Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abada hakan ba zai taɓa faruwa Baban Hanne, domin ku ɗin kun zama wani ɓangare na rayuwarmu ni da Najma. Ba zamu taɓa manta halaccinku da ƙaunar da kuka nuna mana ba,domin kun tallafemu a lokacin da muka rasa dukkan gata.Kun riƙe mu tamkar jininku ba tare da nuna gazawa ko gajiya damu ba, wannan kaɗai ya isa ya sanya mu dauwama muna yi muku addu'ar gamawa lafiya tare da damƙe igiyar zumunta tsakaninmu da juna. Zamu yi kewar da zai wuce yadda zaku yi namu Hakimi, domin daku muka yi sabon da ku kaɗai ku ke sanin farin ciki ko damuwarmu. Ku kaɗai ke fara kawo mana ɗauki a dukkanin abinda ya taso mana, mai daɗi ne ko marar daɗi. Kune cin mu ku ne shan mu tare da suturarmu,taya zamu manta dukkanin wannan alkhairyn har mu kasa cigaba da sadar da zumunta tsakanin mu da juna? Hakan ba zai taɓa faruwa ba Hakimi, ina sake godiya tare da fatan alkhairy ga rayuwarka da ta Iyalinka baki ɗaya." Inna Mairo ta tsaida maganar hawayen tsananin kewar da zasu yi na baro garin giwa su dawo nan ɗin na wanke fuskarta. Gwaggo da Yaya Kabeeru ne suka cigaba da tataunawa akan Hakimi zasu tafi su bar Najma da Inna Mairo a nan ɗin. In yaso nan zuwa kwanaki uku shi da Gwaggo da su Inna Mairon zasu yi mota guda su yiwa Inna Mairo rakiya zuwa giwa, don su yo bankwana da Iyalan Hakimi su kuma ɗakko abinda suke so. Inna Mairo ta dinga sharan hawaye tana tuno fuskar Uwargidan Hakimi Inna Karima, tana ayyana irin kewar juna da zasu yi.Daga ƙarshe Yaya Kabeeru ya janye Hakimi zuwa ɓangarensa, ya yi masa masauki a ƙawataccen falonsa na ƙasa inda yake ganawa da baƙinsa. Sun tattauna muhimman lamura akan abinda ya shafi rayuwar Inna Mairo da ƴarta Najma. Hakimi ya yi masa dukkanin bayanin da ya shafi yadda hawan jinin Inna ke yawan tashi, ya kuma sanar dashi abinda likita ya faɗi na cewa zuciyarta na barazanar kamuwa. Alhaji Kabeer Dukku ya dinga yiwa Hakimi godia tare da jin ƙaunar dattijon na ratsa shi, don Hakimi ya fara zama dattijo don ya haura shekaru hamsin da takwas, kaɗan ya rage ya kai shekaru sittin a duniya.Suka yi sallama da Alhaji Kabeer bayan ya jaddadawa Hakimi cewa suna nan tafe nan da kwanaki uku. Daga shi har Iyalinsa duka zasu rako Inna Mairo garin giwa don tayi sallama da abokanan arziƙinta, shi kuma suyi godiya ga Iyalan Hakimin. Daga Inna Mairo har Gwaggo da Hajiya Zainab, dukkaninsu suka rako su Hakimi har bakin mota lokacin da zasu tafi. Najma na wani irin kuka mara sauti don ita ko kaɗan hukuncin cewa ba zasu koma garin giwa ba bai mata daɗi ba, domin da mutanan garin ta saba,sannan su ta taso ta sani a matsayin komi nata.Don haka a yanzu farat ɗaya ace za a rabota da ƴan uwanta su Hanne tana ganin tamkar rashin adalci ne da datse mata farin cikinta.Auwalu kansa kallon Najma ya dinga yi zuciyarsa na masa wani irin suya, hakanan yake jin bai ji daɗin yadda za a ce ba za su koma giwa ba. Ya dinga mita a zuciyarsa yana faɗin da can mai yasa suka yi watsi da lamuransu, sai a yanzu ne suka san da cewa Inna Mairo ba za ta cigaba da zaman karkara ba? Har Hakimi ya shiga mota Auwalu mita yake a zuciyarsa yana ji tamkar ya sanar da Najma sirrin zuciyarsa a kanta,ya haɗe fuska tamau lokacin da Gwaggo ke masa fatan su isa lafiya. Alhaji Kabeer Dukku kuwa matsawa ya yi daga jikin motar ya miƙawa Auwalu wata ƙaramar envilop, mai ɗauke da damin kuɗin ya ce su sha mai dashi. Auwalu ya amsa ya yi godiya fuskarsa sam babu walwala, sai ma ƙarin baƙin ciki da alhinin daina sanya Najma da zai dinga yi a idanunsa ke sake kassara zuciyarsa. Inna Mairo ta matsa har jikin motar tana sake yiwa Hakimi godiya tare da yi musu addu'ar Allah kiyaye hanya.Ita kam Najma ta kasa isa jikin motar sai tsayawa tayi daga nesa tana cigaba da kuka mai cin rai. Nasreen da ke tsaye daga bayanta ne ke faman rarrashinta akan tayi shiru, amma ko duban Nasreen ɗin ta kasa yi bare ta saurari rarrashinta da take yi. Dukkanin zuciyarta na ga su Hanne da Lubah, waɗanda ta san yau kwanan kuka zasuyi idan suka ji labarin za a rabasu da garin giwa su dawo nan ita da Innarta. Ita ko kaɗan hakan bai yi mata daɗi ba don duk yadda Gwaggo ke wani nuna nadamarta ba birgeta take yi ba, sai ma sake jin zafinta da take yi a cikin zuciyarta idan tana tuna irin yadda Inna ke kuka da idanunta na irin baƙin ciki da ƙiyayyar da Gwaggon ta nuna mata. Hannunta Inna Mairo ta kama lokacin da motar su Hakimi ta bar wajen,ta yi ƙasa da murya tana cewa da Najma, "Ki yi shiru ki tsaida wannan kukan Najma, nan ma gida ne kamar can kinji ko?" Najma ta ja ajiyar zuciya tana cewa, "Amma Inna meyasa zasu ce ba zamu koma can ba alhali ni nafi son can, duk talaucin da muke ciki a can wallahi nafi son can da nan ɗi....." Hannu Inna ta sanya ta rufe bakin Najma tana jifanta da wani kallo mai cike da gargaɗi ta ce, "Karna kuma jin kina faɗin hakan Najma, Gwaggo da Yaya Kabeeru sun yanke hukuncin mu dawo nan ɗin. Kuma hakan shi ne daidai domin sune tilashina ba Hakimi ba, shi halacci yake nuna mana amma ba don nauyin kulawa damu ya rataya a wuyarsa ba. Lokaci ya yi da za a barshi da Iyalansa ya hidimta musu, don koda kuɗin maganina aka cigaba da barinsa tabbas ana shiga rayuwarsa. Ki sani yau da gobe sai Allah Najma,sannan duk yadda zaki yi kewar su Hanne da Lubah bai kai yadda ni zanyi kewar baro garin giwa ba. Domin gari ne da tarihin rayuwar da nayi aciki da mahaifinki ba zai taɓa gogewa a zuciyata ba, sannan ban taɓa sha'awar baro garin ba koda wasa.Don haka ki daina faɗin komi da zuciyarsu ba zai so ba idan sun ji, shi komi NUFIN ALLAH ne Najma. Haka ALLAH Ya NUFA cewa lokaci ya yi ne da zamu baro garin giwa ba don mun gaji da garin ko mun daina son jama'ar cikinsa ba, sai don haka ALLAH Ya so Ya kuma yi NUFIN zai kansance." Inna Mairo ta kai ƙarshen maganar tana duban yadda hawaye ke gudu akan black beauty face ɗin Najmarta. Tuni su Gwaggo sun rigasu yin gaba don su suna takawa ne a hankali Inna na rarrashin Najmar, hakan ya sanya babu wanda ya ji dukkanin kalamai da rarrashin da Innar kewa Najma. Najma ta jinjina kai cikin sanyin muryarta ta ce, "Shikenan Inna, ba zan kuma magana ba amma ki sani zan jima ina kewar su Lubah." Inna Mairo ta gyaɗa kai tana sakin ƙaramin murmushi ta ce, "Na san hakan zai faru Najmata, amma a hankali zaki rage jin kewarsu idan ki ka saba da zaman nan ɗin. Ki yi addu'a ne kawai akan Allah yasa dawowarmu nan ɗin ya zame mana alkhairy kinji ko?" Najma ta jinjina kai ba tare da ta iya cewa Inna komi ba. A haka suka isa part ɗin Gwaggon kaduna, suka sameta zaune a falo alamun jiran shigiwarsu take yi...........✍🏻



*Pay 500 in to this account number👇🏻*
*0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank* *Evidence of payment to this number:08167768704*


🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻*
*MTN*
*GLO*
*AIRTEL*
*9MOBILE*
*MONTHLY VADILITY 💃🏻*

*DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻



#Lovestory#
#Najma#
#Aysha Ɗansabo Lemu🥰
[3/8, 1:05 AM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻
*Arewabooks@ayshadansabo*

*Paid book:500*

*Chapter 12*

_Free page_

Gwaggo ta dubi fuskar Najma da har lokacin da alamun hawaye ta ce, "Kiyi haƙury Najma nan ma gida ne,kuma sannan ga Nasreen nan tsararki ce sai kuyi ta hidimarku ba zaki yi zaman kaɗaici da rashin abokin hira ba kinji ko?" Najma ta gyaɗawa Gwaggo kai fuskarta sam babu walwala ta ce, "Tuh!" Daga haka bata sake cewa komi ba, ta takure jikinta daga gefe guda tana sauraran hirar da Gwaggo ke jan Inna Mairo da shi.Gabaki ɗaya hankali da tunanin Najma na ga ƙauyen giwa ne, tana ayyana ko yasu Lubah zasu amshi zancen barowarsu garin giwa a rana tsaka? Wasu hawaye suka sake cika idanunta tana ƙoƙarin maidasu don bata so ran Inna ya ɓaci.

Gwaggo ko labarin bikinsu Adnan Dukku da Jiddah ta ke faman bai wa Inna Mairo, tana kuma sake bata haƙuri game da yadda ko bikin ba a sanar mata ba. Inna Mairo ta sanarwa da Gwaggo zancen zuwan Adamu drivernta da tarin abin arziƙin da Hajiya Zainab ta aika mata dashi. Gwaggon kaduna tayi shiru na wani lokaci,kafin ta dubi Inna Mairo da tsantsar mamakin da ke haskawa a saman fuskarta ta ce, "Yanzu dama zuwan da tayi ta ce in bata aronsa zata aikesa wani waje giwa ya tafi wajenki?" Inna Mairo ta gyaɗa kai cike da tabbatarwa ta ce, "Wajena ya je Gwaggo, kuma da tarin abin arziƙi babu abinda zance da irin ƙaunar da take nuna mini sai dai in yi mata fatan gamawa lafiya." Gwaggo ta jinjina kai ƙaunar surukarta na sake samum wajen zama a zuciyarta, sabida tabbas Momy mace ce ta gari da Alhaji Kabeer Dukku ya yi sa ar samu. Ta cigaba da kallon Inna Mairo tana faɗin, "Ai Zainab ta haifu Mairo, bani da abinda zan ce sai godia domin Kabeeru ya yi dace da macen ƙwarai mai ƙaunar dukkanin ahalinsa na birni da ƙauye.Don hatta mutanen Dukku hidimta musu take ba tare da gajiyawa ba.Shiyasa nake tsananin ƙaunarta a zuciyata,don tafi matar Ali sanin ya kamata, sannan ta fita son dangin miji da girmamasu." Inna dai jinjina kai tayi ta ce, "Allah sarki, gaskiya Yaya Kabeeru ya yi dace Gwaggo." Daga haka bata tofa akan irin yadda Gwaggo ke tsinan halayyar matar Yaya Alin ba, da alamu bata jin daɗinta sam! Ko kuma bata girmama Gwaggon irin yadda ita Momy ke mata.

Sai dab da kiran sallar magriba Gwaggo ta yiwa Inna Mairo jagora zuwa ɗakin da ta ware musu ya zama mallakinsu. Bedroom ɗin na daga can ƙarshe ta wani corridor na daban bata cikin wanda ake shiga na ɗakin baccin Gwaggon ba, ta sanar da Inna Mairo cewa nan zasu ɗauka sabida yana da yalwa sosai.Inna Mairo ta dinga godia tamkar Gwaggo ta yi mata kyautar wani gagarumi. Ta shige daga cikin ɗakin tana ware idanu,tana kallon tsaruwar ɗakin da komi yake a tsare tsaf! Daddaɗan ƙamshi na tashi a cikin ɗakin don duk ranar duniya sai an gyare ɗakunan baccin duka an goge ko'ina. Najma sai daga baya tabi Inna Mairo zuwa ɗakin da aka ware musun, sosai ɗakin ya ƙayatar da ita amma ko a fuska bata nuna hakan ba. Ta samu saman sofa da ke ɗakin ta zauna ta mai zabga tagumi, don Inna Mairo ta shiga toilet ɗauro alwala lokacin da ta shigo. Koda Innar ta fito kallo ɗaya ta yiwa Najma tayi gaba zuwa wajen da ta shinfiɗa abin sallah.Ganin hakan ne ya sanya Najma tashi jiki a sake ta nufi toilet ɗin ita ma don ɗauro alwalar.

Bayan Inna Mairo da Najma sun idar da sallar isha'i da suka jira aka yi, sai suka fito zuwa falon zuciyar Najma cike da jin haushin yadda zasu kwana basu da ko kayan canji, tunda bada shirin kwana suka zo ba bare har a riƙesu ace sun taho kenan. Gwaggo bata fito daga ɗakinta ba sai wajen takwas da rabi, suka haɗu suka ci abin dare tare da su Inna Mairo.Abinci kala biyu na sashin Gwaggo da Tabawa ce mai yin girkin, sai kuma wanda Momy Hajiya Zainaba ta aiko daga part ɗinta don karrama su Inna Mairon. Sun ci sun yi ƙat! Tare da yin godiya ga Allah, don ba ƙaramin sakin jiki Inna Mairo tayi ta kwashi farfesun kazar da aka yiwa wani irin haɗi na musamman.Najma ma da yake mai son naman kaza ce, ta ci abin ta sosai bata ƙwari kanta ba, sabida Gwaggo basu waje tayi bayan ta ci abu ba mai yawa ba don abinci kaɗan take iya ci ita.

Hira sosai suka dasa tsakanin Gwaggo da Inna Mairo. Gaba ɗaya Inna Mairo sai take ganin komi kamar almara, don abu ne bata tayi sabo dashi ba tun ƙuruciya har girma, a ce wai Gwaggo ta zauna cikin raha da sakin fuska tana hira da ita,wannan abu ne da bai taɓa faruwa ba. Suna tsaka da hiran nasu suka jiyo sallamar Nasreen da Momyn ta, Gwaggo ta amsa sallamar tana basu izinin shigowa. Nasreen ce a gaba hannunta riƙe da wani babban bag, sai Momy na biye da ita hannunta ita ma ɗauke da wani ƙaramin paper bag.Suka samu waje suna gaida Gwaggo tare da sake gaisawa da Inna Mairo cikin fara'a. Najma ta sake gaida Momynsu Nasreen tana duban ɓangaren da Nasreen ɗin ta zauna tana sakin mata murmushi. Momy ta amsa da kulawa idanunta akan Najma take tsokanarta da faɗin, "Mai kuka har kin share hawayen? Banda abinki Najma nan ma ai gida ne." Gwaggo tayi karaf ta ce, "Kema dai kya faɗi Zainab, ni gani nayi sam bata farin ciki da zancen dawowarsu nan ɗin." Najma tayi saurin duban Gwaggo tana mai ɗauke ido daga gareta ta mayar kan Inna Mairo, wacce ta zubawa Najma idanu tana jifanta da harara. Najma ita kaɗai ta ankare da irin hararar da Inna Mairo ke jifanta dashi,don haka sai tayi saurin maida dubanta ga Gwaggo tana faɗin, "Ba haka bane Gwaggo,ina tunanin ƴan uwana su Hanne ne, domin zasu ji babu daɗi idan aka ce zamu dawo nan ɗin." Gwaggo ta saki murmushi mai faɗi tana faɗin, "Karki damu zasu saba da rashinku kamar yadda kuma zaku saba, sannan zaku dinga zuwa kai musu ziyara ba wai za a rabaku da zuwa inda suke bane kin ji ko?" Najma ta gyaɗa kai cike da gamsuwa tana faɗin, "To Gwaggo mun gode!" Momy Hajiya Zainab kallon Najma kawai take yi tana jin ƙaunarta har cikin zuciyarta. Komi na Najmar birgeta yake yi, musamman nutsuwar da take gani tattare da ita.Nasreen da ke kallon Najma ita ma murmushi tayi tana faɗin, "Ai Gwaggo ni rarrashi ma nake mata ɗazu amma ko kallo ban ishe ta ba." Nasreen tayi maganar da wani irin salo na shagwaɓa, hakan yasa Najma zuba mata ido tana mamakin taɓararta ta ce, "Kiyi haƙuri gaba ɗaya hankalina ne ya tashi a ɗazu ɗin." Nasreen ta watsa hannuwa tana faɗin, "Alright! Sis ya wuce, but ni dai i like u, kuma ina so ki sake jiki damu mu zama tamkar twins ko Momy?" Momy ta saki murmushi mai faɗi tana faɗin, "Gaskiya kam da kun gama birgeni idan kuka haɗe kanku daughters ɗina." Tayi maganar da tsantsar nuna ƙaunarta ga Najma da ƴarta Nasreen. Gwaggo da Inna Mairo suka haɗa ido suka saki murmushi, kowanne cikinsu na sake jin ƙaunar Hajiya Zainab na sake yawa a zuciyoyinsu.

Hajiya Zainab ta tura bag ɗin dake gabanta wajen Inna Mairo tana faɗin, "Innar Najma ga kayanan kala 2 mun siyo, kafin zuwa gobe ayi fita na musamman don samo muku kayan sawa da sauran abin buƙatu." Inna Mairo ta janyo bag ɗin tana nunawa Gwaggo ta ke cewa, "An gode da ɗawainiya Momyn Nasreen." Nasreen ma bag ɗin da ta shigo dashi ta miƙawa Najma tana faɗin, "Sister ga naki kema kafin mu fita shopping gobe." Najma ta amsa tayi godiya mai yawa tana mai nuna wa Gwaggo ta ce ta taya ta godia.Gwaggon kaduna ta dubi Momy ta ce, "An gode ƙwarai Zainabu, Allah dai ya saka miki da aljanna.Irin yadda ki ke hidimta wa ahalin Kabeeru da zuciya ɗaya, Allah ne kaɗai zai biya ki.Allah ya yi miki albarka na gode ƙwarai." Momy tayi ƙasa da kai tana cewa, "Bakomi Gwaggo ai an riga an zama ɗaya, Allah dai ya bamu ikon cigaba da yi muku biyayya." Inna mairo tayi saurin amsawa da cewa, "Ameen." Najma ta miƙe ta nufi ɗakin da aka saukesu da bag ɗin kayan,zuciyarta na cika da jin daɗin yadda Nasreen da Momy ke nuna musu kulawa. Koda ta buɗe bag ɗin kayan bacci ne ta gani kala biyu, sai wasu haɗaɗɗun ready made boubous na material masu shegen kyau suma kala biyu. Akwai undies da bra ma kala biyu,sai perfumes masu sanyi da daɗin ƙamshi guda uku. Abu na ƙarshe da ta ciro sune kayan wanka da su brush da toopaste masu kyau. Ta dinga jinjinawa Nasreen a ranta tana mamakin yadda tayi ƙarfin halin zaɓo mata har da bra, alhali gani ɗaya tayi mata a yau ɗin. Ta ɗago bra ɗin tana juyasu a hannu, tana kuma kisima cewa tabbas zasu yi mata daidai. Toilet ta shiga ta cire kayan jikinta ta gwada bra ɗin,sai gashi ya yi mata daidai har yaso ma ya ɗan matseta kaɗan.Amma ta san da zaran an wanke sau ɗaya zai iya ɗan saki,yadda zai mata normal ba takura. Rigar baccin da ta shiga dashi kalan milk ta sanya, ya yi mata kyau matuƙa tsayin rigar ya tsaya iya guiwarta ne. Ƙirjinta da babu bra ya fito sosai, hakan ya sanya tana futowa ta ɗauki hijab ɗin da tayi sallah ta zura. Falon ta sake fita daidai lokacin da su Momy suka miƙe suna wa Gwaggo sai da safe, ta ƙarisa tana duban Nasreen ta ga irin yadda take dubanta daga sama har ƙasa.Ta saki murmushi lokacin da Nasreen ta ƙariso wajenta tana yin ƙasa da murya ta ce, "Sis kin gwada bra ɗin?" Najma kunya ya rufeta ,ta ɗan lumshe manyan idanunta tana gyaɗa ta ce, "Sunyi Sis, na gode." Nasreen ta saki smile ta ce, "Thank god! Sai tomorrow zamu fita ki darji kaya masu kyau sosai, don so nake wannan black beauty skin ɗin naki su sama product masu kyau na body wash dana shafa,ta yadda fatarki zata yi sulɓi black skin ɗin ya fiddo da asalin kalarsa."Najma ta saki murmushi ba tare da ta ce komi ba.Momy ta tayi gaba tana faɗin, "Najma gud night, ko zaki taho mu je ki kwana tare da Sis ɗin naki?" Najma tayi saurin girgiza kai alamun a'a, hakan ya sanya Nasreen tsuke fuska tana magana cike da narkewa take faɗin, "Please! Muje Najma." Inna Mairo da idanunta ke kan Najma sai tayi mata alama da ido akan ta bisu ɗin. Sai Najma ta sakarwa Nasreen murmushi tana cewa, "To muje, amma da yin safe xan dawo wajen Innata." Duka suka saki dariyar yadda Najma tayi maganar cikin ƴar shagwaɓa.Nasreen ta ja hannun Najma suka fice bayan sun yiwa su Gwaggo sai da safe.Momy ta rigasu yin gaba zuwa part ɗin nasu,su Najma suna tafe tafiya ne a hankali Nasreen na mata hira har suka isa cikin haɗaɗɗan part ɗin nasu. Lokacin da suka dangana ga ɗakin baccin Nasreen ɗin, sake baki Najma tayi tana kallon tsaruwar ɗakin.Komi na ciki white ne babu surkin kowani kala, don ita white is her favourite colour. Komi a tsare yake a ɗakin,banda sassanyan ƙamshi da sanyin air condition babu abin ke tashi a ɗakin.Ta samu saman sofa ta zauna, idanunta akan Nasreen da ke amsa call ɗin da ya shigo mata. Najma sai ta ɗauke kai daga dubanta ta mayar kan ƙarewa ɗakin kallo, zuciyarta na sake yaba kyawun komi na cikinsa. Daga yanayin yadda Nasreen ɗin ke wayar ta gane cewa da ƙanwarta Nabeelah ce, don ta ambaci sunanta sannan ta ji tana sanar da ita zuwansu har da koɗawa Nabeelah kyawunta. Ta sauke wayar a kunni tana blushing ta dubi Najma ta ce, "Nabeey na gaidaki, gobe ko jibi zata dawo.Ta je gidan wata friend ɗin Momy ne, age mate ɗinta tayi birthday yau." Najma ta jinjina kai tana faɗin, "Ina amsawa." Nasreen ta sake sakin mata murmushi ta ce, "Ki cire hijab ɗin mana Sis, kamar wata matar liman." Najma ta yi murmushi tana jin nauyin yadda za ta cire hijab ɗin Nasreen ta ga yadda rigar ta fiddo asirin cikar ƙirjinta da ƙasanta. Gane hakan da Nasreen tayi ne ya sanya ta faɗin, "Ni dai ai ƴar uwarki ce, kuma tare zamu rayu in ma baki cire yau na ganki da rigar bacci ba, watarana ma a gabana zaki sanya.So gara kawai ki fara yin komi kai tsaye,ke naga alama kunya tayi miki yawa Najma." Najma ta ɗan saki dariya tana kai hannu ta zare hijab ɗin jikinta. Nasreen ta kafeta da ido tana sake gano asalin kyawun da Allah ya yiwa Najma.Duk da kasancewarta baƙa sosai, Allah ya yi mata baiwar kyawu mai fisgar hankali da cikar halitta. Ta sauke numfashi a hankali tana faɗin, "Sis u are very black beautiful! Gaskiya na jima banga baƙar fatar da ta birgeni irinki ba. Najma tayi ƴar dariya tana ma rasa abin faɗi,don ba yau ne ta saba jin ana koɗa kyawunta ba duk da kasancewarta baƙace sosai. A karon farko Najma ta samu kanta da kwanciya akan gado da shinfiɗa na alfarma, wanda laushin katifar kawai aka bar bawa dashi ni'imace. Tunda tayi juyin farko bata kuma ba sai da kiran sallar asuba ya shiga cikin kumnuwarta.Don sosai ake jin kiran sallar da ake kwaɗashi daga cikin masallacin gidan Alhaji Kabeer Dukku dake daga waje. Ta tashi zaune tana mai karanto addu'ar tashi daga bacci, ta sauka daga gadon ta nufi tsararren toilet Nasreen da ya gaji da haɗuwa.Alwala ta ɗauro ta fito sannan ta tada Nasreen ɗin ita ma.Sai dai tana buɗe ta ɗaura akan Najma sai ta sake gyara kwanciya tana faɗin, "Ina period Sis,yi naki sallar ki dawo mu cigaba da bacci." Najma ta jinjina kai tana faɗin, "Ok to!" Daga haka ta nufi wajen sallar da aka saita shi ya kalli gabas, ta ɗauki hijab akan sofa ta saka ta tada sallar.

Sai da ta gama yin azkar ɗinta gaba ɗaya sannan ta koma gado don sake kwanciya,amma abinka da rashin sabo duk yadda taso bacci ya sake ɗaukanta abin ya gagara. Ta riga ta saba aikin bauta a giwa, sam bata san wani zancen a koma baccin safe bayan anyi sallah ba. Haka ta dinga juyi tana tuno giwa da ayyukan da take gabatarwa a lokuta irin wannan. Wani abu ya tokare ƙirjinta, tana ji kamar ta buɗe ido ta ganta tana suyan ƙosanta ana mata layi ana saye. Wajen ƙarfe bakwai da rabi ta sakko daga kan gadon, don ta san babu wani bacci da zai ɗauketa don bata saba da hakan ba. Falo ta fito ta zauna tayi shiru tana faman tunanin mai zata yi ne? Ta miƙe tsaye tana nufan hanyar da taga mai aikin Momy jiya ta fito daga wajen, ta cigaba da takawa har ta shige cikin corridor ɗin. Daga can ciki ta fara jin karakainan masu aikin, sai ta kutsa kai ciki bakinta ɗauke da sallama. Rabi da Laure masu aikin Momy suka amsa sallamar suna duban Najma cike da mamaki.Ta samu waje tayi tsaye tana gaida su,don Rabi dattijiyace Laure ce kawai matashiya da bazata gaza shekaru ashirin da biyar zuwa da shida ba.
Tambayarsu Najma tayi akan ko akwai aikin da zata iya kama musu? Rabi ta dubeta da kulawa tana faɗin, "Baiwar Allah da dai kin koma kin yi kwanciyarki kada Hajiya ta tuhumemu da sanya ki aiki." Najma tayi saurin girgiza kai tana sanar dasu cewa, kwanciyarce ba za ta iya ba don bata saba da ita ba, gara dai su bata wani abin ta kama musu matuƙar hakan ba laifi bane. Ganin ta dage sai Rabi ta bata ƙullun ƙosai da

Please Login or Register in order to submit comment