Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

eyes ɗinsa akan fuskar Junaid, da ƙarfin gaske Junaid yake jijjiga Doctor amma ko motsi babu, wulli yayi dashi yana faɗin "meyasa kuke gudu na? shin na zamo muku Dodo ne?..."
Ganin kowa yana ta guduwa masa wasu kuma har da suma,
Domin mutuwar Junaid har ya baza ko ina, kowa sai kaji anata cewa "Allah yayi wa ɗan gidan Doctor Fateemah Rasuwa ko kuma ace captain Junaid ya rasu, wasu suna faɗin ya huta da ciwon nan nashin... haka dai kowa yake ta mita,
yanzu kuwa kwatsam saiga Oga Junaid ya bayyano, hakan yasa tin shigarsa asibiti wasu suka rinƙa fece wa,
ma'aikatan asibity haka suka rinƙa guduwa, Nurses kam duk babu mai ƙarfin halin guduwa sai faɗuwar da sukaita yi suna suma,

Abunda ya ƙara firgita su ma shine farar jallabiyan da ya saka har ƙasi, ga kuma kamar wanda aka canza masa halitta, ya ƙara fari sosai sumar kansa ya sauƙo har kafaɗunsa, sajensa ya haɗe da gemun yayi tsayi,
ga ya ƙara tsayi, ƙirar ƙarfin jikinsa ya ƙara fitowa..
haka ya rinƙa bi yana bubbuɗe ɗakunan majinyata yana ƙwalla ƙiran "Yushert! Yushert!! Yushert!!!.." ga ya rasa wanda zai tambaya duk wanda yaci karo dashi sai yace zai gudu ko kuma ya faɗi sumamme,
abun ba ƙaramin ƙona wa Oga Junaid rai yayi ba, shi a tunaninsa sun mayar dashi mahaukaci ne yasa suke guduwa masa, amma yaci alwashin sai ya ɗauki ƙwaƙwaran mataki akan mutanen asibitin nan...
cikin sa'a kuwa yana buɗe wani ɗakin sai yaga wasu likitoci su uku suna duba Ayush,
da gudu Junaid ya shugo ya yo kan Ayush yana faɗin "Yushert, meya faru dake,." murya kamar zaiyi kuka yake magana tareda shafa suman kan Ayush wacce take kwance har yanzu bata farfaɗo ba ansa mata oxygen,
tana sanye da riga blue na waɗanda aka musu operation..

acikin ma'aikatan nan kuwa mutum ɗaya ne ya samu ya gudu, ɗaya kuma ya faɗi sumamme, ɗayan kuma christal ne ya ƙafe guri ɗaya jikinsa sai kakkarwa yake yana faɗin "Jesus Christ amen, any devil can destroying my life God fatafata him in the name of Jesus, Olugos fire, Olugos fire, Olugos 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 Fireee........"

Oga Junaid ganin wannan inyamurin Doctor ya dameshi da surutai ya daka masa wani irin gigitaccen tsawa yana faɗin "you will shut up 😳😳.."
jin wannan tsawar yasa Doctor yasau fitsari a wado daga ƙarshe shima ya faɗi sumamme..

Mommy kuwa ɗakin Junaid ta haura, sai yanzu hankalin ta ya dawo jikinta, ta bari ne akan Junaid dogon suma yayi har ana tunanin ya mutu,
kuma sai Allah ya kawo masa waraka lokaci guda!
yanzu damuwar ta shine jinyar Ayush, abun ya tsaya mata arai tana tunanin meya kawo lalura a cibiyar Ayush, sannan meye dalilin da yasa Ayush taji wa kanta rauni akan cibiyarta har ya shafi cikin cikin cibiyar? abun ya tsaya mata a rai..

saida ta gama gyara ɗakin Oga Junaid tsaf kafin ta fice ta nufi ɗakin Ayush, itama ta gyara mata ɗakin, ta shige cikin toilet ga yanda jini duk ya wanke toilet hawaye mai zafi ne ya soma zubo mata, haka ta wanke toilet ɗin nan tass, tazo fita kenam idonta ya sauƙa akan zobe a cikin sink, hannu tasa ta ɗauka tana jujjuya shi, acikin ranta kuwa cewa take "wannan wani irin zobe ne mai ƙalƙali haka kamar na masarauta, kuma zobe ne mai tsadar bala'i, aina Ayush ta samu wannan zoben??.."
wani zuciyar kuma ya sanar mata cewa "wata ƙil gadon iyayenta ne suka mutu suka bar mata, zan adana mata wannan zoben kuwa domin yana da matuƙar muhimmanci.."

*****
ta ɓangaren Doctor Hasheem kuwa tin dawowarsa gida daya zauna yake ta cewa "a bani ruwa nasha" duk bayan mintuna sai ya buƙaci ruwa, Lailah ce tace "haba Bros nifa nagaji da ɗawainiyan bada ruwan nan fa" yace "maƙogaro nane yake ta bushewa, na tsorita sosai wai ace mutumin da ya mutu lokaci guda aga ya motsa?."

Tace "ai ni nagode wa Allah daya tayar mun da kafaɗun Oga Junaid ɗina,.." gashi kuwa yanda idanuwanta suka yi jaawur tsabar kukan da tasha sanar mata mutuwar Junaid da akayi,
Cikin Doctor Hasheem ne ya dinga ƙurari yana juyawa, da sauri ya tashi yana faɗin "toilet toilet" yana riƙe da ciki ya shige cikin toilet ɗin da yake room ɗinsa,
Laila sake baki tayi tace "Bros abun nakan har ya kai ga gudawa?..."

*****
A can Headquarter Kuma Ogan sojojin ne ya tara su yana balbale su da faɗa, ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba ganin yanda suka taho da gudu suna haki wai don saboda wanda ya mutu ya tashi,
General Muhammad haka ya rinƙa faɗin "kun bawa maza kunya, hakan ma kuna sojoji aga kuna gudu a titi saboda kunga abun tsoro, tirr wannan kakin nakun bashi da wani amfani a waranku, Soldiers kun ban kunya..." haka ya ɗebi wasu Soldiers suka shige motarsu da ɓacin rai suka nufi gidan su Captain Junaid..

Mommy tana kitchen ta kammala girkinta mai shegen ƙamshi, ferfesun kifi ta haɗa mai ruwa-ruwa zata kaima Junaid can Hospital, Ayush kuma tasan bata farfaɗo ba, tayi tuwon shinkafa da miyar Ogusi ga kuma naman chicken a ciki baje², tazo ta yanyanka fruits a cool flask ta zuba ƙanƙara akai ta rufe, ga kuma hot flask wannan milk ne a ciki domin Junaid yana son madara sosai,
tana cikin haɗe-haɗe kayan abinci tajiyo jiniyar motar sojoji sun tsaya a ƙofar gidan..

General ne ya fito daga cikin mota yana sanye da kakin soja na musamman ba kalar tasu ba, idon sa akan motocin su yanda suka guda suka bari, ga bindigoginsu a cikin motocin, girgiza kai kawai yayi a ransa yana faɗin "Allah ya taimakeku bindiga ɗaya ya ɓata, yanzu inda a sambisa ne ya za'a ƙare kenam.."
Haka yabi ko ina da kallo ga butoci a yashe yanda mutane har sun fara alwalar jana'iza, ga kuma get a buɗe ɗaya daga cikin sojojin ne yake bubbuga ɗakin maigadi a tsorace Baba maigadi ya buɗe hannunsa na kakkarwa, shi tinda yaga anata guduwa shima ya shige ɗakinsa yasa sakata,
ce masa sukayi "ya fito bakin aikinsa.."
ya amsa da "to to too naji zan bito."

miƙar hayar da zai sadasu da cikin gidan sukayi,
daman sojojin su huɗu suka zo,
General da kuma Marshal sai canal da S...

Bayan sun iso compound tsayawa suka yi suna knocking ƙofar falo, Mommy ce ta buɗe musu da murmushi a saman fuskarta tana faɗin "your welcome Officers.."
amsa mata suka yi sannan suka shige cikin falon, kowa samun guri yayi suka zauna saman sofa saida suka gama gaisawa sannan suka tambayi Oga Junaid,
Mommy ta sanar musu cewa yaje hospital gano wa sister sa bata da lafiya,
General ne yace "masha Allah ya warke kenam, ai mun tsorita jin labarin mutuwarsa daga baya kuma akace ya tashi..."

Mommy ta sanar musu duk abunda ya faru, da doguwar suman da yayi, tashinsa kuma ya kawo masa waraka gaba ɗaya,."
suka ce "ikon Allah kenam, ku duba kuga baya iya tashi balle tafiya gashi kuwa lokaci guda Allah ya kawo masa waraka, Allah ya ƙara bashi lafiya.." Mommy ta amsa da "Amiin"
tashi tayi tana faɗin "kunsha hanya bari na kawo muku abun taɓawa.."
ta nufi kitchen ta jido kayan abinci ta kawo muku, kowa saida ta zuba masa a plate tuwon shinkafa da miyar Ogusi ta kuma zuba musu ferfesun kifi, ga kayan fruit yanda ta zuba a faranci...

Sai da suka ci sukayi nak sannan suka tashi suna faɗin "masha Allah mu zamu wuce, insha Allah zamu dawo da zaran Junaid ya dawo.."
Da haka suka rabu cikin Aminci,
Mommy wuce wa ɗakinta tayi ta shiga toilet domin yin wanka, shap-shap tayi wanka ta fito ta shirya tab sannan ta ɗauki key ɗin motarta ta fice
kayan abinci ta ɗauka taje tasa a seat back gaba ɗaya, itama ta shige cikin motar takarya kwana a hankali sannan ta miƙi hanyar da zai sadata da gate, kafin ta iso ma maigadi ya buɗe mata gate tayi ficewar ta,

******
Junaid zaune yake akan kujera ya kifar da kansa a bakin gado hannunsa yana riƙe dana Ayush,
Ayush sai da ta shanye ledar jini har uku hakan ma tana neman ƙari ga kuma ledar ruwa biyar,
Bayan Mommy ta shugo asibiti baki ta sake tana kallon ko ina, asibitin yayi wayam babu kowa, waɗanda suka suma kuma da zaran sun farfaɗo hanyar guduwa suke nema, amma duk da hakan ta tarar da wasu a sume a ƙasi, tace "nashiga uku meke faruwa ne a wannan asibitin, daman saida nace wa Junaid karya zo har saina musu bayani tukun gashi yanzu sun tsotstsorita, wayyo Allah.." da sauri ta nufi ɗakin da aka kwantar da Ayush tana buɗewa kuwa ta samu Junaid gashi yana zaune ya kifar da kansa, idonta ta kai kan 2 Doctors da suke kwance a ƙasi, ƙarisa shugowa ciki tayi ta ajiye kayan abincin, ta ɗauki ruwan ƙanƙara ta fara binsu ɗaya bayan ɗaya tana feffesa musu suna tashi kuwa kowa zai nemi hanyar guduwa, duk waɗanda suka suman nan sai da ta farfaɗo dasu,
asibitin sai ya zamo babu ma'aikata ko ɗaya duk sun gudu, sai majinyatan asibitin da bazasu iya tashi ba ko kuma waɗanda ba'a cikin hayyacinsu suke ba..

Mommy koma wa room ɗin da Ayush take tayi, itama kujera ta jawo ta zauna tana faɗin "kaga abunda nake gaya maka ko? gashi duk ka korar mun da ma'aikatan asibiti sun barmun majinyata, saida nace maka kada kazo..." kafin ta ƙarisa maganar Junaid ya daka mata dirarren tsawa tareda faɗin "Mom ni mahaukaci ne? ki gaya mun meye dalilin da yasa ake gudu na, shin akwai wani abun tsoro ne a jikina? ki gaya mun....."
ganin yanda yake mata magana da tsawa yasa Mommy tasa hannu ta zabga masa mari a saman face ɗinsa tana kuka tace "dole kowa ya nemi tsira daga gareka My son, mutuwa fa kayi, kuma kowa yasan ka mutu, ganin haka yasa Ayushert itama tayi ƙoƙarin kashe kanta, gata nan a ƙwance, har anzo za'a maka wanka ka tashi, ya za'ayi kowa bazai yi gudunka ba, shin kasan irin tsananin jinyar da kayi ne? ko motsawa baka iya yi, gashi lokaci guda ka tashi bayan doguwar sumar da kayi, toh yanzu kaji dalilin da yasa mutane suke guduwa maka..."

Hawaye ne yake zuba a ido Junaid yana karkaɗa kai ya maida kallonsa kan Ayush, yakai hannunsa yana shafar fuskarta...

ita kuwa Mommy ƙarewa Junaid kallo take gaba ɗaya ya canza mata, kamannin mahaifinsa sun fito a fuskarsa, har tsayin gashin kafin ya aske, da kuma ƙirar jiki na jaruman sarakuna,
hawaye ne ya fara gangaro wa mommy, tana kallon Junaid da suffar mijinta,

Bata taɓa ganin fuskar mahaifin Ayush bane amma fuskar Junaid yafi kama dana Sarki Raamud,
(kodan saboda tsayin gashin Junaid ne yasa nake ganin haka oho😅)

duk da mahaifin Junaid da kuma mahaifin Ayush twins ne masu kamanni iri ɗaya shiyasa bazaka banbanta kamannin wa yaran suke yowa ba,

inka lura Ayush da Junaid suna ɗibar kama, Mommy ta daɗe da fahimtar haka sai dai bata kawo komai a ranta ba....


*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*

typing📲

🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)

*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)


*WhatsApp me 09065443871*

*Laifin Daɗi qarewa*

*FREE BOOK ZAI ƘARE NE A ƘARSHEN BOOK ONE*

*BOOK TWO DAZAN SHIGA SOON PAID NE,*
*YANA TAFE DA SABON SALO, DA KUMA CAKWALKWALIN CAKWAKIYA, KADA KU BARI A BAKU LABARI DOMIN GANI DA IDO 👀 YAFI JII👉👂*

*MATAR DAMUSAA BOOK 2 PAY ONLY 150👌👇👇👇*

*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*9065443871, OPAY BANK.*

*OR*

*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*2267236949, ZENITH BANK*

*SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER*
👇👇👇
*09065443871*

https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________



💫💫 *{{N W A}}* 💫💫


بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK ONE*
🅿️ ------->87 & 88 <-------

******* Daƙer Mommy ta lallami Junaid yake cin abinci, ita da kanta take feeding ɗinsa ko loma biyar baiyi ba yace "na ƙoshi da tuwon ni milk nake so" Mommy tace "bazaka taɓa ferfesun kifin bane?" kawar da kai gefe yayi sannan yace "idan naci kifi ba halin shan milk, ni kuma idan ban sha milk ba bazan ji daɗin baki na ba.."
Ajiyar zuciya Mom tayi sannan tace "toh ga kayan fruits yanda na haɗo maka"
tasan indai yasha milk bazai buƙaci wani abu ba,
taɓe fuska yayi ya ɗan turo ƙaramin bakinsa yana kallon haɗin fruits, yana yatsine fuska yace "indai ba milk ba bana son komai." Mommy tana jinjinawa wannan miskilanci na Junaid ba yanda ta iya dashi haka ta buɗe murfin flask tana tsiyaya masa milk mai kaurin gaske a glass cup tace "to gashi nidai in har zaka ƙoshi ai ba wani abun tada hankali.."
Hannu ya miƙa ya karɓi cup ɗin milk, idonsa kuwa yana kan Ayush wanda har yanzu bata farfaɗo ba..

Kai ya kifa yana kurɓan madaran, a hankali yake motsa sweet lips ɗinsa, da haka har ya shanye,
bayan wasu mintuna suka ji anata ƙiraye-ƙirayen sallar mangarib, Mommy ta kalli Junaid sannan tace "kaje kayi sallah daga nan kuma saika wuce gida kaima ka kwanta ka huta ko..?"
girgiza kai yayi sannan yace "bazan yi nisa da Yushert ba a halin nan da take ciki, zan zauna tare da ita har Allah yasa ta farfaɗo, kula da ita ya rataya mun a wuya..." ya ƙarisa maganar tareda miƙewa tsaye ya kuma cewa "zanje nayi sallah amma kuma zan dawo.."
Jijjiga masa kai kawai Mommy tayi ta kasa cewa komai,
har saida Junaid ya fice daga room ɗin kafin Mommy ta kawar da kanta daga kallonsa da take, ita har yanzu ta gagara gasgata wa shin Junaid ɗinta ne ko kuma sauya shi akayi aka maido mata da mai siffar mijinta, haka ta wuni tana wannan tunanin, dogon numfashi taja tareda sa hannu tana buga goshin ta alamar ciwo yake mata, daƙer ta iya motsawa ta tashi tana jan ƙafa da haka ta shige toilet ta ɗauro alwala, sannan tasa hannu ta murɗe mariƙar ƙofar toilet ta fito tana jero addu'o'i,
ƙarisa shugo wa cikin ɗakin tayi tana hamma tasa hannu tana kare bakinta ido a lumshe, tsananin bacci ne yake damun ta, ga yunwar da take ji! shimfiɗa sallaya tayi ta zura hijab ɗinta sannan ta tsaida sallah, har tayi nisa cikin sallar ta taga wani irin haske ya bayyano, haske mai kashe ido, tsabar tsananin ƙarfin hasken nan Mommy tana sallah ta ƙanƙame idonta sosai kuma Allah bai nufe ta da katse sallar ba haka ta cigaba da yinsa ido a rufe,
irin hasken da ya taɓa fito wa Ayush lokacin da ta ajiye littafin tarihi a ƙarƙashin gado shine ya ƙara fito wa a yanzu ma,
wani mutum ne ya bayyana a cikin hasken nan, shi ba mutum ba kuma shi ba biri ba, gashi nan tsayayyen mutum ne jikinsa duk gashi, daga kayinsa zuwa fuska har wuya irin na biri ne sak sai tarin gashi sannan yana da jelaa!!!
Wannan shi ake ƙira da *NARASIMHA* mai bada kariya a masarauta, tsohon biri kuma ƙirƙirarren tsafin Sarkin Zaid wato Mahaifinsu Sarki Raamud, baya cutar wa aikinsa shine temako da zaran an nemi temakonsa, har iyau a masarauta yake zaune yana rayuwa ne a cikin madubin tsafi,
NARASIMHA Amanar Sarki Zaid ne, yana kallon duk tsiyar da Sarki Raamud yake aikatawa har Allah ya kawo ƙarshen ta'addanci,
A yanzun ma an turo shi ne don yazo ya temaki Ayush, bazata iya tashi ba har saida temakonsa,

hannu yasa ya yi wa Ayush ɗaukan luɗa sannan ya ɓace da ita, yana tafiya kuwa hasken ya washe daiden lokacin da Mommy ta idaar da sallah da sauri ta miƙe tsaye a ruɗe tana ware manya-manyan eyes ɗinta, ta waiwayo bayanta a tsorace ganin gadon da Ayush take ƙwance wayam babu kowa a kai taja da baya

Please Login or Register in order to submit comment