Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wata tambayar ta ce, "Mai ya faɗi da ki ka ce ni ce na ce ki taho?" Hannah ta ɗago kai ta dubi Momy tana kallon yadda ta haɗe fuska alamun bata son wasa.Sai ta samu kanta da son miƙawa Momy wayar don ta karanta reply ɗin da ya yo mata, sabida ba za ta iya maida mata da baƙaƙen magangun da ya faɗi mata ba.Text ɗin ta buɗo iya inda ya aiko reply ɗin, ta miƙawa Momy wayar tana faɗin, "Gashi ki karanta Momy." Babu musu Hajiya Zainab ta karɓi wayar tana karanta abinda AD Dukku ya aiko.Ta jinjina kai bayan gama karanta saƙon,ta maida dubanta kan Hannah tare da miƙa mata wayarta ta ce, "Muje ɗakina muyi magana Hannatu!" Hannah ta miƙe ta rufawa Momy baya zuwa bedroom ɗinta, don bata buƙatar su Nasreen su fito suji me suke tattaunawa da Hannah ɗin. Bayan Momy ta zauna a bakin bed, sai Hannah ta zaɓi zama bisa sofa tana ji dukkanin jikinta na yin sanyi matuƙa. Momy ta dubeta cike da jin tausayin yadda take ɗawainiya da soyayyar gudan jininta, amma shi sam ba ita bane a gabansa wulaƙanci kawai yake mata son ransa.Tayi gyaran murya tana farawa da faɗin, "Hannatu shi namiji baka yadda ka nuna masa muguwar soyayyar da zai gane baka da wani abin so sai shi, ƙoƙari kake yi ka dinga dannewa soyayyarsa a gaban idanunsa tare da saita kanka ta yadda ba zai fahimci kayi nisa a ƙaunarsa ba,bare har ya gano lagonka da zai dinga ƙuntata zuciyarka da wannan soyayyar da kake yi masa ba.Adnan ɗana ne da ya fito daga jikina tabbas! Sai dai ki sani makauniyar soyayyar da ki ke nuna masa na rashin iya riƙe kai da ajinki sam baya birgeni, domin halin maza duka ɗaya ne indai akan mace ne. Dole ki koyi danne dukkanin soyayyar da kike masa, ki daina nuna masa sai dashi zaki rayu ko in bashi ba zaki iya rayuwa ba.Hakan da kike nuna masa ya sanya har ya fara baki zaɓin ko zama dashi ko kuma kiyi abinda shi yake so, ba tare da la'akari da girman zunubin da zaku aikata inda kin biye masan ba.Ki manta dashi ko sau ɗaya karki yadda ki kira wayarsa ko turo masa saƙo, ko shi ne ya kira ban amince ki ɗaga wayarsa ba.Ki bai wa banza a jiyarsa daga nan har ranar da zai kawo kansa garin da ƙafafunsa, idan Gwaggo ta tambayeki mai kika zo yi ki sanar mata cewa shi ne kawai ya ce kizo zai biyo bayanki daga baya.Ban yarda ki sanar mata komi ba sai idan shi ne ya sanar mata, nima kuma idan ta tambaya abinda zan sanar mata kenan.Ban amince ki sanarwa Hajiyarku ko Laurah ba, don wannan abin kunya ne da dariya a gareki ace miji ya baki zaɓin ko rabuwa da ciki ko zaman aurensa.Alhali watanni biyu kacal akai da auren bama shekaru biyu ba, don haka ban amince susan wannan maganar ba har zuwa sanda xaki koma ɗakinki ko kiyi zamanki a part ɗinku shi ya dinga zuwa miki weekend ko duk bayan sati biyu ne.Amma ciki da aurensa duka kin zaɓa zai kuma zo ya sameni,shi ma kuma Daddy yana jirace dashi ɗin don na sanar dashi komi jibi zai dawo daga Abujan." Momy ta dakata da maganar zuciyarta na matuƙar sosuwa da rashin kirkin AD, da yadda yake wulaƙanta Ƴar ƙawarta ta arziƙi Hajiya Halima.Wacce ke matsayin matar aminin mijinta da suke zuba abin arziƙi sosai da ita,amma ace ɗan cikinta da ta haifa ne ke wulaƙanta mata Ƴa ai hakan babban abin damuwa da tir ne a gareta.Ko kaɗan Adnan baya mata adalci akan wulaƙanta Hannah da yake don kawai an jarabci zuciyarta da soyayyarsa,ba don ta rasa tarin masoya ba sai don kawai shi ɗin ne ta mato a kansa har ta zaɓi aurensa ido rufe, ba tare da ta duba girman kuskuren auren wanda bashi ya ce yana ƙaunarka ba. Hannah ta jinjina kai hawaye na bin fuskarta, tana jin dukkanin jikinta na sake mutuwa da ƙaunar AD Dukku da bata taɓa ganin aibunsa ba.Duk yadda yake wulaƙantata ta kasa rage soyayyarsa a zuciyarta, sai ma gani take tamkar kullum kwanan duniya ninka mata a ƙaunarsa ake yi.Amma tabbas kamar yadda Momy ta buƙata haka za ta yi, dole ne ta koyi riƙe kanta da danne ƙarfin soyayyarsa a zuciyarta matuƙar tana son ta tsira da sauran mutunci a idanunsa,ta yadda zai fara shakkar yi mata wasu kalolin wulaƙancin nasa.Cikin rawar murya take wa Momy godia tare da tabbatar mata da cewa zata yi duk yadda ta buƙata ɗin. Daga haka Momy ta ce mata ta kwanta ta huta abin ta, za ta sanya yanzu a kawo mata snacks ko zata iya ci.Ta fito ta bar Hannah tana faman sauke ajiyar zuciya a hankali, idanunta kuma na hasko mata kyakykyawar fuskar AD Dukku da yadda ya haɗe fuskar a ɗazu da safe yana mata masifarsa da ke kiɗima zuciyarta.Ta lumshe idanunta tana kai hannu ta shafo cikinta, wani irin sanyin ƙaunar cikin da uban cikin na sake keta zuciyarta da shigewa jinin jikinta baki ɗaya. Rabi Momy ta aiko da ƙaramin tray mai ɗauke da plate ɗin da aka zubo samosar ɗazu da suka yi tare da Najma,sai dambun naman kaza da aka yi ya ji spices.Gefe guda an ɗauro table water da sassanyar lemun abarba na gwangwani.Hannah ta gaida Rabi da girmamawa, kafin ta juyo ta fito daga ɗakin baki ɗaya.Hannah na yiwa dambun naman kallo ɗaya taji miyanta ya tsinke, ta kai hannu ta damƙoshi tana kaiwa baki ta fara ci.Daɗinsa da ƙamshin spices ya dinga ratsata,tana sake kai hannu ta damƙo ta kai baki. A haka Nasreen ta turo ƙofar ɗakin ta shigo tana sauke idanunta akan Hannah ta ce, "Anty Hannah hutawa ake a ɗakin Momy haka?" Hannah ta gyaɗa kai tana sakin murmushi ta ce, "Na gaji ne Sis,ga kaina da ke ciwo shiyasa Momy ta ce nayi kwanciyata na huta a nan ɗin." Nasreen tayi mata sannu tana zama kusa da ita ta ce, "But nayi mamaki zuwa ba sanarwa sai dai mu ganki daga sama, hala an tura Yayan aiki wani garin ne ya ce kiyi tahowarki?" Hannah ta sake sakin murmushi cikin son danne damuwarta ta ce, "Eh Nasreen,ina black beauty Sis ɗin naku ta shige?" Nasreen ta saki wide smile tana faɗin, "Najam wai? Ta gudu ɓangaren Gwaggo wajen Innarta." Hannah ta ɗan yi murmushi ta ce, " Nima zuwa anjima zan shiga wajen mutuniyar ai." Nasreen ta sake dariya tana faɗin, "Su Gwaggo manyan ƙasa, sweet heart ɗin na Yaya AD ba.Ayi tsiya ai daɗi, amma duk rashin kirkin da zai mata bata gani,kana magana abu ya juyo kanka." Suka saki dariya sosai, suna tuno kalar dramar da ake sha tsakanin Gwaggo da AD Dukku, wanda sam baya laifi a wajenta. Sai bayan sallar magriba Nasreen ta raka Hannah zuwa ɓangaren Gwaggo don ta kwashi gaisuwa.Sun samu Gwaggo na ɗaki bata fito ba, da alamu sai ta yi sallar isha'i zata fito su taru suyi dinner dasu Inna kamar yadda suka sabayi yanzu da suka dawo nan ɗin......✍🏻




*Pay 500 in to this account number👇🏻*
*0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank*
*OR*
*PAY IN TO DIS ANOTHER ACCOUNT* 👇🏻
*8167768704 AISHA* *DANSABO IBRAHIM*
*ACCOUNT NAME:OPAY*
*Evidence of payment to this number:08167768704*


🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻*
*MTN*
*GLO*
*AIRTEL*
*9MOBILE*
*MONTHLY VADILITY 💃🏻*

*DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻



#Lovestory#
#Najma#
#Aysha Ɗansabo Lemu🥰
[3/12, 10:48 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻 *Arewabooks@ayshadansabo*

*Paid book:500*

*Chapter 17*

_Free page_

Su Inna Mairo ne suka fara fitowa falon bayan sun idar da sallar isha'i kamar yadda suka saba.Sun tadda Hannah da Nasreen zaune a falon suna hiransu kafin Gwaggon ta fito.Nasreen ta gabatarwa da Inna Mairo Hannah,tana sanar da ita cewa matar babban Yayansu Adnan ne.Suka gaisa da fara'a tana tambayar Hannah ina shi Adnan ɗin? Ta sanar da Inna Mairo cewa yana can Port Harcourt ɗin bai zo ba.Hannah ta dinga satan duban Inna Mairo da Najma, tana kallon tsabagen kamanninsu da juna.Sai dai kawai bambamcin kalar skin da ke garesu, kuma ita sai Najma da take baƙa kyawunta yafi birgeta fiye da Inna Mairo da ke jinta jajir da ita.Gwaggo ta fito ta samesu suna ta zantawa da juna, ta ƙariso mazauninta da ta saba zama cikin 2 seater ta zauna.Da zallar mamakin ganin Hannah take amsa gaisuwarta tare da tambayarta ita dawa ta zo garin? Hannah ta yi ƙasa da kai tana bai wa Gwaggo amsa da cewa, "Ni kaɗai na taho Gwaggo, shi zai zo daga baya ina ga zuwa jibi weekend!" Gwaggo ta jinjina kai ta ce, "Kuma shi ne ɗazu da mukai waya bai sanar min zaki zo ɗinba? Ya sako ki a jirgi ke kaɗai kika taho ko tsoro baki ji ba?" Hannah da Nasreen suka saki murmushi,Hannah na duban Gwaggo da girmamawa ta ce, "Gwaggo ai babu wani tsoro,tunda ba daga wata ƙasa na zo ba ni kaɗai ɗin,koma wata ƙasar ce ai babu wata damuwa." Gwaggo ta jinjina kai tare da taɓe baki ta ce, "Eh! Lallai zamani ba ƙarya bane ai, ku Yaran yanzu baku san tsoro ba sabida buɗewar ido da ya yi muku yawa." Ta ƙare maganar tana bin Hannah da wani kallo na ƙurilla don son gano ko abinda take hasashe da gaske ne a jikin Hannar? Don tun kallon farko da ta yiwa fuskarta fa tara zargin da wuya ba ciki ne da ita ba.Kamar Hannah ta gano manufar Gwaggo sai ta juyar da fuskarta baki ɗaya tana facing su Nasreen da ke ta faman hira da Najma.Har aka shirya abincin dinner a tsakiyar falon suna nan zaune, Gwaggo tayi musu tayin in zasu ci a haɗu duka aci tare da juna.Nasreen da bata faye cin abincin dare ba sai wajen 10pm tayi saurin girgiza kai tana faɗin, "Sai dai ko Anty Hannah Gwaggo." Hannah ta ita ma ta girgiza kai tana faɗin, "No! Na ƙoshi wallahi, ni da abinci sai can anjima kuma." Daga haka Najma da Inna Mairo tare da Gwaggo suka haɗu suna cin abincin hankali kwance.Nasreen da Hannah sai suka yi musu sai da safe suka fice, bayan Nasreen ta jaddadawa Najma cewa tana jiranta a ɓangarensu idan ta gama. Kai kawai Najma ta gyaɗa mata amma ba don zata je ɗin ba,don bata son ta zama mai yawan shigewa musamman da yau ɗin Anty Hannah ta zo.Wacce tun daga kallon da Momy ke mata da irin yadda Nasreen ta nuna ɗoki da murnar ganinta, ta gano irin soyayyar da suke mata.Shiyasa take ganin gara ta ɗan ja jikinta yau ɗin, don basu damar sakewa da surukar tasu,kar taje tana takurasu da ganinta a kusa da su.

Gwaggo bayan sun kammala da cin abincin sai ta koma daga gefe guda ta dannawa shalelenta AD Dukku kira.Bugu biyo ya ɗaga wayar cikin sassanyar muryarsa da yake haɗawa da ƴar shagwaɓar gata idan yana waya da ita.Bayan ta gama amsa gaisuwar da ya yi mata,sai kai tsaye ta jefa masa tambayar dake mintsininta, "Adnanu ya aka yi ka baro matarka ita kaɗai ta taho maimakon ku taho tare? Kasan fa nayi kewarka wata guda kenan baka zo dubamu ba,ince dai ko lafiya ta taho ita kaɗai ɗin."

AD Dukku daga ɓangarensa ya lumshe idanunsa,yana sake gyara kwanciyarsa akan sofa dake ɗakinsa. Domin tunda aka tashi office ya dawo gidan.Ya buɗe baki cikin ƙasa da muryarsa ya sanar da Gwaggo cewa Momy ce ta bai wa Hannah umurnin tahowa, sabida sun samu ƴar hatsaniya tsakaninsa da Hannar. Gwaggo ta buɗe baki cikin matuƙar mamaki ta ce, "To hatsaniyar uban me kuma kuka yi? Nifa ka fara bani haushi da wannan ƙiyayya da kake nunawa salihar baiwar Allah.Miye aibun Hannatu ne wai da ba za ka rungumi matarka ku zauna lafiya ba?" Gwaggo tayi maganar da ɗaga sautin muryarta, hakan ya sanya su Gwaggo da ke daga can cikin falon suna jiyo duk abinda take faɗi ɗin.Ta ɗanyi jim! Da alamu tana sauraran abinda yake faɗi mata ne,zuwa can kuma ta sake ɗaga sautin muryarta tana faɗin, "To ai shikenan, ni yanzu zan je wajen Zainabun inji dalilin da zaisa ta ce wa matarka ta zo ba tare da izininka ba.In banda ma shiga uku ina ruwanta da faɗarku da har zata saka ƴar mutane kamo hanya tazo gari ita kaɗai kamar wata wulaƙantatta." Ta dakata da maganar tana sauraren yadda AD Dukku ke narke mata murya yana nuna cewa bashi da wani laifi, Hannah ɗince ta kira Momy ta sanar da ita ƙarya da gaskiya don Momy ta ji zafinsa.Gwaggo ta dinga jinjina kai kamar yana gabanta,kafin ta sake faɗin, "Karka damu zan je yanzu na ce na sameta, kai dai kawai kaxo zuwa ranar sati ɗin ina son ganinka Adnanuna.Amma kuma zamu giwa ranar asabar ɗin, Gwaggonka Mairo da na sha baka labarin tana can,to ta dawo nan kaduna da zama zamu rakata kwaso kaya suyi sallama da mutanan arziƙinta kuma.Amma hakan ba matsala bace, ka dai zo ɗin kaji ko?" Ta sake yin shiru tana saurarensa daga ɓangarensa,kafin ta sake furta, "To shikenan sai ka iso ɗin, ina fata dai yanzu duk kana rage shashancin shaye-shayen nan na zamani daka koyo a turai,don sam bana so Adnanu.Don Allah ka nutsu ka zama mutumin kirki,karka ga ina kareka idan Iyayenka na kyararka nima kaina abin yana damuna a zuci." Ta kai ƙarshen maganar tana sake manne wayar a kunni,tana cigaba da sauraran tsarin da yake mata.Ta sauke wayar a kunni bayan ya kashe,tana mai miƙewa tsaye ta kallo side ɗin dasu Inna Mairo suke.Sun maida dukkanin hankulansu akan kallon TV, Najma kuma ta kan duba wayarta jefi-jefi.Gwaggo ta ɗaga murya ta kira sunan Najma tare da bata umurnin zuwa ɗakinta ta ɗakko mata mayafi.Najma ta miƙe ta wuce don zuwa ɗakkowa Gwaggon mayafin nata, ita kuma Gwaggo ta maida hankali wajen Inna Mairo tana faɗin."Mairo ɓangaren Zainab zani yanzu in jiyo dalilin da zai sanya ta saka ƴar mutane kamo hanya tazo gari bada izinin mijinta ba, ina na taɓa ganin anyi hakan ni Hauwa! In banda dai zamani da ya lalace ma, ina ruwanta da surukar ɗan fari har da zata dinga zaƙewa a lamuransu? To bari in je mata don ba zan bari ma sai gobe ba."

Inna Mairo tayi murmushi tana duban Gwaggo ta ce, "Allah sarki Gwaggo, watakila tana ganin hakan da tayi shi ne daidai ɗin.Amma dai gara kije ki ji ɗin zai fi." Gwaggo ta ɗan kyaɓe baki ta ce, "To ai hakan ma shine gaskiya da gaskiya Mairo, in je mata ɗin tun yanzu inji dalili da abinda ya faru ɗin." Najma da ta iso da mayafi a hannu,sai ta miƙawa Gwaggo tana faɗin, "Gashi Gwaggo." Gwaggo ta amsa mayafin tana faɗin, "Wuce mu je ki rakani ɓangaren Kabeeru Najma." Najma ta amsa da, "To." Tana bin bayan Gwaggo da bata bari ko mayafi ta saka akan rigar jikinta mara nauyi da ta saka ba. Suka isa ɓangaren su Momy tana cike da mamakin yadda Gwaggo ke ta faman mita ita kaɗai,don tunda suka fito take mita da magana ba tare da Najma ta ce komi ba. A nan main parlor ɗin suka tadda su Nasreen dukkansu har da Nabeela da ba a jima da maido ta gidan ba.Momy ta tarbi Gwaggo da kulawa tana faɗin, "Barka da shigowa Gwaggo, ga wuri nan zauna nan." Ta nunawa Gwaggo kujeran 2 seater ta zauna.Ta dubi Momy ɗin tana ɗan gimtse fuska ta ce, "Zainabu wajenki na zo, maza kai ni ɗaki muyi magana in kama kaina ba zama cikin Yara na xo yi ba." Momy ta dubi Gwaggo tana ji a jikinta cewa duk yadda aka yi Adnan ya kirata ya haɗosu kenan da Gwaggon.Ta miƙe tana duban Gwaggo ta ce, "To muje ɗakina Gwaggo." Daga haka suka yi gaba zuwa bedroom ɗin Momy ɗin, suka bar su Nasreen da bin bayansu da kallo, zuciyar Hannah na cigaba da doka mata.

Gwaggo ta dubi Momy bayan shigarsu ɗakin ta ce, "Zainabu miye naki na cewa Hannatu ta kamo hanya ta taho,don kawai sun sami saɓani da mijinta?" Momy ta danne ɓacin ran Adnan da ya taso mata,ta dubi Gwaggo kai tsaye ta ce, "Au! Bai faɗi miki ɓarnar da yake shirin saka Ƴar mutane su aikata ba Gwaggo?" Gwaggo ta haɗe fuska tamau ta ce, "Ina tambayarki maimakon amsa sai kuma ki jefoni da wata tambayar Zainab? To bai faɗi mini komi ba, shiyasa ai na zo inji daga bakinki." Momy ta sauke numfashi mai ɗumi, cikin kwantar da murya ta ce, "Gwaggo so yake ta zubda cikin da ta samu, sabida wai shi bai shiryama haihuwa yanzu ba.Ni kuma tunda ta sanar mini, shi ne nace ta dawo gabanmu don kada ya tirsasata su aikata ɓarna, tunda ya fahimci ta mato a kansa zata iya aikata komi don ta faranta masa.Don Allah Gwaggo ki nuna masa ɓacin ranki a wannan karon,don na san kema ba za ki so a aikata wannan ɗanyan ɓarnar ba." Gwaggo da tunda Momy ta fara magana ta shiga shock! Sai ta riƙe haɓa tana magana a firgice ta ce, "Shi Adinanun ne ya faɗi hakan Zainabu, da bakinsa ya furta cewa bai shirya haihuwa yanzu ba don ubanshi? To wallahi ya yi kaɗan, idan ƙwayoyin da yake sha ne suke gaya masa gaibu,to ya sani sai Hannatu ta haife wannan rabon da Allan ya nufeni da rahamar zan ga jininsa a duniya." Gwaggo ta ɗan numfasa kafin ta cigaba da faɗin, "Au shine har da narke mini kamar wani mai gaskiya, lallai ko zai san cewa bana bayansa a wannan karon.Yanzu dai jeki kirawo min Hannatun ta zo inji zance dalla-dalla daga bakinta." Momy ta saki murmushi a sace tana miƙewa ta fice don kiran Hannah.Gwaggo kuwa sai faman mita take yi tana tsinewa shaye-shayen ƙwayoyin da aka ce Adnan ɗin nayi.
Lokacin da Hannah ta shigo gefen da Momy ke zaune daga bed ta zauna tana yin ƙasa da kanta.Gwaggo ta zuba mata ido tana sake gano alamun mai ciki an tare da ita ɗin.Ta wanj yi ƙasa da murya tana duban Hannah kai tsaye ta ce, "Ke Hannatu da gaske ne Adnanu ne ya ce baya son cikin da kike ɗauke dashi?" Hannah ta gyaɗa kai cike da tsananin jin kunya.Gwaggo ta cigaba da faɗin, "To kuwa wallahi bai isa ba, ai duk laifinki ne da kike nuna masa shegiyar soyayyar da baki ganin duk wani aibunsa da tsiyar da yake shuka miki.Inba ya rainaki ya gano kin gama matowa a kansa ba, har ya iya kallon tsabar idonki ya ce baya son cikin alhali shi ya ɗirka miki,ko kuwa a ruwa kika sha cikin?" Hannah dai kunya kamar ta nitse, haka ta sake dankwafar da kai ƙasa tana sauraran masifar da Gwaggo ke mata.Daga ita har Momy suka yi har tayi mai isarta,ta miƙe tana duban Momy ta ce, "Ki sanar da Kabeeru da gaggawa, Yarinya ta dawo kenan har sai ta haife mana ɗan ko Ƴar sannan sai su ƙarata ta sake binsa can kudun.Amma yanzu tunda ya nuna baƙin cikinsa da hassadarsa akan samuwan cikin, ana bashi ita suka koma zai san yadda ya yi salwanyar da cikin tunda ita shashashace, ta riga ta nuna masa ta gama matowa a kansa gaba ɗaya.Ita ko irin ƴar jan ajinnan ta mata bata iya ba, kyawunsa gaba ɗaya na kula gigita yake,ta yadda idan waje duk take rasa nutsuwarta.Wallahi Hanantu ki yi hankali da zaƙewa a nuna wa namiji muguwar soyayya, inba haka ba kece a wahale a kuma gantale don duk iskancin da ɗebo a kanki zai riƙa saukewa." Gwaggo ta ƙare maganar tana yin gaba don fita daga ɗakin.Momy da Hannah sukai mata sai da safe, ta juyo tana makawa Momy harara ta ce, "Amma Zainab so kika yi ki rufeni,da tun farko baki je kin sanar min wannan iyashegenba.Yanzu gobe sai a buɗe mata ɓangarensu a gyare shi, tunda dama komi na nan kamar yau akai jeren wajen,tayi zamanta ta raini cikinta cikin salama.Ko Iyayenta ban yadda su ji wannan abin kunyar ba, sabida sai ai mata dariya gaskiya." Momy ta jinjina kai ta ce, "Dama nima shawarar dana yanke kenan Gwaggo, shi ma kuma Daddy haka ya ce tayi zamanta kawai." Gwaggo ta fice tana cewa, "To ai shikenan tunda basirarmu duk yazo ɗaya a nan,shi kuma Adinanun zai zo ya sameni har ɗakina." Ta ƙarisa ficewa tana barin su Momy da sakin dariya,don sun yi mamakin yadda Gwaggon ta rufe ido tana masifan jin zafin zancen zubda cikin. Falo Hannah ta koma ta samu Gwaggo ta tasa Najma sun koma ɓangarenta, don ta sanarwa Nasreen cewa gobe lafiyayyan ƙosan da Najma ta iya zata yi musu da safe.Don haka ba za ta kwana anan tana baccin asara da safe ba, har ta gagara komawa tayi musu ƙosan akan lokaci.Hannah ta zauna tana dariyar yadda Nasreen ke bata labarin abinda Gwaggon ta faɗi,ta cigaba da blushing tana cewa, "Nima har naji ina son naci ƙosan Sis,goben na je na samo wajen Gwaggon na ci." Nasreen ta taɓe baki cike da jin haushin hana Najma kwana da Gwaggo tayi ta ce, "Aiko dai zaki ci daɗi, don gaskiya ta iya suyan ƙosai sabida sana'arsu ce a can giwa ta ce." Hannah ta murmusa daidai wayarta na ɗaukar tsuwwa na shigowan kira ta ce, "Aiko da wuri zan aika a amso min ɗin." Daga haka ta ɗaga kiran ganin sunan Anty Laurah ce mai kiran.Sun ɗan jima suna magana, amma sam Hannah bata sanar mata cewa tana KD ba.Ta aje wayar tana kallo agogo zuciyarta na cike da tunanin kome yake can yana yi a yanzu? Ta ɗan lumshe ido tana jin wani zafi da kishi na sukan zuciyarta,don ta san yau ɗin watakila kwana ma zai yi a club tare da ƴan matansa tunda bata gidan baki ɗaya bare ya dawo mata cikin tsakiyar dare ya lalubeta kamar yadda ya saba.Ƙirjinta ta ji yana mata nauyi,sai tayi saurin tashi tana duban Nasreen da Nabeelah da hankalinsu ya koma kan wayoyinsu ta furta, "Gud night Sisis, zan kwanta bacci yazo." Nasreen sukai mata sai da safe ta nufi hanyar bedroom ɗin da Momy ta ce ta zauna a ciki.Su kuma suka cigaba da chart suna kuma kallo rabi da rabi.Kira da ya shigo wayar Nasreen na wani saurayinta Saheeb ya sanyata tashi ta wuce ɗaki, ta bar Nabeey a zaune tana kallo tana cigaba da chart.

*********
*Port Harcourt.*

Ƙarfe uku daidai na dare motar Adnan Dukku ya shigo gidansa.Ya ɓalle murfin motar ya fito bayan ya adanata a parking space, ya nufi cikin gidan yana jin kansa na sara masa sakamakon ƙwayar da ya sha da bai taɓa shan irin ta ba sai a yau ɗin da abokinsa US (Usman Sani) ya zo musu da ita.Shi ma kuma daga ingila ya taho da ƙwayar,wacce ba mai sanya buguwa bace sai dai ta sanyawa mutum ƙarfi da jin kansa a sama tamkar yafi kowa.Ƙarfin da take dashi ke sanya duk wanda ya fara shanta sai ya haɗu da ciwan kai mai tsanani kafin ta bi jikinsa ta fara aikin da ya dace.Ya kai kansa zuwa upstairs yana nufan room ɗinsa kai tsaye,domin burinsa bai wuce ya sakarwa kansa ruwa mai ɗumi ba.Kayan jikinsa da ke fidda mayataccen ƙamshin Leenah ya fidda,ya yi jifa dasu a tsakar ɗakin yana nufan hanyar bathroom ya sakarwa kansa ruwan sanyi.Sai da sanyin ruwan ya gama ratsa kwanyarsa lafin ya sakarwa jikinsa ruwa mai ɗumi,yana jin wani irin yanayi na bin jikinsa.Koda ya fito kayan baccinsa ya sanya, ya nufi wajen ƙaramin fridge ɗinsa ya ciro table water, sai da ya sha rabin gorar ya dire

Please Login or Register in order to submit comment