ta tambayi Najma Inna Mairo ta ce tana ɗaki ta ɗan kwanta ta ce kanta na ciwo.Cikin hanzari Nasreen ta nufi ɗakin su Gwaggo bakinta ɗauke da sallama,ta hangi Najma kwance bisa bed da waya a hannunta.
"Beauty baby ya aka yi ne da kwanciya da ranarnan haka?" Nasreen ta furta hakan tana zama daga bakin bed ɗin.Najma da ƙamshin turaren Nasreen ɗin ya bugi hancinta kafin isar muryarta cikin kunnuwarta, sai tayi saurin tashi zaune da murmushi akan face ɗinta ta ce, "Sis kin dawo? Wallahi kaina ke ciwo amma na sha magani ya faɗa mini,yanzu karatu nake yi a waya." Nasreen ta jinjina kai tana duban fresh black beauty face ɗin Najma da ke glowing ta ce, "Ayyah! Sannu Sis, wato kin fara koyan karatun novel ko? Ni kinga ban iya ba,karatun skull kaɗai ya isheni." Najma ta jinjina kai tana faɗin, "Wallahi Sis na fara koya, kuma ina ƙaruwa sosai,kawai luv ɗin cikin books ɗin ne yake bani kunya da mamakin anya ko ni zan iya wata soyayya kuwa?" Najma tayi tambayar bilhakki idanunta akan Nasreen ɗin.Nasreen ta tuntsire da dariya tana faɗin, "I don't know now,but idan lokaci ya yi zaki iya fiye ma da wanda kike karantawa." Najma ta ɗan ɓata face cike da shagwaɓe murya ta ce, "Ni dai gaskiya bana ji zan iya kam, yanzu dai bani labarin me kika taho min dashi?" Nasreen ta saki smile ta ce, "Nothing beauty! Amma zamu fita yanzu ai sai mu biya musha COLD STONE muci pizza." Najma da sam bata damu da irin abubuwannan ba,sai ta ɗan yamutse face tana faɗin, "Ni dai ban iya shan kayan sanyinnan ba, shi ma pizza ɗin baki ga ban iya cinsa sosai ba." Nasreen ta miƙe tsaye tana duba time a gogon dake ɗakin ta ce, "Oya shirya Najma, lokaci na tafiya gara mu fita yanzu koma dawo kafin Daddy ya ƙariso." Najma ta sakko daga bed ɗin ta nufi closet ɗinsu ta ɗakko rigar da zata saka su fita ɗin.Nasreen na tsaye tana dubanta ta saka doguwar rigar boubou na wata pink ɗin atamfa,rigar ya yi mata kyau kalar kuma ya haska black skin ɗinta mai sheƙi da fresh.Ga kuma sassanyar ƙamshin turaren Miss Dior da ta fesa kaɗan na tashi a jikinta.Ɗankwalin kayan ta ɗaura tana ɗakko wani ƙaramin hijab irin na makkah da Momy ta bata ta saka.Hijab ɗin tsayinsa duka iya cinyarta ya tsaya,amma ya rufe dukkanin hannayenta bai dai ƙarisa sauka zuwa cinyarta bane.Kalarsa milk ne da ya shiga da kayan jikinta,wanda akai wa touch da milk colour a jiki,sai ta fito tayi wani irin mugun kyau.

Jere da juna suka fito zuwa falon Gwaggo, Nasreen nata yaba kyawun da Najma tayi.Daga Gwaggo har Inna Mairo idanunsu akan Najma suke,Gwaggo ta kasa shiru sai da ta furta, "Najma wannan kyawu da kike ta sake zabgawa haka." Najma ta saki murmushi ta ce, "Gwaggo a hakan?" Gwaggo ta jinjina kai ta ce, "Ƙwarai kuwa! Don baki ga yadda kyawunki ke sake fitowa bane shiyasa.Nasreen maza ɗakko min ƙaramar jaka akan gadona na sallameku." Nasreen ta wuce ta ɗakkowa Gwaggo jakan ta kawo mata.Ta amsa tana zuge zip ɗin ta ciro kuɗaɗe ta irga wanda zata basu tana miƙawa Najma tana faɗin, "Ungo Najma, ku siyowa ƙawayenki tsarabar da xaki kai musu gobe kin ji ko?" Najma ta amsa kuɗin tana godia Inna Mairo na taya ta ita ma.Sukai musu sai sun dawo suka fice don zuwa yiwa Momy sai sun dawo ɗin.Ita ma kuɗi ta ƙara musu ta ce Najma ta siya abinda take so,sannan ta sake ba Nasreen wasu kuɗin ta ce ta siya mata wasu abubuwan da zata wuce wa ƴan giwa dashi ita ma.

A gaban motar Nasreen Najma ta kame,hannunta riƙe da wayarta da ke sake shiga zuciyarta.Suna tafiya suna hiransu cike da nishaɗi, Nasreen na faman tsokanar Najma da cewa akwai wani guy da za ta haɗata dashi.Najma ta bankawa Nasreen harara tana faɗin, "Don Allah Nasreeny ki rufamin asiri, nifa wallahi da gaske nake ba zan iya wata soyayya ba." Nasreen tayi dariya sosai kafin ta furta, "Ba za ki yi aure ba kenan?" Najma ta jinjina kai ta ce, "Wannan kuma ai ana yinsa ko babu soyayyah, indai shi mijin zai soni ai shikenan ba dole sai nayi soyayya zan yi aure ba ai." Nasreen ta jinjina kai tana faɗin, "Gaskiya sai yau na yadda ke ɗin auta ce Najma." Najma cike da nuna halin ko inkula ta ce, "Hmmm! Ke wasa ki ke ganin komi Nasreen, ni kam da gaske nake furta dukkanin kalamaina."
Nasreen tayi saurin faɗin, "Kar dai ki cika baki, don ita soyayya bata ƙwanƙwasa ƙofa, shiga kawai take yi duk zuciyar da ta so ba tare da bada notice ba.So kada Yarinya ta zo ta cika baki watarana in ji ana kuka ana faɗin Nasreen ya zanyi da soyayyar wane." Nasreen ta ƙare maganar ta bushewa da dariya, hakan ya sanya Najma sake narke fuska kamar zata saki kuka ta ce, "Allah dai ya yafe miki Nasreeny! Amma kin gama dani yau wallahi."

Sosai suka ɗauki ɗauki lokaci a kasuwa suna siyayyar,Najma duk kuɗin da aka bata sai da ta ƙarar dashi wajen siyawa mutanenta su Lubah kayan gayu masu kyau.

Kafin su wuto gida sai da suka tsaya suka sayi COLD STONE ice cream da Shawarma,suka sake tsayawa a wani waje suka sayi Chicken Kebab sannan suka wuto gida. Suna shigowa Nasreen ta hango motar AD Dukku da ake ɗakkosa daga airport idan ya zo gari a fake a parking space, ƙirjinta ya yi wani irin bugawa da jin haushin zuwansa garin.Ta isa ta raɓa motarta da nesa kaɗan da nasa suka fito daga cikin tasu motar.Najma na kwasan wasu kayan dake back seat take faɗin, "Ina muka nufa?" Nasreen da gaba ɗaya mood ɗinta ya canza da ganin motar Yaya AD ɗin, sai ta ƙaƙaro murmushi tana faɗin, "Mu nufi side ɗin Momy kawai Najma, idan mun yi magriba sai mu je wajen Gwaggo taga siyayyar ko?" Najma ta jinjina kai cike da gamsuwa tana faɗin, "Okey to bari na kwashi waɗannan kayan." Najma ta ƙare maganar tana kwasan mafi yawan kayan da ke back seat ɗin ta nufi side ɗin Momy dasu.Nasreen ta rufe motar tana kwasan sauran kayan ta rufawa Najma baya, wacce har ta kusa isa ga ƙofar shigewa ciki.Kusan a tare suka isa bakin ƙofar shiga babban falon Momy, tun kuma kafin a amsa sallamarsu iska ya kwasowa Nasreen ƙamshin turarensa na CREED AVENTUS mai ƙarshen tsada ya buso hancinta.Muryar Momy da ta amsa sallamar da suka doka tare da basu izinin shiga, ya sanya suka kutsa kai cikin falon.Daddaɗan ƙamshinsa da ya haɗe dana ɗakin ya daki hancin Najma,hakan ya bata tabbacin akwai baƙo ko baƙuwar a cikin falon.Idanunta yakai kan wanda ke zaune ya baiwa ƙofar shigowa falon baya, kalar rigarsa da sassalkan baƙin gashin kansa irin na fulani kawai ake iya hangowa.Daga nesa dasu kaɗan Nasreen ta ce, "Mommy mun dawo bari mu wuce ɗaki." Momy ta jinjina kai tana musu sannu da zuwa, Nasreen kuma ta ɗanyi gaba kaɗan tana ɗaga murya yadda zai jiyota ta ce, "Yaya AD welcome!" Bai juyo ba sai hannu da ya ɗaga mata kawai.Hakan ya sanyata

Please Login or Register in order to submit comment