Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana gaya musu maganganu, ransa a 6ace!
wannan Birin tsohon Biri ne domin tin kafin a haifi su Sarki Raamud yake 'kar'kashin mahaifinsu Sarki Zaid, domin a hannunsa aka haifi su twins wato mahaifin Junaid da Mahaifin Ayush, yasan komai akan masarautar nan, duk abubuwan da suke faruwa akan Junaid ya sani shuru kawai yayi,

'Dan Dattijon Biri kam bayan ya gama tsigale su ya kuma cewa
" *Ni zan koma yanki na, gobe da safe zan dawo na duba jikinta".....*

yana kaiwa karshe yayi tafiyarsa bai tsaya sauraron abunda zasu ce ba..

Uma Bara'at ce ta kalli Sarki Raamud idonta duk ya cicciko da 'kwallah tace "Ina dai gashi duk laifinka ya shafe ni, yana magana yana jam'i baya ware ni acikin maganarsa alhalin bansan komai akan masarautar nan ba...". tana sheshshe'kar kuka,
ya rungume ta yana fad'in nidai tinda Allah yasa na shawo kansa har zai warkar mun da 'Bingel ai Alhamdulillah, kuma yanzu shima Junaid ya warke!."
ya 'karasa maganar da murmushi a fuskarsa,

'Dagowa tayi tana kallonsa tace "da dukkan alamu NARASIMHA yana fushi da Kai, yakamata kaje ka sake neman yafiyarsa, nasan yanzun ma saboda son ranka ne yasa kaje ka nemeshi akan ya warkar da Ayush.."

Murmushi yayi sannan yace "dole na naje na nemi yafiyar Narasimha, saboda akwai ya'ki a gaban mu.."

A rud'e ta sake d'agowa tana kallonsa tace "ya'ki Kuma? aina?.."

ya girgiza kai sannan yace "ya'ki tsakani na da Munafurr..".
ya 'karasa maganar yana kallon cikin kwayar idanuwanta,

A matukar tsorace ta zaro ido waje Baki na kakkarwa tace "wannan mutumin mai ban tsoro? ganinsa ma yakansa mutum ya makance, ga tarukan macije a jikinsa, Ina zaka iya yakar wannan mutumin ko ince wannan Aljanin.."

Yayi murmushi sannan yace "shiyasa ma nake son naje na nemi yafiyar Narasimha domin shi kad'ai ma gayya ne, yana da 'karfin iko fiye da na Munafurr, sannan nima zai temaka mun sosai waran ya'kar Munafuurr,
Bugu da 'kari nasan Narasimha bazai ta6a barin wani da ban ya kar6i mulkin masarautar nan ba sai dai jinin masarautar, shiyasa kika ga ban damu akan batun Munafurr ba..."

Sai yanzu hankalinta ya kwanta tace "Masha Allah, amma fa duba da yanda muke rayuwa iya mu kad'ai a cikin masarautar nan babu kowa kamar wasu mayu...". ta karasa maganar tana turo baki,

'Daukar lud'a yayi mata sannan yace "ki kwantar da hankalinki Sarauniya idan rayuwa tayi dad'i zamu nemo ma'aikata....."
kafin ya rufe baki ta katse shi da cewa "Amma ina ba Aljanu baaa."

A tare suka tintsire da dariya suka haura can sama waran makwancinsu....


******

A ษ“angaren su Mommy kuwa yanda suka ga rana haka suka ga dare domin ba wanda ya rintsa a cikinsu, Junaid kuwa yace bazai koma gida ba har sai yaga Yushert, haka suka kwana a asibitin nan ba tare da sun rintsa ba,.

Har zuwa wayewar gari basu ga Ayush ba, hankalinsu ba karamin tashi yayi ba,
Bayan Malam yazo Mommy ta sanar masa halin da ake ciki, jijjiga Kai kawai yayi amma yasan yanda Ayush take, kuma yasan daga can masarautar su ne akazo d'aukar ta amma bai nuna musu cewa yasan yanda take ba saboda alkawarin da ya d'aukar wa Ayush na cewa kada ya sanar wa kowa ko ita wacece,.

Haka suka zauna suna jimamin su a cikin asibitin nan, ga kuma ma'aikatan asibitin kowa ya dawo kan aikinsa,

Junaid yana zaune a 'kasin tiles ya had'e Kai da gwiwa yayi shuru shi kad'ai yasan kalar rad'ad'in da yake ji a cikin zuciyarsa, shi abun mamaki yake bashi yana tunanin "taya lokaci guda za'a nemi yarinya a rasa? shin lokacin Mommy tana Ina? Anya ba had'a Baki akayi da Mom aka d'auke mun Yushert ba? saboda anaso a raba ni da ita...."

A zabure ya mi'ke tsaye yana fad'in "Mom you known anything, now tell me who thief my Yushert?.."

Mommy ta d'ago tana harararsa tace "kana hauka ne? kana so kace ni na sace ta koh?..."

"But Mom taya za'ace na tafi nabarki da yarinya dawowa ta kuma ace ta 6ata? bayan ko motsawa bata iya yi balle kuce tashi tayi ta tafi, gaskiya duk yanda za'ayi ku fitar mun da Yushert, idan kuma ba haka ba sai kowa yasan da maganar 6atar Yushert a cikin hospital d'in nan....."

Kafin ya kai 'karshen maganarsa Mommy ta taso a fusace ta zabga masa mari a fuskar dama, kafin ya ankara ta 'kara masa wani marin ta 6angaren hagun,
tace "yanzu ka fita kaje ka sanar wa 'yan jarida cewa Doctor Fateema tasa anyi kidnapped majinyaciyar yarinya acikin hospital d'inta, idan kuwa baka je ka sanar haka ba to tabbas baka ci sunanka Junaid ba,
Indai har zanyi kidnapped Ayushert toh Kaima wata rana zansa ayi kidnap d'inka, duk da bansan ala'kar dake tsakani na da Ayush ba amma inaji ajikina tamkar ni na haifeta...."
Kuka ne yaci ranta sosai ta dakata dayin maganar tana tsaye a gaban Junaid,

Malam ne yazo yanda take yana rarrashin ta tareda fad'in "inda kinsan illar kukan uwa akan d'anta toh wallahi da ko kad'an bazaki ta6a barin hawayenki ya zuba akan yaronki ba,
Duk rintsi duk wuya duk 6acin ran da zaki shiga akan yaronki to kada hawaye ya zuba daga cikin kwayar idonki indai na ba'kin ciki ne,
Hawayen uwa guba ne akan 'ya'yanta, wannan d'igon hawayenki shi kad'ai zai iya jefa yaronki cikin hallaka,
Ki rin'ka control kanki Hajia Fatima da kuma furucin da zai fito daga bakin ki, ba kowani magana zaki rin'ka furtawa yaronki ba da zaran ranki ya 6aci,
Kin dai san halin Junaid, sharar dashi zakina yi, ki ringa hakuri da shi, Allah ya d'ora masa wani iriyar zuciya ne, bazai iya control kansa ba...."

Had'iye kukan da take tayi sannan ta girgiza kai ta fice daga cikin room d'in...

Ajiyar zuciya Malam yaja yana sau'ke numfashi ya maida kallonsa kan Junaid yakai hannu ya dafa kafad'arsa yana rarrashinsa,
Yace "Junaid meye ribarka dan kasa mahaifiyarka kuka? shin kasan halin da take cikine yanzun?
Uwa Uwace fa, ba ko wane irin magana zakana gaya mata ba, ka kula sosai akan mahaifiyarka Dan Allah...."

Ri'ko hannunsa yayi yana fad'in "kazo muje gida, insha Allahu Ayshert zata dawo, muje ka kuma bawa Mahaifiyarka hakuri, kada ka bari ta wuni da fushinka..."
yana ri'ke da hannunsa suka fita..

Gaba d'aya jikin Junaid ya yi weak, kamar ba laka a jikinsa haka yake tafiya,
Sai yanzu ya gane cewa ya yi kuskure sosai, bai kyauta wa Mom d'inshi ba, bai ta6a ganin 6acin ranta kamar na yau ba,
ya tsani ganin hawayen Mommy amma yau gashi ta tsaya a gabansa tana kuka tana gaya masa maganganu cikin 6acin rai,
Motsa lips d'insa yayi yana maimaita kalmar data gaya, a 'kasin harshensa ya furta

"idan baka je ka sanar haka ba to tabbas baka ci sunanka Junaid ba......"
Abunda yake ta maimaita wa kenam a cikin ransa,
"Tabbas Mommy ranta ba karamin 6aci yayi ba, tinda har zata iya furta mun wannan kalmar..".
siririn hawaye ne ya zubo masa
Daiden zai shiga cikin motarsa...
Domin kowa da motarsa yazo cikin asibitin daman,
Mommy ta dad'e da tafiya da motar da tazo dashi,
Shima malam shiga motarsa yayi ya tafi, sai kuma Junaid shima tafiya ya yi da motarsa,


******

Kwance take tana fuskantar ceiling ta fara bud'e idonta a hankali tana kallon haskeยฒ da haka har idon ya washe,
tana jujjuya eyes ball d'inta hagun da dama, ganin bata san a yanda take ba yasa ta zabura ta tashi zaune tana kalleยฒ!
Idonta ta sau'kar akan NARASIMHA yana zaune a daddumarsa ido a rufe yana ta juya hannayensa, yana motsi da bakinsa kamar mai karanto addu'a amma ba addu'a yake ba wani tsafinsa daban yake aiwatar wa,
Ayush zaro manyaยฒ eyes d'inta tayi waje ganin mutum mai fuskar Biri jikinsa kuma duk gashi,
saida ta rufe idanuwanta sosai tukun ta rausa uban ihu tana 'kiran "Mommy wayyo Allah Dodo, kizo ki temake niiii, Yaya Junaidddd na mutu naaa DoDooo zai cinye ni, wallahi Dodon Biri ne...."

Narasimha bud'e ido yayi yana kallonta,
Ganin bazata iya yin shuru ba yasa ya watsa mata ruwan sihiri a fuska, kamar wanda aka datse mata harshe haka tayi miqitt tana kallonsa cike da tsoro,
Zaro mata ido yayi yana fad'in "ki kiyayi harshenki domin a gabana aka haifi ubanki dan uwarki ๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ!!!
shegiyar Yarinya ni ne DODO? to Ubanki ma yaci Uwarsa....."

Ayush gaba d'aya jikin ta ne yahau kakkarwa ta manne a jikin gini, ga yanda gumi yake ta keto mata ta gama tsorita sosai ganin yanda Old Monkey yake magana yana zaginta...

Shi kuwa saida ya gama zage ta tass sannan ya kuma cewa "wato kin warke shine zaki tashi kina Kira na da Dodo dan Ubanki, ashe baki da mutunci? tashi na kai ki gurin iyayen nakin, na gama aikin da zanyi..."

tashi yayi ya kamo hannunta yaja ta suka fice daga cikin room d'in na magani,
Jikin Ayush ne yake kafยฒ kafยฒ kafยฒ tsabar tsananin tsoro, ta gwalo ido waje,
ita tinda take bata ta6a ganin mai irin halittan nan ba, gashi masifaffen Dattijon Biri,
har saida ya shiga falon masarautar yana ri'ke da hannun Ayush,

Bara'at ce ta tafo gurin da Ayush take tana fad'in "'yata Ayush.."

Sakin hannun ta Narasimha yayi yana fad'in jeki gurin "uwarki gata nan...."

Ayush ganin Mahaifiyarta yasa ta baje baki tayo kan Bara'at tana fad'in "Umaaa.." tana nufi kanta ta rungumeta, itama Uman rungumar Ayush tayi sosai tana kukan farin cikin ganin d'iyarta tsawon watannu..

shima mi'kewa Sarki Raamud ya yi daga zaune cike da tsananin farin ciki da soyayya yake kallon 6ingel d'insa,

Saida suka gama rungumar juna suna farin ciki Bara'at ta d'ago tana cewa "Ayush da rabon zamu sake ganawa da juna, nayi kewarki sosai, ban ta6a tunanin zanyi nisa dake har haka ba indai da raina da numfashi na...." tana zubda hawaye take maganganunta,

Itama Ayush rasa abun cewa tayi sai hawayen farin ciki da yake ta zubo mata tana ambatar "Uma! Uma!! nayi kewarki Nima.."

Cikin sassanyar murya Sarki Raamud yace "6ingel!!.."
juyo wa tayi tana kallon Abbanta lokaci guda ta d'aure fuska cike da tsana take kallon mahaifinta...

Shi kuwa baiji komai a ransa ba sai ma ware mata hannayen da yayi yana fad'in "zo mana 6ingel Abbanta.."

Kawar da Kai gefe tayi tana fad'in "Uma bana son ganinsa, shine ya kashe mun Junaid d'ina, wallahi bana son sa, bana son ganinsa...." tana kuka tana furta kalmomin da suke fito wa daga bakinta marasa dad'in jii,

Bara'at ce ta katse ta tana fad'in "me kike fad'a hakane Ayush? kin manta cewar shi d'in mahaifinki ne? ki dakatar da wad'annan kalmomin nakin..."

Tace "to Uma shifa ya kashe mun Junaid d'ina..." ta fashe da kuka..

Bara'at tace "kinga ki kwantar da hankalinki Junaid d'in ki yana nan cikin 'koshin lafiya bai mutu ba.."

Da sauri Ayush ta kalli Umanta tace "da gaske Junaid bai mutu ba?.."
tace "eh bai mutu ba..."
ta kuma cewa "Amma meyasa yake wahalar mun da Junaid yake koma wa kamar DAMUSA?.."

Ajiyar zuciya Bara'at tayi sannan tace "bashi yake wahalar miki da Junaid ba..."
tace "to waye ne.?.."

Bara'at tace "kalli cann.." ta nuna da yatsar ta.
abunda Ayush ta gani shine Damusa Sujjur dake kwance a gefen kujerar sarki,
a hankali Ayush take taka 'kafarta saida taje har gaban Damusa ta dur'kusa sannan ta had'e hannayenta biyu tace "nagode Allah da ya kawoni gurinka Damusa, dan Allah ka daina cutar mun da Junaid bawan Allah, bai cutar da kowa ba kaima ka daina cutar da shi duk da nasan wancan mutumin ne yake saka ka azabtar da shi...". ta 'karasa maganar idonta akan mahaifinta Sarki Raamud tana huci cike da jin haushinsa,

zuwa ya yi gabanta shima ya dur'kusa yana kallonta yace "6ingel ki daina jin haushina Dan Allah, Junaid ya warke har abada, kin manta zoben da kika cire a cibiyarki? wannan zoben shi ya ceci rayuwar Junaid,
yanzu inason komai yazo 'karshe, ki kawo 'karshen kiyayyar da kike nuna mun, kiyi hakuri 6ingel, ki yafe mun, na tuba, na kuma shiryu bazan 'kara aikata wani makamancin laifi ba,
Auranki da Junaid kuma halattacce ne a gurina, kuje kuyi Auren ku...."

Murmushi Ayush tayi wani irin farin cikine ya ziyarci cikin zuciyar ta,
fashe wa tayi da kuka ta rungumi mahaifinta.
Shima rungumarta yayi yana rarrashinta...

Sai a wannan lokacin Narasimha yayi magana yace " toh idan kun gama kokeยฒ ku zan mayar da yarinyar yanda ta fito, domin zaman ta anan bazai yuba jininta yana can...."

Ayush tafo wa gurin Umanta tayi a hankali ta furta cewa "Uma ni wannan wayene mai siffar Biri ๐Ÿ’๐Ÿ’?.."

Bata ankara ba taji yace "Wanda ya raini ubanki ne, ni zaki zo ki tambaya ba uwarki ba, sakaliyar yarinya"

d'an turo baki tayi kamar zata yi kuka tana mutsil-mutsil da baki kamar maiyin magana..

Bara'atu ce tayi magana tace "Narasimha muna so kafin Ayush ta tafi zamu nuna mata cikin masarautar nan tinda bata ta6a zuwansa ba sai wannan lokacin, a bamu dama d'aya.."

Kallon ta yayi a fusace yace "baku da wannan damar, a yanzu zata tafi, idan kuma kina son binta zan had'a da ke ne..."

Girgiza kai Bara'at tayi tana fad'in "a'aยฒ Allah ya huci zuciyar ka, idan na bita Junaid harbeni zaiyi wallahi..."

Narasimha ko tsaya sauraronta baiyi ba ya had'e hannayensa biyu sai ga wannan haske mai 'karfin gaske ya bayyano,
Gaba d'ayan su rufe idanuwansu sukayi Banda Narasimha daya je gaba Ayush yasa hannu ya d'auke ta a saman kafad'arsa nan take suka 6ace 6att,
Bai sau'kar da ita a ko Ina ba sai a babban falon gidansu Junaid,
ya kwantar da
ita a kan kujera a yayin da ita kuma idonta a rufe bata san a halin da ake ciki ba....

Shi kuwa Narasimha 6acewa yayi da wannan hasken nasan ya koma masarauta.

A can kuwa Bara'at rungumar sarki Raamud tayi tana kuka mai sosa zuciya,
"wai tana ji tana gani a rabata da yarinyarta, kuma babu ranar sake had'uwa."

Shima Sarki Raamud baiji dad'in tafiyar 6ingel d'insa ba, sai dai ba yanda ya iya dole zata koma ta kasance da Junaid...

*SHARING AND SHARHI FISSABILILLAH๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™*

*๐Ÿค SDEENDTM DATA SERVICES๐Ÿค*
*MTN* . *Airtel*
1GB = โ‚ฆ300. 1GB = โ‚ฆ300
2GB = โ‚ฆ600. 2GB = โ‚ฆ600
3GB = โ‚ฆ900. 3GB = โ‚ฆ900
4GB = โ‚ฆ1200. 4GB = โ‚ฆ1200
5GB = โ‚ฆ1500. 5GB = โ‚ฆ1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = โ‚ฆ350. 500Mb โ‚ฆ500
2GB = โ‚ฆ700. 1.5GB โ‚ฆ1100
3GB = โ‚ฆ1050. 2GB โ‚ฆ1600
4GB = โ‚ฆ1400. 3GB โ‚ฆ2000
5GB = โ‚ฆ1750. 4GB โ‚ฆ2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ
*๐Ÿช€08066268951*

*ASMEETAH NOVELโœ๏ธโœ๏ธ*

*typing๐Ÿ“ฒ*

๐Ÿ… *MATAR* *DAMUSAA*๐Ÿ…
(the wife of a tiger)

*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* โœ๏ธ)


*WhatsApp me 09065443871*


*BOOK ONE*โฌ‡๏ธ
*91 to 92*


*FREE BOOK ZAI ฦ˜ARE NE A ฦ˜ARSHEN BOOK ONE*

*BOOK TWO PAID NE,*
*YANA TAFE DA SABON SALO, DA KUMA CAKWALKWALIN CAKWAKIYA, KADA KU BARI A BAKU LABARI DOMIN GANI DA IDO ๐Ÿ‘€ YAFI JII๐Ÿ‘‰๐Ÿ‘‚*

*MATAR DAMUSAA BOOK 2 PAY ONLY 200๐Ÿ‘Œ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡*

*DIP! DIP!! DIP!!!*

*FARASHI YA QARU DAGA 150 YA KOMA 200,*
*WADANDA SUKA BIYA 150 SU SUKA CI BONONZA*

*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*9065443871, OPAY BANK.*

*OR*

*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*2267236949, ZENITH BANK*

*SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER*
๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
*09065443871*



*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦ™alaminmu ฦดancinmu._* }}
___________________________________



๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ *{{N W A}}* ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ


ุจูุณู’ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู…ู ุงู„ู„ู‘ู‡ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญู’ู…ูŽู†ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญููŠู’ู…



https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt



๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€


Knock! Knock!! Knock!!!
Knocking ake da ฦ™arfin gaske, da ฦ™er ya iya buษ—e bakinsa murya a shaฦ™e yace "waye ne..."
"Yaya ni ce Laylah.."

a tsorace yake kallon bakin ฦ™ofa yace

Please Login or Register in order to submit comment