Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matsawar bai saɓi Allah ba,

Raihana tace haba Umma kullum sai ayita koroni kamar wata akuya?"""",,,,,tunda auren bayayi to a haƙura mana,,,,,,,, umma tace kiyi haƙuri don Allah komai yayi tsanani sauƙi bayansa, don haka tashi kibi umarnin mijinki kamar yanda yace, maza kije ki shirya,,,,,,,,,

Miƙewa tayi tare da zuwa ta ɗora ruwan zafi dan tayi wanka, alwallawa tayi ta shiga ɗaki don gabatar da sallah asuba,,,,,,,,,,

Faruk yana dawowa masallaci , ruwan lipton kawai yasha, bayan ya gama ya ɗauki wayarsa ya kira momy don jin yanda mai jiki ta kwana,,,,,,,,, momy tace nidai kawai yarinyar nan a fitar da ita ƙasar waje,,,,,,, faruk yace babu damuwa, ina za"a kaita ne?""",,,,,momy tace *Egypt* faruk yace to haka yayi ?"" Eh tace shi kuma yace to ba damuwa koma miye sadiq yana nan,

Momy tace kai kafi ƙarfin kaxo ne?"",,,,,, yace nima zanzo da zaran na kammala wasu abubuwa, momy tace to ina sauraren ka yace tam sannan ya kashe wayarsa,

Raihana tana gama sallah wanka ta shiga, bayan ta gama wanka ta fito ne, tana cikin shiri ne, taji wayar ta fara kuka, takai hannunta don dubawa, faruk ne, ɗauka tayi tare da sallama yace hajiyata gani a ƙofar gida, raihana tace mai zan shafa ne, yace haba kiyi sauri fito na shafa maki a mota,

raihana tace nidai don Allah A, a yace to gani nan shigowa gidan, raihana da sauri tace A, a nidai A, a don Allah basai kawani zo ba, ina fitowa, Faruk yace sai nazo gani nan shigowa yanxu, ya kashe wayar,

Raihana tace Umma zai shigo, shigowa zaiyi fa, wannan wane irin abune shiga gidan surukai tun safe?"""",,,,,,duk raihana ce take magana, Umma tace to ai shima gdansu ne nan, haba umma sai ya wani shigo kuma?""",,,,,,,,, umma tace Eh, sallamar faruk sukaji, Umma da sauri ta jawo hijabi ta saka, shi kuma yana tsakar gida yana ƙarewa gdan kallo,

Duk ya wani ɓata fuska, sai girgiza kansa yakeyi kana ganin yanda yake abun kasan ƙanƙami yakeji, ga wata kwata da tabi ta ikin gidan ƙarewa gdan kallo yayi sosai yace Alhamdulillah wannan gda kuma har mutum ya biya kuɗi ya zauna a ciki?""""""",,,,,maganar umma yaji tana cewa ka shigo mana,,,,,,,,

Yace tom, wucewa yayi ya shiga ɗakin ko takalmi bai cire ba, ya tsaya a bakin ƙofa ya tsugunna, sannan ya gaishe da Umma, bayan sun gaisa ne ya sake bata haƙuri akan abinda ya faru yace kuma shi bayanan wallahi baimasan komiye ba, amma don Allah ayi haƙuri haka bazai sake faruwa ba,,,,,,,

Umma tace ba komai, miƙewa tayi tace bara aje a kawo maku kuyi kalaci, niko kaji wani ƙarfin hali bata da ko sisi pha, amma don tana so ta nemawa "yar mutumci dole tayi su,,,,,,

umma na fita, raihana ta kallashi sannan tace sannu ɗan gaye, wato baza ka iya cire takalmin ba, saboda kar ƙafar ka tayi datti?""",,,,, kallo faruk ya bita dashi sannan yace miye haka?"",,,,, tace komai ma, amma a ɗakina ai baka shiga da takalmi sai ɗakin mamana?"",,,,,,, tunda shi ba irin naka bane?"",,,,, sai ka gaisheta da takalmi ko?""",,,,, murmushi yayi sannan yace Allah ya baki haƙuri, takalmin ya cire sannan tace zauna, kusa da ita ya matsa ya zauna, amma faruk kana ganin yanayinsa kasan baiji daɗin ajiye jikinshi a wurin ba,

bawai ƙazanta ba ne, A,a yanda komai yabi yayi wani gashi nan dai, shima tsakar ɗakin wata cinyayyar leda ce, rabi da kwata, da wannan ledar ai gara bbu, duk wani iri yakeji,,,,,,, raihana dai ta fahimci haka amma itama basarwa tayi,,,,

Kallonta yayi sannan yace mujje mana, raihana tace bakaji abinda umma tace ba?""",,,,, yace haba muje don Allah wallahi banaso gari ya waye sosai dan momy batasan naxo ba, raihana tace to koma dai miye Umma tace mu jira muyi kalaci,

kallon agogo yayi sannan ya nuna mata, 06:59am tace to miye, kayi haƙuri mana, ajiyar zuciya yayi sannan ya kwantar da jikinshi saman bayanta, tace miye haka sai Umma taxo ta samemu a haka?"",,, kallonta yayi sannan yayi murmushi yace ƙanshinki nake san inji kwana da yawa naga ke bakima yi wani maraicina ba, raihana tace nayi mana, tana magana tana wasa ido, shiko baki ya saki ya bita da kallo, ƙara jawota jikinshi yayi, sosai salon nasu ya canja kundai san ma"aurata, abun kunya ya bani shiya sa nabi umna da sauri dan gani miye zata basu...,

Umma tana fita daga gida, ashe wayar raihana ta ɗauka, wurin wani mai siyar da shayi taje, bayan sun gaisa tace don Allah yakubu ka riƙe wayar nan ka bani shayi, da biredi a toya man wainar kwai, a komai ma dai a bani, yakubu ya anshi wayar ya duba, sannan yace ki riƙe bara a haɗa maki idan kin samu kin kawo,

Godiya umma tayi , ta jira ya haɗa mata duk abinda take so, sannan aka kulle mata a leda tayo gida, tana zuwa, ɗayan ɗakin ta shiga, ta kira raihana, ta fito, wuri ta kawo komai a zuba, sannan tace taje takai mashi,

bayan takai faruk ya ɓata fuska yace shidai ya ƙoshi, taɓe baki yayi sannan yace amma ke kiyi sauri ki gama mu tafi, raihana tace to idan har bazayi kalancin nan a gidan nan ba, kayi tafiyar, murmushi yayi da gefen bakinsa sannan yace to muje, ruwan tea ɗin kawai yasha, ita kuma raihana itama komai ɗan kaɗan taci, tana fita daga ɗakin faruk ya ciro wani coculate ya saka baki, shidai duk wani iri yake ji, kai amma suna da haƙuri, miƙewa tsaye yayi ya saka takalminshi, ya fita tsakar gida,,,,,,,

yana fita ita kuma ta fito daga ɗakin da umma take zaune, tana zuwa kusa dashi yace ki sameni ƙofar gida, tace to, ɗaga muryarshi yayi tare da cewa Umma mun wuce mun gode sosai, umma tace babu damuwa,,,,,,,,,,,,

Yana fita umma ta shigo ɗakin, raihana tace umma zamu tafi, umma tace to Allah ya tsare na gaba, ta miƙawa raihana wayarta, suna ɗan maganane sukaji ana sallama a zaure, raihana ta fito dan ganin ko waye???""",,,,,,,, wani soja ne ta gani a tsaye, yana girmama ta, a matsayinta na matar Oga, ɗan rusunawa yayi sannan yace gashi,,,,, hannu raihana takai ta ansa sannan yace Umma za,a bawa, raihana tace tam,

Cikin gida ta koma, tana shiga ɗaki tace ma umma gashi, buɗewa umma tayi wata "yar ƙaramin jakane, amma kuɗi daffff a ciki, daga umma har raihana idanuwa suka zaro, kafin raihana tayi magana, kira ya shigowa a wayarta, raihana tace shine, umma tace to wannan fa?""",,,,,,

Raihana tace shine yace a baki, nidai na tafi, umma tayi ma raihana fatan alkairi, raihana ta fito,,,,,,tana fitowa ganin motaci masu yawa a ƙofar gidansu yasa taji wani iri, kundai san irin baka saban nan ba??"",,,,,,,to irinshi raihana taji,

Ga kuma wayarta sai kuka takeyi, ɗauka tayi sannan tace ma faruk nidai gaskiya bana iya fitowa ni ɗaya, dariya yayi sosai, sannan yace kauyissss cikin sigar wasa wasa yayi mata maganar dariya tayi sannan tace kauyisss ba amma kuma matar wayisssss, don haka nidai bazan iya zuwa ba wallahi, daga cikin mota yake hangota zauren su, dariya yayi sannan ya ɗaure fuska ya fita,,,,,,,niko nace maza da fuska shanu aka sansu,,,

Yana zuwa inda raihana take baiyi magana ba, hannunta kawai yaja suka fito daga gidan, suna ƙoƙarin shiga motane ta hango gwaggo, kallon faruk tayi wanda shi kuma sai ƙoƙarin ta shiga mota yakeyi, don hankalinsa ba wurinta yake ba, cewa tayi tsaya mu gaisa da mutane, yace tam, ya saki hannunta,

Tace kaima ai dakai za,ayi gaisuwar ne, yace waye zan gaishe?""",,,,,, raihana ta ɗan buɗe idonta, sannan tayi wani ɗan sheganta taka da harshenta, tace kalli can, tana nuna mashi da hannu kallon inda take nuna masa tayi sannan ya maida dubansa wurinta yace waye ita?"",,,, murmushi raihana tayi sanan tace kai tare da buɗe idanuwanta duka matar bbana ce, murmushi faruk yayi sannan yace "yar baƙin ciki dai, ɗaure fuska raihana tayi cikin sigar wasa, a daidai lokacin da take cewa gwaggo ina kwana, kallonta gwaggo tayi sannan ta bushe da dariya,,,, tace,,,,,,,

Mi kikayi wa gwamnati taxo kamaki tun yanxun?""",,,,,, murmushi raihana tyi sanan tace to kindai gani, gadai sirikin naki ku gaisa,,,,,, tace faruk ga ga gwaggo kallonta yayi sannan yace sannu, ina kwana?"",,, kasa ansa gasuwar tayi dan lallai ta gane fuska, cikin girmamawa gwaggo ta gaishe shi, bayan sun gaisa ne, faruk yayi wa gwaggo bulala da ruwan kuɗi,,,, arrrrrrrr gwaggo anga kuɗi aka wani gigice, faruk yaja hannun matarshi aka wani shige mota cikin gdan baya aka wani kashe, suna shiga driver yaje, sauran motocin suka rufa masu baya, tuni suka ɓace dag wurin suka barɓaɗe wuin da ƙura,

Gwaggo sai ƙara kallon motocin take har suka ɓace, sanna ta farfaɗo daga wannan tunanin ta tafi duniyar jinjiyar dukan ruwan kuɗin da faruk yyi mata haka taja jiki a sukwane tayi gda cike da mamakiyossssssssssss,,,,

Umma kuwa kuɗin ta fiddo ta irga ta tusa ta durza ta muza ta jajjagasu har ta gaji da lissafi don haka ta tattara su ta ajiye, dan lussafin yayi mata yawa, kuɗin yakubu kawai ta cire ta fita dan kai mashi haƙƙinsa, bari inbi su raihana, amana takai maki amaryar faruk nace ayyyyyy tafiyyyyyyyyyyyya,,,,,

tafiyar suke sosai sai ɓarin wuta suke bisa titi kana ganinsu kasan gwamnati ce da ƙafafuwanta bisa kwalta take tafiya,,,,,,,,,,,,,

suna isa birnin tarayya, faruk bayan suna ajiye raihana a gida ya wuce office, yana fita raihana bata tsaya wata wata ba, ta haye gado tayi kwanciyarta dan bacci ne a idon ta sosai,,,,,,,,,,,,,,

Faruk kuma a office wani abokin shine yake tayi mashi shegan taka, yace lallai yau tunda raihana taxo har gida sai yaje ya ganota, kallonshi faruk yayi sannan yace wace raihanar zaka gani ne?""",,,,,, yace madam raihana, murmushi faruk yayi ya kalleshi amma baiyi magana ba,,,,,,,

ita kuwa raihana tana tashi bacci wanka tayi amma bata san kayan da zata saka ba, don ita bata taho da kaya ba,,,,,,,, wayarta ta ɗauka ta kira faruk, bayan ya ɗauka suka gaisa tace mashi ya Office?""",,,,,,yace alhamdulillah, tace sannu, yawwa inji faruk, sai ta kasa magana kuma""""",,,,,, sai tace dama nace bara in maka sannu, yace yawwa ngd, yana faɗin haka ya kashe wayar,

Raihana tace tou pha, to yanxun ya zanyi?""",,,,,, niko nace Oho maki,,,,,,, wurin kayanshi ta nufa ta fara bubbuɗewa sai ɗaga wa take ɗaya bayan ɗaya tana zazzagawa, dariya tayi sannan ta ɗaga wata baƙar jallabiya, tace Allah ke zan saka, ɗauka tayi ta zumbula, sannan ta tattara kayan ta gyara su ta mayar,,,,,,,,,,,

tana gama mayarwa tashi tayi ta matsa gaban madubi ta kalli kanta tayi murmushi sannan tace kuma naɗan yi kyau ba laifi, murmushi ta sake yi sannan ta kashe idon ta ɗaya, da harshenta tasa ta laso leɓonta ta ɗan ɗaga girarenta sannan ta sake lumshe ido ɗaya tayi juyi, da gudu kuma tayi parlour kamar wani yana kallonta,

Tana zuwa zama tayi saman kujera 1seater taɗan harɗe tana maganar zuci,,,,,, ,,, zaman ya isheta ta ɗauko wayarta tace umm bara in kira zulaihat yau muyi zuminci, adaidai lokacin data fara kiran wayar,,,,,,,,,,,

saida ta kusa tsinkewa sannan ta ɗauka, cikin isa zulaihat tace hajiyata yadai?""",,,,,,raihana tace ke bansan sakarci kina ta wani mammatse murya ba mai gdan bane,,,,dariya zulaihat tayi sannan tace shegiyar mata ai koce dole ne inɗanja zare, wallahi baki da kirki, raihana tace me nayi kuma?"",,,,,, tace baki zuminci nazo gdan ki kwanaki bakya nan, raihana tace Allah sarki, zulaihat tace kuma bayan wani lokaci na sake dawowa baki nan, raihana tace lallai,,,, zulaihat tace kila zanzo cikin satin nan tunda kin tuno dani,,,,, raihana tace yanxun ma idan kin sake zuwa bana nan, zulaihat tace kinje ina ne?""",,,,, raihana tace saidai mun haɗu,,,,zulaihat tace to Allah ya haɗamu da alkairi, fira suka ɗan taɓa tare da zaulaya dai irin tasu ta ƙawaye aka ɗanyi ma juna shegantaka kundai gane ko hajijoyi?"",,,,,,,

bayan sun gama firan ne, ta kira farida, bata ɗauka ba, tace to ke kuma umma laisal handasetdana kiraki nace munxo lafiya,,,, haka dai taɗan zame saman kujera ta ɗora hannunta saman goshi ta rufe idanuwanta, ko tunanin mi takeyi Oho naga dai hawaye nata zubowa daga idonta,,,,,,,,,

har Faruk ya shigo raihana bataji zuwanshi ba, duk maganar da yayi inawo an tsunduma cikin tunani, zama yayi kusa da ita, yana kallonta ita ko ta dage sai shashsheka takeyi tare da shan majina, irin dai na masu kuka,,,,,,, ɗagota yayi da sauri ta buɗe idonta, tare da goge hawayenta, rumgumeta yayi sannan yace kukan miye?"""""",,,,,

murmushi raihana tayi sannan tace waye yace inayin kuka?"",,,,,nine na gani, inji faruk,,,,,, raihana tace to yaji ne ya zubar man a ido ai,,,, kallonta yayi sannan yace nine ma yajin dariya tayi sannan tace aiko da bazan bari a shanyeka ba, murmushi yayi sannan yace wannan rigar fa?"",,,,,, dariya raihana tayi a daidai lokacin data zame jikinta daga nashi,,, ta fara tafiyar rainin hankali tana cewa to ai ban samu wasu ba, bayanta yabi yana cewa ke zo nan,,,, shiru tayi ta shige ɗaki shima yabi bayanta..................,

****

*T*o zainab mai ciwo dai an samu ɗagawa zuwa egypt don ganin likita,,,, kuma duka momy yaranta ta tattara ta tafi dasu,,,,,,

Faruk yace ma raihana ta shirya suje ganin zainab tace ita dai bazata samu zuwa ba, ya tambayeta dalili amma ta nuna mashi ba komai haka yayi juyin duniya amma tace ita dai yayi haƙuri baza ta samu halin zuwa ba,,,,,,,,,, ya gaji da lallaɓata yace kada Allah yasa kije idan kinje ma bana so ban gode ba kuma bazan gode ba,,,,,, raihana tace to kuma duk miye yayi zafi,,,,, tsaki yayi yabar ɗakin,,,,,,

Bayan ya fita raihana tace ikon Allah, shi bazai gane ba,,,,,, na fito fili in nuna mashi matsalar mamanshi?""",,,,,,yanxun muna zuwa ta ganni sai kuma tace sai faruk ya rabu dani , tsaki tayi sannan ta miƙe ita ta bar ɗakin,,,,,

ɗakinshi ta sameshi yana waya, bayan ya gama tace don Allah kayi haƙuri duka nan banga abin fushi ba, wani irin kallo yayi mata wanda yasa ta fita ɗakin da sauri,,,,,,,,,,,,

Ko da daddare raihana tace mashi ga abinci daka mata tsaywa yayi yace ta fita daga harkarshi, idanuwa raihana ta zaro tare da cewa wannan wane iri wasa ne?""",,,,,,,, waye zai fita harka naka ne?"",,,,,,,,, yace abinci ko?""",,,, tace Eh , kanshi ya girgiza sannan ya ɗaure fuska sosai yace to bazanci ba, sai kuma miye?"",,,,,,, tace sai shi kenan, yace to a samu ayi waje mana, yana nuna mata hanyar waje da hannunshi,, ɗaukar abincin tayi ta wuce simi simi,,,, tana fita yace aikin banza, ke kin iya cewa inyi abu amma ni dan kin raina man hankali baza kiyi abinda nake so ba,,,,

Tashi yayi ya shiga wanka, yana fito yaci uban gayen shi, yayi kyau sosai, tana farlo zaune tun kafin ya fito taji ƙamshin turare, zubawa ƙofar ido tayi tana jiran fitowarshi,,,,,,,,,,,,,,,,,,

sai gashi ko an wani tsuke cikin ƙananan kaya, ko inda take bai kalla ba, murmushi tayi sannan tace ina zaka?"",,,,,,, bai kalleta ba kuma baiyi magana ba, ta sake cewa bakaji ina magana?"",,,, banza yayi mata,,,,, tashi tayi da sauei taje ta kulle ƙofar da makulli, tana ƙoƙarin rugawa yayi mata wata irin munafikar damƙa, yana rikota ya wanka mata wani irin zazzafan mari sannan ya miƙa hannunshi yace bani?"",,,, riƙe ƙugu tayi cikin kuka sannan tace wallahi bazan bayar ba saida ka kashe ni""""",,,,,, ɗaga hannunshi yayi da niyar ƙara kai mata mari da sauri ta duke sannan tayi ɗaki da gudu, a zuciya ya bita da gudu amma kafin ya kawo harta rufe ƙofa,

Dariya tayi adaidai lokacin data haye saman gado, sannan tace waini za,ayi wa zuciya, a fara fitar majalissa, kaje can kayi ta balbaɗa ni, a baka shawarar banza kaina,,,,,

Bazaki kixo ki buɗe ƙofa ba?""",,,,, tace anƙi a buɗe idan kayi fushi kaje kayi bacci, ni kike cewa idan naji haushi?"",,,, tace Eyyyy ka shaƙa ne?"",,,, nace ki fita harkata baza ki fita ba ko?"",,,,,, tace bazan fita ba,,, tsaki yayi sannan ya koma farlo ya zauna,,,, lokaci lokaci saida yayi tsaki , ita kuwa raihana wanka ta shiga, tana fito tayi shiri mai kyau saƙo da loko na jikinta saida ta bishi ta shafeshi da ƙamshi,

Wasu sheɗanun kayan bacci ta ɗauko ta saka wanda dasu da babu ɗaya ne, kallon kanta tayi a madubi ta girgiza kanta sannan tace , bari muji ya za"a ƙare?"",,,,,, ɓoye makullin tayi sannan ta buɗe ƙofar ta fita,,,,tana shiga farlo daga nesa dashi ta tsaya sannan ta riƙe ƙugunta tace gani,,, kace inxo ko?"",,,, to gani na fito bana tsoro,,,,,,,

Da wutsiyar idonshi ya kalleta, murmushi yayi sannan ya kallota dukanshi, yana kallonta tayi murmushi itama wata "yar girgiza ta fara sannna ta juya tana cewa tunda kaji tsoro saida safe,,, ta nufi hanyar ɗaki,,,,,,

Ƙara kallonta yayi sannan yace zo buɗe man ƙofa nace, raihana tace ƙofa ai baka da ƙarfin ansar makulli,,,,,,,idan kuma mutum yana jin shi sojane ya shigo ɗakina, hmm mutum wayyo, ta yarfa yatsanta alamar zaka gane kurenka,,,,,,

faruk yace ke ni kikewa wannan abun?"",,,, raihana tace anyi tunda ɓaɓatun akan kujera ya tsaya,,,, miƙewa yayi yabi bayanta, ita kuma da gudu ta shige ɗaki, tana zuwa ta soke saman gado,,,daga bakin ƙofa ya tsaya yana kallonta, tace mutum sai cika baki, idan ka isa kaxo nan kaga makulin nan,,, ta karkaɗa makullin,, dariya faruk yayi sannan ya shige cikin ɗakin,,,,,wani shu"umin kallo tayi mashi , yace ni bana san wannan abun, raihana tace ni kuma irinshi nake so..................haka kika ce?"",,,,

Zama yayi a gefen gado sannan yace to matso nan mana, kwanciya tayi sannan tace kai kaxo nan mana, murmushi yayi sannan ya hau saman gadon sosai, zata matsa ya riƙe ƙafarta, ya jawota kisa dashi, sannan yace Allah kin ɓata man rai, raihana tace to nace kayi haƙuri kai komai saurin fushi ka daina ni banajin daɗi, yace aikece ɗin , raihana tace nice ɗin miye?"",,,,,,,,, yace to naji na fasa fitar gani a gidan miye zaki bani?"""",,,,,,,,, raihana tace ba abinda zan baka kawai ka zauna ina ganinka inajin daɗi, yace to idan har kina sona ki shirya muyi tafiya tare dake,,,,,,

bana so kina man gaddama kinga idan kika ce man abu ina maki fa, bana san inga kinyi fushi,,,,,raihana tace to yiman gori, tayi maganar ne cikin wasa, dariya yayi sannan ya sake jawota, ya ɗora kansa saman ruwan cikin ta, hmmm babban take wannan karatun yafi ƙarfin rubutu na.....................
[1/8, 9:46 PM] Jamila Musa Ws: 💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦

*Page* 4⃣4⃣

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION*📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

****
Ina maku albishir da sabon littafina mai taken *RASHIN RABO* wannan littafi kada ku bari a baku labari dan yana ƙunshe da darissa da dama, kada ku bari a barku a baya *RASHIN RABO* ku kasance tare dani,,,,,,,,,,,har kullum ina cewa kune *MAUDU"INA*

**
*Ina baku haƙuri najina shiru kwana biyu kuyi haƙuri banajin daɗine, amma na samu sauƙi zaku jini kullum idan Allah ya amince*

****

*T*o al"amarin miji da mata sai Allah, bayan faruk ya gama samun natsuwa,,,,,,,miƙewa yayi zai fita daga ɗakin , raihana tabishi da kallo,,,,,,,jikinshi ya bashi ana kallonshi don haka ya juyo, ita kuma da sauri ta ɗauke kanta ta maida dubanta wani wuri daban, murmushi yayi da gefen bakinsa sannan yace ko in dawo ne?"",,,,, batayi magana ba, yace ina zuwa,,yana faɗin haka ya fice daga ɗakin...

Yana fita ta miƙe ta shige toilet bayan ta gama abinda takeyi ta fito,,,,mai ta ɗan murza sannan ta shafa powder sama sama da man baki,,,, kayan bacci ta saka tayi kwanciyarta,,,,, { shawara akwai wani ganganci ɗaya da mukeyi ko kuma ince san jiki, sai namiji ya gama kusantar mace wai sai tabi lafiyar gado tayi kwanciyarta,,,,,,, to idan har baki da ikonyin wankan tsarki a lokaci to ki tashi kiɗan gyara jikinki ki wanke, alabashi da safen saiki tsarkake kanki,,, dan kwana da najasa yana illa a jiki don haka mu kula }

Shi kuma yana can ɗakin shi bayan ya gama abinda yake,,,,, wayarshi ya ɗauko ya duba miss calls in da aka tara mashi,,, wayar momy ya fara kira,,,,bata ɗauka ba, ya sake kira bata ɗauka ba, haka yayi ta kiranta daga baya taci gaba da latse wayar,,,, da kiran ya shige sai ta kashe daga baya kuma ta rufe wayar baki ɗaya,,,,, jin waya a kashe yasa gaban faruk faɗuwa, dan lallai yasan akwai matsala,,,,,

Wayar hafsat ya fara kira,,,, bata ɗauka ba,,,, text ya tura cewa baki da lokaci nane?"",,,,,,,momy dake zaune gefe tace kada ki ɗauki wayar barshi ni zai wulaƙanta dan ubanshi?"",,,,har ina kiranshi baya ɗaukar wayata?"""""",,,,, yana can wurin tsinanniyar yarinyar nan, kai wannan yarinya anyi mayatu wallahi,,,,,, hafsat tace kedai momy don girman Allah ki fita harkarsu,,,,,,,

Momy tace ban fita dan uwarki,,,,,, ɗana ni na haifi abuna,,, ba uban wani ya haifar mani shi ba,,,,,, hafsat tace to momy kema dad ai haihuwarshi akayi amma kika aureshi mulkin da kika zuba a gidan waye yayi kamarshi?""",,,,,,,

Kika raboshi da ainahin garin iyayenshi saboda tsangwamar dangin miji kika maidoshi cikin ahalinku,,, kika hanashi auren kowa saike,,,,,,, zainab dake kwance saman gado tana fama da kanta tace,,,,,, kwarai kuwa danni da wayauna nasan lokacin da kike korar dangin dady idan sunxo, amma mamanshi haƙuri tayi tace itama haka taci lokacinta,,,,,,, tace ita iyakarta da dady a duniya amma ta samu wanda tafita kaunarshi,

Momy tace toni babu wanda ya isa yayi man haka a ɗana , hafsat tace anyima an gama gara kisawa zuciyarki haƙuri addu"ar da zakiyi ma ta aihu a gidan, dan kada itama ta kasance kamar sauran matan dan rayuwar yaya tana bukatar samun natsuwa,,,, daga haka babu wanda ya sake magana sai momy dake ta surutunta ita kaɗai,,,,

Ganin basu da niyyar ɗaukar wayarne yasa faruk kwanciya ,,, ita kuma raihana ganin bai dawo ba, yasa ta tashi ta nufi ɗakinshi,,,, lokacin data je har bacci ya fara ɗaukarshi,,,,,,,,,,,,, saman gadon ta hau ta matsa kusa dashi ta ɗaga bargon ta shige,,,,, idonshi ya buɗe ya ganta sannan ya mayar dasu a hankali ya rufe,,,,,,, da hannunshi ya lalubota ya rungume "yar matarshi sukayi bacci,,,,,,,,,,

***

*Y*au faruk yana gida baya zuwa ko ina,,,,, zaune suke dashi da raihana yana bata labari,,, amma ya lura sai wani basarwa takeyi,,,, kallonta yayi sannan yace wai bakiji ina magana ne??"",,, tace magana kake amma ni hankalina yana wani wuri daban,,,,,,, murmushi yayi sannan yace ina hankalin ya tafine?"",,, adaidai lokacin da yake kai hannunshi kusa da ita ya jawota jikinshi,,,,

Raihana tace nidai tsoro nakeji,,,, yace tsoronmi?"",, raihana tace nidai duk ba wannan ba,,,,, yau ina so ka bani labari duk abinda yasa ka rabu da matanka,,,,,,, kallonta faruk yayi sannan yace to wannan kuma ai ba damuwarki bane,,,,, raihana tace damuwata ce, dan duk abinda ya shafeka ya shafeni,,,, ka faɗa man idan ina da wani hali irin nasu sai in gyara,,,, taɓe baki yayi sannan yace baki da irin halinsu ko ɗaya ,,,,, raihana tace to nidai faɗa man don Allah,,,,,,,, Shiru yayi bai sake magana ba,,,,,,,,

ganin yayi shiru ne, yasa raihana miƙewa, tana kama hannun faruk wai suje su girki,,,, zamewa yayi saman kujera ya kwanta yace ni yau banayin girki gaskiya,,,, bata sake magana ba ta wuce,,,,

tana wucewa faruk ya shafa kanshi sannan yayi murmushi yace kaiji yarinyar nan, wai nine zan faɗa mata abinda ya rabani da matana,,,,, dariya yayi sannan yace lallai yarinyar nan kin shiga rayuwata sosai,, yoni wace mace ma zataga fuska har tama fara man wannan tambayar rainin hankalin,,,,,, maganar raihana yaji tana cewa wai ina ka ajiye magin ne duk kabi ka yamutsa komai,,,,,,,, tsaki yayi sannan ya miƙe ya nufi kichen ɗin,,, yana shiga yaga magin a hannunta,,,,,,,

ɗaure fuska yayi sannan yace bagashi a hannunki ba?"",,,, ganin ya ɗaure fuska yasa tayi dariya sannan tace kaga yanda kayi?"",,,, ashe ma haka nan kake dariya?"",,, idan kayi fuska kafi kyau,,,, ansar magin yayi sannan yace mi zaki dafa ne?"",,,, tace abinda raina yake so,,, yace ni kuma tuwo nake so,,, tace to nidai bana san tuwo gaskiya,,,, yace to lallai tuwo za,ayi raihana tace lallai idan dai tuwo saidai kayi da kanka ,,,,, yace to naji,,,, taimaka man,,,,, yiman tuwon ni inyi maki abinda zakici,,,,, tace naji,, haka kowa yaci gaba da aikin gabanshi,,,,,, lokaci lokaci faruk yana magana raihana saidai tace ummm,,,,, shima daga baya shiru yayi ya daina

Please Login or Register in order to submit comment