Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta sake dakatawa tana haɗiye wani abu mai nauyi da ya danne zuciyarta, sakamakon tuno ranar da ba za ta taɓa mantawa dashi a tarihin rayuwarta ba. Ranar da ya zame mata mabuɗin buɗe sabon shafin rayuwa mai cike da jin daɗi da tsantsar ƙauna da kulawar da ta samu daga Malam Mahmuda. Najma ta dubi Inna Mairo tana son jin ƙarishen labarin cike da zaƙuwa, hakan yasa Inna Mairo cigaba da faɗin, "Rayuwar aurena a gidan mahaifinki rayuwace da bazan taɓa mantawa dashi ba, domin na samu ƙauna da tarairaya daga garesa. Malam Mahmuda ya riƙeni da amana ya kuma nuna mini soyayya da kulawa.Ya gatantani shi da ahalinsa su Malam da Inna Hanne, haka ma Gwaggo Salamatu ba ƙaramin soyayya da ƙauna ta nuna mini ba.Suka zame mini tamkar ƴan uwa na jini.Cikin wata ɗaya da yin aurenmu na yi wani irin kyawu da cikar ɗaki, duk wanda ya dubeni yasan cewa ina cikin kwanciyar hankali da samun soyayyar miji. Bani da wata damuwa kullum sai na kira Abbah mun jima muna waya, haka shi ma yana kirana da kansa musha hira, daga ƙarshe ya yi ta mini nasiha akan muhimmancin haƙuri da biyayya wa miji a zamantakewar aure.Koda yaushe bana rasa Yara ƴan tayin hira masu shigo mini, hakama matar Haruna aminin Malam Mahmuda mai suna Karima. Koda yaushe tana zuwa mini hira mu jima tare,sannan kusan duk dare mu kan je gidan Malam muyi hiranmu sai wajen tara na dare mu dawo gidanmu. Malam Mahmuda tuni ya koma yana zuwa kaduna wajen sana'ar ɗinkinsa da sai da yadikan maza da ya fara yi, yana kuma samun ciniki da alkhairy mai yawa. yana dawowa garin giwa duk bayan kwanaki uku zuwa huɗu, ya yi mini kwana uku da ya juya kaduna. Kausar da ke matsayin ƴar ƙanwar Inna Hanne ita ke zuwa tana tayani kwana idan ya tafi, tana da hankali da kirki matuƙa. Duk aikin shara da mopping ita ke yi mini.Da zaran ta kammala take komawa wajen Inna Hanne tunda a hannunta take,sabida ita bata haihu ba shiyasa ta ɗakko riƙon Kausar ɗin.Anyi bikinmu da watanni biyu matar Yaya Kabeeru ta haihu, cike da zumuɗi na shirya muka tafi kaduna da Malam tunda dama an faɗi haihuwar daidai yana garin giwa.Da murnata da komi na shiga gida ina ɗokin son ganin Gwaggo da Abbah, amma tun a irin tarban dana samu daga Gwaggo cikin haɗe fuska da tsare gida jikina ya yi mugun sanyi. A tunanina zuwa yanzu Gwaggo ta gane cewa komi NUFIN ALLAH ne, Allah ne bai nufa Fahad shi ne mijina ba. Na gaisheta ta amsa a wulaƙance tana faman bina da kallon ƙirulla, zuciyarta cike da jin haushin yadda ta ga nayi shar abina. Bata ga makusa a tattare dani ba,domin komin hasadar mutum idan ya dubeni ya san nayi kyawu, irin kyawun da ana gani ansan mutum na cikin kwanciyar hankali da hutu ne. Koda Malam Mahmuda ya shigo gaidata bata amsa gaisuwarsa ba, sai ma tsaki da ta ja ta bar mana falon tana yada mana da ƙananun habaici. Abin ya yi matuƙar taɓa zuciyata amma na danne ban nuna a gaban Malam Mahmuda ba, shi ne ma ya dinga bani baki da nuna mini cewa inyi haƙuri watarana sai labari. Lokaci zai zo da Gwaggo zata yi nadamar duk irin ƙiyayyar da take gwada mana, domin bamu da wani abu da muka aikata mata na rashin biyayya. Mun samu tarba ta mutunci a gidan Yaya Kabeeru daga wajen Anty Zee da ƴan uwanta da suka zo barka. Ta dinga nuna masu ni tana sanar dasu cewa ni ɗin ƙanwar Kabeer ne, suka dinga yaba kyawuna wasu suce muna kama da shi yayinda wasu ke cewa nafi shi kyau nesa ba kusa ba. Sosai na ji daɗin karamcin da muka samu, na sake jin ƙaunarta ya shiga zuciyata. Bamu kwana ba a ranar muka juyo garin giwa, bayan mun bi Abbah har shago mun yi masa barka. Koda ranar suna ya zagayo ban je ba sabida nasan babu abinda zan tsinto sai danasani, don na san Gwaggo cin mutuncina zasu taru suyi ita da ahalinta. Malam ne ya yi siyayyar kayan suna ya haɗa da kuɗi ya kai wa Gwaggo, kayan yace in jini kuɗin kuma nasa. Amma Gwaggo sai ta rufe ido ta ce ba zata amsa komi ba don ba muyi arziƙin da zamu iya yi mata alkhairy ta amsa ba. Wannan abu ya sosa zuciyar Malam matuƙa da gaske, maimakon ya dawo da kayan gareni sai ya nufi gidan Yaya Kabeeru dashi.Ya sanya Mai gadi gadi ya yi masa kiran mai jegon ya bata kayan da kuɗin. Anty Zee ta amsa da murna tana godia, hakan sai ya faranta ran Malam ya wanke masa ɓacin ran da Gwaggo ta kimsa masa. Lokacin da yake bani labarin cin mutuncin da Gwaggo tayi masa, kuka na dinga yi ina sake jin tsoron irin ƙiyayyar da take gwada mana na sake ruɗa zuciyata. Ya dinga bani baki har sai da ya yi nadamar sanar dani abinda ya faru, sabida yadda ya ga na tada hankalina matuƙa. Ban sake tunanin in sake binsa kaduna ba tunda ko na je ba tarban arziƙi zan samu daga Gwaggo ba, sai kawai na rungumi su Inna Hanne da su Karima matar Haruna suka zame mini abokanan arziƙi masu ɗebe mini kewar rashin ƴan uwa na jiki da bani dashi. Abbah ya turo mini lambobin su Yaya Kabeeru ya ce lallai in dinga kiransu lokaci zuwa lokaci ina sadar da zumunci dasu,kada na yadda na ce zan riƙe ƙiyayyar da Gwaggo ke mini a zuciyata har na kasa yin zumumci da ƴan uwana.

Kamar wasa watanni suka miƙa har akai ga shakera da yin aurenmu.Zuwa lokacin ne kuma bikin Yaya Aliyu ya gabato.A lokacin kuma ina tsaka da laulayin ciki mai wahala, hakan yasa ban samu zuwa ba sai Malam ne ya je ɗaura aure har Jos. Ya dawo yana bani labarin irin shagalin da aka yi, domin Yaya Ali akwai son ya ga Ya yi abinda zai birge mutane. Kano aka kai Amarya mai suna Safiyyah, don ya ce ba zai zauna a kaduna ba,zai dai dinga zuwa gaida su Gwaggo ya koma.A waya na kirashi na yi masa fatan alkhairy ya yi mini godia, bayan hakan na kira gwaggo ita ma nayi mata Allah sanya alkhairy tare da sanar da ita uzurina na rashin zuwa bikin da ban samu yi ba. Buɗan bakinta sai cewa tayi ai garama da banzo ba,tunda ko dani ko bani babu abinda za a fasa.Naji ciwon wannan maganar ƙwarai da gaske, don har kuka nayi ina jin tausayin kaina na sake kamani. Ko Malam ban faɗi masa yadda muka yi ba, nayi shiru da bakina tare da haɗiye baƙin cikina. Na cigaba da rainon cikin jikina cikin nuna juriya. Malam ba ƙaramin kula dani da tattalina yake yi ba, duk abinda nake so shi yake mini. Babu abinda na nema na rasa, kayan daɗi kuwa ko wata ƴar birnin sai mai auren mai hali kuma mai zuciya zata sameshi. Na sake fari da cika bayan laulayin ya tsaya mini, sai dai bana iya girki don sam bana son ƙamshin abincin dana girka. Inna Hanne ita ke zubo mini abinci tare da dafo mini abubuwan marmari da mai ciki bata rabo da son cinsa.Idan Malam zai dawo ita ke masa girki na musamman,a haka cikina ya kai watanni bakwai.Na samu sauƙin lamura da yawa,tunda har ina iya girki inci.Da haihuwa ya gabato ranar wata laraba na haifo ɗana namiji kyakykyawa babu inda ya baro kamannina, sai dai kwanansa biyu ya koma wajen Mahaliccinsa. Har kuka sai da nayi domin Yaron ya shiga raina sosai, haka ma Malam ya nuna alhininsa mai yawa. Daga ƙarshe ya dinga rarrashina da yi mini nasiha akan inyi haƙuri Allah zai bani wani rabon. Gwaggo Salamatu matar Hakimi ita ce ta kula dani tamkar mahaifiyata, sabida Gwaggo ta shafewa idonta toka ta ce ba zata taɓa zuwa ƙauye ta kula dani ba. Abbah ya ji zafinta matuƙa akan yadda take nuna masa cewa ƙiyayyar da take mini sake gaba yake yi ma,a maimaikon ya ragu.Amma duk yadda ya nuna mata ɓacin ransa hakan bai sanya ta sakko ta amince ta zo ta kula dani ba. Barka ma bata zo ba sai da akai wajen sati biyu da haihuwar,sannan Abbah ya tasota suka zo suka duba lafiyata. Sun kusa yini a garin giwa, sun samu tarba na alfarma daga gidan Malam Lawal da gidan Hakimi. Bayan kwana biyar da zuwansu Abbah ya sake taso ƙeyar Yaya Kabeeru da Yaya Ali suka zo garin giwa, karon farko kuma da ƙafafunsu ya tako inda nake. Dukkaninsu sun sake zama magidanta waɗanda hutu da jin daɗi ya fara zama musu, musamman Yaya Kabeeru da aka ce samunsa na sake bunƙasa don baya ga aikinsa yana taɓa harkar business sosai. Sun yi mini alkhairy sun bani kuɗi mai yawa suka ce na siyi abinda nake so.Na amsa nayi godia ina mai jin tsananin farin ciki, ina ji tamkar karsu tafi sabida yadda Abbah ya sanyamu a tsakiya muna hira cikin raha da nishaɗi. Na rakasu har wajen mota da zasu tafi ina hawayen da ban san kona minene ba, Abbah ya dinga rarrashina suka shiga mota suka tafi ina ɗaga musu hannu. Bayan na kammala wanka da sati biyu na haɗa kaya na Malam ya ɗaukeni sai kaduna.Kamar yadda Gwaggo ta saba tarbata babu raha bare murnar ganina haka ta tarbeni,hakan yasa jikina ya yi sanyi, naji cewa ba zan iya yin kwanakin da nayi niyya ba.Kwanana uku kacal nayi na samu Abbah nayi masa sallama, Malam yazo muka koma gida giwa cikin sabuwar motarsa 206 da ya siya.Don zuwa lokacin sosai shi ma samunsa ke bunƙasa, ga noma da yake yi mai yawa yana samun alkhairi. Tun daga wannan haihuwar da nayi ban sake samun ciki ba sai dana share shekaru biyar, na sake samun wani cikin amma watanninsa biyu nayi ɓarinsa. A ranar da nayi ɓarin cikin dare Allah ya ɗauki rayuwar Hakimi Alhaji Musa giwa. Mutuwar ta gigita dukkanin jama'ar giwa,domin kowa ya shaidesa mutumin kirki ne mai son jama'arsa. Bayan an share zaman makoki aka naɗa aminin mahaifinki Haruna a matsayin sabon Hakimi. Na tausayawa Gwaggo Salamatu, domin tayi rashin miji mai ƙaunarta, wanda suka rayu tsayin shekaru ba tare da ya yi mata kishiya ba har ya kwanta dama. Rasuwar Hakimi da watanni uku Abbah shi ma ya kwanta jinya, cutar hanta ta kamasa wanda ba a taɓa sanin yana da ita ba sai da cutar taci ƙarfinsa. Hankalinmu ya tashi matuƙa musamman ni da tsoron karna rasa shi ya shigeni.Da kukana muka isa kaduna muma dangana da asibitin kuɗi mai kyau da aka kwantar dashi.Muna shiga naga jikin da sauƙi sai sanya hankalina ya kwanta, amma da ya buɗe yana mini magana sai hankalina ya kuma tashi. Sabida dukkanin kalamansa sun yi kama da wasiyyace a fakaice, ya dinga mini nasiha akan muhimmancin zumunta da sadarda dashi a tsakanin ƴan uwa da makusanta. Yana mai nusar dani cewa ko bayan bashi a raye, karna yarda na yanke zumunta da ƴan uwana.In cigaba da bibiyarsu a matsayina na ƙaramarsu, karna taɓa damuwa da ƙiayyar da Gwaggo ke nuna mini. Na dinga kuka ina sanar dashi zan bi dukkanin nasihunsa amma ya daina ambaton ko bayan bashi, yana raye zan yi dukkanin abinda yake mini nasiha da aikatawa. A haka muka kamo hanyar komawa giwa ina kuka sosai Malam na rarrashina da bani baki. A she bayan barowarmu su Yaya Kabeeru na zuwa ya tasa su a gaba yana musu nasu nasihan akan su riƙe zumunci, su kuma riƙeni da amana, su maye mini gurbinsa domin bani da wani gata da ya wuce su da mijina. Hatta Gwaggo ya yi mata nasiha mai shiga jiki, ya kuma sanar da ita cewa ko bayan ransa bai amince ta raba zumuncin da ke tsakanina da ƴan uwana ba. Tun dana dawo garin giwa hankalina ya gaza kwanciya, sai in kira Abbah sau uku ina jin lafiyarsa. Duk sanda zan kira zan ji muryarsa garas kamar mai lafiya, sai hakan ya fara kwantar da hankalina ina jin daɗin cewa yana samun lafiya. Bayan kwana uku da zuwanmu muka sake komawa dubashi har dasu Inna da amininsa Malam Lawal.Mun ji daɗin ganin yadda ya samu sauƙi sosai, har suka dinga hira da amininsa cikin raha. Bamu kwana ba a ranar muka juya, a kuma ranar aka bashi sallama daga asibiti suka koma gida. Kwanansa biyu a gida ya rasu, rasuwar da ya gigita duniyata ya jefa rayuwata cikin ƙunci mai yawa. Wanda ba don na samu gwarzon miji mai ƙaunata da dukkanin zuciyarsa kamar mahaifinki ba,da tabbas sai zuciyata ta kamu da ciwo tun a wancan lokacin. Shi ya tsaya tsayin daka wajen ganin na rungumi ƙaddara na kuma fauwalawa Allah komi.Ya dinga yi mini rubutu ina sha don samun nutsuwar zuciya da dangana.A haka rayuwa ya dinga turawa har Abbah ya kwashi watanni da rasuwa, aka raba mana gadonsa aka damƙa komi na kasona a hannun mijina kamar yadda na buƙata. Sai da tafiya ta fara nisa na sake gane cewa tabbas na zama cikakkiyar marainiya mara gata, sai dai gatan miji kawai wanda Allah ya taimakeni ya sanya shi ya zame mini mijin marainiya. Gwaggo mutuwar Abbah bai sanya ya zame mata aya ko darasin da zata aje duk wata ƙiyayyar da take nuna ni da mahaifinki ba, sai ma abun ya ƙaru ta yadda ta fito fili ta nuna ko inda take bata so ina zuwa. Sannan suma ƴan uwana su Yaya Kabeeru daidai da rana guda basu taɓa kirana su ji lafiyata ba, bare har na saka rai zasu rungumeni su maye mini gurbin Abbah. Ni ce ke kiransu duk friday mu gaisa,shi ma wani lokacin ba a ɗaukar wayar musamman Yaya Ali yafi yin wannan wulaƙancin. A cikin hakan na sake samun ciki mai wahala, da dinga fama har cikin ya yi ƙwari. Watan haihuwa ya tsaya na haifoki ranar wata asabar da safe a asibitin zaɓawa. Kwana ɗaya aka sallamemu muka dawo gida,ƴan barka duk wanda ya shigo sai ya yi santin kyawunki da faɗin cewa babu inda kika baro ni. Gwaggo Salamatu da Inna Hanne su ne dai tsaye a kaina, suke kula damu suna bamu kyakykyawar kulawa. Gwaggo a waya ta kira tayi mini barka, ta kuma sanya su Yaya Kabeeru suma suka kirani.Yaya Kabeeru ya buƙaci na tura masa lambar asusun ajiyata ya saka mini naira dubu ɗari. Na kira nayi masa godia ina mai yaba masa a zuciyata, domin yafi mini Yaya Ali mutunci sosai.Kwanaki sukai ta ƙarewa Gwaggo bata tako ƙafarta ta zo dubamu ba, sai ana gobe zamuyi arba'in sai gashi drivernta ya kawota cikin sabuwar motarta da Yaya Kabeeru ya siya mata. Bata ɗauki lokaci ba ta ce zasu juya bayan ta aje mini turmin atamfa da dubu goma.Na yi godia tare da yi mata rakiya har waje na ga motar,na yi mata fatan alkhairy da addu'ar Allah ya tsare.A lokacin ne kuma take sanar mini cewa Yaya Kabeeru ya sayi wani gida zasu tashi a gidan hayan da suke su koma koma unguwar rimi. Nan ma fatan alkhairy na yi masa ina jin daɗin cigaban da yake samu har cikin zuciyata, sannan na dinga masa addu'ar Allah ya ƙaro masa buɗi ya raya masa ƴaƴayensa uku da aka haifa masa Adnan da Jiddah, sai ƙaramar da take sa'ar haihuwarkice mai suna Hameedah.Yara ƴan gaban goshin Gwaggon Kaduna kenan,waɗanda da sam bata son abinda zai taɓa su.Musamman Adnan da Gwaggo ke wa wani irin so na fitar hankali.Kusan ma ta ƙwatosa daga hannun uwarsa ne ta maido shi wajenta tana sakaltashi da goyon Kaka. Kina da shekaru bakwai Malam Lawal ya rasu sakamakon haɗarin mota da ya samu akan hanyarsa ta zuwa Daura.Mutuwar ta gigitamu musamman Malam da bashi da sauran gata da iyaye shi ma. Malam Lawal ɗin shi kaɗai ne gatansa kuma uba da yake gani yaji sanyi a rayuwarsa.Sai gashi ya goce mun zama cikakkun marayun da bamu wasu dangin da Zamu iya kamawa. Har gara ma ni ina da ƴan uwa, kawai dai babu shaƙuwa ne da ƙauna mai zurfi tsakanina dasu.Hakan kuma ba laifin kowa ne sai na Gwaggo,domin ita ce ta lalata komi ko ince take kan lalatawarma. Bayan rasuwar Malam Lawal da shekara guda Inna Hanne ta sake wani auren, ta bar garin giwa zuwa Yakawada,sabida ɗan Yakawadan ne mijin da ta aura. Hakan ya sake jefamu cikin maraici da alhini mai yawa. Lokaci ya cigaba da tafiya kina zuwa makarantarki tare da Yaran Hakimi, waɗanda kuke kai ɗaya dasu.Kinyi wayo ga kyawu tamkar ke kika yi kanki,kika zartani a kyawun halitta tun kina ƙaramarki. Sai ke ɗin kin biyo baƙin fatar Malam ne ziryan, wanda hakan bai ragi kyawunki da komi ba sai ma ƙarin kwarjini a gareki.Sannu a hankali buɗi sai ƙaruwar ma Mallam yake yi, har kuma lokacin bai aje sana'ar ɗinkinsa ba.Gadona shi yake juya mini zallar kuɗin, kadaran shanayena kuma yana kula dasu haɗe da dabbobinsa da yake kiwo. Sannu a hankali nima na fara tara kuɗi a asusun a jiyata. Sannu a hankali zama haka bana komi ya fara damuna, sai na fara tunanin ko makaranta zan koma? Amma dana tunkari Malam da maganar kai tsaye ya nuna bai amince ba. Na haƙura na fara kasuwancin sarin atamfofi da kayan Yara ina siyarwa, Allah kuma ya sanya wa sana'ar albarka. Idan zaki iya tuna kina da wayonki mun sha zuwa kaduna wajen Gwaggo ta wulaƙantamu, ko fuska bama gani bare har mu sanya ran zamu iya kwana a gidan. Haka zamu damu ina jin ciwo da damuwa mai tsanani a zuciyata.Zuwan da nayi lokacin da Yaya Kabeeru zasu tare a sabon gidansa, shi ne zuwan da Gwaggo tayi mini wulaƙancin da bani mantawa. Na je ɗaukar lemu cikin uban lemukan da aka jirge don rabawa baƙin da zasu taru a yi walima a gidan Innar, Inna ta tujarani a bainar jama'a.,har tana kirana da dangin mayu. Nayi kuka ranar kamar raina zai fita, na kuma yi murnar da Allah yasa ba dake naje ba na barki a gidan Hakimi ne wajen Inna Karima.Da aka je can gidan Yaya Kabeerun ma akan kunnuwana Gwaggo ke cewa da ƴan uwanta ita wallahi bata ƙaunar wannan naci da binbinin da nakewa ahalinta, domin sam ita ta kasa jin ƙaunata a ranta. Tafi sha'awar na nisanceta ita da ƴaƴanta, hakan kawai zai sanya ta manta dani bare har taji ƙiyayyata a zuciyarta. Jikina ya yi mugun sanyi da jin waɗannan kalaman, na samu wani lungu a gidan na zauna nayi kuka mai yawa ina tunawa da Abbah da tarin nasihunsa gareni akan karna yanke zumunci da ƴan uwana. sai gashi Gwaggo na faɗin waɗannan kalaman. Tun daga ranar na rayawa raina cewa dolene na nisanci zuwa inda suke, matuƙar ina so in tsira da mutunci idanun Gwaggo. Koda na dawo gida ban sanar da Babanki komi ba, naja bakina nayi shiru amma duk daren duniya saina tuna da kalaman Gwaggo na kuma zubda hawayen tausayin kaina. Kina da shekaru tara kika shiga aji uku a primary. A lokacin ne kuma in baki manta ba cutar ƙoda ta kama mahaifinki Malam Mahmuda,cutar da ta kayar dashi ta kuma lashe dukkanin arziƙin da muke dashi har sai da muka saida gidanmu mai ƙyau muka dawo wannan gidan ƙasar a lokacin da aka ce za a yi masa dashen ƙoda. Da ƙyar aka haɗa kuɗin bayan an siyar da dukkanin abinda muka mallaka ni da shi,hatta gadona tas sai da aka siyar da komi aka tattara kuɗin da ke asusun bankina aka haɗa dasu. Bayan anyi aikin ne kuma aka gano cewa hantarsa ita ma ta kamu da ciwo. Hankalin mu ni dasu Hakimi ya tashi,jinya ya da dawo sabo maimakon sauƙi sai abu ya sake taɓarɓarewa. A haka Ubangiji ya amsa kayansa a ranar wata juma'a da bazamu manta da ita ba.Duk wani mai ƙaunarmu ya tausaya mana akan wannan babban rashin da muka yi,musamman ke an tausaya miki matuƙa sanin cewa yana matuƙar ƙaunarki.Sannan kuma kinyi shaƙuwa da shi sosai,sabida irin yadda yake nuna miki gata.Bashi da burin da ya wuce ya kyautata rayuwarmu, amma sai mutuwa tayi mana yankar ƙauna, ta datse dukkanin farin cikin mu wanda har kawo yau bamu daina jin ɗaci da raɗaɗin mummunar rashin bango majinginin rayuwarmu da mukai ba......

Inna Mairo ta dakata da maganar tana kuka sosai. Najma ma kukan ta fashe dashi tana tuno irin shaƙuwarta da Babanta, da irin gatar da ya nuna mata.Ta dinga tuno lokacin rasuwarsa da irin mummunar yanayin da suka tsinci kansu a ciki. Wanda ba don Hakimi da Iyalansa da suka tsaya musu,suka zame musu garkuwa ba.Da tabbas baƙin ciki sai ya yi ajalin Inna Mairo.

Inna Mairo ta ja numfashi tana sauke ajiyar zuciya kafin ta ɗaura da faɗin, "tun bayan rasuwarsa rayuwarmu ke cikin garari, bamu da mataimaki sai Allah sai kuma Hakimi wanda ya haifu cikin uwa da uba. Don ba don shi da Iyalansa da suka rungumemu tamkar ƴan uwansu na jini ba, da yanzu muna yawon bara sabida rashin galihu. Gwaggo idan baki manta ba bata tako ƙafarta ta zo gaisuwa ba sai da Malam ya share kwanaki ashirin a ƙasa, sannan ta zo mini ta'aziyya har da ɗan buhun shinkafarta da taliya da kuɗi. Waɗannan kayan da ta kawo mini suka zameni baƙin kaya domin nafi buƙatar kulawarsu ita da Ƴan uwana.Nafi buƙatar su ƙaunaceni su nuna mini cewa ni ɗin jininsuce da basu da kamata, ba wai su dinga jifana da abin duniyar da zai ƙare ya barni da su ba. Su Yaya Kabeeru kuwa a waya kaɗai naci arziƙin da suka kira suka yi mini gaisuwa, shima sai bayan da Gwaggo ta koma da kusan kwana goma sannan ta sanar dasu. Nayi kuka mai yawa na kuma sake jin sun fita a zuciyata, ba don bana ƙaunarsu ba sai don yadda suke treating ɗina tamkar ƴar riƙon da bata da galihu a wajensu. Sai ya zamana ko waya na kira don in sadar da zumunci dasu,sai suka daina ɗauka sai sun ga dama.Na fassara hakan da cewa suna gudun kar na roƙi wani abu ne daga garesu, ko kuma na sanya ran zasu tallafeni ni da ke. Tun ina kira da biyiyar Gwaggo jefi-jefi ina zuwa gaidata, tana gwado mini kwanon shinkafa da su taliya. Har na gaji na daina na rungumi maraicina, na kuma bar wa Allah komi, domin ba zan iya jurewa irin ƙasƙancin da Gwaggo ke mini ba. Gidan Yaya Kabeeru da kanta ta cewa mai gadin gidan duk sanda na je kada a barni na shiga, tunda ta fahimci cewa matarsa mai kirkice kuma tana sona. Sai ta toshe kafar da zan samu shiga cikin gidan bare har Anty Zee ɗin ta dinga nema mini taimako wajen ɗan uwana.........✍🏻



🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻*
*MTN*
*GLO*
*AIRTEL*
*9MOBILE*
*MONTHLY VADILITY 💃🏻*


*DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻




#Lovestory#
#Najma AD#
#Aysha Ɗansabo lemu🥰
[2/28, 2:36 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻
_*Arewabooks@ayshadansabo*_

*Paid book:500*

*Chapter 6*

_Free page_


Ban sake zuwa kaduna ba koda wasa,ina dai kiran Gwaggo mu gaisa idan naci nasarar ta ɗaga kirana.Suma su Yaya Kabeeru ko basu ɗaga wayata ba sai na tura musu saƙon gaisuwata ta message. A haka rayuwa ta dinga gara mana cikin ƙunci da danuwa.Hakimi da Iyalansa sune tsaye a kanmu wajen tausaya mana da nuna mana ƙauna.Basu taɓa gajiyawa damu ba har kawo yau, sai dai ajizanci irin na ɗan adam da kan saɓa maka a wasu lokutan koda cikin rasani ne. Bayan kun kammala primary ke da su Lubah ne Hakimi ya

Please Login or Register in order to submit comment