Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da malamin nan ya koya muku ke da mahaifiyarki" anan ta tuno da Baba tsoho wanda yayi hijira zuwa dajin da suka zauna yayi tsawon shekara biyar atare da su, Babban malami ne na gaske shi ya koya musu karatun al'qur'ani mai girma tare da addu'oi ya koya musu alwala da yanda ake sallah su wankan janaba da haila ba abunda bai koya musu ba ta 6angaren addini, Ayush lokacin bata wuce 15yrs ba ita kuma mahaifiyarta tana 'kara koyan karatun ne domin wad'annan karatuttukan mahaifin Junaid ya koyar mata su tin suna GHANA.
Damuwar dai Ayush ta samu ta koya duk da itama tana koya mata wasu abubuwan!!

Anan tayi firgitt ta soma jero manya-manyan addu'o'i....

πŸ‘‰. "Allahumma laa sahla illaa maa ja'altahu sahlan wa anta taj'alul hazna izaa shi'ita sahlan"
(Yaa Allah! Babu wani abu mai sau'ki sai abin da ka sanya shi ya zama mai sau'ki, kuma Kai kana sanya tsanani idan ka so ya zama sau'ki)

"'Kadrul laahi wamaa shaa'a fa'ala"
(Kaddarar Allah ce, kuma abin da Allah ya so, shi ne yake aikatawa, domin da-na-sani tana bud'e 'kofar aikin shaid'an).

"Laa ilaaha illallaahul aziimul haliimu,
Laa ilaaha illallahu rabbul arshil aziim,
Laa ilaaha illallahu rabbus samawati wa rabbul ardi wa rabbul arshil kariim"....

Bayan ta kammala addu'o'in ta ta shafa ayatul kursiyu, duk wani tsoro da fargaba da 'kuncin zuciya ya wuce mata ta 'kwarin gwiwarta ta mi'ke tsaye ta nufi d'akin da ake bu'katar taimako!

Upstairs ta fara takawa a hankula har da iso bakin 'kofar d'akin tasa hannu zata ture d'akin...
Aka daka tsawa "kada ki kuskura ki bud'e" amma kash duk wannan maganganun kunnen Ayush ya toshe bata jin maganar
Tana bud'e d'akin kuwa wani irin duhu ne a d'akin babu haske kwata-kwata tana shiga d'akin haske ya bayyana ta ko Ina, still yanda taga mutanen nan a kwance haka ta same su
Ta d'aga kanta ta kalli yanda Junaid yake a manne a jikin gini ganinsa yasa ta tsorita naman jikinsa duk ya farfashe ciwon yanzu yafi na d'azu hakan na nufin har yanzu basu daina azabtar da shi ba,
Girgiza Kai tayi tana maganar zuci "bazan iya kusantar ka ba, ka rigada ka mutu". Toilet ta nufa ta d'auko bucket da ruwa a ciki duk bodyguard d'in da suke kwance ta bisu da ruwa tana kwakwkwara musu cikin sa'a kuwa suka tattashi a firgice suna ajiyar zuci, bayan sun dawo hayyacin su kowa rige-rigen fita yake daga cikin d'akin har mai gadin!
Ta dawo kan Mommy itama ruwa ta yayyafa mata, ajiyar zuciya tayi tana Jan numfashi sama-sama tana ambaton "Junaid! Junaid my son, ya mutu ko? Kamar wata zararriya haka take magana tana bin Ayush ta kallo, mommy bata san waye akan ta kawai dai tana sambatu ne,
Ayush ta tsaya tana tunanin aina ta ta6a jin sunan nan!
Tana cikin wannan tunanin tajiyo kukan mommy ya tsananta sosai tana kuka tana nuna gurin da Junaid yake da yatsanta, kafin kace mai Mommy ta tashi da gudu tayi kan Junaid
Da karfin gaske aka hankad'o mommy baya da sauri Ayush ta tareta badon haka ba fad'uwa 'kasi zatayi.
Lokaci guda idon Mommy ya 'kakkafe ta dafe 'kirjin ta tana shure-shure ciwon zuciyar ta ta tashi,
Ayush ta tsorita sosai da ganin haka da kyar ta iya d'ago Mommy suka fita daga d'akin
Falo ta nufa tana zuwa ta tarar da bodyguards duk sunyi cirko cirko kowa yaji jiki sai ajiyar zuciya suke sau'kewa
Da sauri sukayi kan mommy
'Daya daga cikin bodyguard ne ya d'aga mommy cakk yayi waje duk sauran ma binsa sukayi a baya
Motor suka shiga gaba d'ayansu
Motor biyu suka d'auka
Biyu suka shiga d'ayan motor and order car shima mutum biyu a ciki,
Kafin one minute sunbar harabar gidan, iya Ayush da mai gadi kawai aka bari a gidan, da sauri Ayush ta nufi gurin mai gadi tana fad'in "Ina zasu Kai ta?"
In short amsa mai gadi ya bata "Asibity" yana fad'an hakan ya shige cikin d'akinsa zallar tsoro ne a tattare dashi...

"Anya kuwa ba Aljanu a cikin d'akin nan? Junaid kuma? Uma ta ta6a bani labarinta akan Junaid, a'a ba wannan Junaid bane, to aina Zan samu Junaid d'in da Uma take so na taimake shi??
Waye wannan Junaid d'in? Innalillahi wa ina'ilaihi raju'un shi na gani acikin mafarki na idon sa kamar na namun daji,
A'a sharrin mafarki ne bashi bane......
Haka ta rin'ka sa'ke-sa'ke a raanta!...


(KASHH HABA AYUSH KIJE MANA KI TAIMAKI JUNAID MIJIN ASMEETAH 😁😁😁 )

Yawwa dan Allah masoya kuyi hakuri a bisa jinkirin da ake samu waran yin posting, ba NEPA kullum chaji 100 naira, still i'am a student Ina bu'katar yin karatun exam, still I'm married not a single Ina wasu ayyukan gida da kuma Oga worker πŸ˜…πŸ˜…πŸ˜…πŸ˜…. Hhhhhh amun uzuri please πŸ™πŸ™πŸ™


*🀝 SDEENDTM DATA SERVICES🀝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦350
2GB = ₦600. 2GB = ₦700
3GB = ₦900. 3GB = ₦1000
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1300
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1600

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½
*πŸͺ€08066268951*


*ASMEETAH* *CE* ✍️✍️✍️

*FREE* *BOOK*
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

πŸ… *MATAR* *DAMISA* πŸ…
(the wife of tiger)

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* ✍️✍️


*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alΖ™alaminmu Ζ΄ancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

πŸ’«πŸ’« *{{N W A}}* πŸ’«πŸ’«


بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ Ψ§Ω„Ψ±Ω‘ΩŽΨ­Ω’Ω…ΩŽΩ†Ω Ψ§Ω„Ψ±Ω‘ΩŽΨ­ΩΩŠΩ’Ω…

*BOOK* *ONE*
*PAGE* ➑️23 to 24.

Tana cikin nazarin duniya kamar wacce aka zabure ta tayi cikin falo da gudu kamar wanda taga abun tsoro, daga nan ta haura upstairs ta shige d'akin Junaid, da sauri taje gabansa ta tsaya tana ajiyar zuciya! Still a yanda ta barshi anan ta dawo ta same shi, lokaci guda taji wani irin tausayinsa ya kamata ta wani 6angaren kuma tarin tsanar sa ne acikin kwayar idanunta, bata kaunar ganin fuskar shi sunkuyar da kanta 'kasi tayi tana tariyo lokacin da ya buge mata mahaifiya da kalar wulakancin da ya yi mata itama yaso ya rabata da duniyar a lokacin, zazzafar hawaye ne yake gangaro mata ta d'ago da manya- manyan idanuwanta wad'anda sukayi jawur lokaci guda, kallon tsana takeyi mishi tana maganar zuci "saboda mahaifiya ta zan taimakeka, ba don haka ba ba abunda zaisa na ceci rayuwarka a halin yanzu sai dai ka hallaka! Allah yasa ka mutu" a halin yanzu mutuwar Junaid shine farin cikin Ayushh.
Rufe idonta tayi sosai ta d'ago da hannayenta biyu zata jawo shi, wani irin murya ne mai ban tsoro ya daki dodon kunnen ta
"KEE AYUSH KADA KI KUSKURA KI TA6A SHI, UMARNI NAKE BAKI, KAR KI KARYA MUN DOKATA, YANA CIKIN HUQUBA TA" tan fa ta bara jin kukan namun daji dana mujiyoyi πŸ¦‰ cikin firgici da tsananin tsoro yasa ta rungumi Junaid ta 'kan'kame shi cikin rashin sani,
(Ita da ake bata dokar kada ta ta6ashi amma tsananin tsoro yasa ta rungume shi gaba d'aya) dogon numfashi yajaa tare da d'ago kansa sama ya bud'e jajayen idanuwansa wad'anda suka canza launi tsabar azaba, wani irin sanyi yaji a cikin zuciyar shi kamar wanda aka watsa masa ruwan sanyi, sakin shi akayi daga sama ya tafo luuuu ya fad'a kan Ayush atare suka fad'o 'kasan lallausar carpet 'Kara Ayush tayi saboda jin yanda Junaid ya fad'o akan ta ga ciwon breast d'inta da ya fame mata shi!
Shi kuwa sai 'Kara narkewa yake ya 'kara 'kan'kameta, shi yasan kalar nutsuwar dayake samu daga gareta ba tare da yasan ko ita wacece ba, haka yake maida numfashi sama-sama!
Guri kuwa yayi tsitt ba alamar motsi sai numfashin da suke ja a tare.
(Ayush itace samun nutsuwar Junaid, itace kuma samuwar warakar sa indai ta samu rauninsa wanda yake jikinta, in har ta kusanci yanda Junaid yake to babu wani abun cutarwar da zai sameshi, a yanzun mah itace ta ceceshi daga azabar da ake gana masa, domin suma kansu Aljanun tsoronta suke,
Ita d'in dai itace AYANAR JUNAID πŸ§šβ™€οΈπŸ§šβ™€οΈ ).
Dakyarr Ayush ta tattaro iya 'karfinta ta ture Junaid gefe tana mai da numfashi duk ya kashe mata jiki, ta d'ago zata mi'ke ta nufi yanda yake kwance da rarrafe ta Isa waro ido waje tayi tana 'kare shi da kallo abun mamaki duk ciwon dake jikinsa babu shi, jikinsa ya koma normal kamar bashi ne wanda akaita azabtarwa ba babu tabo ko 'kurzune d'aya sai tarin gargasar dake kwance saman kirjinsa,
Abun ba karamin bata mamaki yayi ba aranta take fad'in "Anya ba Aljani bane, nashiga uku nayi gamo" a tsorace taja da baya zata gudu yayi caraf ya ri'ke hannun ta, a hankali yake bud'e idanuwansa yana ganin Dishi-dishi har idon ya washe nan ya sau'ke kyawawan idanuwansa akan ta idon ya washe ya komo fari soll, a hankali yake lumshe ido still hannunsa yana ri'ke da nata a hankali yake motsa 'karamin bakin shi murya Ciki-ciki yake fad'in "Wace ce ke?" Murya na kakkarwa tace "Ni ni ni ni" ta rasa mai zata ce tsabar tsoro kuma lokaci guda yayi mata kwarjini ga wani shakkar sa datake ji! Tana cikin motsa baki ba tare da yasan mai take fad'i ba ya katsar da ita "please can you carry me to go inside bathroom?"
Yayi maganar da harshen turanci, waro Manya-manyan idanuwanta tayi waje tana binsa da kallo, seriously taji abunda ya ce! Duk da batayi karatun boko ba amma ta iya turanci sosai ta koya agurin mahaifiyarta domin Umanta sai data zo Nigeria sannan ta koyi Hausa amma yarenta daga Ghananci sai turanci ta kuma iya yaren French, haka itama Ayush duk ta iya yaren sai dai yaren mahaifinta ne bata iya ba wato fulatanci.......
Ita dai bazata iya maida masa da amsa ba sai dai tayi magana da zuciyarta "How comes Zan iya d'agaka kana nam gardi da Kai, amma sai dai kyakykyawa ne mutumin" tana cikin maganar zuci taji ya ri'kota zai tashi ai tunin ta fad'a jikin shi 'karfinsa ya ninka nata sau goma πŸ˜„
Shima komawa yayi ya kwanta yana binta da kallo, d'agowa tayi a hankali suna fuskantar juna, numfashin su yana dukan na juna, ido cikin ido suke kallon juna! Dakyar Ayush ta iya cewa "you're a strong man, I can't....... Kasa 'karisa maganar tayi sakamakon Breast d'inta dake mata ciwo ga wani feeling da yake shirin kawo mata ziyara duk ya kashe mata jiki shi kuwa babu wani abunda yake ji babu sha'awa a ransa an gusar masa da shi,
Gaba d'aya jikinsa ne yake masa ciwo, shi bai San meya faru dashi ba a tunaninsa duk abunda ya faru dashi mafarki ne saboda ya duba jikinsa babu alamar ciwo...
"I need to bath, please d'agani mana ko na zama gadon kwanciyarki ne" yana magana ne a lokacin da yake shirin tashi...
A kunya ce Ayush ta tashi daga kansa, ita dalilin dayasa ta cigaba da kwanciya masa rad'ad'inda Nononta keyi mata ne yasa ta kifar da kanta saman kirjinsa hakan yasa yayi mata magana.
Tashi yayi yana tafiya a hankali zuciyarsa kuwa cike tam da tambayoyi "shin meya same ni haka bana jin dad'in jikina, and than who is dis girl? And what she her doing inside my room in dis midnight?? still ni da nake kwance on my bed meya kaini 'kasa?". Haka ya shige cikin toilet yana wannan tunanin!
Itama tashi tayi tana maganar zuci "tabbas wannan shine ya sha'ke mun wuya bayan ya buge mun mahaifiya da mota, Anya kuwa yanada lafiya kuwa, Ina tantama akansa wannan ba mutum bane, na ganshi a wani mummunan hali yanzu kuma Gashi lafiyarsa klau ba ciwo a jikin shi Anya ba mafarki nake yi ba..? Shin meye silar faruwar haka..? A lokacin da ya raunana mun breast nabar d'akin normal amma kuma bayar faruwar haka meya faru..? Zanyi bincike akan wannan al'amarin......"
Nufan hanyar fita tayi taji an tsayar da ita "where are you going....?"
Waiwayowa tayi da sauri ta kalle shi fuskarsa a d'aure ba annuri yana d'aure da towel a kunkumin shi alamun ya watsa ruwa ne a jikinsa..
Nufan wurin da take tsaye yayi har sai da 'karaso gurin da take GAF to GAF suna fuskantar juna ya ri'ke kunkumin sa yana mata kallon tuhuma,
Ganin kallon yayi yawa yasa ta sunkuyar da kanta 'kasa tana kallon carpet, hannu yasa ya tallafo ha6arta suna fuskantar juna ya ce "who are you...?"
Shuru tayi batace komai ba sai siraran hawayen da ya gangaro mata.
Sakin fuskarta yayi yana fad'in "can't took to me..? Okay have a seat" ya nuna mata bakin gado, ya koma gaban mirrow yana Milka jikinsa da cream mai shegen 'kamshi! Ayush zama tayi a bakin gadon kamar yanda ya umarce ta tana ta sa'ke-sa'ke a raanta cewa "yanzu kenam yana nufin ya manta da fuskata..? Ya manta da matar da ya d'auki raanta...?" Lokaci guda kuwa taji kamar ta sha'ke shi ta baya.. Tana bin duk surar jikinsa da kallo "gaskiya yana da 'kirar jiki mai kyau, ga tsayi ga fad'i ga d'aurarran jiki ga kuma gargasa ta ko ina a kwance luff-luf gwanin sha'awa sai dai kuma shi baya yabon mace kamar yanda mace take yabonsa bcox baya ra'ayin mace kwata-kwata, bai ta6a jin son mace ko sha'awarta ba haka yake zaune daga gida sai gida ko aiki baya zuwa yanzu....
Ayush fah ta kafa idonta akan Junaid bata San lokacin da take sauwa murmushi ba,
Shi kuwa gaba d'aya ya tsargu da kallon da takeyi mishi , ransa a 6ace ya juyo gareta akaci rashin sa'a jikin mirrow ya Kama towel d'in dake d'aure dashi ya zame gashi bayan towel babu komai a jikinsa .
Ayush tana ganin haka ta zaro ido waje wani irin ihu tayi tabi saman gadon yaraff ta fad'i sumammiya taga abunda bata ta6a gani ba tinda uwatta ta haifeta....... Shi kuwa ihun datayi ne yasa ya bita da kallo bai bi takan towel d'in ba haka ya tsaya zigidirrr yana kallon Ayush wacce ta suma akan gadonsa........


*TO* *BE* *CONTINUE* *INSHA* *ALLAH*

*🀝 SDEENDTM DATA SERVICES🀝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦350
2GB = ₦600. 2GB = ₦700
3GB = ₦900. 3GB = ₦1000
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1300
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1600

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½
*πŸͺ€08066268951*


*ASMEETAH* *CE* ✍️✍️✍️


*FREE* *BOOK*

πŸ… *MATAR* *DAMUSA* πŸ…
(the wife of tiger)

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* ✍️✍️

The writers of...

1️⃣ Ikram ko Kausar.
2️⃣ Rayuwar Siyama.
3️⃣ Baby Ogah.
4️⃣ Yayana Zan Aura.
At now
5️⃣ *MATAR* *DAMUSA*


*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alΖ™alaminmu Ζ΄ancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

πŸ’«πŸ’« *{{N W A}}* πŸ’«πŸ’«


بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ Ψ§Ω„Ψ±Ω‘ΩŽΨ­Ω’Ω…ΩŽΩ†Ω Ψ§Ω„Ψ±Ω‘ΩŽΨ­ΩΩŠΩ’Ω…

*BOOK* *ONE*
*PAGE* 25 to 26.

Tsaki yaja ya nufi yanda jerin kayan baccin sa yake ko sauraronta baiyi ba, haka yake taku tsindir ba kaya a jikinsa ga towel kuma a yashe a 'kasa, Riga da wando ya zaro marasa nauyi sleeping dress milk colour ya sanya su a jikinsa ba 'karamin kyau kayan sukayi masa ba, sai hasken sa ya Kara bayyana!
Ya feffeshe jikinsa da turare mai sanyaya zuciya, yana kammalawa ya nufi hanyar fita zai dubo mommyn sa kamar wanda aka dakatar da shi ya tsaya cak sannan ya dubi clock dake manne a jikin bango 3:30 fasa fita yayi a bayyanai yace "nasan kinyi bacci yanzu, rest in peace my Mom" juyawa yayi ya nufi gurin bed d'insa yabi ta gefen Ayush ya kwanta, jawota yayi close him ya kashe light d'in d'akin sannan yaja musu mayafi rungumarta yayi suna fuskantar juna, da haka har bacci yayi awun gaba da shi! Itama Ayush daga suma ta wuce da yin bacci,
Asubar fari anata 'kiraye- kirayen sallah dai dain lokacin wayar Junaid ya hau ringing
Juye-juye Ayush ta Fara yi tana mur'tsika ido tana 'ko'karin bud'e idonta taji an 'kan'kameta juyar da kanta tayi tana fuskantar Junaid Wanda numfashin su yake gaurayuwa, a firgice ta zaro ido waje ga tsananin tsoro da ya bayyana akan fuskar ta, a hankali take janye jikin ta daga nasa har ta samu ta zame kanta tana maida numfashi tare da dafe kan kirjinta tana kallon kyakykyawar fuskarsa shi kuwa sai sharar baccin sa yake lokaci guda tasau murmushi har saida dimple d'inta ya bayyano, haka kawai take jin nutsuwa a tattare da ita..
Wayarsa ce ta sake ringing

Please Login or Register in order to submit comment