Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

carbi alamu sun nuna tayi sallar dare ne, domin yanzu ake ƙiran sallar asuba ma...

a hankali yake motsa bakinsa yace "Yushert.." bata kula shi ba sai ɗagowa tayi ta kalle shi sannan ta kawar da kanta tana kallon gabanta bakinta na motsi alamar tana tasbihi..

tashi yayi ya sauƙa daga kan gadon zai fita a ɗakin har yazo daf da bakin ƙofa yaji tace "meya kawo ka ɗakina?.."

murmushi yayi sannan yace "nazo duba lafiyarki ne, ya jikin nakin?.."
daga nan bata ƙara cewa komai ba ko amsa bata bashi ba ta cigaba da jan carbinta..

ganin ta sharar dashi ne yasa ya girgiza kai sannan ya fice, kai tsaye ɗakinsa ya nufa yana shiga kuwa ya shige toilet ya yo alwala ya fito da sauri ya sauƙa down yayi ficewarsa ya tafi masallaci...

misalin ƙarfe 9 na safe mommy tana zaune a falo tana jiran shugowar Junaid tin fitar Asuba, tana so a fara shirye-shirye tin yanzu kafin a fara yin baƙi duk da tasan sai wajen la'asar a buɗe taron, kuma a cikin gidan za'ayi taron a babban hall wanda sai an buɗe wani ƙatoton get a cikin gidan kafin a shiga fili ne guda duk an mamaye gurin da floor, wajen daman an tanadar da shi ne saboda taro na musamman, an ƙayatar da wajen sosai ga kujeru a jere na musamman, ga wasu ƙayatattun kujeru kuma du a saman yanda manya-manyan baƙi zasu zauna da kuma shi kansa Junaid, ga wasu haske masu ƙayatarwa sai walwali suke suna bada haske kala-kala, duk an mammanna photunan Junaid a jikin bangon an tsara shi shima..

(wannan taron da za'ayi nima ina gayyatar members na group ɗin matar damusa dasu halacci gurin taro amma sai kunada card na gayyata domin tin jiya aka raba wa manya-manyan baƙi idan baku samu ba toh ba shiga gurin taron sai dai a baku labari ko kuma ku kalli video, ni kuma Asmeetah ga kujerar Oga Junaid ga nawa🤪🤪 kuma in baku labari raƙumi da saniyoyi uku za'a yanka..)


Mommy tana zaune a saman sofa saiga Rumana ta fito daga cikin ɗakinta tana sanye da gajeran wando zuwa gwiwarta mai kakin soja da kuma ƙaramin best sai dai ta saka breziya ata ciki kafin ta ɗora best akai, zuwa tayi ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun falo tana faɗin "gud morning mom.."

Mummy da murmushi a fuskarta ta amsa mata dake yanzu da turanci tayi gaisuwar bada french ba..

Mommy tace "ga can kayan breakfast asaman dinning..." tayi mata maganar ne da turanci,
yamutsa fuska tayi sannan tace "where is Junaid?.."

"I don't known.." mommy ta bada amsa a takaice,
Rumana ta kuma cewa "ok bari yazo muyi breakfast a tare..."
daga nan basu ƙara cewa komai ba.

saiga Ayush ta fito sanye da zureren hijab har ƙasi ta fitar da hannunta waje dake hijabi mai hannu ne..
saida tazo gaban mommy ta durƙusa tana gaisheta,
mommy amsawa tayi da murmushi a fuskarta tace "antashi lafiya my dota?.."
Ayush ta amsa mata tareda miƙewa tsaye har fuskarta yayi fiyau farinta ya ƙara fitowa,
zuwa tayi gaban Rumana ta durƙusa mata sannan itama ta gaisheta,

tana turɓune fuska tareda yamutsa shi daƙer ta buɗe baki ta amsa mata,
dake tana zargin akwai wata alaƙa dake tsakaninta da Junaid tin a daren jiya, Rumana sarkin kishi kenam...

Ayush miƙewa tayi mommy tace "Dota ga can kayan breakfast kije ki karya kinji, nasan kina jin yunwa..."
Ayush ta ɗaga mata kai tareda cewa "toh Momy.."

taje ta zauna a dinning tana zuba fried chicken domin shi take sha'awar ci ta haɗa wannan la'anannen shayinta nan mai masifar kaurin gaske domin tana zuba madara kam bana wasa ba sannan ta zabga sugar,
haka take ci tana ɗibar tea da spoon tana haɗawa da shi,
ba ƙaramin yunwa ta tashi dashi ba,
tana cikin karyawa sai ta jiyo sallamar Junaid ya shugo yana jan trolly ta bayansa kuwa wata zankaɗeɗiyar mace ce domin wannan ta wuce ace mata yarinya,
Ayush dakatar da karyawa tayi tana kallon ikon Allah,

miƙewa mommy tayi tsaye tana faɗin "ina kaje Junaid tinda asuba?.."
bata ƙarasa maganar ba taga mata ta shugo tana bin falon da kallo tareda faɗin "wow nice this parlour is so fantastic.." tana magana da yaren china gashi kuwa tayi zubi da chinoni hatta ƙananon idanuwan da ƙaramin baki,

Junaid ne yace "Adity look at my mom.." ya ƙarasa maganar yana nuna mommy shima da yaren china yayi maganar, sannan ya kalli mom itama yace "mommy ganan Aditi fah ta ƙaraso.."

Mommy yaƙe kawai take tace "eah ai na gani, ganan zubinta kuwa irin na chinoni, wato zaka haifo mun jikoki masu kamanni daban daban kenam, a cikin akwai chinoni da kuma turawa.."

Dariya Junaid yayi sannan yace "ita kuma Angel fa?..."
mommy tace "ai wallahi gwara Angel duk ta fisu kyau, ita wannan ai kamannunta irin namu ne.."

Aditi ce ta katse mommy da cewa "mom you are so beatiful, glad to see you.." ta ƙarasa maganar tareda rungumar mommy,
mommy dai kawai ta biye mata ne tana dariyar yaƙe amma daga Aditi har Rumana ba wacce ta ƙwanta mata a rai..

Rumana tana zaune ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya tana zabgawa Aditi harara kamar idonta zai faɗo ƙasi saboda tasan itama budurwar Junaid ce,
Adity ganin yanda Rumana take hararar ta yasa ta fusata tayo kanta zata naushe ta Junaid yayi saurin riƙota yana faɗin "don't allow if not you'll see what am going to do.."

Adity juyowa tayi tana kallon Junaid da fici-ficin idanuwanta, duk zafin ranta tana shakkar Junaid, ba china ba ko itace sarkin faɗan chinoni ce bazata iya gabzawa da Junaid ba...
turo baki tayi tace "nuna mun ɗakina.." tayi maganar da yaren china cikin sauri-saurin magana,
yana riƙe da hannunta yaja ta suka nufi ɗakin dake kusa dana mommy ɗayan hannun kuma yana riƙe da jakarta suka shige ɗakin...

dogon tsuka Rumana taja sannan ta miƙe ta nufi ɗakinta,
Mommy dai tsayawa tayi tana kallon drama baki a sake,
bata ankara ba tajiyo Ayush tana kwashewa da dariya har da tafa hannayenta, ita abun ma dariya ya bata madadin taji haushi, saboda ba iya mutum ɗaya ya kawo ba sannan ta uku tana tafe bazata ji haushi sosai ba..

kallonta Mommy tayi tace "ke idan wannan ƴar china ta fito zaki ƙwala, kinga irin mazgar da sukeyi a film ko to irinsa zatayi miki.."
zaro ido waje Ayush tayi tace "toh kuwa zanyi mata biyayya yanda ya kamata.." tana kaiwa haka ta cigaba da tura abinci a baki tareda shan kakkaurar tea ɗinta..

(tab da Junaid ya bari fa Adity dukan tsiya zata yi wa Rumana domin ta fita ƙarfi nesa ba kusa ba, duk da gaba ɗayansu sojoji ne)..

bayan Junaid yaja Adity ɗaki zaunar da ita yayi yana mata warning akan baya son yawan faɗa, yana cewa "idan kina son ganin farin cikina to karki nemi kowa da faɗa kinji ko?.."
yana magana ta yaren china.
miƙewa tayi akan gado tayi shame-shame ba tareda tace masa komai ba, ta lumshe ƙananun idanuwanta kamar mai yin bacci..

shima miƙewa yayi saman kanta ya kawo ƙaramin bakinsa saitin kunnenta yace "please my war make everything for easy.."
yayi mata haka ne saboda ya rarrashe ta domin yasan halin Aditi indai baiyi mata magiya ba kafin ta koma saita tayar da ƙaramin yaƙi a cikin gidan nan,

hautsinar dashi tayi gefe tana cewa "impossible duk wanda ya taɓani nima dole na taɓa lafiyar jikinsa, leave me alone i wanna to rest..."
ta ƙara miƙewa a saman gadon ta kuma cewa "ƙarfe nawa za'ayi walimar?..."

miƙewa yayi ya nufi hanyar fita tareda cewa "4 O'clock na yamma, ƴar masifa kawai, kafin ki tafi saina miki dukan tsiya wallahi idan baki maida hankalinki ba..."
daiden zai fita ta wurga masa pillow tana huci tareda faɗin "don't hot my heart..."
juyowa yayi ya kalleta sannan ya girgiza kai ya yi ficewarsa domin yasan idan ya biye mata zata sha duka ne yanzun nan, daman koda yaushe Junaid da Adity acikin faɗa suke, duk da yana mata dukan tsiya amma hakan bayasa ta daina abunda take yi, wani sa'in ita take nema suyi faɗa tana kawo masa naushi shi kuwa ya tattaka ta a wajen, dake lokacin da yake zuwa aiki ana yawan tura shi ƙasar china anan zasu haɗu suyita faɗa, tana jawowa yayi mata duka, akwai wani sa'in daya taɓa gurɗata a hannu irin nan ta kawo masa naushi shikuwa ya riƙe hannun ya murɗe anan ta gurɗe,
su waɗannan kalar soyayyarsu kenam shine faɗa....

bayan Junaid ya fita falo ya tarar da Ayush ta kammala karyawarta, zuwa yayi daf da ita ya tsaya a gabanta yana faɗin "kin koyi girman kai ko? mai kike taƙama dashi ne? kodan kinga ina biye miki ne shine zakina wani isarki kina rashin mutunci yanda kike so! to ki sauƙe wannan girman kan nakin tin kafin na hukunta ki..."
ya ƙarasa maganar yana kallonta, ita kuma kanta a ƙasi tana wasa da yatsunta,
hannu yakai ya jawota jikinsa yana faɗin "ba magana nake miki ba?.."

ɗagowa tayi da sauri tana kallonsa kamar zatayi kuka tace "to meka ce?.."
"cewa nayi ya jikin nakin?.."

tana baza manya-manyan idanuwanta tana kallonsa a hankali take motsi da ɗan ƙaramin bakinta tace "da sauƙi.." murya a sanyaye, hakan ba ƙaramin jefa shi yayi a cikin wani irin yanayi ba, jikinsa ne yayi wani yarrr tinin yaji wani abu ya ɗigo masa a cikin wandonsa,
bai ƙara cewa komai ba sai matso da fuskarsa da yake yi saitin fuskar Ayush, numfashin su har ya soma gaurayuwa yana shirin haɗe musu baki guri ɗaya,
ji sukayi an harba bindiga bullet ya fita ta window!

tsabar firgici da tsoro a razane Ayush ta ƙwarara ƙara mai razanarwa ta toshe kunnuwanta kanta asaman ƙirjin Junaid nan danan jikinta ya soma kakkarwa,
Junaid rungumarta yayi sosai saboda yasan ba ƙaramin tsoro taji ba, shi kuwa ko a jikinsa bai tsorita ba saboda yasan ɗaya ne daga cikin ƴanmatansa Rumana ko Adity, a hankali ya juyo bayansa domin yaga ko wacece a cikinsu yana bubbugar bayan Ayush alamar rarrashi...

ganin yanda mommy ta fito da gudun gaske ko ɗan ƙwali babu akanta tana salati a ruɗe saboda taji ƙarar bindiga ga kuma ihun Ayush a tunanita an harbeta ne,
sai kuma ga Rumana itama ta fito da sauri tana son ganin meke faruwa..

duk tsayawa sukayi sun yi cirko-cirko danin mutum tsaye yana sanye da baƙaƙen kaya ajikinsa,
wando baƙi da kuma rigar sanyi baƙi masu jikin leda sai sheƙin baƙi kayan suke, da baƙin hula a kansa na sanyi, ga kuma ya rufe fuskar da facemark sannan ya ɗora baƙin glass a ido,
yana sanye da safar hannu baƙi, takalmin ƙafarsa baƙi irin takalmin nan mai safa amma yanada tudu, yana goye da ƙatuwar baƙar jaka a baya, hannu kuma riƙe da ƙaramin bindiga..

Adity ce itama ta fito tana masifar waye ya tasheta a bacci,
tsayawa tayi itama tana kallon mutumin buɗe baki tayi tace "ɓarawo a gidan nan?..."
tayi maganar ne da turanci yanda kowa zai jita,

Rumana ce ta ari bakinta da cewa "ɓarawo kuma da rana?.." itama ta mayar da amsa ta turanci..

Mommy kam ba bakin magana ta tsaya tana kallonsa jikinta har ya fara rawar sanyi, zuciyarta kuwa haka yake bugun 3+3...

har yanzu Ayush kanta yana kife a saman ƙirjin Junaid ta kasa ɗagowa..

Junaid bayan ya ƙareta da kallo shi dai yasan wannan ba namiji bane tayi zubi da mace,
murmushi yasau mai ƙayatarwa sannan yace "you are crazy my Angel...."

jin ya canki sunanta yasa ta motsa, tasa hannu ta cire hular kanta saiga baƙin sumar gashin ta ya wantsilo har gadon bayanta, sannan ta cire glass ɗin idonta saiga dara-dara idanuwanta sun bayyano sun sha kwalli kuwa, ta cire facemark ɗin fuskarta saiga ƙaramin pink lips ɗinta sun fito da ƙayataccen murmushi a fuskarta, tana dariya har fararen haƙoranta suka fito, a hankali take motsa lips ɗinta tace "my Man soyayya ne haka kodai itace kishiyar tawan?.."

shima murmushin ne a saman fuskarsa baice mata komai ba sai ware mata hannu da ya yi alamar taje ta..

da gudu taje gurin shi ya rungumota da ɗayan ɓangaren hannunsa yana bubbuga bayanta a hankali a saitin kunnenta yace "kin tsoritar mun da mata shin kin kyauta mun?..."

dariya tayi tana bugan ƙirjinsa..
ta ɗayan ɓangaren hannunsa kuma Ayush ce itama yake rungume da ita har yanzu bata ɗago da kanta ba,
haka ya haɗa su ya rungumesu a tare.....

mommy ajiyar zuciya tayi ganin ashe Angel ce har hankalinta ya kwanta...

Rumana kam ɗaukar ɗan ƙaramin glass cup tayi ta doka a ƙasi ya dagargaje tana huci ta koma ɗakinta..

Adity kuma idanuwanta fici-fici haka ta dinga fin-fincina su tana son ganin shin meke faruwa ne....


Junaid kuma haka ya haɗe kayuwan Angel da Ayush guri ɗaya asaman faffaɗar ƙirjinsa, shima ya kifar da kansa a tsakiyar kayuwansu .....


*KUYI HANZARIN TURO KUDIN KU DOMIN CIGABA DA BOOK TWO*


*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

*ASMEETAH NOVEL*

*typing📲*

🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)

*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)


*WhatsApp me 09065443871*


*BOOK ONE*⬇️
*99 to 100*

*👉 END 👉 END 👉 ENDED OF BOOK ONE*

*DOMIN SAMUN LITTAFI NA BIYU KU HANZARTA BIYAN KUƊIN KU A FARASHI MAI SAUƘI...*

*MATAR DAMUSAA BOOK 2 PAY ONLY 200👌👇👇👇*

*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*9065443871, OPAY BANK.*

*OR*

*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*2267236949, ZENITH BANK*

*SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER*
👇👇👇
*09065443871*



*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________



💫💫 *{{N W A}}* 💫💫


بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم


𝐔𝐩! 𝐔𝐩!! 𝐔𝐩!!! 𝐇𝐮𝐫𝐫𝐲💃💃💃

𝐒𝐀𝐅𝐍𝐀 𝐆𝐑𝐀𝐏𝐇𝐈𝐂𝐒 𝐃𝐄𝐒𝐈𝐆𝐍.
ᴴᴼᴹᴱ ᴼᶠ ᴳᴿᴬᴾᴴᴵᶜ ᴰᴱˢᴵᴳᴺ
ᵂᴱ ᴰᴱˢᴵᴳᴺ ᴬᴸᴸ ᴷᴵᴺᴰ ᴼᶠ ᴰᴱˢᴵᴳᴺ ˢᵁᶜᴴ ᴬˢ:
𝐿𝑂𝐺𝑂* 𝑃𝑂𝑆𝑇𝐸𝑅* 𝐵𝐴𝑁𝑁𝐸𝑅* 3𝐷 𝑀𝑂𝐶𝐾 𝑈𝑃 𝐿𝑂𝐺𝑂* 𝐹𝐿𝑌𝐸𝑅* 𝑆𝑇𝐼𝐶𝐾𝐸𝑅* 𝑃𝑅𝑂𝐷𝑈𝐶𝑇 𝑆𝑇𝐼𝐶𝐾𝐸𝑅* 𝐼.𝑉 𝐶𝐴𝑅𝐷* 𝐼.𝑉 𝑉𝐼𝐷𝐸𝑂* 𝐵𝐼𝑅𝑇𝐻𝐷𝐴𝑌 𝑉𝐼𝐷𝐸𝑂 𝐹𝐿𝑌𝐸𝑅* 𝑃𝐻𝑂𝑇𝑂 𝐹𝑅𝐴𝑀𝐸* 𝑅𝐸𝑀𝑂𝑉𝐸 𝐵𝐴𝐶𝐾𝐺𝑅𝑂𝑈𝑁𝐷* 𝑃𝑅𝑂𝐹𝐸𝑆𝑆𝐼𝑂𝑁𝐴𝐿 𝐼.𝑉 𝐶𝐴𝑅𝐷* 𝑆𝐴𝑉𝐸 𝑇𝐻𝐸 𝐷𝐴𝑇𝐸* 𝐸𝑋𝑃𝐿𝐴𝐼𝑁𝐸𝑅 𝑉𝐼𝐷𝐸𝑂* 𝐿𝑌𝑅𝐼𝐶𝑆 𝑉𝐼𝐷𝐸𝑂 𝐴𝑁𝐷 𝑀𝑂𝑅𝐸...
𝗣𝗟𝗘𝗔𝗦𝗘 𝗖𝗔𝗡𝗧𝗔𝗖𝗧 👉 08148318396 𝗦𝗔𝗙𝗡𝗔 𝗚𝗥𝗔𝗣𝗛𝗜𝗖𝗦.


🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀

Adity ganin yanda Junaid ya rungumi ƴan mata a jikinsa yasa ta fusata cikin zafin nama ta tashi sama ta dirƙo a gaban Junaid, hannu ta kai musu zata cabki wuyan su Angel da Ayush kenam Junaid yayi saurin riƙe hannayenta biyu ya ɗago da dara-daran idanuwansa yana kallonta cikin fushi, girgiza mata kai yayi sannan ya tureta gefe,
tana huci tace "waɗannan karuwanka ne suma ko? toh ka fito fili ka zaɓi wacce kake so a cikin mu, bazan yadda da irin cin amanar nan ba da kuma yaudara, kayi mun alƙawarin zaka aure ni yanzu kuma sai ganin ƴanmata kala-kala nake kuma duk naka, yau ba wacce zan bari da lafiyarta..."
haka ta gama surutan ta da yaren china,
Mommy kuwa kallonta kawai take ita kallon mahaukaciya take mata, ga maganar ta sauri-sauri..

Duk maganganun da Adity tayi Junaid yana sauraronta,
Angel ce ta ɗago tana kallonsa kafin ta maida idonta kan Adity tana faɗin "my man baka so zaman lafiya ba tinda acikin ƴanmatanka har da china, mezakayi da china kuwa?..."
kafin Angel ta rufe baki Adity ta tafo da gudu ta girbe mata ƙafa sai yaraff ta faɗi ƙasi,
cize leɓɓenta tayi da

Please Login or Register in order to submit comment