Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce kawai ta fara yin tauri na nuna alamun girma ya kamata.Gwaggo ta sake duban Inna Mairo dukkanin mafarkan da take yawan yi da Abbansu na dawo mata. Wasu irin mafarkai da ke birkita lissafinta da jefa zuciyarta cikin zullumi, don duk lokacin da zata yi mafarkin shi take gani riƙe da hannuwan Mairo yana tahowa gareta. Sai dai da zaran ya kusa isowa inda take sai ta dinga jiyo wani irin sautin murya daga bayansa ana faɗin, "Karka isa gareta domin ta kasance azzuluma bai yanke zumunta da raba tsakanin ƴan uwa." Sai taga Abbah ya juya cikin fushi Mairo na kuka tana waigowa baya tana kallon inda take. Ta sauke wani irin numfashi tana buɗe baki ta ce, "Mairo ku sha ruwa da lemu kuyi sallah kafin a kammala girki sai kuci ko?" Inna ta jinjina kai tana duban Najma ta ce, "Najma sha ruwa, ni kam bari na fara da gabatar da sallah tukunna." Gwaggo ta nuna wa Inna Mairo hanyar da zai shigar da ita zuwa ɗakin baccinta tana mai cewa, "Shiga daga ciki kiyi sallar Mairo, bari in aika a sanar da Zainab zuwanku. Kabeeru shi ma yana gari amma bada jimawa ba ya fita wajen wani ɗauri aure da aka gayyacesa, amma zan yi kiransa daga can ya wuto gida tunda gaki Allah ya kawoki a lokacin da nake buƙatar hakan." Gwaggo ta dakata da maganar ganin Inna Mairo ta shige corridor ɗin da zai sadata da ɗakunan baccinta. 3 bedrooms ne daga cikin corridor ɗin masu ɗauke da toilet a cikinsu,sannan duka akwai kayan alatu da aka zuba masu inganci da nauyin kuɗi. Inna Mairo ɗakin da ta gani a buɗe nan ta nufa, ta lalubi inda toilet ɗin yake ta shiga don ɗauro alwalar. Daga can falo kuwa Gwaggo ce ta dubi Najma ta ce, "Sannu Najmatu, kin zama budurwa sosai ina fata kin samu yin ilimi boko?" Najma ta jinjina kai ta ce, "Na kammala secondary school ɗina, daga nan ne dai ban samu cigaba ba sai islamiya da nake zuwa,shi ma mun kammala ajin ƙarshe an yaye mu."

Gwaggo ta gyaɗa kai idanunta har lokacin akan Najma suke, tana ganin kamar da Inna Mairo take magana a lokacin da take budurwa tamkar Najmar. Amma black beauty face ɗin Najma na tunasar da ita cewa wannan kyakykyawar budurwar ɗiyar Mahmuda ce bata Malam Muhammadu ba. Ta cigaba da yi mata tambayoyi game da zamansu a ƙauye, tana kuma bincikan wane ne ya ɗauki nauyin karatun Najmar? Najma da tarin baƙin ciki da jin haushin Gwaggo ke ƙaruwa a zuciyarta, sai ta dinga bata amsa a gajarce cikin rashin sakin fuska da walwala. Fitowar Inna Mairo ya sanya ita ma Najma ta miƙe ta shige don zuwa tayo nata sallar, Inna Mairo ta ƙariso ta zauna a inda ta tashi. Gwaggo ta miƙe ta fice don zuwa ta aika Sabeera mai aikinta ta yo mata kiran Hajiya Zainab, don bata faye zuwa sashinsu da kanta ba sai da dalili. Ita dai Hajiya Zainab ɗin da Yaranta ne ke shigowa duk safe su gaidata kafin su wuce school, idan sun dawo zuwa yamma ko dare Nasreen da ta fi shiri da Gwaggo ta kan shigo mata hira ita ma. Bayan ta aika Sabeera kiran Hajiya Zainab, sai ta bai wa Tabawa umurnin a shirya abinci a kai wa su Hakimi dake daga can ɗakin baƙi dake nan cikin part ɗinta. Suma su Inna abincin aka shirya musu a table, amma sai Gwaggo ta bada umurnin a sauke musu daga ƙasa don ba kowa ke jin daɗin cin abinci a sama ba.Tare da Gwaggo suka haɗu a tsakiyar falonta suka ci lafiyayyan shinkafa da miyar kaji,ga kuma haɗaɗɗyar haɗin salad daga gefe. Sosai girkin ya yiwa Najma daɗi matuƙa, musamman haɗin salad ɗin da bata taɓa cin irinsa ba.Suna kammala cin abincin Hajiya Zainab na shigowa ɗakin cikin tsananin fara'a da farin cikin ganin Inna Mairo.Cike da zallar farin ciki Hajiya Zainab suke gaisawa da Inna Mairo, idanunta akan Najma da fuskarta ke haskawa da ƙaramin murmushin ganin yadda Hajiya Zainaba ɗin ke nuna murnarta na ganin Inna Mairo. Ta risina ta gaida Hajiya Zainab ɗin cike da ladabi.Hajiya Zainab ta amsa da tsantsar kulawa tana yaba kyawu da nutsuwar da Najma ke dashi. Ta maida dubanta ga Inna Mairo tana faɗin, "Yanzu Najmar ce ta zama budurwa sosai haka? Koda yake ga tsararta can Nasreen ita ma ta zama budurwa har ta shiga aji biyu a jami'a." Inna Mairo tayi murmushi tana faɗin, "Ai girman Yara mata ba wuya Hajiya Zainab,musamman idan suna samun ingataccen abinci mai gina jiki." Gwaggo dake saurarensu ta dubi Inna Mairo tana faɗin, "Mairamu leƙa wajen baƙin idan sun kammala ki shigo dasu nan falo mu gaisa." Inna Mairo ta amsa da cewa, "Tuh Gwaggo." Ta miƙe ta fice daga ɗakin Inna zuwa waje tana raba idon gano inda ɗakin baƙin yake. Daga can hanyar fita part ɗin ta hango ɗakin,ta isa tana mai yin sallama daga baƙin ƙofar shiga. Auwalu da Hakimi suka haɗa baki wajen amsa sallamar, Inna Mairo ta sanar dasu cewa su shigo daga ciki inji Gwaggo. Tana tsaye daga bakin ƙofan suka fito, tayi musu jagora har zuwa falon Gwaggon kaduna. Cikin mutunci da girmamawa Hakimi Alhaji Haruna Musa giwa suka gaisa da Gwaggo da Hajiya Zainab, bayan sun kammala gaisawa da tambayar lafiyar Iyali sai Hajiya Zainab ta janye Najma zuwa sashinta don su bai wa su Gwaggo damar tattaunawa.

Shi ma Auwalu Hakimi sallamarsa ya yi ya ce ya koma ɗakin baƙi ya jira shi a can, don basu damar tattaunawa da Gwaggon kaduna da Inna Mairo.
Gwaggon kaduna dukkanin jikinta a sanyaye yake lokacin da Hakimi ya buɗe zaman da addu'a tare da farawa da yi musu nasiha mai ratsa zuciya. Ya dubi ɓangaren da Inna Mairo ke makuye kanta a ƙasa ya ce, "Mairo ina so ki bai wa Gwaggo haƙuri akan yadda kika yi zuciya dasu kika yanke zumuntar da ke tsakaninki da ƴan uwanki, ta hanyar daina bibiyarsu da kawo musu ziyara." Inna Mairo ta ɗago manyan idanunta ta saci duban Gwaggo tana mai farawa da faɗin, "Ki gafarceni Gwaggo, tabbas nayi kuskure kuma daga bisani abin yana damuna domin na kasa cire ƙawazucin ƴan uwana a cikin zuciyata.Ina roƙo ki yafe mini akan dukkanin abinda ki ke zaton da gangar nayi miki Gwaggo, wallahi dukkanin abinda ya faru ya faruwa bisa ƙudurar Ubangiji.Banki Fahad don ya kasance jininki ba sai don haka ALLAH Ya NUFA ba shi ne zai zamo miji a gareni ba.Sannan ba laifin Baban Najma bane shi ma,domin shi kansa Abbah ne ya kira shi ya ce ya bashi aurena.Ki yafe mana Gwaggo ki sassauta mini irin ƙiyayyar da kike mini ko xan samu sassauci cikin rayuwata...." Inna Mairo ta kasa kaiwa inda take so takai a kalamanta,dalilin kukan da ya taho mata kai tsaye ya hanata ƙarisa kalaman da ta faro. Gwaggo da dukkanin jikinta ya gama sanyi, ta ɗago ido ta aza akan Mairo tana jin wani irin abu mai kama da nadama na ratsa zuciyarta. Murya can ƙasa ta soma da faɗin, "Mairo ki gafarceni, tabbas banyi miki adalci ba ban kuma yiwa kaina ba,domin na kasa cika wasiyyar Malam a kanki. Na biyewa son zuciyata ne kawai wajen raba zumunci da ƴan uwantaka,alhali nafi kowa sanin kinfi kowa buƙatar mu cikin rayuwarki domin mu kaɗai ne tilashinki.Nayi nadama Mairo tun daga sanda na fara wasu irin mafarkai da mahaifinku....Komi ya wuce Mairamu kamar yadda nake fata zaki yafe mini don ni ce mai laifi bama ƴan uwanki ba, sabida ni ce nayi miki katanga dasu na kuma hana ki cigaba da raɓanmu don na san tabbas da kin cigaba da zuwa garemu zuciyar Kabeeru dole ta amsheki,ya kuma cika wasiyyar mahaifinku ya kula dake.Ba sai na tsaya tone-tone ba Mairo, ki yi mini afuwa ki manta baya mu fuskanci gaba, don gyara abinda ya rushe." Gwaggo ta kai ƙarshen maganar tana duban Hakimi da Inna Mairo wacce ke kuka da hawaye. Ta cigaba da roƙon Inna gafarar abinda ta aikata mata na ƙiyayya a baya, tare da basu labarin irin mafarkan da take tayi da Abbah da Inna Mairon. Hakimi ya ɗaura da yiwa Gwaggo nasiha akan illar abinda ta aikata na son raba zumunci da nesanta tsakanin ƴan uwan juna. Wanda hakan babban kuskure ne wanda shari'a tayi tir da masu aikatashi, sannan aka yi musu albishir da azaba mai tsanani idan suka mutu a akan turban aikata irin abinda ta aikata ɗin. Gwaggo hawaye kawai take sharewa, dukkanin nasihun Hakimi na ratsa zuciyarta tare da kassara gaɓɓan jikinta. Lokacin da ya kammala nasiharsa tare da sanar da Gwaggo buƙatarsa na son ta rungumar Inna Mairo tamkar ƴar cikinta, sai ya rufe da addu'ar Allah ya haɗa kawunansu Inna Mairo da ƴan uwanta. Gwaggo ta share hawaye tana duban sashin da Inna Mairo take ta fara da faɗin, "In Sha Allah! Na ɗauki nasiha da shawarwarinka Hakimi, sannan ina baka tabbacin daga yau komi zai sauya don ba zan so na mutu da hakkin cigaba da ƙuntata rayuwar Mairo ta hanyar rashin kyautatawa ba. Kamar yadda Allah bai bani ƴa mace ba ina so a yanzu na riƙeta a matsayin ita ce makwafin ƴa macen da bansamu ba..... Ta ɗan dakata kaɗan tana duban yadda Inna ke share hawaye ta cigaba da cewa,"Kiyi haƙuri Mairo, ban baki wannan matsayin a lokacin da ya dace ba sai a lokacin da tsufa ya fara kamani.Lokacin da hakan ba lallai ne ya yi miki daɗi a zuci ya kuma wanke baƙin cikin dana cusawa rayuwarki ba, sai dai koma yaya ne ina so ki amshi wannan sabon matsayin don bani ikon kyautata rayuwarki da ta Najma ko yaya ne." Ta dakata tana duban yadda Inna Mairo ke faman gyaɗa kai hawaye na zarya akan fuskarta. Da ƙyar ta iya fisgo kalaman bakinta ta ce, "Na baki dama Gwaggo, sannan ina godiya da sabon matsayin da kika bani. Allah ya bani ikon yi miki irin biyayyar dasu Yaya ke miki koma na ninka.Allah ya jiƙan Abbah da Malam yasa suna cikin aljanna maɗaukakiya, Allah kuma ya haskaka makwancinsu tabbas da suna raye da yau sun yi alfahari da zuwan wannan ranar da suka sha kwaɗaita mini zata zo gareni. Amma gashi ranar ta zo a lokacin da ƙasa ya jima da rufe idanunsu...." Inna Mairo kuka ya kwace mata ta kasa ƙarisa kalamanta, ta dinga kukan sosai na tsananin zafin rashinsu Abbah da Malam Mahmuda da tayi.Gwaggo da Hakimi jikinsu ya sake yin sanyi, tausayin Inna Mairo ya dinga kassara zuciyar Gwaggo matuƙa da gaske. Suka haɗa baki da Hakimi wajen rarrashin Inna Mairo da kalamai na kwantar da hankali,har suka samu ta tsaida kukan da take yi ɗin. Gwaggo ta ɗaga wayarta a karo na biyu ta kira layin Alhaji Kabeer Dukku don jin ko ya kusa ƙarisowa gidan? Sabida da sukai waya da farko ya shaida mata cewa ba zai jima ba zai ƙariso gida daga wajen ɗaura auren da ya halarta a nan cikin garin kadunan. Ta aje wayar lokacin da ya bata tabbacin yana dab da ƙarisowa gidan nasa.

******
Daga can ɓangaren Hajiya Zainab kuwa, tasa Najma tayi da hira tana tambayarta akan abinda ya shafi karatunta. Najmar ta ɗan saki jiki da ita tana bata amsa a takaice,gefe guda kuma gaba ɗaya ta shagala a kallon tsaruwar falon Hajiya Zainab ɗin. A cikin zuciyarta take kisima suko wani irin dukiya suke dashi haka? Domin a falon kaɗai aka barka zaka san cewa ba ƙananun dukiya aka kashe ba. Kyakykyawar budurwa mai shekaru sha bakwai zuwa sha takwas ce ta fito daga wani corridor. Ta sauke idanunta akan Momynsu da baƙuwar fuskar da ta gani tare da Momyn. Sannu a hankali ta cigaba da ratsowa zuwa cikin falon, idanunta kyam! Akan black beauty face ɗin Najma.

Najma ita ma idanunta ne ya kai kan kyakykyawar farar budurwar dake tunkaro inda suke zaune, sai ta samu kanta da kasa ɗauke idanunta daga kan budurwar domin gani tayi suna satan kamanni da Innarta. Sai dai kawai wannan ɗin a yanzu tafi Inna fari da kuma dogon hanci, amma hatta yana yin tafiyarsu iri ɗaya ne dana Inna Mairo. Budurwar ta ƙariso cikin falon tare da samun waje kusa da Hajiya Zainab ta zauna tana faɗin, "Momy sannu da hutawa,baƙuwa muka yi ne?" Momy Hajiya Zainab sai ta dubi Ƴarta da murmushi akan fuskarta ta bata amsa da cewa, "Nasreen wannan ba baƙuwa bace, she's ur sister, ita ce Najmar dana taɓa baki labarinta na ce daughter ɗin Gwaggonku Mairo da suke zama a ƙauyen giwa kin tuna?" Wacce aka kira da suna Nasreen tayi saurin gyaɗa kai tana duban Najma sosai ta ce, "Wow! She's very black beauty Momy, and sunanta kuma ya dace da kyawunta. Nice to meet u sis!" Ta kai ƙarshen maganar tana sake ƙure kallonta akan Najma, wacce ta sakarwa Nasreen murmushi ita ma. Cikin sanyin muryarta kuma ta ce, "Nice to meet u too sis, thank u!" Ba Najma ba hatta Momy tayi mamakin yadda Najma tayi wa Nasreen magana da harshen turanci,don sunyi zaton koda tana ji ba lallai ta iya maida martanin magana da yarenba.Duba da cewa a ƙauye ta tashi, koda ace tayi karatu ba lallai ta iya turanci ko ta ji sosai ba sabida yadda ake faɗin lalacewar makarantun gwamnatin karkara da babu wasu ƙwararrun malamai.Cikin tsananin farin ciki Momy ta dubi Najma tana faɗin, "Very good daughter! Ashe dai makarantun karkara ma na ƙoƙari wajen koyar daku harshen english. Da alamu idan kika sake samun wanda zai koyar da ke harshen ba ƙaramin ƙwarewa zaki yi wajen iya speeking da shi ba." A kunyace Najma ta jinjina kai tana faɗin, "Na gode Momy!" Ta faɗi sunan yadda ta ji Nasreen ta kira Hajiya Zainab ɗin dashi. Nasreen ta dubi Najma tana jin ƙaunarta na kama zuciyarta, cikin muryarta mai cike da iyayi irin na ƴan boko take tambayar Najma inda ta tsaya da karatunta. Najma ta sanar da ita cewa iyakarta secondary school, shi ma ba a garin giwa suka yi ba a wata makarantar ƴan matane dake garin basawa.

Cikin nutsuwa da sakin fuska Nasreen da Momy suka dinga jan Najma da hira don ta ɗan sake dasu. Momy ta sanya an kawo mata tarin snacks da dambun nama an tasa mata a gaba, ga kuma lemuka kala har biyu na gwangwani an aje mata. A kan kunnuwarta kuma Momyn ta bai wa mai aikinta umurnin kai wa su Inna suma snacks da dambun naman, haka kawai sai Najma ta ji matar ta shiga ranta ta kuma kwanta a zuciyarta matuƙa da gaske. Don yanayinta da irin yadda take mu'amala da hatta masu aikinta zai baka tabbacin mace ce ita da tasan darajar mutunta ɗan adam! Sam bata fito a cikin irin matan masu arziƙin dake taka talaka suna wulaƙantashi ba. Sai da Alhaji Kabeer Dikku ya iso gidan ne Najma ta sulale ta koma sashin Gwaggo bayan ta gaida shi ya amsa da sakin fuska. Shi ma babban rigarsa da ta damesa a jiki kaɗai ya yarɓar akan kujera ya fice zuwa sashin Gwaggon. A can ya samu mai girma Hakimi da Inna Mairo suna ta hira da Gwaggo gunin sha'awa.Najma na daga gefe guda ta maida dukkanin hankalinta akan kallo TV, wanda yake a kunne an saita shi akan tashar Arewa24. Sallamar Alhaji Kabeer Dukku suka amsa yana mai ƙarisowa cikin falon ya zauna kusa da Gwaggo, idanunsa akan tilon ƙanwarsu Mairo ya saukesu yana mamakin ganin yadda ta lalace tayi duhu. Wani abu yaji mai tauri ya danne zuciyarsa, don ko kaɗan bai jin daɗin hakan a ransa ba. Bayan sunyi musabaha da Mai girma Hakimin giwa, sai ya maida kai wajen duban Inna Mairo tare da amsa gaisuwar da take masa cike da girmamawa. Najma sake gaida shi tayi tana mai miƙewa ta fita waje don basu waje, ba tare da ta san inda zata dosa ba kuma. Tunanin ya tsaya akan ta je ɗakin baƙi wajen Yaya Auwalu, sai kawai ta nufi hanyar wajen kanta tsaye tana mai rafsa sallama lokacin da ta isa ƙofar ɗakin.......✍🏻



*Pay 500 in to this account number👇🏻*
*0504192664 Ibrahim Aisha Dansabo GTbank* *Evidence of payment to this number:08167768704*


🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻*
*MTN*
*GLO*
*AIRTEL*
*9MOBILE*
*MONTHLY VADILITY 💃🏻*

*DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻



#Lovestory#
#Najma#
#Aysha Ɗansabo Lemu🥰
[3/3, 11:27 AM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻
_*Arewabooks@ayshadansabo*_

*Paid book:500*

*Chapter 11*

_Free page_

Auwalu ya amsa sallamar Najma yana mai bata izinin shiga ɗakin.Ta shiga ta samu wajen zama bisa kujerar da ke nesa da shi,ta dubesa da murshi akan fuskarta ta ce, "Sannu da hutawa Yaya Auwalu, an barka kai kaɗai kana ta jira shiyasa na ce bari in zo in tayaka zama kafin su Baba Hakimi su gama magana da Kawu Kabeeru. Auwalu ya aza mata idanunsa da ke cike da zallar ƙaunarta yana faɗin, "Kin kyauta Najma, dama duk zaman ni kaɗai ya dameni." Daga haka ya fara janta da hira yana mai jin tsananin nishaɗi a zuciyarsa.

Daga can ɓangaren Gwaggon kaduna dasu Inna Mairo kuwa, Baba Hikimi ne kewa Alhaji Kabeeru Dukku nasiha mai ratsa zuciya. Yana mai tunasar dashi illar yanke zumunta da cin amanan ƴan uwantaka, domin tabbas sunci amanar zumunci da ƴan uwantaka akan yadda suka wofintar da Inna Mairo. Ya ɗaura laifin baki ɗaya akan Alhaji Kabeer yana mai sanar dashi cewa, "Amatsayinka na babban Yaya a garesu, kamata ya yi ace lokacin da ka kula cewa Mairo ta daina zuwa inda kuke wajen Gwaggo ka bincika da kanka ka gano miye matsalar, me kuma akai mata ko ke tayi da ta yanke hukuncin nisantarku da mahaifiyarku? Amma sai kayi biris ka cigaba da biyewa son zuciyan Iyayenmu mata, waɗanda dama sune ke assasa wutar irin waɗannan rashin jituwar da ke faruwa tsakanin ƴan uba.Domin kaso casa'in cikin ɗari na lalacewar zumunci a gidaje, Iyayenmu mata ne ke jagorantarsa, ba kuma sabida komi ba sai biye son zuciyoyinsu da mummunar kishin da ke rufe idanunsu. Idan ba anyi sa a da jajirtaccen uba mai sanya ido matuƙa da gaske ba, sai ka ga kafin kace kwabo sun raba kan ƴan uwa tare da jefa ƙiyayyar juna a zukatansu.Wanda wannan babban kuskure kuma babban zunubi, domin Ubangiji ya yi tir da bawan da ke yanke zumunta tsakanin ƴan uwan juna.Kana da laifi matuƙa da gaske wajen yin biris da lamuran Mairo, alhali kai ka fi girman hakkin kulawa da ita, sabida babban Yaya makwafin uba yake.Amma kai kayi watsi da amanar da Abbanku ya damƙa maka na riƙeta da amana ku kuma maye mata gurbinsa.....

Hakimi ya ɗan dakata domin bai wa Yaya Kabeeru damar magana.Yaya Kabeerun da ya yi shiru yana mai faɗawa duniyar tunani da nadama, sai ya ɗago manyan idanunsa ya ɗaura akan Inna Mairo yana faɗin, "Ki gafarceni Mairo tabbas mun yi kuskure, sai dai fatan kada Allah ya maimaita.Sannan kema kina da kaso mai yawa wajen aikata kuskure Maryam, don bai kamata ace ko wani irin abu Gwaggo ke miki zaki iya yin zuciya ki daina zuwa inda take ba, koda ace ita ce ta buƙaci hakan da kanta.Domin su Iyaye ba a fushi dasu sai dai ayi ta binsu ana rarrashi da kwantar da kai har su gano kuskuransu.Amma ke sai ki ka nuna cewa tabbas ba ita ce ta kawoki duniya ba, domin da Inna ce ke raye kome take miki ai ba zaki iya daina zuwa gareta ba.Don haka kema kinyi kuskure bana buƙatar a gaba ki sake aikata makamancin hakan. Ki yafe mana baki ɗayanmu kuskuren da muka aikata wajen wofintar dake, alhali munfi kowa kusanci dake kuma mu ya cancanta mu riƙe ragamar rayuwarki a lokacin da kika rasa miji da mahaifi, amma ba muyi hakan ba duk da cewa Allah ya bamu arziƙi da damar yin hakan. Ki yafe mana wannan babban kuskuren Maryam, In Sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba.Zan yi amfani da bakina wajen roƙawa Ali gafararki shi ma, kafin ya zo ya roƙa da bakinsa idan yazo gari tunda a yanzu ya dawo ƙarsar yana can da Iyalinsa a garin Lagos." Inna Mairo ta jinjina kai tana sake share hawayen da ke zubo mata,wanda bana komi bane na farin ciki ne da Allah ya nuna mata wannan ranar da take zaune gaban Gwaggo da Yaya Kabeeru suna roƙon afuwa a gareta.Tabbas ta sake gasgata cewa mai haƙuri shi ke da nasara,sannan babu abinda ke dauwama a duniya walau jin daɗi ko akasin hakan. Baba Hakimi ya jima sosai yana nusar da Gwaggo da Alhaji Kabeer illar abinda suka aikata tare da sanar dasu lalurar da ta kama Mairo, duk kuma a sanadiyyar baƙin ciki da ƙuncin rayuwa ne da suka jefa zuciyarta a ciki. Don ba za a ce rashin ci ko sha ne ya sababba mata shiga ƙunci da yawan tunanin da har ya sanya ta kamu da cutar hawan jini ba, sabida iyakan ƙoƙari yana yi dasu wajen ganin basu nema abin ci ko abin sha da kuɗin cefane sun rasa ba. Illar ƙiyayyar Gwaggo gareta da kuma juya mata baya da suka yi ya janyo mata shiga halin ƙunci da yawan tunani. Jikinsu Gwaggo ya yi mugun sanyi, tausayin Mairo ya sake kamasu musamman Alhaji Kabeer da har wani ƙunci da kunyar Inna Mairo ya dinga ji. Ya sake bai wa Mairo haƙuri tare da yi mata albishir da cewa komi ya wuce a yanzu, don ba zasu sake barinta ba. Hasalima ta sanya a ranta ta dawo hannunsa kenan da zama ba za ta koma ƙauye ba ita da ƴarta, sai dai kawai su je suyi bankwana da mutanen garin su dawo.Inna Mairo ta dubi Yaya Kabeeru fuskarta na bayyana tsananin mamakin kalamansa, domin ba tayi zaton hakan ba cikin gaggawa. Kafin ta iya cewa komi ko Hakimi ya ce wani abu, Gwaggo ta rigasu da faɗin, "Tabbas Mairamu ba zaki koma ba kun zo kenan, muna godiya da tarin karamci da ƙaunar da Mai girma Hakimi da Iyalinsa suka nuna muku. Tabbas Hakimi ka cika amini na ƙwarai, kuma wanda yasan girman halacci a rayuwa. Mairo dawowarta garemu baki ɗaya shi yafi dacewa a yanzu, domin hakan ne kawai zai sake bamu damar kusanci da assasa ƙaunar juna a tsakaninmu." Mai girma Hakimi ya jinjina kai yana jin wani abu mai nauyi na son danne zuciyarsa. Cikin murya marar amo yake faɗin, "Alhamdulillah! Da wannan hukunci naku Hajiya Gwaggo, duk da cewa ni da dukkanin ahalina wannan hukunci ba zai mana daɗi ba. Amma a zahirin gaskiya hakan shi yafi dacewa, Mairo ta dawo ƙarƙashin kulawarku ko don ku kula da lafiyarta da samar mata magungunanta akan kari.Don a can ɗin wani lokacin kuɗin sayen magungunan kansa gagara yake. Zamu shiga alhini mai yawa idan ya kasance mun buɗe ido mun ga babu Iyalan Malam Mahmuda a kusa damu, amma hakan ba zai hana mu taya Mairo farin ciki ba domin wannan shi ne irin gatan da ya dace ta samu daga gareku. Allah ya haɗa kanku ya baku ladar zumunci,ke kuma Mairo ina fata barinki garin giwa ba zai zamo silar lalacewar zumunci da ƙaunar da ke tsakaninmu da juna ba ni da ahalina baki ɗaya?" Hakimi ya kai ƙarshen maganar fuskarsa na bayyana zallar alhini da irin kewar su Inna da zasu yi. Don sabo shegen abu ne, musamman su da suka riƙi juna tamkar ƴan uwa.Inna Mairo ta share hawaye tana duban Hakimi a karon farko ta ji wani irin abu na dukan zuciyarta game dashi, ta lumshe idanunta tare da sake buɗe shi akansa ta ce, "Har

Please Login or Register in order to submit comment