Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

magana har suka gama abinda suke, suka fito,,,,

Raihana ta gyara kicin ɗin ta goge,,,, sannan tace kai kuma idan an gama sai ka wanke kwanukan,,,, hararta yayi cikin sigar wasa sannan yace bazan wanke ba,,,,,,, raihana tace to ni bara in wanke in samu ladar, tattara kayan tayi ta nufi kicin,,

****

*T*ou pha, yau gaban raihana sai faɗuwa yake, tsoronta ya bayyana, duk bata cikin mood ɗinta,,,, kana ganinta saika gane,,, faruk yayi juyin duniya ta faɗa mashi abinda yake damunta taƙi ta faɗa,,,, tun yana rarrashinta har ta fara bashi haushi,,,,, sai yanxun ya gane damuwarta wato bata san suje ganin zainab,,,, kanshi ya jinjina dan ya gano matsalar ,,,, kallon raihana yayi dake zaune gefen gado sai goge hawaye takeyi,,, tsaki yayi sannan yace mamana abin tsoro ne a wurinki?"",,,,, raihana tayi shiru, dan faruk bazai gane ba, kuma kai tsaye bata isa ta fito fili ta faɗa mashi ba,,,,,,,,

yace to nagode,,,,,, idan ma bazaki je ba komai nine suka zamar ma dole don haka ki barshi kawai bama sai kinje ba,,,,, raihana cikin kuka tace nifa ba haka nake nufi ba,,,,,, cikin ɗaga murya faruk yace kada Allah yasa kije idan kinje ban gode ba,,,, wannan ai shirman banza shirman wofi,,,,, raihana da sauri ta miƙe tsaye tasha gaban faruk dake ƙoƙarin fita daga ɗakin,,, tace tsaya kaji cikina yake ciwo fa,,,,,,

wani irin kallo yayi mata sannan ya janyeta gefe guda ya fita daga ɗakin da gudu tabi bayanshi ta sake shan gabanshi ta durƙusa sannan ta haɗa hannuwan ta biyu tace don girman Allah kayi haƙuri wallahi baka fahimceni ba,,,,,, ganin faruk zai wuce yasa raihana riƙe ƙafafuwanshi ta saki wani irin kuka mai ban tausayi,,,,,,, harya fara jan ƙafarsa ya fara tafiya ta riƙe ƙafar gamm,,,,,,, taci gaba da kuka tana cewa don Allah miye haka?"",,, kayi haƙuri mana,,,, tsayuwa faruk yayi,,,, amma baiyi magana ba,,,,,

raihana ta miƙe tsaye tana kakkaɓe jikinta,,,,,, kallon faruk tayi sannan tace don Allah ka daina saurin fushi,,,, ni bance bazanje ba,,,, cikina ne yake ciwon kai , tayi maganar cikin sigar yarinta,,,,,,, abun ya bashi dariya amma baiyi dariyar ba,,,, har yanxun fuskar nan murtuke take kamar wanda yaƙi ya riga fada,,,,,,,

raihana tace kayi haƙuri?"",,,,,, yace to shirya muje,,,,,, wata "yar rawa tayi sannan ta nufi ɗaki da gudu,,,,, zama yayi saman kujera,,,, sannan yayi murmushi wai cikinta ne yake ciwon kai,,,,,,,, har ta shiga ɗaki ta fito kuma,,,,, yace miye?"",,,,, tace wanka zanyi fa,, kallon agogon hannunshi yayi sannan yace to yi sauri bara inje wani wuri in dawo kafin ki gama,,,,,, raihana tace vyeeee,,,,,, baiyi magana ba,,,, yayi waje,,,,,, ɗaga murya tayi tana cewa nace fa a dawo lafiya,,,,, yace ai naji,,,, lekowa tayi waje sannan tace yau sarauta kake ji ko saraki?"",,,,, baiyi magana ba, ya wuce,,,, ita kuma ta koma ɗaki ta shiga wanka,,,,,,,,

Bayan ta fito, wayarta ta ɗauka ta kira farida,,,, bayan sun gaisa raihana ta fashe da kuka tace nidai ki taimaka man da addu"a zamuje ganin ƙanwar mai gida,,,,, nasan kila mamanshi zatace sai ya sakeni ne,,,,,, nidai Allah ya haɗani da jarabtar uwar miji bata ƙauna na, bansan abinda nayi mata ba,,,,,,,, farida tace ki kwantar da hankalinki, insha Allah babu abinda zai faru sai akairi raihana tace to Allah yasa,,,, farida tace amin,,,,,,, kashe wayar tayi sannan ta fara shiri,,,,

Harta gama faruk bai dawo ba,,,,,,, wata zuciyar tace mata kodai faruk yayi fushine ya tafi?"",,,,, ajiyar zuciya tayi sannan tace lallai aiko daya kai sarkin fushi,,,,,, wayarta ta ɗauka ta fara kiranshi,,,,,,,,, bai ɗauka ba,,,sake kira tayi ,,,,, bai ɗauka ba,,,,bayan wayar ta tsinke ne,,,,, ya turo mata text wai yana meetig, zaizo insha Allah,,,, bayan taga text ɗin baki ta taɓe sannan tace a bayyane kullum meeting kullum meeting,,,,,,,

Kwanciya tayi,,,,,, saman gado,,,, tace ni umma ko da wace waya zan riƙa samun ta ne?""",,,,,,, baiwar Allah tana can ko wane hali take ciki yanxun?"",,,,, Allah sarki rayuwa,,,,,,,,,, haka duniya take,,,, goge hawayen da suka zubo mata a fuska tayi,,,, sannan tace insha Allah uma muna dawo zanzo wurinki,,,,,,

Wayarta ta duba dan ganin mai kiranta,,,,,,,, tace Ummm ,,, a daidai lokacin data ɗauki kiran,,,,,,, yace kin gama ne?"",,,,,, raihana tace Eyy yace don Allah dafa man lepton na kusa isowa,,,,, raihana tace to, bayan ta gama ne ta ajiye wayar ta nufi kichin,,,,, bata daɗe da shiga ba, ya shigo gidan,,,,,, kai tsaye dama kicin ya nufa,,,,, raihana tayi mashi sannu da zuwa,,,,,,,

Yawwa yace,,, yana nan har ruwan zafin ya tafasa,,,, da kanshi ya juye a kofi, sannan yace ɗauka man muje,,,,,, a daidai lokacin da yake ɗaukar wayarshi yana cewa ina zuwa don Allah,,,,,,,,, ya kashe wayar,,,, suna fita ta ajiye mashi a farlo ita kuma ta nufi ɗaki,,,, ɗaukar kofin yayi yabi bayanta yana cewa baki cewa a ɗaki zamu je,,,, shima bayanta yabi ya shige ɗakin,,,,,

yana shiga yayi dariya ganin raihana tana ta shirya kaya,,,,, yace ina zaki da su?"",,,, raihana tace ko sunyi kaɗan ne?"",,,, murmushi yayi a daidai lokacin daya kai kofin a bakinshi ya fara shan lepton ɗin,,,,,,,, ta saman kofin yake kallonta,,,, ita kuma harkar gabanta takeyi,,,,, saida ya gama sannan ya miƙe daga inda yake,,,,,,kusa da ita ya matsa ya riƙe hannunta,,,,,,,,,,

Kallonshi tayi tace miye?"",,,,, yace nace ina zakije da kaya ne?"",,, raihana tace ba kace zamuyi tafiya ba?"",,,,, murmushi yayi sannan yace sai kace wasu "yan gudun hijira hajiyata?"",,,,,, tace sunyi yawa ne?"",,,, yace babu abinda zaki tafi dashi,,,, raihana tace bazamu kwana ba?"",,,, baiyi magana ba,,,,,, inda ta ajiye gyalenta da jakarta ya ɗauko ya miƙe mata yana cewa muje,,,,,, ansar gyalen tayi ta yafa,,,, shi kuma ya riƙe mata jakar, suka fito,,,,,

suna fitowa wani yaronshi yace ranka ya dade kawo a riƙe,,,,, kallonshi faruk yayi sannan yace aikin hajiyane,,,,,,, raihana tace nidai bani jakana kada ace ka zama mijin hajiya,,,, murmushi yayi sannan ya maida dubansa wurin raihana yace ke sai yau kika san na zama mijin hajiya?"", yaci gaba da cewa ai tuni mutane sun sani,,,,,, hannunta yaja har yanxun jakar tana hannunshi,, haka suka isa har wurin da aka shirya motoci,,,,,, sai filin jirgi,,,,,,,,


tou pha zo kaga raihana a cikin jirgi daka ganta kasan sabon shiga ce,,, sai raba idanuwa takeyi kamar wanda tayi ma sarki ƙarya,,,,,,, saidai ta kalli faruk ta kalli kanta,,,, shi baima san tanayi ba,, to bayan jirgi ya gama ibarsu mutane,,, aka rufe sai egypt....,,,,

Suna isa faruk yayi ma wani abokinshi waya,,,, cewa sun iso,,,, yace to yana zuwa yanxun insha Allah,,, faruk yace ba damuwa ,,,,, bayan ya gama wayar ne,,,, yace ma raihana tsaya kiga matarshi wallahi sanshi take sosai,,, raihana tace to dama an taɓa macen da batasan mijinta?"",,,,, kusa da ita ya matsa sannan yace ke yarinya wannan soyayyar tasu ta daban ce,,,,,,, raihana tace haba kila dan baya da saurin fushi shi yasa suka fahimci juna,,,,,,, murmushi faruk yayi sannan yace abin kuma harda habaici?""",,,,,

raihana batayi magana ba,,,,,,, faruk yace yawwa gasu can sunxo,,,, muje,,,,, kama hannunta yayi suka isa wurin,,,,,, faruk ya buɗe mota raihana ta shiga,,, sannan shima ya shige,,,,, suna shiga matar ta juyo sannan tace ranka ya daɗe daba kaine ba,,,, babu mai fito man da miji cikin daren nan,,,,, faruk yayi murmushi sannan yace kin fara ba?""",,,,,, abokinshi nasir yace gaskiya ta faɗi ai,,,,,

Kaima kasan irin wannan lokacin ai lokacin masoyane,,,,,, duk wani maiji da kanshi ai yana can rungume da matarshi,,,,, matarce tace sannu baiwar Allah,,,,, raihana tace yawwa,,,,,,, tace kece raihanar?""""",,,,,, ai munji labarinki tun kafin mu ganki,,,, to ina maki murna gaskiya,,, amma saidai kinbi sannu dan wannan mijin naki yan..... Faruk yace waike mie haka?""",,,,,,, tace to nayi shiru,,,,, kallon raihana yayi wanda hankalinta sam ba a wurin firansu yake ba,,,, tunanin yanda zasu haɗu da momy kawai takeyi,,,,,,, su kuma haka sukaci gaba da ma faruk shakiyanci,,,, wani yayi magana wani ya barsu danshi ba mutum bane mai san surutu,,,,,,

haka dai sukaci gaba firarsu har suka iso asibiti,,,,,,,, bayan nasir yayi parking , gaba ɗayansu suka fito,,,,,,, kallo ɗaya zakayi wa raihana ka gane tana cikin tashin hankali,,, matar nasir ta kalli faruk sannan tace miya sami matarka ne?""",,,,,,, baki faruk ya taɓe sannan yace bansani ba,,,,,

nasir ne yace kila gajiya ce,,,,, itama mai maganar ai haka takeyi idan munyi tafiya,,,,,, murmushi sa,adatu tayi sannan tace ai tafiya nidai tana wahalar dani,,,,,,,, da nasir da faruk sukayi gaba,,,,, da raihana da sa,adatu kuma suna bin bayansu,,,,,, har suka isa ɗakin da su momy suke,,,,,,

Bayan sun shiga ne,,,,,,, kowa ya samu wuri ya zauna, dan momy tana toilet,,,,,,,, inda faruk yake zaune kusa dashi raihana taje ta zauna kamar zata koma cikin cikin shi, da wutsiyar idonshi yake kallonta, sai yaji duk ta bashi tausayi,,,,,,, zainab dake kwance tace yaya sannu da zuwa,,,,, yace aha,,,, ta gaishe shi,,,,, yayi mata sannu,,,,,, sa,adatu tace zainabu ya jiki?"",,,, tace da sauƙi aunty,,,,,,,, shima nasir yayi nata sannu,,, raihana ma tayi mata ya jiki amma bata ansa na raihana ba,,,,,,,,

faruk yace bakiji ana maki sannu?"",,,,,,, tace nace yawwa,,,,, momy ce ta fito daga toilet,,,,,,,, kowa ya fara gaisheta,,,,,, hafsat ce itama ta shigo,,,,,,, to raihana dai duk tabi ta rikice, wai ance da ɗan fulani ga aljanna ga garken shanu,,,,, yace aini duk ma kun rikitani,,,,,

Raihana ce ta fars gaishe da momy amma saita share tana cewa umar ya hanya?",,, yace alhamdulillah,,,, bayan sun gaisa da nasir ne,,,, yace ranka ya daɗe bari muje mu dawo don Allah wani saƙo zamu anso,,,,, faruk yace babu damuwa,,,,, ita sa,adatu ta fahimci wani abune, don haka ta tura mijinta text wai su fita,,,, don haka tashi sukayi suka bar ɗakin,,,,,,,

Kamar jira momy take su fita tace ma raihana dan ubanki ke baki iya zama dole sai kinje kusa dashi ne?"",,,,,, ke nan "yar mitsitsiya dake kinsan daɗin miji,,,, ɗan guntun tsaki tayi sannan tace tashi daga nan dan uwarki,,,,,, raihana tace to,,,, miƙewa tayi daga wurin ta koma wani wuri daban ta zauna,,,,,

faruk yabi raihana da kallo ba damar yayi magana,,,,,,, momy tace ka tashi kaje ka huta,,, dare yayi,,,, faruk yace to,,,,, miƙewa yayi sannan yace raihana tashi mu tafi,,,,, momy tace ina zaka tafi da ita ne?"",,,,, yayi shiru,,, momy tace kayi tafiyarka ka huta,,,, ka barta nan cikin "yan uwanta tayi kwanciyarta mana,,,, faruk yace to,,,,,,,

kallom raihana yayi sannan yace zo...........
[1/8, 9:46 PM] Jamila Musa Ws: 💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦

*Page* 4⃣5⃣

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*JAMEELA MUSA*

***

Karku manta da shi mai taken *RASHIN RABO* yanan tafeeeeeeeeeeee,

***
*M*omy salati tayi tare da tafa hannunta ta riƙe haɓarta,,,,, tace umar yaushe ka zama sakaran namiji?"",,, yaushe ka koma namijin da baya da aji?"",,,, yaushe ka bari mata suka daina binka saidai kai ka bisu?"",,, wannan yarinyar har zaka bari tayi ta juyaka kamar mijin tace?"",,,,,, innalillahi gaskiya "yan maza sun laushi,,,,,,,,,

Faruk yace kiyi haƙuri kawai saƙo zan bata ne,,,,, momy tace wane irin saƙone da bazaka iya bata a gabanni uwar dana haife ka da cikina?""",,,, murmushin ƙarfin hali faruk yayi sannan yace raihana barshi,,,,,, yana faɗin haka ya fita daga ɗakin,,,,,, yana fita momy ta tashi cikin zafin rai tayi kan raihana takai mata wani irin mari,,,, sannan tace shegiya na bani garin aure aure gayanan ya auro mayya zata kashe man ɗa,,,,

Hafsat tace don girman Allah momy ki daina, wannan bai kamata ba wallahi,,, ƙaramin yaro ma kayi mashi abu ya riƙe bare ita da hankalinta da komai,,,, duk abinda kikai mata zata riƙeshi saita aihu ta faɗa ma "ya"yanta kuncin da kikai mata zasu rayu cikin ƙiyayyarki saboda baki ƙaunar uwarsu,,,,

Kuma da kika hana tabi mijinta ina ruwanki dasu?"",,,, ya daɗe bai maidata cikin cikinshi ba dan tsananin kauna,,,, wani mari momy takai ma hafsat sannan tace kema asirin ya kamaki ko ba haka ba?"",,,, toni dan uwarta duk tsafinta nan zata ganni tabarni,,,, kuma sai kin rabu da ɗana dan uwarki tunda ba innarki ta haifa manshi ba,,,,,, hafsat zatayi magana momy ta sake kasheta da mari,,,,,, raihana dai anyi muƙuiii, sai raba idanuwa takeyi,,,,,,

Faruk yana fita,,,, duk yaji babu daɗi,,, baima san ranar da momy zata daina wannan halinba,,,,, sauƙi ya nemar mata, sannan yayi murmushi,,,,, kai tsaye wurin motar su nasir ya nufa,,,, ita matarshi ma harta fara bacci tana kwance da kanta saman kafaɗar mijinta,,,,, yana zuwa yace ma nasir suje,,,,,,,, shiga mota yayi suka bar wurin,,,,,,,

Duk sanyin da ake momy ta hana raihana ɗaukar bargo ta lullɓe,,,,, kuma ta ɗauke katifar wai saidai ta kwana a ƙasa,,,,, hafsat tace towai momy mijinta ne fa ya siyi komai na wurin nan, sai ki bar mashi mata a ƙasa sanyi ya kamata,,,, momy tace hasatu idan kika sake magana saina tsine maki albarka,,,, zainab dake kwance tace momy duk miyayi zafi ne?"",,,,, momy tace uwarki tayi zafi,,,, shiru sukayi babu wanda ya sake magana ganin momy duk ta haukace lokaci guda,,,,,,,

Haka raihana ta raɓa ƙasa ta kwanta,,,,, saman tantagaryar tayils,,,, ga sanyin ƙasa gana sama,,,,,,,,,,

A ɓangare faruk kuwa sai juyi yake ya kasa bacci da tunda yazo da raihana abuja bai kwana babu ita ba,,,,, kullum yana bayanta,,, ita kuma tana gabanshi yana rungume da ita,,,, lallai yau ya ƙara ganewa raihana ta shiga rayuwarshi sosai,,,,,, murmushi yayi sannan yace ko zata iya bacci ne?"",,,,, yace lallai momy kinyi haƙunci sosai,,,,,,, Haka yayi ta juyi amma fur bacci ya gagareshi, tashi yayi yaje yayi alwallah yayi ta sallah,,,,,

***
*T*unda safe momy ta tashi ta fara jaraba,,, wai tanajin jiya umar sai turo ma wannan yarinyar saƙo yakeyi a cikin waya,,, babu wanda yayi mata magana,,, haka ta ƙari jarabarta harta gaji da kanta tayi shiru,,,

Raihana data kwana batayi bacci ba,,, ta kalli inda wayarta take data rufe tun jiya,,, amma momy tace ita faruk yake turawa saƙo,,,,,,, hafsat ce ta shiga tayi wanka bayan ta fito zainab taje tayi , duk sun gama,,, raihana ta miƙe,,, momy tace dawo, dawo nan dan uwaki,,,, uwar mi zakiyi ne?"",,,,, raihana tace wanka zanyi,,,, momy tace wato kishi kike yi da "ya"yana?"",,,,, O wannan yarinya bakiji daɗin halinki ba gaskiya,,,,,,,

raihana komawa tayi ta zauna,,,,, tana kallon momy ,,,, momy tace kallarni da kyau kurwata tafi ƙarfinki aradun Allah,,,,,, raihana dai batace komai ba,,,,,,,, suna nan zaune kowa yayi jugum, babu mai magana,,,,,,,,,,

wayar momy ce ta fara ƙara miƙewa tayi ta nufi inda wayar take,,,, ganin faruk ne yake kira yasa tace yau da yake matarshi ta kwana anan kunga tunda safe yake kirana,,,,,, yasan ba dama ya kira wayarta tsaki tayi sannan ta ɗauki wayar,,, suka gaisa yayi mata yamai jiki,,, tace da sauƙi,,,,, sannan ta kashe wayar,,,,,

Nasir dai abokin faruk ne,,,,, sunyi makaranta tare shima yana da rufin asiri daga baya Allah ya kawo mashi karayar arxiki,,, shine faruk ya jawoshi yasa shi cikin harkokinsa,,,, to akwai abinda yake a egypt faruk ya bashi gida yake zaune a ciki,,,,

tunda su momy suke zaune a asibiti daga gidan nasir ake kawo masu abinci na safe, rana, da dare,,, nasir yana kuƙa dasu sosai, dan yace faruk ba ƙashin yadawa bane,,,,

to mai aikin gidan nasir koda ya kawo masu kayan break momy cewa tayi banda kason raihana,,,,,, kamar wata mayunwaci,,,,, hafsat ce tace momy idan kin hanata mi zaiyi maki?""",,,,, momy tace hasatu idan baki fita harkata ba na rantse da Allah saina munanta ki,,,, ko banaci da in bata gara na zubar dashi a kwata,,,,,

hafsat tace to Allah ya tsare,,,,,, momy tace amin dan kutumar ubanki,,,,, hafsat tabi momy da kallo ganin duk tabi ta firgice,,,,,

faruk baizo asibiti ba,,,, saida rana sosai,,,, momy tace sai yanxun kaga damar zuwa ne?"",,, faruk yace naɗanje wani wurine,,,,, momy tace aida ka bari sai gobe kaxo, yace ayi haƙuri,,,,, haka kowa ya gaishe shi,,,,,,, ya ansa,,,,, itama raihana gaishe shi tayi,,,, kallonta tare da sakar mata wani lallausan murmushi mai sauke kasala,,,, itama murmushi ta mashi duk wannan abun da sukeyi saman idon momy,,,,,, kanta girgiza sannan a ranta tace lallai umar ya mallaku,,,, har wani murmushi yake mata,,,, ina macen ta isa,?"" ko ɗiyar zinarice ,,,,

Haƙiƙa umar yayi sanyi,,,,, kuma koba komai yarinyar nan tana tare da wani ɓoyayyen al"amari tare da ita,,,,, maganar hafsat ce ta dawo da ita daga tunanin da takeyi tana cewa momy wayarki ake kira tun ɗaxu,,,, ɗaukar wayar tayi sannan tabar ɗakin,,,,,,

tana fita faruk ya matsa kusa da raihana dake zaune ƙasa,,,, ɗan durƙusawa yayi ya matsa sosai sannan yace hajiyata barka da rana,,,,,, kallonshi raihana tayi sannan tace ina yini,,,, hannunta ya riƙe hafsat ganin ya riƙe hannun raihana yasa ta fita,,,,, ita kuma zainab taja bargo ta lulluɓe fuskarta,,,,,,, kama hannun raihana yayi ya ɗaga ta,,,,, sannan ya rungumeta yana sauke ajiyar zuciya a wahalarce,,,,, hannunta ya riƙe yana ɗan murzawa a hankali,,,,, sannan yayi magana a daidai kunnenta yace hajiyata jiya banyi bacci ba,,,,, gaba ɗaya tunaninki nake,,,,,,, raihana tace nidai kada momy taxo ta ganmu haka don Allah yace ke basar ,,,,,, ya ƙara riƙeta sosai,,,,,, raihana dai tasan idan aka gansu haka tafi kowa shiga matsala don haka ta zame jikinta daga nashi,,,,,, kallonta yayi sannan yace miye haka?"",,,,,,,

Ɗan lumshe idanuwanta tayi sannan tayi murmushi,,, batayi magana ba,,,, momy ta shigo ɗakin,,,,, tana kallon faruk dake tsaye,,,, sai kuma ta kalli raihana,,,,, shidai ko kwalar rigarshi amma kallo ɗaya zakayi wa raihana ka gane akwai wani abu,,,,,, dan haka itace ta tona su,,,, yanda take kame kame ne yasa momy ta gane wani abu ,,,,,,, maida dubanta tayi wurin faruk sannan tace to tafi tunda ka gama ,,,,,,,, sosa kanshi yayi sannan ya duka ya ɗauki wayarshi yayi waje,,,,,,,,,,,

momy tabi shi da kallo harya fice ,,,,,,, kallon zainab dake kwance ta rufe fuskarta tayi sannan tace zainaba lafiya?"",,,, zainab ta buɗe fuskarta sannan tace momy,,,,,,,

kusa da ita momy ta matsa sannan tace miye?"",,,, zainaba tace momy kibar yaya ya tafi da matarshi a daidai lokacin da hawaye suka zubo daga idonta,,, taci gaba da cewa wannan ya isa ya zamar maki darasi momy yaya yayi aure fiye da mace babu adadi dan faɗin baya da amfani ko fa"ida,,,, amma abin dubawa anan shine tunda har Allah yasa ya samu natsuwa da wannan kada ki raba shi da matarshi, don girman Allah ki fita harkarsu ,,,,

dan da tana da matsala ko wani abu kinsan yaya ba,a rakashi kashi a baro shi wallahi ke kanki kinsan da ya rabu da ita yanxun,,, dan abinda na fahimta rabashi da raihana tamkar yanke halaƙa ne tsakanin rayuwa da lumfashi,,, da kunne naji yana cewa jiya baiyi bacci ba,,,,,, yana faɗa mata ynda daren jiya ya kasance ba tare da ita ba,,,,, momy na roƙeki kiyi haƙuri idan wani abu yarinyar nan tayi maki ki sanar da ita zata gyara don Allah,,,,

Momy tace zainab keda nake alfahari dake kema zaki kware man ba ko?"",,,, zainab dake kwance ta tashi zaune sannan ta kamo hannun momy ta riƙe,,,, tace momy kina iya faɗin mace nawa yaya ya aura ya saki?"",,, kinsan dalilin da yasa yake rabuwa dasu?""",,,,, kinsan wane irin abu suka shuka mashi?"",,,, to lamarin namiji da mace ba wani ne ya koyama kowa yanda zaiyi rayuwar aure ba,,, kowa tashi take ficceshi,,, don haka kiyi haƙuro tun kafin ki jefa ɗanki cikin wani hali,,,

hafsat dake gefe tsaye ta matso kusa da inda momy take zaune tace momy idan baki manta ba,,,,,,, yaya yace maki baya iya rayuwa da macen da bata san kanta ba, kuma tsanani idan ya daɗe da mace wata biyu ne,,,,ya korata ya kawo wata,,, wata macen ma bata sati ukku a gidanshi,, amma ita wannan gata tayi kusan wata takwai mi kika fahimta game da zamansu?"",,,,,,

Zainab tace aunty hafsa mata wane iri ne yaya bai gani ba?"",,,, kuma tunda yake aure bai taɓa auro sakarar mace ba,,, mata masu aji ya auro wa,,,, wayayyi "yan boko wanda suka san kansu,,,,, amma babu wanda yasan abinda yasa yake rabuwa dasu,,,,,,,,, duk macen daya aura iyakarta wata ɗaya biyu tayi tsananin daɗewa,,,, to an auro mai wata takwas,,,,,,

momy tace idan na fahimceku kuna bayan ɗan uwanku, zainab tace kema kina bayan ɗanki ,, dan duk macen da yake aurowa wannan kika ɗauki ƙaran tsana kika ɗoro mata,, mi tayi maki momy?"",,,, momy tace to dan nace ta zauna nan shikenan sai abun ɓacin rai?"",,,, hafsat tace to miyasa shi ɗan naki baki ce ya kwana anan ba?"",,,, shine ɗanki shi kike iko dashi dasai kice ya kwana,,,,,,,, momy tace aiku yarana baza ku gane abinda nake nufi ba,,,, hafsat tace duk mun fahimceki amma yau kibar miji da mata su kasance tare,,,,,, momy tace aisai yaxo ya ɗauketa,,,,, da hafsat da zainab sukayi dariya,,,,, momy tashi tayi ta fita dan duk "ya"yanta su kware mata baya,,,,,,,

bayan ta fitane,,,, hafsat ta kalli inda raihana take zaune sannan tace matar yaya,,,, wai miyasa kika firgita mana yayanmu ne?"",,,,, zainab tace haba keko ƙanwar miji miyasa kike wannan tambayar?"",,,,dariya sukayi suka kashe amma raihana ko inda suke bata kalla ba,,,,,,,, hafsat tace gaskiya yarinya Allah ya baki sa"ar rayuwa, dan yayanmu jarumin namiji ne ba ko wace gajalar mace zata iya kamashi ba,,,,,, mudai fatanmu Allah yasa ki zama mai adalci,,,,,, zainab tace amin,,,,,

da daddare da faruk yaxo dubasu ya ɗan daɗe sosai , suna fira da momy amma duka babu wanda ya saka baki a cikin maganarsu,,, dan dama idan momy tana magana da faruk bbu mai cewa tuff harsai ya tafi sannan zasu samun bakin magana,,,,

haka suka gama firarsu sannan ya miƙe yayi masu saida safe,,,, inda raihana take zaune ya kalla sannan yace "yan mata zan tafi,,, raihana tace sai da safe,,,,, yace yawwa,,,, harya kusa fita daga ɗakin ya juyo yace raihana babu rakiya?"",,,,, momy tabisu da kallo su duka biyun,,,, ita dai raihana batayi magana ba,,,, faruk yace dake nake,,,, tayi shiru,,,, yace zo kiji,,,,, raihana dai batayi magana ba kuma bata tashi ba,,,,,, momy tace tashi kije,,,,, raihana ta kalli momy ,,,,, kai momy ta ɗaga sanna tace jeki, saida safe,,,, faruk dake tsaye yace momy saida safe kika ce?"",,,,,,,

tace Eh,,,,, kaga yau sai kayi bacci,,, subahanallah inji faruk da sauri ya fice daga ɗakin,,, dariya momy tayi sannan tace raihana jeki,,,,,, kunya ta hana raihana tashi momy tayi juyin duniya amma raihana tace ita anan zata kwana,,,, hafsat tace ke tashi ki tafi kinji ,,,,, raihana tace ita dai A, a, momy da kanta ta tashi ta isa inda raihana ke zaune ta kama hannunta taja ta suka fita daga ɗakin......

tana fita hannun raihana na riƙe hannunta ta fara kiran wayar faruk tace ya tsaya tana zuwa,,,,, momy na fita daga ɗaki da zainab da hafsat suka sheƙe da dariya sannan suka kashe,,,, zainab tace momy taji ance jiya ɗanta baiyi bacci,,,, haka da sukayi ta shaƙiyanci,,,,,,

itako momy har wurin mota takai raihana da kanta ta buɗe motar ta tura ta ciki,, sannan ta rufe,,,, ta juya ta tafi,,,,,, faruk bai tafi ba yabi momy da kallo harta ɓace,,,,, sannan ya maido dubanshi ga raihana yace waye yace ma momy banyi bacci ba?"",,,, raihana tace kana tunanin nice zan faɗane?"",,,, lakatar mata hanci yayi sannan yace nidai ba ruwana a daidai lokacin da yake fara tafiya da mota,,,,,

Momy kuma tana tahowa wuri ta samu tasha kukanta sosai wanda ita kanta bata san dalilin yanshi ba,,, saida ta gama kukanta sannan tace Allahidan yarinyar nan alkairi ce a rayuwar umar Allah kasa man ƙaunarta cikin raina, idan tana da wata manufa ta daban Allah ka ankarar da umar ya gane,,,, ya rabu da ita,,, uhum niko nace ga abinda ya kamata kiyi tun farko,,,,,,

Huhuuuuuu suko masoya sun samu yanda ake so,,,,, suna zuwa masauki raihan da sauri ta cire kayan jikinta ta tafi wanka,,,, faruk shima towel ya ɗauka ya bayanta toilet ɗin yana cewa nima banyi wankan ba,,,,,, bayan sun fito daga wankan ne faruk yake ta dariya ,,, raihana kuma duk ta hayaƙa,,,,,, sai nunawa yake yanda take zama a gaban momy da yanda take magana,,, sai dariya yake mata,,,,, ita kuma tayi banza ta ƙaleshi,,,,,, kwanciya yayi saman gado sanann yace haka kike yin magana,,,,, fa,,,, ya fara kwaikwayon maganar ta,,, yanda yayi abun ne ya bata dariya dan babu banbanci da maganarta,,,, kallonshi sannan itama tace kaima ai haka kake yi itama ta fara nuna yanda yake a gaban momy da sauri ya sauko

Please Login or Register in order to submit comment