Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ta dubi Najma tana bata tabbacin zata sanar da ita tarihin rayuwarta baki ɗaya, da yadda aka yi Malam Mahmuda ya yi nasarar aurenta, har ya ɗakkota daga birni ya kawota ƙauyen garin giwa. Ta muskuta tana gyara zamanta sosai, ta fuskanci Najma da tayi zuru tana sauraren jin cikakken tarihin rayuwar Inna Mairo da Mahaifinta Malam Mahmuda...........✍🏻


🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻*
*MTN*
*GLO*
*AIRTEL*
*9MOBILE*
*MONTHLY VADILITY 💃🏻*


*DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻




#Najma#
#Luvstory#
Ayshat Ɗansabo lemu😘
[2/28, 1:23 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!🤲🏻*
*Arewabooks@ayshadansabo*

*Paid book:500*

*Chapter 3*

_Free page_


*WAIWAYE...*

Inna Mairo ta dubi Najma da take sauraren jin ta bakinta, ta saki murmushi mai faɗi kafin ta fara da faɗin, "Kamar yadda kika sani Babanki Malam Mahmuda haifaffan nan garin giwa ne.Ya taso cikin maraicin rashin iyaye,don Ya rasa iyayensa tun yana ƙarami.Hakan yasa ya taso a hannun ƙanin Mahifinsa mai suna Malam Lawal, Malam Lawal Malamin addini ne mai karantar da almajirai karatun addini anan babban zauren dake gidansa.Kasancewarsa Malamin addini ya sanya Babanki ya samu ilimi mai zurfi na addini a wajensa.Musamman karatun qur'ani da yafi zurfi a cikinsa, har ya kai ga haddacesa tun yana da shekaru goma sha biyu a duniya. Malam Lawal bai taɓa haihuwa ba, hakan ya sanya ya rungumi Babanki tamkar shi ya haifesa. Ya bashi dukkanin gata da kulawa, sannan Ya sanya shi a makarantar boko sabida bai yadda da zama cikin jahilci ba. Tun daga kan matakin primary Malam Mahmuda bai tsaya da karatun boko ba har sai da Ya kai matakin diploma,inda Ya yi karantun diploma ɗin nasa a jami'ar Ahmadu Bello dake zaria. Ya karanci fannin Business ne, don shi yafi sha'awar Ya zama ɗan kasuwa ba ma'aikacin gwamnati ba.Bayan Ya kammala karatun diploma ɗinsa ne Ya tattaro Ya dawo gida giwa, Ya cigaba da sana'ar yin ɗinkinsa na maza da ya ƙware akai. Don tun yana matakin sakandiri yake koyan ɗinkin har Ya ƙware, Ya mallaki keken kansa Ya buɗe shago anan zauren gidan Malam ɗin Yana sana'arsa. Sosai kuma yake samun rufin asiri da ɗinkin, domin Ya yi ƙwarewar da har daga birni yake samun ɗinkuna. Bayan Ya dawo gida ya cigaba da sana'ar ɗinkinsa ne, sai kuma tunanin son zurfafa iliminsa a ɓangaren addini Ya shigesa. Ya samu Malam Lawal Ya sanar dashi buƙatarsa, shi kuma sai Ya ji daɗi tare da bashi goyan baya har Ya yi masa alƙawarin danƙashi wajen wani babban amininsa wanda yake shi ma babban Malami ne garin kaduna. Malam Mahmuda ya yi farin ciki mai yawa, daga ƙarshe suka rabu da Malam ɗin akan cewa zai yi magana da aminin nasa mai suna Malam Muhammad Kabeer Dukku.Kwanaki biyu bayan sunyi maganar Malam Lawal ya kira Babanki ya shaida masa cewa ya fara shiri, don kuwa Malam Muhammadu ya yi na'am yana kuma maraba dashi a matsayin sabon ɗalibinsa. Kamar da wasa maganar tafiyar Malam Mahmuda karatu ya tabbata, ya yi sallama da dukkanin abokanansa su Haruna ɗan gidan Hakimi, da sauran abokanansa da suka tashi tare. Ya kama hanyar ya bar garin giwa bisa jagorancin Malam Lawal da matarsa Hanne da suka yi masa rakiya, suka kaisa har rigasa gidan babban aminin Malam Lawal ɗin.....

Inna Mairo ta ɗan dakata tana duban yadda Najma ke saurarenta da dukkanin nutsuwarta, ta lumshe ido kaɗan tare da sake buɗesu akan Najma ta ce, "Kin san waye wannan Malamin da aka kai Babanki wajensa?" Najma tayi saurin girgiza kai alamun bata sani ba,hakan ya sanya Inna Mairo yin ƙaramin murmushi tana mai cigaba da faɗin, "Ba kowa bane sai mahaifina Malam Muhammad Kabeer Dukku. Shi ɗin ɗan asalin garin Dukku ne dake ƙaramar hukumar jihar Gombe. Bafulatani ne sosai domin uwa da ubansa duk fulani ne, neman karatun addini ne shi ma ya kawosa garin kaduna daga Dukku. Daga nan ne Ya ji daɗin zama har Ya fara sana'ar sai da zaruruwan ɗinki, yana kuma taya Malaminsa noma da kiwo. Sannu a hankali har Ya yi ƙarfi Ya buɗe ƙaramin shagon saida kayayyakin ɗinki a Kawo, gefe guda kuma yana kiwon kaji idan sun isa ci Ya fitar Ya sayar. Cikin hakan Ya haɗu da Gwaggo Hauwa,wacce take haifaffiyar ƴar cikin hayi rigasa ce. Bayan sunyi aure sai buɗi ya yi ta samuwar masa, samunsa na sake bunƙasa har ya kai Ya buɗe babban shago anan kawo. Shakerarsu biyu da aure aka haifi Yaya Kabeeru, bayan shekaru uku kuma aka sake haifo Yaya Ali. Daga nan sai haihuwar ta tsayawa Gwaggo, sai da ta share shekaru kusan takwas ta sake haifo ƴa mace. Sai dai ko kwana jaririyar bata yi ba ta bar gidan duniya, daga nan ne kuma Gwaggo bata sake haihuwa ba,har kawo yanzu da shekarun tsufa suka risketa.Abbah kamar yadda muke kiran mahaifinmu, Ya auro mahaifiyata ne bayan kusan shekaru talatin da aurensu da Gwaggo. A lokacin su Yaya Kabeeru har sun zama samari sun kammala deegree ɗinsu, don Abbah bai yi wasa ba wajen basu ilimin zamani dana addini. Hankalin Gwaggo ya tashi matuƙa da wannan ƙarin aure da Abbah Ya bijiro dashi.Ta dinga shuka tsiyataku kala da kala amma hakan bai sauya komi ba,don Abbah koda wasa bai ji cewa zai fasa auro Innata ba. wacce ya ganota a can Kaita mahaifarsa.Marainiyace da bata taso a hannun iyayenta ba duk sun rasu, ta taso ne a hannun wani ƙanin Babanta anan kusa da gidan Iyan Dukku, wato mahaifiyar Abbah kenan. Bafulatanace ita ma,uwa da ubanta duk fulani ne.Tausayin maraicin da take ciki da gallazawar da ake mata a gidan riƙonta, ya sanya mahaifiyar Abbah mai suna Iya bai wa Abbah ƙwarin guiwa akan Ya auri Innata mai suna Maryam. Ta kuma ƙara da kwaɗaitar dashi cewa watakila ya samu wani rabon,tunda haihuwa tuni ya ɗaukewa Gwaggo. Lokacin da aka yi bikin haukane kawai Gwaggo bata yi ba, sabida tsananin zafin kishi kamar yadda Iya ke bani labari. Malam bai aje Innata Mairo gida ɗaya da Gwaggo ba, sai ya kama mata haya a wata unguwa da ake cewa hayin banki. Wata ɗaya da auren Innata ta samu ciki, murna a wajen Abbah ba a cewa komi. Iya ma dake can Kaita da labari ya je mata murnar tayi sosai, tana taya shi addu'an Allah ya bashi ɗiya mace,don Iya na matuƙar son ƴaƴa mata domin ita Allah bai bata ba. Duka yaranta uku maza ne, Abbah kuma shi ne babba a cikinsu, sai ƙanninsa biyu Mansur da Salihu. Waɗanda suka rasu suna ƴan samari dasu, sun rasu ne sakamakon haɗarin mota da ya ritsa dasu akan hanyarsu ta komawa makarantar kwana da suke yi a bakori.Sai ya zamana Abbah shi kaɗai ya rage wa Iya, baya ga shi bata da kowa sai ƴaƴan ƴan uwa da take xagaye dasu.Abbah Ya yi juyin duniya ta dawo wajensa da xama taƙi, ba kuma komi ya sanya hakan ba sai rashin kirkin Gwaggo. Don ko kaɗan bata mutunta Iya da duk wasu dangin Malam,ƴan uwanta da ƴaƴanta kawai take gani da mutunci take kuma so. Gwaggo ji tayi kamar ta mutu don baƙin ciki, lokacin da maganar samun cikin Innata ya risketa.Ta sake ninka tsanarta da jin kishinta mai zafi a zuciyarta,duk da cewa ba gida ɗaya suke ba.Amma hakan bai taɓa sanyaya zuciyar Gwaggo ba,kullum cikin nuna kishi da ƙiyayyar da take wa Innata take. Tasha faɗi akan kunnuwar Abbah cewa ta tsani Innata, kuma ba zata taɓa son duk wani abu da zai fito daga tsatsonta ba. Malam ya yi nasihan ya yi faɗan ya yi rarrashin har ya gaji ya zuba mata ido, sai dai fatan shiriya da yake nema mata ba dare ba rana. Sabida a cewarsa zafin kishinta har ya yi yawa,dole a dinga roƙo mata sassauci a wajen Mahaliccinta. Da cikin Innata ya isa haihuwa ne Iya ta haɗo kayanta daga Dukku ta dawo kaduna, don Allah ya ɗaura mata son Innata tare da jin tausayin maraicinta. Daren ranar wata juma'a naƙuda ya kama Innata,kafin asuba an haifoni bayan Inna tasha matuƙar wahala.Ana murna ta sauka lafiya sai kuma jini ya ɓalle mata,kafin aje ga asibiti rai ya yi halinsa ta amsa kiran Ubangijinta.Faɗin irin tashin hankalin da Malam ya shiga bazai misaltu ba, hatta da samarin ƴaƴansa su Yaya Kabeeru mutuwar ya jijjigasu.Don duk irin ƙiyayyar da Gwaggo kewa Innata tana kuma cusa musu ra'ayin su ƙita,hakan bai yi tasiri a zuciyarsu ba sabida Innata bata taɓa yi musu koda kallon banza bane.Duk sanda zasu je wajen Malam idan yana gidanta,kyakykyawar tarba suke samu daga gareta.Take aka yi mini huɗuba da sunan mahaifiyata Maryam, bayan an kammala zaman makoki ne sai Iya ta tafi dani Dukku. Don ta ce bata amince a bai wa Gwaggo ko dangin uwata riƙona ba,tunda ita ma Innata marainiyace a cikin rashin gata ta rayu bare ace zasu iya riƙeni. Gwaggo kai tsaye dama ta ce ba za ta taɓa riƙon Ƴar kishiyar da kowa ya shaidi irin soyayyar da Abbah ya nuna mata,sabida ya aurota tana a ɗanya sharaf ɗinta. Iya ta tattara komi nawa muka wuce garin Dukku, na fara rayuwa a hannunta cikin tsananin gata da kulawa.Kusan koda yaushe Abbah na kan hanyar zuwa dubani,domin dukkanin soyayyar da yake wa Innata Mairamu sai ya koma kaina. Baya iya sati biyu bai je Dukku ya ga lafiyata ba, kuma baya zuwa hannu rabbana sai ya yi mana siyayya mai yawan gaske. Wannan sunturi da Yake yi a kaina da yadda ko a gaban Gwaggo ne Yake nuna tausayina da yake ji a cikin zuciyarsa, sai hakan ya haifar da ƙiyayyata a zuciyar Gwaggo. Ta juyar da dukkanin ƙiyayyar da take wa Inna zuwa kaina, bata taɓa yin kara tabi Abbah Dukku don ta dubani ba ko sau ɗaya.Wannan rashin karan da ƙiyayyar da take nuna mini akan idanun Iya idan munzo kaduna,sai ya sake haifar da rashin jituwa a tsakaninta da Iya. Sabida a lokacin duk wani mai son ganin ɓacin ran Iya to ya gwadamin rashin ƙauna, ko nuna min halin rashin kirki.Na taso da tsananin kyawu da shiga rai, sabida babu inda na baro kyawun Innata na asalin fulani. Jajir nake ga gashi har gadon baya, a haka na taso ina samun tattali da kulawa wajen Iya, wacce bata taɓa bari nayi kukan rashin uwa ba.Hasalima ita na taso na sani a matsayin Innata, sai dana fara girma nayi wayo har na shiga aji uku a primary, sannan Iya ta sanar dani cewa ita Kakata ce,Innata ta rasu tun ranar da ta haifeni. Sam banji komi a raina ba lokacin da take faɗa mini hakan, domin ni ita na taso na sani a matsayin uwata. Ban fara kukan rashin gata da rashin uwa da nayi tun ina tsummar goyo ba sai da Allah ya ɗauki ran Iya, a lokacin ina aji biyu na sakandiri. Nayi kuka kamar zan zautu sabida ita ce kaɗai gatana, da ita na rayu nayi sabon da bana iya ɓoye mata dukkanin abinda yake damuna. Ita kuma bata gajiyawa wajen yi min dukkanin abinda nake so matuƙar baifi ƙarfinta ba.Ban saba da Yayuna su Yaya Kabeeru ba, domin basa zuwa inda muke ni da Iya sai in wani abu ya faru, ko sallah tazo haka sai zo gaisheta.Sai kuma idan Abbah ya taso su a wasu lokutan, to shine zasu zo tare da shi. Amma baya ga gakan takanas dai su taka suje Dukku basa yi,musamman da ya zama sun kama aikin gwamnati a lokacin.Kuma dukansu ba a garin kaduna suke aikin ba, Yaya Kabeeru na NNRA Abuja ne.Wani abokin Abbah ne ɗan siyasa ya amshi takaddun Yaya Kabeerun Ya samo masa gurbin aiki wajen,wanda babban waje ne da ake biyan albashi mai tsoka matuƙa.Idan ba Ƴaƴan manya bama ba a cika bai wa wasu gurabin aiki a wajen ba, sai masu ƙafa da hanya kamar yadda ya kasance da Yaya Kabeerun. Shi kuma Yaya Ali ya samu aikinsa ne a gidan gwamnatin Kano, yana lallaɓawa da albashinsa yana kuma neman scholarship don yana da burin son fita waje ya yo masters deegree ɗinsa a can. Rasuwar Iya shi ya janyo mini dawowa hannun Gwaggo da zama,dawowar da ya zame mini tashin hankali da jefa rayuwata cikin ƙunci mai yawa.Domin Gwaggo ta amshi riƙona ne don babu yadda zata yi,sabida Abbah ya nuna bashi da wata mai riƙe masani, don haka dole in dawo ƙarƙashin kulawarsa tunda gata a raye matsayin matarsa. Tunda na dawo kaduna wajen Gwaggo ban taɓa ganin soyayyata a idanunta ko kan fuskarta ba, kullum na kalli idanunta tsanata nake hangowa a cikinsu. Abbah bai ɓata lokaci ba wajen nemo mini gurbin karatu a wata private secondary school, na cigaba da zuwa makaranta inda aka aje a JS3.Fara zuwa ta skull ɗin ne ya rage min ƙuncin da nake ji na xaman takura da bautar dani da Gwaggo ta fara yi, kuma da zaran na dawo daga boko ƙarfe huɗu zan shirya na wuce zuwa islamiya.Islamiyar a nan kusa damu ne bamu da nisa sosai,hakan yasa da ƙafa nake gangarawa na je.Bana shigowa gida sai ƙarfe shida na yamma,sai ya zama bani da wani lokacin kaina in ba alhamis da juma'a da bana zuwa islamiya ba. Shi ma kuma a ranakun Abbah ƙarfe huɗu yake baro shagonsa a Kawa,Ya dawo gida don karantar dani wasu littafan addinin. Duk wannan rashin lokacin da bani dashi, hakan bai hana Gwaggo nemo hanyar da zata cigaba da bautar dani ta ƙuntata mini ba.Sai ta koma tashina a bacci tun ƙarfe huɗu na asuba,a lokacin zan yi mata duk wasu ayyukan bautar gyaran ɗaki da wanke-wanken kayan da muka ci abincin dare. Ni zanyi abin karin safe kafin in tafi school, sabida tun a Kaita Iya ta horar dani ɗaura sanwa. Don ta sha ce mini Mairona iya girki shi ne martaba da adon mace, don haka ki dage wajen ganin kin iya sarrafa hatsi kar ki zama mai son jiki ta wannan fannin domin ke mace ce aure zaki yi. Hakan da Gwaggo ta gane ina da bai wa ta fannin iya girki,sai ya sanya ta sallami mai aikinta wacce dama Yaya Kabeeru ne ya ɗaukar mata ita, Ya ce lokaci ya yi da xata fara hutawa tunda sun kawo ƙarfi.Abbah bai san duk halin da nake ciki ba, don ta iya takunta a gaban idanunsa bata nuna min rashin ƙauna sosai. Sannan shi ba mazauni bane a kasuwa yake yini a shagonsa, sannan tun asubahin farko yake ficewa zaure don bai wa almajiransa karatu. Ba zai shigo gida ba sai anyi sallar asuba ya jasu jam'i, hakan ya sanya har in kammala dukkanin bautar da nake yi bai ma sani ba. Ina cikin wannan rayuwar aka kawo mahaifinki Malam Mahmuda Najma, na dawo daga makarantar boko na cidda mun yi baƙi ashe mahaifinki ne da ƙanin ubansa Malam Lawal da matarsa. Na gaidasu na wuce ɗakina da yake can ciki,bayan na sauya kayan jikina nayi shirin islamiya kamar yadda na saba yi.Na ci abincin rana da shi kaɗai Gwaggo keyi don dole tunda ina skull, na gabatar da sallar la'asar na ɗakko jakata na fito don tafiya islamiya. Anan na tadda baƙin da muka yi suma suna haramar tafiya, Abbah ya shigo har falo suna gaisawa da Inna Hanne. Na yi musu fatan sauka lafiya na fice don tafiya makaranta, a zaure naci karo da wani kyakykyawan matashin saurayi baƙi sosai dashi. Amma yana da kyawun fuska da suran jiki sosai,na wuce ina ayyanawa a zuciyata cewa tare suke da baƙin Abbah kenan. Bayan magriba mun kammala cin abincin dare tare da Abbah, wanda lokuta da yawa tare muke cin abincin dare dashi. Muna yi yana lallaɓani da yi min nasiha akan inyi haƙuri da rayuwa, da kuma duk halin da zan tsinci kaina a ciki. Ina matuƙar jin daɗin irin ƙauna da shaƙuwar dake tsakanina da Abbana, wanda hakan ne ke daƙile kaso mai yawa na jin zafin ƙiyayyar da Gwaggo ke mini, da kuma yadda sam babu shaƙuwa tsakanina dasu Yaya Kabeeru. Don ko sun zo gida tsakanina dasu gaisuwa ce kaɗai, baya ga haka basu taɓa jana a jikinsu sun nuna mini kulawa ko ƙauna ba.A matsayina na ƙanwarsu mace tilo da suke da ita, sam basu taɓa nuna min cewa suna maraba dani a matsayin ƙanwa garesu. Bayan mun gama cin abincin muka taɓa hira har aka kira sallar isha'i, Abbah Ya je sallar isha'i Ya dawo ne.Ya taramu ni da Gwaggo ya yi mana bayanin cewa ya samu baƙon ɗalibi da xai riƙa ɗaukar karatu a wajennsa, sai dai wannan ɗalibin yasha bambam da sauran ɗalibansa.Don shi wannan a matsayin ɗa yake a wajensa, sabida haka anan cikin gida za a riƙa zuba masa abinci sau uku a rana kamar yadda su Yaya Kabeeru zasu ci idan suna gari. Sannan yana da hurumin da zai iya shigowa ciki idan yana buƙatar wani abu ko don gaisawa da Gwaggo,Ya shaida mana cewa sam bai yi masa shamaki da hakan ba, matuƙar mu'amalar da zai yi a cikin gidan ba zai wuce tsakanin babban falo zuwa kicin ba. Muka yi shiru ni da Gwaggo muna sauraren jawabin Abbah, yayinda zuciyata ke hasaso mini cewa, ba kowa bane baƙon Abbah sai wannan black beauty ɗin matashin dana gani a zaure ɗazu. Gwaggo ta jinjina kai bayan ta gama jin jawabin Abbah, sannan ta buɗe baki ta ce, "Abbansu yanzu don kawai an kawo saurayi ɗan amininka shi ne har zaka bashi damar shigowa cikin gida ya yi mu'amala kamar yadda su Kabeeru zasu yi? Kana ƙoƙarin nuna cewa zaka daidaita matsayinsu kenan ko me?" Abbah ya dubi Gwaggo cikin nuna rashin jin daɗin maganar da tayi ya bata amsa kai tsaye da faɗin, "Hakane zan daidaita matsayinsu ne Hauwa, don inda kara ɗan da yake a matsayin ɗan aminina to nima yakamata na ɗaukesa matsayin ɗane.Don haka ki iya harshenki akan furta kalamai marasa kan gado akan Mahmuda, sannan zuwa da safe zan gabatar muku dashi..........✍🏻


🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻*
*MTN*
*GLO*
*AIRTEL*
*9MOBILE*
*MONTHLY VADILITY 💃🏻*


*DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻






#Lovestory#
#Naj....AD#
#Aysha Ɗansabo Lemu😘
[2/28, 2:19 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻
_*Arewabooks@ayshadansabo*_

*Paid book:500*


*Chapter 4*

_Free page_


Inna Mairo ta cigaba da cewa, "Washegari bayan mun gama karyawa da safe, Abbah ya gabatar mana da baƙonsa. Lokacin da baƙonsa ke gaida Gwaggo ido kawai ta zuba masa tana jifansa da wani mummunan kallo, wanda ni kaɗaine na kula da haka sabida shi da baƙonsa hankalinsu ba a kanta yake ba. Na gaida baƙon Abbah ya amsa da fara'a yana tambayata skull, na bashi amsa da cewa komi lafiya. Gwaggo ta fara barin falon zuciyarta na cika da jin haushin yadda ta kula baƙon Abbah ya shiga ransa farat ɗaya! Ni ma bayanta nabi don Abbah hira suka dasa sosai da baƙon nasa. Kwanaki biyu da zuwansa gidan na fahimci cewa Gwaggo bata ƙaunarsa, domin ko abinci aka gama aka zo zuba masa a kular da ta ware dominsa sai tayi ta mita tana faɗin Allah Ya yi wadaran ƴan karere. Sannu a hankali Mahmuda wanda Abbah yake kira da Malam Mahmuda ya fara jana a jiki, yana koya mini assignment idan an bani. Sannan mafi yawan lokuta shi Abbah ke sawa yana ɗaura min karatun littafan addini da nake ɗauka a wajensa.Hakan sai ya yi saurin haifar da sabo da shaƙuwa a tsakaninmu,musamman da ya kasance dama bani abokin hira, kuma bani da ƴar uwa ko ɗan uwa na jini da zasu zame mini abokan hira ko ɗebe kewa. Gwaggo bata sakar mini fuska, tsakanina da ita hantarace da sanyani aikin bauta.Baya ga haka ban isa ta zauna tayi hira dani ba, bare har taji damuwata ko sanin halin da nake ciki. Ko pad nake so idan ina period Abbah nake zuwa na faɗa mawa ya siya mini, sabida ban samu fuska a wajenta ba bare har na tunkareta da ire-iren waɗannan buƙatun nawa. Shiyasa da Malam Mahmuda ya fara nuna min kulawa, yana treating ɗina tamkar ƙanwarsa ta jini, sai nima nayi saurin sakin jiki dashi na ɗaukesa tamkar Yayana na jini. Lokutan da yake ɗaukar karatu a wajen Abbahna shi ne daga bayan sallar magriba zuwa isha'i ne, da anyi sallar isha'i shi kuma Babanki Malam Mahmuda sai ya karantar da almajiran Abbah. Haka suke yi kullum babu fashi, kuma sosai Abbah ke tsananin ƙaunar Malam Mahmuda a ransa sabida ya yaba da tarbiyarsa da nutsuwarsa. Wataninsa huɗu da zuwa garin kaduna, Abbah ya yi masa magana akan cigaban karatunsa,amma sai ya nuna baya ra'ayi yafi sha'awar business ga kuma sana'arsa ta ɗinki da yake matuƙar girmamawa. A lokacin Abbah ya san cewa ƙwararren tela ne shi, sai ya bashi umurnin zuwa gida giwa ya taho da kekunan ɗinkinsa biyu da ya mallaka.Abbah ya nema masa hayan ƙaramin shago, wanda zai aje kekunansa ya cigaba da sana'ar ɗinkinsa. Cikin sa a Babanki ya fara sana'ar ɗinki a garin kaduna, kafin wani lokaci ya zamana yana da tarin customers masu bashi ɗinki sabida ƙwarewarsa da cika alƙwari. Gefe guda yana cigaba da ɗaukar karatu a wajen Abbah, kuma yana cigaba da taimakon Abbah wajen karantar da almajiransa duk bayan sallar isha'i. Shi kuma Abbah ya ɗaura musu karatu da kansa bayan sallar asuba, haka suke yi har zuwa lokacin da Malam Mahmuda ya samu tsayin shekaru guda a gidan mu. Zuwa lokacin bazan iya misalta miki irin sabo da shaƙuwar da ya shiga tsakanina dashi ba, don ma shi yana matuƙar janye jiki da nuna takatsantsan a kaina.Musamman dana fara zama wata iriyar cikakkar budurwa,kyawuna ya sake bayyana kamar yadda duk wata baiwar ƙiran cikar halitta da Allah ya yi mini suka gama fallasa kansu.Gabaki ɗaya sai ya janye jikinsa daga gareni, baya son ko kaɗan ina raɓar inda yake sai idan Abbah na nan, ko kuma idan ya shigo cikin gida ɗaukar wani abu ko gaida Gwaggo sai mu gaisa. Idan ina da assignment sai dai in jira sai Abbah ya dawo mu baje a falonsa yana koya mini suna hira da Abbah, hakan da yake yi ya sake ƙara masa martaba a idanun Abbah. Ita kam Gwaggo zuwa lokacin Malam Mahmuda ya gama shaida irin tsanar da tayi masa, sabida hatta gaisuwarsa da take amsawa ta daina sabida jin zafin yadda ya yi kane-kane a zuciyar Abbah. Har ya kai kafin ya yi mata maganar su Yaya Kabeeru sau ɗaya,sai ya ambaci sunan Mahmuda sau goma. Sai ta fara cewa asiri ya yiwa Abbah don ya mallaki zuciyarsa, ta yadda zai cire soyayyar Ƴaƴansa a zuciyarsa. Waɗannan kalaman gaba da gaba Gwaggo ta tari mahaifinki Malam Mahmuda ta sanar masa, tun kuma daga ranar ya daina shiga cikin gida gaba ɗaya. Dama idan ba ruwan zafi ko wani abu yake so ba sam bai faye shiga ba, sai ya koma sanyani kai masa duk abinda yake da buƙata idan buƙatar hakan ya taso. Shi ma kuma ya hana in dinga shigar ɗakin nasa sai dai na aje masa abin da ya sanyani in kai masa daga bakin ƙofa, shi sai ya fito ya ɗauka. Duk yana yin hakan ne sabida gudun zargi, duba da yadda Gwaggo tayi mugun sanya mana idanu. Dukkanin ƙiyayyar da take gwada mini sai ta sake riɓanyashi, ta kuma haɗamu mu biyu dashi tana

Please Login or Register in order to submit comment