Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sameni da maganar cewa makarantar kwana zai sama muku, hankalina sai ya tashi domin bani da sha'awar kiyi nesa dani tunda ke kaɗaice gareni da nake kallo inji sanyi a rayuwata.Amma girman Hakimi a idanuna da yadda yake ƙoƙarin ganin bai bar rayuwarki ya tagayyara a bayan idon mahaifinki ba, sai hakan ya hanani nuna masa rashin jin daɗina. Nayi masa godia tare da addu'ar fatan gamawa lafiya,sai da ya tafi ne na samu zarafin share hawayen damuwar da zai riskeni na rashinki a kusa dani. Ban taɓa nuna miki bana son ki da makarantar kwana ba, musamman da naga irin ɗoki da murnan da kuke yi ke dasu Lubah.Sai na kasa nuna rashin jin daɗina domin bana so ki bijirewa tafiyar, alhali soyayya da ƙaunace ta sanya za a yi miki wannan gatan. Na fara shirin tafiyarki ta hanyar yi miku ƴan ƙananun siyayyar da ɗalibi zai nema a makarantar kwana.Bake kaɗai na yiwa siyayyar ba har dasu Hanne da Lubah, don ba zai yiwu ace banyi karaba kamar yadda ni ake mini. Na ɗauki wasu kayayyakina na siyar nayi muku siyayya ba tare da kinsan cewa wani abu na ɗaga na siyarba.Ranar da kuka tafi makarantar kwana na Ƴan mata dake garin Basawa, nayi kuka da dare kamar ba zan daina.Damuwa ya fara yi mini yawa a zuci,sabida kewar rashinki dana mahaifinki. Ga kuma kewar rashin iyayena duka dana rasa, sannan ga baƙin ciki da damuwar yadda na kasa samun soyayyar ƴan uwana.Damuwoyi suka haɗu suka yi mini yawa Najma, sai dai da safe bayan na gama hidimata in kulle gidan in tafi gidan Hakimi wajen Inna Karima,musha hira ina tayata da wasu ayyukan gida. Haka na dinga yi har zuwa lokacin da Hakimi ya jajibo maganar ƙarin auren da zai yi, bayan ya yi tayi mini naci in bashi dama ya aureni na nunar masa cewa hakan ba zai taɓa yiwuwa ba. Ya yi naci har ya gaji, shi ne ya samo wata bazawara ƴar garin gangara ya aura. Tunda ya sake aure saina janye jikina da yawan zuwa gidan, sabida gudun husuma tunda gida ɗaya ya haɗe kan matansa, dole akwai buƙatar ka iya takunka. Na duba naga zama haka bazai yiwu mini ba, domin kwabo sai yafi ƙarfina. Hakimi ba ko yaushe yake bani kuɗi ba sai duk bayan sati biyu yake aiko mini kayan abinci da kuɗi naira ɗari biyar. Kuɗin basa yi mini kwana biyar sun ƙare, sai dai nayi ta maze-maze ina shiga takura kafin ya bani wani kuɗin.Dibara sai ta faɗo mini akan na ɗaga kujerun ɗakina guda biyu na siyar naja jari,in yaso sai na bar ragowar guda biyun. Na tafi gidan dillayi nayi mata magana, cikin kwana uku aka samu shigar dasu aka bani ƴan kuɗaɗena. Ina ta murna na fara tunanin mai zan fara, sai Inna Karima ta bani shawarar in fara suyan ƙosai sabida babu mai yi anan kusa.Na amince da shawararta na fara suyan ƙosai kamar da wasa, sai ga ciniki ya buɗe mini ana saya sosai. Tun ina soya mudu a rana har na dawo soya kwano guda.Da tafiya tayi nisa ma dawo ina soya har kwano biyu a rana. Ke duk bakisan da yawan gwagwarmayar da nasha ba,tunda sai hutu kuke dawowa gida.Dukkanin siyayyar da nake aiko muku keda su Hanne a ranar zuwan duba ɗalibai, duk da kuɗin sana'ar suyan ƙosai da nake yi. Na samu alkhairy mai yawa da wannan sana'a domin nafi ƙarfin komai, a cikin cinikin nake yiwa kaina cefane mai kyau.Duk ranar cin kasuwa zan je in yo siyayyata ta sati in dawo gida. Hankalina ya fara kwanciya sosai, amma damuwa da yawan tunani basu bar zuciyata ba. Duk dare sai na share hawayen baƙin yadda ƴan uwana suka manta dani, ni kuma ina son zuwa amma da zaran na tuna kalaman Gwaggo da irin tarban da nake samu daga gareta sai naji na sare bazan iya sake tunkarar inda take ba.Watarana na tara cinikina da nayi na ƙosai,kuɗi sun haɗu har dana wake da mai da nake siya na tuya. Da tsakar dare ƴan iskan ɓarayi biyu irin ƴan taurinnan suka shigo mini, suka nuna mini wuƙa suka ce kuɗi ko suyi mini yankan rago. Jikina na ɓari na fiddo musu dukkanin kuɗaɗen suka tafi dashi. Ba zan iya misalta miki irin tashin hankalin dana shiga ba,domin na shiga tsananin ƙunci da ɗimuwa. Inna Karima na je da kukana na sanar mata tashin hankalin daya sameni.Ta tayani baƙin ciki, ta tayani kuka domin kuɗine da sai dana wahala na tarasu,ko ince ina ma kan wahalar. Ta je ta samu Hakimi ta sanar dashi abinda ya sameni, ya kirani ya yi mini jaje tare da min alƙawarin zai bani wani jarin ko kaɗan ne in cigaba da sana'ata. Kuɗin da ya bani ba wani bane dubu biyarce, na amsa nayi godia na cigaba da sana'ata cikin maneji da ƙarfin zuciya. Tunda suka shigo mini sai ya zamana bana iya bacci, duk dare ina cikin fargaban karsu dawo mini su sake rabani da ɗan kuɗin da nake juyawa. Kafin wani lokaci sai yawan tunani da damuwa ya fara haifar mini da wani irin ciwon kai na ɓari ɗaya, na dangana da asibiti don likita ya dubani. Bayan anyi mini gwajin BP na amsa ƴan tambayoyi sai Likitan ya sanar dani cewa jinane ya hau sosai, dole in daina yawan tunani da sanya damuwa arai domin idan na cigaba to lashakka abin zai dinga cigaba ne. Ya kwantar mini da hankali sosai tare da karanta mini tarin illolin da sanya damuwa da yawan tunani a zuci ke janyowa lafiyar bawa. Nayi masa godia bayan ya rubuta mini magunguna kala biyu yace lallai in siya in fara sha, zuwa sati biyu in dawo a sake gwada BP ɗin aga ko ya sauka. Na dawo gida na sake zurfafa a tunanin yadda rayuwa ke gara mini, na fita da kaina na je nemo maganin a wani babban chemist a cikin gari. Da na bada takaddar suka duba sai aka faɗa mini kuɗin maganin dubu biyu har da ɗari uku,nayi shiru ina tunanin idan na siya duka kuɗin da nake juyawa ne zai rushe.Hakanan dai na siyo na dawo gida na tasa maganin ina hawaye,tausayin kaina na sake kamani sannan kalaman Likita shi ma na dawo mini. Maimakon in cire damuwa da tunani sai ma abu ya sake yin gaba, don bansan ta yadda za a yi a halin ƙuncin da nake ciki ace in cire damuwa a raina ba.A hankali cutar hawan jinin dai da likita ke guje mini ya sameni,ban taɓa faɗiwa kowa ba sai da jarin hannuna ya kai ga rugujewa sabida siyan magani. Na samu Inna Karima na sanar da ita halin da nake ciki, ta tausaya mini ta kuma yi mini nasiha akan in daure in daina sanya damuwa a zuci.Ina cikin wannan halin azumi ya zo, lokacin kun dawo hutu idan zaki iya tunawa.Ana saura kwana biyar azumi Gwaggo ta yo mana aiken kayan abinci da turmin atamfa aka ce inji Yaya Kabeeru. Ni ce dana fita wajen drivern yake mini tsegumin cewa ai Yaya Kabeeru ya kuɗance sosai, har ya sake gina danƙareran gida ya ɗauke Gwaggo ta koma hannunsa da zama.Sannan babban ciki ɗansa ma ya fita dashi ƙasar waje karatu.Na dinga mamaki nayi musu fatan alkhairy, ina ayyanawa a zuciyata cewa zan yi ƙoƙari inje in yima Gwaggo Allah sanya alkhairy tunda drivern ya rubuta mini address ɗin gidan. Kayan abincin kinsan muka sai da rabi don na sake samun jari, sauran muka aje bayan na ɗibarwa gidan Hakimi taliya da shinkafa ƴar gwamnati. Bayan sallah da sati biyu na kama hanya naje kaduna, idan kin tuna har kinso muje tare na nuna miki cewa ki bari na fara zuwa idan na samu fuska sai muje dake watarana.Cikin rashin sa a koda naje bansamu tarba wajen Gwaggo ba, sai a wajen Anty Zee da ta tarbeni cikin fara'a. Ta dinga tambayata abinda yake damuna domin duk taga na lalace, nayi duhu alamun ina cikin damuwa da matsaloli. Ban sanar da ita komi ba sai dai murmushi da nayi kawai na yaƙe.Ban samu ganin Yaya Kabeeru ba don ance ya yi tafiya zuwa wata ƙasa.Ina nan zaune sauran yaran suka dawo makaranta, waɗanda biyu daga ciki ma bansan fuskarsu sosai ba don tun suna ƙananu rabona dasu. Suka gaidani na amsa da fara'a ina yaba kyawunsu, dukansu mata ne su biyu waɗanda babu inda suka baro kamannin Momynsu. Babar cikin wacce ta fara zama cikakkar budurwa kamarki,ta ce mini sunanta Nasreen shekarunta sha biyar. Sai ƙaramar ta ce sunanta Nabeelah, shekarunta sha biyu ita. Ita asalin babbar Yayarsu mace mai bima babban ɗan Yaya Kabeeru Adnan, mai sunan Gwaggo Hauw suna kiranta Jiddah.Hajiya Zainab ta sanar mini tana Abuja a can take karatu a jami'ar NILE. Shi kuma Adnan yana London shekarunsa biyu kenan, saura shekara guda ya kammala amma ba zai dawo ba har sai ya yo masters ɗinsa.Na yi fatan alkhairy na fito daga sashin Hajiya Zainab da tsayawa misalta tsaruwansa ma ɓata baki ne.Ta haɗa mini sha tara ta arziƙi,na na koma sashin Gwaggo wanda ya gaji da haɗuwa domin an kashe mata dukiya ba kaɗan ba ina murna sosai. Babban gidane na garari Yaya Kabeeru ya gina a unguwar Rimi GRA. Ganin abin arziƙin da Hajiya Zainab ta haɗa mini ya sanya Gwaggo sake haɗe mini fuska, ta dubeni cikin ɗaure fuska ta ce, "To Mairo ba kin zo kinga arziƙi an haɗa miki abin kirki ki ce zaki dinga ɗakko jikina kina zuwa ƙaf da ƙaf ba, a dinga ɗaga ƙafa ana haƙuri da halin da aka tsinci kai. Tunda tunda fari kece kika zaɓi baƙauyen mijinki kika ce kinji kin gani, sai gashi rayuwa ta juya miki kinyi rashinsu daga shi har Abbanki da ya ɗaure gindi ya zaɓa miki rayuwar ƙauye.Kin ga yanzu dole ki rungumi ƴarki ku rayu a inda Ubangiji ya zaɓa muku, tunda kun sha faɗi a gabana cewa komi NUFIN ALLAH, to kema haka ALLAH ya NUFA a ƙauye zaki ƙare rayuwarki. Sai kiyi ta haƙuri zamu dinga aiko miki da taimakon da ya samu, don haka karki ce sai kin dinga ɗakko jiki kina yawan gidan ɗan uwanki kina zubda masa mutunci a gaban matarsa, tana ɗaukan abin hannunta tana baki ba." Gwaggo ta dakata da maganar tana kallon yadda hawaye ke gudu akan fuskata.Domin tunda ta fara magana naji wani abu mai nauyi ya danne zuciyata, na dinga ji tamkar in rufe ido in ganni a giwa na bar gaban Gwaggo. Ta taɓe baki ta cigaba da faɗin, "Ba kuka zaki yi ba Mairo, gaskiya nake faɗi miki don bana ƙaunar ganin kina kusanto inda nake.Har yanzu zuciyata bata daina jin zafin yadda kika zaɓi bare kika bar ɗan uwana ba, ban daina jin kishin yadda Abbah ya fifita ƙaunarki dana bare akan ƴan uwanki ba. Don haka yanzu lokacin mune gara ki bamu dama muyi rayuwa cikin kwanciyar hankali, ba tare da kin cigaba da ƙuntata zuciyata da ganinki kusa dani akai-akai ba. Kiyi haƙuri ki zauna a inda Allah ya zaɓa miki, zamu dinga taimakonki da abinda ya samu lokaci zuwa lokaci." Daga haka ta miƙe ta nufi hanyar wani corridor ta shige ciki, bata jima ba ta fito hannun duntse da kuɗi. Ta iso inda nake zaune ina kuka tamkar raina zai fita, ta aje mini kuɗin akan cinyata tana faɗin, "Ga kuɗi nan ki riƙe, zan sanya a zuba kayan abinci a mota sai Adamu driver ya maidaki gida.Kin ga kin huta da wahalar bin motar kasuwa." Har ta dasa aya na kasa ɗagowa na dubeta tsabagen yadda na muzanta a gabanta,maganganunta suka dinga ci mini zuciya ina ji tamkar in mutu inbi su Abbah ko zan huta da gani wannan baƙin ciki da tozarcin na Gwaggo. Kamar yadda ta faɗi ta sanya aka zuba mini kayan abinci a bayan mota,aka haɗa harda su kayan tea masu yawa duk aka jibga mini.Ko kaɗan wannan kyauta bai yi mini daɗi ba, domin ba don kar Gwaggo ta ce na ci mutuncinta ba, tabbas da ko tsinke ba zan fito dashi daga gidan Yaya Kabeeru. Muna tafe ina kuka har muka shigo garin giwa sannan na share hawayena don bana so ki tambayeni mai ya faru,sabida naci alwashin ba zan sanar dake irin cin mutuncin da Gwaggo tayi mini ba.....

Inna Mairo tayi shiru tana jin yadda wani abu mai tauri ya danne zuciyarta. Najma dake sauraren Inna Mairo zuciyarta na tariyota mata a halin da Inna ta dawo lokacin. Don a ranar kwana tayi tana kuka har sai da hawan jininta ya motsa sabida damuwa da rashin bacci.Kuma duk yadda taso sanin abinda ya faru da Innar taƙi sanar da ita, daga ƙarshema sai tayi mata kashedin cewa karta sake damunta da saita san meyafaru matuƙar tana son ganin kwanciyar hankalinta. Inna Mairo ta numfasa tana cigaba da faɗin, "Ba saina tsaya maimaita miki komi ba Najma, domin wannan zuwa da nayi shi ne zuwana na ƙarshe garin kaduna wajen Gwaggo. Na kife babinsu tare da danne dukkanin ƙawazucinsu a can ƙasan zuciyata.Kiran wayar ma da nake yi na daina, a ƙarshema wayar nawa ta lalace. Dukkanin abinda muke dashi a hankali ya dinga ƙarewa,tun ina ɓoye miki halin damuwar da nake ciki har kuka kammala karatu kika dawo gida baki ɗaya.Ta yadda komi ya cigaba da kasancewa akan idanunki.Hakimi dai shi ne gatanmu bayan Ubangijin da ya haliccemu. Shi ne komi namu hatta kuɗin maganina daga baya shi ya ɗauki ya dinga ɗaukar nauyin saye, tunda jarin sana'ar nawa ya jima da rushewa. Sannan likita ma ya hanani kusantar wuta tun wani kwanciya da nayi jinya nasha baƙar wahala. Dawowarmu gida ne kika ce kin ji kin gani ke zaki amshi sana'ar ki cigaba da yi, da ɗan ragowar kuɗin gadon ɗakina da muka siyar. Cikin maneji da ƙarfin zuciya muke cigaba da gudanar da rayuwarmu, har zuwa lokacin da lafiya yaƙi min hannu domin na kasa daina tunani da jin zafin wofintar dani da ƴan uwana suka yi. Shi Yaya Ali ma a bakin drivern Gwaggo da take aikowa duk azumi ya kawo mana hatsi da atamfa na ji cewa ya bar ƙasan,shi da Iyalinsa ya koma ƙasar Cairo da zama. Nayi masa fatan alkhairy a cikin zuciyata ko ke ban sanarwa ba, don banga amfanin sanar dake ɗin ba. Wannan shi ne tarihin rayuwata Najma, da irin baƙin ciki da ƙiyayyar dana fuskanta daga wajen Gwaggon kaduna.Har kuma kwanan yau ina cikin baƙin yadda na gaza samun soyayya da kulawar matar uba,na gaza samun soyayyar ƴan uwana da su ɗaine suka rage mini a duniya. Na kasa daina jin ciwon yadda na kasa cigaba da bin wasiyyar Abbah na cewa karna yanke zumunta dasu, amma zuciyata ba zata iya cigaba da kusantar Gwaggo da Ƴaƴanta suna ƙunsa mini baƙin ciki ba. Duk da cewa nafi ganin laifinta domin shi Yaya Kabeeru ina da tabbacin ba don Gwaggo ce ke yi mini katanga dashi ta hanyar nuna ƙarfin ikonta akan su bi dukkanin umurninta ba, da zan samu sassauci da kusanci dashi. Musamman da ya kasance matarsa mai zuciyar alkhairy da tausayi ce, ita ma babu yadda ta iya da Gwaggo ne shiyasa bata zaƙewa akan son daidaita tsakanina da ɗan uwana.Ba laifina bane Najma, dolece ta sanyani nisantarsu ba don zuciyata na son hakan ba, sai don na tsira da mutuncina na kuma gujewa zuciyata ɓacin ran da zai iya assasa ciwona ya sake munana. Sai gashi na barsu amma takaici da baƙin cikin yadda suka wofintar dani bai bar zuciyata ta huta ba, sai ma barazanar kamuwa da cuta da take shirin yi. Na horeki da karki sanya damuwar jin wannan tarihin nawa a ranki har ya zama kin riƙesu a zuciyarki, don zuwa yanzu na aminta na kuma tabbatar cewa tabbas haka ALLAH Ya yi NUFIN rayuwata ta kasance." Inna Mairo ta kai ƙarshen maganar tana kuka da hawaye. Dukkanin rauninta ya gama bayyana, domin ta famo mikin da ta jima da danneshi a ƙasan zuciyarta. Najma kuka sosai take yi tana mai jin tsananin tausayinsu na sake keta zuciyarta, sam bata san irin waɗannan cin mutuncin Inna Mairo ta fuskanta daga wajen Gwaggon Kaduna ba. Da tabbas ba zata matsa mata da son jin tarihin rayuwarta ba, sai dai kuma ta wani fannin taji daɗin hakan domin a yanzu ta gane cewa ba laifin Inna Mairo bane.Babban mai laifin ita ce Gwaggo, amma kuma shi ma Yaya Kabeeru a matsayinsa na babba da Abbah ya bashi amanar Innar ya ce su maye mata gurbinsa, bai kamata ace ya wofintar da wasiyyar Abbah ya biyewa son zuciyar Gwaggon ba. Da ace ya ji kulawa da ita zai dinga bibiyarta koda a wayane yana sanin halin da take ji, idan suna da buƙata ya taimaka musu yadda ya kamata ba tare da ya bari Gwaggo ta san yana yi ba. Koba zasu tako ƙauyen garin giwa ba, yaci ace suna kulawa da rayuwarta ya hanyar samar da wani da zai dinga zuwa yana duba musu ita ya kuma kawo mata tallafin da duk take da buƙata daga garesu.Amma sam bai yi hakan ba sai ya biyewa son zuciyar Gwaggo ta raba zumuntarsu, ta nesanta Innar daga zuwa gareta bare har ta raɓi ƴan uwan nata ko Iyalansa. Najma ta sauke zazzafan numfashi tana jin tsanar Gwaggon Kaduna na samun gurbi a zuciyarta. Hannu ta kai kan fuskar Inna Mairo tana share mata hawayen da suka kasa tsaya mata.Cikin sanyin murya take faɗin, "Kiyi haƙury Inna, tabbas baki da laifi domin koni ce iyakar matakin da zan ɗauka kenan na ƙaurace musu. Allah shi zai cigaba da zama gatanmu, ba zai taɓa bari mu tagayyara ba Inna In Sha Allah! Ki cigaba sa haƙuri tare da danne dukkanin baƙin cikinsu, koma ince ki cireshi baki ɗaya daga zuciyarki. Lafiyanki shi ne abin tattalawa a yanzu, ba wai sake sanya tarin damu da ƙuntata zuciyarki ba. Ba zan sake miki zancensu ba Inna, kamar yadda ba zan so kema ki cigaba da sanya damuwa a ranki ba." Ta kai ƙarshen magiyarta ga Inna tana duban fuskar Innar da ya yi jajir sabida kukan da take yi. Inna Mairo ta sauke hannuwan Najma daga kan fuskarta tana jinjina kai ta ce, " Na gode Najma! In Sha Allah zan kiyaye lafiyata ko dan ke dana mallaka, nake kuma burin rayuwa tayi mana tsayi tare da juna. Allah ya haska rayuwarki Najma,Ya yi miki albarka tare da shiriya na addinin musulumci, ke da ɗaukacin ƴaƴan musulmi baki ɗaya. Gwaggo ita ma ina mata addu'ar Allah ya ganar da ita, ya kuma juyo da hankalin ƴan uwana zuwa gareni." Najma ta amsa da cewa "Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum Inna!" Daga haka suka tashi sakamakon kiran sallar la'asar da aka yi, Inna ta nufi tsakar gida don ɗaukar buta ta yo alwala,yayinda Najma ta nufi ɗakinta tana ji zuciyarta na cigaba da yi mata rawa.Tausayinsu dana rayuwarsu na sake samun wajen zama a zuciyarta. Cikin ranta ta dinga jin ƙarin ƙaunar Hakimi da ahalinsa, domin sune suka zame musu haske a rayuwa,kuma sune suka zame musu bango majingina. Ba don su ɗinba da yanzu suna cikin halin ƙunci mai muni, musamman ita Najmar da yanzu bata samu feature mai kyau ta samu ilimin zamani dana addini da ta samu a yanzu ba. Wanda har take da burin cigaban karatun idan rayuwa ya zo mata da sauyin da hakan zai iya kasancewa.Inna na shigowa ɗakin ta fito ita ma ta nufi waje don ɗauro nata alwalar............✍🏻


🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻*
*MTN*
*GLO*
*AIRTEL*
*9MOBILE*
*MONTHLY VADILITY 💃🏻*


*DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻




#Lovestory#
#Najma#
#Aysha Ɗansabo Lemu🥰
[2/28, 2:39 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻
_*Arewabooks@ayshadansabo*_

*Paid book:500*

*Chapter 7*

_Free page_


Bayan sun idar da sallar la'asar ɗinne Najma ta sanya hijab ta nufi gidan Adama dillaliya. Ta taki sa a ta sameta a gida bata fita ba, don sam bata faye zaman gida ba sai yawon neman hajan saye da siyarwa. Najma na sanar da Adama maƙasudin zuwanta, tayi mata sallama ta kamo hanyar dawowa gida. Tafiya take yi cikin takunta mai cike da nutsuwa ta halitta, ko kaɗan bata kallon ko'ina sai inda ƙafafunta suke takawa. Kamar daga sama ta jiyo muryar Luban gidan Hakimi daga bayanta, sai tayi saurin waiwayawa fuskarta na haskawa da murmushi mai faɗi. Lubah ta ƙariso wajen da Najma ta ja tayi tsaye tana faɗin, "Hey! B beauty daga ina? Najma ta sake sakin murmushin da har fararen haƙoranta suka bayyana, sannan ta dubi Lubah tana bata amsa da faɗin, "Daga gidan Adama nake, wai ku kam ba za ku daina kirana da B beauty ɗinnan ba ko?" Lubah ta saki ƙaramar dariyar tana faɗin, "Yo ai sunan daidai da ke ne Najma, domin kowa ya yi miki kallo ɗaya zai shaida cewa ke ɗin black beauty ce ta gaske." Najma ta jefawa Lubah harara suna mai jerawa da juna suka cigaba da tafiya don komawa gida. Suna tafe suna hiran tuna baya na school ɗinsu da irin wuyar da suka daga farko farkon zuwansu makarantar kwanar. Najma ta dinga jin wani shauƙi da kwaɗayin son cigaban karatunta na kamata. Ta sani cewa a yanzu babu wannan halin, domin Baba Hakimi burinsa suyi aure ne ba karatu ba.Bashi da ra'ayin mace ta zurfafa karatu sai maza,hakan yasa ya bai wa su Lubah umurnin fiddo mazajen aure. Najma ce kaɗai bai matsawa ba don Inna ta sanar masa sam bata son ana mata maganar aure. Gashi akwaita da farin jinin samari, duk da cewa duk masu zuwa sai ta ce basu yi mata ba Sabida basu da wadatacciyar ilimi kamar yadda take da burin samun abokin rayuwar mai wayewa da ilimin addini dana zamani.Don haka sam bata sauraren dukkanin samarin ƙauyen giwa da ke nufota da ƙoƙon bararsu, don yawancinsu duk basu yi karatun kirki ba.Tun Inna na mata faɗa akan ta dinga sauraran masu zuwa gareta har ta gaji ta zuba mata ido, tana dai yi mata addu'a Allah ya yi musu zaɓi na gari, don komi lokacine ta sani idan lokacin auren yazo Allah xai kawo wanda zai sace zuciyar Najmar farat ɗaya har ta amince masa. Sannu a hankali suna tafe suna hira har suka iso ƙofar gidan Hakimi, wanda shi ne na farko kafin a yi can gaba sannan a isa gidansu Najma ɗin. Lubah ta dubi yadda Najma ta toge a tsaye alamun ba shiga gidan nasu zata yi ba,ta buɗe baki ta ce, "Najma yanzu muzo har ƙofar gida tare ba zaki shiga ku gaisa da Inna ba?" Najma ta ɗan saki murmushi tana narke fuska ta ce, "Afuwan my Lubcy! Sauri nake na je na sanar da Inna yadda muka yi da Adama, zan zo na musamman gobe na yini musha hira." Lubah ta harareta tana faɗin, "Allah ya kaimu goben, ki gaida min Inna Mairo ki sake mata sannu da jiki." Najma tayi gaba tana faɗin, "Zata ji In Sha Allah!" Daga haka ta cigaba da takawa har ta isa gida.A tsakar gida ta samu Inna Mairo ta shinfiɗa tabarma tana zaune tana lazumi da carbi riƙe a hannunta. Ta samu waje kusa da ita ta zauna tana faɗin, "Inna sannu da hutawa, na samu Adama ta ce zuwa da safe za ta zo ta ga girman katifar." Inna Mairo ta jinjina kai tana faɗin, "Allah ya kaimu Najma." ta ɗaura da cigaba da cewa, "Kina fita Babanku Hakimi ya aiko Ummaru da kayan abinci, gasu can an aje a madafi har da kuɗi dubu ɗaya ya haɗo dashi." Najma ta sauke nunfashi, girma da ƙaunar Hakimi na sake girma a zuciyarta. Cikin tsananin

Please Login or Register in order to submit comment