Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kakkarwa tace wa Ayush "ki koma ciki kar yaji miki rauni Ayush, ki shiga cikin ɗakin ki rufe, ki barni zanji da shi.."

Junaid kuma tsayawa yayi yana fuskantar Ayush ya zuba mata raunannun idanuwansa sai gurnanin daya ƙaru, itama Ayush tsayawa tayi tana kallon sa ta kasa motsawa.
Mommy ce tayo kansa da igiya a hannun ta zata ɗaure shi, ta lallaɓo ta bayansa ta wurga masa igiyar ai kuwa ita da igiyar haka ya yi wurgi da su wani irin ƙara mommy tasau Allah yaso ta akan doguwar sofa ta faɗo abun yazo mata da sauƙi,
a razane Ayush tace "Mommyyy" tayo kanta da gudu ta ɗagota, cikin ƙirar ƙarfi Junaid ya yo kansu gadan-gadan zai kai musu hannu da gudu Ayush ta shige tsakiyar sa ta rungume shi sosai jikinta na kakkarwa, ta ƙanƙame idonta rub tana jiran ta yanda za'ayi wurgi da ita sai kuma abun mamaki wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sau yana numfashi sama-sama ya rufe idanuwan sa rubb, wani irin hajijiya ne ya ɗebe shi zai faɗi ƙasi Ayush ta rirriƙe shi sosai a hankali ta kaishi ƙasi ta kwantar da shi,
kanta ta kwantar saman ƙirjin sa, tana jin yanda zuciyar sa take harbawa da ƙarfi-ƙarfi da haka har zuciyar sa ta dawo normal, sai dai jikin sa ba ƙwari ya kasa motsa ɗan yatsar sa ma still idonsa a rufe...

Mommy sake baki tayi tana kallon ikon Allah, a ranta tana furta "wacece wannan yarinyar? daga ina take? anya kuwa mutum ce, a karo na uku kenam ina ganin yanda take ceton Junaid, Alhamdulillah Allah na gode maka daka kawo mana ɗauki ka kawo mana wacce zata magance mana matsala..."
Murmushi ne akan fuskarta ga haƙorin makkan ta kuwa ya yi matuƙar yi mata kyau,
a hankali take tafe tayo kan Ayush tace "Ayushert ki taso..."
"a'ah Mommy jikinsa da sauran zafi idan na raba jikin mu ciwon zai iya dawowa"

a hankali yake motsi da hannayen sa da ƙer ya iya ɗago hannun ya ɗora su akan gadon bayan Ayush, idonsa ya fara buɗewa a hankali yana kallon dishi-dishi har idon ya washe,
Idonsa ya washe sosai ya koma fari sol kamar ba shi bane idonsa ya koma green colour ba,
Lips ɗinsa yake motsawa a hankali ya furta "Yushert..."
itama ɗagowa tayi suna fuskantar juna ido cikin ido,
"are you okay?" ya furta hakan yana kallon ta! kaɗa masa kai kawai tayi tana ƙoƙarin miƙe wa, Mommy tayo kan Junaid tana tana cewa "my son kana lafiya, tashi maza sannu ko" ta kai hannun ta kansa ta tallafa masa ya tashi idonsa kuwa na kan Ayush wacce ta kawar da kanta gefe ga ido ya yi jawur daga ƙarshe kuwa ta juya da gudu ta koma cikin bedroom ɗin su,
soyayyar Junaid zai mata illah sai dai yaƙi amince wa da soyayyar ta, zuwa tayi ta kwanta a saman gado wani sabon kuka ne ya sake zuwa mata, a cikin ranta kuwa tana faɗin "dole na koya wa zuciya ta hakurin rashin Yaya Junaid, meye amfanin soyayyar da ba Aure? meye mafita? wani shawara zan ba wa zuciya ta?"
tana kwance tana raya abubuwa da dama a cikin ranta, can kamar wanda aka zabureta ta tashi tana faɗin "na samo mafita, yes! yes!! yes!!!, zan ƙaurace masa na wasu kwanaki shi da kansa zai nemeni, ni kuwa nace masa indai bai aure ni ba bazai ƙara gani na ba tinda naga yanzu inbai ganni ba baya jin daɗi"
tana cikin wannan tunanin saiga Mommy ta shugo idon ta akan Ayush tazo ta zauna kusa da ita, tace "Ayush nagode sosai da ceton Junaid daga halin da yake ciki, haƙiƙa ke ƴer baiwa ce, kuma ke kece maganin Junaid! zan so ki Aure shi Ayush kuma naga kin shaƙu da shi sosai, soyayyar ku ya yi zurfi" tayi ajiyar zuciya sannan ta dafa kafaɗar ta tace "kun dace da juna"
juyowa Ayush tayi tana kallon Mommy tana motsi da leɓen ta a hankali tace "Mommy Yayana Junaid baya sona, yace kada na sake masa maganar Aure.." ta ƙarasa maganar tana zubda ƙwalla, Mommy ta jin jina kanta ta ɗanyi jimm kaɗan kamar mai tunanin wani abu daga baya tace "baza su bar shi yayi Aure ba..."
Ayush ta juyo da sauri tana kallon Mommy baki na kakkarwa tace "su waye?.."
"Azzaluman da suka shiga rayuwarsa" Mommy ta faɗi hakan tana zubda kwalla...
"Amma inaso kimun wata alfarma!"
Ayush ta ɗago tana kallon Mom, tace "ina jinki Mommy"
Mommy ta kamo hannayeta biyu tana fuskantar ta tace "ki rinƙa yawan zama kusa da shi, kina shiga jikinsa kamar dai a yanda na ganku yau, insha Allahu a hankali komai zai dawo normal, ciwonsa kuma zaiyi ƙasa, inhar ya shiga jikin ki sosai zakiga kina masa zancen Aure zai amince.."
wani irin haɗiyar yawu Ayush tayi sannan tace "to Mommy amma kince zuwa gobe na fitar da wanda nake so acikin su biyu.."
"eh na gaya miki haka ne saboda Junaid, nasan yana matuƙar kishi da Dr, idan baki sani bama akan ki Junaid ya yi wa Hasheem duka, kada kisa damuwa a ranki kinji ko Doughter??"
kaɗa kai kawai Ayush tayi idonta akan Mommy.....

"to yanzu dai kije ki gyara masa ɗaki, zuwa dare kema zan kai ki ɗakin ki kibar mun ɗaki nima" ta ƙarisa maganar tana miƙewa tsaye tace "bari ni kuma naje kitchen na girka masa wani abincin baici komai ba.."

cikin sanɗa Ayush take taka upstairs, tana raya cewa shin a wani hali zata ga Junaid,
gabanta ne ya yi wani irin bugawa ganin ƙofar ɗakin a cire, ƙarasa shiga tayi tana bin ko ina da kallo yayi kaca-kaca da ɗakin ga mirrow ya dagargaza shi, katifar gadon anyi wulli dashi, ɗakin dai ya zamo kamar wanda akayi wasan dambe a ciki!
a razane ta kai idon ta kan Junaid yana tsaye ta gaban ta ya goya hannayensa kan chest ɗinsa, ya kafa mata eyes ko ƙibtawa baya yi..

Ayush a cikin ranta tace "na shiga uku taya zan fara gyara ɗakin nan, bazan iya ba gaskiya" tana cikin wannan tunanin taji anyi sallama ta bayanta juyawa tayi tana kallon wanda ya shugo, wani mutumi ne ya shugo yana faɗin "Ogah an kawo kayan furniture zamu fara aiki yanzu" Ok kawai yace ya riƙo hannun Ayush yace "muje za'a canza kayan ɗakin..."
har zasu fita ya waiwayo yana kallon ɗakin sirri ya tuna ya danna key a room ɗin, ba wanda yasan da gurin...

1hour
gaba ɗayansu suna zaune akan dinning table suna night lunch, ba wanda ya kula kowa
Ayush juya spoon kawai take yi bata jin cin abincin, sai Junaid kuma yana ci yana satar kallon Ayush, itama idan ta ɗago suka haɗa eyes sai ta sunkuyar da kai ƙasi,
Mommy duk ta lura da hakan, shiyasa tayi saurin kammala nata lunch ta tashi tabar musu gurin.
can itama Ayush ganin babu wanda ya kula kowa a cikinsu yasa ta tashi da sauri zata tafi
ya dakatar da ita yana faɗin "ina zaki je ?"
kallonsa tayi ta wutsiryar ido tace "kwanciya zanyi bacci nake ji.." "ok before jeki dubo mun ɗakina gyaran da akayi ya yi kyau"
turo baki tayi tana tafiya kamar bazata yi ba, da haka ta haura upstairs, shima daga baya ya biyo bayanta, zuwa yayi ya same ta tana tsaye ta zuba wa ɗakin ido,
ba ƙaramin haɗuwa ɗakin ya yi ba, ya tsaru sosai komai na ɗakin launin pinck ne!
Labulaye, carpet, bedroom, mirrow, wadrobe, duk launin pinck aka saka, hatta flowers ɗin da aka saka suma pinck sai sheƙi suke, launin hasken ɗakin kuwa shima light pinck sai wal-wall yake ga wani sanyi A.C mai shegen daɗi ga ratsa jiki....,
yana zuwa yakai hannun sa ya rungumota ta baya yana faɗin ɗakin yayi miki kyau ne? ko kuma a sauya launin ɗakin?"
Jin tayi shuru bata ce komai ba yasa ya leƙa fuskar ta yaga ashe gyangyaɗi take a tsaye, jin ta akan faffaɗar ƙirjinsa yasa doguwar bacci ya ɗauke ta ga sanyin da yake ratsata....
murmushi yasau ya cicciɓe ta ya fice da ita direct ɗakin Mommy ya kaita ya kwantar da ita, akayi sa'a kuwa Mommy itama tayi bacci! ya rufe musu ƙofar ɗakin....

shigar room ɗinsa toilet ya shiga ya watsa ruwa yayi shigar sleeping dreesing ya kwanta shima tare da jero addu'o'i....

*WASHE GARI*

******
Lailah kenam ana zaune a bakin gado tasa photon Junaid a gaba wanda ta sato a gurin Mommy tana ta kalla tana murmushi "Oga Junaid ina matuƙar ƙaunar ka, bana kula kowa saboda kai, meyasa nima bazaka so ni ba? zan juri duk wani wulaƙancin da zaka mun, zan kuma Aure ka a halin da kake ciki na rashin lafiya! kaiɗin na daban ne a cikin maza, zuwa gobe zanje na saka ka a idona ko zanji daɗi a raina My husband to be 😘..."

******
Da ƙer Doctor Hasheem yake taka wa yana ɗingishi ya shige room ɗinsa ya zauna a bakin gado duk yanda ya waiwaya Ayush ce take masa gizo, ya rasa yanda zaiyi da soyayyar Ayush, "Dan Allah kizo mun a gaske mana, ki daina wahalar da ni haka ko sau ɗaya ina son sakaki a cikin idanuwa na, Ayush ina matuƙar ƙaunar Gimbiya ta, idan ban mallake ki ba haƙiƙa zan rasa rayuwa taaa...." yana cikin wannan sambatun yaji ana bubbuga door ɗin ɗakinsa.
"waye shugo mana" ya faɗi haka yana jan tsuka tare da faɗin "yanzu haka nasan wannan shashashar Autar tamun ce, ina cikin maganar tauraruwa ta zata zo ta takura mun"
a hankali aka turo ƙofar ɗakin da sallama a bakin ta, ganin wacce ya gani yasa ya yi saurin miƙe wa yana mata kallon ƙurilla tareda murƙusa idonsa da hannayensa don ganin ko gizo ake masa, still wacce ya gani ya sake haɗa ido da ita,
murmushi tasau masa tace "Barka dai Doctor," baki kawai ya sake yana kallonta shima murmushi ya sake mata,
"Shin anya kuwa Ayush nake gani a gaba na?? kar dai ace an fito mun ne da siffar aljana.."
Yana faɗin hakan tare da zaro eyes ɗinsa.
Dariya ta ɗanyi sannan tace "a'a ni ce Dr nazo ganin yana yin jikinka ne, ance baka da lafiya"
yana dariya yana faɗin "eh, eh ƙwarai da gaske, taho ki zauna ga kujera bari na samo miki drinks ko.."
kafin ya fice daga ɗakin ta dakatar da shi tana faɗin "a'ah ka barshi kawai ni da Yaya Junaid muka zo, shima yana waje, daman Mommy ce tace ya kawoni na duba jikinka sauri nake yi zamu koma gida yanzu"
wani irin dipppp Dr yaji a zuciyar sa lokaci guda ya ɗaure fuskar sa, ya juyo yana kallon Ayush sai dai ita ya ɗan sau mata murmushin yaƙe amma a cikin zuciyar sa kamar ana wura masa wuta tsabar kishi, shi baya ma tunanin dukan da Junaid ya yi masa, domin Ayush ce a gabansa...

Daman suna zaune a falo Mommy tace suzo su duba mata jikin DR kafin zuwa gobe itama tazo duba shi...

matsowa daf da ita yayi yana faɗin "okay thank you, nayi kewar ganinki daman..." kafin ya ƙarisa maganar ta katse shi da cewa "eh hakane tin a asibity ko?"
Kafin ya yi maganar suka ji an bankaɗo ƙofar ɗakin
Laila ce ta shugo da gudun gaske tana ƙiran "Bros! Bros!! Bross!!! zo kaga Ogah Junaid yazo wayo farin cikina yazo yana harabar gidan a cikin motar sa," ko tsaya lura da Ayush ma bata tsaya yi ba tayi ficewar ta tana ta kwashe wa da dariya..
shima Dr dariya ta bashi banda Ayush wacce ta tsaya baki a sake tana kallon ikon Allah!..

Da sauri Laila tayo kan Junaid tana zuwa ta buɗe murfin motar ta shiga ciki tana washe baki tareda faɗin "Oga Junaid yau kaine a gidan mu? ka daɗe baka zo ba.."
Junaid juyo wa yayi yana kallon ta daga bisani ya maida kansa kan wayar hannunsa da yake ta dannawa baice komai ba, "amm Ogah baka ga nayi kyau ba, har kwalliya naje nayi maka fa kuma kaƙi kulaniii!" tayi maganar tana shagwaɓa ta turo baki kamar zata yi kuka.
"Hmmm!" abunda yace kenam ya ɗago ya ƙara kallon ta ya kuma maida kansa kan wayarsa.
abun yayi mata ciwo aranta ƙin kulata da ya yi "Hummmm! toh ya zanyi tinda haka Allah ya ɗora mun, son wanda bai damu da mace ba, amma zan ta naci akan ka har Allah ya mallaka mun kai..."
Yana jinta amma yaƙi kulata..!
leƙa cikin wayar sa tayi taga meyake yi ne haka har danna wayar ya fita mahimmanci, abun takaici ashe GAME ma yake ta yi na wasan harbi.
turo baki tayi tana kallonsa kamar tasa kuka......

*FOLLOW ME TO NEXT*
*DAN ALLAH AYI COMMENT DA SHARHI*
*EDITED*


*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

*ASMEETAH NOVEL✍️✍️✍️*

🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of tinger)

*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️✍️)


*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫


بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK ONE*
🅿️ -------> 65 & 66 <-------


"Please banzo gidan ku don ki dameni ba fa?"
ya ƙarisa maganar yana zaro mata manya-manyan idanunsa,
turɓune fuska tayi tana faman masa muzurai, kaiwa hannu yayi zai doke bakin cikin zafin rai tayi saurin tare wa da hannun ta, "get out inside my car" yana nuna mata alamar fita da ɗan yatsar sa,
"dan Allah Oga Junaid ka saurare ni mana..."
kafin ta kai ƙarshen maganar ya katseta da cewa "before i count one to three leave my car, if not you'll see what am going to do" ba shiri Lailah tabar cikin motar da sauri domin ta riga da tasan halin mutumin yanzu zai iya hargutsewa.

fitar ta cikin motar yajaa wani dogon tsuka ya cigaba da wasan game a wayar sa,
da gudu Lailah tayi cikin compound tana rera kuka haka ta wuce su Dr da Ayush a falo suna shan hira ganinta yasa suka tsayar da hirar suka bita da kallo, shi dai Dr yasan dalilin yin kukan ta kawai ya share miƙewa Ayush tayi tare da faɗin "Dr zan wuce Yaya Junaid yana jira na"
"ok tam muje na rakaki gimbiya" ya ƙarisa maganar dai den lokacin da ya miƙe shima yana ƙareta da kallo domin ba ƙaramin kyau tayi mishi ba,
tana sanye da after dress black mai duwatsu ata front ɗin rigar an jera su, gyalen rigar tayi rolling ɗinsa akanta tana riƙe da handbag.
ita ta soma yin gaba tana taku a hankali cikin nutsuwa shi kuwa yana biye da ita, da haka har suka fito harabar gidan suka nufi yanda Junaid yayi parking da motar,
tana zuwa gurin ta buɗe murfin motar ta shige shi kuwa Dr zagaya wa yayi ta yanda Junaid yake drave ya yi knocking yana cewa "well done Ogah kana shaƙar hayaƙi fa, inba busa ba ɗaga hannu ne." wanda yake cikin motar kuwa a hankali ya sauƙar da glass ɗin motor da murmushi a face ɗinsa yanda yake motsa bakin kai kace abu yake ci duk hakan cikin ji da kai ne kamar bazai yi magana ba after some minute da ƙyar ya buɗe baki yana faɗin "how is ur body" murmushin takaici Dr ya yi sannan shima ya maida masa martani "Hmm! Am ok.." abunda Dr ya faɗa kenam idonsa akan Ayush wacce take ta wasa ta jakar hannun ta duk abunda suke yi tana jinsu, already tasan akwai ƴer tsama a tsakanin su amma a ranta tana jinjina irin girman kai na Junaid, "kai kaji wa mutum ciwo amma gaishe shi da jiki sai ya zamo aiki" magana take a ranta idonta akan Junaid dai den lokacin da zai karya kwana da sitiyarin motar ya miƙi hanyar da zai sada shi da gate, sai da ta waiwaya bayanta tana kallon Dr yanda yake jan ƙafarsa da ƙyar yake tafiya abun tausayi, sai da kwalla ta kusan yanke mata da sauri ta tare fuskarta da hannu kar Junaid ya fahimci wata matsala.

direct super market suka nufa zasu yo shopping ɗin dresses da kuma shoes with handbag and others.
duk siyayyar nan a Ayush za'ayi su, duk wasu abubuwa na amfani wanda mace zata yi using dasu gaba ɗaga za'a siyesu.
tafiya suke ba wanda ya kula kowa a cikin su, ya turɓune fuska gira a haɗe cikin ɓacin rai ya daki sitiyarin ɗin motar ya soma wasa akan titi yana jujjuyar da kan motar da ƙarfin gaske yake danna kan sitiarin wani irin ƙara motar take yi, ganin haka yasa Ayush ta toshe kunnuwan ta da hannenta biyu tana ihu "dan Allah Yaya Junaid kar ka kashe mu, kayi hakuri" tayi matuƙar tsorita sosai jikinta har ɓari yake, wani irin burki ya danna gaba ɗayanta ta tafo fuskan nan ya daki gaban motar ta ciki nan kuwa bakin ta ya fashe sai jini dake tsiyayo wa, tsayar da motar yayi yana faɗin "now tell me meyasa kika daɗe da Dr Hasheem a cikin ɗakinsa?"
bai ma lura da jinin dake bleeding a bakin ta ba, tsabar ƙololuwar baƙin ciki ko kulashi bata yi ba. jin shuru yasa ransa ya ƙara hargutsuwa cikin zafin nama ya wani daka mata tsawa "baa magana nake miki

Please Login or Register in order to submit comment