Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jiki da sanya tsantsar shauƙi. Duk yadda Hannah ta so zamewa daga tarkonsa kasawa tayi domin da alamu a yunwace ya shigo garin,don bai barta ba sai da ya samu biyan buƙatar da ya sanar mata somi ne kafin ya ci abinci zuwa anjima tayi biyan bashin mai dalili.Ta nufi bathroom ɗinsa don yin wanka tana jin dukkanin jikinta na amsawa,don ya sameta sosai irin yadda yake buƙata. Sun fito falo sun tadda Nabeelah ta gudu abin ta, Hannah tayi serving ɗinsa abincin da Momy ta aiko.Yana cin abincin yana amsa call da ke shigo masa time by time,ita kuma Hannah na daga gefe tana dubansa tamkar mai gadin kada a zo a sure mata shi.Wani irin soyayyarsa take ji a zuci mai yawa, duk yadda ya kai ga haɗe mata face kyau yake mata tana jin zuciyarta na sake matowa a kansa.Tana son bashi haƙuri akan zancen cikin tana tsoron kalaman da zai gasa mata,hakan ya sanya ta ja baki tayi masa shiru har ya kammala cin abincin ya tashi.Ta dubesa cikin ido time ɗin da ya doshi hanyar fita falon ta ce, "AD fita zaka yi ne alhali baka jima da shigowa ba?" Wani kallo ya juyo ya aika mata,yana cigaba da takawa ya furta, "Wajen Gwaggo zani ko laifi ne yin hakan?" Hannah tayi ƙasa da kai zuciyarta na taɓuwa da yadda ya haɗe mata fuska tamkar bashi ya gama sambatu a bed ba ɗazu, tayi saurin faɗin, "Allah ya baka haƙuri ka gaisheta." Ya yi ficewarsa ba tare da ya sake tanka ta ba, don gaba ɗaya idan yana tuna tana ɗauke da cikin da bai shirya samuwarsa ba haushinta yake ji na rufe zuciyarsa.Sai dai ni'imar da ya kwasa a jikinta yau ɗin, ya sanya shi nishaɗi domin ta kaishi wata iriyar duniyar maji daɗi.Ya wani ja ƙaramin tsaki ƙasa-ƙasa yana cigaba da takawa ya fito daga side ɗin baki ɗaya zuwa na Gwaggo.Bai samu kowa a falon ba don 10pm ta gota, tuni Inna Mairo ta sha maganinta ta kwanta.Ita kuma Gwaggo na ɗaki na kintsa kayan da zata kai tsaraba giwa a gobe.Najma kuma Momy da Daddy sun ƙi bari ta dawo side ɗin Gwaggo, don Daddy cewa ya yi ma ta dawo kenan sai dai ta riƙa shiga gaida su tana dawowa nan ɗin.Hatta kayan sawarta ya ce suna dawowa giwa ta tabbatar komi nata ya dawo ɗakin Nasreen,don yana so kansu ya sake haɗuwa su kuma shaƙu da juna sosai. Direct ɗakin Gwaggo AD Dukku ya nufa, don ya yi mugun sabo da indai ya shigo garin baya iya kwanciya bai shigo ya yi mata sai da safe, sun ɗan taɓa hira tare da cin wani abu idan ya shigo dashi ba. Ya zauna saman sofa ya zauna yana faɗin, "Sweet granny shirin dai tafiya ƙauyen ne? Why not ki barsu Momy su wuce ke ki yi zamanki musha hira gobe kafin in wuce Abuja,daga can kuma zan wuce port harcourt ba xan dawo ta nan ba." Jin abinda ya faɗi ya sanya Gwaggo saurin dubansa tana faɗin, "Kana nufin gobe zaka wuce Habujan?" Ya jinjina kai tare da ɗage mata gira guda.Hakan ya sanya ta tsuke fuska tana faɗin,"Amma baka da tausayi Adinanu, inyi wata biyu ban sanya ka a idanuna ba amma ka zo sai ka ce min kuma gobe zaka tafi.Gaskiya baka kyauta mini ba, wannan ai dama baka zo ba kawai yafi." Adnan ya ɗan murmusa yana duban Gwaggo cike da so ya furta, "Karki damu sati na sama zan zo nayi one week, yanzu aiki ne zai kaini Abuja ɗin Gwaggo.Kuma dole in wuce a gobe ɗin babu yadda na iya,amma zan dawo karki damu tunda kun riƙemun mata anan ma ai xaki dinga gani na akai-akai don Daddy ya ce lallai na riƙa zuwa duk weekend ko bayan sati biyu." Gwaggo ta jinjina kai tana faɗin, "Har kunyi magana da Kabeerun ne? Amma shi ne da ya shigo bai ce min komi akan zancen ba.Sai ka kula dai ka aje duk wani shashancin banza na gaya maka,don duk wannan jinkan naka da tsare gida na banza ne tunda kana shan shegun ƙwayoyin da ke sake ƙonar maka da zuciya da sanyaka rashin kunya kala-kala ko?" AD Dukku bai shiryawa yin dariya ba amma sai da ya dara.Ya dubi Gwaggo da wani irin so yana mai faɗin, "Gwaggo dama akwai ƙwayar da take sanya rashin kunya ce?" Gwaggo tayi saurin gyaɗa kai tana faɗin, "Ƙwarai kuwa, haka naji ana faɗi kuma wallahi na yadda don idan kuka afa bakwa ganin kowa da mutunci ehe!" Wannan karon baki ya taɓe yana danne dariyar da ke cinsa ya furta, "To ni dai ba ita nake sha ba Gwaggo, yanzu dai ki aje maganar wata ƙwaya ki ɗakko min irin naman ɗaxu naci shi na shigo ci." Gwaggo ta harareshi tana cigaba da masa mita akan shan ƙwaya da illolin da yake janyowa mai yinsa,sannan uwa uba ɓarewar mutunci a idanun duk wani mai maka kallon daraja da cikar kamala.Adnan dai jinta kawai yake yi ba tare da ya tanka ba, suka fito falo ta nufi kitchen don ɗebo naman, ta haɗo da sassanyar madarar shanu da aka zuba zuma a ciki ba sugar ba.Ya ci naman mai yawa da madarar, yana ci suna hira har ya kammala.Ya yiwa Gwaggo sai da safe ya wuce side ɗinsa,yana ji zuciyarsa na sake cika da ƙaunar gwaggon nasa mai shagwaɓashi.Ya samu Hannah har ta gaji da jiran shigowarsa bacci ya kwasheta bisa sofa, ya bi rigar baccin da ke jikinta da kallo wanda babu maraba da babu.Ya ɗan lumshe idanunsa yana sake buɗesu akan tsayayyun ƙirjin da babu bra a jikinsu,sai wani tsokane idanunsa suke yi domin rabinsu sun bayyana a waje.Ya taka a hankali ya isa bakin sofa ɗin, yana mai rankwafawa ya basu wani light kiss kafin ya saɓata a kafaɗarsa zuwa room ɗinsa.Yana aje ta a tsakiyar bed ɗin tana farkawa, ta sauke idanunta a kansa lokacin da yake cire jallabiyar da ke jikinsa.Wani irin ƙishi taji tana ji,hakan ya sanyata sakkowa daga bed ɗin ta nufi ƙofar fita don ɗakko ruwan sha. Ganin zata fice ya sanya shi yi mata magana a kausashe,ta narke masa tare da sanar dashi ruwa kaɗai za ta ɗakko ta dawo.Tana fita hawaye suka cika idanunta,tana mamakin rashin kunyar AD Dukku.Domin ta gama gane gangar jikinta kawai yake so ba ita ba, ta gama sanin bata da wani amfani da ya wuce biyan buƙatar sha'awarsa.Sai kuma albarkacin soyayya da amintar da ke tsakanin iyayensu da ya zamewa aurenta da shi garkuwa,irin garkuwar da yake ɗaga mata ƙafa ya kuma amshi auren da hannu biyu amma ba don ƙauna ko soyayyah ba.Ruwan kaɗai ta sha ta yo fitsari tare da ƙaro turare akan wanda ta sanya time ɗin da ta saka rigar baccin.Tana shigowa ɗakin ta tadda ya kashe hasken ɗakin, sai mai duhu da ya bari.Ta lallaɓa ta hau bed ɗin zuciyarta na cigaba da matsewa da wani yanayi mai wuyar fassara.Tana jin sanda ya miƙo hannuwansa ya jata zuwa jikinsa yana shinshinan ƙamshinta kamar wani maye.Sai ta sauke ajiyar zuciya tana hana kanta shigewa cikin jikinsa sosai,amma duk yadda taso nuna masa gajiyarta kasawa tayi.Hakanan ta biye mishi ya sake samun cikakken gamsuwa daga gareta.Ko wanka bata iya yi ba baccin wahala da gajiya ya kwasheta, shi kam sai da ya yo wanka ya dawo ya kwanta don sam baya yadda ya kwana da janaba a jikinsa.

*```WASHEGARI``*


Koda AD Dukku ya shiga gaida Gwaggo, ita kaɗai ya samu ta gama karyawa kenan bata tashi a wajen ba. Inna Mairo tana ɗaki tana shiri don Daddy ya ce da wuri za a fita,don su samu su isa da wuri su kuma dawo akan lokaci.Ya samu kusa da Gwaggo ya zauna yana buɗeta da daddaɗan ƙamshin dake tashi a jikinsa,ya gama yin kyau cikin ƙananun kayan da ke jikinsa.Gwaggo ta amsa gaisuwarsa tana tsaida idanunta a kansa cike da ƙauna ta ce, "Ba dai har kayi shirin wucewa Abujan ba?" Adnan Dukku ya ɗan kwaɓe fuska cike da shagwaɓar da ya saba yi mata ya ce, "Eh na shirya Gwaggo, daga nan sai wajen Daddy zan wuce muyi sallama in kama hanya don ni zanyi driving da kaina." Gwaggo ta sauke numfashi tana faɗin, "To Allah ya tsare hanya,muma nan da lokaci kaɗan zamu gama shiri mu kama hanya.Don Allah Adinanu ka rungumi Hannatu ka bar wa Allah ikonsa,don da alamu aurenku da juna alkhairy ne tunda gashi zaku fara tara zuri'a.A hankali zaka ƙaunaceta kamar yadda take ƙaunarka,ko kaɗan bata da wani aibu kai nema mai aibun amma a hakanan take ƙaunarka da zuciya ɗaya.Don haka kaji tsoron Allah wajen sauke hakkinta dana abinda take ɗauke da shi, karka ga mun dawo da ita gabanmu hakan ya baka damar cigaba da sharholiyarka a can.Idan bama ganinka Ubangiji yana kallo,kuma zai yi mata sakayya gwargwadon yadda kaci amanarta kona namu ta hanyar saɓa mana da saɓama Ubangijinka.Ka taimakeni ka rabu da duk wasu abokanan banza da ke sake tunzuraka a aikata saɓo,domin ba tarbiyan da Kabeeru ya yi maka kenan ba." Gwaggo ta dakata tana duban yadda mood ɗin AD Dukku ya canza,don bai saba ta tasa shi tana masa irin wannan faɗa da nasihun ba.Ya ɗan haɗe fuska yana faɗin, "Gwaggo wallahi ni ba zina nake yi dasu ba,sune kawai ke manne mini amma ban taɓa kwanciya da ƴar kowa ba.Kin san ina da ƙyanƙyami so bana kusantarsu ta wannan hanyar da ku ke zargi,sannan kuma ni abinda nake sha ba buguwa nake yi kamar ɗan giya ba Gwaggo.Amma zan yi ƙoƙari na rage koma miye don na faranta muku, amma ba za a ce in daina gaba ɗaya a lokaci guda ba." Ya ƙare maganar yana ɗaura kansa a kafaɗarta.Ta kai hannu ta shafa lallausar suman kansa tana faɗin, "Naji Adinanu, amma shi saɓo duk sunansu ɗaya,koda baka kwanciya dasu tarayyarka dasu ɗin ai saɓo ne tunda ba matanka bane ƴan iskan bariki ne marasa tarbiyyya,ni dai ka nisancesu ka kuma nisanci zuwa inda suke domin komin son su da kai idan basa ganinka dole su ɗaga maka ƙafa.Ka daina ganin kyawunka na ruɗarsu,akwai lokacin da kyawun zai disashe." AD Dukku ya saki murmushi mai faɗi,kafin ya raba kansa da kafaɗarta yana miƙewa tsaye ya ce, "Na gode Gwaggo da nasiha, ni zan wuce tunda naga alamun wannan karon ba wani soyayya ki ke son nuna mini ba." Kafin Gwaggo tayi magana sallamar Najma cikin sanyin muryarta ya doki kunnuwarsu.Gwaggo ta amsa sallamar tare da bata izinin shigowa cikin falon, ta shigo kanta a ƙasa hancinta na shaƙan fitinannan ƙamshinsa da tun jiya ta gama saki cewa ƙamshin na musamman ne.Duba ɗaya ta yiwa inda suke ta ɗauke kanta tana tsugunawa nesa dasu ta gaida Gwaggo,Gwaggo ta amsa da fara'a tana faɗin,"Sannu Najma, yanzu nake cewa a raina sun riƙeki baki shigo da wuri ba." Najma ta ɗan saki smile tana faɗin, "Eh Gwaggo, wallahi Nasreen ce duk ta hanani shigowa tunda sassafe,bari in shiga mu fara shiri Daddy ya ce da wuri za a wuce." Gwaggo ta jinjina kai ta ce, "Haka ya ce kuwa, Mairo ma gata can a ɗaki nasan shirin take yi." Najma ta miƙe tana satan kallon gefensa taga hankalinsa na kan danna wayarsa,sam bai muna alamun ya san da wanzuwarta a falon ba.Har zata wuce sai taga rashin dacewar ƙin gaida shi,tunda ko banza shi ne babba a gidan kuma Iyayensa nada ƙima da mutunci a idanunta.Hakan yasa ta ɗan ɗaga sautin muryarta yadda zai jiyota ta ce, "Ina kwana,da fatan an tashi lafiya." AD Dukku da sassanyar muryarta ya bugi kunnuwarsa,sarai ya gane shi take gaidawa amma isarsa da zafin kansa ya hanashi ɗagowa ya dubeta.Hannu kawai ya ɗaga mata ta wuce yana cigaba da danna wayarsa, sai da ta shige corridor ɗin gaba ɗaya sannan Gwaggo ta dubesa tana jin haushin yadda ko kallon Najmar bai yi ba ta ce, "Yanzu ana gaidaka amma ko kallo bata isheka ba Adinanu, ita ce fa ƴar Gwaggonka Mairo da nake faɗi maka ka riƙeta tamkar su Nabeela.Gaskiya bana son wannan wulaƙancin naka,irin haka ne duk saika saka ta muzunta haba Adinanuna!" AD Dukku ya ɗago ya zubawa Gwaggo idanunsa yana faɗin, "Gwaggo mai zance mata tuh? kuma ko ban kalleta yau ba watarana zan ganta ai tunda sun dawon nan ɗin." Don haushi Gwaggo bata kulashi ba har ya yi mata sallama ya wuce side ɗin Daddy.

A can ma side ɗinsu Momy bai daɗe ba ya yi musu sallama dasu, ya fito zuwa side ɗinsa.Ya samu Hannah ta tashi tana yin breakfast kenan.Tayi kyau sosai cikin ƙananan kayan da ta saka,waɗanda suka fidda suranta sosai da kuma bayyana fresh ɗin da tayi.Sallama ya yi mata akan zai wuce Abuja daga can kuma gobe zai koma PH ɗin,duk sai ta ji babu daɗi a ranta domin bata san cewa a yau ɗin zai juya ba.A sanyaye tayi masa fatan isa lafiya tana ji haka kawai hawaye na cika idanunta, domin bata san ranar da zata yi darajar da zata dinga sanin abubuwan da suka shafesa ba.Har ya kai ƙofa ya dawo da baya yana rankwafawa ya sumbaci fuskarta zuwa ƙirjinta,murya can ƙasa ya kai bakinsa bisa kunnuwarta yana faɗin, "Take care! Zan dawo zuwa next week okey!" Daga haka ya juya ya barta da lumshe idanunta hawayen da take riƙewa na sakkowa daga cikin idanunta.Wani irin ƙaunarsa ke sake huda kafan jininta,tana ji tamkar ta bisa su juya tare ko zata dinga ganin kaikawonsa da dakon jiran dawowar cikin tsakiyar daren da ya saba kaiwa ɗin.Don a nan ɗin bata da tabbacin zai dinga zuwa kamar yadda su Momyn suka faɗi.Da ƙyar ta iya ƙarisa cin abincin ta tashi ta nufi ɗakinta,ta sako hijab ta fito zuwa side ɗin Gwaggo don gaidata.Daga can ta wuce side ɗinsu Momy ta tadda suna ta shirin wucewa giwa, don Momy har ta gama cin ado cikin wani rantsatstsan lace mara nauyi mai shegiyar tsada.Nasreen ma ta sha ado cikin wani red and black jacquard voile mai kyan gaske.Ɗinkin straight gown ɗin da akai wa kayan ya amshi jikinta tare da fidda kyawun surarta matuƙa. Nabeela shadda ce a jikinta da yaji embroidery ɗinki ta ko'ina, tayi kyau har ta gaji ita ma don ita ma kyakykyawace wacce ta ɗakko kammanin Daddy sak! Ko kaɗan Hannah bata ji daɗin yadda za a barta ita kaɗai a gidan ba sai ƴan aiki.Ganin duk jikinta a sanyaye yake sai Momy ta ce idan za ta iya zuwa ta je ta shiryo kawai a wuce tare da ita ɗin.Aiko cikin zumuɗi ta koma ta shiryo cikin shiga ta alfarma cikin wani lafaya lace da ya amshi jikinta.

Ƙarfe 11:30am suka kammala shiryawa aka loda tsarabar kayan abinci da kayayyaki masu yawa a bayan boot.A cikin ƙatuwar motar Daddy suka ɗunguma,inda Momy da Inna Mairo da Gwaggo ke ta seat ɗin farko.Yayinda Najma da Nasreen da Anty Hannah da Nabeey ke seat ɗin baya,sai Daddy da ya kame a front seat shi kaɗai.

Wani irin tafiya aka yi mai cike da nishaɗi, ana hira tsakanin juna har suka isa garin giwa.Gidan Hakimi nan suka fara yin masauki,sun kuma samu kyakykyawar tarba daga kariman mutane irin ahalin Hakimi.Suka rasa inda zasu saka kansu da murnar ganin ahalin Inna Mairo da su kansu su Innar Mairon, waɗanda aka yi kewar rashinsu tsayin kwanaki bakwai kenan.Najma da Nasreen da su Nabeela suka ƙule a ɗakin su Hanne suna kwasan hira cike da nishaɗi,an cika gabansu da kayan cima da Hakimi ya fidda kuɗi aka yi cefane mai kyau don tarban su Gwaggo.Lafiyayyan wainar shinkafa da haɗaɗɗiyar miyau taushe da aka zuba naman kajin da aka yanka a ciki, gefe guda kuma an soya musu wasu kajin har da zabi guda biyu ma.An sayi soft drink da su ruwan sha,duk don a fita kunyar su Inna Mairo da hamshaƙan ahalinta waɗanda tun daga kan suturun jikinsu da kalar motar da suka zo a ciki zaka san cewa masu kuɗine ƴan gaske. Daddy da Hakimi tare da wasu cikin amintattun Hakimi ne ke zaune daga falon Hakimin, an baje abinci da kayan arziƙi ana ta hira cikin nishaɗi mai yawan gaske.Daga ɗakin uwargidan Hakimi Inna Karima kuwa,su Gwaggo da Momy ne suke ta shan shafta da tuno baya akan irin rayuwar ƙunci da Inna Mairo tayi bayan ta rasa gwarzon mijinta Malam Mahmuda.Inna Karima ta dinga basu labari,tana sanya Inna Mairo tuno memories ɗin tamkar a lokacin wasu abubuwan ke faruwa.Da hira ya yi hira akan irin kirki da karamcin Malam Mahmuda sai ga Inna Mairo na share hawaye akai-akai,tana ji dukkanin memories ɗin rayuwarta dashi a garin giwa na dawo mata.Sukai masa addu'ar fatan alkhairy suna rarrashin Inna Mairo da ke kuka har da hawaye,tana tunawa da Malam Mahmuda,wanda har a tashi duniya bata ji zata so wani ɗa namiji irin yadda ta so shi,ta kuma ƙaunacesa da dukkanin zuciya da gangar jikinta.

Bayan sun gabatar da sallah sun ci abinci, sai Hakimi ya aiko aka yi kiran Inna Mairo zuwa falonsa.Suka tattauna batu akan gidansu da zasu bari a kulle tare da kawo shawaran ko zasu sanya ƴan haya a gidan ne? Inna Mairo ta dubi Hakimi Alhaji Haruna Musa giwa ta ce, "Hakimi duk abinda kaga ya dace ayi shi za a yi In Sha Allahu!" Hakimi ya jinjina kai yana duban Alhaji Kabeer Dukku dake saurarensu ya ce, "Ni a ganina Mairo gara a saka ƴan haya bayan an yiwa gidan kwaskwarima,domin barinsa a haka xai cigaba da lalacewa ne ƙarshe ginin ya faɗi tunda damina za a shiga.Amma ga ɗan uwanki Alhaji nan kuyi shawara a tsakaninku." Alhaji Kabeer Dukku ya dubi Hakimi kai tsaye ya ce, "Shawararka ita ce abin ɗauka don barin muhalli babu kowa a cikinsa babban kuskure ne,gara ko yaya ne a saka waɗanda zasu cigaba da raya wajen.Don haka idan muka isa can ɗin naga yana yin wajen sai a san wani irin gyara za a yiwa wajen, idan so samu ne ma a bugesa ayi ginin bulo da bulo a saka ƴan hayan da zasu kula da wajen basu lalata ba.Tunda gadonsu ne da xasu yi alfahari da ganin wajen,yana tuna musu da marigayi Malam Mahmuda,wanda muke fata yana kyakykyawan matsayi a yanxu." Inna Mairo ta jinjina kai hawaye na taruwa a idanunta ta ce, "Na gode Yaya Kabeeru,Baba Hakimi kaji abinda Yaya ya ce." Hakimi ya jinjina kai ya ce, "Madallah Alhaji, wannan shawara ya yi, kuma In Sha Allah ba za a saka mutanen da za su lalata wajen ba."

Daddy ya gyaɗa kai cike da gamsuwa yana faɗin, "Mun gode sosai Mai girma Hakimi, Ubangiji ya biya muku dukkan buƙatunku na alkhairy ya raya Iyali.Tabbas abinda ku ka yiwa Mairo Allah ne kaɗai zai biya ku,Allah kuma ya duba gaba da bayanku." Hakimi ya amsa da cewa, "Ameen." Inna Mairo na sake yiwa Hakimi godia ita ma.
Gwaggo da Momy suma falon Hakimi suka fita aka sake gaisawa,su Najma da Nasreen suma tare da su Hanne suka zo zuwa falon suka gaida Daddy.Ya amsa da kulawa yana tambayarsu skull,suka sanar dashi sun kammala sakandiri shekaru biyu baya tare da Najma. Bayan sun koma daga ciki ne Daddy ya tambayi Yaya Auwalu da Umar matakin karatunsu,Auwalu ya sanar da Daddy cewa iyakarsa secondary school.Umar ne kaɗai yake NCE a garin Zaria yanzu,yana ma dab da kammalawa don shi yana son zurfafa karatu ba kamar Auwalu bane da sam yafi ganewa business da noma da kiwon da ya amshe sa. Daddy ya sanar da Umar cewa da zaran ya kammala ya nemesa,sannan shi kuma Auwalu lallai ya yi ƙoƙarin komawa makaranta don yanzu zamani ya sauya, dole mutum ya tashi ya nemi ilimi.Musamman su da suke maza majiya ƙarfi a yanzu, waɗanda ake da burin nan gaba su zama wani abu.Idan babu ilimin sai rayuwar ya zama koma baya,sabida haka lallai ya dage ya koma makaranta.

Dukkaninsu suka ɗunguma zuwa gidansu Inna Mairo da suka rayu a cikinsa cikin ƙunci da damuwa.Daddy sai da ya share hawaye sabida tausayi da baƙin cikin yadda Mairo ta rayu a gida irin wannan, alhali su suna cikin arziƙi da wadatan da har yake iya kyautar gida da motar hawa.Amma ace sun bar ƙanwarsu ta rayu a cikin irin wannan gidan,sabida rashin bibiyanta da wofintar da rayuwarta da suka yi.

Gwaggo hawaye ita ma take yi sosai,tana jin tsananin nadama da danasanin abinda ta aikatawa Mairo a baya.Nasreen da Hannah kuwa mamaki ne ya daskarar dasu,domin basu taɓa zaton a wannan gidan ƙasar Najma suka rayu ba.Inna Karima ita ce ke bai wa Momy labarin cewa, cutar da Malam Mahmuda ya yi fama dashi ne, jinya ya cinye komi nasu har suka saida asalin gidan da ya gini na zamani a garin,suka dawo wannan gidan suka cigaba da rayuwa har Allah ya karɓe rayuwarsa.
Daddy ya shaidawa Hakimi cewa rusa gidan za a yi baki ɗaya asake sabon ginin bulo,don gabaki ɗaya gidan ya yi tsufan da ya kamata ace an sabunta gininsa koda na ƙasa ne.

Inna Mairo basu ɗauka wasu kaya ba don Gwaggo cewa tayi karsu ɗauki komi duk su rabarwa jama'an gari.Daddy ma hakan ya faɗi yana mai jin tsananin kunyar Mairo da jin takaicin kansa da kansa,gaba ɗaya ji yake yi tamkar Abbah na can na Allah wadai dashi da rashin riƙe masa amanar Mairo da suka yi shi da Yaya Ali.Inna Karima, Inna Mairo ta ce ta kwashe duka kayan ɗakinta da suturunsu a rabarwa mabuƙata bayan ta zaɓi wanda take so a cikin masu ƙararin cikin.Suka koma can gidan Hakimi aka shiga fiddo kayan abinci da kayayyakin da Momy da Gwaggo suka saya don kawowa matan Hakimi da ƴaƴayensu.Hakimi da Iyalansa suka rasa bakin godia, don kaya ne da ba a taɓa sauke kamansu a gidan ba.Su Hanne kuwa rungume Najma suka yi suna kuka da hawaye,na tsananin murnar alkhairyn da ta zo musu dashi da kuma alhinin yadda zata bar garin giwa baki ɗaya.....✍🏻


*Pay 500 in to this account number👇🏻*
*0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank*
*OR*
*PAY IN TO DIS ANOTHER ACCOUNT* 👇🏻
*8167768704 AISHA* *DANSABO IBRAHIM*
*ACCOUNT NAME:OPAY*
*Evidence of payment to this number:08167768704*


🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻*
*MTN*
*GLO*
*AIRTEL*
*9MOBILE*
*MONTHLY VADILITY 💃🏻*

*DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻



#Lovestory#
#Najma#
#Aysha Ɗansabo Lemu🥰
[3/20, 9:39 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻 *Arewabooks@ayshadansabo*

*Paid book:500*


*Chapter 20*

_Last free pages_


Da suka tashi tafiya har bakin mota dukkanin jama'ar gidan Hakimi tare da maƙwafta,waɗanda Inna Mairo tabi gidajensu tayi musu sallama suka yo musu rakiya har bakin mota. Masu sharan hawaye irin su Inna Kareema nayi, masu kuka sosai irin su Hanne da Lubah ma nayi.A haka su Najma sukai sallama da kowa suka shige mota,tana ji tamkar tayi zamanta a ƙauyen garin giwa.Amma kuma can ƙasan zuciyarta tana son cigaban rayuwarta ta fannin samun ilimi mai zurfi da take da buri.Anty Hannah tausayin Najma ta dinga ji tunda Inna Kareema ta bayar da labarin wahalar da suka sha,ta kuma gane cewa marainiyace bata da uba.Daddy bayan uban kayan abinci da suturu da aka kaiwa Hakimi, sai da ya bashi kyautar kuɗaɗe masu yawa tare da yin alƙawarin ɗaukar nauyin karatun Yaya Auwalu har ya kammala idan ya samu addimision.Sun kamo hanya Najma na faman share hawaye,domin su Lubah sun gama karya zuciyarta da irin kukan da suke na rabuwa da ita,kai kace an rabu kenan har abanda ba za a sake ganin juna ba.Gwaggo dasu Momy har ma da Daddy ne suka dinga rarrashin su Inna Mairo,don ita ma lokaci bayan lokaci take kai bakin mayafi ta share hawayen dake zubo mata. Hawayen da ke fita tare da jin tarin kewa da alhinin

Please Login or Register in order to submit comment