Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga cikin matasan cann.."

hawaye yana zubo wa Mommy tace "Malam idan banyi hakuri ba ya zanyi, ban isa na dawo masa da ransa ba, saboda haka hakuri ya zama dole......"
Mommy bata ƙarasa maganar ba suka jiyo ihun Ayush na lokaci guda,
da sauri Mommy ta miƙe ta fice daga ɗakin,
Malam shima bin bayanta yayi yana faɗin "subhanallah me kuma du ya faru.."

Ɗakin Ayush suka shige suna duba ta ganin babu kowa a bedroom Mommy tace "Ina take kuma, ina tsoron kar a kuma rasa rai a cikin gidan nan, mutuwar Junaid ma kaɗai ya isheni.." tana ƙarisa maganar tana kuka sosai,
Malam yace "to ko tana cikin toilet ne ki dubo ta,
Shi dai malam tsoronsa kar Ayush ta cire wannan zoben tinda Junaid ya riga da ya mutu, kar itama ta rasa tata rayuwar..

Bayan Mommy ta shige cikin toilet abunda ta gani ne ya tayar mata da hankali, ta dafa ƙirji tace "nashiga uku, innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Malammm!!!..."

shima da sauri ya shige cikin toilet ganin Ayush kwance a ƙasan tiles ko motsi babu ga kuma jini ta ko ina,
jini ne yake ɓulɓulowa daga cikin cibiyar ta duk ya wanke cikin toilet gaba ɗaya, itama tana kwance cikin jinin tayi jarab da jinin,
hannun Mommy ne yake kakkarwa kamar wacce aka jona wa shocking,
Malam ne ya ɗago ta yana faɗin "mu hanzarta hospital jinin jikinta zai ƙare fa, ɗaukar luɗa yayi mata sannan yayi waje da ita, itama Mommy bin bayansa tayi duk tabi ta ruɗe da haka suka isa harabar gidan suka shige motor gaba ɗayansu, miƙar hanyar da zai sadasu da gate yayi da gudun gaske,
har zasu fita Malam ya sanar da mai gadi cewar kar ya bar kowa ya shugo gidan nan, Baba mai gadi ya amsa masa da toh.."

---------------------> Isar su cikin hospital kenam, likitoci da nurses suka nufi yanda Malam yake ɗauke da Ayush, kwantar da ita akayi akan gadon nan na turawa kai tsaye emergency room aka kaita,
Mommy Office ɗinta ta nufa ta zauna akan kujera ta kifar da kanta saman table tana rera kuka mai cin rai...

*******

Daƙiƙa 5 tana cika Ayush ta finci zoben Dish da ƙarfin gaske cikin zafin nama,
Junaid yana zaune acan sahara shi da Damusar sa suna jiran cikar wahadi, yana lissafin lokaci har sai da yazo kan na biyar kuma na ƙarshe yaga wani haske mai ƙulƙule ya taho kamar walƙiya ya shige jikinsa hasken yabi ta hannunsa ya ratsa jikin Damusar dake hannunsa yana kan Damusa Sujjur,
wani irin baƙin hayaƙi ne yake fita daga jikinsu, har saida wannan hayaƙin ya gama fice wa sannan aka ɓatar dasu, ruhinan ko wannen su ya koma kan gangan jikinsa...


******

Sarki Raamud ne ya tashi yana shirin barin wajen da gawar Damusa yake, har ya bar falon fadar,
Kamar wanda aka zaburi Damusa da ƙarfin gaske ya miƙe tsaye yana karkaɗa gashin jikinsa,
a tsorace Bara'at dake gurin ta ƙwalla ƙiran sarki "Shugabaaa...."

Jin wannan ƙiran yasa ya taho da gudu a tunaninsa MUNAFURR ne ya dawo, ganin Damusa a miƙe ya tashi yasa sarki ya nufi gurinsa da gudu yana faɗin "Sujjurr! Sujjur ka tashi nagode Allah, zunzurutun farin ciki ne kwance saman fuskarsa, yana shafar bayan Damusar,

Ji yayi ya shiga cikin wani irin yanayi da sauri yaja da baya yana faɗin "zoben dish, Ɓingel ta cire.." ya kalli Bara'at yana murmushi, ya kuma cewa "ita ta taimake su, ita ta ceci rayuwarsu, amma kuma ita tana cikin mawuyanci hali..."
kafin ya rufe baki wani baƙin hayaƙi ne shima yake fita daga jikinsa, raɗaɗin da yake ji kamar ƙunar wuta,
ya ƙanƙame jikinsa da hannayensa biyu yana fitar da numfashi sama-sama, ga jijiyoyin jikinsa sunyi burtsi-burtsi shi kaɗai ne yasan irin ƙunar da yake ji a jikinsa,
wannan hayaƙin duk tsafin da yake jikinsa ne yake ta fita..
har shima Damusan yanzu babu wani tsafi a jikinsa,
Sarki Raamud yana cikin wannan halin har hayaƙin nan ya fita gaba ɗaya, yana maida numfashi ya ɗago yana kallon Bara'at wacce ta zuba masa ido tana kallon abun mamaki, ya soma girgiza kai yace "yanzu babu wani abun tsafi da ya ragu a jikina, normal nake yanzu...""
Damusa ne yayi wani irin girgiza sai da wannan macijin da aka wurga masa ya faɗo ƙasi a mace, ...

******

Junaid yana ƙwance saman gado yasa hannu ya yaye mayafin da aka rufeshi da shi, ya tashi cikin hanzari hannun sa yana kan fuskarta sakamakon hasken da yayi masa yawa, daƙer ya buɗe kyawawan eyes ɗinsa fari sol, haske fatarsa ya ƙara fitowa, a hankali yake lumshe ido kamar mai jin bacci ya sauƙar da ƙafafuwansa ƙasan gado, yana miƙa tare da Hamdala ya tashi yana duban kansa,
abunda ya faru dashi ne yake dawo masa kwakwalwa abun yayi matuƙar bashi mamaki, ganin lokaci guda waraka tazo masa,
a hankali yake motsa sweet lips ɗinsa yana faɗin "Deams, mafarki nayi, taya hakan zata faru?..."

yanzu baya jin komai a jikinsa ga wani irin kyau daya ƙara, komai nashi ya canza, hatta sumar kansa yayi tsayi yazo masa kafaɗarsa ga yanda yayi baƙi sai sheƙi yake yi gwanin burgewa,
sajen nan ya kwanta asaman fuskar sa har zuwa gemunsa ya ƙara tsayi ga laushin bala'i baƙi ƙirin sai sheƙi shima yake,
ga ƙaramin baki kamar wanda aka ɗosana! maroon lips ɗinsa ya ƙara fito wa kamar wanda aka shafa maroon stick,
yayi fari sol ya fito asalin kalar iyayensa Bahindiyawa,
he look like his father and d same like sarki Raamud.....
Junaid an dawo masa da cikakkiyar lafiyarsa da kuma ƙirar ƙarfi, ya zama zankaɗeɗe dashi kamar wanda aka ƙara masa tsayi da kuma ƙirar ƙarfi....


*MASHA ALLAH*

*A SAMU A FARA PAYMENT FAH SABODA AN KUSAN GAMA BOOK 1 FREE*


*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*
*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*

typing📲

🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)

*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)


*WhatsApp me 09065443871*

*Laifin Daɗi qarewa*

*FREE BOOK ZAI ƘARE NE A ƘARSHEN BOOK ONE*

*BOOK TWO DAZAN SHIGA SOON PAID NE,*
*YANA TAFE DA SABON SALO, DA KUMA CAKWALKWALIN CAKWAKIYA, KADA KU BARI A BAKU LABARI DOMIN GANI DA IDO 👀 YAFI JII👉👂*

*MATAR DAMUSAA BOOK 2 PAY ONLY 150👌👇👇👇*

*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*9065443871, OPAY BANK.*

*OR*

*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*2267236949, ZENITH BANK*

*SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER*
👇👇👇
*09065443871*

https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________



💫💫 *{{N W A}}* 💫💫


بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK ONE*
🅿️ ------->83 & 84 <-------


Ayush tana ƙwance rai a hannun Allah, dole sai anyi mata aiki a cikin cibiyarta sakamakon fincikar zoben da tayi da ƙarfin gaske hakan ya jawo mata tsinkewar jijiyar cibiya, wanda Allah ne kaɗai zai iya tasar kafaɗunta, likitoci ne zagaye a kanta kowa da kalar maganin da yake mata,
wasu sunyi mata operation suna mata aiki a ciki, wasu kuma suna ƙoƙarin ɗaura mata ledar jini saboda ba ƙaramin jini ta zubar ba,
kwana sukayi akan Ayush suna aikin ceton rai...

da sassafe misalin ƙarfe 6 Malam ya shugo Office ɗin Mommy yana ƙiran ta cikin damuwa tareda faɗin "mun bar Gawar Junaid ya kwana ko waiwaya shi ba'ayi ba, yanzu haka ina tunanin ya sanƙare tin jiya da rana.."

Mommy ce ta ɗago hankali a tashe tace "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, hankali na baya jikina wallahi na manta.."
Shima Malam cewa yayi "wallahi kuwa nima ina gida Junaid ya faɗo mun a rai, bansa a raina ya mutu ba,
amma na ƙira malaman da zasu masa wanka wata ƙila mu tarar dasu a gidan.."
da sauri suka shige motar suka fice daga cikin hospital,
A ƙofar gidan suka samu mutane har an taru ga malaman da suke jira suma, har da Doctor Hasheem shima ya samu labarin mutuwar Junaid a gurin Malam, Baba maigadi ne ya buɗe musu ƙofa yana shaftar kuka domin mutuwar Junaid ba ƙaramin girgiza mutane yayi ba,
su Mommy suna shiga cikin gidan saiga jiniyar motar sojoji har guda 10 suma labari ya riske su,

iya waɗanda zasu je ɗakin Junaid sune daga Malam Lawan sai Doctor Hasheem sai kuma wasu malamai su 2 da kuma wasu sojoji suma su biyu haka suka haura upstairs suka nufi ɗakin Junaid, ita kuwa Mommy a falo ta zauna tana sake rera sabon kuka..

shigarsu ɗaki suka tarar da Junaid ƙwance ya kalli sama tareda jan mayafi ya rufe kansa kamar dai yanda aka barshi, sai dai shi a yanzu bacci yake,

Bayan tashin shi ya shiga toilet ya yi wanka ya canza kaya yayi sallah sannan ya sauƙa down stairs ya nufi kitchen cikin sa'a kuwa ya samu abun taɓawa, yaci abinci yayi nakk ya kora da ruwan sanyi, ya kwanta akan sofa har bacci ya ɗauke shi, a falon ya kwana sai da asuba ne ya tashi ya koma room ɗinsa ya ɗauro alwala sannan ya tsayar da sallar asuba, daga nan ne ya haura bed ɗinsa ya lulluɓe kansa da mayafi sakamakon sanyin da akeyi..

kowa da ƙwalla a fuskarsa haka aka yaye masa mayafi za'a ɗauke shi akai shi toilet, wasu suka riƙe hannayensa wasu kuma ƙafafu akayi sama dashi,

a firgice Junaid ya buɗe idonsa yayi wani irin murɗewa ya miƙe tsaye yana faɗin "lafiya kuwa, suwaye kuu.."

Ai kuwa suka ce ƙafa mai naci ban baki ba kowa ta kansa yake, a ɗari suka bar ɗakin ko tsaya sauraronsa basu yi ba, sai gariyar malamai kake gani suna furawa, rawaninsu kuwa duk sun jejjefar a gurin,
suna fita ƙofar gida da gudu sauran mutanen ma suka feffece duk da basu san meya faruba,
toh fah 🤔 sojojin ma anan suka bar motocinsu, iya Mommy kawai aka bari tana zaune kan kujerar falo ta ƙafe guri ɗaya gaba ɗaya ta rasa ƙarfin jikinta ko motsi ta kasa yi...

Junaid ganin haka abun ya bashi mamaki yana maganar zuci "wai meke faruwa ne naga waɗannan mutane haka akaina? kodai akwai abunda ya faru dani ne?..." yana cikin wannan tunanin idonsa ya sauƙa akan likkafani a cikin leda, yasa hannu ya ɗauka tareda cire wa still turare ya sake gani kuma a jikin turaren ga photon gawa a kwance, Junaid ido ya zaro waje tareda faɗin "kenam a matacce suke ɗaukata?"
hankalinsa ne ya koma kan bedsheet ɗin gadonsa yaga duk jini ya ɓata gadon, tin jiya bai lura da shi ba,
ɗaga hannayensa yayi sama yana duban kansa yana kuma cewa "nifa naga lafiyata klau, bana jin komai a jikina.."

ficewa yayi daga ɗakin ya sauƙa down da saurinsa, ganin Mommy yayi a zaune ko motsi babu sai idonta da suka ƙafe alamun dai kamar suma tayi, da gudu ya nufi frig ya ɗauko cool water a jerkan ya since murfin sannan ya fara watsa mata a fuska,
farfaɗowa tayi tana jan numfashi sama-sama, idanuwanta ne suka sauƙa akan fuskar Junaid yana ƙiran sunanta "Mommy! Mommy!! Mommy wake up mana, open your eyes please"
gani yayi ta ƙara sumewa tayi baya yayi saurin tarota yana cigaba da ƙiran sunanta amma shuru,
ruwan goran ya sake watsa mata, a ruɗe ta tashi tana faɗin "taimako jama'a fatalwa, taimakoo..."
ido ta sake haɗawa da shi kuma du sai luuuuu ta ƙara sumewa a karo na uku kenam, ruwa ya sake watsa mata ta farfaɗo ido a rumshe, Junaid ne yakai hannunsa saitin gefen fuskarta, yana faɗin "Mom yau nine kike suma a kaina? Meyake faruwa ne?.."
itama hannu takai saitin fuskarsa tana ambaton "Junaiddd! Junaid kaine? daman baka mutu ba, bakada lafiya to amma ya akayi yanzu ka dawo kana tafiya, ɗaga hannu sama tayi tana hamdala, Allah na gode maka! Yaa Allah lokaci guda ka tayar mun da yarona, Alhamdulillah Addu'a ta ta karɓu, ta ƙarasa maganar tareda rungumarsa tana kukan farin ciki,
ɗagowa yayi yana faɗin "Mom where is my Yushert...?
Mommy tana kuka tace "Ayush tana kwance a gadon asibiti.."

"what? Mom what happened to her?..."
Mommy kasa magana tayi sai kukan da yaci ranta,
"Don't worry Mom, it's okay bari naje na gano ta.."
Momy ce tayi saurin riƙe hannunsa tace "karka fita yanzu kowa yasan ka mutu.."
"Please Mommy ki barni naje naga Yushert ɗina, bazan iya juran rashin ganinta ba.."
ya fizgi hannunsa sannan ya haura upstairs da gudu, ya nufi room ɗinsa, farar jallabiya kawai ya ɗora akan gajejen wandonsa ya ɗauki key ɗin mota, sannan ya sauƙo down stairs, bai tsaya duban ta kan mommy ba, kai tsaye motarsa ya nufa ya shige ciki da gudun gaske ya fice daga gidan
sai asibiti.....


*WALLAHI BACCI NAKE JI SOSAI SHIYASA NA BAR MUKU IYA WANNAN PAGE, KU BIYONI BASHI NETX PAGE ZANYI TYPING MAI TSAYI*


*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*
*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*

typing📲

🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)

*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)


*WhatsApp me 09065443871*

*Laifin Daɗi qarewa*

*FREE BOOK ZAI ƘARE NE A ƘARSHEN BOOK ONE*

*BOOK TWO DAZAN SHIGA SOON PAID NE,*
*YANA TAFE DA SABON SALO, DA KUMA CAKWALKWALIN CAKWAKIYA, KADA KU BARI A BAKU LABARI DOMIN GANI DA IDO 👀 YAFI JII👉👂*

*MATAR DAMUSAA BOOK 2 PAY ONLY 150👌👇👇👇*

*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*9065443871, OPAY BANK.*

*OR*

*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*2267236949, ZENITH BANK*

*SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER*
👇👇👇
*09065443871*

https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________



💫💫 *{{N W A}}* 💫💫


بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK ONE*
🅿️ ------->85 & 86 <-------

Parking yayi a harabar asibity da ƙarfin gaske yasa ƙafa ya ture murfin motar, ya nufi cikin asibitin da gudu yana ƙwalla ƙiran "Yushert! Yushert!!."
ya cakumi gaban rigar wani Doctor yana faɗin "tana ina? kada ku sanar mun cewa ta mutu" ganin Doctor ya ƙafe guri ɗaya ko motsi babu ga ya tsayar da

Please Login or Register in order to submit comment