Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mommy kallon ta take cike da mamaki tace "to banda abunki nifa mace ce er uwarki sannan in baki manta ba ni Doctor ce, dubaki zanyi naga wani kalar magani ya dace ki sha" da kyar Ayush ta yadda ta zame rigarta daga sama sannan a hankali ta zame breziyar ta Mommy tana ganin yanda Breast d'inta d'aya ya kumbura suntum ga yayi jawurr abunka da farar mace
"Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Ayush duk wannan ciwon a buguwar 'kofa yake? Ki duba kiga?".
Banda zubda hawaye ba abunda Ayush take, ita kad'ai tasan irin rad'ad'in da take ji!
Da sauri Mommy ta tashi tana fad'in "wannan bana zama bane kina bu'katar treatment"
Ta fice daga d'akin gaba d'aya ta susuce a ranta tana tunanin Junaid ne yayi mata wannan d'anyen aiki daman ya nuna baya son zamanta a gidan.
Ayush kuwa tashi tayi ta nufi toilet tsayawa tayi a gaban mirrow tana fad'in "wannan bawan Allah ba 'karamin mungu bane, azzulumi daga tashin sa a bacci yaci abinci shine zaiyi mun wannan hukunci, Allah zai saka mun" ta 'karasa maganar tana zubda zafafan hawaye, ga Nono d'aya kuwa yayi timm kamar Wanda ya Tara ruwa.
Tana cikin sambatun ta tajiyo bud'an 'kofar d'aki.
Mommy ce ta shugo hannun ta ri'ke da boxes na pharmacy, ta 'kara ficewa ta dawo da kulolin abinci ta ajiye a saman table, zama tayi a bakin gado tana jiran fitowar Ayush, ba jumawa Ayush ta fito da d'aurin towel a kirjinta tayi using da hot water domin jikin ta ya samu 'kwari.
"Ayush en mata anyi wanka kenam, Bari na za6a miki 'karamar riga wanda zakifi jin dad'in zama da ita"
Ta bata doguwar riga sleeping dress mai short hand marar kauri ta Sanya a jikinta bayan pant babu komai a jikin ta sai wannan longer shirt, zama tayi kusa da mommy wacce ta d'auko magunguna tana 'ko'karin bud'e mata su ta bata lokaci guda ta Kora su, daga baya Mom ta d'auko Allura tana 'ko'karin yi mata, tabb d'in Ayush taga makiyarta wato Allura da gudun gaske ta nufi toilet ta danna sakata tana fad'in "wallahi baza'a mun Allura ba, Dan Allah Aunty kiyi hakuri ki ban ko wani irin magani amma banda Allura"
Mommy sake baki tayi tana kallon ikon Allah kwashewa da dariya tayi tana fad'in "Ayush da girman ki kike tsoron Allura? Nake ga Allurar zaifi miki amfani cikin gaggawa KO!"
Ba yanda mommy bata yi da Ayush ba akan ta fito amma furr Ayush ta'ki Allura sai hakura tayi tace "toh shikenam ganan Abinci kizo kici tinda kin'ki Allura"
Momy cikin fushi tabar d'akin ba wai saboda Ayush ta'ki Allura bane, tana so taje ta samu Junaid ne akan Abunda yayiwa Ayush, Sam bai kyauta mata ba,

Bayan fitar Mommy daga cikin d'akin Ayush ce ta bud'e 'kofar toilet a hankali ta lalla6o ta d'auki Alluran da mommy ta ajiye saman table tasa a cikin boxes ta rufe, sannan ta d'auki flask din abincin ta zuba a plate paten doya ne da wake, sai ta tsiyayi ruwan tea a cup tana ci tana Kora tea, daman ba 'karamin yunwa take ji ba, tinda ta shugo gidan nan take had'uwa da 'kaddarorinta bata samu tasa komai a cikita ba, Ayush fah ansamu eating kamar ba gobe, tana ci tana yarfa hannaye tsabar zogin da Nononta yake yi mata kawai dai jurewa take........

Mommy
Kamar zata dungura haka take hawa upstair nan tana zuwa ta bangaje 'kofar d'akin tana shirin yin masifa, abunda ta gani ne yasa ta tsaya cakk ta zaro ido waje bakinta na kakkarwa take fad'in "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, JUNAIDDD"
wani irin gigitaccen ihu tayi ta fad'i 'kasi sumammiya....

Ikon Allah mai Mommy ta gani haka???

Duk yanda akayi taga abunda yafi 'karfin tunaninta ne!.

*TO* *BE* *CONTINUE* *INSHA* *ALLAH*

Sorry en uwa ina ganin complain d'inku akan rashin poster littafina da wuri, Dan Allah ayi mun uzuri Ina busy ne shiyasa, ga rashin wutar NEPA!
Please my fans pardon me ๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™


*๐Ÿค SDEENDTM DATA SERVICES๐Ÿค*
*MTN* . *Airtel*
1GB = โ‚ฆ300. 1GB = โ‚ฆ350
2GB = โ‚ฆ600. 2GB = โ‚ฆ700
3GB = โ‚ฆ900. 3GB = โ‚ฆ1000
4GB = โ‚ฆ1200. 4GB = โ‚ฆ1300
5GB = โ‚ฆ1500. 5GB = โ‚ฆ1600

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = โ‚ฆ350. 500Mb โ‚ฆ250
2GB = โ‚ฆ700. 1GB โ‚ฆ500
3GB = โ‚ฆ1050. 2GB โ‚ฆ1000
4GB = โ‚ฆ1400. 3GB โ‚ฆ1500
5GB = โ‚ฆ1750. 4GB โ‚ฆ2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ
*๐Ÿช€08066268951*



*MATAR* *DAMUSA* ๐Ÿ…๐Ÿ…๐Ÿ…. Littafi kyauta domin nishad'i ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ
Qirqirarren labari from me ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

*ASMEETAH* *CE* โœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธ

*FREE* *BOOK*

๐Ÿ… *MATAR* *DAMUSA* ๐Ÿ…
(the wife of tiger)

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* โœ๏ธโœ๏ธ

The writers of...

1๏ธโƒฃ Ikram ko Kausar.
2๏ธโƒฃ Rayuwar Siyama.
3๏ธโƒฃ Baby Ogah.
4๏ธโƒฃ Yayana Zan Aura.
At now
5๏ธโƒฃ *MATAR* *DAMUSA*


*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦ™alaminmu ฦดancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ *{{N W A}}* ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ


ุจูุณู’ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู…ู ุงู„ู„ู‘ู‡ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญู’ู…ูŽู†ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญููŠู’ู…

*BOOK* *ONE*
*PAGE* โžก๏ธ19 to 20


Mommy fad'uwa tayi sumammiya ganin halin da Junaid ya shiga, tinda uwarta ta haifeta bata ta6a ganin wannan al'ajabin ba sai yau akan d'anta wanda ta haifa.

Junaid ne a manne da jikin gini an d'aga shi sama yayi cross kamar yanda akayiwa Jesus Christ, jikinsa yayi jawur sai tabo-tabon 'kunar wuta ga shatar bulala ajikinsa duk ya faffashe babu kaya a jikinsa sai jageren wando wanda baije gwiwarsa ba, kansa a sunkuye wuya ya karye kamar wani matacce ko numfashi bayayi, sai gumin da yake gangaro mishi daga cikin sumar kansa,

Abunda ya faru da shi shine ๐Ÿ‘‰. Naushin AYUSH da yayi a rashin sani shi ya jawo masa wannan bala'i, domin Naushin ba iya ita kad'ai taji ciwo ba hatta mahaifinta sarkin matsafan duniya sai daya jijjiga da wannan naushin! hakan yasa ya turo mutanensa wato Manya-manyan Aljanu guda uku don su hukunta shi,
Allah sarki bawan Allah yana cikin baccinsa yaji sau'kar bulalar kaca wacce aka cirota daga cikin wutar su na tsafi, duka d'aya fatar jikinsa ya fashe a razane ya tashi yana waiwaye amma baiga kowa ba su kuma suna tsaye a kansa, cikin fushi babban aljanin cikinsu ya yi wurgi da shi sai da kansa ya bugi jikin gini, kafin ya Ankara an sake d'agashi sama aka buga shi a 'kasan tiles, haka suka cigaba da buga shi da 'kasa tsabar wahala ko kuka ya gagara yi balle ihu, har sai dayayi jina-jina suka d'aga shi kamar tsumma ko motsi bayayi sai numfashi sama-sama, suka d'aure hannunsa d'aya da kacar wuta haka d'ayan hannun, wannan aljanin ya ri'ke hannun dama shima wannan ya ri'ke na 6angaren hagun sawayensa suka had'a biyu suka d'aure guri d'aya, suka manne shi a jikin gini.
Cikon na ukun kuma bulala ya fara zabga masa shi kuwa hatsabibin uba wato Ayush father watsa masa garwashi ya Fara yi ajiki ta cikin madubin tsafi, ana jibgarsa kuma ana watso masa garwashi, haka jikinsa ya koma ba dad'in gani jiki duk ya farfashe suna cikin gana masa wannan azabar wuyansa ya karye ba alamar motsi, shi Ogan yasan bai mutu ba doguwar suma yayi domin tsafin Damusar su bazai bari ya mutu ba sai dai yasha iya wahalarsa.
(Innalillahi wannan ai gwara mutuwarsa).

Haka *BOKA* *ZALIMU* ya bada umarni a cigaba da hukunta shi har na tsawon kwana uku ๐Ÿ‘Œ

Farin Bafulatani mai Ba'kar Zuciya, Sarkin Matsafan Duniya (Boka Zalimun) Baban AYUSHH

Shi a fad'ar sa daka ta6a Ayush gwara ka ro'ki mutuwarka,
Domin duk duniyan nan ba wanda yake so sama da d'iyarsa Ayush, ko cinyaka ce ta cije ta saiya zaro hannunsa ta cikin madubi ya mur'kushe ta ๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ
(Anya kuwa d'aukar fansar Junaid zaiyu akan d'iyar Bara'atu kuwa ๐Ÿค”).

___________________________
Ihun da Mommy tayi ne ya jawo hankulan kowa na gidan,
Ayush tana cikin cusa abinci sai da ta razana daga zaune ta mi'ke tsaye, sarkin tsoro har jikinta ya Fara 6ari tayi cikin toilet da gudu ta danna sakata!

Security gidan kuwa suma da gudun gaske suka shiga cikin d'akin direct d'akin Junaid suka nufa saboda sun san duk wani problem daga d'akin Junaid yake fitowa,
Suna shiga cikin d'akin suka tarar da abun al'ajabi, zaro idanuwa sukayi waje sun firgita da ganin Junaid a haka ga kuma mommy a shanye a 'kasi sumammiya, cikin zafin nama suka nufi gurin da Junaid yake Gadan-gadan sun d'ago hannu zasu jawo Junaid nan sukaji an had'a kayuwansu biyu aka gwara kamar daga sama kuma basuga kowa ba, ba 'karamin buguwa akayi musu ba kwakkwalwarsu ne ya fara juyawa kafin nan kowannen su suka fad'i sumammu, sauran two bodyguard suma ganin hakan yasa suka nufi gurin babu tsoro a fuskarsu zasu sa hannu su finciki Junaid daga jikin gini sukaji an sha'ko wuyansu duk su biyun an d'aga su sama kakaki suka farayi suna ri'ke wuyansu, saiga mai gadi shima ya shugo da gudu cikin d'akin abunda ya ganine yasa shi tsayawa cakk ganin gardawa a sama suna lilo da 'kafafuwansu kuma bai ga abunda ya d'agasu sama ba, nan take yasau fitsari a wando jikinsa ne ya hau 6ari,
Su kuwa sai da numfashin su ya tsaya cak sannan aka wurgar dasu kan mai gadi da yayi sumar tsaye, sai yaraff duk su biyu akan mai gadi shima saida yayi asalin suma jin Manya-manyan gardawa a samansa.

Bayan 1hour Ayush dai tana cikin toilet jin ihun da akayi yasa ta 6oye a gurin, tana tsugune har ta gaji jin babu komai yasa ta bud'e 'kofar toilet tana Le'ke-le'ke cikin sand'a take tafiya har ta sau'ko falo babu kowa,
A hankali take 'kiran sunan "Aunty, Aunty, kina Ina ne" taji shuru ba'a amsa mataba, ta nufi kitchen tana bud'ewa taga wayam ba kowa
Anan fa ta fara rawar jiki tsoro ne ya bayyana akan fuskarta, "innalillahi wa inna'ilaihi raju'u, Allah yasa dai ba 6arayi bane suka shugo gidan, naji ihu kuma yanzu babu kowa"
Tana magana cikin kuka hawaye ne sharaf-sharaf suka fara gangaro mata a saman kunci, ta lalle'ka ko Ina amma bataga Mommy ba, ta duba agogon saman bango 12:30 ne.
Tayi hanyar waje ko zataga security hankalinta zaifi kwanciya,
"May be an kirata ne a asibiti" a cikin ranta take wannan maganar!
Abun mamaki ko dataje waje bata ga kowa ba hatta mai gadin sai haske Dara-dara ta ko Ina,
Wani irin yawu ta had'iya ga gumi kuwa daya fara tsirto mata, kakkarwa ta somayi tana tunanin kar itama a sace ta
Da gudun gaske ta koma cikin d'aki tana maida numfashi,
Ta zauna a saman kujera 1seater dafe kanta tayi ta fara rera kuka
Ita kanta ta rasa shin kukan mai takeyi
Shin na rashin ganin mutanen gidan ne ko kuma kukan tsoro ne, tana cikin wannan halin ta tuno da Junaid! Da sauri ta d'ago kanta idonta sun rine sunyi jaa "Ina yaron gidan, ko shima an sace shi" tana magana tana kallon upstairs d'in d'akin Junaid
Cikin rawar jiki ta mi'ke da sauri tayi hanyar d'akin Junaid tana taka matakala da sauri-sauri kamar zata kife,
Tana zuwa daf da d'akin tasa hannu zata bud'e naushin da Junaid yayi mata ne ya fad'o mata a rai, tsayawa tayi cak cike da fargaba ta fara tunanin "ya za'ayi na shiga d'akin wannan azzalumin d'azu ya naushe ni yanzu kuma ban san wani muguntar zai 'kara mun b, ta juya zata bar gurin ta koma falo sai wani tunanin ya sake fad'o mata shin idan kuma shima ansace shi fa? Inma ba'a sace shi ba ai zai fita ya nemo mutanen gidan!

Knocking ta fara yi taji shuru ko motsi bataji ba ta sake buga 'kofar still ba motsi
Almost 30minute tayi a tsaye tana sa'ke sa'ke a raanta
Daga baya ta yanke shawarar shiga kawai, cikin rashin sa'a tana shiga tayi tuntu6e da mutum a gabanta,
Juyowa tayi ta kalli gurin ganin Mommy a kwance yasa taji fad'uwar gaba,
"Innalillahi was inna'ilaihi raju'un Aunty meya sameki" jijjigata ta somayi taga babu alamar motsi
Juyawar da zatayi taga mutane uku aguri d'aya 2 bodyguard da mai gadi ja da baya tayi cikin firgici da tsoro tana waiwaya gabanta taga still 2 bodyguard kwance ba motsi
Daman bodyguard 4 ne a gidan sai mai gadi

Bakinta ne ya soma kakkarwa ko magana ta kasayi
Ga wani irin guminda yake yarfo mata
Cikin fargaba da tsoro take bin d'akin da kallo
Karaff idonta ya sau'ka akan Junaid dake manne saman bango rai a hannun Allah, 'Kara ta sau tare da toshe bakinta kuka ne yaci ranta yau taga abunda tinda aka haifeta bata ta6a gani ba.

Da gudun gaske ta nufi gurin da Junaid yake, jinin da yake d'idd'iga daga jikinsa duk ya 6ata tiles d'in d'akin,
'Dagowa da kanta tayi ta 'kura wa fuskarsa ido lokaci guda kuwa ta zaro Manya-manyan idanuwanta waje bakinta ne yake motsi kamar maiyin magana, jikinta kuwa rawar sanyi ta soma, cikin firgici ta jaa baya da sauri sai da ta fad'i 'kasi still idonta akan Junaid
Da kyarr ta iya bud'e bakinta cikin kuka ta fara fad'in
"Wayyo Allah nah Umma nah, Kaine ka kashe mun Ummana bazan yafe maka ba, ka sanya ni cikin maraici! Saika tozarta a rayuwa, sai kayi mutuwar wulakanci kamar yanda ka kashe mun mahaifiyata"
Gaba d'aya Ayush idonta ya rufe bata ganin halin da Junaid yake ciki, kamar zautacciya haka take maganganu cikin fitar hayyaci,
Saida ta gama surutanta ta mi'ke da gudu ta fice daga cikin d'akin...

Shi kuwa Junaid duk abubuwan da yake faruwa bai saniba , baya cikin hayyacinsa,
A halin yanzu taimako yake bu'kata
Kuma Ayush ce kawai zata iya wannan taimakon, in har ba itaba ba Wanda zai iya ceton Junaid daga hannun azzaluman Aljanun nan da kuma mahaifinta.

Barin Ayush cikin d'akin falo ta nufa ta kwanta 'kasan carpet tana rera kukanta mai cin rai, a halin yanzu ba mutumin da Ayush ta tsana kamar mutumin da ya kashe mata mahaifiya,
Kuma saita d'au fansar mahaifiyarta akan sa,
Wato JUNAID.........



TO BE CONTINUE INSHA ALLAH.



*ASMEETAH* *CE* โœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธ

*FREE* *BOOK*

๐Ÿ… *MATAR* *DAMUSA* ๐Ÿ…
(the wife of tiger)

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* โœ๏ธโœ๏ธ


*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦ™alaminmu ฦดancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ *{{N W A}}* ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ


ุจูุณู’ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู…ู ุงู„ู„ู‘ู‡ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญู’ู…ูŽู†ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญููŠู’ู…

*BOOK* *ONE*
*PAGE* โžก๏ธ21 to 22


Ayush! Ayush!! Ayush!!! Cikin sassanyar murya ake kiran sunan nan, ita kuwa Ayush tana kwance akan carpet kuka yaci ranta taji ana kiran sunanta kamar daga sama, dakatar da kukan tayi tana sauraron kiran da ake mata, sautin zazza'kar murya ne yake dukan kunnenta a hankali take d'ago da kanta wani irin hajijiya ne yake d'iban ta a haka ta tashi zaune!
Da dara-daran idanuwanta wad'anda sukayi jawur ta d'agosu ta kalli yanda sautin sunanta yake fitowa, cikin firgici taja da baya ta zaro manya-manyan idanuwanta waje tsoro ne ya kuma bayyana akan fuskarta, baki na kakkarwa ta ambaci "Umaa" abunda ya fito daga bakinta kenam tana kallon gurin da wata zankad'edd'iyar mata take tsaye, tana sanye da fararen kaya daga sama har 'kasa ta rufe doguwar suman kanta da farin mayafi, da murmushi a kan fuskarta...
Ayush ce ta sake motsa baki tana fad'in "Umaanah" tana kuka kuma tana had'awa da dariya tayi farin cikin ganin mahaifiyar ta a wannan Daren misalin karfe 2:00
Itama Uman da murmushi a fuskarta cikin sanyayyar murya tace "Yarinyata nazo gareki ne domin na tunasar da ke abunda kika manta a baya, ki kasance mai taimakon al'umma idan kika fuskanci suna cikin wani irin hali, kada ki dubi girman laifin da mutum yayi miki idan ya bu'kaci taimakon ki kawai ki taimake shi kema wata rana idan kika shiga wani hali Allah zai taimake ki, kada ki tsani bawa! kada ki cutar da bawa!! kada ki bari ata sanadiyarki a cutar da bawan Allah, Ayush d'iyata! 'Dan uwanki yana bu'katar taimakon ki kije ki taimake shi kada ki damu Allah yana tare da mai hakuri, kije ki, ki je ki taimake shi........!
Tana kaiwa karshen maganar ta 6ace 6attt.
A firgice Ayush ta tashi zaune tana fad'in "Umaa! Umaana!! Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, mafarki Ayush tayi kwanciyar da tayi tana kuka ashe bacci 6arawo yayi awun gaba da ita, zuwan da mahaifiyar ta tayi acikin mafarki ta zo mata.
Ta waiwaya ko Ina bata ga kowa ba ga hawayen da ya bushe mata akan fuskar "tabbas mafarki nayi, Uma tazo mun" a lokacin ta fara tariyo maganganun mahaifiyar tatan lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka, Junaid ne ya fad'o mata a rai "Uma mutumin da ya rabaki da rayuwarki shi kike so na taimaka?" Kuka ne ya kwato mata sai wani tunani yazo mata a cikin zuciyarta take fad'in "Mahaifiyar shi ta taimake ni, ba don ita ba bansan Ina zan nufa ba, shin itama tana raye ne ko ta mutu? Tabbas suna bu'katar taimako a wannan halin" ta mi'ke tsaye cikin sauri lokaci guda kuma ta tsaya cakk
Alamar ta tsaya tunanin wani abu "amma meyasa naga shi wannan mutumin a manne da jikin gini ba tare da an d'aure shi ba, kuma jikinsa a faffashe kamar ma ya mutu"... 'Kirjinta ne yayi wani irin bugawa ta zabura da gudu ta nufi hanyar d'akin takawa d'aya biyu taji kamar an ri'ke 'kafarta ta doku a 'kasi danma carpet ne mai gashi da tunin taji ciwo,
Tana shirin d'agowa kunnuwanta suka jiyo mata kukan mujiya ๐Ÿฆ‰๐Ÿฆ‰ mai firgitarwa a tsorace ta kalli saman cilling yanda ta jiyo kukan kenam, wutar nepa gidan ne ya d'age sai duhun daya biyo baya ko hannunta bata iya gani wani irin tsoro ne yabi jikinta, kamar daga sama tajiyo wata 'katuwar murya ana cewa "AYUSHHHH KADA KI KUSKURA KI TAKA 'DAKIN NAN, WANDA YA KASHE MIKI MAHAIFIYA ZAKI TAIMAKA? TO LALLAI KEMA ZAI KASHE KI KAMAR YANDA YA KASHE MIKI MAHAIFIYA, KIYI TUNANI SHI BA MASOYINKI BANE MAKIYINKI NE, YANA NEMAN AHALINKU NE DOMIN YA GAMA DA RAYUWAR KU GABA DAYA HAHAHAHA, HAHAHA, HAHAHAHA haka ta ringa jiyowa dariya marar dad'in ji,
Jikinta ne ya hau 6ari murya na kakkarwa tace "waye Kai?"
"NIIII MAI BAKI KARIYA NE, still ya 'kara tintsirewa da razananniyar dariyar shi mai ban tsoro....
Lokaci guda kuwa haske ya bayyana ta daina jin kukan mujiyan.
"Innalillahi wa inna'ilaihi raju'unnn wannan wani irin bala'i ne a cikin gidan nan, Aljanu da mutane duk suna rayuwa a gidan nan" zuciyarta ne ta soma magana kamar haka "Ayush kar ki manta wannan Addu'ar

Please Login or Register in order to submit comment