Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cusguna mana ta hanyar jifanmu da alkaba'i kala da kala. Ƴaƴanta su Yaya Kabeeru sam basa sakin ma Malam Mahmuda fuska,domin Gwaggo ta riga ta cusa musu ƙinsa ta hanyar sanar musu cewa basa gaban Abbah kamar yadda wannan ɗan almajirin maɗinkin ke gabansa. Yanayin yadda Abbah ke daidaitasu a komi yana kuma nuna musu cewa su ɗauki mahaifinki tamkar ƙani a garesu, sai hakan ya sanya suka gasgata maganar Gwaggo na cewa Malam Mahmuda ba ƙaramin shiga zuciyar Abbah ya yi ba, tunda har yake ƙoƙarin ganin ya cusa soyayyarsa a zukatansu. Hakan ya janyo suke jin kishinsa a zuciyarsu har ya kai basa ƙaunar suzo weekend su haɗu da shi a falon Abbah,bare har Abban ya tasa su da tarin nasihunsa yana kwaɗaitar dasu su haɗa kawunansu.Duk bayan sati biyu ko uku Malam Mahmuda ke haɗa shatara ta arxiƙi ya nufi garin giwa wajen ƙanin mahaifinsa Malam Lawal, ya kanyi kwanaki biyu ko uku sannan ya juyo kaduna. Sosai sana'arsa ta ɗinki da noma da ya fara gwada yi a gonar Abbah da ke cikin hayi ya bunƙasa, yana samun kuɗi sosai da gaske.Musamman da ya kasance Malam mai mutane ne kuma yana yawan tallata masa sana'arsa ta ɗinki, ta yadda yake samun ƙarin customers. Ina SS2 a secondary school wani cousine ɗin Gwaggo mai suna Fahad ya bijiro da zancen cewa yana sona, hankalina ya yi masifar tashi don na nafi kowa sanin Fahad bashi da kamun kai. Sabida akan kunnuwa na sha ji Gwaggo da ƴan uwanta idan sunzo suna zancensa. Yana da kuɗi domin matuƙin jirgin samane da ke ganiyan ƙuruciyarsa,don a shekaru ba zai wuce ashirin da biyar ba a lokacin. Gwaggo duk tabi ta gigice da wannan zance na Fahad don tana cikin irin matannan masu shegen kwaɗayi da son abin duniya.Ban taɓa sanin Gwaggo ta iya magana mai daɗi da nuna kulawa ba, sai da Fahad ya mato a kaina. Ta dinga sanyani a ɗaki tana min romon baka akan in amince da ɗan uwanta domin idan na aureshi ba ƙaramin hutawa zamuyi ni da ita ba. Ni dai bana iya ce mata komi domin tsoranta ya riga ya ginu a zuciyata, sannan ni sam bana sha'awar aure a wannan lokacin.Na fiso in zurfafa karatuna kamar yadda dukkanin ƙawayena ke da buri, amma abinda ban sani ba ni shine shi kansa Abbah bashi da burin barina nayi zurfin karatu a gabansa. Ban san hakan ba sai da Gwaggo ta tunkaresa da batun Fahad, sai ya sanya ta kirani don yaji ta bakina. Amma duk yadda yaso ince wani abu a gaban Gwaggo kasawa nayi, don ina tsananin tsoronta da kuma fargabar yadda zan sanar da Abbah cewa bana son Fahad ɗin. Gwaggo sai ta bamu waje tana cewa Abbah ya bini a hankali yaji ta bakina, a tunaninmu duka ni da Abbah ta bar falonsa baki ɗaya ta shige daga ciki.Ashe laɓe tayi tana sauraran dukkanin abinda muke tattaunawa da Abbah. Ban san hakan ba don dana sani ba zan taɓa iya buɗe baki in yiwa Abbah bayanin cewa bana son Fahad ne sabida bashi da kamun kai kamar yadda naji su Gwaggo na faɗi ba. Abbah ya kwantar min da hankali tare da sanar dani cewa bashi da burin nayi zurfin karatu a gabansa sai a ɗakin mijina, sabida haka idan har bana son Fahad inyi ƙoƙari kafin mu fara zana jarawar waec ya zama ina da tsayayye. Idan so samune nema in samu mijin da za a haɗa bikinmu ayi rana ɗaya dana Yaya Kabeer, wanda aka sanya masa ranar aure watanni biyu da suka wuce. Ƴar wani mai kuɗice ya samo a garin katsina daga zuwa ɗaura auren abokinsa ya haɗu da Yarinyar, Babanta mai kuɗine ɗan siyasa wanda ke riƙe da muƙamin kwamishinan ilimi na garin katsina. An sanya ranar auren ne watanni biyar kacal, shi ma ba don iyayenta sun so hakan ba sai don Gwaggo da ta kafe ba za a sanya mata biki ba tare da an bata isasshen lokaci ta shiryawa bikin ba.Hankalina ya tashi da maganar Abbah, domin ni bani da wani saurayi don ban taɓa kula kowa ba, hasalima duk kyawun da nake dashi bani cikin irin masu farin jinin da za a ce duk inda suka shiga sai sun saurayi ba. Fahad shi ne na farko da ya fara tunkaroni da batun soyayya, kuma akai rashin sa a bai taɓa birgeni ba bare har naji cewa zan iya bashi zuciyata. Na fito daga falon Abbah bayan ya sallameni ina jin kaina na wani irin juya mini,na wuce zuwa ɗakina ba tare da na san cewa Gwaggo ta gama jin komi da muka tattauna da Abbah ba. Washegarin ranar ina cikin saka uniform sai gata kamar an jefota ta shigo mini ɗaki, kallo ɗaya nayi mata naji wani irin faɗuwar gaba da tsoro sun shigeni. Sabida gabaki ɗaya fuskarta a haɗe take babu ɗigon annuri.Ta samu gefen gado ta zauna tana cigaba da kiɗima zuciyata da mummunar kallon da take jifana dashi. Ko gaisuwata bata amsa ba ta fara buɗe mini wuta akan cewa ban isa na wulaƙantata nace ba zan aminta da jininta a matsayin miji ba, inda take shiga banan take fita ba tana zagina tana zagin uwar data kawo duniya.Daga ƙarshe ta bani umurnin cewa inje da kaina in sanar da Abbah cewa ina son Fahad, don Fahad ɗin ya matsa mata a kaina ya kuma ce yana so da zaran na kammala skull ne muyi aurene. Na rasa bakin magana sai kuka da nake yi tun fara balbalin faɗan da take mini.Ta fita ta barni cikin tashin hankali ina kuka mai yawa, domin bansan yadda zan ɓullowa lamarin ba. Daga ƙarshe dabara ta faɗon mini akan in samu mahaifinki in nemi shawaransa akan yadda zan ɓullowa lamarin Gwaggo har na kuɓuta daga tarkon da take son jefani ciki, na son in auri mutumin da tafi kowa sanin cewa bana gari bane. Bayan na dawo school sai duk na ƙosa su Abbah da Yaya Mahmuda su dawo kamar yadda nake kiran mahaifinki a lokacin, sabida har cikin zuciyata matsayin Yayana na jini na ɗaukesa. Don yadda nake jinsa a zuciyata ma bana jin su Yaya Kabeeru haka, sabida sam su basu taɓa nuna mini ƙauna ba bare su nuna kulawarsu a kaina ba. Shi kuwa har kuɗi yake kashe mini yana mini siyayyan kayan kwaɗayi dana ƙyale-ƙyalen mata kala kala. Bai jin ciwon kashe mini ko nawane matuƙar ya yi niyyar hakan. Dana samesa da batun shi ya bani shawaran in bida Gwaggo a yadda take so, in yaso shi Abbah sai inyi magana dashi mu haɗa baki ya nunawa Gwaggo cewa shi da kansa ya yi bincike ya gano cewa Fahad ba mutumin kirki bane,don haka ba zai bashi aurena ba koda ni ɗin ina ƙaunarsa. Wannan shawara ta Malam Mahmuda ya kwantar mini da hankali tare da jinjina hikimar da yake da ita, don koda na sanar da Abbah ga buƙatata shi ma ya yi mamaki har saida ya tuhumeni wanda ya iya shirya mini wannan dabarar. Na sanar dashi cewa Yaya Mahmuda ne, sai naga ya yi dariya mai yawa kafin ya sallameni ya ce in tashi in tafi zai yi magana da Gwaggon. Na tafi ɗakina zuciyata wasai tamkar an cire mini wani dutsen da ya danne zuciyata, domin kwana biyu da damuwar maganar Gwaggo nake kwana na tashi.Na dinga kasa kunni ko zan ji Gwaggo ta sake tarata da maganar Fahad amma sai naji shiru, sai dai ta ninka tsanar da take mini a baya don ko gaisuwata daina amsawa tayi. Abu kaɗan zanyi na kuskure zata kifeni da mari ta shiga zagina tana kirana dangin mayu masu baƙin hali. Abin na mini ciwo amma haka nake dannewa, sai dai in shiga ɗaki inyi kukana na share hawayena. Cikin kwanaki ƙalilan duk na rame sabida damuwa da shiga ƙuncin yadda Gwaggo ta uzzura mini, sam bani da sukuni inba ina makaranta bane. Amma da zaran na dawo gida bani da sauran kwanciyar hankali. Abbah da kansa ya fahimci ina cikin damuwa, kuma ya san ba zai wuce dai akan zancen Fahad bane da ya kashe maganar. Don ya sanar da Gwaggo ba zai taɓa bai wa ɗan giya auren ƴarsa ba koda ace zan mutu da soyayyarsa ne,sannan ya yi mata kyakykyawar gargaɗin ya daina zuwar masa gida ma baki ɗaya.Don da gaske Abbah ya yi bincike a kansa, ya kuma gano cewa ɗan giyane tantiri na gaske. Ya kirani Ya yi mini faɗa da nasiha akan muhimmancin maida lamura zuwa ga Allah, sannan ya nusar dani cewa a komi na rayuwa in dogora da cewa komi NUFIN ALLAH ne bana mutum ba. Kome kaga ya faru da bawa NUFIN ALLAH ne idan ya NUFA abu Ya kasancewa,kasancewa yake ko mutum naso ko baya so. Haka idan bai Yi NUFIN abu ya kasance ba ko duniya sun taru basu isa sawa ko hana wannan abun kasancewa ba.Don haka in sanya haƙuri da dangana In Sha Allah! Fahad ba zai zamo mijin aurena ba. Anan ne kuma ya sanar dani ya yanke shawaran zai zaɓa mini mijin da yake ganin ya dace dani, don yana so ya aurar dani don kawo ƙarshen ƙiyayyar da Gwaggo ke mini da kuma kawo ƙarshen wannan dambarwa na magana ɗan uwanta, domin ta gane cewa da gaske yake ba zai taɓa bashi aurena ba. Hankalina maimakon ya kwanta sai ma ya sake tashi Najma, domin na sanya zullumi a raina na waye zaɓin da Abbah zai mini alhali na sanar dashi bana ra'ayin aure karatu nake so. Haka nan dai na dinga ɓoye damuwata amma a tsaye duk na rame duk da cewa ba wani ƙibace dani ba dama, amma dai nayi rama don ada ina da murjajjen jikin da ko ƙashin wuyana ba a gani.Duk wanda ya ganni ya san ina da damuwa dannewa kawai nake yi, amma Gwaggo bata taɓa zama dani ta tambayeni miye damuwata ba. Burinta bai wuce in bijerewa Abbah in auri ɗan uwanta don biyan buƙatan kanta ba, ni kuma banyi yadda take so ba shiyasa ta ninka tsanata ni da mahaifinki don ta fito fili ta ce shi yake sake hure mini kunni. Bayan wani lokaci kaɗan Abbah ya gabatar mini da zaɓinsa.......

Inna Mairo ta ɗan dakata kaɗan tana ɗaura manyan idanunta akan Najma,wacce duk ta ƙagara taji ƙarshen tarihin rayuwar Inna da mahaifinta. Ta dubi Inna cike da jin wani irin tausayinta ta ce, "Waye zaɓin da akai miki Inna?" Inna Mairo ta jinjina kai tana danne dukkanin raunin da ya bijiro mata na tunawa da gwarzon mijinta Malam Mahmuda. Ta dubi Najma tana mai cigaba da faɗin, "Mahaifinki shi ne zaɓin da Abbah ya yi mini Najma, wanda da fari na so na bijire domin ni a matsayin Yayana na jini na ɗaukesa. Amma daga baya sai naji zuciyata ta aminta dashi, muka fara fahimtar juna ni da shi. A hankali kuma soyayyarsa ta fara shigata wacce jigonta ƙaunace matuƙa da gaske, kamar yadda na fahimci shi ma ya jima yana ƙaunata da sona a cikin zuciyarsa. bai samu damar bayyanawa bane sai da Abbah ya furta masa ƙudirinsa na son ya haɗamu aure, anan ne ya amsa tayin Abbah cikin matuƙar farin cikin da Abbah bai taɓa gani akan fuskarsa ba. Malam Lawal takanas ya yo yazo ya yiwa Abbah godia mai tarin yawa, domin lamarin ya faranta ransa duk da cewa ba a kai ga sanya lokaci ba.Don Yaya Mahmuda ya ce sai ya kammala gininsa na zamani da ya ɗakko yi a garin giwa,sannan sai ayi auren hakan zaifi masa daɗi da kwanciyar hankali. Gwaggo a lokacin da hukuncin Abbah yaje kunnuwarta na cewa Malam Mahmuda ne zaɓinsa,kuma nima na amince da shi a matsayin wanda zan aura, sai taji tamkar ta haɗamu ta kashe ko zata huta da ƙiyayyarmu a cikin zuciyarta. Tun daga ranar ta ɗaura ɗammaran sake cusguna mana,daga ni har mahaifinki bamu sake jin daɗin zama da Gwaggo ba.Tsakaninmu da ita zagi da habaici ne kala-kala. Ta dinga jifan mu da kalamai marasa daɗi tana mugun fata,tare da kushe mahaifinki ba dare ba rana.Kullum sai ta tsinesa ta ce Allah ya yi wadaran zaɓin Abbah, Ya rasa wanda zai zaɓa mini sai baƙin munafukin almajirinsa wanda bashi da komi sai sana'ar ɗinki. Ta raina mahaifinki ta kuma raina arziƙinsa, don gani take duk abinda ya mallaka bai wuce ya zama mai wanki da gugan Fahad ba.Ni kuma abin na mini ciwo matuƙa,domin da gaske zuciyata har cikin zuciyata nake jin zafin yadda Gwaggo ke tsinan Malam Mahmuda. Ana cikin maganar sanya mana rana ne bikin Yaya Kabeeru da zaɓinsa mai suna Zainab ya zo, aka shiga hidima baji ba gani.Kan Gwaggo ya fara ɗaukar caji, hakan ya janyo ni da mahaifinki muka samu lafiya daga tujararta. Shiri ake wa bikin sosai domin ƴar masu dashi ne zai ɗakko, kuma shi ma ya tara kuɗi sosai tunda albashinsu mai tsokane. Tuni ya kama hayar gida mai kyau a cikin garin kaduna, wata unguwa da ake cewa Malali. Bikin na saura kwana biyar gidanmu ya fara ɗaukar baƙi, mutananan Dukku dangin Abbah tsiraru da suka rage duk sun sauka ana ta hidima. Haka ƴan uwan Gwaggo na kusa da nesa duk sun fara hallara, sai shiri akeyi na aurar da ɗan gaban goshin Gwaggo.Domin tana tsananin son Yaya Kabeeru sabida yana kyautata mata da bata kuɗi sosai. Sannan yana mata biyayya baya tsallake maganarta, duk abinda ta zana masa shi yake yi saɓanin Yaya Ali dake da zuciya da saurin hasala. Anyi biki lafiya an kawo Amarya daga katsinan Dikko.Mun yi kallon arziƙi a ɗakinta domin an kashe mata dukiya matuƙa da gaske.Taro ya watse cikin aminci sai kuma jiran namu lokacin wanda aka sanya rana watanni takwas masu zuwa.Ranar ɗaura auren Yaya Kabeeru aka bi ƴan uwa da minti da goron sanya rana. Aka dinga taya ni murna yayinda wasu dangin Gwaggo da suka san da zancen Fahad suka tasani da tsina da haibici kala-kala.Ni dai hakan bai dameni ba, don ji nake yi duk ma na ƙosa ayi auren na bar wa Gwaggo gidan kona huta da wannan ƙiyayya nata dana danginta.......✍🏻


🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻*
*MTN*
*GLO*
*AIRTEL*
*9MOBILE*
*MONTHLY VADILITY 💃🏻*

*DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻





#Lovestory#
#Najma..AD#
#Aysha Ɗansabo lemu🥰
[2/28, 2:30 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻
_*Arewabooks@ayshadansabo*_

*Paid book:500*

*Chapter 5*

_Free page_


Na cigaba da zuwa school ɗina bayan baƙi ƴan biki sun kama gabansu, muka maida hankali wajen shirya-shiryen jarabawar waec da zamu fara bada jimawa ba. Malam Mahmuda sai ya maida hankalinsa kan gininsa da yake yi a garin giwa, domin ya sanar da Abbah cewa yafi sha'awar ya kai Iyalinsa mahaifarsa ya zauna kamar yadda shi ma Malam Lawal yake da buƙata. Sabida bashi da ɗa shi kaɗai yake kallo a matsayin jininsa, don haka baya buƙatar ya aje Iyalinsa a bariki yafi sha'awar ya kawota gida in yaso sai ya dinga zuwa yana komawa kaduna wajen sana'arsa. Abbah bai yi musu ba bai kuma ji komi don za a ɗaukeni daga birni kamar kaduna a kawoni ƙauyen giwa ba.Ni ma da yake ƙauna da soyayyarsa sun rufe idanuna, ban taɓa jin cewa wai ci baya bane don na dawo ƙauye da zama na baro birni. Gwaggo na jin zancen cewa a ƙauye za a ajeni ta sake samun makamin yaƙata da kalamai marasa daɗi,tana mini gorin kaicona da zan ƙare a ƙauye,dama ta san tunda na liƙewa wannan baƙin almajirin matsiyacin Yaron, to lashakka sai ya gurɓa rayuwata domin a kyawuna da zubin halittar da Allah Ya yi mini ban dace da lusarin ɗan ƙauye kamar mahaifinki ba. Ranar da tayi mini wannan cin mutunci ɗaki na shiga nayi kuka tamkar ba zan daina ba, nayi kuka har dana rashin Iya da nayi don da tana raye tabbas ba zan fuskanci irin wannan ƙiyayyar da cin mutuncin da Gwaggo ke mini ba.

Malam Mahmuda ya nuna mini zanen gininsa da yake har ya yi nisa an kusa yin rafta, gini mai kyau da tsari irin zamani yake yi.Babu wanda zai ce a ƙauye ne idan aka kammala shi,hakan dana gani sai hankalina ya sake kwanciya tunda naga cewa ba a mummunan waje zai aje ni ba bare burin Gwaggo ya cika na son ganin rayuwata ta tagayyara idan na auresa. Mun kammala zana jarawar waec ɗinmu a lokacin bikinmu saura watanni huɗu, zuwa lokacin Malam Mahmuda ya kusa kammala gininsa. Don har an rufa kwano anyi filasta da komi, saka tiles da sauran finishing ne kawai ba a ƙare ba,hatta ƙofofi da windows duk an sanya.Baya zama sam a kaduna yanzu sosai, kullum yana hanyar giwa don shirye-shirye. Yara ya zuba a shagon ɗinkinsa suna aiki kuɗi na taruwa, sai dai shi ya leƙo ya yi wasu ayyukan na manyan mutane da ke bashi ɗinki ya juya garin giwa. Ni kaina sai ya kasance munfi yin waya don baya ma son zuwa gidanmu sabida habaicin da Gwaggo bata gajiya da sakin mana, tunda a falon Abbah muke zama kuma sai ta san yadda aka yi ta shigo idan muna tare ta yada habaicinta ta fita. A haka lokaci ya ja biki ya gabato ya rage saura sati biyu, tun kuma ana saura sati uku jama'ar giwa suka kawo kayan lefe na gani na faɗa. Sabida Malam Mahmuda da kansa ya haɗa kayansa a nan garin kaduna, shi ya samu wata wayayyar mace cikin masu kawo masa ɗinkunan yaransu, ya roƙeta akan ta taya shi haɗa lefe aurensa ya tashi. Ta kuwa tsaya tsakani da Allah ta dinga zaɓar masa kaya masu kyau da nagarta.Shiyasa kayan suka zama a tsare daidai dana mai rufin asiri. Duk yadda Gwaggo taso kushe kayan bai samu ba, domin ƴan uwanta kansu da suka ga kayan sunyi mamaki sabida sun raina arziƙin Malam Mahmuda. Abbah ya kammala siya mini komi na kayan ɗaki, babu abinda bai siya mini ba tun daga kan kayan kicin har zuwa gadaje da kujeru. Yaya Kabeeru da Yaya Ali sun yi bajinta suma domin a wajensu Abbah ya amsa dukkanin kuɗaɗen da ya siya mini kayan, sabida ya ce musu sune zasu aurar dani bashi ba tunda Allah yasa sun kawo ƙarfi kuma suna da babban aikin da suka tara rufin asiri. Gwaggo sam bata san sune suka bada kuɗin da Abbah ya ragargaza mini siyayyar kaya na ƴaƴan gata ba, don da ta sani baƙin cikin da zata shiga sai yafi wanda tayi, sabida a hakan ma bata sani ba na sha tsina da zagi tana ce mini na zame mata baƙin ciki a rayuwa. Har taba cewa watakila uwata mayyace, kafin ta rasu sai da ta lashe kurwar Abbah ta yadda ko bata a raye abinda ta bari kawai zai dinga kallo da mutunci. Ni dai tun lamarinta na sanya ni kuka har na dake, don na gane cewa ƙiyayyata a zuciyar Gwaggo na musammance,duk kuma abinda zan mata na kyautatawa ba zai goge wannan ƙiyayyar ba. Wata Innar Abbah mai suna Inna Larai ita ce ta zo daga Dukku ta fara gyareni, don Gwaggo cewa tayi babu ruwanta da hidimar aurena kada ma a sanyata a komi na hidimar bikin don ba za tai ba. Tunda har naƙi ɗan uwanta na tozartata, to itama tabbas ba za ta taɓa shiga sabgar aurena da Yaron da take jin tsanarsa har cikin zuciyarta ba. Tunda tayi waɗannan kalaman a gaban Abbah ya ce kar a sake sanyata a harkar komi, a zuba mata ido tayi duk iya rashin mutuncin da taga dama aure ne dai babu fashi. Gwaggo sai ta sake tunzura ta kuma sake janye jikinta, ta zubawa dangin Abbah da wasu daga cikin na Innata da suka zo daga Dukku ido.Suka dinga hidimarsu cikin kwanciyar hankali domin Abbah ya sakar musu bakin aljihu sosai, don ya sake ƙuntata zuciyar Gwaggo. Ranar da aka tafi jere aka dawo kwana aka yi ana yaba kyawun gidana da irin dukiyar da Abbah ya zuba mini. Masu babbar waya a cikinsu har vedio suka yo, aka kuma samu wacce ta kunnawa Gwaggo ta gani. Aiko sai zuciyarta ta sake tunzura, ta dinga cewa wannan gini ba dai Malam Mahmuda ne ya yi ba,Abbah ne ya kwashe kuɗinsa ya bashi. Kuma kayan ɗakin ma tasan sai da aka matse ƴaƴanta aka amshe musu ƴan kuɗaɗensu, don kawai a tozartata a nuna mata cewa bare yafi ƴaƴanta matsayi. Babu wanda ya biye mata bare ayi tashin hankali da ita, aka barta tayi mitarta har ta gaji bata samu abokin tayi ba. Abbah bata ga fuska a wajensa ba, domin ya iya da ita baya sauraren duk wani shirmenta.Hakan ya sanya ta sake jin tsanar aurena da Malam Mahmuda ya sake ninkuwa a zuciyarta. Matar Yaya Kabeeru zuwa lokacin har ta samu ciki wata biyu, mace ce mai kirki da fara'a sam bata da damuwa domin ko irin rawar kai irin ƴaƴan masu kuɗi ita bata dashi. Duk yadda take mini fara'a na kasa sakin jiki da ita sabida Gwaggo, na sani ba za ta taɓa bari alaƙar aminci ya shiga tsakanina da matar Yaya Kabeerun ba sabida ƙiyayyarta a gareni. Don haka sam ban yaudari kaina ince zan dinga cusa kaina a wajent ba, tsakanina da ita gaisuwar mutunci ce sosai muke yi.Koda bikina ya gabato kuma ta kawo mini kayan decor na ɗaki masu tsada da kyawu, ta kuma sanya Yaya Kabeeru ya bani kuɗi masu yawa har nayi mamakin hakan. An ɗaura aure lafiya a babban masallacin da ke hayin rigasa, bayan ɗaure auren bada jimawa bane kuma aka ɗaukeni daga kaduna a kawo garin giwa, bayan na sha tarin nasihu da addu'o'in fatan alkhairy daga Abbah. Gwaggo koda wasa bata sanyawa aurena albarka ba bare tayi mana fatan alkhairy, koda aka kaini ɗakinta muyi sallama cewa kawai tayi in sauka lafiya tana mini kaicon rayuwar ƙauyen dana zaɓawa kaina. Nayi kuka tamkar zan haɗiyi zuciyata sabida kalaman Gwaggo sun raunata zuciyata matuƙa, na dinga ayyanawa a zuciyata wani irin ƙiyayyace Gwaggo ke wa Innata da har ƙiyayyar yake bibiyata? A haka muka iso garin giwa kaina na matuƙar ciwo sabida kukan dana sha. Mun samu kyakykyawar tarba daga ahalin Malam Mahmuda,akai ta shigowa ɗakin Inna Hanne inda aka saukeni don ganin Amarya. A gidan na kwana aka yi buɗan kai na al'adah kafin ƴan uwana da suka kawoni suyi haramar juyawa kaduna.Dama kuma mutum huɗu ne suka rakoni sai ƙawata Hafsa wacce da ita kawai nafi shaƙuwa a school. Da yamma sakaliya Inna Hanne da matar Hakimin giwa mai suna Gwaggo Salamatu suka yi mini rakiya zuwa ɗakina. Kowa ya ga gidana sai ya san cewa daga birni aka ɗakkoni, birnin ma kuma gidan rufin asiri da wadata domin an kashe mini dukiya a ɗaki sai dai maƙiyi ya kushe. Duka dangina da suka rakoni kafin su tafi dama sai da suka je ɗakina suka ga irin kyawun da ya yi, kowa ya tafi yana sambarka domin faɗi suke babu mai cewa a ƙauye nake idan yana cikin gidana don komi yaji sai sambarka. Inna Hanne da matar Hakimi sun tafi sun barni tare da wata budurwa mai suna Kausar, wacce Inna Hanne ke riƙonta, ita zata tayani zama kafin zuwa dare ango ya shigo ɗakinsa. Na dinga kuka ina sharan hawaye, kewar Abbah na rufar mini tamkar in rufe ido in ganni a kaduna. Misalin ƙarfe tara na dare su Haruna ɗan gidan Hakimi da sauran abokanansa suka rakosa, bayan sun sayi baki suka yi mana addu'o'in fatan alkhairy tare aje min ledojin kaji da kuɗi suka tafi abinsu. Malam Ya yiwa Kausar rakiya har zuwa gidan Inna Hanne, sannan ya dawo ya kulle gidan ya shigo cikin zumuɗi.....

Inna Mairo

Please Login or Register in order to submit comment