Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nufi ɗaki,,,, harta kwanta ta tuna batasha maganin da momy ta kawo mata ba,,, saukowa tayi daga saman gado ta shiga toilet, ta daɗe sosai sannan ta fito, tana fitowa farlo ta nufa komi tayi oho, bayan ta dawo ne, ta zauna a gefen gado,,,,,

zuwa wani lokaci ta tashi taje ta ɗauko maganin inda ta ajiye,, sannan ta ɗauki ruwa , ta fasa ruwan tasha a bakinta bata haɗiya ba ta riƙesu,,, tana ɓallar maganin faruk ya shigo,,, da sauri ta miƙe tsaye, ta ɓoye maganin a hannunta, niko nace waya ga marowaci,,,,

yanda tayi abunne yasa faruk yace miye?"",,,,, har yanxun bata haɗiye ruwanba, da su take magana irin mummmm,,, alamar dai akwai wani abu a bakin mutum,,, dariya yayi sannan yace mi kike ci ne?""" aciciya, a daidai lokacin daya matsa kusa da ita ya latsa mata cikinta, tayi dariya, har yanxun ruwan yana cikin bakinta,,,,,

shima dariya ya sakeyi sannan yace wai mi kike ci ke?"",,,, raihana ta girgiza kanta tare daja da baya,, dan samun inda zata yada maganin,,,, shi kuma ganin tana ja baya yasa shima ya fara binta, tana matsawa shima yana matsawa, harta isa wurin kusurwar bango ta maida hannunta ta baya ta ɓoye,,,,,,, kuma har yanxun baƙi ta haɗiye ruwan ta mashi magana,,,,,

faruk murmushi yayi yana cewa da Allah wai miye kike ɓoyewa,?"",,, kai ta girgiza alamar ba komai,,, yace to muga hannunki, miƙo mashi hannu ɗaya tayi ya riƙe sannan ya sinsina shi, murmushi tayi, shima murmushin sannan ya riƙe hannun yace muga ɗayan shima,,,, da sauri ta matse maganin a cikin cinyoyinta,,,, ta miƙa mashi ɗayan hannu, shima yanda yayi ma wancan haka yayi ma wannan , jawota yayi daga inda take rakuɓe,,, tana matsawo maganin ya faɗo,,, faruk yace muga abinda kike ɓoyewa, sai yanxun ta haɗe ruwan bakinta tana cewa Allah kada kasha man abu,,,,,

Duƙawa yayi ya ɗauki maganin,,,, gaban faruk ya faɗi, lokaci guda kuma yanayinshi ya canja,,,, kallon raihana yayi lokaci guda kuma launin idonshi ya canja,,,, wani matattacen murmushi wanda lokaci guda idonshi ya kawo hawaye, sannan yace innalillahi wa"inna ilaihir raji"un, ke kuma da wannan salon kika zo?"",,,,,, a daidai lokacin da hawayen suka gangaro daga idonshi,,,,

Ganin faruk yana kuka yasa raihana matsawa kusa dashi tana cewa miye?"",,,, wani irin kallo yayi mata wanda yasa ta sakin fitsarin tsaye,,,,, dan tunda take bata taɓa ganin faruk a irin wannan yanayin ba,,,, lokaci guda kuma jikinta ya fara kyarma,,,,, tsaki faruk yayi sannan yabar ɗakin,,, yana fita da gudu raihana taje ta rufe ƙofar ɗakin sannan ta dawo ta shige toilet ta cire kayan jikinta,

dawowa tayi ta gyara wurin taje tayi wanka ta wanke kayan data cire,,, bayan ta fito ta shirya, kasa fita tayi dan gaba ɗaya tsoron faruk ya kamata,,, zama tayi a gefen gado komi ta tuna Oho,,,,,, sai kawai ta kama kuka,,,,

shi kuma faruk yana fita ɗakinshi ya tafi,,,, yana zuwa ajiye maganin yayi,,,, ya shiga wanka, bayan ya fito, zama yayi a gefen gado,,, murmushi yayi sannan yace a bayyane gaskiya yarinya baki more ma faruk ba,,,,,, nine na more maki,,,,,

Raihana saida tasha kukanta ta gaji,,,,, sannan ta ɗauko wayarta ta fara kiran faruk, lokacin daya ga,,,,, kiran ta,,,,,, tsaki yayi sannan yace ai na gama dake , na goge babinki a zuciyata,,,,,,,

wani kiran ne,,,, ya sake shigowa,,,,,, bai ɗauka ba, haka tayi ta kiranshi amma yaƙi ɗauka,,,, ganin bai ɗauki wayar ba,,,, yasa ta tashi cikin dakiya ta nufi ɗakinshi,,,,,

sallama tayi ta shiga,,,,, amsa sallama itace ta zama wajibi, dan haka daga ita bai sake magana ba,,, raihana tace zaka sha lipton?"",,,, kallonta yayi amma baiyi magana ba,,,,,, yanda yake kallonta yasa taji gabanta na faɗuwa,,,,,,,, cikin tsoro ta dake tayi wurinshi,,, ta kusa hawa saman gadon yasa ƙafarshi ya halbata ta faɗi ƙasa,,,,,, cikin fushi raihana tace wannan wane irin wasa ne?"",,,,, yace baki san na isa mugun wasa ba saina fasa maki da bindiga, a daidai lokacin daya ɗauko bindiga daya ajiye a gefenshi,,,,,

da sauri raihana ta duƙe ta riƙe kanta da hannuwanta, ta rufe idonta ,tana jiran ta ina zataji saukar harsashi?"",,,,, jin bai harbeta yasa ta buɗe idonta tana kallonshi,,,,, faruk yace tashi ki fita,,, raihana tace wai mi nayi maka ne?"",,,,, tsawa ya daka mata tare da maimata abinda ya faɗa,,,,, kuka raihana ta fara, faruk yace shi kike so kiyi ne?"",,,, raihana tayi shiru,,,, yace tashi ki fita nace,,, bansan ganin ki kwata kwata,,,, ki fita tun kafin inbi ta kanki in wuce,,,,, cikin kuka raihana tace zan fita,,, amma saika faɗa man abinda nayi maka,,

rainin hankali wato bata ma san abinda tayi ba,,, faruk ya faɗa a ranshi,,,, miƙewa yaje inda take tsaye ya yayimeta saida ya fitar da ita farlo sannan ya koma ya rufe ɗakinshi,,,, miƙewa tayi ta koma ɗaki,,,,

haka ta kwanta cikin ɓacin rai, dan ita a haƙiƙanin gaskiya bata san komi yasa faruk yake fushi ba,,,, saida tayi kukanta ta gaji sannan ta kwanta bacci......

***

*A*bu kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba,,, dan kwata kwata yanxun faruk ya daina yadda yama haɗu da raihana,,,, kuma ko abinci yanda ta kawoshi haka zatazo ta ɗauka,,,, kuma idan zaiyi tafiya yama daina faɗa mata,,, zaiyi tafiyarshi,,, yayi iyakar kwanakinshi ya dawo,,, kuma idan ya dawo harya gama zaman shi raihana bata ganin shi,,,,,,,, waya ma idan ta kira baya ɗauka,,,, kuma idan ta tura mashi saƙo dashi da bbu haka ya ɗauka, dan baida lokacin karantawa ma,,,,

Dan haka ta gaji da zaman gidan duk yayi mata babu daɗi,, saboda tana ta ganin abinda bata saba gani ba,,,,,, magani kuwa idan momy ta kawo saida ta ajiye,,, tunda taga maganin ne ya haɗasu faɗa da faruk,,, duk raihana ta rame ga wahalar ciki,, ga kulawar da take samu yanxun babu ita,,, abinci kuwa kamar jaka haka takeci,,,,, amma babu kama bbu alama,,,,,

wayarta dake ringing yasa ta miƙewa,,,,,taje inda ta ajiyeta ta ɗauka,,,, ganin farida ne yasa tayi murmushi,,,,, bayan ta ɗauka suka gaisa,,, farida tace mata gani nan zuwa gidanki , raihana tace to Allah yasa kuxo lafiya,,,,, farida tace amin,,,,,,,

Raihana har tayi bacci ta farka bataji zuwan farida ba, don haka ta kirata, farida tace yi haƙuri gani nan insha Allah,,,, raihana tace to,,,,,

suna gama wayarne,,,,, ta tashi ta fito farlo,,,,, bata daɗe da zama ba, farida tayi mata waya, taxo, tashi tayi ta fita dan tarota, tana zuwa ta rungume farida,,,,, tana dariya,,,,, haka suka rantafo suka nufo ciki dukansu sai dariya suke su biyu,,,,

bayan sun shigo a farlo suka yada zango, suna gaisawa, dan raihana kwata kwata batasan faruk yana gidan ba,,,, shi kuma tun lokacin da raihana ta taro farida saman idonshi , yana kallonsu, da suka shigo farlo kuma duk maganar da suke kamar a gabanshi yana jinsu,,,,

raihana tace farida dama ina san kixo wallahi,,,, farida tace miye?"",,,,,, raihana tace muje ɗaki, farida tace ki muyi zamanmu anan mana, raihana ta matsa kusa da farida ta fashe da kuka,,,, faruk dake saurarensu gabanshi ya faɗi,, yace kardai yarinyar nan wani zata faɗa ma halin da muke ciki?"",,,,,

Bai gama tunanin ba yaji raihana tana cewa nidai banda lafiya,,,,, farida tace miya sameki?"",,,,, raihana cikin kuka tace "yan hanjina suke tsintsinkewa cikin tashin hankali farida tace wane irin "yan hanji kuma?"",,,, faruk dake sauraransu yayi tsaki sannan yace kaji wani shirme kuma?"",,,,,

Farida tace ya kike ji ne?"",,,, cikin kuka raihana tace cikina yake man yawo,,, farida tayi dariya sannan tace banza amosanin ciki ne,,,,, dan itama farida batasan ciki ba,,,, tunda bata haihu ba, ta taɓa ɓari so ɗaya, kuma har yanxun bata sake samun ciki ba,,,,, faruk saki ya sakeyi sannan kace kaji wata yarinta kuma,,,,,, banda sakarcin raihan farida likita ce?"",,,,,,

farida tace nidai lokacin da nayi irin wannan ciwon cikin likita cewa yayi in daina aiki sosai , wai ke ya kike jin abun ne?"",,, ita raihana bata san ciki ne ba,,,, ita kuma farida bata fahimce abun ba, dan haka gaba ɗaya sai shirme suke,,,, tsaki faruk ya sake yi sannan yace kaji wani hauka kuma,,,, wai ta faɗa mata yanda take ji,,,, tsaki ya sakeyi,,,,,,,

Maganar raihana yaji cikin kuka tana cewa,,,,, nidai ina yawan bacci, wani lokaci kuma inacin abinci sosai,,,, sai cikina,,, wana man wani wuntsil wuntsil,,, shidai baiji ƙarshen firarsu ba, saboda wayarshi tayi ringing ya ɗauka,,,,,

farida tace ke wannan ciwo naki saidai kije kiga likita, daga nan suka canja fira,,, wani faruk yajisu wani bayaji,, wani yayi dariya wani yayi tsaki,,, haka dai sukasha firarsu,,,, sosai, sannan farida ta tashi tafiya,,,,, raihana ta shiga, ta haɗo mata talatin da tara ta arziƙi,,,,,, tayi mata rakiya har wurin motarta,, saida ta tafi sannan ta dawo .....

tana dawowa, ɗaki ta wuce,,,,, tana shiga saman gado tahau ta kwanta, sannan ta ɗauki wayarta, ta fara kiran ƙawarta zulaihat, bata ɗauka ba,,,,,,

Dawowa tayi farlo ta zauna tayi jigum dan gaba ɗaya gidan ya daina mata daɗi,,,,,, wayarta ta duba dan ganin mai kiranta, zulaihat ce,,,,,, ɗauka tayi suka gaisa tace kwana biyu, zulaihat tace ai dama nasan saina aihu zaki zo,,, raihana tace insha Allah gobe zanzo,,,, niko nace kaji ƙarfin hali,,, ashe bani ba, har faruk yaji, to sai nazo insha Allah ta kashe wayarta,,,,,,

faruk tashi yayi sannan ya fito,,,, raihana dake zaune da sauri ta tashi zata ruga ya riƙota,,, rufe idanuwanta tayi da sauri tana ihu,,,,,, daɗe mafa baki yayi sannan yace ina zaki?"",,,,, buɗe idon tayi a hankali sannan tayi ajiyar zuciya, dan ita bata ɗauka yana nan ba,,,,,

Ƙara ajiya ajiyar zuciya tayi sannan ta gyara tsayuwarta, cikin shasheka tace ai dama nasan kaine,,,,, tana sake nishi kuma ƙarya take tsorata tayi,,,, ɗaure fuska faruk yayi sannan yace miya sameki ne?"",,,, har harxun nishi takeyi sannan tace ba komai,,, mika gani ne?"",,,,,,,, kallonta yayi sosai sannan yayi tsaki,,,, yace jeki shirya inkaiki asibiti,,,,,, raihana tace ka daina fushin ne?,,,, baiyi nagana ba,,,,, ya koma ɗaki,,,,,,,,,,,

Yana komawa ɗaki,,,, yace kila maganin da kike ɗirkawa kanki ne yasa maki matsala,,,,,,

Ita kuma tana zuwa ba ɓata lokaci ta shirya,,,, ta fito, ɗakinshi ta shiga, tace ta shirya, kallonta yayi sannan yace *KHADIJA* wato ainahin sunanta ya kira,,,, raihana tace na"am,,,, yace zo ,,, matsawa tayi kusa dashi,,, hannunta ya riƙo ya zaunar da ita kusa dashi, sannan ya dafa ƙirjinta yana halɓawa da alama tana cikin tsoro,,,, kallonta yayi ta ɗauke kanta,,,,, da hannunshi ya maido fuskarta tana fuskantar tashi yaci gaba da kallonta,,,,,,

raihana tace don Allah ka daina man haka wani iri yake man,,,,, faruk yace in tambayeki?"",,,,, raihana tace Eh, yace kada ki boye man komai,, tsakanin ki da Allah waye ya baki wannan maganin ?"",,,, raihana tace wannan magani maganin miye don Allah, wani kallo faruk yayi mata,,, sannan yace ni ban tambayeki ba,,, kina tambayana?"",,,, raihana tace idan har ka yadda dani maganin rashin lafiya ne,,,, faruk yace miya sameki ne?"",,,, raihana tace kawai ina yawan bacci ne,,,, yace to wane likita ya baki shi?"",,, raihana tace likita na ne,,,,, faruk yace waye shi?"",, raihana tayi shiru,,,

Juyawa bayanshi ya ɗauko "yar ƙaramar bindiga ya ɗora a saman kanta,,,,, zufa ta keto mata,,,, hawaye suka cika mata ido,,,, ta haɗiye miyan bakinta kamar ta haɗiye kunama,,,,,,,,,, tana kallon faruk jikinta sai karma yake,,,, faruk yace ko ki faɗa man wanda ya baki ko in fasa maki kai,,,, hannun raihana yana karma takai hannunta zata taɓa faruk yaja baya yana zaro mata ido yace ki faɗa man idan ba haka ba,,,,, anan zan fasa kanki inje inba karnuka su cinyeki kowa ya huta,,,,,,

kuka raihana ta fara sosai,,,, faruk yace kuka na tambayeki ne?"",,,, cikin kuka raihana tace don Allah faɗa man maganin miye,,,,sai in faɗa maka,,,, yace idan kika sake cewa maganin miye saina zaro maƙoshi na faɗa maki,,,,, raihana sai kuka takeyi ta kasa magana,,, dan bata san ko maganin miye ba,,, idan tace mamanshi ta kawo bata san yanda zai ɗauki maganar ba,,,,, dan taga ya ɗauki zafi akan maganin sosai,,,,,

Faruk yace inajinki,,,,,, sallamar da sukaji a farlo ne, yasa raihana ta yage baki tayi wani irin ihu tana cewa a kawo mata ɗauki,,,,...............

💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦

*Page* 4⃣8⃣

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

****

*C*ikin tsananin ɓacin rai momy ta sake cewa Assalamu alaikum,,,, sai yanxun raihana ta ɗauki murya dan haka tayi shiru bata sake kukan ba,,,, faruk kuma da sauri ya miƙe ya shige toilet,,,,,

Bai daɗe da shigewa ba,,,, momy ta bayyana a cikin ɗakin, da sauri raihana ta sauko daga saman gadon tana gaisheta,,,,, momy tace mi akayi maki kike kuka ne?""",,,,,,,

Cikin girmamawa raihana tace ba komai,,, momy tace an taɓa abinda baya da dalili ne?"",,,, raihana tayi shiru,,,,,, tsaki momy tayi sannan tace,,,,,, ya akayi umar yasan ina kawo maki magani ne?"",,,,

Raihana tace ni ban faɗa ba,,,,,, momy tace zanyi maki ƙarya ne?""",,,, raihana tace bance kina ƙarya ba,,,,, kiyi haƙuri momy don Allah,,,,,,, kallonta momy tayi sannan tace to faɗa man ya akayi umar yasan na baki magani?""",,,,

Raihana tayi shiru,,,,, momy tace ina magana,,,, raihana tace don Allah momy kiyi haƙuri, dan ita raihana ansa a tsakiya ,,,dan bata san yanda sukai da faruk ba,,,

Momy tace ina magana fa,,,,, kai innalillahi wa"inna iaihir raji"un, inji raihana,,,, cikin kuka raihana ta sake cewa nidai don Allah bansan komai ba,,,,, momy tace ina umar ɗin yake ne?"",,

Faruk dake toilet gabanshi ya faɗi, yace Allah yasa kada aciciya tace ina nan,,,,,,, bai gama tunanin ba, yaji raihana tana cewa ni bacci nake momy bansan ko yana nan ba,,,,, wato ta bada baki biyu, idan momy ta ganshi shike nan idan bata ganshi ba, shikenan,,,,,,,,

Momy tace keda ke kuka zaki ce kina bacci?""",,,,,, raihana ai farkawa nayi,,,, momy tace ƙarya kike yana gdan nan,,,,,,,, tsaki tayi sannan tace lallai ma yana ɗakin nan,,,,,,, faruk yace subahanallah,,,,,,, ita kuma raihana da sauri ta kalli ƙofar toilet ɗin,,,, hmm duk wanda yafi ka shekaru sai yafi ka tunani,,,,,,,

Momy ta kalli raihana sannan ta kalli toilet ɗin,,,,, tace Oho a can ya ɓoye ko?"",,,,,,, raihana tace nidai bansan ko acan ba,,,,,, jin an faɗi haka faruk da sauri ya cire kayan jikinshi ya fara wankan dole,,,,,,, dan yasan dole momy sai taxo tunda ta fara zargin yana ci,,,,, jin motsin ruwa yasa momy tayi dariya sannan tace duk ka gama iskanci ka fito ka sameni,,,,

Dan na faɗa maka gaskiya ka daina ɗauka wayata ko?"",,,,, ka daina zuwa gaisheni ko?"",,,,, to ko zaka kwana yau ina gdan nan saika fito,,,,, munafiki wanda baya san uwarsa,,,,,

Momy ta kalli raihana sannan tace ,,, dukanki yayi ne?"",,,,, raihana tace A, a, tace mi yayi maki ne?"",,,, raihana tace ba komai,,,, murmushi tayi sannan tace barni dashi,,,,

faruk har yanxun yaƙi ya fito,,,, dan baisan da wace momy taxo ba,,,,,,,, momy tace na rantse da Allah idan baka fito ba , zan maka rashin mutunci,,,,,, faruk yayi shiru,,,,, momy taci gaba da cewa idan na sake maka magana kasan sauran,,,,,, faruk goge hawayen da suka zubo mashi yayi sannan ya jawo rigar wanka yasa ,,,,, ya fito,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,

Yana fitowa daga bakin ƙofar toilet ɗin yayi tsaye,,,, momy tace ni zanzo nan in sameka?"",,,,,, har yanxun baiyi magana ba,,, kallom momy yayi sannan ya kalli inda raihana take tsugunne,,,,, murmushi yayi sannan yace momy wai miye?"""""",,,,,,

momy tace uwar kace,,,,,,, kallon raihana yayi sannan yace ke zo nan,,,,, momy tace bazata zo ba, dan ubanka,,,,,, murmushi faruk yayi da gefen bakinsa sannan yace wai momy mi nayi kuma?""",,,,,, momy tace idan ka sake magana saina ci uwarka na faɗa maka,,,,,,,,

uhum faruk yace sannan ya sake cewa ke zo nan,,,,,,, momy tace idan ka sake cewa taxo wallahi saina maka rashin mutunci,,,,, a gadarance faruk ya taho cikin isa zai nufi inda raihana take zaune,,,,, momy tace idan ka taɓa ta ban yafe maka ba wallahi,,,,, faruk yaja yayi tsaye,,,,,,,

tashi tayi taje inda raihana take tsugunne ta kama hannu zasu fita daga ɗakin faruk ya juya bayanshi sannan yace ke raihana kike ko wa?""",,,,, idan kika fita ban yafe maki ba,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,

Wannan maganar da yayi yasa momy ta dawo cikin ɗakin har yanxun hannun raihana yana riƙe a hannunta,,,,, tana zuwa takai ma faruk wani gigitaccen mari,,,, amma ko a jikinshi,,,,,,,,,, ya kalli momy sannan yace momy kiyi haƙuri a daidai lokacin da yake kai hannunshi zai jawo raihana,,,,,,,,,,,, yana kuka,,,,,,,,

dariya momy tayi sannan tace yaushe ka fara kuka akan mace?"",,,,,,,,, goge hawayen idonshi yayi da hannunshi,,,,,,,momy ta kalli raihana sannan tayi murmushi tace yarinya Allah ya baki,,,,,, muje,, ta sake jan hannun raihana, ita dai raihana batayi magana ba har yanxun saidai ta kalli momy ta kalli faruk kamar wadda ta farfaɗo daga suma,,,,,,,

faruk cikin ihu yace wallahi raihan kada ki fita a gidan nan,,,,,, dariya momy tayi sannan tace kai ka hafeta ne?""",,,,,,, da sauri faruk ya matso kusa da momy , da sauri momy ta maida raihana bayanta,,,,, sannan tace irin wannan baƙin cikin irinshi ne ko wace mace take ji idan zaka saketa umar,,,,,,,

Kabi ka ɓatani wurin "yan uwanka kace ni ɗin nan nake sa kana sake matanka,,,,,,, tsakanin ka da Allah duk auren da kke yi wace ce?""",,,, ka saki da izinina?""" faruk yayi shiru,,,,,,, tace saboda Allah ya rufa maka asiri kanaji da kuɗi da giyar mulki sai kayi ta aure kana ketawa "ya"yan mutane mutunci sannan ka sakesu?"""",,,,, haka ake rayuwa?""",,,,,,,

tace to kai mahaukaci ne.........""""" ni kuma uwarka ce nafika sanin cuta,,,,,,, kuma wannan yarinyar ina santa,,,,,, duk abinda nayi mata ina auna irin san da kke mata ne dan insan yanda zanci uwarka cikin ruwan sanyi,,,,,, dan aure aurenka ya isheni,,,, sai na sa ka saketa,,,,,,, nan na auna ka,,,, sai gashi kana kuka da idonka,,,,,, kuma a lokacin duka wata biyu tayi tare dakai,,,,,,,

dan duk matan da kke aure sunyi gudun tsiya wata ɗaya wata biyu,,,,,, ni da kaina nice nasa Alhaji ya auro yarinyar nan,,,,,,,idanuwa faruk ya zaro yana kallon momy,,,,,,, dariya tayi sannan tace har kaji tsoro?"":",,,,,,

Faruk baiyi magana ba,,,,,,, tace kuma dakaina na kawo mata magani, da hannuna na bata,,,, sakamakon kai da kke sawa ana ma mace allura,,,,,, faruk ya kalli raihana,,,, momy tace idan ka sake kallonta saina cake maka ido,,,,,,,

momy taci gaba da cewa kuma duk abinda nayi mata a asibiti dan inga idan tana sanka kuma tayi biyayya a gareni saka makon wata tsinanniya data riƙa zagina,,,, duk abinda nayi masu sai sunje sun gaya maka,,,,, kai kuma sakarai gurinka ka auri mace kayi gwanjonta ko?""",,,,,,kai mai kuɗi ko?"""",,,, ka auri mace gurinka ka biya buƙatarka ka saketa,,,,,, to wannan yarinya sai ka rabu da ita dan tana halin kirki ba matarka bace na faɗa maka,,,,,

faruk yace momy don girman Allah kiyi haƙuri,,,,, momy tace lokacin da nake baka haƙuri ka zauna da matanka kada ka sake su,,,,,, ai cewa kake kai kasan bala"in da kke ji,,,, to sai yanxun ka zauna da wannan ka cuci rayuwarta,,,,,

Momy taci gaba da cewa umar ni na haifeka amma koni ina da ɗiya ban baka aurenta saboda kai halinka baiyi ba,,,,,,,,,, faruk yace to kiyi haƙuri don Allah,,,,, tace sai ka tattara man "yan uwanka dukansu sannan ,,,,, tana kaiwa nan , taja raihana suka fice daga ɗakin,,,, faruk yabi bayansu..........

Yana cewa ke na faɗa maki idan kika fita dai ban yafe ba,,,,,,, momy tace ni kuma idan baka janye wannan ƙudirin ba, nima ban yafe maka ba,,,,,,,,,,,,,,,, faruk yace shikenan kibi momy,,,,,,,,, na yafe maki,,,,,,,,

haka momy taja hannun raihana suka fice,,,,,,,,, suna fita mota suka shige, suka bar gidan,,,,,,,,,,

Faruk komawa yayi ɗaki ya saka kaya,,,,,,, sannan yayi alwallah ya fita daga gidan,,,,,,,,,,,,, kai tsaye wurin Alhaji ya nufa,,, wanda ya auro mashi raihana........

yana zuwa a ƙofar gidanshi yayi farkin sannan ya fita kai tsaye gdan Alhajin ya shiga ,,,,, bayan sun gaisa da matan alhaji , sukace ya shiga yana ciki,,,,,, kai tsaye farlonshi ya nufa,,,,, yana shiga ya sami alhaji zaune yana kallo,,,,,,,, bayan ya shiga ya zauna suka gaisa,,,,,, bayan gaisuwa faruk yace Alhaji dama wata "yar matsala ce,,,,, dariya Alhaji yayi dan momy ta faɗa mashi komai,,,,,,,, amma sai yace wace irin matsala kuma?""",,,,,,,,, faruk yaɗan sosai ƙeyarshi sannan yace momy ce tace itace ta auro raihan ,,,,,, yayi shiru,,,,, cikin rashin bai gane abinda faruk yake nufi ba , Alhaji yace kamar ya itace ta auro ta?""",,,,,,,

faruk yace haka tace itace ta sa ka auro ta,,,,,, murmushin girma Alhaji yayi sannan yace haƙiƙa,,,,,,, yaci gaba da cewa lokacin da kazo man da maganar yarinyar nan,,,, ni dakaina naje nayi mata magana,,,,,, nace mata kaga wata yarinya kana so kuma,,,,, hajiya tace man kai kuma?""",,,,, nace mata Eh,,,, tace lallai kila banji ba,,,,,, nace mata haka kace man,,,,,,

Hajiya tace to gaskiya ta hanaka aure, nace miya sa?"",,,,, tace man kowa itace yake zagi, ta hanaka zama da mata,,,,,, tace man kuma laifin duka yana wurinka,,, tace man kuma wannan kace kana santa iyaka wata ɗaya zuwa biyu,,,,, dan baka aure tsakaninka da Allah saidai kayi dan biyan buƙatarka,,,, wannan kuma ba rayuwa bace,,,,,,

ni na lallaɓa ta da kaina tare da bata haƙuri,,,,,, har na samu na samu kanta,,,, kai kuma dakaje gidansu akace anyi mata aure ,,,,, ni kuma wurin aurenta Allah ya kaini,,,, kuma da naji anfasa na auro ta,,,,,,, kaga ai na gama nawa,,,,,

faruk yace to momy tace tunda ba tare aka aifemu ba saina sake ɗiyar mutane,,,,, Alhaji yace to kaje ka bata haƙuri sha,ani na uwa da ɗa, sai Allah,,,,,,, daga nan faruk bai sake cewa komai ba,,,,, godiya yayi ya miƙe yabar farlon,,

Yana fita Alhaji yace ai gara tayi maganinka ,,,,, wannan ba halin kirki bane,,,,,,,,

faruk yana fita ,,, ya shiga mota gida ya koma,,,, bai daɗe da zuwa ba,,, aka fara kiran sallah magrib,,,, alwallah ya sakeyi sannan ya nufi masallacin cikin gidanshi,,,,,,,

Momy kuwa suna fita, gida suka nufa,,,,, suna zuwa zainab taga momy da raihana,,, tace momy lafiya?"", dariya momy tayi sanndn tace ai saina ƙuro ma umar iskancin sa,,,,,, kinsan nan nayi mashi faɗa ko?"",,,,, to shine ya nuna man baida kunya wai zaije yaci uban yarinyarnan ma,,,,,,,,,

momy ta kalli raihana sannan tace je kiyi sallah,,,,,,,,,,,, wucewa tayi ciki ba tare da tayi ma kowa magana ba,,,,,,, momy taci gaba da cewa , kinsan iskancin umar saishi,,,, ya cuci "ya"yan mutane,,,,,,, duk an caccakesu da cirinji,, waishi yanxun yana san haihuwa,,,,, wai matarshi tana shan magani,,,,,,,,,,

Wato har yanxun dai mai hali baya barin halinsa,,,, dana bashi haƙuri cewa yayi sai daketa shi mai zuciya,,,, ni kuma nace to ya daketa tunda shine babanta,,,,,,, zainab tace yanxun yana ina?"",,,, tace wama yasan ma sakarai,,,,,,

zainab tace ni nasan umar nasan halinshi amma duk duniya ku gani kuke nine bana san yana zama da mata,,,, ai nace duk saiya haɗaku ya baku labarin tun daga aurensa na farko har zuwa kan raihanar tunda abun yazo haka,,,, idan nice zan barshi ya zauna da raihana, idan shine saina raba auren dan rayuwarta bata dace da rayuwar umar ba,,,,

zainab tace to Allah dai ya sawaƙe momy tace amin,,,,,,, shi kuma saida ya gama sallar isha,i sannan ya koma cikin gida,,,,,,,,,,

Yana zuwa kayan jikinshi ya cire yasa jallabiya,,, zama yayi a gefen gado ya riƙe kanshi da hannu biyu,,,,,, yana tunani,,,, daga baya kuma yayi wani mataccen murmushi da gefen bakinsa,,,,,,,,,

Kwanciya yayi fuskarshi tana kallon sama,,,, hawayen da suka taru a idonshi suka samu damar zubowa,,,,,,,, a bayyane yayi magana,,,, da cewa astagfurillah,,,,,,

Tou ita kuwa raihana tana gama sallah kwanciyarta tayi, dan dama ita yanxun bacci baiyi mata wahalar zuwa saidai idan bata hau gado ba,,,,,,, momy ce ta shigo ɗakin tana cewa raihana ta tashi taci abinci,,, raihana tace ta ƙoshi,,,,, momy cikin kulawa tace miya sa baza kici ba?""",,,, raihana tace haka nan,,,,,,, dariya momy tayi sannan tace kema haushina kikeji kamar mijinki?""",,,, tayi maganar ne cikin zolaya,,,,, murmushi raihana tayi sannan tace haba momy A, a, momy tace haushina yakeji dan na faɗa masa gaskiya,,,,,, kuma sai nayi maganinshi,,,,,,,,, zainab kawo mata cimar mijinta nasan itama ya koya mata, a daidai lokacin da momy take fita daga ɗakin,,,,,,,

Tana fita raihana tabi ƙofar da kallo,,,,,,, a ranta tace ni ina ruwana , kawai ku barni inyi tafiyata gidanmu keda ɗanki kun hana man zaman lafiya,,,, duk kunbi kun caja man kai,,,,, tayi ɗan gajeren tsaki a bayyane,,,,,,,,

zainab ce ta shigo da kofin tea,,, tace gashi tana miƙawa raihana,,,,, raihana dake kwance ta kalli kofin murmushi

Please Login or Register in order to submit comment