Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a Karo na biyu, idonta na kan wayar batada niyar picking har sai da ya kusan katsewa sannan takai hannun ta kan wayar, Doctor Hasheem taga an rubuta picking tayi ta Kara akan kunnen ta tana sauraron Wanda ya Kira "Hello Captain Junaid, mahaifiyarka tana cikin mawuyancin hali sunanka kawai take ta ambato, please kazo yanzu har saita ganka kafin mu iya magance matsalar ta....! Shuru yaji anyi ba amsa, ya sake cewa "Hello Captain Junaid kana jina kuwa...?" Katse wayar Ayush tayi ba tare da ta amsa masa ba, wani irin kuka ne mai cin rai yazo mata, tana cikin kukan taji wani 'kiran ya sake shugowa wayar da sauri ta katse 'kiran tayi switch up d'in wayar gaba d'aya ba tareda tasan Ina ta danna ba domin Ayush ko keypad bata iyaba balle wannan 'katuwar waya 'kirar iPhone 11. Bud'e wardrobe tayi ta tusa wayar cikin kayansa ta katse wayar ne saboda kar ya Kai mata naushi kumadu, tayi waje da gudu tana toshe bakinta da hannayenta kuka ne yaso ku6uce mata....
Bedroom d'insu ta nufa tana shiga ciki ta doku a saman gado, lokaci guda ta fashe da kuka tana fad'in "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, mahaifiyata ta tafi ta barni itama wacce take kula dani tana kwance rai a hannun Allah, Allah ka taimake ni ka bawa Auntyna lafiya, idan ta mutu bansan Ina zan sa kaina ba, wayyo niii"...
Bayan ta gama kukanta mai isanta ta tashi ta shige toilet jiki ba 'kwari Alwala tayi sannan ta tsayar da sallah tare da lafulfuli, Addu'o'i ta shiga karantowa tayi Addu'a a mahaifiyarta tare da nema mata gafarar ubangiji sannan tayiwa momin Junaid Addu'ar nema mata lafiya...

Junaid yana kwance yanaji har an shiga sallah yanaso ya tashi yayi sallah amma dai dai lokacin aka shagaltar dashi da wani mafarki mai ban tsoro da kuma firgici....!
Gashi a cikin tsakiyar ruwan da bashi da iyaka, crocodiles ne sun kai goma suka nufo shi a cikin ruwan nan, yanata gudu a cikin ruwan ya kasa isowa karshen ruwan su kuwa sunyi daf dashi suna bud'e manya-manyan bakinan su, wani 'karamin jirgin ruwane yazo ya tsaya ta gabanshi sai dai jirgin ya d'anyi nesa da shi wata kyakykyawar Yarinya ce mai sanye da fararen kaya dogi da suman gashin ta har gadon bayanta yarinyar farace soll ta ware hannayenta biyu tana fad'in "Junaid taho, kazo gareni don ka tsira da rayuwarka...."
Tsayawa yayi cakk a cikin ruwan yana kallon kyakykyawar yarinyar dake masa magana, zazza'kar muryarta ne ya sake dukan dodon kunnensa "JUNAIDDDDD ka kula bayanka" kafin ya ankara har sun kawo masa hari, "JUNAIIDD ga wannan, ta cillo masa wata doguwar tokobi mai she'ki irinta sarakuna.
Hannunsa yakai ya cafko wu'kar kafin yakai musu sara har sun rufa mishi 'kasin ruwa suka lumar da shi.
"Junaaiidddd" yarinyar ce ta kwalla mishi 'Kira sannan ta ce "karka bari suyi Nasara akan ka, ka zamo jarumi na gaske, kayi ya'ki dasu kamar yanda kake a filin dagaaa...... Bata 'karisa maganar ba taga jini duk ya malale ruwan, fashewa tayi da kuka tana fad'in "why! Why!! Why!!! Meyasa zaka bar ma'kiya suyi Nasara akan ka Junaiid.."
Ji tayi an ri'ke jirgin da sauri ta le'ka 'kasin ruwan
Junaid ta gani ya d'ago da kansa duk ruwa ta ko Ina a jikinsa, kallon juna suka tsayayi murmushi yasau mata itama ta mayar masa da martani
Mi'ka mata hannu yayi ta ri'ko shi d'aya hannun kuma yana ri'ke da takobin nan ya haura cikin jirgin still bai daina kallonta ba itama idonta akansa
Daga bisani ya soma motsa lips d'insa zaiyi magana tayi saurin katse shi ta d'ora yatsanta akan lips d'inta "Shhhhhhh ๐Ÿคซ๐Ÿคซ you wanted to ask me who I'm again...?"
Abun ya d'aure mishi Kai a ransa yace "wace ce wannan" kamar tasan abunda zai tambayeta kenam!
Murmushi tayi ta kanne masa ido d'aya 6atttt ta 6ace masa, a firgice ya mi'ke tsaye yana waiwaye baiga kowa ba....
Firgitt ya tashi daga baccin da yake duk gumi ya wanke masa jiki duk da A.C dake d'akin
Yana furta "Laa'ilaha ilalla, Muhammadu rasulullah S.A.W"
Agogo ya kalla 8:30 waro ido waje yayi "A'Uzubillahi Mina shaid'anin rajin, sallar Asuba has already pass" a gaggauce ya tashi ya shige toilet yayo alwala ya tsayar da sallah...........

Mommy kuwa tana kwance a gadon asibiti tana 'kiran sunan Junaid har numfashin ta ya d'age cak oxygen aka sanya mata domin da sauran bugun zuciyar,
Likitoci sunyi ta 'kiran wayar Junaid switch up daga farko ya shiga amma daga karshe kuma switch, bodyguards kuwa suna kawo mommy hospital suka fece Junaid yafi karfinsu zai iya hallaka su wata Rana.
Doctor Hasheem har gidan yaje dubo Junaid saidai an'ki bud'e gate, shima mai gadi yana kwance zazza6i mai zafi ya rufeshi ko kwakkwarar motsi baya iya yi, hakan yasa Doctor Hasheem juyawa yayi tunanin babu kowa a gidan, shima kanshi ya shiga damuwa ganin Doctor Fateemah a wannan halin
Yana tu'kin motor yana nazarin "shin meya faru da Junaid? Kodai ciwon shi ne ya tashi a wani gurin! Amma Ai Doctor Fatima bata shiga irin wannan tashin hankalin akan ciwon Junaid saboda ta Saba dashi tin yana yaro..."
Haka ya ringa tunani har ya shiga cikin hospital.
Wata Nurse ce ta nufi gurin da Doctor ya parker motorsa tana fad'in "Doctor baka samu Junaid bane? Zata iya rasa rayuwar ta indai bata sa Junaid a Idonta ba, bugun zuciyarta ya Fara low! Doctor please we should help her.."

Junaid bayan ya idar da sallar baccinsa ya cigaba da yi
Allah sarki duk a tunaninsa momminsa na a cikin gidan....

Itama Ayush bacci ne yayi awun gaba da ita domin jiya bata samu isashshen bacci ba, duk ta mance da wayar da tayi da Doctor akan Ana neman Junaid, amma tasan mommi tana asibiti sai datayi mata Addu'a kafin bacci ya d'auketa.........



*๐Ÿค SDEENDTM DATA SERVICES๐Ÿค*
*MTN* . *Airtel*
1GB = โ‚ฆ300. 1GB = โ‚ฆ350
2GB = โ‚ฆ600. 2GB = โ‚ฆ700
3GB = โ‚ฆ900. 3GB = โ‚ฆ1000
4GB = โ‚ฆ1200. 4GB = โ‚ฆ1300
5GB = โ‚ฆ1500. 5GB = โ‚ฆ1600

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = โ‚ฆ350. 500Mb โ‚ฆ250
2GB = โ‚ฆ700. 1GB โ‚ฆ500
3GB = โ‚ฆ1050. 2GB โ‚ฆ1000
4GB = โ‚ฆ1400. 3GB โ‚ฆ1500
5GB = โ‚ฆ1750. 4GB โ‚ฆ2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ
*๐Ÿช€08066268951*



*ASMEETAH* *CE* โœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธ

*FREE* *BOOK*

๐Ÿ… *MATAR* *DAMUSA* ๐Ÿ…
(the wife of tiger)

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* โœ๏ธโœ๏ธ


*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦ™alaminmu ฦดancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ *{{N W A}}* ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ


ุจูุณู’ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู…ู ุงู„ู„ู‘ู‡ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญู’ู…ูŽู†ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญููŠู’ู…

*BOOK* *ONE*
*PAGE* โžก๏ธ27 & 28.


Around 12:50 Junaid ya tashi daga baccin da ya kwashe shi tin sallar asuba, tashi yayi a kasalance yana duban agogon dake manne a jikin bango, yana jan 'kafa ya nufi toilet brush yayi sannan ya had'a ruwan wanka mai 'Dumi-d'umi ya yi wanka cikin kulawa after 30minute ya fito d'aure da white towel, tsayawa yayi a jikin mirrow kafin ya fara shafa cream d'insa mai shegen 'kamshi ta ko'ina ya milmilka ya d'auki turare mai jikin Silva ga 'kamshi kamar mai! Yana fesa jikinsa duk gidan sai da ya gauraya da wannan 'kamshin turare (ma'abocin son 'kamshi kenam) bayan ya gama da wannan ya d'auki kum yana taje suman kayin sa ya d'auki cream na gyaran gashi ya soma mulmulkawa daga suman gashin har zuwa sajen har d'an gemun daya bari shima yana bada nashi 'kamshin, lips oil kumadu ya d'auko mai 'kamshin chaculate ya mulka a saman maroon lips d'insa, nan fa lips d'in ya fara bada armashi yana she'ki (wal-wall) ๐Ÿ˜˜ jikin wardrobe d'insa ya nufa ya bud'e 6angaren Jeans da kuma T-shirts kala-kala sai da ya tsaya tunanin kayan da zai saka kafin ya kai hannu ya zaro wani dan'kararren Jeans skie blue sannan ya duba wata T-shirt wanda ya kasance shine mahad'insa mai zanen blue and white mai dogon hannun leaps, ya sanya kayan nan ga rigar ta kama jikinsa kayan tsaf sun kama jikinsa sosai gwanin sha'awa ya dubi takalmi white colour shima mai sawun ciki, gaskiya Yaron ya fito kamar kamar dai Indian man awesome, turare ya d'auka ya feffeshe kayan jikinsa da shi, ya kammala tsaff ya duba kan table zai d'auki phone d'insa wayam babu alamar sa saman bed d'insa yakai idonsa still ba waya ga gadon nan yayi kaca-kaca ba gyara daman Mom d'insa ce mai masa gyaran d'aki, tsayawa yayi yana nazarin wani abu kafin ya nufi hanyar fita a hankali yake taka stairs a falo ya tarar da Ayush zaune ta kafa ido akan TV star bata san da zuwan sa ba sai ji tayi ance "where's my Mom?" atakaice ya yi maganar da sauri Ayush ta mi'ke tsaye tana fad'in "gud morning Sir" d'aga mata kai kawai yayi ya wuce ta gefen ta ya nufi d'akin Mom d'insa Ayush ce ta yi saurin tsayar da shi tana fad'in "am she went hospital" dakatawa yayi da tafiyar cike da mamaki yake furta "hospital? but Mom bata ta6a tafiya batare da tamun sallama ba, ko Ina bacci takan ajiye 'karamin letter!" Kuma kafin ta tafi tana kai masa kayan breakfast..
Duk acikin ransa yake wannan jawabai, juyowa yayi yana facing d'inta ido ya 'kura mata har sai da taji wani iri aranta sunkuyar da kai tayi 'kasi, a hankali ya furta "tin yaushe ta fice" a d'an tsorace tace "in midnight"
Jinjina Kai ya yi yace "OK night duty"
Ya maida kallonsa kanta still yace "my phone โœ†" kallonnsa tayi a d'an rud'e tace "inside wardrobe" atakaice ta bada amsa
Jinjina kai yayi zai haura upstairs dakatawa yayi ya juyo yana kallonta yace "ke ce yarinyar da Mom ta kawo?" Amsawa tayi da "eh ni ce" Kai a sunkuye,
"OK je ki nemo mun abunda zanci am hungry"
Zaro ido tayi waje zuciyarta kuwa yana bugun uku3 tara9 ya had'ata da babban aiki domin tinda take bata ta6a shiga kitchen ba, ko natural tea bata iya had'awa ba balle azo ganjin girki
"Wayyo Allah na" abunda ta fad'a kenam acikin raanta, shi kuwa tin tinin ya haura upstairs ya wuce bedroom d'insa..
Jiki a sanyaye take tafiya ba kwari a haka ta shige kitchen, fuskar sa ne yake mata gizo domin ba'karamin kyau yayi ba, ga sajen nan ba'ki 'kirin fuskar kuwa tayi fiyau sai hasken sa ya 'Kara bayyana ga lips kuma sai she'ki yake, lokaci guda kuwa tasau kayataccen murmushi, sai dai kuma tana mungun jin tsoronsa ga kuma shakkarsa da takeji kwarjini yake mata ita har yanzu a Aljani take d'aukarsa bata yadda cewa mutum bane, tana cikin tunaninta ta dawo hayyacinta gata ga gass anan ta shiga taitayinta ko kunnawa bata iya ba! Tunanin mai zata dafa ta shiga yi kawai ta yanke hukuncin tayi indomie kawai
Murd'a gass tayi har sai da tayi highly d'isa sannan ta kunna ashana wani irin bond yayi wuta ne yake tashi da gudu taja da baya bata San yanda zatayi ta rage karfin wutar ba haka ta d'auko tower ta d'ora ta tsiyaya mangyad'a too much wutar nan haka yake shiga cikin tukunyar tsabar yawan da wutar yayi ga kuma ta zabga granut oil ta d'ebo ruwa cikin cup sau uku tana zubawa cikin tukunyar da 6are ledar indomie ta juye shima guda uku ta fasa eggs guda goma a cikin indomie d'in sannan ta Fara zuba Maggi da kayan had'in a ciki kafin ta kammala zuba Maggi har ruwan ya tsotse ya Fara 'kona abincin ga eggs kuma a kwance saman indomie gasu Aunty Maggi kuma a saman eggs ko gaurayawa ba'ayi ba.
Ya salam kamar 'kauri na soma ji kafin ta Ankara indomie kam ya 'kone ga wutar gass kamar Wanda ake rura shi sai bin jikin tukunyar yake Ayush fa anaso a sau'ke pot kuma abu ya gagara ga jikin gass d'in kuma yad'au zafi sosai (ke Ayush kar fa kiyi musu gobara ๐Ÿ˜ณ )
Tsayawa tayi cak tana kallon tukunyar da abun cikin yake ta 'konewa qauri ne ya gauraye gidan.
Jin motsin mutum a bayanta ne yasa ta waiwaya da sauri cike da tsoro da fargaba take bin Junaid da kallo Wanda shima 'kaurin da ya jiyo ne yasa shi fitowa
Hannu yakai ya kashe gas d'in duk da yaji zafin wutar haka ya jure bai nuna ba
Ya sau'ke tukunyar da yayi ba'ki 'kirin hannunsa har yayi jawur tsabar 'Kunar wutar, ga kuma indomie fa shima yayi ba'ki 'kirin gwanin ban kwad'ayi ๐Ÿ˜‹๐Ÿ˜‹
Juyowa yayi yana kallon ta da sauri ta sunkuyar da Kai 'kasi.
Juyawa yayi yakai hannu kan wata flass mai ruwan tea a ciki ya tsiyayi ruwan a jug ya had'a tea mai kaurin gaske ga yasha madara sai dai suger kad'an yasa saboda baya son suger sosai ya d'auki bread mai yanka-yanka rufaida bread dai,
Yayi had'insa a sau'ka'ke ya mi'kawa Ayush cup na tea da kuma bread shima ya d'auki nashi ya fice daga kitchen upstairs ya haura sai bedroom d'insa
Itama fitowa tayi ta zauna a kujerar falo da murmushi a fuskarta "wow godiya nake daman yunwa nima nake jii" Ayush ce tayi maganar tana d'an Kora tea tare da bread kunnenta har rawa yake tsabar had'in da yasha..

Shima ata 6angarensa yana cikin karyawa yayi dialing call number Mom d'insa amma sai dai switch up yayi tunanin idan ya kammala break zai samota a hospital domin bazai iya wuni baiga Mom d'insa ba abun alfaharin sa, yana cikin wannan tunanin yaji sau'kar message a wayarsa Wanda daman yana hannunsa bud'e sa'kon yayi (( *captain* *junaid* *sorry* *for* *your* *loss* *doctor* *fateemah* *she's* *die,* *idan* *ka* *tuna* *da* *mahaifiyarka* *tana* *hospital* *kazo* *ka* *dauki* *gawarta* ))

Da sauri Junaid ya mi'ke tsaye yayi wurgi da wayarsa yana fad'in "whatttt my Mom, impossible" kafin kace mai gumi ya wanke masa ilahirin jikinsa da gudun gaske ya sau'ka falo ya wuce sai da Ayush ta tsorita kofin shayin ya zuba mata a cinya 'Kara tayi jin zafin ruwan shayin a jikinta ..

Shi kuwa Junaid har ya fizgi motarsa ya nufi hanyar get da gudun gaske!
Shi da kansa ya sau'ka a motar ya bud'e get d'in bai tsaya sauraron mai gadi ba
Fincikar motar yayi sai tafiya hospital ga gida a wangame bai tsaya rufe get d'in ba.........

Ga kuma mai gadi a cikin d'akinsa rai a hannun Allah, ya tsorita da ganin junaid a cikin Daren nan ga kuma jefo masa manya-manyan gardawa akai har su biyu, Allah sarki dattijon Allah.........




*๐Ÿค SDEENDTM DATA SERVICES๐Ÿค*
*MTN* . *Airtel*
1GB = โ‚ฆ300. 1GB = โ‚ฆ350
2GB = โ‚ฆ600. 2GB = โ‚ฆ700
3GB = โ‚ฆ900. 3GB = โ‚ฆ1000
4GB = โ‚ฆ1200. 4GB = โ‚ฆ1300
5GB = โ‚ฆ1500. 5GB = โ‚ฆ1600

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = โ‚ฆ350. 500Mb โ‚ฆ250
2GB = โ‚ฆ700. 1GB โ‚ฆ500
3GB = โ‚ฆ1050. 2GB โ‚ฆ1000
4GB = โ‚ฆ1400. 3GB โ‚ฆ1500
5GB = โ‚ฆ1750. 4GB โ‚ฆ2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ
*๐Ÿช€08066268951*


*ASMEETAH* *CE* โœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธ


*FREE* *BOOK*

๐Ÿ… *MATAR* *DAMUSA* ๐Ÿ…
(the wife of tiger)

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* โœ๏ธโœ๏ธ


*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦ™alaminmu ฦดancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ *{{N W A}}* ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ


ุจูุณู’ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู…ู ุงู„ู„ู‘ู‡ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญู’ู…ูŽู†ู ุงู„ุฑู‘ูŽุญููŠู’ู…

*BOOK* *ONE*
*PAGE* โžก๏ธ29 & 30

________________Yana shiga cikin harabar asibitin ko tsayar da motar baiyi ba ya bud'e yayi cikin compound da gudun gaske duk ya fita hayyacinsa, sauran kad'an ya buge wata nurse yana duba d'akunan da aka kwantar Mom dinsa sukayi kici6us da Dr Hasheem
Kwalar rigar Dr ya ri'ke da hannu bibbiyu yana fad'in "where is my Mom, what happened to her?" yana magana ya na huci ya zazzaro ido waje...

"Look Junaid sau nawa kakeso na Kira akan batun mahaifiyarka?......... Dr. bai 'karisa maganar ba Junaid ya katse shi da cewa "am not felling well, I wanna see my Mom right now" murya a disashe yake magana kamar zaiyi kuka.

Dr. yace " it's okay, muje kaga mahaifiyarka" Dr. yayi gaba shima Junaid d'in ya bishi a baya kamar zaiyi tuntu6e suka shiga emergency room na alfarma har da plasman aciki ga wani 'karamin glass table a ta gefen gadon da Mom take kwance, anyi covered d'in baki da hanci da Oxygen ga ledar drink da aka d'aura mata, ido a rufe.....

Da gudu Junaid ya 'karisa gurinta yana fad'in "Mom don't leave a way please, meya faru da ke har haka bansani ba" kuka ne yaci ransa ya kifar da kansa a bakin gadon hannunsa ri'ke da nata.

Ji yayi an dafa kafad'arsa ya d'ago da rinanan idanuwansa yana kallon Dr. Hasheem wanda ya dafa shi!

"Am Sorry Junaid naso ace na sameka a waya na fahimtar da kai halin da mahaifiyarka take, amma sai dai na kira wayar since 3:00am anyi picking sai dana sanar maka rashin lafiyarta amma you didn't answer me daga 'karshe ka katse wayar, idan nayi call sai ayi rejected daga karshe akayi switch d'in wayar abun ya d'aure mun Kai matuka, har gidan naje amma ankasa bud'e get har na gaji nayi tafiyata!
Gata nan munyi iya 'ko'karin mu kuma Allah ya bamu nasarar ceton ranta, yanzu haka bacci take munyi mata allurar baccin tana bu'katar hutawa"

Duk maganganun da Dr. yake Junaid na sauraronsa ya jinjina kai yana maganar zuci "tabbas nayi mamakin

Please Login or Register in order to submit comment