Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"you are very stupid, meya kawo ki ɗakina da sassafe?.."

turo baki tayi tana gunaguni daga baya tace "yoo Yaya nazo tambayar ka Maimoon ce ko kasan yanda taje ta, yanzu Ammynta ta ƙira waya tana tambaya wai bata kwana a gida ba..."

gaban Doctor Hasheem ne yayi wani irin bugawa yana zazzaro ido waje lokaci guda kuwa ya rikirkice yana ƙiƙƙina yace "ba b b ba ban san inda taje ba, ki tafi ki ba ni guri..."

Laylah cike da mamaki ta kama baki tana maganar zuci tace "subhanallahi ya naji Bros kamar yana cikin matsala? yanzu haka nasan bazai wuce akan wancan daƙiƙiyar yarinyar ba.." taja dogon tsuka sannan ta nufi ɗakinta..

yana zaune yasa Maimoon a gaba ya yi tagumi, har zuwa yanzu ya kasa tsinana komai ga jini baje-baje akan gado, bata farfaɗo ba har yanzu,
lokaci guda ya zamo abun tausayi, shima kansa yayi regreted akan abun da ya aikata wa Maimoon, domin tinda yake bai taɓa aikata zina ba, yau sai gashi ƙaddara ta riga fata, yana fitar da furuci a bakinsa "wai yau ni ne Doctor Hasheem na yi fyaɗe a yarinya? ni ne mai ceton rayukan al'umma yau gashi an wayi gari zanyi sanadiyar rasa rayuwar yarinya..." bubbuga goshinsa yayi tare da fashe wa da kuka...

wata zuciyar ce ta sanar masa cewa "ka tashi ka ceci rayuwarta..."
a zabure ya tashi ya rungumota caɗatt ya ɗagata ya nufi toilet da ita,
ya kunna ruwan zafi a cikin seat bith ya tsundumata, sai da tayi 5 minute a cikin hot water kafin ya wanke ta, sannan ya ɗagota suka nufi bedroom, kwantar da ita yayi a ƙasan carpet ya cire bedsheet mai jini ya canza wani sannan ya kwantar da ita akai,

a hankali take buɗe eyes ɗinta, ruwan zafin ya ratsa jikin ta sosai, sai hawayen da yake ta faman zirya a saman fuskar ta, ta kasa motsawa ko da ɗan yatsanta ma,
ganin ta farfaɗo ne yasa ya haura saman gadon yana ƙiran sunanta "Maimoon! Maimoon ki kwantar da hankalinki zaki warke kinji, kiyi haƙuri na aikata miki babban kuskure ki yafe ni dan Allah, duk ke kika jawo hakan ta faru...."
ya ƙarasa maganar yana goge mata hawayen da suke zubo mata...

ita kuwa kallon sa kawai take ta kasa motsa lips ɗinta ma, bazata iya magana ba...

tashi yayi da sauri ya nufi hanyar fita, buɗe ƙofa ya yi ya fice kai tsaye ɗakin magani ya nufa, yaje ya ɗauko abubuwan da zaiyi wa Maimoon ɗinki a farji domin yaga ba ƙaramin farkewa tayi ba, duk ya yayyaga ta,
fito wa yayi da akwatin maganinnuwa da allurai ya shugo falo da sauri zai wuce room ɗinsa ƙwatsam ya tarar da Laylah zaune akan kujerar falo da robar ruwa a hannunta tana waya da Ammy tana faɗin "ki kwantar da hankalinki Ammy insha Allahu za'a sameta, wata ƙil gidan su ƙawarta taje dare ya yi mata acan, amma zan bincika kafin dai Abul ya ankara da ita zan nemo ta....."

juyowar da zata yi suka haɗa ido da Dr Hasheem ga kuma boxe na farmacy a hannunsa, babban abunda ya ɗaga mata da hankali shine jinin da ta gani a gaban jallabiyarsa, zaro ido tayi waje murya a harharɗe take cewa "Ammy zan zan ƙira ki daga baya, duk yanda ake ciki zan sanar miki..." da sauri ta katse ƙiran tare da tasowa da sauri tazo gaban Dr tana kallon jinin gaban rigarsa tace "Yaya aina ka samo wannan jinin? ciwo kaji ne ko meye?.." ta ɗago tana kallonsa.

hannunsa ɗaya yakai saitin goshinsa ya dafa tareda rufe idanuwansa kansa ne yake masa wani irin ciwo, sai da ya ɗan juma bai bata amsa ba still idonsa a rufe, a hankali yake ƙoƙarin buɗe idonsa buɗewar da yayi yaga wayam ba Laylah a gurin, waro ido waje yayi yana maida numfashi sama-sama shima da sauri ya nufi ɗakinsa har hajijiya yana shirin ka dashi,
shigar sa cikin ɗakinsa ya tarar da Laylah akan gado tana ta ƙiran sunan "Maimoon! Maimoon meya faru dake haka, dan Allah kiyi magana mana.."

Maimoon ba abunda take sai kuka, hannunta yana kakkarwa ta ɗago da shi ta ɗora hannunta a saitin wajen farjinta,
tana lulluɓe da mayafi Laylah ta kai hannu ta yaye mayafin domin ba yau ta saba ganin tsaraicin Maimoon ba haka itama,
Laylah ido ta zaro waje sosai ganin yanda gabanta ya yi fata-fata, fashe wa tayi da kuka ta kalli yanda Yayanta yake tsaye a bakin ƙofa
tace "Yaya fyaɗe kayi mata? saboda rashin imani da tausayi? mahaifiyar ta tana can ta tayar da hankalinta akan rashin ganin ɗiyar ta ashe tana nan rai a hannun Allah! tirrrr...."

ɗago wayar ta tayi tana dannawa tare da faɗin "bari na ƙira mahaifiyarta na sanar mata tazo ta ɗauki ƴarta tin kafin ta mutu a nan...."
da gudu Doctor Hasheem ya yo kan Laylah yana faɗin "dan Allah ƙanwata ki rufa mun asiri, ki temake ni nima nasan nayi kuskure, banyi niyar aikata mata haka ba tsautsayi ne..."
ya ƙarasa maganar tareda fashe wa da kuka yana riƙe da hannun Laylah..

Laylah itama kukan take tana bubbugan bayan Yayanta alamar rarrashi, tayi matuƙar tausaya masa a halin da ya shiga, gashi har ya ɗan rame idonsa sunyi jawur,
tace "to shikenam Yayana ya isa haka banason jin kukan ka, amma meyasa ka aikata mata haka, ko dan saboda yanzun baka sonta shine dalilin da yasa ka ɗauki ƙwaƙƙwaran hukunci har haka? Yaya idan har baka sonta bai kamata kayi mata haka ba..."

"ƙanwata wallahi ba da son raina nayi mata wannan aika aikan ba, ban san ta shugo ɗakina ba tin 1:00 cikin dare, nasan daga gida take a wannan lokacin tazo ta gana da ni ne, maimakon na rarrashe ta sai nabi son raina na aikata mata laifi...." kasa ƙarisa maganar ya yi yana hawaye idonsa akan Maimoon wacce itama kallonsa take tana hawayen baƙin ciki, magana ne bazata iya yinsa ba amma a cikin zuciyarta ji take kamar ta sheƙe kanta, lokaci guda kuma taji tsanar Doctor Hasheem a cikin zuciyarta tinda tasan da mugunta yayi mata haka har da shaƙe mata wuya yana so ya kasheta,
haka take tariyo abubuwan da ya faru a tsakaninsu da marin da ya rinƙa jera mata, girgiza kai kawai take sai yanzu ta ƙara tabbatar wa Doctor Hasheem ba ƙaunar ta yake ba, baya sonta,
itama a wannan lokacin ta cire soyayyarsa a cikin zuciyarta ta mayar da ƙiyayya gurbin soyayya....

Laylah ce ta sauƙe ajiyar zuciya sannan tace "tooh Yaya yanzun meye mafita?.."

Abunda Doctor yake son ji kenam da sauri ya ɗago yana faɗin "a yanzu inaso zanyi mata aiki ne a wajen da taji ciwo saboda idan aka bar gurin zata samu babban matsala daga ƙarshe kuma cancer zai iya shiga..."

Jijjiga kai Laylah tayi tace "ka samu kayi mata aikin Yayana, zanje waje na jiraku.."
sauƙa tayi daga kan gadon tana sharar hawaye ta fice a ɗakin...

shi kuwa akwatin ya buɗe ya ciro allura sai da ya mata allurai tukun ya ware mata sawaye ya soma mata ɗinki, acikin alluran da yayi mata har da na kashe jiki yanda bazata ji ciwo ba,
kafin ya kammala har tayi bacci saboda har da allurar bacci yayi mata!
ya haɗe ta sosai ciki da waje..
sannan ya maida mata da kayan jikinta ya rufe ta da mayafi...

a falo ya tarar ta Laylah zaune ganinsa yasa ta zabura ta tashi tana tambayarsa "yadai ka gama ne, ina tana lafiya?.."
shima zama yayi a kujerar yana sauƙe numfashi, yace "anyi nasarar yimata aikin, yanzu dai tana bacci.."

Laylah ta kalli Yayan natan tace "toh Yaya ya zamuyi da ita yanzun? kaga bazata iya tafiya ba, kuma gidan su zasu tsorita sosai da rashin ganinta.."

tagumi yayi sannan yace "nima haka nake tunani, bansan ya zanyi ba Laylah, tunani na ya gushe, bazan iya sama wa kaina mafita ba, tabbas nasan idan wannan maganar ta fito ba abunda zai hana na tafi prison, mahaifinta bazai ƙyaleni ba duk da shi ɗin abokin mahaifin mu ne, ina tsoro wallahi.."

Laylah ce tace "toh amma Yaya kana ganin Maimoon zata rufa maka asiri ne?.."
ta ƙarasa maganar tana kallon cikin ƙwayar idanunsa,
ƙararar zallar tsorone a cikin eyes ɗinsa yace "nima ban saniba.."
Tace "Yaya ga mafita ɗaya.."
da sauri ya kalle ta yana faɗin "ina jinki Autar.."

tace "mezai hana mu riƙe ta a cikin gidan nan har ta warke, idan ta warke ta iya tafiya sai mu tura ta gida, kafin nan su kuma iyayen natan sun ankara da an sace ta, duk neman da zasu bazasu ganta ba, mu kuma mun ɓoyeta a cikin gidan nan, zamu karɓi wayarta mu kashe, sannan zamanta a cikin ɗakinka babu tsaro zamu gyara ɗakin ajiyar marigayi Abban mu dake can bayan ɗakunan gidan, tinda kaga ba'a san da ɗakin nan ba,
zamu cigaba da kula da ita, tinda ni yanzu bana zuwa school kula da ita ya rataya mun a wuya kai kuma sai ka cigaba da zuwa gurin aikin ka hankalinka a ƙwance ba mai zarginka akan kai ka ɗauke Maimoon, nima kuwa zan cigaba da zuwa gidansu saboda nuna baƙin cikina akan ɓatar Maimoon, itama idan ta warke insha Allahu bazata tona maka asiri ba ai bazata daina sonka ba..."

Doctor Hasheem sake baki yayi yana kallon Laylah,
a ransa yana jinjina mata da irin wannan basiran da Allah ya bata,
"Yarinya ƙarama ta iya samo mafita haka.." yana maganar zuci.
har saida ta kammala jawaban ta tukun ta kalleshi tace "toh ya kaga Yaya hakan yayi?.."

da sauri ya jijjiga kai yana faɗin "of course my yonger sister, kin kawo shawara mai kyau, hakan ma za'ayi, sai na cigaba da mata magani a nam ba,
toh amma Haydar fah? kinga yana gidan kar wata rana ya gano mu, duk da nasan bazai toni asirin mu ba amma nafison daga ke kar wanda yasan da wannan maganar.."

Laylah tace "to ba daman yanaso ya tafi katsina gurin Kakan mu ba ka hanashi! yanzu kuma saika barshi ya tafi tinda sun kammala exam.."
yace "gud.." yana farin ciki sai yanzu hankalinsa ya dawo jikinsa..

Laylah ta kuma cewa "wato Yaya harda zagina ɗazu saboda na ƙwanƙwasa maka ɗaki ko? kana so ka ɓoye mun aika-aikan da kayi, toh yanzun inda ban saniba ya zakayi da ita?..."

shuru Doctor yayi yana murmushi yace "ke dai bar maganar nan, mu fara zuwa ɗakin can mu gyara shi sosai, mu kai katifa ɗakin kinsa babu komai a ɗakin sai gayyar datti da takardu..."

tace "toh shikenam amma kafin mu fara kaje kayi wanka ka canza wannan jallabiyar takan mai jini, kar kayi baƙo kuma a shige su..."


gaba ɗayan su suka ƙwashe da dariya,
ya tashi ya nufi ɗakinsa yana faɗin "bari naje kar addu'arki ta karɓu azo ayi baƙi..."



*******

Ɓangaren su Junaid...

Bayan ya shugo da zuƙeƙiyar motarsa direct waran ma'ajiyin motoci ya nufa yayi parking ana kusa da motar Mommy, sauƙowa yayi yana jan ƙafa ya nufi motar Mommy wacce tin isowar ta bata fito ba sai kanta data kifar akan sitiyari, buɗe murfin motar yayi ya shugo...

yana motsi da bakinsa daƙer ya iya cewa "Mom please forgive me, nayi kuskure babba dana sanya ki kuka, dan Allah Mom kiyi haƙuri insha Allah bazan ƙara aikata makamancin abunda nayi miki ba, bansan ya zanyi ba ina matuƙar ƙaunar Yushert...."

ɗagowa Mommy tayi da murmushi a fuskarta ta kai hannu tana shafar gefen fuskar Junaid tace "da gaske my son! kana son Ayush amma baka son maganar Aure?.."
ta ƙarasa maganar tana kallonsa cike da zolaya,
yamutsa fuska yayi sannan yace "nifa bance bazan Aure ta ba.."
dariya Mommy tayi sannan tace "shikenam my son, nayi haƙuri nima kayi haƙuri da marin dana maka..."
turo baki ya yi yana faɗin "nifa banji zafin marin ba, ganin hawayen ki yafi komai ƙona mun rai kuma naji raɗaɗi sosai a cikin zuciyata..."

"it's okay My son, nima ba'a son raina na mareka ba, sannan ba wai akanka nake zubar da hawaye ba, sai dan rashin ganin Ayush kuma ba'a san yanda take ba,
ina zaune cikin ƙunci da takaici ina nazarin taya akai Ayush ta ɓata a cikin ɗaki ina sallah, sai gaka kai kuma kayo kaina kana mun wasu surutai, hakan yasa na zuciyo na huce takaici na a kanka,
Junaid! ba wai kai kaɗai ka ke cikin matsala ba, nima kaina ina cikin damuwa..."

hura iskar bakinsa yayi sannan yace "toh mom aina zan samu Yushert?..."
ta juyo tana kallonsa tace "za'a sameta ka ƙwantar da hankalinka ɗan albarka na, ɗan fari kyakykyawa naaa..." tana masa wasa duk dan hankalinsa ya kwanta, shi kuwa ba alamar annuri a fuskarsa sai ma kawar da kansa gefe da ya yi..

yace "Mom ina dai kin haƙura ko?.."
ajiyar zuciya Mommy tayi sannan tace "Junaid na haƙura mana, a rayuwata bana ƙaunar na mareka saboda daraja uku da kake dashi a gurina,
na farko siffarka irin na mahaifinka ne kamar ku ɗaya sak, idan na mareka gani nake kamar na mari mijinaa,
na biyu kai mai sunan mahaifi nane kuma abun alfahari na JUNAIDD, kamar yanda bazan so na ƙuntata wa mahaifina ba haka bazan so na ƙuntata maka ba albarkacin suna,
na uku kuma fuskarka yana da matuƙar daraja, bazan so na rinƙa marin fuskar ba saboda kai ɗaya nake da akwai, baka da Yaya baka da ƙanne shiyasa nake jii dakai my son, hakan yasa na sanya wa asibiti na suna JUNAIDU, GENERAL HOSPITAL ABUJA.
bana son abunda zai ɓata maka rai my Auta..."

murmusawa Junaid ya yi jin abunda mom ɗinsa take gaya, ta sashi a gaba tana ta masa surutai kamar wani yaro ƙarami...

yace "Mom fito mu tafi to.."
tace "ni ba yanda zanje ni daga cikin motar nan har saika mun dariya.."
kallon ta yayi shi har ga Allah bashi da niyar yin dariya a wannan lokacin, amma saida mommy ta nace masa akan saiya yi dariya,
ba tare da ya kalleta ba yayi murmushi har sai da waɗannan twince dimple ɗinsa suka lotsa, ba ƙaramin kyau yayi ba, mommy tace "wow gaskiya Ayush tayi dacen samun kyakykyawan namiji anan, thank god..."
yana jinta bai ce ƙala ba shi kaɗai yasan irin ƙololuwar baƙin cikin da yake cikin zuciyarsa na rashin Yushert ɗinsa,
haka suka fito daga cikin motar suka nufi compound,
mommy key tasa a ƙofar falo sannan ta buɗe suka shiga ciki....

duk da sun san babu kowa a cikin falon amma sai da sukayi sallama,

Ayush jin sallamar Mommy yasa ta buɗe eyes da sauri, ta ɗago tana faɗin "Mommy! Mommy!! ina Yaya Junaid ɗina..."
ta taso ta nufi gurin da suke a tsaye suna kallon ta cike da mamaki a fuskarsu,
Mommy kam bata gaskata cewa Ayush bace, kafin Ayush ta iso gurin da suke Mommy tayi waje da gudu tana faɗin "mun shiga uku aljanaaa...."

Ayush tsayawa tayi a gaban Junaid tana kuka tace "Yayana! daman da gaske ne baka mutu ba?..."

Junaid girgiza kai kawai yayi bai tsaya bata amsa ba ya sa hannu ya rungumota jikinsa yana caccakuɗa sumar kanta tsabar tsananin farin ciki,
rungumarta yayi sosai kamar zai mayar da ita cikin cikinsa, itama rungumarsa tayi tana kuka.....

Mommy tana daga waje sai leƙen su take ta window,
ta ɗan buɗe kafar labule ta kanne ido ɗaya tana leƙensu, zuciyarta kuwa bugun uku-uku take, ga gumin da yake tsirto mata, a tsorace take sosai, ganin ɗaki a rufe taya Ayush ta shugo? kuma yarinyar da take kwance rai a hannun Allah lokaci guda ta miƙe?,
igiyar kan Mommy ne ya fara sincewa,
tana faɗin "waɗannan yaran zasu haukatar dani,
haka shima Junaid yayi kuma du ga Ayushert? anya kuwa da mutane nake rayuwa a cikin gidan nan??..."

tana cikin wannan tunanin ta sake leƙasu taga basa falon, a ruɗe ta juyo ta bayanta taga gasu nan a tsaye sun zuba mata ido suna mata dariya hannayensu riƙe dana juna,
hajijiya ne yake shirin ka da Mommy tana faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, subhanaka inni kunta minaz zalimiin, innahu min sulaimanu wallahi ku kuke ganin mu bamu ke ganinku ba, kuyi mun raiiiii...." sai luuu zata faɗi ƙasi Junaid yayi saurin taro ta yana ƙiran "Mom! Mom!! please..." ta riga da ta suma a wajen, ɗaga ta yayi suka shige cikin falo kai tsaye ɗakinta ya nufa da ita ya kwantar da ita akan gadonta,
sai ga Ayush itama ta shugo da gudu hannunta riƙe da bottle na ruwa da sauri ya karɓa ya since murfin yana watsa mata ruwan akan fuskar ta,

a firgice ta tashi tana salati har idanuwanta sun shan-shanye kamar wacce tasha maye!
haka take binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, da ƙer ta iya furta "Ayushh?.."
girgiza mata kai kawai Ayush tayi ga hawaye shaɓe shaɓe akan fuskarta ganin Mommy a wani irin yanayi.....

*MOMMY DOLE FAH KI RIKICE🤔🤔*
*YA ZA'AYI MUTUM YANA KWANCE A ASIBITI KO MOTSI BABU

Please Login or Register in order to submit comment