Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rashin Malam Mahmuda tare da shafewar babin rayuwarta a garin giwa,wanda tsananin kewar da take ji a zuciyarta ke sanya hawaye tsere akan fuskarta.

Ana dab da kiran sallar magriba suka iso kaduna,domin sunyi yamma a garin giwa basu fito da wuri ba.Dukkaninsu side ɗin Gwaggo suka nufa,amma banda Momy da Daddy da suka nufi side ɗinsu kai tsaye.Anty Hannah bisa sofan ɗakin Gwaggo ta zube tana sauke numfashin gajiya tamkar yau ta saba tafiyar mota,don sosai take jin gajiya ga wani irin yunwa da ke neman hargitsata.Ta rasa meyasa tunda ta samu ciki sai cin abinci,sam bata jure yunwa a ƴan kwanakinnan.Gwaggo ce da ta shigo daga ƙarshe ta dubeta tana faɗin, "Hannatu gajiyarce haka,ko kina buƙatar wani abu ne?" Hannah ta gyaɗa kai a kunyace ta ce, "Gwaggo ko akwai fura a fride ɗinki in ɗan sha?" Gwaggo ta ƙwalla kiran Tabawa da ke niyyar fitowa tarbansu dama, ta bata umurnin kawowa Hannah fura tana cewa a haɗo mata da soyayyiyan naman ragon jiya.Hannah ta ji wani daɗi ya ratsata,har ta ƙosa a kawo naman da furan gabanta.Nasreen da Nabeela basu wani zauna sosai ba suka nufi side ɗinsu don watsa ruwa,sabida yadda suke jin gajiya a jikinsu.Najma da Inna Mairo ma ɗakinsu suka nufa jikinsu a sanyaye,don hankulansu duka naga su Inna Karima da suka baro suna kukan rabuwa dasu.Wanka Najma tayo ta saka riga mara nauyi,tana tsaka da ɗaura ɗankwali aka kira sallah,sai kawai ta nufi wajen da suka keɓe domin sallah a ɗakin ta tada sallah.Inna Mairo ma toilet ta nufa ta watso ruwa,ta fito ɗaure da alwala ta saka riga da hijab ita ma don gabatar da sallah.

Hannah ma tana gama shan furan da naman ta yiwa Gwaggo sallama ta nufi side ɗinta.Wanka da sallah ta gabatar,tana idarwa ta janyo wayarta zuciyarta na ingizata akan ta kira AD Dukku taji muryarsa da yadda ya isa garin Abuja ɗin.Sai dai tana danno lambar ta dinga tuna kalaman da Momy ke mata akan sai fa ta dinga daraja kanta da jan zarenta a kansa domin rawar ƙafar da take nuna masa har ya yi yawa.Wani sashi na zuciyarta ya dinga tuna mata cewa shi ya dace ya kirata ya ji lafiyarta dana babynsa,amma bai yi hakan ba alhali ya tafi ya barta tana kukan rashin samun kulawarsa da sam bata yi.Sai ta aje wayar tana ji zuciyarta na cika da wani irin ɓacin rai, ta dinga jin cewa yakamata ta ɗan ja zarenta a wannan karon wajen nuna masa baya gabanta ita ma.Koda ta sake janyo wayar line ɗin Hajiyarta ta kira suka sha hira,Hajiyar na tambayarta zamanta da AD Dukku ana samun cigaba ko kuwa tana nan tana sake zubda kanta yana takata don baya ƙaunarta? Hannah ta ɗan narke murya tana sanar da Hajiyar komi normal ne.Sam bata sanar mata da zancen tana da ciki ba, bare ta bata labarin iskancin da AD ɗin ya yi na cewa bayi son cikin.Bata sanar mata cewa tana kaduna ba,domin Momy ta roƙeta karta faɗa ɗin a yanzu.

Ƙarfe takwas da rabi Najma suka haɗu tare da Gwaggo suka ci abincin dare kamar yadda suka saba,Inna Mairo ta ɓalli magungunanta ta sha kamar ko yaushe. Tana jin daɗin magungunan da aka canza mata fiye dana farkon,don yanayin yadda take ji a jikinta ada sam ba haka take ji yanzu ba.Suna kammala cin abincin bada jimawa ba Inna Mairo ta yiwa Gwaggo sai da safe ta wuce ɗaki,don ta gaji bacci kawai take son yi da wuri tunda dama ita bata saba da hiran dare sosai ba.Najma da Gwaggon ta bari a falo suna hira,Najma na baiwa Gwaggo labarai kala-kala nasu Hanne da gidan Hakimi.Wayar Najmar da ke kan jikinta ya ɗauki ruri, tana dubawa taga sunan Nasreen kamar yadda tayi saving sai ta ɗaga wayar da gaggawa. "Sis please ki taho yanzu,Momy ta ce ki ɗan zo mata da fura da ba a dama ba idan Gwaggo na dashi." Nasreen ta furta hakan daga ɓangarenta.Najma ta amsa mata da cewa gatanan xuwa ɗin,ta kashe wayar tana duban Gwaggo ta isar da saƙon Momy.Gwaggo ta ce taje kitchen cikin fridge zata ga furan a leda ta ɗiba,ta haɗa ma har nonon duk ta kai don tasan Daddy za a damawa furan, kuma shi ma yafi so adama da zallar nono kindirmo bada youghort ba.Sai da Najma ta koma ɗaki ta ɗaura zani akan rigar baccin da ta saka iya guiwa, sannan ta maida ƙaramin hijab ɗin da tafi zama da shi irin wannan lokutan idan ta sanya kayan bacci.Ta fito ta nufi kitchen ta ɗebi fura da nonon,ta yiwa Gwaggo sai da safe da fice zuwa side ɗin Momy ɗin.

A falo ta samesu dukkaninsu suna ta hira har Hannah da ta kasa zama a side ɗinta ita kaɗai ta yo nan ɗin.Najma ta yiwa Momy barka da hutawa tare da tambayarta gajiyar hanya,Momy ta amsata da fara'a tana faɗin, "Babu wata gajiya sosai Najma,har kin gama kukan kin dangana?" Najma ta saki murmushi cike da jin kunya ba tare da ta ce komi ba.Furan da nonon Momy ta amsa ta wuce kitchen don damawa Daddy ta kai masa,domin dama abinda take jira Najmar ta kawo kenan.Najma ta samu gefen Nasreen ta zauna tana yiwa Anty Hannah ya gajiya cikin fara'a, ita ma ta amsa da kulawa tana faɗin, "Yau dai na ga garin giwa Najma, amma gaskiya garin baya samun cigaba yadda ya dace.Sam ciyamomin da ke riƙe garin basa yin ayyukan raya ƙasa da ya kamata, amma gari kamar giwa yaci ace ta samu cigaba sosai." Najma da ita ma rashin samun cigaban garin nasu ke damunta, sai tayi saurin gyaɗa kai cike da tarin takaici ta ce, "Bari kawai Anty Hannah, wallahi haka kowa ke wannan ƙorafin.Gaba ɗaya cin kuɗi kawai da gina Iyalansu da haram suka sani, amma sam babu wasu ayyukan raya ƙasa da garin ke samu.Kullum ka shiga garin giwa ba dai kaga wani ci gaban azo a gani ba sai ma koma baya.Gabaki ɗaya babu wani abin nunawa na azo a gani." Najma ta ƙare maganar fuskarta na bayyana takaicinta a fili.Haka suka zauna suna zantawa akan garin giwa da irin cigaban da ya dace ace garin ya samu,Nasreen ta dinga Allah wadai da rashin kishin garin da ciyamomin garin basayi.Nabeelah dake gefe tana karatun wani book na turanci a wayarta,ita ma baki ta sanya tana tsinewa rashin cigaban garin da lalacewar hanyoyi.Suka ɗauki lokaci mai tsayi suna zantawa kafin Hannah tayi musu sai da safe ta janye Nabeelah zuwa side ɗinta don taya ta kwana.Su Najma basu bar falo ba sai wajen 10:30pm bayan Nasreen ta ci abinci mara nauyi kamar yadda ta saba, bata cin abincin dare da wuri.Suna isa ɗakin Nasreen ɗin Najma ta samu saman sofa ta kwanta, ta kunna wayarta tana dialling lambar Inna Karima.Bugu biyu ta jiyo murya Lubah ta ɗauki wayar, cike da murna da sake jin kewar rashin juna suke wayar.Daga ƙarshe tayi sallama da su don har Hanne ta amsa wayar sun yi magana,Najma ta basu sallahun gaida Inna Karima.Alwala ta ɗauro bayan kammala yin wayar, tana fitowa daga toilet ɗin ta zare hijab ɗin da ke jikinta tare da kwance zanin data ɗaura akan rigar baccinta mara nauyi ta nufi bed don kwanciya.Nasreen da zuwa lokacin tana kwance daga gefen gadon tana faman amsa call ɗin Saheeb ɗinta, sai tabi Najma da kallo tana sake yaba kyawun surarta da ya bayyana a cikin rigar baccin. Najma ta shige duvet sabida sanyin AC da ya cika ɗakin yana ratsa fatar jikinta.Bata san lokacin da Nasreen ta kwanta ba, don ita tana kwanciya badajimawa ba bacci ya ɗauke ta.

~*BAƘIN DARE...!*~

Misalin ƙarfe biyu da wasu mintuna na tsakiyar daren,motoci biyu dake ɗauke manyan gawurtattun ƴan fashin suka shigo gate ɗin gidan Alhaji Kabeer Dikko.Mai gadin suka fara gamawa dashi ta hanyar ɗauresa tamau ƙafa da hannu,bayan sun zamge masa baki suka yi jifa dashi a gefe guda.Kusan rabinsu zagaye gidan suka yi baki ɗaya,hannunwansu riƙe da bindigogi da makamai.Yayin da asalin ogan nasu da wasu daga cikin Yaran nasa suka doshi side Gwaggo.Yanayin yadda suka doshi side ɗin kai tsaye zai baka mamaki,domin kamar dama sun san kan komi na gidan ne.

Gwaggo da Inna Mairo har ma da Tabawa dake ɗakinta dake daga waje,sun farkane cikin wani firgici da tashin hankalin da basu taɓa riskar rayuwarsu a ciki ba.Tashin farko Gwaggo suka ɗaurewa hannu da ƙafafu,bayan ta sanar musu da inda take aje kuɗi da gwalagwalanta da su Daddy suka siya mata.Ita ma Inna Mairo da aka taso ƙeyarta daga ɗakinta cikin razani da firgicin da ya kusa tsaida bugun numfashinta,ɗaure mata hannu sukai da baki.Tabawa kuwa fitsari ta saki a wando tana faman zare ido tamkar ta shiɗe tsabagen tsoro da firgici.Sai da suka gama operation ɗinsu tas a side ɗin, suka tarwatsa komi na ɗakunan suka kwashi kuɗin duk da ke ɗakin Gwaggo da gwalgwalanta.Sannan ogan ya kwance bakinta dake ɗaure babu halin ihu ko magana,ya nuna ta da bakin bindigar dake hannunsa yana faɗin, "Mai gidan na nan ko?" Gwaggo da duk jikinta ke faman ɓari ta girgiza kai murya na rawa ta ce, "Mu kaɗai ne baya na....." Tsawar da ogan ya daka mata tare da ɗauketa da wani bahagon mari ya sanya Gwaggo tuntsurawa ƙasa tana sakin ihu.Ya ɗaga murya yana faɗin, "Karki raina mana hankali mana, bamu shigo ba sai da muka shirya muka kuma samu bayanan komi a kansa.Don haka maza mu je ku nuna mana asalin side ɗin da yake,domin shi muke da buƙatan gani yau." Gwaggo jiki na rawa ita da Inna Mairo da kanta gabaki ɗaya ya yi mata wani irin nauyi,haka aka tasasu suka fito zuwa side ɗin Daddy.Ta ƙofar shiga falonsa ta waje suka shiga cike da al'ajabin yadda ogan na dafa hannunsa a jikin ƙofa yake buɗewa ba tare da anyi amfani da komi ba.Har cikin ɗakin baccin Alhaji Kabeer Dukku suka tasa Gwaggon kaduna ta kaisu.Daddy da Momy dake manne da juna cikin Duvet suna sharan bacci,sai jin mutane sukai a kansu tamkar almara.Suka tashi a firgice sakamakon buga gadon da ogan ya yi da ƙafansa da ƙarfin gaske, ƙaran ya sanya dukkaninsu farkawa a razane suna yin ido huɗu da mala'ikun duniya.Wani irin frigici ne ya kama zuciyar Momy, ta wani zabura zata ƙwala ihu ogan ya yi saurin ɗaura mata kan bindiga akai yana hanata yi musu ihu.Sai ta sulale ta sakko daga kan gadon dukkanin jikinta na ɓari,gashi rigar bacci ne a jikinta da bashi da wani kaurin kirki.Daddy suka nunawa bindiga tare da sanar dashi cewa kuɗi ko rayuwarsa da ta Iyalinsa.Cikin matuƙar tashin hankali da shiga ruɗu yake roƙonsu karsu kashesa ko taɓa Iyalansa,indai kuɗi ne zasu samu ko nawa suke da buƙata.Ogan ya jinjina kai yana yima ɗaya daga cikin Yaransa magana akan ya fara da kashe dukkanin wayoyin su Daddyn,kafin su tasa ƙeyar Momy suna bata umurnin nuna musu sauran ɗakunan da ke side ɗin.Bayan sun gama da side ɗin Daddy ne, ogan ya taso su shi da Gwaggo da Inna Mairo zuwa babban falon gidan ya yi wurgi dashi a tsakar falon.Yana dubansa Yaransa yake basu umurnin shiga sauran ɗakunan suyi operation tare da fiddo ko su wayema a cikin ɗakunan.Inna Mairo da Daddy ji suke yi tamkar su haɗiyi zuciya,domin basu taɓa riskar tashin hankalin gamo da marasa imanin mutane irin waɗannan ba.Lokacin da aka taso ƙeyarsu Najma da Nasreen zuwa falon ne,hankalin Inna Mairo ya sake tashi sakamakon ganin yadda aka fito dasu cikin shigan da bai gama rufe tsiraicinsu ba.Don rigunan bacci ne a jikinsu waɗanda sam ba masu kauri bane na shan iska ne.Daga Najma har Nasreen ihu suke son yi amma an rufe bakunansu babu halin yin hakan,sai mazari kawai jikinsu keyi na tsabagen shiga tashin hankali.

Ogan ya juyo ya sauke idanunsa akan su Najma yana waiwayawa ya dubi su Daddy ya ce, "Dama akwai ƴan mata a gidannan?" Daddy ya gyaɗa kai mummunan tashin hankali na bayyana a kan fuskarsa.Momy da aka taso ƙeyarta daga ɗakinta zuwa falon,bayan an gama yashe duk wani kuɗi da kadaransu na gwal da suke saye ita da Yaranta su Nasreen.Ta ƙariso cikin falon mummunan faɗuwar gaba na riskarta,domin tayi ta addu'ar kada Allah ya basu ikon shiga ɓangaren Yaran ashe har sun shiga sun fiddo mata su. Idanunsa ogan ya sauke akan Najma wacce ke dab da shiɗewa tsabagen yadda take cikin firgicin ganin waɗannan mutane da ake kira da mala'ikun duniya a gabanta.Wani irin kallo yake bin ta dashi daga sama har ƙasa, kafin ya ɗauke ganinsa a kanta ya mayar kan Daddy da hankalinsa yafi na kowa tashi a wajen ya ce, "Ranka ya daɗe naga kayan marmari mai ƙayatarwa a gidanka,don haka zan ɗan huta da ita kaɗan daga ciki." Ya ɗauke ganinsa akan Daddy ya mayar kan ɗaya daga cikin Yaransa da suka taso ƙeyar su Najma ya ce, "Shiga min da wannan black beauty ɗin kayan daga ciki." Yaran nasa ya janye Najma zuwa ciki tana wani irin fisga tamkar zata shiɗe.Nasreen da Gwaggo da Momy tare da Inna Mairo ma dukkaninsu jikinsu ya ɗauki rawa,bakunansu na son fasa ihu amma babu halin hakan don bakin a ɗaure yake.Ga kuma ƙattin da ke tsare dasu da bindigogi a hannunsu.A kan idanunsu ogan ya bi bayansu Najma zuwa ɗakin baccin Nasreen, aka yada ita bisa bed ɗin daidai da shigowar ƙaton mutumin da idanunsa ke rufe da baƙin masks ƙwayar idon kawai ake iya gani jajir a waje.

Daga can falo Daddy Kabeer Dukku ne ke ji tamkar ransa zai fita sabida shiga tashin hankali,don bai taɓa ganin tashin hankali makamancin wannan da yake ciki a rayuwarsa ba.Ihun da Najma da tayi lokacin da yake cin galabar shiga mutuncinta,shi ne ya janyo hankalin Inna zuwa ga sulalewa ta sume gau a wajen.Momy da Nasreen ma sumewar sukai sabida yadda ihun Najma da aka kwancewa baki don sai da ya tsotse saƙo da lungun bakinta tas da salon kiss ɗinsa.Alhaji Kabeer Dukku tare da Gwaggo da tayi suman zaune bata gane komi a lokacin, sai ihun Najma da ke cika kunnuwanta yana mata amsa kuwwa.Sun kasa komi sai uban hawaye dake tsere akan fuskarsu,don babu halin kuka da sauti.Tsayin lokaci suka ji ta tsaya da yin ihun da take yi, sai ga mutumin ya fito daga ɗakin yana gyara zaman wandonsa.Fuskarsa na fidda wani irin murmushi,wanda ya sanya zuciyar Gwaggo sake shiga ƙunci.Ya taka zuwa gaban Daddy yana kai hannu ya fincike abinda aka ɗaure bakinsa da shi.Kamar jira Daddy yake yi ya saki wani irin kuka mai cin rai tamkar ƙaramin Yaron goye, domin tunda ya tabbatar an ɓata rayuwar Najma yaji komi ya kwance masa.Ogan ya kai hannu ya shafa kansa tare yi masa alamu da ya yi shiru.Ya buɗe baki cikin gadara ya ce, "Bar kuka Alhaji banyi ban ruwa a cikin gonarta ba, daga waje na zubda ruwan.Don haka bana tunanin ko mun tafi zan bar baya da ƙura,abinda kawai zaku yi ku kaita asibiti a ɗinketa da safe domin nayi ɓarna don taƙi bani haɗin kai.Tana da matuƙar daɗin da ban taɓa jin irinsa ba,da ƙyar na iya barinta ba don na gamsu ba." Ya kai ƙarshen maganar yana ɗane bakin Daddy da ya kasa cewa komi sai rawar baki yake,hawayen zallar baƙin ciki da takaici na cin zuciyarsa.

Uku da mintuna kusan arba'in suka gama operation ɗinsu suka bar gidan,bayan sun kwance ɗaurin da sukaiwa hannu da ƙafafun Daddy.Jikinsa na wani irin rawa ya nufi Gwaggo ya kwance hannayenta dake zamge da bakinta,suka kwasa a guje zuwa ɗakinsu Nasreen ba tare da sun bi takan Momy da Nasreen da ke yashe a sume a tsakar ɗakin ba. Wani mugun jiri ne ya ɗebi Gwaggon kaduna lokacin da idanunta suka sauka akan Najma dake yashe daga ƙasan bed ɗinsu.Rigar jikinta a yage ana ganin tsayayyun ƙirjinta da suka sha matsa a hannun ɗan fashin,ga gabanta da ya yi face-face da jini,gefe guda ƙazantar da ya fitar ne daga gefe kamar yadda ya faɗi da bakinsa bai yi ban ruwa a cikin gonarta ba.A hankali ƙafafun Gwaggo suka murɗe,ta silale ƙasa tana sakin wani shegen kuka mai razanarwa.Daddy ma kallo ɗaya ya yiwa inda Najma ke kwance ya fice a guje yana kuka kamar ƙaramin Yaro.A falo yaja birki yana nufan wajen da su Momy ke yashe ya kwance musu ɗaurin da akai wa baki da hannuwansu.Ya nufi side ɗin masu aiki da nan ne kaɗai basu shiga ba ƴan fashin, ya samesu sunyi carko carko suna ɓarin jiki.Don tun shigowar Ƴan fashin side ɗin suka farka, tsananin tsoro ne ya hanasu yin ko wani irin motsi ko ihun da za a san dasu a wajen.Cikin wani irin tsawa Daddy ke basu umurnin kawo ruwa da gaggawa zuwa falon don kwarawa su Momy ko zasu dawo hayyacinsu.Rabi ce ta fito a guje riƙe da sassanyar ruwan gora ta nufi wajen da su Momy ke yashe,ta ɓalle bakin goran ta kwara musu ruwan a jiki da fuskarsu. Suka kawo numfashi kusan a tare,suna tashi zaune jikinsu babu inda baya ɓari.bin kowa da komi suke yi cikin son tantance daga mafarki suka farko ko kuwa? Sai dai daga sanda idanunsu ya sauka akan Daddy dake zaune bisa sofa,ya dafe kansa da hannu bibbiyu yana kuka tamkar ƙaramin Yaro suka gane cewa ba daga mafarki suka farkaba.Nasreen ta miƙe a guje ta nufi ɗakinsu zuciyarta na bugawa da wani tashin hankali da tsoro da firgici mai tarin yawa.Tana yin ido huɗu da Najma da Gwaggo dake kuka wiwi ta saki wani razanan ihun da ya kawo Momy a guje zuwa cikin ɗakin.Ita ma kallo ɗaya ta yiwa Najma da halin da take ciki ta sake wani irin ihu tana dafe kanta da hannuwa bibbiyu.Ya tabbata dai ɗan fashinnan yaci galaban yin raping Najma,irin raping ɗin da dole a tausayawa wanda aka yiwa shi.A hankali Momy ta isa wajen da Najma ke yashe babu alamun numfashi a tattare da ita, ta janyo duvet ta rufa mata a jiki.Cikin muryar kuka ta bai wa Nasreen umurnin kawo ruwa,Nasreen da jikinta ke rawa tana zuba wani irin kuka mai cin rai ta nufi falo a guje tana sake sakin gunjin kuka. Da ƙyar Najma ta kawo numfashi tana buɗe idanunta akan Momy,ta saki wani irin ihu tana jijjiga kanta tamkar a lokacin abin ke faruwa.Ta motsa ƙafarta tana jin wani azaba na ratsa cinyoyinta zuwa ƙasanta da take jin tamkar ba a jikinta yake ba.Take komi da ya faru ya sake dawowa kwanyarta,wani irin tashin hankali da ƙunci da bata taɓa sanin akwai irinsa ba ya dinga rufe zuciyarta.Kiran sunan Inna Mairo ta dinga yi tana wani irin jijjiga tamkar numfashinta zai sake barin gangar jikinta.Inna Mairo da ke kwance warwas a falo bayan farfaɗowarta, sam ta kasa motsawa sai zuciyarta da ke mata wani irin zafi,kanta na sake yi mata nauyi da wani irin ciwo mara misaltuwa. Ihun Najma da ta sake jiyowa ya sanya numfashinta sake barin gangar jikinta,ta sake somewa take don zuciyarta ba za ta iya ɗaukar baƙin cikin da ke tunkaro rayuwarta da ta tilon ƴarta ba.Daddy ya nufi kanta yana kuka sosai,irin kukan da ke bayyana halin ƙaƙanikayin da bawa ke ciki.Wayoyinsa ya tuna dasu,sai ya miƙe a guje ya nufi side ɗinsa.A kan table ya hango laf wayoyinsu babu wanda suka tafi dashi, domin sun samu kuɗi da kadaran gwalagwalan da ba za su yi wahalar ɗaukar waya ta zame musu kaya ko hanyar tonuwar asirinsu wajen sanyawa ayi tracking nasu ba.Ɗaukar wayarsa ya yi ya kunna cikin rawar jiki,yana mai fara laluban lambar doctor Bakory.Bugu biyu ya ɗauka cikin alhinin ganin kira da sassafe daga Daddy ɗin,cikin rawar murya Daddy ke roƙonsa alfarman yazo gidansa don bada taimakon gaggawa ga Iyalinsa,bayan ya sanar dashi dukkanin abinda ke faruwa.Ya kashe wayar bayan doctor Bakory ya bashi tabbacin gashinan bisa hanya nan da ɗan wani lokaci.

Falon ya koma wajen Inna Mairo yana ƙoƙarin ganin numfashinta ya dawo amma bai yi nasara ba.Momy ita ma daga can ɗakin su Nasreen ƙoƙarin sake dawo da numfashin Najma da ya sake ɗaukewa suke yi amma abin ya faskara.Hakan ya sake jefa Nasreen cikin halin tashin hankali,tana ji dukkanin duniya na tsaya mata cak! Ta ɗakko wayarta da ke yashe a kashe bisa kan tiles ta kunna,tana mai jin relief da basu tafi da wayoyin kowa daga cikonsu ba.Layin Nabeelah ta soma kira,waɗanda su kaɗai ne suka tsira daga riskar wannan mummunan tashin hankalin.Domin sam ƴan fashin Allah bai basu ikon shiga side ɗin Yaya AD ɗin ba,don ga dukkanin alamu kamar suna tare da wani wanda ya san kan gidan da kuma mutanen da ke rayuwa a kowane ɓangare na cinkinsa ne.Basu ɗauka cewa akwai mutane a side ɗin ba tabbas da sai sun kai ziyara har nan ɗin.Bugu uku Nabeey ta ɗaga wayar cikin mayen bacci,Nasreen tayi saurin sake mata kuka tana sanar da ita mummunan yanayin da suke ciki.Bata bai wa Nabeelah damar magana ba ta kashe wayar, tana sake rushewa da kuka mai cin rai. Nabeey ta tashi Anty Hannah a firgice tana sanar da ita abinda Nasreen ta gaya mata,sai ta tashi a firgice tana ware ido da maimaita kalmar ƴan fashi da kuma raping a bakinta.Dukkaninsu cikin tashin hankali suka fito daga side ɗin nasu don isa nasu Momy.Suna fito wajen compound ɗin motar doctor Bakory na shigowa ciki.Bai yi mamakin ganin gate a wangale ba,domin Daddy ya sanar dashi komi a waya.Ya fito a gaggauce yana nufan wajen da Mai gadi ke yashe yana rawar jiki baki da hannuwansa a ƙulle.Ya kwancesa yana nufan cikin gidan a gaggauce,domin bada taimakon gaggawa ga wacce aka yiwa raping da kuma Inna Mairo da itama bata san inda kanta yake ba.Kusan a tare suka iso cikin falon tare dasu Nabeey,suka nema waje suka yi carko-carko suna kallon yadda Daddy ya fita a hayyacinsa tsabagen tashin hankali da ɓakin da yake ciki.Ɗakin su Nasreen suke shirin nufa amma sai Daddy ya dakatar dasu,suka dawo da baya suka tsaya akan Inna Mairo.Shi kuma ya yiwa doctor Bakory jagora zuwa ɗakin Nasreen ɗin.Basu jima da shiga ba su Gwaggo da Momy suka fito suna kuka wiwi na tausayin halin mummunar ƙaddarar data afkawa rayuwar Najma a dare ɗaya. Gwaggo ta nufi wajen da Inna Mairo ke yashe babu numfashi, ta fasa wani irin ihun tana jijjigata da kiran sunanta cikin ɗimuwa da tashin hankalin da bazai misaltu ba.Nasreen ma wajen Anty Hannah da Nabeey ta nufa tana wani irin kuka mai ɗaga hankali.Bakinta na faman furta, "Yayi raping ɗinta,wallahi ya yi raping ɗinta Anty Hannah!" Ta ƙare maganar tana sake fashewa da matsanancin kuka.Hakan ya sanya Nabeey durƙushewa ta saki wani irin kuka itama mai cin rai.Hannah ma jikinta rawa kawai yake yi, tana jin wani irin tausayi da tashin hankalin ƙaddarar da ya dirarwa kyakykyawar budurwa kamar Najma na ɗaga hankalinta.Suka rintse idanunsu baki ɗaya suna sake sakin kuka a tare, lokacin da kunnuwansu ya jiyo musu wani razananniyar ihun da Najma ta saki.

Daddy ya fara futowa daga ɗakin yana sharan hawayen da suka kasa tsaya masa.Ya yiwa su Momy duba ɗaya yana yafutota da hannu alamun tabi bayansa zuwa ɓangarensa,hakan ya sanya ta miƙe jiri na ɗibarta ta rufa masa baya.Ta bar su Nasreen na cigaba da rasgar kuka,kowanne a cikinsu na cike da alhini mai yawa a zciyarsa.Lokaci kaɗan Daddy da Momy suka fito cikin shirin fita,Momy na sanye da hijab dogo har ƙasa.Ta dubi Anty Hannah ta ce, "Hannatu zaki zauna anan mu je asibiti mu dawo,don daga Inna har Najma dole su samu kyakykyawar kulawa daga wajen likitoci." Daga haka suka nufi ɗakin Nasreen don ganin halin da Najam ke ciki, wacce ta farfaɗo amma kuma ta sake sumewa lokacin da doctor Bakori ke ƙoƙarin duban wajen da kyau.Momy na shigowa doctor Bakory ya sanar mata dole sai an yiwa Najma ɗinki.Nasreen ce ta shigo ta roƙi Daddy cewa zata bisu, sai ya amince don hankalinta ya kwanta.Daddy ne ya saɓa Najma a kafaɗarsa zuwa mota,Inna Mairo ma doctor Bakory ne ya saɓota zuwa mota da ƙyar, don tana da ɗan jiki da nauyi. Daga Anty

Please Login or Register in order to submit comment