Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

umma, gwaggo tace saida a mutu da yunwa""" raihana dai bata sake magana ba, ta koma ɗaki madubi ta ɗauko tana kallon yanda gwaggo taci ma fuskarta mutunci,

Allah yayi man sakayya haka rainaha kawai ta faɗa , ta koma ta kwanta, wani bacci wahalar ya ƙarayin gaba da ita,,,,,,,,,,


💦💦💦
*zawarci*
💦💦💦

*R*aihana tashi kiyi sallah mana, umma ce take tashin raihana , a gajiye raihana ta fara buɗe idanuwanta da sukai mata nauhi, hawayen wahala suka fara safa da marwa a idonta, umma tace ki tashi kiyi sallah nace, a daidai lokacin da umma take cire hijabin jikinta,

A gajiye raihana ta miƙe ta fito, buta ta duƙa ƙofae ɗakinsu ta ɗauka, gwaggo sai habaici take, tsaki raihana tayi sannan tace idan dai kare yana haushi idan bai samu aboki ba ya zama mahaukaci, gwaggo tace uwarki waccan tana nuna ɗakin su to itace mahaukaci, kuma itace karya, dariya raihana tayi sannan tace ga irin halin nan kinayi , gwaggo tace shegiya mai baƙin hali, raihana tace ai a turbar kika ɗrani tun ina yarinya,

Gwaggo tace zawarar banza, raihna tace , Allah ya kaddara man kuma kema dake da ahalinki Allah ya ɗora maku jawarci kuji abin idan daɗi ne,

Gwaggo tace ni kike cewa "ya"yan na zasui *zawarci*? Tsaki raihana tayi , bata sake magana ba ta fara alwalla,

Gwaggo sai masifa take, ala dole wai raihana tace za"a sako mata "ya"ya daga gidan aure, taci gaba d cewa ke kaɗai kika zamo haka kuma kece kaɗai zaki lalace haka , a daidai lokacin da raihana ta gama alwalla tace tare dai zamu lalace mai faɗa da ɗiyar cikin ta, ki kashe mata aure dan ki aura ma ɗiyar aminiyarki, sai Allah ya maki abinda baki zato, tana faɗin haka ta shige ɗakin su,


Gwaggo kuma taci gaba da cewa anje an kashe aure uban waye yasa tun farko baki san mijin,?"" kuma har ki mutu baza ki samu wanda yakai darajar aminu ba, yar banza lalata,

Raihana dai bata sake magana ba, gwaggo ko banda tsinuwa da la"ana babu abinda take yi,,,,,,,,


Bayan raihana ta gama sallah , uma tace mata ga abinci can badiyya ta aiko maki dashi, kuma tace zata kawo maki wanki idan Allah ya kaimu, raihana tace tou, ɗauko abinci tayi ta matsa kusa da uma tace suci, ua tace ta ƙoshi, haka raihana ta caka hannu ta fara cin abincin,

Tana cin abinci umma tace raihana, kada ki kuskura ki sake cewa gwaggo ta kashe maki aure, abincin data ibo zata kai bakinta ta fasa kaiwa, tace umma wallahi itace ta kashe man aure, umma tace haka Allah ya ƙaddara kada ki kuskura ki sake faɗin haka kinji na faɗa maki ko?"" raihana tace Eh, umma tace gama cin abinci yau ki ƙarasa man labarin nan, murmushi raihana tayi tace to,


Haka tayi ta cin abincin bayan ta gama, ta fita ta wanko hannunta ta dawo, maganin da umma ta siyo mata ta miƙa mata, bayan tasha maganin ne, tace umma zan fara murmushi raihana tayi sannan taci gaba da cewa...........................




*MEELAT MUSA* ke cewa ku kasance tare dani!!!
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦

*Page* 1⃣1⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

🔵🔵🔵🔵🔵
🔵🔵🔵🔵
🔵🔵🔵
🔵🔵
🔵 *ZAWARCI*

*H*ar yanxun yana zaune inda raihana ta barshi a farlo , ya ɗan zame saman kujera ya kwanta, lallai wannan wane irin fitina ne?"" yana da mata amma shida babu uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, tsaki yayi ya miƙe ya nufi ɗakin shi,

Yana zuwa babu ɓata lokaci wanka yayi ya shirya ya fito fess abunshi , ɗakin raihana ya dawo, bayan ya shiga ya sameta kwance saman gado, shima saman gadon ya hau, da sauri ta matsa da baya, hannunshi yasa ya jawo ƙafarta zuuuu ya matso da ita kusa dashi,

Saman ruwan cikinta ya hau, ya matsar da fuskarshi kusa da tata, daidai bakinta ya ɗora nashi, idanuwanshi suna kallon nata, sannan yace wallahi kiji tsoron Allah idan har kika kuskura a wannan halin kika mutu zaki haɗu da fushin Allah nine mijinki so da kauna yasa na aureki ki baki sona raihana ya kamata wani abun ki riƙa ragewa saboda rayuwa,

Wai miyasa ma baki sona?""" shiru raihana tayi saboda bata da dalili, riƙo haɓarta yayi da hannu, ya haɗa bakinshi da nata, da sauri ta fizge bakinta ta jawo wani kallabi ta goge bakinta , dariya yayi yace kyamata kike?""" raihana tace bana kyamarka nidai kawai bakai man ba,

Yace miyasa ban maki ba?""" a daidai lokacin da ya sauka daga saman jikin ta, raihana tace nifa ban taɓa ganinka ba, duka sau nawa na ganka aka ɗaura mana aure dakai?""" Aminu yace to miye aibuna?"" raihana?"" ya ƙarashe maganar yana kwantar da kanshi yayi yanayin tausayi,

Yace kiji tsoron Allah , ubangiji yana fushi da matar da take ma mijinta irin abinda kike man, ki daina abinda kike tun kafin ki haɗu da fushin Allah,

So nawa aka aurar da mace ga namijin da bata taɓa gani ba?"" kuma suna zamansu hankalinsu kwance, kiyi haƙuri ki soni kinji raihan?""" wallahi zan jiyar dake farin ciki?"" ya ƙareshe maganar hawaye yana bin fuskarshi,

Ajiyar zuciya raihana tayi sannan tace to kayi haƙuri duk abinda nayi maka insha Allah bazan sake ba, yace yawwa ko kefa?""" haka yayi ta mata nasiha, raihana tanajin nasiha tana bin jikin ta, amma fa har yanxun baiwai dan tana san Aminu ba, kawai saboda yana faɗi nata nau"in azabobin da Allah zaiyi ma wanda bata biyayyar aure yasa jikin ta yayi sanyi,,,,,,,

*** *** *** ***

*B*ayan haka da sati biyu, wata rana gwaggo ta kawo ma raihana ziyara da ita da aminiyarta *Ladi* raihana tayi farin ciki da zuwansu sosai sabida haka taje ta kawo madu ɗan abun ci da sha, bayan sunci sunsha, gawaggo tace raihana niko na ganki duk kinyi baƙiƙirin kin rame,

Murmushi raihana tayi sannan tace babu wani abu da nayi gwaggo, kawai dai dan kin daina gani na kike ganin haka, ta ƙarasa maganar tana taɓe baki, gwaggo tace to ya zaman naku yake?""" raihana tace *alhamdulillah* gwaggo tace amma gaskiya yaron nan yana cutar dake, raihana tace babu wani cutuwa muna zaune lafiya,

Gwaggo tace ai kece kike zaune lafiya dashi shi kwata kwata baya kaunarki, cewa yake daya samu yayi maki ciki zai sakeki ya auro wata, tunda dama baki sanshi, raihana ta ɗago ta kalli gwaggo cikin zaro idanuwa, raihana tace a,a, gwaggo Aminu bazai man haka ba, gwaggo tace baza ki gane ba, aike yarinya ce, tashi muje ladi, har yanxun akwai kuruciya a kanta,

Raihana tana ganin gwaggo ta mike tace gwaggo tsaya, gwaggo tace ai ina faɗa maki gaskiya bakya gani ne, raihana tace ni wallahi yana so na, kuma har kuka yake saboda yanda yake kauna na, gwaggo tace yaudara ce, ba sanki yake ba, raihana tace tou Allah dai ya sawaƙe, gwaggo tace amin, haka suka rantafa ita da ladi suka bar gidan...............

Fitar gwaggo da larai basu zame ko ina ba, sai gidan uwar mijin raihana, bayan sun gaisa gwaggo tace kin gane ni?""" maman Aminu tace na ganeki mana, gwaggo tace dama maganar yarinyar nan ne, dama maman Aminu bata san raihana, tunda taji labarin bata kaunar Aminu taji kuma tace itace ajalinsa, wannan dalilin yasa ta tsani raihana,,

Gwaggo tace dama cewa nayi tunda dai har yanxun naga ta kasa haƙura su zauna lafiya ɗiyar ƙawata na kawo dama ki haɗasu suyi aure, ita dama tana kaunar Aminu , tana sanshi tun tuni, maman Aminu tace to ai dama ya kwana da sannin bana kaunar yarinyar nan dole ya rabu da ita tunda ba tare aka haifesu ba,

Haka gwaggo taci gaba da zuga maman Aminu, daga baya suka tashi suka tafi daga gidan,

Suna fitowa gwaggo tace k sai in bari ta zauna a gidan can?"" duk tafi su bushira gidan miji, wato ɗiyarta kenan, da sauran "yan uwanta, tace shegiya sai ta fito wallahi, kuma babu ita babu ƙara auren mai kufi saidai ta samu talaka ta aura, haka sukaci gaba da magana suna kulla makircin su, daga baya suka rantafa suka nufi gida.................................,


Raihana zaune a gaban Aminu, tace Aminu laifin mi nayi maka?"" har kake burin kayi man ciki ka sakeni?"" cikin rashin fahimta yace ban gane abinda kike magana ba?"" tace abinda kaje kana faɗi a gari shine yake dawo man!!!

Aminu yace ƙarya ne, duk wanda yace bana kaunarki ƙarya yake kinji wallahi ina sanki, yakai hannunshi ya jawota, ya rungumeta, sannan yace kuma kike maganar zan maki ciki in rabu dake ai kinga har yanxun ban taɓa maki wani abu ba ko?""" raihana tace tou nidai na baka haƙuri akan abinda ya faru kuma nayi alƙawarin duk abinda nake maka na daina a shirye nake zama dakai kuma duk abinda baka so insha Allah na daina, yace to Allah yayi maki albarka, raihana tace amin,

Haka rayuwarsu taci gaba da tafiya cikin kula da juna tare da nunawa raihana kauna, itama ganin har yanxun Aminu baiyi mata komai ba yasa ta saki jiki............


Bayan wasu kwanaki gwaggo taje taja aminiyarta, ladi suka koma gidan maman Aminu, tace ga hoton yarinyar da take san ɗanta, itama da yake irin tunaninsu ɗaya da gwaggo ta karɓi hoto tare da ɗaukar ma gwaggo alƙawarin cikin satin nan za"a saki raihana, haka sukai godiya sukai tafi...............


Suna fitowa gwaggo tace ma ladi dan zalincin malam wato baban su raihana, tace munafikin Allah duk ni bai samo ma "ya"ya na masu kuɗi ba, sai raihana ya sami ma, tahe gidan kuɗi taci daɗi, wallahi yanda basu auri mai kuɗi ba, itama haka zata dawo ta samu talaka ta aura,

Niko nace wannan baƙin ciki da miye yayi kama?""" da ɗiyar mijin gwaggo wai gara ɗiyar aminiyarta!!!!!!


Allah ya sawaƙe,


A madadin *Ameenci writer's* meelat musa ke cewa ku kasance tare dani.................................
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦

*Page* 1⃣2⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

🔵🔵🔵🔵🔵
🔵🔵🔵🔵
🔵🔵🔵
🔵🔵
🔵 *ZAWARCI*

*Wannan shafin naki ne , ƙawata ASMEENAT XEEYAN amana takai maki ƙawar arxiki*

*** ****

*T*ou anyi haka bada daɗewa ba, ita dai *Raihana* ita da Aminu zaman lafiya abinsu suke, yana lallaɓata saboda ya lura tana da saurin ƙufula amma tana sauka kuma idan ya mata nasiha tana ɗaukar abinda ya faɗa mata,

** **
*R*aihana da Aminu zaune suna cin abinci, a farlo, maman shi tayi sallama ta shigo, cikin farin ciki da nuna kauna raihana tayi mata sannu da zuwa, bayan mama ta zauna, raihana ta gaishe ta, mama tace rufe man baki baƙar munafika, gafara ki bani wuri ba wurinki nazo ba, wurin ɗana nazo,

Inda Aminu yake ta kalla sannan tace, idan kai ɗana ne, kua haihuwar da nayi maka ka gode ta, tunda nake ban taɓa neman wani abu a gareka ba amma yau ɗin nan basai gobe ba inso ka saki wannan yarinyar, ta nuna inda raihana take zaune, da sauri raihana ta ɗago kai ta kalli mama ta durƙusa tace mama kiyi haƙuri don girman Allah,

Mama tace rufa ma mutane baki baki, shima uban naki dayaje ya jawo man ɗa ya haɗa dake dan ya rasa mai jajibarki , an rufa maki asiri kina ma mutane wulaƙanci,

Ta daka ma Aminu tsawa tace wallahi sai ka saki ɗiyar nan idan ba haka ba na tsine maka albarka ta bika tsinuwar har cikin kabarinka yaci da wuta balbal,

Aminu yace kiyi haƙuri mama ina santa, kuma tana so na, raihana aidai muna san juna ko?""" murmushi raihana tayi tace ina sanka, mama tace ni zakai ma bariki?""" ke dan bindin uwarki baki kaunar ɗana yau basai gobe ba sai kin bar gidan kuma alkur"an sai Aminu ya baki rasiɗi zaki tafi,

Wato yanxun kika gane mahimmanci ɗana , kina tsoron ya sakeki ki koma gidanku abinda zaki ci sai yayi maki wahala,

Anan bayi ɗaya naki ke kaɗai amma acan sai kin jera layi da uwarki, haka mama tayi ta cin mutumcin raihana da gorin arziki,

Saida tayi wanda ya isheta sannan tace na rantse da girman Allah idan baka tashi ka saki yarinyar nan ba wallahi zan tunɓuee maka albarka ɗan banzan lalataccen nan, mama irin matan nan ne masu masifa wanda basu san ƙaddara ba kuma basu san tausayi ba, haka taci gaba da ebe ma Aminu karama, da faɗin ta irga ukku idan bai saƙeta ba sai ta ɗaɗɗake mashi albarka sannan kuma saiya saki raihana kuma idan tayi mashi baki ya lalace a gidan duniyar nan,

Cikin kuka raihana tace kiyi haƙuri insha Allah babu abinda zai sake faruwa kuma wallahi lafiya qalau muke zaun........ Bata ƙarasa maganar ba mama ta sharara ma raihana mari tace idan na sake jin maganarki wallahi sai naci uwaki,

Raihana ta sake ceqa kiyi haƙuri mama, wani harbi a ciki mama takaima raihana wanda yasa lunfashinta ɗaukewa na wani lokaci,,,,,,,,,

Haka Aminu ya tashi dan mama tace ɗaya, ɗakinshi ya nufa ya ɗauko memo da biro, ya dawo lokacin mama tace ukku da sauri ya durkusa gabanta yace mama ki rufa man asiri wallahi ina san raihana, tace uwarka ce raihana, kana kaunarta bata sanka yace mama zata soni wata rana wallahi , tace kai rufe man baki sakaran banza bata kaunarka haka take faɗi a gari,

Sakarta goben nan za"a ɗaura maka aure sakarta nace dan ubanka ta ƙarasa maganar cikin tsawa da bala"i, haka Aminu ya darkaka ma raihana saki, wanda bata buɗa ba, yana gama rubutawa ya fashe da kuka, mama kuma ta nannaɗe ta wurga ma raihana takarda, sannan ta tusa ƙeyarta ta fita daga gidan dan tace ko tsintsiya babu ɗan iskan daya isa ya ɗauka a gidan nan,

Ajiyar zuciya raihana ta sauke sannan tace nidai iya wannan kaɗai na sani,

Umma tace to kinga ba gwaggo ta kashe maki airw ba, Allah yasa zamanki dashi ya ƙare ki ɗauki ƙaddara sai kiyi addu"a Allah ya zaɓa maki wanda yafi shi alkairi, raihana tace Amin, Umma tace muje muyi sallar la'asar,


Da daddare bayan baba ya dawo ya kira umma da raihana, yace, wato kece kike ɗaure ma yarinyar nan gindi tana iskanci ko?"" Umma tace mi kuma nayi yanxun?""" baba yace banda iskanci tace yusufa idan yana santa sai ya samo miliyan biyar baba yace wannann wane irin zance banza ne?"" Umma tace bansani ba amma a kirata a tambayeta danni jiya tace man yusufa ya turo kuma haka nazo na faɗa maka,

Baba yace kirawo man ita , Umma ta ƙwaɗa ma raihana kira, bayan taxo baba yace ya kukai da yusufa ne?""" raihana tace nidai nace mashi ya turo shine yace man sai ya samu miliyan biyar zai aureni , dan yaga ni jibgaro ce aurena na farko ma sadaka ka bayar dani, kuma yanxun an sakoni, wai idan zan jira ya samu miliyan biyar sai yaxo ya aureni dan yasan har ya tara kuɗin ban samu mai aurena ba,

Wannan wace irin sakarar magana ce kike faɗi?"" raihana tace ai baba da gaske nake ni da farko ma da yayi maganar na ɗauka wasa yake man, baba yace barshi dani yake zancen jeki, Allah ya zaɓa maki alkairi raihana tace amin, ta miƙe ta nufi ɗakinsu,


Bayan tafiyar raihana baba yace ma umma amma daga ita har yusufa na kasa gane waye mai gaskiya, shi yace itace tace ya samo miliyan biyar ita kuma tace shine, Umma tace to abundai sai addu"a, gwaggo daga ɗaki tace babu wani addu"a kawai ya turo a ɗaura aure basai an tsaya wani dogon zance ba, baba baiyi magana ba, haka umma umma tashi tayi ta nufi ɗakinta,,,,,

Tsakar gida gwaggo ta fito tace lallai bari inje ince ma yusufa ya aiko saboda kada ayi ma yarinya baƙin ciki, ga inda zatayi aurenta ta huta har muma muje muɗansha jar miya amma ake mana hassada?"""

Baba yace to waye ya aikeki?""" gwagho tace ai basai an aikeni ba saboda tana ɗiyata shiyasa zan miƙe kafin a ɗurkusar da mu, tsaki baba yayi sannan yace to ban aikeki ba, haka ta dawo gida taci gaba da mita da tsegumi.....................


Raihana kuma a ɗaki dariya kawai take mara sauti, saboda haka ita kaɗai tasan abinda take ma dariya , tana gama dariyarta tayi kwanciyarta bacci ya kwasheta saida safe nima nace mu tashi lafiya...................................................
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦

*Page* 1⃣3⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT* 🌹

***

*T*unda Raihana tayi sallah asuba bata koma bacci ba, haka taci gaba da wankin da aka kawo mata jiya, wanki take sosai har antsi ya fito, sai lokacin ta sassauta saboda ta rage wankin sosai, hijabinta taje ta ɗauko ta fita daga gidan,

Tana fita bata sharce ko ina ba sai shagon shamsu, bayan sun gaisa tace don Allah ya bata garin tuwo anjima zata kawo mashi, yace gaskiya bazan bayarba, raihana tace miyasa don Allah idan na tambaya baka bani laifin mi nayi maka don Allah,?"" yace haka nan bazan bayar ba, murmushi raihana tayi sannan tace to Allah ya sawaƙe, bai sake magana ba, saboda haka raihana ta juyo tayo gida..............................

Bayan ta dawo ta tadda badiyya ta kawo mata wankin da tace zata aiko, kuma sauƙi ɗaya an aiko mata da kuɗin wanki , don haka ta karɓa ta tura yaron ya siyo mata gari da kulili, ya karɓa ya tafi, ita kuma taci gaba da wankin kuma har yanxun bataci komai ma cikinta ba,

Bayan wani lokaci ya dawo ya kawo mata, ta jiƙa garin, ta kwaɗa , umma takai ma umma tace ita bata cin garin kwaki, raihana tace umma kiyi haƙuri kici don Allah abunda ya samu ai dashi ake aiki a rayuwa, umma tace kai gaskiya bana ci, haka raihana ta zauna ta shafe garin tatas ta bulbili ruwa a jarka tasha, fitowa tayi taci gaba da wankin ta, don yinin ranar haka ta yini tana wanki, harna badiyya duka ta haɗa ta wanke fess , bata gama wankin ba sai bayan salƙar isha"i, Allah ka raba mu da wahala duniya da lahira ameen,,,,,,,,


Lokacin da ta gama wanki wanka tayi , tana kwanciya don hutawa gwaggo tace ai lallai sai ta fito tazo ta aiketa, raihana bata da yadda zatayi saboda baba yana nan haka ta fito, a tsakar gida gwaggo ta nuna mata wani rabin buhun gero tace wai ta ɗauka takai ma ladi aminiyarta,

Raihana tace to banda abinki gwaggo ina ni ina ɗaukar wannan?"" gwaggo tace iye?""" lallai sannu ɗan wanke kinfi ubanki kinfi uwarki, to udan baza ki iya ɗauka ba sai ki raba biyu idan kinje kin dawo sai kikai sauran, raihana tace indai samu yara sukai kawai sai inbi bayansu idan mun dawo in biyasu, gwaggo tace wallahi babu yaron da zaki ɗora ma yaje ya gudu da geron nan,

Baba dai baice komai ba, saboda haka gwaggo tace duk ubanda ya tsaya mata lallai ta ɗauki geron nan takai shi, wasu hawayen baƙin ciki ya zubo mata, matsawa tayi ta ɗauki wata katuwar rober ta rage geron ta ɗaure sauran ta ɗauka ta tafi,

Saida takai geron sannan ta dawo ta kwashe sauran takai , bayan ta dawo gida , har zata shiga taga yusufa tsaye a ƙofar gida, ko inda yake bata kalla ba, har zata shige gida yace raihana ina magana, cikin fushi tace ji nan malam fita harkarta ina kuma kada in sake gani ƙafarka a ƙofar gidan nan idan ba haka ba saina sa an kulleka,

Dariya yayi sannan yace haba raihana miye yayi zafi haka don Allah?"" raihana tace kawai idan kana so mu daidaita dakai kada ka sake zuwa nan gidan harsai na neme ka?"" yusufa yace to babu damuwa ina jiranki, tace yawwa sai kaji ni, ta shige gida shima ya juya ya tafi...............,,,,,,,,,,,

Tana shigowa gida gwaggo tace taje ta siyo mata maganin sauro, raihana ta karɓa ta fita, a ranta ita kaɗai tasan yanda take ji, wannan wace irin rayuwa ce?"" komai itace zatayi kuma dan ɗaukar alhaki aikenma baza a haɗa mata ba sai guda guda kamar ƙaramar yarinya?""" lallai idan har haka *zawarci* mara galihu yake baiyi ba,

Sallama tayi ta shigo gidan, bayan ta bawa gwaggo maganin sauro har zata shiga ɗaki gwaggo tace rahanatu, nace "yar uwarki bushira tana can babu lafiya yanxu aka zo aka faɗa man idan Allah ya kaimu ai sai kije ki zauna kwana biyu kafin ta samu sauƙi,

Raihana tace miyasa saini zanje?"" gwaggo tace to waye kullenki?"" tunda baki da aure ai sai kije """"" raihana tace to bazanje ba, idan ciwon yayi tsanani a dawo da ita gida.........

Baba dai yana zaune a gefe baice nasu komai ba, raihana ta shige ɗaki gwaggo kuma taci gaba da mita.....................,,,,,,,,,


****

Da safe misalin 9:30am raihana ce take ta faman haɗa kayan wanki data wanke tana kulleqa kiwa nashi, haka duk ta haɗasu ta ajiye ma kowa nashi gefe ɗaya,

Wata yarinya ce ta shigo ta kawo murji taliya, raihana ta karɓa, sannan tace anjima ta dawo ta karɓa, yarinyar tana fita raihana ta fara murhe taliyar, bayan ta gama ta ɗauko wankin kayan baba da gwaggo tace ta wanke tun jiya,

Tana gama wanki ta tafi ɗaki ta kwanta don huta ma rayuwarta,

*T*ana kwanciya abinda ta fara tunani shine, a gidan Aminu bata wanki saidai yakai a wanke mata amma yau itace take wanke kayan wasu , Allah sarki rayuwa da tayi haƙuri ta zauna mijinta yana santa amma ita sai wulaƙanci take mashi yanxun ga yanda takaita, sai tayi wahala sannan take samun abinci taci, sannan kuma wani lokaci sabulun wanka tsaye yake mata, idan tayi wanki kuma ta samu kuɗi dasu take samu taci ɗan abu mai ɗan text, abunda take tunani shine yanxun kuma da a gidan haya suke ko ya zasu ƙare?"""

Lallai wato duk inda Allah yakaika shi hakuri nasara ne na rayuwa, duk da tayi haƙuri lallai da bata kai wannan matakin ba, hawaye ya zubo mata daga idonta, ajiyar zuciya ta sauke sannan tace yanxun kuma ko waye zai aure ne?"""""" shin yana da kirki?"" zai soni kamar aminu?""" gidan rufin asiri ko akasin haka?"" tayi ta jero ma kanta tambayar da babu amsa,

Allah sarki da banda mahaifiya a gidan nan lallai da bansan yanda rayuwata zata kasance ba, wai ance ana sallama da raihana!""" maganar wani yaro ne ya katse mata tunani.!!!""" daga ɗaki raihana tace je kace waye?"""" ba"a daɗe ba yaron ya dawo yace wai ance *honoravel* ne, da aauri raihana tace je kace tana zuwa,

A gaggauce raihana taje tayi wanka ta fito taci kyau cikin wani lallausan material ta haɗu iya haɗawa, sannan ta ɗauko turare ta feshe jikinta dashi kamshi yace salama alaikum, ita kanta da ta kalli kanta a madubi kasa gane kanta tayi, saboda haka tayo waje,,,,,,hhhhhhhhhhh

*zawarci*

*A* zauren gidansu tana ƙoƙarin fita taji yace barka da war haka gimbiyar mata!"""" kallo ɗaya raihana tayi mashi sannan ta ɗauke kanta, tana ƙoƙarin fita daga zauren ya sake magana bata sake bi takanshi ba tayi waje...............

Fitar ta ƙofar gida ta ware idanuwanta iyakar ganinta bata ga kowa ba, haka ta haƙura ta dawo, tana shigowa ciki zata wuce yace ranki ya daɗe ai nine na aika a kiraki!!!

Kallonshi raihana tayi ta sake kallonshi ƙasa da sama sannan tace kaine waye?"" yace honarabil tsaki raihana tayi sannan tace to ya akayi?"" murmushi yayi zai fara rattafo sirrin zuciyarshi raihana ta dakatar dashi ta hanyar ɗaga mashi hannu, saurara yanxun fita zanyi ka bari wani lokaci ka sake dawowa , tana faɗin haka ta ƙutsa kanta tayi cikin gida,

Tana shiga cikin gida tace Allah ya isa ɗan iska nama ɗauka honorabil ɗin gaskiya ne, shege na ɓata gugar kayana na ɓata turare na a banza, tsaki tayi sannan ta sake tuno ma yanda ta ganshi

Ƙutuƙutu yake kamar an tono shi daga cikin rami, tace ɗan iska baka da arziƙin takalmi mai kyau sai silifas, tsaki tayi sannan tace wato idan dai kai *zawara* ne shara da bola sai yazo wurinka, da sauri ta shiga ɗaki ta cire kayanta, tana ma honarabil Allah ya isa...............,,,,,,,,


*** ***

*Y*au gidan su *raihana* babu kwanciyar hankali saboda ɗiyar gwaggo tayo yaji, babbaf ɗiyarta, mai suna *fiddausi* tunda fiddausi taxo ta faɗa ma gwaggo abun ya ɓata mata rai sai safa take da marwa a tsakar gida tana tsine ma mijin fiddausi, lallai yaufa an taɓo gwaggo abun babu daɗi,

Ƙorafin da fiddausi take mijinta baya bata abinci sannan kuma sai yayo shaye shaye yayi mata shegen duka, ga neman mata kuma ƙarshen wulaƙanci a gidan ta yake kawo su,

Please Login or Register in order to submit comment