Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya soma jin qamshin jini mai dad'in gaske da kuma ratsa zuciya,
A cikin baccin yake bud'a hanci yana shan-shane shan-shane, lokaci guda kuwa ya mi'ke daga baccin yana tafe a hankali yana bin wannan qamshin jinin nan kamar Karen da yake bin mushe.

Yana sau'ka a up stairs jikinsa ba 'kwari ga dafin alluran da Doc. Fatima tayi mishi ga kuma qamshin jinin da ya 'Kara kashe masa jiki,
Ido kuwa like tiger still bai washe ba.
A haka har ya iso daf da Ayush yana bibiyar jinin jikinta, ita kuwa flowers sun d'auke Mata hankali..............

Tana sumewa a gurin kuwa nan take ya dawo hayyacinsa, ya dawo asalin JUNAID d'insa,
Yana dafe da goshinsa yake bin ko Ina da kallo, kamar komai na gidan ya dawo masa sabo, bai Lura da Ayush dake kwance a 'kasi ba sai daya juya zai bar gurin sannan kyawawan idanunsa suka sau'ka akanta dai dain lokacin Sucuirity sun shigo falon jin ihun da sukaji itama sai ga Doctor Fatima ta nufo waran da gudu tana fad'in "lafiya kuwa mai yake faruwa a gidan"
Junaid binsu yake da kallo d'aya bayan d'aya still ya maida kallonsa kan Ayush tare da fad'in "Mom! Who's dis girl?? Yayi tambaya tare da Kai idonsa kan Mom d'insa.

Security kuwa komawa sukayi tinda komai normal Tiger ya dawo Mutum.

Cikin 'kik'kina Mom take fad'in "am daman marainiya ce, inaso ta zauna damu a gidan nan....
Bata 'karisa maganar ba taji ya katseta da cewa
"Enough, enough Mom! you known bana son kasancewa cikin mutane, bana son hayaniya, bana son ko wani 'kazamin mutum ki kawo shi gidan nan....
"Junaidddd!" Mom ce ta Kira sunansa cikin jaaa alamar dakatar da shi,
"Meyasa kake haka ne? Wannan Yarinya bafa house worker bace balle kayi tunanin haka, inason maye gurbin mahaifiyar ta data rasa ne"

Kama qugunsa yayi tare da jan dogon numfashi "koma meye ne, I don't want her to stay wit us, ki San yanda zakiyi da ita ni dai tabar gidan nan kawai, inaso zanyi bacci". Ya karasa maganar yana tafiya ya haura upstairs.

Cikin mamaki Mom ta Kira sunan sa "Junaid kana bani umarni ne? Shin Kai ka haifeni ko ni na haifeka?"

Juyowa Junaid yayi yana kallon Mom d'insa daga nesa "Ba Umarni nake baki ba, idan kinason taimaka mata ki tabbatar kin nesanta ta daga gareni saboda karai lafiyarta".
Yana kai karshe ya kule room d'insa.

Mom girgiza kai kawai tayi domin ba yau ta saba jin haka daga gare shi ba,
Junaid asalin miskilin mutum ne marar son mutane, idan yace baya son abu to kuwa bazai ta6a son abun ba, ga tsirin tsira baya son raini, Mom tasha kawo house worker cikin gidan Junaid yana koransu,
Hakan yasa Ayyukan gidan suke yiwa mom yawa, Gashi tana zuwa hospital ta rasa yanda zatayi,
Junaid baya cin abincin kowa inba ta Mom d'insa ba...

Haka Doc. Fatima ta cicci6i Ayush zuwa d'akinta.............

Continue. ✍️
Junaid yana a bakin gado da wata er glass table a gaban sa yanata pressing d'in computer yaji ana knocking
"yes coming" ya furta hakan ba tare da ya d'ago kansa ba.
Turo kofar akayi ta shugo ciki tare da mayar da kofar ta rufe ,
"my Son! anata business kenam sarkin danna computer fatan dai kayi sallar Isha'i?"
Tayi maganar a daidain lokacin da ta zauna a kusa da shi.
"Let me finish dis work be4". Ya furta hakan yana cigaba da Danna computer!
Mom ce ta juya tana masa kallon 'kurilla cike da mamaki tace "you finish what?? Junaid are you serious? A tunani na Sallah shine gaba da komai"

"Oh god! Mom nayi sauran sallolin only isha'i ne banyi ba, shi kuwa lokacinsa baya wuce wa da wuri, kinsan dai bana wasa da ibada na KO"

Jinjina kai Mom tayi "OK! I known that"
In short amsa ta bada.
Daga nan ta shiga nazari tayi shuru kamar mai yin tunanin wani Abu
Juyowa Junaid yayi yana kallon mom d'insa yasau murmushi sannan yace "let me go and pray, naga kamar ranki ya sosu KO?"
Yakai karshen maganarsa tare da mi'kewa ya nufi toilet.
Itama murmushin tayi jin abunda yace.

Ita daman tazo taga lafiyarsa ne da kuma ta bashi hakuri akan yabar Ayush ta zauna da su .

Tayi tunanin ta 6oye Ayush a cikin gidan yanda bazai ganta ba, sai dai duk lokacin da ya gano hakan bazai barta ba saiya hukunta ta, domin ba abunda ya tsana illa a munafurce shi da kuma 'karya...

Zaman jiranshi tayi har yayi sallar sa ya had'a da lafuloli.
Daga bisani kuma yazo kusa da mominsa ya zaune yana fuskantar ta
"Is there any problem". Ya furta hakan yana kallon ta.

Murmushi tayi sannan tace "Junaid kana son ganin farin ciki na?"

"Of course Mom" ya bata amsa a takaice!

"Idan kuwa hakane!
Inaso ka saurari abunda zance maka, Nan ta kwashe labarin Ayush ta gaya masa, ita marainiya ce daga asibiti bata San Ina zata nufa ba"
Ta dakatar anan tana kallonsa, so take taji abunda zaice,
Sai dai kuma bataga alamar tausayawa daga fuskar Junaid ba , hakan yasa Tasha jinin jikinta, tasan bazai bar yarinyar ta zauna a nan ba.

'Dan turo 'karamin bakin shi Junaid yayi ya kalli mom d'insa ta wutsiryar ido yana yamutsa fuska yace
"Ni fa mom duk wannan tatsuniyar takin ban fahimce shi ba, naji labarin Kwata-kwata bai shafeni ba"

"Junaid please be patient and help her" murya a sanyaye mom take magana.

Juyowa yayi ya kalleta "how comes Zan iya temakan wanda ban Sani ba,
Mom don't trust any body, yanzu mutane ba abun yadda bane, wani zai iya shugo rayuwarka domin ya cutar da kai, tin Ina yaro na fara ganin yanda rayuwar take, karki ga laifi na don Ina Koran house worker da kike kawowa because House worker ce tayi sanadiyar *MUTUWAR* *MAHAIFINA* mutumin kirki bai aikata komai ba! Wallahi Mom bazan bar kowa ya kusance mu ba, kuma har yanzu Ina kan bakata na d'aukar fansan mutuwar Mahaifina, idan ban d'au fansa akanta ba sai dai bata Raye to kuwa Zan d'au fansa akan *IYALANTA* har yanzu Ina kan bincike na kuma insha Allahu Zan samesu, hukunci na kuma kisa ne ko wa nasamu acikin familyn ta!
Hakan yasa na shiga Aikin *soja* ban damu da ciwon dake jikina ba, nasan Allah ne ya d'ora mun ciwon kuma Ina neman warakarsa".......

Doctor Fatima ba abunda take sai kuka domin an fame Mata ciwon dake zuciyarta,

Shima kawar da fuskarsa yayi gefe yana 'ko'karin share hawayen da ya zubo masa............


*ASMEETAH* *CE* ✍️✍️✍️

*FREE* *BOOK*

🐅 *MATAR* *DAMUSA* 🐅
(the wife of tiger)

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* ✍️✍️

The writers of...

1️⃣ Ikram ko Kausar.
2️⃣ Rayuwar Siyama.
3️⃣ Baby Ogah.
4️⃣ Yayana Zan Aura.
At now
5️⃣ *MATAR* *DAMUSA*


*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫


بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK* *ONE*
*PAGE* ➡️16

Fitowarta kenam daga toilet, tana d'aure da towel a kirjinta, gashin kanta a baje agadon bayanta ta wanke shi fess har wani shining yake ga ba'ki ga tsayi har ya kusan isowa 'kugunta, dake gashin Fulani ne da ita!
Ayush farar mace ce ta asali, ga manya manyan idanuwa gashin ido kuwa zara-zara ba'a magana, azo kan gashin gira acike tam da gashi har girar ya kusan had'ewa 2, ga shaden ta luf-luf kwance da gashi, gashin gaban goshinta kuwa ya sau'ko sun had'e da girar ta.
Allah yayiwa Ayush baiwar suman gashi ga kyau ba'a magana, ga tsayin hanci kamar Wanda kullum ake dad'a tsayinsa, lips d'inta kuwa kamar bakin tsuntsu tsabar 'karanta tana da 'karamin baki, colour bakinta yaci maroon sosai kamar wacce ta shafa jan-baki, kuma haka bakinta yake tin tana jaririya,
Ayush ko kad'an bata makeup saboda kwalliyar fuskarta Wanda Allah ya tsara mata mah ya isheta,
Ko tayi makeup ko kartayi kullum Ayush a cikin kyau take, doguwar mace ce, siririya marar kauri, sai dai akwai kayan alatu kam
Ta waran 'kirjinta ba'a magana a cike fam kamar meyin ciko sai dai bata saka rigar breziya, saboda gurin da ta zauna da mahaifiyarta basa samun kud'i balle suyi siyayyan kayan da zasu saka, sai riga kala d'aya da take using dashi kullum.....
Anzo gurin kuma wato waran Baanbom d'inta ga hips kuwa kamar ita tayiwa kanta, ta ko Ina a cike yake a jinkinta duk da batada jiki amma tana da kyakykyawar surar jiki....
Tsayawa tayi a gaban mirror ta kammala shafa cream mai shegen 'kamshi ta feffesa turare a jikinta ta gama gyara gashin kanta ta d'aure da rivon, shikenam makeup d'inta kenam ko powder bata shafa ba amma fuskar yanda kasan an tsara kyakykyawan makeup ne.
Ta nufi yanda Doctor Fatima ta ajiye mata kayan da zata saka, wata dan'kararriyar doguwar riga ne na kanti mai bell a jiki black color.
Zura rigar tayi sannan ta d'aure kunkumin ta da bell d'in, kunkumi kamar na sauro sai tilin 'kugu, ga breast d'in ya fito sosai Masha Allah kayan ba 'karamin kyau sukayi mata ba.
Ba tare da ta rufe kanta ba ta bar room d'in tana taka matakala a hankali ta sau'ko falo, ta nemi d'aya daga cikin jerin kujerun falon ta zauna ta d'aura 'kafanta d'aya akan d'aya tana fuskantar television Wanda a ciki ake showing India film.
( (Ashe Ayush er Hutu kenam, wato da ace a gidan masu kud'i Ayush ta fito waii da anyi 'karyar rai))


"Mom please stop crying, banyi haka don na 6ata miki rai bane, just I can't believe any body, ni ban yarda da wannan yarinyar ba, zaifi ta bar mana gida"
Junaid ne yayi maganar yana ri'ke da hannun mom d'insa.
Doctor Fatima d'agowa tayi da rinanan idanuwanta wad'anda sukayi jawur tsabar kuka, "Junaid ba wai na'ki batunka bane kana da gaskiya, bama bu'katar yarda da kowa domin yarda da Bara'atu ne yayi silar mutuwar mijina mahaifinka, wanda Inna tuno da hakan nakanyi kuka mai rad'ad'in gaske, amma abunda nakeso ka Sani shine wannan yarinyar da zata zauna damu Yarinya ce 'karama like bazata wuce 20yrs ba
Bata da mummunan 'kudiri a ranta face neman taimakon da takeyi, tana bu'katar kulawa,
Mace ce mai rauni inta bar gurin mu bamu San hannun wanda zata fad'a ba maybe mai cutarwa ne,
Kar muyi gaggawar rabuwa da ita domin idan ta shiga hannun mungu tabbas sai Allah ya tambaye mu tinda nasan mahaifiyar ta bata raye marainiyace bata san yanda mahaifinta yake ba shin yana raye ko ya mutu sai Allah,
Please my son"
Dogon Numfashi yaja sannan yace "OK mom na Amince ta zauna a tare da mu, but idan naga robish anything can happen". Yakai karshen maganar yana kallon mom d'insa
Murmushi ita kuwa tasau na farin ciki tace "insha Allahu ba abunda zai faru, thank you my son"
Mi'kewa yayi akan lallausar gadon sa yana fad'in "OK call her for me, I want to see her"
Mi'kewa tsaye tayi tace "to Zan kuwa Kira ta yanzu tazo ta gaida Boss d'in gidan". Tana shirin fita yace "mom please am hungry let me eat something" yana kai karshen maganar ya wani d'aure fuska kamar bai ta6a yin murmushi ba,
Mommy kuwa ganin hakan yasa ta kwashe da dariya tana fad'in "OK don't worry, yaro ba wasa da eating" fita tayi ta bar d'akin, shi kuwa rufe idonsa yayi kamar maiyin bacci ...

Shima fa Junaid asalin kyakykyawa ne, white chaculate ba ba'ki bane still bai kai asalin farin fata ba domin ko rabin farin Ayush bai d'auko ba, but mutumin akwai dogon hanci ga bigger eyes bakin shima 'karami ne, dirarren namiji ne ga tsayi ga fad'i ga jiki ga-ga-ga-gaaaa abubuwan sunyi yawa yara kamar su suka halicci kansu , shima akwai tara suman Gashi akansa baya son aski sai dai akwai son gyara suman kullum Gashi a kwance lufff azo kan jikinsa duk gargasa ne ta ko Ina a jikinsa a kwance luf domin ba 'karamin cream na gyaran jiki Junaid yake amfani da shi ba, Gashi tin daga kan sajensa har zuwa gemunsa a kwance yake.....

Fitowar Doc. Fatima falo ta tarar da Ayush zaune tana ta kallo hankali kwance,
Sauran kad'an Mommy ta juya da gudu ganin Ayush ta d'au Aljana ce
Ayush ce ta kalli gurin da mommy take ta sau murmushi "Aunty na fito ban ganki ba"
Ajiyar zuciya mom tayi sai a yanzu hankalinta ya dawo dai dai jin muryar Ayush d'in
"Wayyo Alhamdulillah Ashe Ayush d'in ce". Ta 'karaso yanda Ayush d'in take.
"Masha Allah Ayush kinga yanda kikayi kyau ne, danma bakiyi makeup ba da ba'a San irin kyau d'in da zakiyi ba, said dai a kulleki saboda sumar da samari zaki rin'ka yi a titi"

Kwashewa da dariya Ayush tayi
Tana kallon Doctor Fatima wacce ta 'kura mata ido
Ita kuma Ayush sai zabga uban murmushi take dimple d'in nan gwanin burgewa.

"Gaskiya zanso Junaid yaga yarinyar nan ko zai 'kyasa, inada burin ta zamo surkata na samu jikoki kyawawa" Doctor Fatima ce maiyin maganar zuci, daga bisani tayi gyaran murya sannan tace "Yawwa Ayush Oga yana son ganinki"
Cikin mamaki Ayush take kallon Momy tace "wayene Oga kuma Aunty? Kodai mai gidan kike fad'a?"
Duk lokaci guda tayi tambayar still Idonta akan Mom,
Short laugh Mom tayi sannan tace "eh kusan hakan ne, 'karamin maigidan ne domin babban maigidan ya rigamu gidan gaskiya, 'karamin maigidan kuma shine yaron gidan"
Sai a yanzu Ayush ta dawo nutsuwarta taja ajiyar zuciya
"Toh shikenam Aunty Zan jeni, Allah ubangiji ya ji'kan maigidan"
Amsawa Mom tayi da Amiin.
Mi'kewa Ayush tayi tana tambayar yanda yake zata je gaisuwa,
Nuna mata hanya Mom tayi yanda zai sadata da d'akin Junaid, ta fara tafiya kenam Mom ta tsayar ta tana fad'in "tsaya ki tafi masa da lunch d'insa domin ya sanar mun da cewa yana jin yunwa.
Tsayawa Ayush tayi tana jiran momy cikin en mintina saiga Mom da manya manyan kuloli har kashi hudu asaman glass tray ta d'aura a kayi hannunta ri'ke da flas da'kananun kofina a Jere saman glass tray d'in,
Yanda Mom ta d'auko haka Ayush ma ta d'auka
Tana hawan upstairs a hankali tabi yanda akayi mata kwatance sai gata a d'akin Junaid,
'Daki wayam ba kowa, sai'karewa d'akin kallo take yayi matukar burgeta
Ta sau'ke kayan abincin a saman dinning d'insa,
Taje gaban mirror tana duban kanta, kwatsam sai ta hangoshi ta cikin madubi yanata sharar bacci akan gadonsa, dake akwai labule ta tsakanin gadon hakan yasa bata ganshi da wuri ba.
Juyowa tayi da sauri tana le'kashi ta bud'e labulan a hankali tana so taga fuskar shi amma sai dai hannayensa suna kan fuskarsa ta kasa ganin fuskar...........



*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦350
2GB = ₦600. 2GB = ₦700
3GB = ₦900. 3GB = ₦1000
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1300
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1600

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*


*ASMEETAH* *CE* ✍️✍️✍️


*FREE* *BOOK*

🐅 *MATAR* *DAMUSA* 🐅
(the wife of tiger)

*MALLAKIN*
*ASMEETAH* ✍️✍️

The writers of...

1️⃣ Ikram ko Kausar.
2️⃣ Rayuwar Siyama.
3️⃣ Baby Ogah.
4️⃣ Yayana Zan Aura.
At now
5️⃣ *MATAR* *DAMUSA*


*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫


بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK* *ONE*
*PAGE* ➡️17 to 18


Ayush tsayawa tayi a bakin gadon da Junaid yaketa sharar baccinsa ya rufe fuskar da pillow, tana tunanin ta tashe shi ne ko kuma ta kyale shi kawai tayi tafiyarta
Lokaci guda ta yanke shawarar tashin shi yaci abinci kada yayi sanyi, cikin 'karfin hali ta haye saman gadon tana rarrafawa a hankali cike da fargaba saida tazo saitinsa ta tsaya cak ta kasa tashin shi.
Shi kuwa adai dai lokacin ya fara wani irin mafarki mai tsoratarwa, A cikin baccin yaga wata ba'kar Damusa mai jajayen idanuwa ta tsaya daf dashi tana shirin Kai masa hari! A gigice Junaid ya Kai mata naushi da iya 'karfinsa
Wayyo a madadin ya naushi Damusan ashe a Ayush ya kaiwa wannan naushin a saman Nononta ta 6angaren dama, wani irin 'Kara tayi ta wantsilo 'kasi sai datayi dungure sau uku ta tsinci kanta a bakin 'kofa, hankali a tashe ta mi'ke tana tangal tangal kamar wacce tasha kayan maye! a haka ta fice daga d'akin...
Shi kuwa cigaba da baccinsa yayi hankali kwance.

Mommy tana shirya musu kayan abinci a dinning
Ta jiyo kukan Ayush da sauri ta waiwaya bayanta domin ganin abunda take ji,
Ayush bata tsaya wata-wata ba sai yaraf ta fad'i 'kasi tana ta faman juye-juye da shanbe-shanbe "wayyo Allah Zan mutu, kirjina ya fashe ciwoo". Ta Kama Nononta da hannunta domin ba 'karamin zogi yake yi mata ba
Duk ta rasa Ina zata saka kanta, idanunta duk sun kad'a sunyi ja tsabar azaba ga wani gumin da yake yarfo mata..
"Ayush lafiyanki kuwa? Ke da waye? Meya sameki" haka mommy taita jero mata tambayoyinda bazata iya amsa su ba a yanzu,
Ganin yanda taketa juyi a gurin yasa mommy tsorita da sauri ta kamo Ayush tana fad'in muje mu d'aki kiyi hakuri"
Ayush KO mi'kewa bata iya yinsa kamar Wanda wuta yake ci akan Nonon haka take jin rad'ad'in nan.
Zaunar da ita tayi a bakin gado, tana fad'in "sannu ko, wai meya faru ne Ayush?"
A lokacin Ayush ta d'an dawo hayyacinta duk da zafin da gurin yake yimata da 'kyar ta bud'i baki tace "buguwa nayi" bakinta na kakkarwa kamar maijin sanyi,
"A'a Ayush ki gaya mun gaskiya, shin da mai kika bugu?
Kamar bazata yi magana ba can tace "na bugu da 'kofar d'aki ne" murya sanyi sanyi take magana.
Mommy tace "kin tabbata?"
Kai Ayush ta d'aga mata alamar eh.
Mom tace "to muga gurin da kika ji ciwon" ta 'karasa maganar tana faman cire rigar Ayush!
"A'a Aunty ki Bari kawai ba wani ciwo sosai bane" a cewar Ayush wacce kanta ke kallon 'kasi alamar kunya.


Please Login or Register in order to submit comment