Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sake cewa kayi alƙari?"" alhaji yace nayi alƙawari!!!! Faruk yace babu damuwa, Alhaji yayi godiya sannan ya tashi ya tafi,

Raihana tanaji Alhaji ya fita, da sauri ta ruga ta haye saman gado, tana jinjina wata biyu zatai a gidan nan, hawaye ya zubo mata daga idon ta, ta goge tace lallai haka maza zasu riƙa man wasan kura da rayuwa?""

tace lallai sakayya ce, an aura man aminu bana sanshi , amma shi yana so na, an shi kuma wannan an aura man shi bansan bai san ni ba, shi kuma baya so na, taf ai dama haka rayuwar take,

Bata gama tunanin ba, taji an yaye bargon data lulluɓe dashi, jikinta ne ya mutu ganin wanda ya riƙe bargon a hannunshi, sannan yace ke jaka, sauka wannan gadon a lokacin da yake ɗora ƙafarsa saman gadon kuma ko takalmin ƙafarshi bai cire ba,

Hawan gadon nan sai macen daraja kamilalliya ba irinki ba, dan tsiya da talauci ya ƙare a gidanku gadon ma baza a siya maki ba?"" to saurareni da kyau kiji duk ranar dana sake ganinki saman nan ya ɗan bubbuga ƙafarsa saman gado yace saina lalata maki fata kinji na faɗa maki,

kallon ƙasa da sama raihana tayi mashi sannan tace sannu mai kuɗin sayen gado kaci baya girman ka da ƙimarka kamar yanda na gani a tattare dakai ya wuce ace saboda wannan ƙazamin gadon ka tsaya kana wani tada jijiyoyin wuya ba,

Kuma ni nafi ƙarfin ka kirani talaka , dan duk abinda mai kuɗi yake taƙama dashi Allah yayi man nima, kuɗi kuma da Allah ya baka ai ba yawan ibadarka ko tsare kanka da rashi zina yasa aka baka su ba,

to yau ɗin nan kuma yanxun kasan ni nafi ƙarfin wulaƙanci gadonka banza, sai mi idan ban kwana akan gado ba, a gidanmu ƙasa nake kwanciyata kuma ka ganni ai ban mutu ba, kuma idan na mutu dole a cikin ƙasa za"a rufeni dani talaka dakai mai arxiki kabarinmu baya da banbanci, banbanci ɗaya ne, wanda ya gyara shi zaifi morewa a ciki idan ya shiga, amma dai a duniya ginin iri ɗaya,

wani irin halbi yakai wa raihana wanda harsa da tayi yunkurin amai, yace banza ke harkinsan mai kyau ko mara kyau?""

Raihana tayi magana cikin taurin rai tace ai idan bansan mai kyau ko mara kyau ba, yanxun ya wajabta a gareka tunda ina ƙarkashinka saika ka koyaman idan kuma kaima kan naka kamar nawa dani dakai duk sai mu koma makaranta, wani irin mari yakai mata, tace a cikin sharuɗɗan aure ba duka,

Haushi ya kamashi danshi ba mutum bane mai yawan magana kuma haka baya san magana, kallon raihana yayi sannan yace a gidanku miyasa ba"a saka ki makarantar ba?"" raihana tace dan ansan zan aureka ne, kaga nan da wata biyu na samu ilimi idan nayi gaba naje nayi aurena sai mijin ya sake maida ni makaranta, wani irin ƙululu ya tsayawa faruk a maƙoshi, haushi ya kamashi , har ya juya zai fita ɗakin komi ya tuna?"" ya dawo belt in jikinshi ya cire , raihana da sauri ta miƙe tace lalalalaaaa bari haba yi haƙuri don Allah kada ka dakeni,

jirama zan bar maka gidanka yanxun nan basai wani lokaci ba, Allah ya baka haƙuri don Allah da sauri ta sauka ta fara tattara "yan kayanta,

kallonta faruk yayi sannan yace babu idan zaki je, tunda na riga nayi alƙawari, fita yayi daga ɗakin sannan ya kulle ƙofar ta waje,

yana fita raihana tace kam Allah ya rufa man asiri, daya cicci ubana, kuma insha Allah bazan sake kwanciya a gadonka ba,

Faruk yana fita a farlo zama yayi sannan yace lallai ma yarinyar nan da gaske fa batajin magana wai zataje tayi aurw kam amma duk ranar da ta sake man irin wannan abun wallahi saina zane mata fata, tsaki yayi sannan ya miƙe ya nufi ɗakinshi,

Ita kuwa raihana saidai ta gyara kwanciya tana siffanto kamannin faruk tace kila dan yana da kyau yake wulaƙanci ko miyasa haka Oho, itama dai haka tayi ta juyi har bacci yayi gaba da ita,

***
Da safe faruk ya mance daya kulle raihana ta waje yana tashi wanka yayi ,ya shirya tsaff, sannan ya fita daga gidan,

raihana kuma tana tashi agogo ta duba taga ta makara kuma ko sallah batayi ba, da sauri ta shige toilet tayo alwallah bayan ta gama sallah ne, tana zaune a wurin taji ana taɓa ƙofar ɗakinta,

batayi magana ba, amma tanajin magana ana cewa wallahi momy taƙi ta buɗe , raihana jin an anbaci momy yasa ta miƙe da sauri har tana ganin jiri, tana matsaya ta taɓa ƙofar itama taji rufe gamm,

momy tace ina nan zai dawo ya sameni itama ta fito dan uwata, inji waye ubanta a garin nan?""

hankalin raihana ya tashi saboda bata san matsalar da zata fuskanta ba, raihana tana cikin ɗaki tayi jugum, suma su momy suna farlo sunyi jugum su suna jiran dawowar faruk,

To shidai faruk tunda ya fita harkokin gabanshi yake, ganin baida alamar dawowa yasa momy ta kirashi tace duk abinda yake yanxun nan tana neman shi yace yana zuwa yanxun insha Allah , bayan sun gama wayar ne momy tace wato ita tsinanniya hada wani kulle ɗaki kamar gidan ubanta,

raihana dai tana jin yanda wannan mata take ta ɗaɗɗake mata albarka,

suna nan jugum har faruk yaxo gida, sallama yayi sannan ya shiga cikin farlon, ƙannenshi suna ganin ya shigo bayan sun gaishe shi kuwa ya tashi ya fita, saboda baya da wasa, kuma horonshi ne, idan yana wuri basu zama dan zafi gareshi,

momy tace ina wadda za"a ɗauko ma "yar aikin?"" kai banda kake jakki kidahumi waccan jakar zaka ɗauko ma mai aiki?"" to idan har ina nunfashi babu wanda ya isa ya kawo mai aiki a gidan nan, idan baza tayi da kanta ba ta daina,

faruk yace momy ai dama wai sai kuma yayi shiru, momy tace zance banza, a gidansu wankau takeyi, da surfau ta saba da wahala kamar baiwa, dan haka kaima wankin ka da komai naka itace zata maka, banga dalilin kuma da za"asaka masu gadi tsaronta ba, ai bata kai macen da sodoji zasuyi gadinta ba, dan haka kowa ya kama gabanshi, idan taci uwarta da wahala itama ta gaji ta fece,

je kira man banzar in ganta, dan naji ta rufe ɗaki, raihana tace ikon Allah, zafi biyu kenan ƙannen miji uwar miji da kuma miji, shi kuma sai yanxun ma ya tuna daya rufeta a ɗaki, dan haka ɗakinshi yaje ya ɗauko maƙullin yaje ya buɗe ta, yana buɗe ɗakin ya ganta tsaye a baƙin ƙofa, baiyi mata magana ba, itama batayi mashi ba, ta raɓa shi ta wuce,

Tana zuwa daidai inda momy take zaune saman kujera raihana ita kuma ta zauna a ƙasa, sannan ta gaisheta, momy tabita da kallo , sannan ta kalli faruk daga nan momy bata sake cewa komai ba, shima faruk baiyi magana ba, miƙewa tayi ta fita daga farlon faruk yabi bayan ta, raihana ta taɓe baki tace Allah ya sawaƙe kujerar da momy ta tashi saman ta raihana ta ɗora kanta,

shi kuma a zuciye ya shigo farlon inda raihana take zaune ta ɗora kanta saman kujera yaje yakai mata wani irin halbi , sannan ya shaƙe mata wuya ya riƙe gam har ya miƙar da ita tsaye, sannan yace mi nace maki?"" raihana cikin kuka tace mi kace man ne?"" yace in sake maimata maki ne?"" raihana tace tom,

Nushi da halbi ya shiga kai mata ta ko ina, saida ya tabbatar tayi laushi sannan yace gado kujera bargo komai idan nawa ne, a kiyayi taɓa man ,

A wahalce raihana tace abinci kuma fa?"" faruk yace ki aika gidanku a kawo maki, ba garin kwaki bane da taliyar hausa?""

Raihana taji wani baƙin ciki ya riƙe mata ƙirji, tana so tayi ido huɗu da faruk amma baya yuwuwa, kallon ƙasa tayi sannan tace a ba gidanmu suke da ikon ciyar dani ba, amma idan kaji kai baza ka iya ba, hanya mafi sauƙi ka sauƙe man kowa sai huta,

Faruk yace an gaya maki bazan iya sakinki ba ne?"" raihana tace bance ba, idan har kana iyawa ka sawwaƙe man , tsaki yayi sannan yace idan na tashi aibazanyi shawara dake ba,

raihana tace to magana ɗaya zan gaya maka , ka daina dukana bana so, baiyi mata magana ba, ya juya zai fita, har ya kusa fita daga falon tace don Allah ka kawo man abinda zanci, ko garin kwaki ɗin ne, ina so, yanayin yanda tayi maganar kuma yaga ya wulaƙanta ta, amma abin baiyi mata ciwo ba, wato ko garin zataci, yace naji zan bada a kawo maki, sai kuma mi?"" raihana tace ba komai Allah ubangiji ya tsare Allah yasa ka dawo lafiya, kuma ina addu"a Allah ya kare maka sharri, har yabar farlon tana mashi addu"a,

Shi kuma yana fita, a waje ya samu wata plastic chair ya zauna, addu"ar da raihana tayi mashi yake tunani, tunda yake aure auren shi bai taɓa samun mai mashi haka ba, kuma ya kyautata masu sosai amma ita ya daketa ya mata gori still fatan alkairi take mashi, yace to mata kowa da irin halinshi,

a gidansu yayi waya ƙanwarshi yace ta kawo mashi abinci, da sauri, tace yaya mi kake so yace duk abinda ya samu, tace to,

Bai daɗe dayin wayar ba, sai gashi taxo ta kawo mashi abinci, a inda yake ta ajiye shi kuma ya ɗauka ya shiga ciki ita kuma ta koma gida,

Raihana dake zaune farlo ta rakuɓe a gefe tana zaune ƙasa, tana ganinshi ya buɗe ƙofar ta tashi da sauri taje ta anshi kayan hannunshi tana mashi sannu da zuwa, bai amsa ba, haka ya shigo ciki ya zauna saman kujera a inda ya zauna kusa dashi ta ajiye kayan , sannan ta fara cire mashi takalmin ƙafarshi, da safar,

Kallonta yayi sannan yace miyasa kika cire man?"" murmushi tayi sannan tace kasha iska wai, idan zaka tafi sai in sake sakama , kallonta yayi sannan yace to ga abincin nan, tace tom,

ɗauka tayi bayan ta duba, ita tunda take a duniya bata taɓa ganin wannan abun ba, kuma bata taɓa cin irinshi ba, kallon faruk tayi cikin sanyi murya tace mashi ranka ya daɗe ba"asamu garin ba?"" yace Ey anan ba"a siyarwa sai wannan kici, tace to kaifa?"" yace ns ƙoshi, tace don Allah muci mana, yace ah ah, murmushi tayi sannan tace to yiman lomar manya, sai zan cinye sauran ansar abinci yayi yaci sannan ya bata , tana ansa ta juya mashi baya ta fara cin abincin,

ta ɗauka zaiyi magana taji baice komai ba, ta juyo tace baza kace miyasa na juya ba?"" yayi mata shiru tayi dariya sannan tace banso kaga loma na ne, ko inda take bai kalla ba, yaci gaba da latsa wayarshi,

haka take tayin surutu bai bata ansa, har ta gama cin abincin, sannan ta rufe sauran tace gaskiya na gode Allah ya ƙaro buɗi mai albarka yace amin,

Tashi tayi ta nufi ɗakinta, shi kuma yana nan zaune,


da daddare raihana tayi wanka taci gayunta sosai ta fasa turare duk inda ya dace ƙamshi yakai, sleeping dress inda aka kawo mata cikin kayan da ƙanen faruk suka kawo ta saka, sannan ta ɗauki ƙatuwar hijabi ta saka ta nufi ɗakin faruk,

Sallama tayi ta shiga, shi kuma a daidai lokacin daya fito daga wanka hibajin ta m cire ta linke bayan ta ajiye ta kalli inda faruk yake tace mai gida gani, kallonta yayi ya sake kallonta yace waye yace ina neman ki,?"" tace ba kowa nice naga ya dace inxo faruk yace to ki tafi na sallameki, raihana tace kada kuma sai na tafi kaci yatsa fa, murmushi yayi sannan yace bazanyi ba, raihana tace anya ka ganni da kyau kuwa?"" kallonta yayi sosai sannan yace na gani, tace to Allah ya sani na fita haƙƙinka, banda zunibi, hijabinta ta ɗauka ta saka tace saida safe, yace to, har zata fita, ta juyo da sauri tace kai na manta, bara in tayaka shafa mai faruk da sauri yace a, a don Allah yi haƙuri, matsawa tayi kusa dashi daidai bakinshi tayi mashi muah, 💋 , jinshi yayi ya sandare daga tsaye, ita kuma ta fita daga ɗakin cikin sauri,

tana zuwa ɗakinta ta sauke ajiyar zuciya, tace wai Allah na nayi ƙoƙari fa, goge zufa tayi sannan tace kuma duk zafin ranshi yaga mace yayi shiru, kam lallai dani akai bari muga wanda zai iya rabuwa da wani nan da wata biyu, gado ta haye tayi kwanciyarta bacci mai daɗi ya ɗauketa,

a ɓangaren faruk kuwa , raihana tana fita yabi bayanta da kallo yace lallai shi yasa maza da yawa suke san auren zawara saboda ita ta goge idonta ya buɗe kuma ta mallaki hankalinta, da haka ake samun mata miye zai saka ɓacin rai?"" ajiyar zuciya yayi ya jawo wata jallabiya ya saka dakel ya haye gado, bayan ya kwanta tunanin abinda raihana tayi mashi yake, haka yayi ta juyi har bacci yayi gaba dashi,

****
Da safe raihana wanka tayi ta zuge cikin ƙana nan kaya, sun karɓi jikinta sosai, ta fito farlo dan gyarawa, ganin bata ganshi ba, yasa ta shiga ɗakinshi, yana kwance yana waya, tsayuwa tayi harya gama sannan ta gaishe shi, ya amsa dakel, kusa da gadon ta matsa ta riƙe ƙafafuwanshi tace ka gaji ne?"" gurgiza kanshi yayi alamar ah ah, tace na ɗauka ka gaji yanxun nan dana gasaka da ruwan zafi, kallonta yayi baiyi magana amma har yanxun idonshi kan dukiyar fulaninta yake, ta kula da haka, murmushi tayi sannan ta matsa kusa dashi ta durƙusa tace mi kake kallo?"" shiru yayi ya ɗauke kanshi, inda ya mayar da kan ta koma, tace miyasa zaka haramta ma kanka halal ?"" faruk baiyi magana ba, sai kallonta yake, murmushi tayi ta miƙe, tana juyin rainin hankali, itama tasan dan jan faɗa take abun, tace yanxun dai aiki yayi yawa ni zanyi shara kai kuma tunda saraki ne, sai kayi girkin abinda zamuyi break dashi,

shiru yayi baice komai ba,ganin bazaiyi magana ba, yasa ta fita taje ta fara goge goge, tana gamawa, ta dawo ɗakin, itama saman gadon ta hau , sannan ta ɗora kanta saman ƙirjinshi,

yace waike miye haka don Allah?"" tace nida mijina?"" har kace man miye haka?"" tace to kauna ce, bai sake magana ba, ita kuma bata tashi ba, har bacci ya ɗauketa., kwantar da ita yayi yaje yai wanka, kching ya nufa dan girka masu abinda zasu ci shima yunwar yane ji ,

yana fita raihana tayi dariya, ashe idon ta, biyu, tace waikai mai zafin rai fushi duka harbi da bindiga, sai nayi maganin taurin kai, wani irin tsalle tayi daga kwance sannan kuma yau a ɗakin nan zan kwana in ɗanɗana maka gumin jikina, idan ka tafi wani wuri sai kaji baka iya kwana ko ina sai a bayan raihana, dariya tayi sannan ta tafa hannunta, tace duk macen data bari namiji yake mata wulaƙanci ita taso, nidai zanyi maganin faruk cikin ruwan sayi,...............

Bayan ya gama abinda yake , ya dawo ɗakinshi raihana tanajin motsinshi tayi sauri ta rufe idonta, yana shigowa yace ke tashi an gama,

fara murje ido tayi kamar mai baccin gaske, tace waisu sodoji basu iya tada mata ba idan tana bacci?"" faruk ɗaure fuska yayi sannan yace mi kika gani?""tace to aisu naga ko "yar soyayyar nan basa yi ma matansu, tsaki yayi ya juya fita, dariya tayi sannan itama tabi bayanshi,..................
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦

*Page* 3⃣5⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

****
*KISSAR KWALIYA*:• kwalliya jigo ce ga rayuwar ma"aurata, "yar uwata kada ki rinƙa yin ɗinkuna kina jibgesu, baza kisa ba sai zaki unguwa, haba hajiyata wa zako nunawa a waje wanda yafi mijinki?""

"yar uwa idan gari ya waje da kin gama haɗa break, shiga toilet ki sheƙa wankanki, da kin fito ki shafa mai kishafa powder kiyi jagira ki shafa jan baki ko man leɓo,

Duba cikin kayanki ki jawo atamfa ko leshi ko shadda ko boyel ko material duk wanda ya samu dai, idan kika saka sai kiyi ɗaurin ɗan kwali irin wanda kika san "yan mata suna yayi, sai ki feshe jikinki da turare, kinsan sunan wannan kwalliyar?""" barka da tashi mai gida"""""

Shi kansan idan ya hangoki kin nufo shi kina taku ɗaiɗaya kamar hawainiya zakiga yanda zai tareki cikin farin ciki da nishaɗi,

Bayan kunyi break ki riƙe masa abinda yake hannunsa ki raka shi ya fita, da yamma kiyi ƙoƙarin gama komai da wuri , ki sakeyin wanka ki sake shiri sai ki gyara fuskarki kanki yasha gyara idan yafi san kitso a yarfa maki shi mai kyau ko kalaba asa duwatsu a jiki, idan mai san gyaran gashi ne, ki rinƙa yi akai akai

Kisa ɗinkin ki matsatstse mai fito da surar jiki komao naki yana girgiza da kinji shigowarsa ki maida kanki kamar wata baby , ki tafi cikin taƙon slow a hankali kina oyoo yooo, barka da dawowa mai gida,

Zakiga da saurinsa zaizo ya tareki yana maijin daɗin ganinki, yana yaba tsarin ƙwalliyarki zaiga kinyi masa kyau yaita yabawa yanajin daɗin ganinki,

Da daddare sai ki sake wanka ki cakuɗa jikinki da sihirtaccin turaruka ki shafa powder a fuskarki kinsa man baki kisa yalouwar rigar bacci saiki ɗora after dress akai ko hijabi sai ki nufi ɗakin mai gda da kinje sai ki cire after dress ɗin ko hijabinki ki zauna gefen gadon sa, "yar uwa idan mai gida ya ganki a haka yaya zaku ƙarke?"""""

*ZAWARCI*

****
*A* parlour ta sameshi zaune a ƙasa ya jingina bayanshi da kujera ya ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya, kusa dashi ta isa itama a ƙasan ta zauna ta matsa kusa dashi sosai ta jingina jikinta da nashi, baiyi magana ba, amma sai ya ɗan matsa, itama matsayawa ta sakeyi sannan ta ɗora kanta saman ƙafaɗarshi,

Tsaki yayi sannan yace wai miye haka?"" ke a dole baza ki zama ba sai kinxo kusa dani?"" sai kiyi ta kwantawa a jikina kamar wata mage?"" kallonshi raihana tayi sannan tace to don Allah ka rama mana,

Bai sake magana ba, ya zawo abinda ya haɗa na break ya fara cusawa cikin cikinshi, itadai raihana bata fara cin komai ba, kallonta yayi da wani irin yanayi wanda ni kaina bansan kallon abinda yake nufi ba, amma raihana dai tayi sauri ta rufe idonta, murmushi yayi ya kalli raihana data rufe idonta, sannan yace uhum kici mana, wasu yaudararrin hawaye ta zubo daga idonta sannan ta fara magana cikin shagwaɓa, wai ita bata iya cin abinci da kanta , faruk yace ashe ko zaki mutu da yunwa, daga nan bai sake magana ba yaci gaba da kalacinshi,

har ya gama raihana bata sake kallon inda abincin yake ba, tashi yayi ya koma ɗakinshi yayo shirin zai fita............,

yana fitowa da sauri ta tashi taje inda yake tsaye yana ɗaura agogo a hannunshi, riƙe agogon tayi taci gaba da saka mashi tana kallon hannun dan saka mashi agogon shi kuma ya saki baki yana kallonta, har ta gama, kallonshi tayi sannan tayi murmushi da gefen bakinta, tace gaskiya ka haɗe da yawa,

Baiyi magana ba, ya raɓa ta gefenta yaci gaba da tafiya, har zai fita taci gaba da cewa Allah ya kareman mijina ubangiji ya dawo dakai lafiya,

Bai saurareta ba, ya fice daga farlon, yana fita raihana tayi dariya, sannan ta tafa hannunta, ta ruga inda abincin break in yake ta buɗe tacinye shi tatas , ta tattara kayan ta wanke, dariya tayi sannan tace a bayyane, idan ya dawo sai ince na zubarwa karnuka sun cinye, murmushi tayi sannan ta tashi ta nufi ɗakinta,

Faruk kuma yana fita, gidansu ya nufa, da yaje bayan sun gaisa da momy, taƙi ta amsa faruk tambayar ko yayi laifi ne?"" momy tace idan har zata fara ansa gaisuwar shi sai ya saki wannan karuwar yarinyar, dan abin kunya ne, kamarshi da ƙimarshi da kuɗin da muƙaminshi yanda aka sanshi a duniya ya lalace ga auren ɗiyar talakawa kuma yarinya marar tarbiyya,

Faruk yace to momy duk yanda kika ce haka za"ayi , momy tace zanzo gidan ni dakaina zan korata, faruk yace to momy, kallon faruk tayi shidai bai sake magana ba, dan haka tace yaushe zaka tafi ne?"""" yace insha Allah ƙarshen watan nan, momy tace miyasa sai ƙarshen wata?"" yace wani ɗan abunda zan gama ne, tsaki momy tayi sannan tace to shikenan, kuma daga yau kada ka sake zuwa gaisheni na faɗa maka, faruk yace momy miyasa?""

tace haka nan , idan kuma kazo ba tare dani nace kaxo ba, akwai matsala dan haka sai ka kiyaye, faruk yace to, momy tace tashi ka tafi, miƙewa yayi bayan ya miƙene yaɗan risina sannan yayi mata fatan alkairi, bata sake magana ba,

Faruk ya fito duk baiji daɗi ba, tunda shi baisan abinda yayi ma momy ba, haka ya nufo gida cikin damuwa,

raihana bayan tafiya faruk tana shiga ɗaki, kwanciya tayi, ta jawo wayarta, farida ta kira duk ta rantafa mata halin da suke ciki, farida tayi dariya sannan tace ki ƙara zage damtse kinji hajiyata, kuma kada kiji tsoron komai yau ki kwana a ɗakinshi, kamar dai yanda na faɗa maki kinji ko?"" raihana tace tom, amma nidai kunya nake ji wallahi sai ya ɗauka kamar da gasken ni banda kamun kai ne,

farida tace yarinya rufa ma kanki asiri nemi mafita tun kafin wata 2, raihana tace to Allah ya shige mana gaba, farida tace amin, shawara ta ƙara bawa raihana tare da ƙara bata ƙarfin guiwa, godiya raihana tayi sannan ta kashe wayarta,

Tana nan tana ta nunani iri iri, har bacci yayi gaba da ita, baccinta take cikin natsuwa da kwanciyar hankali, shi kuma faruk bayan ya dawo shima ɗakin raihana ya shigo,

hango raihana yayi saman gado kwance tana bacci, yana so yayi mata wulaƙanci amma saboda tana mashi biyayya bakin iyawarta yasa bai tasheta ba, bare yayi mata maganar tahau mashi gado, parlour ya zauna,

raihana kuma ƙarar wayarta ta tasheta, ganin mai kiranta yasa ta tashi zaune da sauri, k"b, ta faɗa neman mi kake man kuma?""" tsaki tayi ta kashe wayar baki ɗaya,

Miƙewa tayi ta shiga toilet alwalla tayo tayi sallah la"asar, tana gamawa ta fita farlo, a daidai lokacin da faruk yake shegewa ɗakin shi, bin bayanshi tayi itama ta shiga,


yana shiga kayan jikinshin ya fara cirewa ya rage daga shi sai gajeren wando, towel ya ɗauka zai shiga toilet, raihana tace sannu da zuwa, bai amsa ba, ya shige toilet, dan ya lura tana neman mashi problem a rayuwarshi,

ganin ya shige baiyi magana ba, yasa itama ta koma ɗakinta, itama wanka tayi ta shirya cikin ƙana nan kaya, sun karɓi jikinta sosai, tana gamawa ta tafi ɗakinshi, tana zuwa shi kuma yana fesa turare, yana gamawa ya ajiye, raihana ta ɗauka itama ta fesa, shi kuma fita yai yabar ɗakin, itama fitowa tayi,

Farlo ta nufi wurinshi, wani irin kallo yayi mata wanda yasa ta kasa ƙarasawa, tayi tsaye sai dabur dabur take, ƙafeta yayi da idanuwanshi masu ba mutane tsoro, gabanta ya fara faɗuwa, miƙewa yayi yaje kusa da ita, taja baya shima matsawa yayi haka sukayi tayi har ta dangane da bango,

Kallonta yayi sama da ƙasa, sannan yace daga yau idan na sake ganinki ɗakina zakiji a jikinki na faɗa maki, wata zufa ta keto mata, ta haɗiye miyau dakel, sannan tace tou,

Cikin tsawa yace wuce kiba mutane wuri, da gudu ta wuce tayi ɗakinta, tana zuwa saman gado ta haye ta fara ihu tana kuka, wai ita miye laifinta ?"" dama haka rayuwata take?"" daga kawai an aurota bada ixinin mutum ba kawai komai idan tayi batayi daidai ba, sai ta sake fashewa da kuka,

Wayarshi ya fiddo yayi "yan latse latsenshi sannan ya kara a kunne, magana ya fara , kamal yanxun zan wuce , raihana dake ɗaki taji faruk na cewa zai wuce da gudu ta fito kamar mahaukaci tana kuka, tana shigowa cikin farlon tana ƙoƙarin isa inda faruk yake zaune da uniform in sojoji jikinshi, taja tayi turus wani irin tsoro taji ta kasa isa wurinshi, ta juya zata koma ɗaki , murmushi faruk yayi sannan yace zo,

juyowa tayi amma bata tafi ba, ta tsaya, sake cewa yayi zo nan nace, raihana ta kasa matsawa dan yayi mata wani irin ƙwarjini, a ranta tace haka faruk yake,?"" juyawa tayi ta sake kallon wurin tunaninta kikla

Please Login or Register in order to submit comment