Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nuna farin cikinta ta ce, "Ma Sha Allah! Allah dai ya ƙara masa lafiya da nisan kwana.Gaskiya Inna babu abin zamuce da Baba Hakimi sai dai addu'ar gamawa da duniya da lafiya. Allah ya ƙara masa nisan kwana mai albarka, Allah kuma ya duba bayansa a lokacin da ƙasa zata rufe idanunsa." Inna Mairo ta amsa da cewa, "Ameen!" Najma ta miƙe ta nufi kicin ɗin don duba abinda aka aiko musu dashi tunda ita ce mai sarrafawa, domin tunda aka hana Inna yawan kusantar ɗumin wuta sai ya kasance ita ce mai yin girkin. Kamar dai yadda ya saba aiko musu wake da shinkafa ce sai gero da garin tuwo da ake niƙo masa sai dai kawai ayi ta ɗiba ana amfani dashi. Ta sake gode masa cikin zuciyarta tana tunanin abinda zasu sarrafa suci da dare. Tunaninta ya tsaya akan ta dafa musu shinkafar manja da alayyu kawai, tunda da rana kwaki suka ci da ƙuli. Koda ta sanar da Inna abinda take da niyyar dafawar, sai ta miƙa mata dubu ɗayan ta ce ta je tayo cefanan ɗari biyar ta dawo da ɗari biyar. Najma ta sake fita tayo cefanan ta dawo tana mai fara shirin ɗaura girkin. Inna tana daga zaune ta taimaketa da gyaran kayan miya da alayyahun, ita kuma Najma ta nufi kicin don kiciniyar rura gawayin da zata yi girkin da shi.

Washegari Adama dilalliya da safe ta zo ta duba katifar tayi masa kuɗi. Inna Mairo ta raina darajar da katifar tayi domin ta san cewa katiface mai nagarta irin ta da.Sai dai dagewa da Adama tayi akan cewa ba zata ƙara farashi daga yadda tayi masa kuɗi ba,sai kawai Inna tq amince domin a matse suke da son kuɗin. Zuwa yamma Adama ta zo da mai ɗaukar katifa ta biya kuɗi aka ɗauka, Inna Mairo sai da tayi ƙwalla lokacin da aka fita da katifar akan idanunta.

Najma ta damƙawa kuɗin bayan tafiyar Adama tana mai cewa , "Gasu Najma, sake irgasu mu gani." Najma ta amsa kuɗin ta sake irgawa tana sanar da Inna Mairo yawan kuɗin. Suka zauna suka lissafa kuɗin wake dana mai da za a siyo don cigaba da sana'arsu da ya karɓesu na tuyan ƙosai, wanda Najmar ce zata jagorancin cigaba da yi tunda Inna ba damar ta cigaba sabida kiyaye lafiyarta.

Ragowar kuɗin da ya ragu Inna ta amsa ta aje, da tunanin cewa washegari zata aika da kuɗin wajen Hakimi don a nemi ciko a sayo maganinta guda ɗaya da ba a samu saye ba sabida tsadarsa. Sai dai koda ta aika Najma da kuɗin Hakimi cewa ya yi a dawo mata da kuɗinta, yana sane da maganar da zaran ya samu hali za a sayo a kawo mata. Inna Mairo ta tasa kuɗin a gaba tayi zuru tana zurfafa tuni akan irin ɗawainiyar da Hakimi ke yi dasu, wanda ba kowani amini bane zai yiwa amininsa wannan halaccin da Hakimi ya gwadayi ba. Kuɗin sai ta sake rabashi biyu ta bai wa Najma rabi ta ce ta siyo musu mangyaɗa da manja na girki wanda zai jima musu, ragowar kuɗin kuma ta adana a hannunta don tsaran lalura.

Najma ta cigaba da suyan ƙosai kamar yadda suke yi, kuma ana samun ciniki mai yawa don sana'ar ta amshesu da gaske. Sabida yadda suke tsaftace sana'ar da kyau, suke kuma yinsa da arha matuƙa basa bin mugun riba mai yawa,don albarkan suke nema ba wai yawan kuɗin da za a zare albarkarsa ba. Tun ƙarfe bakwai idan ta kafa yin tuyan bata tashi a wajen sai ƙarfe goma, sosai Inna ke tausayinta tare da jinjinawa ƙoƙarin Najma sabida irin wahalar da take sha.Inna ke ɗan taimakawa da yin ayyukan gida irin su shara da gyaran ɗaki don ragewa Najma wasu wahalhalun. A haka suke cigaba da sana'arsu suna manejin rayuwa, da daɗi babu daɗi haka nan suke nuna godiyarsu ga Allah kullum.A hakan suke samun ƙarin wadatuwan zuci a koda yaushe,wanda shi ne kuma babban arziƙin bawa.

Ranar wata asabar da misalin ƙarfe sha biyu na rana, Najma ta fito daga wanka kenan tana shiryawa suka fara jiyo sallama daga bakin zauren shigowa gidan. Inna Mairo ta zari Hijab ta fice don ganin mai sallamar, duk da cewa kunnuwanta na jiyo mata murya kamar ta drivern Gwaggon kaduna ne. Tana fita kuwa tayi ido huɗu da Adamu driver,ta saki murmushi tana masa maraba da zuwa.A tsaye suka gaisa kafin ta juya zuwa cikin gida don ɗakko masa tabarma, ta shinfiɗa masa a nan zauren suna sake gaisawa cikin mutunci. Adamu ya dubi Inna Mairo cikin jin tausayin yadda duk ta lalace ya ce, "Hajiya Zainab ne ta aiko ni da saƙo, ta ce a gaidaki da kyau sannan idan na iso in kiraki zaku yi magana da ita ta wayata." Inna Mairo da ke sauraren saƙon Adamu driver, sai ta dubesa tana mamakin kalamansa. Ya cigaba da faɗin, "Bari a kwaso saƙon daga mota, in yaso sai na kirata kamar yadda muka rabu da ita akan ina isowa na kira kuyi magana." Inna Mairo ta jinjina kai tana faɗin, "To badamuwa Adamu, bari a kawo maka koda ruwan sha ne kafin a ɗaura sanwar rana ka ci." Adamu ya yi godia yana mai fita zuwa wajen ƙatuwar motar Hajiya Zainab Kaita da ya taho da ita. Inna Mairo kuma ta shiga cikin gida don kawo masa ruwan sha, tana mai sanar da Najma cewa drivern Gwaggo ne Adamu yazo. Ta cigaba da cewa, "Ya ce matar Yaya Kabeeru ce ta aikosa Najma, Allah dai yasa lafiya don ta ce idan ya bani saƙon ya kirata muyi magana. Naga dai ba azumi bane yanzu, ba kuma sallar layyane ya gabato ba bare ace saƙon da aka saba yo mini aike dasu ne suka iso." Inna ta kai ƙarshen maganar cikin sanyin murya, hakan yasa Najma dubanta da kulawa ta ce, "Bakomi Inna,alkhairy ne In Sha Allah! Kai masa ruwan kiga abinda ya zo dashi, sannan kiji mai zata sanar miki ɗin." Inna ta jinjina kai tana gamsuma da kalaman Najma,ta juya ta fito daga ɗakin hannunta riƙe da wani matsakaicin jug ɗin roba da ta ɗibarwa Adamu ruwan randarsu. Ta samu ya jibge manyan paper bags har guda uku daga gefe guda cikin zauren, ɗaya gefen kuma ya jingine buhun shinkafa da su taliya da kayan shayi. Ta ɗauke idanunta daga kan kayan tana mayarwa kan Adamu ta ce, "Adamu yanzu duk waɗannan kayan daga Hajiya Zainab suke? Kodai Gwaggo ce ta aiko ka ta ce ka ɓoye hakan?" Adamu ya yi murmushi, can ƙasan zuciyarsa yana sake jin tausayin Inna Mairo sabida yadda ƴan uwanta da Gwaggo basu damu da ita ba. Ga arziƙi can kamar yaci kansa, amma ita gata a cikin ƙauyen giwa da sam garin ya kula baya samun wani cigaba. Kullum yazo jiya iyau yake ganin garin, ba ya ganin wani sauyi na a zo a gani da garin ke samu. Ya sauke nunfashi yana faɗin, "Inna Hajiya ce ta aiko ni ba Gwaggo ba, don ita bata ma san nan nayo ba domin Hajiya Zainab cewa tayi ta ara mata ni zata aikeni wani waje. Don haka bata ma san cewa nan zan zo ba Inna, amma bari na kira Hajiyar kuyi magana." Daga haka ya zaro wayarsa daga gaban aljihun rigarsa yana mai danna kiran Hajiya Zee Kaita. Bugu biyu ana uku ta ɗaga wayar, Adamu ya shaida mata cewa ya iso, ta buƙaci ya sadata da Inna Mairon.Ya miƙawa Inna wayar ta amsa, hannunta na rawa ta kai wayar kunni bakinta ɗauke da sallama.Daga ɓangaren Hajiya Zainab ta amsa mata sallamar tana tambayarta lafiyarta dana ƴarta Najma. Inna ta bata amsa da cewa suna cikin ƙoshin lafiya. Hajiya Zainab sai ta tafi kai tsaye da tambayar Inna dalilinta na rashin zuwa wajen bikin manyan Yaranta biyu da aka yi wata ɗaya da ya wuce. Cike da kaɗuwa Inna Mairo ke duban Adamu tana sake damƙe wayar akan kunninta ta ce, "Yanzu kina nufin ki ce anyi auren Adnan da mai sunan Gwaggo banji labari ba?" Cike da tsantsar mamakin jin kalaman Inna Mairo ita ma Hajiya Zainab da bata tabbacin haka take nufi. Inna Mairo ta saki salati tana mai jin zuciyarta na matsewa da wani irin ɓacin rai mara misaltuwa. Mamakin halayyar Gwaggo da irin ƙiyayyar da take mata na sake tayar da hankalinta, domin bata taɓa tunanin hakan zai iya faruwa ba koda wasa. A ce wai anyi auren manyan Yaran Yaya Kabeeru ƴan gaban goshin Gwaggo, amma bata aiko an sanar mata ta halarci bikin ba sabida kawai Gwaggon ta nuna mata cewa har yanzu zuciyarta bata risina akan nuna mata ƙiyayyah da rashin son ta raɓi inda suke ba. Wasu hawaye masu zafi wanda bata shirya fitowarsu ba suka gangaro daga fuskarta, ta sanya hannu tana sharesu tana cigaba da sauraren kalamai na rarrashi daga bakin Hajiya Zainab ɗin. Wacce zuwa lokacin da suke wayar da Inna ta gama gane duk wani laifi na wuyar surukarta Hajiya Gwaggo, wacce ita ce bata son Inna ta raɓi ƴan uwanta bare har ta amfana da ni'imar da Ubangiji ya yi musu na tarin arziƙi. Domin zuwa yanzu arziƙinsu kullum sake bunƙasa yake, sun samu ɗaukaka a rayuwa matuƙa da gaske. Musamman mai gidanta Alhaji Kabeer Dukku,wanda ya gama zama babba sosai a wajen aikinsa, sannan ya zama ɗan siyarsa ɓoye dake ci da gwamnati.Yana samun manyan kwagiloli daga gwamnatin tarayya, sanadiyyar amininsu dake kusa da shugaban ƙasa sosai. Inna Mairo ta dinga sauraren maganganun Hajiya Zainab da irin ban bakin da take mata na cewa ta daure ta cigaba da kai musu ziyara,karta cigaba da biye Gwaggo ta zo don sadar da zumunci tsakaninta da ƴan uwanta ne. Ita dai Inna tana jin Hajiya Zainab ne kawai, amma zuwa lokacin zuciyarta ta riga ta kulle da tsananin baƙin cikin wannan tozarci da nuna mata iyakarta da Gwaggo tayi. Don bata yi zaton duk lalacewarta da yadda Gwaggon bata sonta zata iya bari ayi auren Ƴaƴan ɗan uwanta uba ɗaya amma ace wai bata sani ba. Tabbas dole zuciyarta ta girgiza, ranta kuma ya sosu domin iyakan tozarci da rashin ƙauna har ma da ƙyama duk an nuna mata. Ta danne zuciyarta har zuwa lokacin da suka kammala yin magana da Hajiya Zainab ɗin,sannan tayi mata godiya mai tarin yawa akan abin arziƙin da ta aiko mata da shi. Ta miƙawa Adamu wayarsa tana mai jin ƙaunar matar Yayan nata na mamaye zuciyarta, babu abinda zata ce mata sai godiya don ta fiye mata ƴan uwanta da Gwaggon.Tunda har ita taji ciwon rashin zuwanta bikin, ta kuma aiko takanas don a ga lafiyarta a kuma ji dalilinta na rashin halartan bikin. Bata bar ta haka ba kuma sai da ta aiko mata da tarin abin arziƙi, wanda take kyautata zaton kayan biki ne a waɗancan jakunan takardan.Sabida sai a yanzu take ganin tambarin sunan Yaran da aka aurar ɗin a jikin paper bags ɗin.Cikin wani irin sanyin murya ta dubi Adamu driver tana mai miƙa masa wayarsa ta ce, "Adamu ga wayar taka na gode, ka yi haƙuri ka jira Najma ta kammala abinci sai kaci ka yi sallah kafin ka juya." Adamu ya dubeta cike da sake jin zallar tausayin yadda yaga ɓacin rai kwance a idanunta ya ce, "Kiyi haƙuri Inna, komi na rayuwa mai wucewa ne." Inna Mairo ta jinjina kai tana kai wa matuƙa wajen sake danne damuwa da ƙuncin da ya mamaye zuciyarta ta ce, "Bakomi Adamu, tabbas komi mai wucewa ne. Allah dai ya bamu ikon cin jarabawarmu ta rayuwa, domin kowa akwai ta inda ake jarabtarsa." Adamu ya jinjina kai yana sake kwantar da hankalinta da kalamai masu daɗi, don ya hango ɓacin rai mai yawa kwance a idanunta. Shi ya shigar mata da kayan abincin zuwa ciki, ita kuma ta ɗauki jakunan duka ta nufi cikin gidan, tana nufan ɗakinsu dashi zuciyarta na mata wani irin nauyi da zugi.......✍🏻

🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻*
*MTN*
*GLO*
*AIRTEL*
*9MOBILE*

*MONTHLY VADILITY 💃🏻*

*DUKA AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DON SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻




#Lovestory#
#Najma#
#Aysha Ɗansabo Lemu🥰
[3/2, 1:57 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻
_*Arewabooks@ayshadansabo*_

*Paid book:500*

*Chapter 8*

_Free page_


Bayan Adamu ya ci abinci ya gabatar da sallar azuhur anan cikin zauren gidan Inna Mairo, sai suka yi sallama da juna ya juya don komawa garin kaduna.Inna Mairo ta juyo zuwa cikin gidan daga yi masa rakiya da tayi,tana ji zuciyarta na cigaba da yi mata matsananci zafi. A nan tsakar falonta ta samu Najma na fiddo kayan da ke cikin waɗannan paper bangs ɗin.Ta nemi guri ta zauna tana cigaba da kallon kayayyin da Najma ke fiddowa.Kayayyaki ne da aka raba wajen bikin irin cups da su plate, sai su towels na wanka da su mafitai masu kyau da sauran tarkace. Ɗaya bag ɗin kuma turmin atamfa ne mai tsada haɗe da wani laces mai shegen kyau, sai takalmi flat shoe product ɗin CHANNEL. Najma ta dinga juya kayan tana yaba kyawunsu, yayinda Inna Mairo da ke kallonta ta dinga ji zuciyarta na karyewa.Hawaye suka fara taruwa a idanunta ,ta dinga jin ƙaunar Hajiya Zainab na sake samun waje a zuciyarta. Cikin wani irin sanyin murya ta dubi Najma ta ce, "Watakila ta siya mini waɗannan kayan ne a tunaninta zan isa da wuri sai a ɗinka mini inci biki dashi.Ki taya ni yi mata fatan alkhairy domin yadda take nuna mini ƙauna ta fiye mini ƴan uwana da sam bana cikin zuciyarsu." Inna Mairo ta ɗan dakata da maganar wani abu mai mauyi na sake danne zuciyarta. Da ƙyar ta iya cigaba da faɗin, "Najma aurar Yara biyu fa aka yi amma ban yi darajar da zanji koda labari ba, wata iriyar ƙiyayyace Gwaggo ke mini har haka? Meyasa idan ita ba zata sanar min ba Yaya Kabeeru da kansa ba zai iya aikowa a sanar mini ba? Sabida ni ɗin basu damu dani bako? Suna ƙyamar na raɓi hidimarsu don za a nuna ni a ƙasƙance ace ni jininsu ce dana fito daga ƙauye ko? Meyasa zumunci ya yi lalacewar da ɗan uwanka na jini ke maida kai bakomi ba matuƙar aka ce kai ɗin ba kowa bane, ko wanda ka ke tare da shi ba kowa bane? Zafi nake ji sosai a cikin zuciyata Najma,na rasa yadda zanyi na cigaba da yin sabo da irin wannan tozarcin da ake yi mini don anga ba idanun Abbah a raye...." Inna Mairo ta kasa cigaba da maganar sakamakon kuka mai ƙarfi da ya taho mata, ta dinga yinsa har da shashsheka tana ji tamkar ƙirjinta zai buɗe sabida zafi da ciwon da take daga cikin zuciyarta. Hankalin Najma ya tashi da ganin irin yadda Inna Mairo ke kuka,wani irin tausayin Inna ya kamata. Hawaye suka dinga zarya a fuskar Najma tana rarrashin Inna Mairo.Tsana da jin zafin Gwaggo da Ƴan uwan Inna na sake zama a zuciyarta. Da ƙyar tayi nasarar tsaida kukan da Inna Mairo ke yi,ta sanya hannu tana share mata hawayen da suka kasa tsayawa. Cikin tsananin raunin muryar da tausayi da zallar damuwa suka kassarashi Najma ke faɗin, "Inna kiyi haƙuri, ki sake akan wanda ki ke yi.Komi zai wuce, zasu yi nadama wataran, domin sun cutar da zuciyarki a lokacin da kike matuƙar buƙatar su nuna tausayi da kulawarsu gareki. Kina dani Inna kuma In Sha Allah sai na share miki hawayenki na sanya farin ciki a zuciyarki,farin cikin da zai wanke damuwa da ƙuncin da suka cusawa zuciyarki.Don Allah Inna karki saka wannan baƙin cikin a zuciyarki ta yadda zai tada ciwonki, domin ni kaɗai kike sanyawa cikin firgici da ɗimuwa a duk sanda zan ganki cikin halin ciwo." Najma ta dakata da maganar hawaye na cigaba da zarya akan fuskarta. Inna Mairo ta dubi ƴarta tana sake jin tausayin kansu na kamata, ta miƙa hannu ta riƙo na Najma tana faɗin, "Ba zanyi hakan ba Najma, amma ki sani dole zuciyata da shiga ƙunci da irin wannan abinda aka yi mini.Ki tayani addu'a Allah ya danne zuciyata domin bana ji a yau zan iya koda rintsawa ne. Zuciyata zafi take yi ina jin ciwo mai yawa a cikinta Najma." Inna ta dakata tana zare hannunta daga riƙon da tayi wa Najma ta nufi ɗakinta jiri na ɗibarta. Hankalin Najma sai ya sake tashi,tabi bayan Inna da kallo wasu hawayen masu zafi na sake ɓalle mata. Duk yadda ta yi ƙoƙari wajen tausar zuciyar Inna Mairo ta kasa, domin ko abinci cokali uku Innar ta kai baki ta ce ta ƙoshi. Da ƙyar ta sha ruwa ta haɗiyi maganinta na rana ta kwanta,tana cigaba da jinyar zuciyarta da ke mata tsananin ciwo har lokacin. Zuwa yamma bayan Najma ta kammala yiwa Inna ɗan faten tsaki da yakuwa, sai ta juye a kula ta nufi ɗakin Inna dashi ta aje.Ɗakinta ta nufa ta zuro dogon hijab ɗinta har ƙasa kalar sararin samaniya,kalar ya yi mata kyau matuƙa tare da haske black beauty face ɗinta. Ta leƙa ɗakin Inna ta sameta a kwance har lokacin bisa katifarta,ta rufe idanunta tamkar mai yin bacci.Amma a zahiri idanunta biyu ta dai rufe idanun ne kawai, don bata buƙatar barinsu a buɗe sabida yadda idanun kansu sukai mata wani irin nauyi. Najma ta sanyaya murya ta ce, "Inna zan ɗan leƙa gidan Baba Hakimi, zan dawo yanzu bada jimawa ba." Kai kawai Inna Mairo ta gyaɗa wa Najma, ba tare da ta iya buɗe baki tayi mata magana ba. Najma ta juyo ta fice zuciyarta cike da damuwan halin da Innan ta shiga sanadiyyar kawai ba a sanar da ita bikin Ƴaƴan ɗan uwanta Yaya Kabeeru ba. Tafiya take yi cikin sanyin jiki har ta isa ƙofar gidan Hakimi, ta samu mutane zaune daga wajen zauren bisa shinfiɗu. Ta risina ta gaidasu ta wuce zuwa cikin gidan, tana ji ƙafafunta na faman harɗewa sakamakon idanun maza da suka yi mata rikiya. A tsakar gida ta samu Inna Karima na gyaran gyaɗar da za ta zuba a miyar taushe. Da fara'a ta ɗago tana amsa sallamar Najma tana faɗin, "Lale Najma, yanzu Hanne suka gama zancenki ita da Lubah." Najma ta ƙarisa inda Inna Karima ke zaune bisa kujerar tsugunno, ta gaidata cike da ladabi tana faɗin, "Alllah sarki, na tsaya na kammala yiwa Inna fate ne shiyasa ban fito da wuri ba." Inna Karima ta jinjina kai tana faɗin, "Ya jikin nata Najma, da fatan dai tana shan magungunan? Ɗazu Hakimi ya gama maganar cewa Auwalu zai je a sayo cikon ɗaya maganin." Najma ta saki murmushin yaƙe tana cewa, "Jiki da sauƙi Inna, tana shan maganin bisa ƙa'ida. Amma yanzu haka a kwance na baro ta, tana cikin ɓacin rai mai tsanani Inna." Inna Karima tayi saurin aje tray ɗin hannunta tana duban Najma ta ce,"Subhanallahi! Mai ya sameta Najma, ana murna jiki ya yi sauƙi kuma?" Najma ta sake narke fuska alamun tana cikin damuwa, ta dubi Innarsu Hanne cike da sanyin murya ta mayar mata da yadd aka yi. Inna Karima ta sauke zazzafar numfashi bayan ta gama sauraren Najma, ta buɗe baki cikin ɓacin rai ta ce, "Wannan Gwaggo wai wace iriyar zuciyace gareta? Meyasa ba zata mance abinda ya faru a baya ta gane cewa komi fa NUFIN ALLAH ne, yadda duk yaso hakan dole zai kasance. Mairo bata da laifi domin ba ita ce ta sanya mahaifinta auro Innarta ba, ba kuma ita ce ta zaɓawa kanta auren Malam Mahmuda ba. Allah ne ya yi nufin hakan zai kasance, don me ba zata saduda ta gane komi yin Allah bane? Ki kwantar da hankalinki Najma, zan yi magana da Hakimi domin lokaci ya yi da ya kamata ace ya shiga cikin wannan lamari ya daidaita tsakanin Mairo da Ƴan uwanta koda son ran Gwaggo ko babu. Domin idan aka cigaba da tafiya a hakan, tabbas watarana za a wayi gari baƙin cikinsu ya yi ajalin Mairo.Wanda mu ne za a yiwa asara basu ba, domin su ɗin basu san daraja da ƙimarta a matsayinta na mace tilo a cikinsu ba." Inna Karima ta kai ƙarshen maganar fuskarta na bayyan zallar ɓacin ran da ke zuciyarta. Najma da tayi zuru tana saurarenta,ta ɗaga manyan fararen idanunta tana duban Inna Karima ta ce, "To Inna da ko na gode idan ki kai wannan taimakon, domin ina cikin matsanancin damuwa. Ina jin tsoron ciwon zuciyar da ke barazanar samunta ya sameta, idan hakan ya faru na shiga uku Inna." Najma ta kai ƙarshen maganar cikin rawar murya. Inna Karima ta dinga rarrashin Najma tana kwantar mata da hankali, daga ƙarshe ta ce ta tashi ta isa ɗakin su Hanne suna nan a ciki. Ta ja ƙafa a hankali ta isa ɗakin amininan nata su Hanne, zuciyarta na yin sanyi da kalaman da Inna Karima tayi mata na kwantar da hankali. Shafin hira suka buɗe da ƙawayen nata su Hanne, waɗanda take kallo a matsayin ƴan uwa na jini da bata dasu. Sun ɗauki lokaci suna raha a tsakaninsu, sai da Najma ta kalli agogo ta ga lokaci ya ja sosai, sannan ta miƙe tana sanar dasu cewa zata wuce gida ta baro Inna ita kaɗai bata jin daɗi kuma. Cike da alhini suke tambayarta me yasamu Innar? Najma ta basu amsa da cewa jikin ne dai ya ɗan motsa mata, bata sanar dasu gaskiyar abinda ya kawo ɓacin rai a zuciyar Inna Mairon ba. Suka yo mata rakiya har zaure bayan tayi sallama da Inna Karima da Amaryar Hakimi mai suna Ladiyo.

Ta isa gida ana daf da kiran sallar magriba, ta wuce direct ɗakin Inna Mairo don duba halin da take ciki. Bata sameta a ɗakin ba hakan ya bata tabbacin ta fita zuwa bayi ne, sai ta nufi ɗakinta tana zare hijab ɗin jikinta ta aje bisa katifarta. Fitowarta falo ya yi daidai da shigowar Inna Mairo, ta dubi Najma tana faɗin, "Sai yanzu ki ka dawo Najma?" Najma ta ɗan narke fuska tana faɗin, "Inna kiyi haƙuri, wallahi ban ankara ba naga lokaci ya tafi.Inna Karima suna gaidaki sun ce ai miki sannu da jiki, sannan Baba Hakimi ya bai wa Auwalu kuɗin maganinki da ba a sayo ba." Inna Mairo dake sauraren Najma sai tayi murmushin yaƙe tana faɗin, "Alhamdulillah! Allah ya biya shi da gidan aljanna Najma." Najma ta amsa da cewa, "Ameen." Tana mai wucewa waje don zuwa ta ɗauro alwala.

Suna zaune tare da Inna Mairo bayan sallar isha'i suka jiyo sallamar Hakimi da Inna Karima. Najma tayi saurin fita tana musu barka da zuwa. suka ƙariso cikin ɗakin Inna Mairo Hakimi na amsa gaisuwar da Najma ke masa cike da kulawa. Inna Mairo tayi saurin shigewa ɗaki ta sanyo hijab, kafin ta fito ta zauna daga kusa da Najma tana yiwa su Hakimi barka da zuwa. Bayan sun gama gaisawa da tambayarta jikinta, sai Hakimi ya ɗaura da yi mata nasiha kamar ko yaushe akan ta cigaba da haƙuri da rayuwa. Inna ta dinga gyaɗa kai tana jin ƙarin nauyi a zuciyarta, musamman da ya ambato mata sunan Gwaggon kaduna. Hakimi ya cigaba da duban Inna Mairo yana faɗin, "Mairo lokaci ya yi da zamu je gani gaki gaban Gwaggo ta gaya mana mi kika yi mata da ta riƙeki haka a zuci? Meyasa ba zata gane cewa komi mai wucewa bane, sannan Ubangiji na son masu yawan yafiya da manta sharrin mutum su rungumi alkhairinsa.Zaki tasa ƴarki Najma mu je gani gaku domin kawo ƙarshen wannan ƙiyayya,don naga alamun lamarin kullum sake lalacewa yake yi maimakon ya gyaru. Bai kamata ace an kawo lokacin da har za a aurar da Ƴaƴan Kabeeru amma ace baki yi darajar da zaki sani ba, sabida an kai maƙura wajen nuna miki cewa ke bakomi bace. Abin ya yi mini ciwo matuƙa

Please Login or Register in order to submit comment