Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

meya sameki"

Ita kuwa cewa take "mutuwa zanyi na huta, rayuwata batada wani amfani,
Um Um Um Umaaaa naah wayyo nagaji da ganin takaicin nan, bazan iya cika miki alkawarinki ba, I can't, I can't wallahi.....

Umanta ne ta fara yimata gizo a cikin fararen kaya da hawaye kwance saman fuskarta,

Hannu Ayush take mi'ka mata alamar tazo ta tafi da ita.......
Muryarta ne ya dishe ta gagara yin kukan ma!
Sai idonta daya fara kakkafewa, yawu ne yake gangarowa ta gefen bakinta
Daga nan aka nemi hankalin Ayush aka rasa ta sumaa!!

Shima Junaid ne yayo kanta yana bubbugan gefen fuskarta amma ba numfashi ya tsaya cakk sai ido a bud'e ya 'kafe....

Lokaci guda Junaid ya rikice yana fad'in "mo mo momm moomm Doctor zata mutu fah," ya nufi waje da gudu yana kiran " Doc Doctor! Doctor!! Doctor!!! Gaba daya ya fita hayyacinsa.....


*****

Abunda ya faru da Junaid kuwa a daren jiya
Shi kad'ai ya kwana a gida sai kuma mai gadi dake d'akinsa wanda yake bakin gate...

1:00am yana cikin baccinsa yaji wani irin gurnani a cikin baccin a hankali yake bud'e idon a tunaninsa mafarki yake kamar Wanda ya Saba, ashe abun ba haka yake ba a zahiri aka fito masa wannan karan!
Idonsa ya bud'e sosai still bai daina jin gurnanin ba
Yakai hannu ya kunna ligh d'in d'akin
Haske ne ya bayyana idonsa ne ya sau'ka akan wani ba'kin Damusa 'katoto dashi ga idonsa jawurrr daga gani kasan na tsafine,
Junaid ja da baya yayi ya manne a jikin karfen gadon,
Tsorone ya bayyana akan fuskarsa gaba daya ya mance da Addu'o'in da akace yanayi, jikinsa 6ari ya soma yi!
Shi kuwa Damusan kansa yake yowa da wasu fikokinsa a waje
Wani irin sufa yakai wa Junaid
Shima Junaid yun'kurawa yayi da 'karfin gaske ya cafki wuyan Damusa.....
Ido cikin ido suke kallon juna idon Junaid ne ya Fara komawa na Damusa sai dai shi nashi Blue eyes ne,
Wani irin yakushi Damusan nan yakaiwa Junaid a wuya, jin zafin yakushin ne yasa Junaid yayi wulli da Damusar jikin mirrow saida madubin ya dagargaje,
Cikin karfin hali Junaid yayo kan Damusan zai kai masa naushi rashin sa'a yasa Damusar zamewa Junaid kuwa ya doku a 'kasi, hakan ya bawa Damusar daman hawowa kan Junaid ta baya yakai bakinsa saitin wuyansa zai cije shi,,,
Wani irin juyi Junaid yayi ya cakawa Damusan glass d'in jikin mirror a wuya....
Wani irin Ihu Damusar yayi ya 6ace 6aatt!
Jinin Damusan daya zube a tiles shima kamar Wanda aka goge waran ba alamun jini...
Damusar ya tsani ganin jini a jikinsa domin yana had'e da jinin Junaid ne hakan zai bada matsala sosai daga 6angaren su,
Hakan yasa Damusar yayi saurin 6acewa....

Junaid kuwa kansa ne daya bugu a 'kasi ne ya fara ciwo sosai ga jinin da Damusar ya yakushe shi a wuya sai zuba yake ga rad'ad'i ga ciwon jiki, gaba d'aya jikinsa ne yahau yin ciwo
Abu kamar a mafarki!!

Sai a yanzu Junaid yake furta
"Innalillahi wa inna'ilahi raju'un, wannan wani irin masifa ce.."

Dakyar ya tashi ya shige toilet yayi wanka ya fito ya shirya ya nufi falo d'akin medicine ya nufa yaje yayi treat d'in ciwon dayaji a wuya,,,
Daga lokacin bai samu yin bacci ba har asuba
Yayi sallah.....

Ya wayi gari da mungun 6acin rai, bayason kula kowa, da haka har yaje hospital d'in, yana tsananin mamakin kansa "how comes Zan iya ya'kar Tiger?" Abunda yake yawo masa a rai kenam.........




Sorry my fans kuyi manage da wannan banida time ne ๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™



*๐Ÿค SDEENDTM DATA SERVICES๐Ÿค*
*MTN* . *Airtel*
1GB = โ‚ฆ300. 1GB = โ‚ฆ350
2GB = โ‚ฆ600. 2GB = โ‚ฆ700
3GB = โ‚ฆ900. 3GB = โ‚ฆ1000
4GB = โ‚ฆ1200. 4GB = โ‚ฆ1300
5GB = โ‚ฆ1500. 5GB = โ‚ฆ1600

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = โ‚ฆ350. 500Mb โ‚ฆ250
2GB = โ‚ฆ700. 1GB โ‚ฆ500
3GB = โ‚ฆ1050. 2GB โ‚ฆ1000
4GB = โ‚ฆ1400. 3GB โ‚ฆ1500
5GB = โ‚ฆ1750. 4GB โ‚ฆ2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ
*๐Ÿช€08066268951*




*ASMEETAH* *CE* โœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธ

*FREE* *BOOK*

๐Ÿ… *MATAR* *DAMUSA* ๐Ÿ…
(the wife of tiger)

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* โœ๏ธโœ๏ธ


https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt


*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦ™alaminmu ฦดancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ *{{N W A}}* ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ


ุจูุณู’ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู…ู ุงู„ู„ู‘ู‡ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญู’ู…ูŽู†ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญููŠู’ู…

*BOOK* *ONE*
*PAGE* 37 & 38



Ganin Junaid a wani irin yanayi yasa Dr. Hasheem tasowa da sauri yana fad'in "Kai lafiya kuwa Junaid meya faru haka"

Karasowa wajen Dr. yayi yana huci yace "She's die, Please go and check her"

Shima kansa Dr. ya razana yace "Who? Kodai jikin mommy ne?"

"Noo not my mom, tana nan kwance zata mutu"
A cewar Junaid gaba d'aya baya cikin hayyacinsa.

Dr. gaba d'aya ya kasa motsawa sai cewa yake "ba mom ba to wace ce?"...

Cikin zafin rai Junaid ya finciko hannun Dr. suka nufi room d'in da Ayush take a kwance.....

"Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un meya sameta....?"
Dr. ne yake fad'in haka tareda sa hannu zai d'auketa....
Junaid yayi saurin dakatar da shi yana fad'in "Leave her.."
Yasa hannu ya d'auketa ya d'orata akan gadon da aka kwantar da mom, Dr. murmusawa yayi a ransa yake fad'in "Toh me hakan yake nufi? Ya hanani d'aukarta sai shi! Allah yasa dai ba wai sonta yake ba, na tabbata ba abunda zai hana zuciyata bugawa" domin tin ranar da ya fara tozali da Ayusha yaji 'Kaunarta ya mamaye mashi duk ilahirin farfajiyar zuciyarsa, kullum da sonta yake kwana kuma yake tashi sai dai kuma ya kasa furta hakan yana jiran lokacin da zai sanar da hakan, 'Daukar da Junaid yayi mata ba 'Karamin 'kona masa rai yayi ba, ba 'karamin kishi yaji a ransa ba.....!

"Dr. Hasheem please ka taimaka karta mutu" Junaid ne ya katse shi daga dogon tunanin da ya zurfafa,
dasauri Dr. yayi kan Ayush yana cewa "Please kayi waje inason dubata" Yana 'kokarin sa mata oxygen...

mommy ce ta ri'ke hannun Junaid tana fad'in "Son muje waje ko Dr. zai dubata, ba'a treat d'in mutum a gaban mutane am sorry.."

Waje suka fita tareda mommy itama a halin yanzu ba abunda zata iyayi domin a tsorace take, hankalinta ya kasa kwanciya.....

Fitarsu Junaid yaja mommyn sa zuwa gida domin ta samu hutawa, gashi akan gadon asibiti ta tashi jikinta ba 'kwari..

............shi kuwa Dr Hasheem bayan ya gamawa Ayush allurai da sauran abubuwan da take bukata,
zaunawa yayi a bakin gadon da Ayush take ya zuba mata eyes yana mata kallon kauna!
Ita kuwa ido a rufe har yanzu bata farfad'o ba, duk a wuni gudan nan Dr. shi yaketa hidima da lafiyar Ayush,
bayan nan zuwa mangrib Ayush ta farfad'o Dr yana bata kyakykyawar kulawa, yayi mata wasu siyayya na kayan ci da sha,

sai dai har zuwa yanzu Junaid da Mommy a cikinsu ba wanda yazo duba Ayush....

(Bari kuma mu le'ka 6angaren su Junaid)....

*****

Bayan komawar su Junaid gida,
mom ta shiga damuwa sosai ganin halin da Ayush take, dakyer Junaid ya samu nutsuwa har ya rarrashi mommy, tayi wanka ta shirya already ta ci abinci zuciyarta cike da damuwa ta shigingid'a akan bed d'inta har bacci yayi awun gaba da ita....

Junaid bayan ya kammala abubuwanda zaiyi, zama yayi a bakin gadon sa ya dafe kansa da hannayensa biyu, kai a sunkuye ganin yanda ya rikice akan Ayush abun ya d'aure masa kai mamakin kansa yake, yana maganar zuci
"Meye matsala ta da wannan yarinyar har na damu haka? Shin akwai wata ala'kane a tsakanin mu? no imposable hakan bazai ta6a faruwa ba, bana jinta a raina.."
kawai ya d'auki hakan a matsayin tausayi.....
tashi yayi domin zaman tunanin bashida wani amfani,
beside wadrobe yaje jikin bangon d'akin ya tura sai kawai naga ya bud'u...
ashe 'kofa ne a gurin, ba banbanci da bangon d'akin domin har fentin d'akin irin na 'kofar ne kuma bashida mari'ka,
gani nayi ya shige d'akin, bazaka ta6a cewa akwai d'aki a wajen ba...
ashe d'akin sirri ne, duk wasu abubuwansa na 'kundin sirri a d'akin yake, bayan shi da mommy ba wanda yasan da d'akin a cikin room d'in Junaid...

Bayan ya shiga!
d'akin duhu d'irin saida ya kunna haske,
(wow fashion room)

'Dakine na alhurma 'karami had'add'e,
ga kujeru a jere guda hudu da table a tsakiyar kujerun,
ta 6angare guda kuwa wata 'katuwar laptop ne a ajiye saman katuwar table...

sai wasu photuna a manne jikin bango an jejjerasu sannan an rubuta *Attack* a jikin photunan.....
wad'anda aka kai musu hari kuma an ja cancels da jan maker....

wato photunan manya-manyan masu laifi ne, wadanda aka kama da wadanda ake so a kama....
aciki har na hango photon mahaifiyar Ayush wato Bara'at ita an rubuta ATTACK wato anaso a kamata kenam...

sai kuma wani 'katoton Poster mai d'auke da photon wani mutumi fari tass dogo mai suman gashi a kwance, poster shi a tsakiyar sauran 'kananun photunan, wannan shine babban mai laifi wanda duniya gabaki d'aya nemansa suke
'Kasashe daban daban har kudi trillions 100 aka d'aurawa duk wanda ya kamoshi,
Junaid kuwa ya d'orawa ransa saiya kamo mutumin nan ba dan kud'i zai kamoshi ba sai don duniya ta zauna klau....

idan kuka zuba ido akan mutumin kamar sa sak irin ta Ayush, sai dai ba kowa ne zai fahimci hakan ba,
Amma shine mahaifin Ayush wanda yaketa wahalar da Junaid.......


Masha Allah
to be continue next...


*๐Ÿค SDEENDTM DATA SERVICES๐Ÿค*
*MTN* . *Airtel*
1GB = โ‚ฆ300. 1GB = โ‚ฆ350
2GB = โ‚ฆ600. 2GB = โ‚ฆ700
3GB = โ‚ฆ900. 3GB = โ‚ฆ1000
4GB = โ‚ฆ1200. 4GB = โ‚ฆ1300
5GB = โ‚ฆ1500. 5GB = โ‚ฆ1600

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = โ‚ฆ350. 500Mb โ‚ฆ250
2GB = โ‚ฆ700. 1GB โ‚ฆ500
3GB = โ‚ฆ1050. 2GB โ‚ฆ1000
4GB = โ‚ฆ1400. 3GB โ‚ฆ1500
5GB = โ‚ฆ1750. 4GB โ‚ฆ2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ
*๐Ÿช€08066268951*




*ASMEETAH* *CE* โœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธ


๐Ÿ… *MATAR* *DAMUSA* ๐Ÿ…
(the wife of tiger)

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* โœ๏ธโœ๏ธ


https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦ™alaminmu ฦดancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ *{{N W A}}* ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ


ุจูุณู’ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู…ู ุงู„ู„ู‘ู‡ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญู’ู…ูŽู†ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญููŠู’ู…

*BOOK* *ONE*
*PAGE* โžก๏ธ 39 to 40 โฌ…๏ธ


zaune yake akan kujerar table yanata danna laptop a cikin wannan akurkin d'akinsa na tsaro, yana duba yanda zai samu sarkin matsafa yasan sunan dajin domin wani babban malami ya sanar masa yanda wannan bokan yake sai dai akwai tsaro sosai a wannan dajin,
ansha tura manya-manyan sojoji cikin wannan dajin domin kamo shi amma ba wanda yake fitowa da rai!
ansha d'aukowa sojojin 'kasar waje har daga pakistan amma duk asarar rayukansu ake har sun ha'Kura, amma shi gogan Junaid yace yayi alkawari saiya kamoshi..

seaching yayi daga computer ya rubuta *DAJIN* *MAQARQASHE* Dajin dayafi ko wanne hatsari a duk fad'in duniya...
yana so ya kutsa cikin dajin ta computer amma abu ya gagara Error ! Error !! Error !!! Kawai yake nunowa, koda na'kura baza'a iya shiga ciki ba...

masu tsaron wannan dajin sune manya-manyan ba'ka'ken aljanu masu hatsarin gaske,
ga namun daji masu hatsari na tsafi an bazasu a cikin dajin nan ta ko ina, kafin ka iso gurin bokan nan tafiya ne mai nisan bala'i har sai anyi sati guda ana cikin wannan dajin ba'a isa gurin sarkin ba,
a gaba akwai wani 'katoton rami na gaske, 'kasin ramin wuta ne yake ci koda yaushe yana kan ruruwa, abu na tsafi sai a hankali!
siririyar gadane aka d'ora akan ramin wanda za'a bi kafin ka tsallake, idan kayi kyakykyawan taku kuwa tsabb zaka fad'a cikin wutan...
bayan wannan ramin sai ka had'u da manya-manyan kadoji na bala'i masu jajayen idanuwa (crocodiles)
suma saika tsallake su, sai kuma a gaba 6angaren macije masu kayuwa biyu-uku har da masu kayuwa biyar biyar masu dafin tsiya kana ganinsu kasan na tsafine,
saika tarar da masifu da bala'i a cikin dajin nan kafin kazo 'kofar get na fada wanda masu gadin kofar wayyo ganinsu ma masifa ne, ba 'kananun masifun aljanu bane, ko tsuntsu basa bari ya shigo cikin wannan fadar wanda baka iya hango tsayin get d'in.......
kafin ka wuce harabar fadar sai kayi tafiya mai nisan bala'i hakan ma kana tafiya kana taka garwashi mai 'kunar gaske sai 'kafarka ya gama toyewa kafin ka iso mashigar cikin fada na biyu shi kuma 'kusosi zakaita takawa har ka isa mashigar kofa ta uku, anan kuma zallar taron aljanune manya da 'kananu masu tsoritarwa kowannensu da madubin haske duk ilahirin jikin mutum
shi wannan madubin tsaraicin mutum yake nunawa saboda kar a shugo musu da abun ya'ki, hakan mah tsaro ne.!
Daga nan sai kofar shiga cikin fadar sarkin matsafa, nan ma kafin ka shiga akwai kofar tantancewa sai da shatin hannun wani ba'kin 'katon aljani mummunan gaske kallonsa abun tsoro, wannan idan bil adama ya kalleshi ba abunda zai hana ya tafi lahira tsabar bashida kyan gani, saida shatin hannunsa kafin wannan kofar ta bud'u sai kayataccen fadar sarki ga kujerarsa na alhurma...
gashinan mutum ne dan adam fari tass dashi kyakykywa suman gashin sa akwance har gadon bayan sa kamar mace,
gashi da 'kirar yahudawa, sai wasu tarukucen sar'ko'ki a wuyansa, kujerarsa mai zanen Damusa ne, ga kuma wani 'katoton Damusa a gefen shi yana zaune, (Damusar Junaid ba)
A gaban sarkin wani kayataccen madubi ne mai she'kin bala'i wanda a cikinsa yake ganin duk abunda yake faruwa a cikin gari,
duk waran da yakeson gani haka madubin zai nuna masa, madubin tsafi kenam....

saman jikin bango kuma an manna kalandar photon Ayush an sanya mata hular sarauta a kanta da rigar sarauta irin wedding gown fari sol, ga gashi yala yala a kanta har gadon baya sai she'ki yake...
(Ku lura itace take fitowa a cikin mafarkin Junaid da wannan shigar sarautar ๐Ÿ˜ƒ)....

Idan kaga sarkin matsafa kaga Ayush a wanda ya lura kenam...



Please Login or Register in order to submit comment