Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

don't know..". Junaid ne yake fad'in hakan tare da gyara kwanciyarsa shi dai so yake yayi bacci!

Sai ji yayi tace "my son where is Ayush?"
Ji yayi kamar an dasa masa abu a zuciyarsa da sauri ya tashi zaune yana fad'in "Yushert Ina take? Bazan Iya tuna lokacin da na ganta ba, I can't but I known tana cikin matsala! I can't leave her, let me go and fine her..."

Da sauri ya mi'ke tsaye zai tafi
Mommy tayi saurin ri'ke hannun sa tana fad'in "Ina zaka? Wallahi ba yanda zakaje Junaid,
Bari na Kira waya zance a dubo mun ita."
Ta karisa maganar tana press d'in wayanta, cikin kankanin lokaci akayi picking
Other hand "hello hajia barka da yammaci.."
Amsawa tayi da "Doctor Musa meyasa Wayan Hasheem baya tafiya ne tin jiya?"
Other hand "haba hajia duk abunda ya faru baki sani ba?
Anan ya kwashe komai ya gayawa mommy, daga karshe ya sanar mata cewa yanzu haka Dr. Hasheem rai a hannun Allah....."

Sake wayar hannunta tayi tana fad'in "innalillahi wa Inna ilaihi raju'un, na shiga uku na Junaid you want to kill Dr. Hasheem? me yayi Maka? haba my son ka manta ku abokai ne?"

Shi dai Junaid kallon mom d'insa yake na rashin fahimta yace "wai menayi wa Hasheem ne?
Kinga mom kibar maganar nan please."

Mommy bata tsaya ta saurare shi ba ta fice daga d'akin Junaid, da sauri ta dauki key din motor ta nufi harabar gidan tana fadin "Allah yasa Junaid baiyi kisan kai ba wayyo niii"......

Sai tashin mota kawai Junaid yaji har mom ta fita daga gidan!
Asibiti ta nufa..

Shi har cikin zuciyarsa ya mance da abunda ya faru, sai ma wani irin bacci ne ya d'auke shi...
Gashi da 3 quarter a jikinsa sai rigar wandon mai hannun singlet fari soll kayan sunyi masa kyau sosai,
A kwana d'aya har Junaid ya rame fuskarsa ya yi fiyau haskensa ya 'kara bayyana...

Baccin Junaid yayi nisa sosai har ya fara mafarkin wata Yarinya tana zaune a bakin ruwa yana tayin ambaliya, ta 'kankame jikinta da hannayen ta biyu tana ta kuka, gurin ta yaje yana tsaye ta bayanta yace "Yushert! Why are you crying?
Because of me? Please am so sorry I will not try to hurt you again..?
Kaiwa hannunsa yayi saitin kafadar ta zai dafa ta,
Tashi tayi da sauri tana fad'in" don't try to touch me, I hate you Junaid,
Ina sonka har cikin zuciyata amma kai Baka da burin da ya wuce ka wulakanta ni ka tozarta ni a idon duniya,
Why Junaid? Why! Why!! Why!!!.."

Tana tafiya ta baya tana shige wa cikin ruwan, bayan ta kuwa 'katoton rami ne wanda ruwa yake shigewa ciki ba'a ganin karshen ramin!
Saida ta zo dab da ramin ta tsaya sannan ta Kuma cewa " Junaid zan tafi na bar maka duniyar"

"please Yushert kar kiyi mun haka, ki yafe mun, nayi miki alkawarin bazan kara cutar da rayuwar ki ba, bazan kara musguna miki ba I promise you ๐Ÿ™"
Hawaye duk ya wanke masa fuska yana rokonta...

Itama hawayen take tace "Junaid kaji dadin ka kawai..."
Sai luuuuu ta fad'a cikin Wannan ramin.

"Yuuuushertttt.."
Da karfin gaske ya kwalla mata kira, yayi gurin ramin da gudun gaske...

Dai den lokacin ya tashi daga mafarkin a tsorace yana huci, zuciyarsa kuwa sai bugawa take.
Gudu_ยฒ sauri_ยฒ ya mi'ke ya soma bubbud'e drowowinsa cikin sa'a ya samu key na mota motocin sa sunkai goma duk mallakinsa,
Haka ya fice daga gidan ba tare da mom ta sani ba!
Karfe 10 na dare yanzu, ga kuma ruwan sama da aketa zabgawa kamar da bakin karya...

A haka Junaid yabar gidan, hanya d'aya ya mi'ka zaije nemo Ayush, hankali sa bazai kwanta ba indai bai nemo yarinyar nan ba, gudu kawai yake da motor yana duba lunguna amma baiga Ayush ba,
Ya gama shan yawonsa har su bayan gari, tituna duk ya zagaya amma ba ko alamunta, ga ruwan sama kuma sai Kara yawa yake, daker yake iya wuce wa gurin da ruwa ya taru...

A bakin hanya ya yi parking yana zaune cikin motarsa, duk yabi ya damu kamar yayi ihu haka ya daki kan sitiyarin motar yana fad'in "ooh my God, ban ganta ba, ohhh Yushert where are you, nasan nayi miki laifuka amma kiyi hakuri Kar ki barni, idanuwa na sun riga da sun saba ganinki a koda yaushe! kar kiyi nesa da idanuwa na Yushert, don't leave me alone...."

Kwantar da kansa yayi akan sitiyarin motar, kamar mai yin bacci! Lokaci guda Kuwa ya tashi ya soma jan motarsa a hankali duk jikinsa ba kwari, yana cikin jan motarsa kwatsam sai yaga wata doguwar Yarinya ta gaba da motarsa tana tafiya a hankali ta rungume jikinta da hannayen ta, gajeren wando ne a jikinta wanda ya tsaya mata a iya gwiwa, sai kuma ta maida rigarta kamar mayafi ta rufe jikinta da shi! sai suman gashi kuma a kwance saman gadon bayan ta,
Tafiya take ruwan saman yana mata duka,
Duk ruwan nan da akeyi duk akanta ya 'kare, sai kakkarwa take tana rawar sanyi....

Parking yayi a gefenta yana kiran "Yushert! Yushert!! Yushert!!!" amma bata kula ba, ita har yayi parking bata sani ba kiran sunanta da yake yi duk bata ji ba,
Tafiya kawai take yi amma hankalin ta baya jikinta, banda qarar ruwan sama ba abunda take jii...

Saida ya fito yasha gaban ta ya ri'ke hannun ta yana fad'in "Yushert Ina zakije ne, d'ago ki kalleni Junaid d'inki ne fa.."

Ita kuwa kanta a 'kasi ta kasa d'agowa,
'Dago da ha6arta yayi yana fad'in "took at me mana Yushert..."

Fashewa tayi da kuka ta rungume shi sosai a jikinta, shima rungumarta yayi ya d'ora d'ayan hannunsa ya d'ora akan sumar gashin ta...

Ruwan sama ne yake jibgarsu amma sun kasa motsawa sai da Junaid yayi jagab shima! daman ita kam a jiqe take.
Sun dad'e suna rungume da juna kafin nan Junaid ya yi mata d'aukar jaririya ya shigar da ita cikin motar sa,
Suka nufi hanyar gida....................




*๐Ÿค SDEENDTM DATA SERVICES๐Ÿค*
*MTN* . *Airtel*
1GB = โ‚ฆ300. 1GB = โ‚ฆ350
2GB = โ‚ฆ600. 2GB = โ‚ฆ700
3GB = โ‚ฆ900. 3GB = โ‚ฆ1000
4GB = โ‚ฆ1200. 4GB = โ‚ฆ1300
5GB = โ‚ฆ1500. 5GB = โ‚ฆ1600

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = โ‚ฆ350. 500Mb โ‚ฆ250
2GB = โ‚ฆ700. 1GB โ‚ฆ500
3GB = โ‚ฆ1050. 2GB โ‚ฆ1000
4GB = โ‚ฆ1400. 3GB โ‚ฆ1500
5GB = โ‚ฆ1750. 4GB โ‚ฆ2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ
*๐Ÿช€08066268951*

*ASMEETAH* *CE* โœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธ

*FREE* *BOOK*

๐Ÿ… *MATAR* *DAMUSA* ๐Ÿ…
(the wife of tiger)

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* โœ๏ธโœ๏ธ


*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦ™alaminmu ฦดancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ *{{N W A}}* ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ


ุจูุณู’ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู…ู ุงู„ู„ู‘ู‡ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญู’ู…ูŽู†ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญููŠู’ู…

*BOOK* *ONE*
*PAGE*โžก๏ธ49 & 50โฌ…๏ธ


Bayan isowar su Junaid gida ya bude murfin mota
Ya rungumo Ayush kamar wata jaririya da sauri ya nufi daki da ita, itama cakumar sa tayi idonta akan kyakykyawan fuskar Sa!
Direct upstairs ya haura da ita ya nufi dakin sa....

Mommy kuwa tana can tare da Doctor Hasheem bazata iya baroshi a halin data ganshi ba, tayi matukar tausaya masa ga ba uwa ba uba duk basa raye sai en uwansa...

Junaid kwantar da Ayush yayi saman gadonsa duk sunyi jirib da ruwa, juyawa yayi zai nufi toilet tayi saurin ri'ko hannunsa,
Juyowa yayi yana kallonta!
Daker take motsa baki tace "inaso zanyi wanka, jikina ciwo yake mun, ka taimaka mun na shiga toilet..

Jinjina kai kawai yayi ba tareda yace komai ba, yasa hannu ya tallafa Mata, rigar data d'aure jikinta dashi ne ya sulale 'kasi!
Yazamana babu komai a jikinta sai breast d'inta da suka bayyana!!!
kallonta yake daga sama har 'Kasa idonsa ne suka sauqa akan gajeren wandonta dake ji'ke da jini duk ya 6aci...

Ita kuwa baiwar Allah ta rufe idanuwanta rub tsabar kunya, sai hannayenta data rufe breast d'inta dasu,

Duba gaban kayansa yayi yaga duk ta 6ata masa jiki da jini,
Kallon face d'inta yayi yakai hannunsa ya tallafo kanta still idanuwanta a rufe.
Yace "what happened to you?"

Girgiza kanta tayi kawai ta kasa cewa komai..

"Somebody try to rape you?.."
Da sauri ta bud'e idonta tana masa kallon 'kurilla,
Lips d'inta ne ya soma motsi yana kakkarwa, kasa magana tayi sai kukan daya ku6uce mata...

Gabansa ne ya fad'i Rassss!
kar hakan ta tabbata fa,
Yayi maganar a cikin zuciyarsa! Idan kuwa hakane zanyi kisan kai...

Idonsa ya kuma kaiwa kan wandon,
Yakai hannunsa saitin wajen yana matsa gurin.

Ido ta zaro waje tana kallonsa ta dakata da yin kukan.
Ganin bata yi wani shock ba yasa shi yin murmushi yace "your period..."
Domin yasan inhar raped d'inta akayi dole zataji zafin gurin, rufe fuskar ta tayi da hannunta..

Bata ankara ba taji ya yi mata d'aukar jaririya
suka nufi toilet ajiyeta yayi a cikin bahon wanka, cikin wani irin yanayi yace
"you want me to remove your nicket?.."

Da sauri ta girgiza masa kai alamar a'a,
"OK" yace tareda fita daga cikin toilet ya rufe mata kofar!.

Bayan fitar sa bakin gado ya samu ya zauna ya dafe kayinsa da hannayensa wani irin tunani ne ya fad'o masa,
"ya akayi banga kaya a jikin yarinyar nan ba? to ina taje, Kuma meya faru da ita!!
Wani irin tambayoyi yake jerawa kansa wanda shima kansa baisan amsar su ba...

Itama tana cikin seat birth ta fara maganar zuci tana fad'in
" yaushe Junaid ya canza haka? ba'a haka na barshi ba, to meya faru? shin ya suka 'kare da Doctor Hasheem?"
wadannan tunanin ne ya fad'o Mata..
Daga bisani kuma ta kalli wandonta tana fad'in "wannan jinin kuma daga ina? bansan dashi ba, period d'ina yazo ba alamun komai!"

Daker ta Iya tashi ta kunna shower a kanta, tayi wanka cikin nutsuwa dake ruwan da zafinsa.

Bayan wasu mintuna ta fito daga cikin toilet tana d'aure da towel a jikinta,
Ganin ta yasa ya zuba mata eyes
Tsayawa tayi ta kasa motsawa ko ina kallon da yake mata ne yasa jikinta macewa, tsinkar jikinta ne yake zubawa,
A hankali ta d'ago da manya-manyan idanuwanta wadanda suka shanye itama kallonsa take cike da sha'awarsa a wannan yanayin da ake ciki ga canjin weather duk garin ya d'au sanyi...

Shi kuma gogan ba fa kallon sha'awa yake yi mata ba sai dai kallon burgewa da kuma kauna, tinda shi bai san yanda ake jin feeling ba, ko mafarki bai ta6a yi ba, balle yaji a ransa wai yana son kasancewa da mace, bai ta6a kawowa hakan a ransa ba...

Ganin ta'ki motsawa yasa ya d'auki ledar da yake gefensa ya nufi gurin da take tsaye
Ya ciro paad leda guda da pant ya mi'ka mata su,
Jiki a sanyaye ta kar6a ta koma cikin toilet ta sanyasu kafin ta sake fitowa
Ba'kar jallabiya ya ciro a cikin wardrobe dinsa, shi da kansa ya sanya mata shi, ya tattaro suman gashin ta yayi rolling dinshi, turare ya d'auka akan mirror ya feffeshe jikinta da shi..
Ita kuwa ta tsaya kamar gunki sai kallonsa take ko qibta ido bata yi, abun ma mamaki yake bata a ranta tace "wai anya kuwa wannan Junaid ne?"

Katse ta yayi da cewa "bakya gajiya da kallo nane.."

Kawar da idonta tayi gefe cikin jin kunya...
Wuce wa yayi ta gefenta shima ya shige toilet domin yin wanka..

Kafin ya fito kuwa ta canza bedsheet din gadon ta gyara room d'in yayi matukar kyau, ta goggoge tiles da su jikin mirror ta feshe d'akin da turare mai kamshin gaske,
zama tayi a bakin gadon tana hutawa a daiden lokacin shima ya fito daga toilet, ganin yanda room d'insa ya tsaru yayi kyau abun ya burge shi,
Ga bedsheet mai launin milk, labulayen room suma milk, ga carpet ma milk, ta canza colour hasken d'akin ya koma green light!
Abun sai wanda ya kalla gwanin burgewa...

Ita kuwa tana zaune a bakin gado Suna facing juna,
Gani yayi ta koma masa kamar wata aljana farin ta ya fito sosai, dama gata fara ce sol sai kuma gashi tana period haskenta ya koma yellow-ยฒ
Gashin kanta kuwa baqi wulik sai she'kin da yake yi, ga bakar jallabiya a jikinta,

(wow farar mace, doguwa mai gashi ko mayya ce muna sonta inji yayana ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ)...

Nufan gurin mirror yayi idonsa kuwa akanta, ta zuba masa manya-ยฒ idanuwanta ga eyelashes d'inta Zara-Zara.
Ta zamo masa kamar bil jinni har yaso ya tsorita,
Kyanta yayi yawa, bugu da qari ma suman kanta har tudun duwaiwayan ta sai dai a yanzu masoyi Junaid yayi mata rolling d'insa,
Tsayi kuwa duk tsayin Junaid da kad'an ya d'arata tsayi,
Asalin doguwar mace ce sai dai ba qiiba...
Lips d'inta kuwa jaawur kamar wacce ta shafa red lipstick.

Cream d'insa yake shafawa mai shegen kamshi yana yi yana waiwayo Ayush, a tunanin sa kar yaje aljana ce!

Amma kuma ta wani 6angaren tunani yake yana maganar zuci "wannan kamar ita nake gani a cikin mafarki na, tayi mun kama da yarinyar cikin mafarki na! kuma yanayinsu d'aya da wannan Yushert, komai nasu iri d'ayaaa!.......


MASHA ALLAH
IDAN LITTAFIN YAYI MUKU INASON GANIN RUWAN COMMENTS,....
A KUMA TEMAKA MUN DA SHARING ๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™

Nagode masoya na, kamar yanda muka hadu Anam gidan duniya Ina fatan Allah ya hada kayuwan mu a gidan aljanna ๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™



*๐Ÿค SDEENDTM DATA SERVICES๐Ÿค*
*MTN* . *Airtel*
1GB = โ‚ฆ300. 1GB = โ‚ฆ350
2GB = โ‚ฆ600. 2GB = โ‚ฆ700
3GB = โ‚ฆ900. 3GB = โ‚ฆ1000
4GB = โ‚ฆ1200. 4GB = โ‚ฆ1300
5GB = โ‚ฆ1500. 5GB = โ‚ฆ1600

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = โ‚ฆ350. 500Mb โ‚ฆ250
2GB = โ‚ฆ700. 1GB โ‚ฆ500
3GB = โ‚ฆ1050. 2GB โ‚ฆ1000
4GB = โ‚ฆ1400. 3GB โ‚ฆ1500
5GB = โ‚ฆ1750. 4GB โ‚ฆ2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ
*๐Ÿช€08066268951*

*ASMEETAH* *CE* โœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธ

*FREE* *BOOK*

๐Ÿ… *MATAR* *DAMUSA* ๐Ÿ…
(the wife of tiger)

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* โœ๏ธโœ๏ธ


https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt


Wannan page ษ—in sadaukarwa ne wa masoyana masu mun comments da kuma sharing ๐Ÿฅฐ๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜


*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦ™alaminmu ฦดancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ *{{N W A}}* ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ


ุจูุณู’ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู…ู ุงู„ู„ู‘ู‡ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญู’ู…ูŽู†ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญููŠู’ู…

*BOOK* *ONE*
*PAGE* โžก๏ธ51 & 52โฌ…๏ธ




Please Login or Register in order to submit comment