Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daddafa har na haihu ɗaya, bayan na haihu iskanci yaci uban na da, idan ya kawo man pampers sai in ɗauka in siyar ga shige shige maƙota, bana zama gida wannan abun yana mashi ciwo , ga rashin kunya da rashin gurmamawa ,

Tsakani na da "ya"yanshi sai zagi sai tsunuwa yana nuna man rashin jin daɗin hakan amma dan nasan baya so kullum sai na nayi ,


Muna cikin haka ne, wata maƙociyarmu ta kirashi tace mashi taga yana ƙokarin kyautata man amma bana godewa saboda haka yazo ta bashi ɗiyarta, ta ƙara da cewa ai duk macen da ƙoshi yai mata yawa iskancin da take baya kalluwa, shi yasa maza da dama suke tafiya su auro yar ƙauye , duk abinda zata ba miji saita rusuna sannan kuma ga biyayya amma su matan binni sai raini da girman kai suka iya,

tace ka auri ɗiyata ina da yaƙinin zata maka biyayya, kuma ni bazata fito cikin unguwa ta wulaƙanta ka ba, ko a cikin gida baza tayi maka ba, bare har ta fito a idon duniya ta maka rashin kunya,

Haka ya amince da buƙatar ta, haka aka tsayar da lokacin aure , aka ɗaura mashi aure da ita, haƙiƙa nayi tashin hankali nayi bala"i nayi masifa amma a banza, tana shigo babu sanya taci gaba da kyautata mashi

Ladabi biyayya aka barni da haukan banza, ina da ciki na biyu, na kama matarshi nayi mata shegen duka yana dawowa shima na rufe shi da masifa, haka ya gaji da bala"ina ya sakeni saki ɗaya, nace mashi saina samu wanda yafi shi yace man baya baƙin ciki, Allah ya bani inma auri shugaban ƙasa baya man hassada,

Haka na dawo gida ga mahaifiyata babu rai, matar babana baba yace mata tunda abun iskanci ne abuna inji baba miyar gidan nan kada a sake kaɗata da gishi sai naci ubana tunda dai *zawarci* na zaɓa, raihana wahala ta isheni na rasa inda zan saka rayuwata, ajiyar zuciya raihana tayi sannan tace kema banda abinki sai a sakeki kuma sai ki kwaso "ya"ya jagal jagal ki taho?

wannan rayuwar babu wanda yake san ɗan wani, shawara ɗaya da zan baki yaran nan ki mayar dasu wurin ubansu, kima ji da kanki ko Allah ya fito mana da mazaje muyi auren mu,

zulaiha tace to zan mayar dasu, raihana tace to yanxun shi ina tsohon mijinki na abuja?"" zulaiha tace yana can , kuma har yanxun baiyi aure ba, raihana tace miya sa baza ki koma wurin shi ba?"""

tace ai baya kirana, raihana tace kina da number shi?""" tace banda ita, raihana tace yanxun dai ki fara maida yaran nan wurin ubansu tunda duk maza ne sai musan mafita, zulaiha tace , to

haka sukayi ta "yar firarsu daga baya ta tashi ta goya yaronta ta kama hannun ɗayan tayi ma raihana sai anjima, a bakin zauren gidansu raihana ta rakata sannan ta dawo,

Raihana ta dawo gida tana ta nunanin wannan urin hauka na zulaiha, tsaki tayi sannan taje tayo alwalla don an kira sallar magrib,

hmmm Allah dai yasa mu dace,
💦💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦

*Page* 2⃣0⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

*****

*R*aihana tana shiga ɗaki zama tayi a gefen katifa, hawaye yaci gaba da ambaliya daga cikin idanuwanta, kuka take sosai tana addu"a Allah ubangiji ya bata mijin tayi aure wannan musifa ta isheta, shin wai da tana da ƙanne ya zatayi?"" lallai da ba ƙaramin raini zasuyi mata ba,

Kanacin gashin kanka amma ka dawo gida sai abinda aka kasa aka baka, wannan wace irin rayuwa, amma ita zulaiha Allah ya bata dama amma tayi sakaci, kuma ta tashi ta kwaso yara jagal jagal to banda hawanta inama zata wuce a so ta?"" hawayen ta goge sannan ta miƙe ta fara sallah,

Raihana tana cikin sallah ta jiyo gida ya kiɗime, wasu na salati wasu kuma suna cewa gara da akai haka, wasu kuma kamar dai suna ɗan kuka kuka, raihana ita kuma tana gama sallah ta dawo bakin ƙofar ɗakinsu ta cikin labule ta laɓe don tabbatar da abinda taji gaskiya ne?"""

Lallai kunnen gaskiya ya jiyo mata, wato an siyar da wannan gidan da suke ciki kuma ga wanda ya siyi gidan tsaye a tsakar gida yana cewa yaba duk wanda take cikin gidan nan notices daga yanxun zuwa gobe da safe duk wanda takai la"asar a gidan nan tou pha zataga abinda zai biyu baya,

Ajiyar zuciya raihana tayi sannan taja jikinta ta koma saman katifa, *innalillahi wa"inna ilaihir raji"un* kwai take iya faɗi, raihana a bayyane tayi magana tana faɗin wannan wacd irin rayuwa ce?"" amma lallai bari Umma ta dawo dole gidan gwaggo zamu koma saidai duk bala"in da za"ayi ayi dan basu da inda zasu zauna,

Taci gaba da cewa gashi nan munma fara "yar sana"ar mu muna samun abinda zamu rufawa kanmu asiri, wayyo Allahna ya Allah kaji ƙaina ka rufa man asiri dan matsayin manzan Allah S. A. W, ka taimakeni ka bani miji inyi aure wallahi nayi hankali in Allah ya yadda nayi aure ko bansan mijin wallahi zama zanyi Allah ka yaye man haka nan, ta sake farkewa da wani irin kuka, sannan tayi magana ƙasa ƙasa tace Allah ka taimaka man kada in mutu banyi aure ba,

Umma ce tayi sallama ta shigo ɗakin da sauri raihana ta goge hawayen idonta tunda ɗakin da duhu umma bata san raihana tana kuka ba,

Umma sannu da zuwa, umma tace yawwa raihana tace kin daɗe baki dawo ba, umma tace wallahi, raihana tace kinji kuma abinda aka zo mana dashi?"" umma tace miye?"" hmmm umma wai an tada kowa na gidan nan, umma tace bisa wane dalili?""" raihana tace mai gidan ya siyar wanda ya siya kuma yace kada wanda takai mashi la"asar a gida, ajiyar zuciya umma tayi sannan tace Allah yasa haka shine alkairi,

Raihana tace haba umma wand alkairi kuma don Allah a tashe mu kina cewa Allah yasa alkairi ne, Umma tace haba raihana da ilimikin da hankalinki ya kike abu irin na jahilai?"" duk abinda kika ga ubangiji yayi a rayuwa yana da sila, jin umma zata fara wa,azi ita kuma tana cikin zafi dan haka kawai tace shikenan,

yanxun ina zamu koma?"" umma tace mu bari da safe sai musan nayi, raihana tace Allah ya bamu aron rayuwar, umma tace amin, anma fara kiran sallah muje muyi sallar, raihana tace ita tana da alwalla buta umma ta ɗauka ta fito tsakar gida donyi alwallah,

****
*G*ari na waye kowa fidimar gabansa yake masu fita da kayansu dan mutanen gidan sunce alhaji baya da mutumci, dan haka gara su tafi kafin a wulaƙanta su, raihana tace ma umma kodai mu koma gidan gwaggo, umma tace haba raihana sai kace dai karnuka?"" tunda an koremu ai sai muyi haƙuri mu matsa gaba ko Allah yasa mu dace, raihana tace to, umma ce tace bara inje in cigita mana gida ko mun samu dan wannan ɗaukar alhakine ace an bayar da notices daga jiya zuwa yau, taka dai ta fita daga ɗakin tana mita, dan yau ko abincin siyarwa basui ba,

haka kowa yaci gaba da kwashe kayanshi yana fita, raihana kuma tana ɗaki kwance tana baccin da bayada ma"ana, umma kuma tunda ta tafi har harxun bata dawo,

Raihana tana ɗaki kwance tana bacci bata san gidan kowa ya gama kwashewa ya fita ba, ita kaɗai a ɗaki kwance tana bacci,

alhaji ne ya shigo gidan dashi da rundunar shi, ganin ɗakin su raihana cikin fushi ya yaye labulen ɗakin ya leƙa, hango raihana yayi kwance tana bacci yace kam lallai amma wannan yarinyar tama raihana mana hankali, wani ya kalla sannan yace waccan matar waye?"" yace ranka ya daɗe bata da aure,

tsaki yayi sannan yace waye ubanta, aka ce mashi ɗiyar marigayi mai wankin takalmi ne, alhaji yace shirmen banza maza hau sama ka kware man rufin ɗakin,

raihana na kwance tana bacci, taji ƙarar kwano sama dan ya fara cire kwanon ga kuma rana tana ɗan hasko ta haɗi da ƙasa data fara zubowa, raihana da sauri ta miƙe tana faɗin lafiya?"" daga waje "yan kwarakon alhaji suka fara cewa mai gidane yake iko da abunshi

Raihana tace to miyasa ake cire kwanon ɗakin?"" alhaji yace saboda nawa ne, raihana ta fito daga ɗakin ta kalli alhaji tace "yar laɓai miyasa sai kwanon ɗakinmu za"a cire?"" tsaki yayi sannan yace gyara za"a, raihana tace okey to bari in kwashe kayan in mayar dasu wancan ɗakin, ta nuna wani ɗaki da hannunta, alhaji yace ke nan gidan bakuda wurin zama kowa ya tashi gidana zansa a rusa man, murmushi raihana tayi sannan tace ai babu komai zamu zauna a haka idan an kawo maka kayan aiki dani da ummana sai mu riƙa kular maka dasu kuma ma basai ka bayar da kuɗin kula dasu ba,

Alhaji yaga lallai raihana tana neman raina mashi hankali don haka yace a shiga ɗakinsu a fiddo kayansu waje road dasu, raihana tace haba bawan Allah dan matsayin annabin rahama kayi haƙuri wanda ya shiga ɗakin nasu ta kalla tace idan har kana san Allah ya kyautata lahirar ka kada ka tona mana asiri a cikin unguwa jira kallon alhaji tayi sannan tace Alhaji ka rufa mana asiri kada ka bari a wulaƙantamu a idon duniya,

dan Allah ya baka arziki bai kamata ka wulaƙanta wanda baya dashi ba, hawaye ya zubo daga idonta, taci gaba da cewa tunda kai Allah ya baka kayi haƙuri ka tausaya ma wanda baya dashi, ka rufa mana asiri kaima sai Allah ya rufa maka, zamu tashi kada kasa a watsa mana kaya ummana tun safe ta tafi nemar mana gida har yanxun bata dawo ba nasan bata samu ba, kayi mana wannan alfarmar sai kaima Allah yayi maka, ka rufa mana asiri sai Allah ya rufa maka ,

idan ka koremu anan bamu da inda zamuje, ka bamu aron gidanka mu zauna na lokacin da muka samu, alhaji duk abinda ka samu anan ka sameshi kuma anan zaka barshi babu abinda kowa yaxo dashi kuma duk abinda ka sama anan babu idan zaka je dashi, arxiki kuma da Allah ya baku dan ku taimaki wanda baya dashi idan ka barmu mun zauna a gidan nan babu abinda zamu rage shi, taimako da tausayi shine halin girma,

tunda ta fara magana taƙi tayi shiru bare taji abinda Alhaji zaice, sai taci gaba da cewa kayi mana alfarma dan baka san abinda gobe zatai ba, murmushi tayi sannan ta kalli alhaji tace kayi haƙuri insha Allah zuwa gobe zamu tashi,

umma ce tayi sallama ta shigo, ta gaishe dasu alhaji sannan tace ma raihana an samu gidan, raihana tace alhamdulillah, raihana tace alhaji kaji ma mun samu to mun gode Allah ya ƙara arxiki, umma wannan shine ya sayi gidan kiyi mashi Allah yasa alkairi, umma tayi ma Alhaji addu"a Allah yasa alkairi ubangiji kuma yasa yawancin rai akaimaw, alhaji ya kasa magana, komi yasa Oho,

haka su raihana suka fara cire kayansu dan babu wasu abun arxiki a ɗakin daga wata lasarsar katifa sai kayansu na sakawa da tabarma, haka suka ci gaba da ɗaukar kayansu har suka gama raihana ta sake ma alhaji godiya, suka fita daga gidan,

Suna fita alhaji yace ma wani bisu kaga inda zasu koma, yace to sannan ya fita daga gidan,

raihana da umma sunyi "yar tafiya sosai tsakaninsu da gidan da suka tashi sannan su isa ƙofar gidan da suka koma, sallama sukai sannan suka shiga,

wanda yake binsu ta baya yana ganin inda suka shiga sai ya juyo ya dawo gidan daya bar su alhaji,

Su kuma suna shiga, da sallamar su, matar gidan ta fito tana ma su umma sannu, bayan sun shiga sun zauna, sai matar gidan tace wannan fa?"" ta nuna raihana, umma tace ɗiyata ce, matar tace kai gaskiya wanann nana zankaɗaɗiyar bana zama da ita, wannan ai sai ta kashe man aure, umma tace ah ah baza ta kashe maki aure ba, tana da hankali itana ta taɓa aure, matar ta zaro ido tace *zawara* ce?"" umma tace Eh matar tace kam maima illar kenan wallahi na ɗauka ke ɗaya ce amma gaskiya bana zama da zawara taje ta aure man miji ko kuma ina can sake da baki tayi ta man lalata da miji, umma tace *subahanallah* raihana ba haka halinta yake ba, matar tace ɗan yau ai baka shedarshi tunda ba tare kuke fita ba,

Macen data san daɗin namiji kuma lafiyayyar mace kamar wannan ance maki dutse ce ita da bata buƙatuwa?"" ke tsohowa wallahi ban zama da zawara, kiyi haƙuri, raihana tace kedai zamu bawa haƙuri, amma a ko wane lokaci ka kyautata zato ga mutum, dan ance maki ni *zawara* ce sai akace maki ni karuwa ce?"" kiji tsoron Allah kuma kiyi sauri ki tubar ma Allah sannan kuma ki nemi gafarana in yafe maki, dan ita shedar zina girma gareta, amma daga gani na sai kije zanje inyi ta lalata da mijinki?"" kawai dai kice bayan tafiyarta kin sake shawara bazaki zauna da ita ba,

matar tace to naji bazan zauna da ita ba, ai gidana ne bana uban wani ba?"" kuma shima mai gidan ba nashi bane nawa ne ni na siya dakai na shima na raɓa shi, raihana tace Allah ya baki haƙuri abin duk baikai na zagi ba, Kallon inda umma take zaune tace tashi muje, umma ta miƙe jiki a saɓuƙe tabi bayan raihana suka fita daga gidan,

haka suka ƙusa suka ci gaba da tafi basu ma san ina zasuje ba, ga kuma magrib ta karato, raihana tace umma kiyi haƙuri kawai mu nufi gidan ku,


umma tace baza ki gane abinda nake nufi ba gidanmu baki iya zaman shi, raihana tace zan iya, ajiyar zuciya umma tayi sannan tace muje, suka fara tafiya raihana tace kinga idan mukaje sai mu nemi wani gidan da zamu koma ko?"" umma abun ya kasheta saboda haka bata sake kula raihana ba dan ita kaɗai tasan matsalar da take gidansu raihana ita kaɗai tayi ta magana ba tare da umma tana bata amsa ba har suka isa gidan su umma,

Suna shiga da sallama umma duk bata jin daɗi dan gidan ya haɗa da mutane iri iri, lokacin da sukai sallama suka shiga wani ɗan yayar umma ne kaɗai a gidan zaune da gajeren wando babu ko singilet ya ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya yana shan sigari,

Umma ta fara mashi magana yace sannu , ku kuma daga ina kuke haka kamar "ya sansanin gudun hijira, ke kuma kin ɗauko wannan lasassar katifar ko ƙyanƙyanmin ta bakya ji?"", umma dai batayi mashi magana ba, sannan tace ma raihana su shiga daga ciki, shima tasowa yayi ya biyo su yana cewa *raihan* babbar yarinya, kusa da raihana yaje ya zauna sannan ya miƙa mata hannu alamar su gaisa, ko inda yake bata kalla ba, don haka ya tashi ya fita daga ɗakin,

Yana fita daga ɗakin, umma tace kinga ɗaya........................,,,,,
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦

*Page* 2⃣1⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA*

*Jinjina gare ku ameenci writer's bisa namijun ƙoƙarin da kuke Allah ya ƙara basira da zagin hannu ubangiji ya ƙara lafiyar ido da ƙwarinsu,*

*wannan shafin nakune ameenci fans, kuma Allah ya ƙara maku lafiyar idanuwa dan kuji daɗin karatu,*

*Ƙawata Asmeenat Xeeyan ina tare dake a kowane lokaci alkairin Allah yakai maki haɗ sakoton shehu*

*****

*R*aihana ta kalli umma sannan tace ai ban bashi hannun ba, umma tace baki san halin kabir ba , dan ɗan iskane jigunanne saboda haka sai kin kama kanki sosai sannan kuma kada ki kuskura ki sakar mashi fuska, wannan shine dalilin daya sa nace maki zaman gdan nan bayayuwa wurin, raihana tace to umma munje mu kwana saman titi?"" umma tace Allah dai ya sawaƙe ina gaya maki magana ki a kawo man shirmen banza,

Shiru sukai na wani lokaci sannan umma tace bara inje inyi alwalla, raihana tace to, umma ta ɗauki buta ta fita, bayan tayo alwalla ta dawo itama raihana ta fita danyo alwalla,

Kabir yana tsaye tsakar gida sai sigari yake zuƙa yanda yake ɗaga bakinshi idan zai fita da iskar sigarin tun daga nan zaka gane tataccen ɗan iskane, raihana ta wuce kangal kangal zata nufi bayi, shima bayanta yabi, juyowa tayi taga ita yake bi,

Kaucewa tayi gefe ɗaya don bashi hanya ya wuce, kallonta yayi da idanuwanshi masu jan tsiya, raihana ta sake ja da baya dan gani take kamar hanyar bata isheshi ba, inda ta raɓe shima wurin ya koma lokacin daya sake sanya karan sigarin a bakinshi ya ja, sannan ya busa mata hayaƙin, tsaki raihana tayi ta nufi bayi ta shige ta kulle, saida ta gama abinda take sannan ta fito, tana buɗe ƙofar ta ganshi tsaye tace malam bani hanya kaji,

Cikin maganar yan iska yace nayi farin cikin ganinki fa, ke bakiji daɗi da kika ganni ba?"" raihana tace bara in gama abinda nake sai muyi magana, kabir yace ai kin gama yanxun, tace sallah zanyi, kabir yace wace sallah kuma ga umma can tana maki basar kawai ta sammaki ladar, raihana ta wuto zata wuce ya sake shan gabanta, yace an mata ana nan ana hutawa shi yasa kika ƙi aure ko?""

Raihana tace da Allah gyara man hanya in wuce, yanda tayi maganar babu alamar wasa kabir cikin maganar tashanci yace keji yarinya waini zaki ma fuska?"" uhum bara dai anjimar tayi, tunda muna tare in daina zumiɗi, raihana dai bata sake magana ba ta raɓa shi ta wuce,

alwallah tayi sannan ta shige ɗaki danyin sallah,

suna nan zaune ita da umma sukai magrib suna wurin har aka kira isha"i suyaka yi, bayan sun gama raihana tace umma wai miyasa ita umma halima ta rufe wancan ɗakin?"" ai sai ta buɗe mana dani dake mu shiga ciki, umma tace ai sai kije ki faɗa mata,

dariya raihana tayi sannan tace Allah ya baki haƙuri, umma bata sake magana ba,

bayan wani lokaci raihana tace umma idan kina da kuɗi kawo inje in samo mana ko gari ne mu jiƙa ni wallahi yunwa ma nake ji, umma tace banda su, raihana dai ta kula umma cikin fushi take saboda haka ta tashi taje ta kwanta saman wani gadon ƙarfe da yake cikin ɗakin, bata daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗauketa dan ta gaji sosai, ita kuma umma hankalinta ya kasa natsuwa dan haka ta kasa kwanciya tana nan zaune kuma ɗakin babu fita ɗakin dumm yake da duhu,

Raihana bacci take sosai , saboda haka cikin bacci taji umma sa"a na cewa wanda ta isa ce ta hau man gado sauko, umma ita kuma tana cewa wai ku duk ina kuka shiga sai yanxun zaku dawo gida don Allah?""

umma sa"a tace neman kuɗi muka je, umma tace neman kuɗi kuma kamar wasu mazaje?"" tsaki tayi sannan tace wai mima kuka zo yi nan ne?"" umma tace a gidan da muke haya ne aka tashe mu, zamu zauna nan kafin mu samu wani,

umma sa"a tace amma baki da hankali fatima, in banda hauka kinsan nan gidan ɗaki ɗaya ne, sai kuma ki kwaso saboda Allah ki taho , ita raihanar aikin mi takeyi ne da baza taje wurin masu santa su baku wurin zama ba, to miye amfanin *zawarcin* nata?""

raihana dake kwance taji abun yaƙi ƙarawe ta tashi ta sauka daga saman gadon kusa da umma ta koma ta zauna sannan tace umma sa"a ina yini, umma sa"a tace wane ina yini?"" ina amfaninki raihana?"" da kyanki da ɗirinƙi da sigarki babu namijin da zai ganki hankalinshi bai tashi ba, ina ni"imar da Allah yayi maki dan baƙin ciki sai ki zauna bahagguwa dake duk masu sanki sai kice su baki gidan zama ,

amma sai ku kwaso dake da uwarki kuyo mana nan?"" mu a ina zamu ajiye ku?"" ki dage ki more rayuwarki raihana ki samar maku "yanci har muma muzo cin arxiki,

umma sa"a, yayar umma ce, idanuwanta sun bushe saboda ita tana da san abun duniya sannan kuma tana da san kai ita kullum yaranta tana ƙoƙarin ɗorasu kan turba ta gaskiya, amma ɗan wani duk inda zata turashi ga halaka kullum ƙoƙarin neman haryar take, amma ita ga "ya"yan ta nan duk basujin magana ,

*zawara* sunkai biyar a gidan su umma idan hada raihana da umma mutum bakwai kenan wansa basu da aure,

raihana dake nake magana , kina jina kin wani man kamar baki sna ina magana ba, cikin sanyi raihana tayi magana tace umma naji,

umma sa"a tace to banda abinki ke fatima ina zamu kwana, kinsan babu wuri a ɗakin nan, yanxun ina zaku kwanta?"" kabir daga waje cikin maganar ƙauraye ga sholisha yana murzawa yace umma ita raihana ai sai mu kwana ɗaki ɗaya da ita, tunda ita muharrama tace, umma tace kai da Allah rufe mana baki , umma sa"a tace to fatima miye?"" dan kabir da raihana sun kwana ɗaki ɗaya miye?"" tunda abun duk gidane ai sai a haɗu a rufa ma kai asiri, ke raihana ki kwana a ɗakin kabir ɗin ita kuma fatima sai muyi sikwacin nan da ita,

dariya raihana tayi sannan tace umma sa"a kenan wannan kasafin naki yayi, amma huɗubarki ta farko itace na ɗauka zanje yau cikin daren nan in samo mana gida, umma sa"a tace ah ah ki bari sai goben, kabir yace ke "yar rainin hakali ummata zaki fara gayama magana?"" ni ban ɗaukar iskanci idan dai aka taɓo man ummata, raihana tace yi haƙuri banzo wurinka ba, da yar uwata nake magana,

kabir ya taso daga inda yake zaune cikin layi ya shigo ɗakin gaban raihana ya tsaya sannan yayi magana cikin muryar daba yace shegiya *zawarar* banza iskancin ki zai tsaya akan uwata ne,?"" wata tagulla ya fito da ita daga cikin aljihunshi sannan yace kinga wannan?"" ina iya aika ki lahira da ita,

murmushi raihana tayi da gefen bakinta, sannan ta ɗago ta kalli kabir ta jinjina kanta, yace ni kike cewa zakici uwata?"" raihana tace ai ban zagin uwarka saboda uwarka uwata ce saida in lalata maka fata da duka, dan bari ganin umma sa"a tana magana kana neman raihana ma mutane hankali raihana zafi ne da ita, dan idan na sadda kaina ƙasa ni nafi guguwa bala"i, daka taɓoni gara kaje ka rungumi transfomer, ɗaure fuskarta tayi sosai sannan tace umma kwanta,

Umma tabi raihana da kallo da tasan raihana ba magana tasha mata kaiba, ita kuma raihana ta ɗauri aniyar duk wanda ya sake taɓota bata mashi sauƙi tunda ba"a tausayinsu, kuma yanxun babu inda zata je, anan zasu kwana,

umma ki kwanta nace, umma tabi raihana da kallo, ita kuma miƙewa tayi taje wurin kayansu ta buɗe jakar kayanta ta fiddo wani wandon jeans ta saka ta ɗaure gamm sannan ta dake cinyarta tace dani dakai duk wanda ya fasa yaci uwashi , tana gama maganar ta koma ta haye saman gadon umma sa"a, tace umma sa"a, kezo nan muyi sikwacin, maganar data faɗa ma ummarta ta rama mata,

Umma sa"a tace ma kabir jeka, haka umma sa"a taci gaba da mitarta, daga bayan taje ta raɓa kusa da raihana ta kwanta, sda guda guda haka zawarawan gidan su umma suka ci gaba da shigowa, ko ina suke zuwa ohon masu, dan ita dai raihana tuni bacci yayi gaba da ita,

*****

Da safe kowa ya tashi lafiya, raihana koda safe batayi ma kowa magana ba,

Kowa shine yakd siyen kalancin shi da kanshi, umma ta bawa raihana kuɗi itama taje ta siyo masu koko, taje ta siyo masu koko da alewa ta dawo gida, bayan sun gama kalaci kowa ya fara wanka dan fita,

itama umma shiri tayi dan tafiya nemar masu gida, da zata fita tace na raihana ta kula da rayuwarta, dan kabir bayada mutumci raihana tace to umma, bayan taja mata kunne ne ta fita tabar gidan , haka kowa yayi ta fita ɗaya bayan ɗaya,

gida ya rage daga raihana sai kabir..........................................
💦💦💦💦
💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦
💦💦💦

*Page*2⃣2⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA*

*****

*R*aihana ta fito daga ɗaki taxo taja ruwa, bayan ta gama jan ruwan ta koma ɗaki taje ta cire kayanta ta ɗauro zani ta ɗauki hijabi ta saka , kwandon wanka ta ɗauko tayo waje, tana zuwa ruwa ta ɗauka ta nufi bayi,

Kabir yana ganin raihana ta shiga bayi shima ya fito daga cikin ɗakinshi ya nufi ƙofar bayin ya fara kwankwasawa, gamgamgamm bambambamm, raihana saidai tace Ehem Ehem, yaci gaba da kwankwasawa, raihana tayi masji banza, yace raihana buɗe zan shigo bayan gida zanyi, raihana tace wai kai wane irin tantirin ɗan

Please Login or Register in order to submit comment