Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mota ya shiga sai airport, haka ya tafi da maraicin raihan,

****
Watan faruk ɗaya da tafiya amma har yanxun baiyi waya da raihana ba, raihana kuma an wani goge anyi kilinar an wani zama "yan gayu, idan ka ganta baka gajiya da kallonta, ita matsalarta tana so farida taxo amma batama san sunan anguwar ba, kuma ita bata da number faruk haka dai ta haƙura amma tace mata insha Allah idan ya dawo zata xo

Raihana zaune an wani kashe saman kujera , tana ta tunanin duniya iri iri, hafsat ce ta shigo cikin farlon tare da sallma, raihana ta amsa amma bata daga inda take ba, kuma ba baki ta saki tayi dariya ba, tunda ta ansa sallamar ta basae dan tasan ƙarshe wulaanci zata mata,

zama tayi bayan ta zauna tace ma raihana inayini?""",,, raihana tace lafiya qalau, hafsat tace yaya ya aikoni, raihana tace uhum, hafsat tace yace zaiyi magana dake, raihana tace faɗa man number zan kirashi, hafsat ta karanta mata, daga nan bata sake magana ba, hafsat ta gaji da zaman ta, tace ma raihana sai anjima, tace to, daga nan bata sake cewa komai ba, saida hafsat ta tafi sannan ta tashi ta tafi ɗakinta don kiran *Faruku*..................
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦

*Page* 4⃣2⃣

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA*

*Gaisuwa ta musamman gareki ya sayyada, mujadda, malama, hafiza, kamila, ustaziyya, hajjajju Rabi Musa Alkairin Allah ya isoki har cikin bargon baccinki*

*Ban manta dake ba Ƙawata Asmeenat Xeeyan Alkairin Allah yakaimu ranar 1/1/2018*

*Wannan feji nakune masoya littafin Zawarci ina tare daku dan kune alfahirina, farin cikinku shine maudu"ina, ina kaunarku sosai*😎
***
*SHAWARA GA MAZA* :• Don Allah don annabi ku riƙa riƙe matanku cikin daraja da mutunci ku tuna fa mata marufar asirinku neeeeee😉 domin duk kyan gida da tsaruwarsa idan akace babu mace a cikin gidan ya zama kangoooo☺ don ko "yan uwanka bazasu riƙa zarya a cikin sa ba, saboda gudun zargi, kada ku wulaƙanta matanku ku rinƙa gani dole tayi maku abu kuna ganinta kamar baiwa,,,,,

To wallahi ba dole bane, saidai kawai tayi don kyautata da kuma neman aljannarta don cewa akayi , idan kun auri mata komai kuyi masu, ku ciyar da ita, ku shayar da ita ku tufatar da ita😌, abinkin da in kunfita kun nemo mune muke girka maku dan tsaron lafiyar🤓 don kuma kuci mai daɗi hankali kwance, kunsan girki iyalikune duk wani koyi munayin koyi da ma"aki S. A. W

To manzan Allah yana zama yayi wasa da dariya da matansa yana tayasu aiki a cikin gidansa ya lallaɓa matansa baya bari suyi fushi baya girman kai, bayacewa shi annabi ne sai komai anyi masa, manzan Allah yana ɗauko kaya daga kasuwa ya kawo har gdansa , manzan Allah yana huɗɗa da talakawa da masu kuɗi da miskinai baya ware wani yace da wannan zaiyi harka, bazaiyi da wancan ba, fiyyen halitta kenan,

Kai kuma ka gama wasa da dariya a waje sai ka dosa gida ka haɗiye rai kamar wani mala"ikan mutuwa,🙄 waikai kada mata suga fuska su rainaka , to raini na nawa kuma?"" ta gama karewa halittarka kallo da daddare., kayi faramfaram kayi wasa da dariya da iyalinka idan kuna cikin nishaɗi da raha kuyi "yar goyo kuyi wasan "yar ɓurum ɓurum ,ka rufe idonka ko ta rufe nata , idan ta kamaka tayi tsalle tana murna ta kamaka,

Kuyi ƙwallon ƙafa, kuyi wasa kuyi rawa tare kuyi "yar tseral, idan ta tafi kicin ka bita tana aiki kana taimaka mata da wasu abubuwan idan yarane daku ka shiga cikin yaranka su sake dakai ka taimaka mata wurin shirin makarantarsu ita tana haɗa break kai kana sa masu uniform, ka taimaka mata wurin basu break ɗin su shaƙu dakai so soka su rinƙajin kaunarka a ransu duk inda suka shiga su rinƙayi maganar Abbansu, duk abinda kayi wa iyalinka ka wadata "ya"yanka da matarka da sutura, kada kai kana fita fess fesss 😇 su suna fita kamar almajirai, wallahi jama"a rainaka zasuyi😔 za,a daina ganin girmanka,

yaro baya mantuwa duk abinda kayi masa yana ƙarami bazai manta ba, duk yanda ka kula dashi da wahalar daka sha akanshi da yadda ka tsaya masa wurin iliminsa yana sane, wata rana sai yayi maka gata, haba bawan Allah ɗanka ne fa, kuma amana Allah ya baka,

Mata don Allah mu kula kada dan an auro mu munxo mun tarar da ɗan da babu uwarsa a gidan mu shiga mu fita mu raba ɗan nan da ubansa, kece kullu masa wannan sharrin kece ƙulla masa wannan makircin, harsai kin rabasa da ubansa, uban ya wulaƙanta masa rayuwa, ƙarshe yaron ya zama ɗan iska, saboda bai samu gatan da zai gyara masa rayuwa ba, kada mu "yan uwa, akwai ranar da zamu mutu , a gama a haɗa ka za,akaika kabari taku ɗaya na ƙafar ɗan adam za,a zana ayi ta haƙawa duk kibarka duk kaurinka a taku ɗayar nan za"a saka ka, bafa za"a ƙara maka ba, a mayar da ƙasa a rufe jama"a su juya su tafi a barka shikenan ,

Suna juyawa sun fara tafiya za,s dawo maka da ranka, """" tashi ka bisu""" ina zaka iya motsi ƙasa ta gama riƙe ka gam?" kaga mala"iku masu firgitarwa wanda girmasu bazai musultu ba,

suyi maka tambayoyi , waye ubangijinka waye annabinka ?"" idan kayi shiri babu amsa su ɗaga guduma su rotsa maka, saboda tsanin duka sai ka nutse a ƙasa har kaje ƙasa ta bakwai ƙasa tace , """fito fito munafikin Allah bazan ɓoye wanda ya saɓi ubangiji ba, """" ta bultsoka kafin ka gama fitowa ƙashinka ya gama gurgujewa , haƙarƙarinka kana dama ya ɓullo na haggu sun karairaye sun gama gutsin gutsin amma a haka za,a sake mayar da halittarka aci gaba da maka tambayoyi,

Allah ka kiyashemu ka nufemu da aikata alkairi Ameeeeeeen,,,,😭🙏🏻

***
*ZAWARCI*

*T*ana shiga ɗaki saman gado ta haye, saida ta kwanta sannan ta fara lalubar number faruk, haka ta shiga ta ƙari ringing bai ɗauka ba, sake kira tayi, shima bai ɗauka ba, saida ta tsinke sannan ya biyo kiran a karo na biyu,,,,,,,

Raihana ta ɗauka da sallama ta fara magana, bayan ya ansa ne, tace Raihana, murmushi yayi sannan yace ai na gane, ya kike?"",,,,, tace lafiya qalau, yace bakiyi maraicin mijinki ba?""",,,,, raihana tace nayi mana, yace gaskiya bakiyi ba, tace miyasa banyi ba?""",,,,, yace da kinyi aida kin kirani mana, tace ai banda number ka, yace ni na damu ke na kiraki inji lafiyarki,

raihana tace lafiya qalau komai , amma inajin babu daɗi saboda baka tare dani, dariya yayi sannan yace nima nayi missing naki sosai, nayi missing ɗin bargonki , kullum sanyi baya barina ina bacci , raihana tace kai nima duk haka nakeji, yace da gaske?"",,,, raihana tace sosai ma, yace to kina so na?"",,,, bata bashi ansa ba taji an banko ƙofa da ƙarfin tsiya,

da sauri ta miƙe gabanta ya fara faɗuwa don ganin wanda ta shigo ɗakin, tabar wayar a saman gado shi kuma sai fama hello yake, lallai wato har kin samu matsayin da Faruk zai ajiyeki a gidan nan ne?""",,,, gaban faruk ya faɗi jin muryar momy, raihana yaji tana cewa Momy sannu da zuwa, momy tace sannu da zuwan uwaki,

Kinxo kin wani bi gado kin lafe kin samu gidan gayu uwarki na gidan haya, hada wani kwanciya saman gado da uwar wa kike wayane?""",,,,, cikin ladabi raihana tace da faruk, momy tace umm lallai, to miyake cewa?""",,,, raihana tace yace ina lafiya?"",,,,, nace lafiya qalau nake, sai yace mi?"",,, raihana tace sai kikax xo ,momy tace to kira man banzan inji,

saboda ke harsai an taso man ɗiya daga gidan aure?"",,, wato ke kina ɗakikin ki kin zauna ki samu lada, ni kuma ɗiyata taxo ta samu zunibi ki shiga aljanna tawa taje gidan wuta, raihana tace momy kiyi haƙuri don Allah,

tsaki tayi sannan tace to bani wayar dan ubanki, ni nama barki ki aihu gidan nan?"",,,,,, bani wayar, da sauri , faruk ya kashe kiran, ita kuma ta ɗauki wayar ta miƙawa momy,

ansa tayi sannan ta duba number faruk ɗin, tace ummm lallai lifepartner ko?"",,,,, to idan na raba ku kuma ya zai koma?"",,,,raihana tayi shiru, momy ta fara zagaya ɗakin tana ɗan ɗage ɗage, wato da nace kada yayi maki lefen nan saidai yayi?""",,,,, kam kenan ba a bakin komai nake ba?"",,,,,, to wuce mu tafi dan ubanki a gidana zaki koma da zama,,,,,,,

kallo raihana tabi ta dashi sannan tace momy yace kada in fita, tsawa ta daka mata sannan tace munje dan uwarki"""",,,,,, raihana ta ɗauki hijabinta tabi bayan momy zugui zugiii, drivern momy yajasu har gidanta.........,,,,,,,,

Ajiyar zuciya faruk yayi sannan yace kai momy ta shiga rayuwar yarinyar nan mi raihana tayi mata ne?"",,,,,, lallai koma miye hafsa ce tayi munafincin amma lallai zatci ubanta wallahi,

suna isa gidan momy, bayan sun fito daga motar wata yayar momy suka gani, tace haba ni na gaji da jiranki har zan tafi nazo bakya nan, momy tace E naje inci uwar yarinyar nan, tace wace yarinya,?"""""""",,,,,,,, juyawa tayi ta nuna mata raihana, tace ina kika sako ta ita kuma?""",,,,,,,

momy tace matar Faruk ce, tunda ya auri tsinanniyar yarinyar nan baida zama lafiya, gaba ɗaya ta burkuta man hakalin ɗa, dan ubanshi har sawa nayi ya saki ɗiyar nan ashe ɗan iskan yaron nan bai saketa ba,

waisai ya rubutu kiyi haƙuri raihana ki zauna a gida idan komai ya daidata zan dawo dake, tana maganar tana taɓe baki ne, yayar tace haka ne?"",,,,,, momy tace E, tace ki rufa ma kanki asiri kada ki kuskura ki shiga rayuwar ma"aurata idan har kikace wannan halin zakiyi haƙiƙa rabo dai aikaki lahira,,,,,,

Cikin bala"i momy tace ai nice rabo kuma saina raba wannan ɗan iskan aure, yarinya tabi man ɗa ta kanannaɗe kamar masifa, duka auren wata biyu da satittika amma har idan baiyi waya da ita ba, zai taso ma ɗiya daga gidan aure takai mata waya, saboda ya raina nasu auren,

da nayi mashi magana nace duk ina masu gadi bazaice sukai wayar ba?"",,,, sai yace wai kada suje su gane mashi mata, sai ita hafsat da mijinta baya kishinta?"",,,,,, to wata biyu kenan, ina ga tayi shekara ko ta aihu?""",,,,,

Yayar momy tace keda ba ruwanki faruk kuma ba ƙalle bane, mata nawa ya aura?"",,,,, ke zaki nuna mashi matar data dace dashi?""",,,,,,,,tunda ya auri wannan ki barshi kiyi mashi uziri, da kanshi zai saketa dan wannan yarinyar ni na bata wata huɗu badai faruku ba?"",,,,,, hmmm dan Allah ki barta, momy tace to wallahi saidai in kaita gidan uwarta can idan ya dawo zai saketa,

Tace kedai barta ta koma gidanta, momy cikin bala"i tace gidanta?"",,,,, harma gidan ya zama nata kenan?"",,,,,,, yayarta tace towai ke wannan masifar duk ta miye?"",,,,,, momy tace koma ta miye wallahi yau gidansu zata kwana, aje can ayi wanka a bayin tsakar gida,

da safe abinda za,aci ma sai yayi wahala, aje kwana biyi baza,asha AC ba, ɗakin uwarki ko fanka babu, bare ledar tsakar ɗaki wallahi bansan ki, bako wani dalili yasa bana kaunarki ba, saboda kawai ina ganin zaki rabani da ɗana, dan na tsani auren zawara, saboda idan ta kama namuji batai mashi sauƙi,

da yana da mata nasan kila yanxun da kinyi waje da ita, wuce mu tafi dan ubanki, yaya momy tana mata magana amma ina, tace wallahi sai raihana ta kwana gidansu, haka ta tasa ƙeyarta suka shiga mota gar ƙofar gidansi takaita, tace a fita yau akwana cikin sauro, haka raihana ta fita jiki a sanyaye, sannan momy ta wurga mata wayarta,

Su momy najan motarsu raihana taga gwaggo tsaye gabanta, wata irin dariya gwaggo tayi tare da tafa hannu, tace an ƙara dawowa?"",,,,,,, ai na gaya maki babu ke babu zaman aure, "ya"ya masu gata ma basu tafi gidan kuɗi ba sai ke?"",,,, ke a suwa?"",,,,,,, dariya ta ƙarayi sosai sannan tace gidan kuɗi sai masu matsayi , ta ɗaga hannunta tayi ma raihana dakkuwa, ta wuce tana dariya,

duƙawa raihana tayi ta ɗauki wayarta ta shige cikin gida, tana shiga wayarta ta fara ringing, Faruk ne, tsaki tayi bata ɗauki wayar ba, wani kiran ya sake shigowa, bata ɗauka ba, Umma dake ɗaki tace waye?""",,,,, raihana kamar jira take ayi magana ta fashe da kuka, umma da sauri ta fito daga ɗaki tana tambayar lafiya?""",,,,,,,,, ashe gwaggo biyowa tayi ta laɓe, raihana tace umma na gaji nidai wannan auren na haƙura dashi kamar kaina farau uwar miji?""",,,,, kullum da abinda zatace nayi mata?"",,,,,,,, uma tace kiyi haƙuri, ɗauki wayarki ana kiranki,

raihana tace bazan ɗauka ba umma faruk ne, umma tace to miye yayi maki?"" wannan laifin ai ba nashi bane, ɗaki kiji abinda zaice, gwaggo dake zaure tayi dariya sannan ta fita tana murna raihana ta gaji da aure, niko nace ai baki tsaya kikaji ƙarshen film ɗin ba,

Ɗaukar wayar raihana tayi, tana ɗauka abinda faruk yace mata don Allah kiyi haƙuri, insha Allah gobe ina nan zuwa, kiyi haƙuri kinji?"",,,,, raihana tace to , yana faɗin haka ya kashe, wayar,

Umma tace miye?"",,,, raihana ta faɗa mata, sannan ta faɗa mata yanda sukayi da faruk, umma tace to kiyi haƙuri ki jira zuwansa, raihana tace to,

Momy tana komawa gida, tun a bakin get take jiyo ihun zainab da gudu ta shiga gidan tana tambayar lafiya?"",,,, amma zainab sai ihu take kamar zata mutu tana sulalacewa tana faɗuwa ƙasa tana kuka mai tada hankali,,,,,,

momy tace dan ubanki lafiya?"",,,,, miye akayi maki ne?"",,,,,,,, zainab tace momy an cucuce an takaita man rayuwa an gama dani Allah ya tsine ma uwar miji marar adalci wanda bata barin surukai lafiya, momy tace waike miye?"",,,, zainaba tashi tayi taje kusa da momy sannan tace momy uwar miji takaini asibiti aka zubar man da ciki, wayyo Allahna kila ma bazan sake samun ciki ba, wayyo Allahana,

momy hankalinta ya tashi a suƙwane da sulale saman kujera tana sake tambayar a bisa wani dalili?"",,,, zainab tace momy cewa tayi na malleke mata ɗa, komai ni kaɗai yake mawa, duk nemansa akaina ya ƙare kuma tace ya sakeni idan bai sakeni ba zata tsine mashi amma yace bazai sakeni ba, ita ta gane ina da ciki shine ta haɗa kai da likita yayi man allura cikin ya ɓare saida akayi man wankin ciki, yiiiiiiiiiiii taci gaba da kuka,

yayar momy dake gefe tace to kinga ishara?""""",,,,,, tun kafin aje ko ina ko?""",,,,,,,, ke kince baki barin raihana ta aihu a gdan faruk toke ɗiyar taki ta samu ciki an zubar dashi, kuma gata tana cewa kila baza ta sake samun wani cikin ba?""""",,,,,,,,,,,,,,,,

Ya kika ji baƙin ciki yau a ranki don Allah?"""""",,,,,,momy tayi shiru, yayarta tace to yanda kikaji yau irinshi ne maman raihana zataji, wallahi ba muyi ma kanmu adalci ke ayi ma ɗiyarki gata, amma ku, kuma ku auro na wasu ku ƙuntata masu wannan rashin adalci ne wallahi,,,,,,,,

kallon zainab tayi sannan tace ya mijin naki yace ne?"",,,,,, cikin kuka zainab tace cewa yayi inyi haƙuri zaizo, yayar momy tace to Allah ya jishemu alkairi, kallon momy tayi da hawaye yake zubo mata daga idon ta, sannan tace kuka ma yanxun kika , kiyi maza ki fara tuba , yau da raihana kika sa aka saki kema taki za"a koro daga gidan aure, kiyi ta kanki ki canja rayuwa tun kafin gaddara tahau maki wadda tafi wannan bala"i,

tana faɗin haka tayi gaba, zainab sai kuka takeyi,,,,,,,,momy ma kuka takeyi,

Umma ce ta tisa raihana a gaba tana tayi mata nasiha tare da nuna mata haƙuri da jarabawa imani ne, komai yayi farko zaiyi ƙarshe kuma duk wanda Allah yaso ɗaga darajarsa to sai anjarabe shi don auna imaninsa tana bata haƙuri ta ƙara da cewa ta saurari zuwan faruk ɗin suji,

ranar dai raihana haka tayi bacci ba cikin daɗin rai ba, tunanin wulaƙancin da momy tayi mata takeyi, saida ta goge hawaye, haka tayi ta juyi har bacci yayi gaba da ita,

***

*F*aruk yana gama sallah asuba, ya fara shirin tahowa, dan gaba ɗaya ji yake kamar ya miƙa hannunshi ya ɗauko raihana, duk ta bashi tausayi dan gorin da momy tayi masu wai basu da muhallin , yace Allah sarki da wata "yar rashin kunyarce ai sai ta zage momy fess dan akwai surukai masu rashin ladabi, amma ita sai bata haƙuri take amma momy ji take kamar ana zugata, hmm insha Allah kun gama haya, aini banma san ba gidanku bane, wayarshi ce ta fara kuka, yakai dubanshi wurin wayar sannan ya ɗauka,

Sallama yayi , tare da cewa momy kun tashi lafiya?""",,,,,,, lafiya qalau ga zainab nan an dawo da ita bata da lafiya tun jiya ,,,,,,, faruk yace miye ya sameta?""",,,,,,, momy ta faɗa mashi duka abinda ya faru,,,,,,,, salati yayi sannan yace to yanxun miye matsalarta?""",,,,,,, momy tace aini kada ma baƙin ciki ya kasheta saboda an zubar mata da ciki,,,,,,,,,,


faruk yace an kaita asibiti ne?""",,,,,,,,, momy tace A, a, faruk yace bari sadiq zaizo yakaita , momy tace to kai sai yaushe zaka dawo ne?"""",,,,,,,, faruk yace cikin satin nan, tace to kashe wayarta tayi, """anan kunga saboda matsatsi da takura irin wanda take mashi dashi da iyalinsa yasa ya ɓoye mata wani abu"""",,,,

bayan ya gama wayar ne, ya kira raihana, ita kuma cikin bacci taji waya tana ta ihu , don haka a gajiya cikin yanayin bacci takai hannunta inda takejin kukan wayar ta lalubo ta ɗauka, a kunnenta ta kara, tare da cewa hello cikin maganar bacci,

shi kuma cikin sigar jan faɗa yace in sani hankalinki kwance kina bacci kinajin daɗin ki ko?"",,,,,,,, uhum tace sannan tace bacci bafa wani daɗine dashi ba, kawai ma dan yana ɓarawo ya saceni , yace to gani nan zan taso yanxun insha Allah, tace to Allah yasa ka iso lafiya ubangiji ya tsare hanya, yace amin, ta kashe wayar,

tana ajiyewa wani kiran ya sake shigowa, sake jawo wayar tayi ta ɗauka tare da karata a kunnenta, tace ranka ya daɗe miye?"",,,, murmushi yayi sannan yace na mance bance maki i love u ba, murmushi raihana tayi sannan tace ngd, ta sake kashe wayar,

murmushi faruk yayi sannan yace anya yarinyar nan tana so na?""",,,,,,, tsaki yayi sannan yace bara in sake kiranta sai tace man tana so na, kirane ya shigo cikin wayarshi don haka yana dubawa ya miƙe tare da ɗaukar wasu takaddu yayi waje,

momy kuwa tana can ta shiga tashin hankali , saboda abun zainab yaci tura kuka take tana ƙarawa saidai ta faɗi dan duk jiya batayi bacci ba, baƙin cikin an zubar mata da cikinta takeyi,,,,,,,, momy tayi rarrashin duniya amma zainab sai wani ɗauke nunfashi takeyi kamar zata bi cikin ta iskoshi,

momy wayar faruk ta kira, number busy ta kira yafi babu adadi amma maganar ɗaya ce, user busy, haka ta haƙura ta zauna tana sauraron ikon mai sama"u,,,,,,,,,

sadiq kuwa sai ƙarfe 10:09am ya iso gidansu faruk , don haka yana zuwa babu ɓata lokaci momy suka kamo zainab akai asibiti da ita, niko nace candai,

Shi kuma faruk sai 9:08pm ya shiga cikin gidanshi tare da motocin da sukayo mashi rakiya, ko parking ɗin kirki ba,a gama ba, ya fice daga motar burinshi kawai yaga raihana,,,,,,,, yana shiga ɗakinta ya nufa, yana ayyanawa wasu abubu a ranshi,


yana shiga yaga gado babu kowa, toilet ya duba bata nan, A,a dubawa yayi ko ina babu raihana, wayarta ya fara kira, bayan ta ɗauka ne, yace kina ta ina ne haka?""",,,, raihana tace to ai ina gida!"""""",,,,,,, wane gida?""",,,,,,, tace ina gidanmu, yace gdanku kuma?""",,,, wannan wace irin magana ce kuma?""",,,,,,, raihana tace ba wata magana bace, kayi haƙuri , ta kashe wayarta, tsaki faruk yayi sannan yace wai yaji tayi?""",,,,,,,,,,, ai sai kije kiyi tayi ba nace kiyi haƙuri ba, haka yayi ta sabbatu kamar raihana tana kallonshi, danshi baisan momy ta korata ba, kawai dai abinda yaji tana mata gorin gida,

tsaki yayi sannan yace lallai inbar abinda nake in taho saboda ke, dan ƙarshen ki wulaƙanta ne, shine zaki tafi gidanku?"",,,,,,, hmm ni ban iya biko ba, nayi na farko tunda nine nayi laifi amma yanxun bansan abinda yasa kika tafi ba, sai ayi maki uziri muga,,,,,,,,,,

Umma tace ma raihana cewa yayi zaizo ne?""",,,,, raihana tace barshi umma wani fushi fushi yakeyi ma, umma tace to ya yace maki?""",,,,,, raihana tace baice komai ba, Umma tace kirashi to kic......,,,,,, bata ƙara maganar ba raihana tace don Allah umma ki barshi, ai cewa yayi zaizo baizo ba, barshi,,,,,, tou pha, abunda dai duk kowa ya kasa ba kowa uziri,,,,,,,,,

tsaki faruk yayi sannan ya sake kiran raihana, bayan ta ɗauka yace waike da kika tafi mi akayi maki ne?""",,,,,,,,,, raihana tace ba komai, yace momy tace wani abu ne?""",,,,, raihana tace tace inxo gda sai ka dawo,,,,,,,,,,, faruk yace dagashi fa?""",,,,,,, tace haka aka tsaya, yace to yayi kyau,,,,,,,,,,,,,,,

Likita ya shedawa momy cewa lallai zaiba ta rage damuwa idan ba haka ba, lallai zata jawa kanta matsala, ya ƙara da cewa tayi haƙuri ubangiji zai bata wani, cikin kuka zainaba tace ciki fa?"""ɗana ?""",,,,, nasha wahalata sai a zubar man da zalinci?""",,,,,,,,,, sai kuka takeyi ganin abun na zainab ya zama hauka yasa likitin fita yabar ɗakin, dan ana kwaɓa kai yana ƙara hawa,,,,,,,,,,,,,,,,

wani tunani faruk yayi don haƙa kiran raihana yayi bayan ta ɗauka yace kiyi haƙuri insha Allah da safe zanzo, raihana tace to Allah ya kaimu, yace amin , sannan ya ajiye waya, shawarar daya yanke itace lallai zai ɗauki raihana kawai yabar garin da ita, har momy ta sauko dan baisan abinda raihana tayiwa momy ba, haka dai ranar ya kwana saidai ya saƙa ya kwance,

***

*Y*ana tashi da asuba, wanka yayi , yana fitowa wanka wayar raihana ya kira cewa tayi sauri duk abinda zatayi yana zuwa gida yanxun nan, yana faɗin haka ya kashe wayarshi, ya wuce masallaci,

Umma kuma tace waye yake kiranki ne?""",,,,,,, raihana tace Faruk ne, Umma tace lafiya?""",,,, raihana tace wai yace in shirya yana zuwa yanxun, umma tace to tashi ki shirya tunda baki san abinda zai kawo shi ba..............................
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)


WHATSAPP NO:
+2349030159301
[1/8, 9:44 PM] Jamila Musa Ws: 💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦

*Page* 4⃣3⃣

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹
***

*MACE TA GARI*:• Abokin zaman ki bazai taɓa yiyuwa ki sameshi 100% ba, don haka zai iya kuskurewa, rayuwar Aure zo mu zauna ce kuma zo mu ɓata saboda haka ba kullum ne za,asha zuma ba, Rayuwar aure tana buqatar haquri juriya da yiwa juna afuwa, Abokin zamanki yana da halaye biyu , mai kyau da marar kyau, idan yayi miki marar kyau ɗin toh ki hararo ɓangaren mai kyau ɗin yin hakan na iya sanyaya miki rai ya kuma rage miki raɗaɗin damuwarki,

Babu yadda xakiyi ki samu abinda kike buri a xaman aurenki 100% domin kuwa a duniya kike rayuwa ba"a Aljanna ba, duk halin rashin jin daɗin rayuwar aure da kikeyi da abokin zamanki akwai wayanda nasu yafi naku muni don haka saiki godewa Allah ki kuma miqa lamuranki gareshi, zaman lafiyar rayuwar aurenki tana buqatar agaji daga wajen Allah saboda haka ki rinqa saka shi a cikin addu"o"inki,

zaman aure yana buqatar sirri saboda haka ki taqaita bayyana matsalolin gidanki ko daga waliyyenki ne, Acikin makusan tanki bazai rasa maqiyan ɓoye ba, da masu maki hassada saboda haka bayyana matsalalin gidankina iya faranta musu sai kiyi hattara da masu baki shawara,

*Nagode sosai saƙon yaxo gareni SAFEENAH IDREES JA"EH { SAFFAH ONEE } nagode sosai da addu"a,*

Masoyana ina tare daku baki ɗayanku duk inda kuke a faɗin duniyar nan saƙon ku yana zuwa gareni ngd sosai da addu"ar ku, masu bina PC idan kunga banyi reply ba kuyi haƙuri don Allah ba ina basarwa daku bane, A, a wallahi abubuwane sunyi yawa ngde sosai da addu"a har kullum ina cewa kune *MAUDU "INA* taku har kullum mai san farin cikinku wato *MEELAT MUSA*

*ZAWARCI*

****

*U*mma tace towai ina zakije ne?"""",,,,,raihana tace Oho Umma nima dai ban sani ba, amma koma dai miye ni bama zan wanije ba,,,,,,,,, umma tace kull kada ki kuskura kiyi haka, mijinki ne idan dai har kina san samun tsira da dacewa da rahamar Allah kiyi biyayyawa mijin

Please Login or Register in order to submit comment