Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yau abinne yaci tira saida yayi mata shegen duka ita kuma ta tattaro "ya"yan ta ta taho gida,

Ita kuma gwaggo tace tunda an wulaƙanta mata ɗiya baza ta riƙe ɗan uban kowa ba, ita kuma fiddausi tana cewa itama babu mai rabata da yaranta,

To gasu nan dai koya zaman zai ƙare tsakanin gwaggo da fiddausi da kuma raihana da yaranta?"""


Raihana dai tana cikin far gaba saboda fiddasi bata da mutumci bata da ragowa, ga san abun duniya sannan kuma ta kware wajen iya bariki,............


Kam cakwakiya kenan, wannan zama nasu koya zasu yi shi ne?"""


Ku kasance tare dani, *Ameenci writer's association* ke maku fatan alkairi ni *meelat* nake cewa ku kasance tare dani!!!
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦

*Page* 1⃣4⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT* 🌹

*T*o koda baba ya dawo ya tambaya lafiya yaga fiddausi a gida?"" gwaggo tace ta kashe auren nan dan ta gaji da iskanci, baba yace abinda baya yuwuwa dole ta koma ɗakin mijinta, amma gwaggo tace babu gidan ubanda zata je, ta ƙara da cewa aiga raihana nan itama tana zauniyar ta sai neman kuɗi take abinta, duk inda baba ya shiga gwaggo tace fiddausi baza ta koma ba, dole ya haƙura,

****
*S*ati ɗaya da dawowar fiddausi gwaggo da kanta ta shiga maƙota duk inda ake kawo ma raihana wanki tace su daina kai mata ga fiddausi ta dawo kuma da kyau take wanke wa suyi fesss,

*R*aihana kwance a tsakar gida ga yunwa ta isheta ta rasa inda zata saka ranta, ita baƙin cikinta ma kuɗin da zata siyi pard take nema, bata da ko sisi, tana kwance fiddausi ta kwaɗa mata kira, ke raihana?"" raihana tace na"am, zo maza ɗauki usman kiyi mashi tsarki yayi kashi,

Raihana tace to, miƙewa tayi ta nufi wurin da fiddausi take zaune, ta duƙa ta ɗauki yaron taje tayi mashi tsarki ta dawo mata dashi, har ta ajiyeshi zata tafi tace jeki ɗakin gwaggo ki tattaro kayan fitsarin shi ki wanke , kuma ki gyara ɗakin, raihana tace to amma don Allah ki bari inci abinci yunwa nake ji,

Fiddausi ta buɗe baki sannan tace lallai yarinya nuna man kin balaga, duk ina nan zaune harsai kin gama uzurinki zakiyi man nawa?""" raihana tace ba haka bane wallahi duk yau banci komai ba, fiddausi tace to ni na hana kici?"" raihana tace ban samu ba, suna maganar akai sallama wani yaro ya kawo wanki, raihana tace kawo, yazo gabanta ya ajiye mata wanki sannan ya bata kuɗin, ta karɓa fiddausi tace kawo nan mu gani!!""" raihana tace kuɗin wanki ne, fiddausi tace to ki bani dan uwarki, miƙa mata tayi kuɗin, ta karɓa sannan tace to ki wanke kayan mana,

Raihana tace to, ɗaukar kayan tayi ta matsa dasu ƙofar ɗakinsu ta ajiye sannan ta shiga ɗakin umma tana shiga ta zauna kusa da umma ta fashe da kuka,

Umma tace lafiya?"" raihana tace Umma wannan ai cutane tunda fiddausi ta dawo gidan nan nice nake komai da komai inyi nata inyi na yaranta, dan kuma rashin imani duk abinda zasuci a gabana sukr ci basa bani, yanxun an kawo wanki zanyi ta kwace kuɗin kuma wai in wanke kayan, bazata bani ko sisi ba,

Umma tace kiyi haƙuri, raihana tace inyi haƙuri da yunwa umma?"" Umma tace to idan baki haƙuri ba mi zakiyi?"" raihana tace nidai gaskiya zanzo in fara sana"a ko abinci siyarwa ne inyi ina kaiwa waje ina siyarwa, amma bazan iya wahalar banza ba inyi wanki ta kwace kuɗin kuma duk wahalar yaranta a kaina zai ƙare,

Umma tace to kiyi abincin siyarwar Allah yasa ma neman albarka raihana tace amin,

Naira hamsin umma ta bata tace taje ta siyo shinkafa da wake taci, kuɗin ta karɓa sannan ta fita daga ɗakin, tana fita umma tace Allah ya sawaƙe, shi yasa idan ka samu inda ka raɓa ake so kayi haƙuri, Allah dai ya baki miji na gari raihana,

Ina kuma zakije?"" fiddausi take tambayar raihana inda zataje, raihana tace zanje in dawo ne, tace babu inda zakije kixo ki wanke kayan mutane mana, raihana tace zan wanke zanje in samo abincine in dawo, to kiyi sauri dan bana so ki ɓata man lokaci, raihana tace to sannan ta fita daga gidan,


Bayan taje ta siyo abincin ta dawo, ɗakinsu ta shiga taci, sannan ta fito, ta fara wanki, saidai ta wanke kayan fess kamar wata inji sannan taje tayi wanka,

Gwaggo tace ta ɗauki niƙa takai mata, raihana tace gwaggo duk ga yara nan ki aike su mana, fiddausi tace anƙi a tura yaran mana sai sunje sun zubar da masarar anjima uwarki zamu ci muyi bacci?"" tsaki raihana tayi sannan ta duƙa ta ɗauki kwaryar ta nufi shagon yusufa,


Lokacin da ta isa wurin cike yake yana niƙa, raihana ta ajiye ta samu wuri tayi tsaye kamar wata sojanya, saida ya gama niƙa wani niƙa ya hangota,, ya yashe baki yace baiwar Allah kece?"" raihana ta ɗaure fuska shiko sai fara"a yake wai yaga masoyiya, ina niƙan naki yake ne?""" raihana ta nuna mashi ya ɗauka ya niƙa mata danshi ya ɗora mawa yace yakai mata gida, kuɗin ta ajiye mashi don idan ta bashi baya karɓa, tana ajiyewa tabar wurin, dariya yayi sannan ya ɗauki kuɗin ya saka a aljihu,

Lokacin da raihana ta dawo gida, gwaggo sai faɗa take wai ta ɗora ma yaro niƙa ya zubar mata, ko inda take raihana bata kalla ba ta wuce ɗakinsu,

Tana zuwa ta buɗe kayanta, wani less ta ɗauko mai tsadar gaske, ta saka a leda , sannan tace ma umma sai ta dawo, umma tace to,

Raihana tana fita, maƙota ta shiga gidan wata dillaliya, ta bata less in, tace zata siya dubu goma, raihana tace haba hajiya ki ƙara don Allah tace ai hakanma na zura jikina da yawa, raihana tace duka so ɗaya na taɓa sakawa wallahi , hajiya tace ai su gwanjo babu ruwansu da so nawa ka saka, idan kin siyar a haka in bayar idan baki siyar ba to in baki kayanki, raihana tace to kawo,

Hajiya ta shiga ta ɗauko mata kuɗin ta bata, tana karɓa, ta nufo kasuwa, dan siyp cefane da abinda zata buƙata wurin abincin siyarwa, ta haɗo duk abinda zata buƙata ta nufo gida,


Tana dawowa fiddausi tace ina kika shige ne "yan mata?"" raihana tace taje kasuwa, fiddausi tace kawo muga abinda kika siyo tace ba nawa bane, tana faɗin haka ta shige ɗakin su............

Fiddausi tace tou pha yau naga munafinci tsurarshi yarinya ina magana bama tada lokacina, ita dai raihana bata sake magana ba, haka umma bata yi magana ba, haka sukayi ta jarabarsu a tsakar gida ita da gwaggo har suka gaji sukai shiru dan kansu..................,,,,,,,

****

*D*a safe raihana ta fara aikinta, fiddausi da gwaggo suka fito suna tambayar ko lafiya?"" raihana tace zata fara siyar da abinci ne, haka taci gaba da aikinta, au fiddausi suna kallon ikon Allah,

Koda baba ya fito zai tafi kasuwa gwaggo tace Allah ya hutashshe ka ɗiyarka ce zata riƙa ciyar da kowa a gidan nan tayi kuɗi ubanta ya huta,

Raihana dai batace komai ba, saboda haka baba gwaggo ta hana shi ya bayar da ɗan abinda yake bayarwa saboda haka yasa kai ya fita daga gidan,


Koda raihana ta gama haɗa komai nata, gwaggo tazo da ƙaton wuri ta kwashe abinci kafff, raihana tace yana ga haka kuma?"" gwaggo tace ya kuwa baza kiga haka ba?"" ai gida bata ƙoshi ba baza akai daw ba, dan haka sai kowa yaci ya ƙoshi sannan,

Baƙin ciki ya ishi raihana saboda duka abinci gwaggo ta kwashe shi, doƙe ta haƙura ta kina ɗaki, da tace ma umma yau sai taci uwar kowa a gidan umma tace tayi haƙuri kada ace tana zaune gida tana faɗa da matar babanta, umma ta ƙara da cewa kuma ko aurenki aka zo nema haka za"ayi ta faɗa ace baki da ragowa, haka raihana tayi haƙuri ta tashi a tutar babu, duk miye yaja mata??""" *zawarci*

Umma to yanxun miye ya kamata in fara siyarwa kuma?"" umma tace sai ki nemi aiki a gidaje, raihana tace kai haba Allah dai ya sawaƙe, nje inyi ma wata ƙatuwar banza aiki, umma tace to Allah ya kawo mafita raihana tace amin..................




*B*ayan kwana biyu, mijin fiddausi yaxo biko, gwagho tace baza ta koma ba, raihana kuwa addu"a take Allah yasa ta koma ita kuma ta samu ta huta .................................
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦

*Page* 1⃣5⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

````MEELAT``` 🌹

*G*waggo ta bushe fitalar ido tas tace fiddausi baza ta koma gidan mijinta ba, shi kuma daya fi su iskanci ya tattara dukan yaranshi har na goyen bai bari ba, ya tafi dasu kuma yace bazai saketa ba,

*F*iddausi keta fama kiran raihana, ita kuma raohana tana kwancd babu lafiya, shirun da fiddausi taji raihana tayi yasa ta tashi ta taho ɗakin a fusace,

Ita kuma raihana tana kwance sai rawar sanyi take, idonta sai fitar da hawayen wahala yake, fiddausi tace ubanmi ya sameki?"" cikin yanayin wahala tayi magana tace banda lafiya, fiddausi tace ai nasan baki lafiya nake tambayar abinda yake damunki raihana tace masassara da ciwon kai,

Fiddausi tace Allah ya sawaƙe, idan kina da 100 bani zanyi amfani da ita, tsaki raihana tayi cikin ranta sannan tace kaji wani zancen banza idan ina da ɗarin ni da banje ko cemist ba?"""

Fiddausi tace ina magana kinma mutane shiru, raihana tace banda su, tsaki tayi sannan ta fita daga ɗakin,

Umma ce ta shigo ɗakin ta cire hijabin jikinta tana ma raihana sannu, tace ni banma samo kuɗin ba, raihana tace to umma babu komai , Umma tace wane babu komai kin kwanta da ciwo ba magani kuma duk yau bakici komai a cikinki ba?"" raihana tace shin,

Fiddausi ina zakije ne?"" gwaggo take ma fiddausi magana amma ko inda take bata kalla ba, haka ta fece tabar gidan,

Yinin ranar haka raihana ta yini babu zuwa asibiti umma duk buga bugarta ta rasa ina zata samu kuɗi kuma ciwo sai ƙara tubirewa yake, dan raihana sai wani farfar da idanuwa take, hankalin umma ya tashi sosai, saboda haka ta fito take gayama gwaggo, tare suka shigo ɗakin ganin halin da raihana take ciki gwaggo hankalinta ya tashi sosai,

Ta kalli umma tace an ajiye ɗiya a gida ciwo babu magani?"" umma tace nidai banda kuɗi kuma duk yinin jiya da yau bata samu taci abinci ba, har gari ta siyo gashi can ta kasa ci,

To Allah ya sawaƙe, to yanxun ya za"ayi?"" kafin gwaggo ta rufe bakinta, raihana tayi wata irin ajiyar zuciya, lokacin da suka maida kallonsu wurinta wani kumfa yake fita daga bakinta, tana kakkafafewa, umma tace innalillahi wa"inna ilaihir raji"un, gaba ɗaya suka matsa kusa da ita, lokacin da suka ɗaga raihana babu nunfashi, gaskiya gwaggo taji babu daɗi da gudu ta fita , tana fita mijin badiyya ta gani jikinta yana karma tace mashi ka taimaka mana raihana babu lafiya

Har ta suma, yace to suje su ɗaukota akaita asibiti, da sauri gwaggo ta koma ita da umma suka kamo raihana a motar shi aka sakata, suka nufi asibiti,

A asibiti ana kai raihana likitoci suka fara gwaje gwaje don gano abinda yake damunta, bincike sosai akai likita ya tabbatar masu da raihana ciwon yunwa { ulcer } sannan kuma tana da damuwa sai kuma ta rage amfani da ruwa sosai idan ba haka ba, limonia tana neman kamata,

Duk kuɗaɗen da aka kashe a asibiti mijin badiyya ne ya biya, sannan yayi ma su umma fatan samun sauƙi, sannan ya tafi,

Kwanan raihana 3 a asibiti aka rubuta masu sallama , suka dawo gida, duk zaman da raihana tayi a asibiti fiddausi ko leƙe bata leƙa ba,

Yusufa yazo yaga raihana yace baisan bata lafiya ba, sai yau ake faɗa mashi, yayi mata sannu , tare da mata addu"ar samun sauƙi,

Hankalin raihana ya tashi, wato banda mijin badiyya lallai da bata san yadda zata ƙare ba, saboda basu da kuɗi, lallai *zawarci* da matsala, shi yasa idan ka samu inda Allah ya ajiyeka kayi haƙuri ka zauna wata rana sai labari,

Fiddausi kuma zaman gidansi ya fara isarta, dan babu ma mata wanki bare ta samu ɗan kuɗin kashewa, dama raihana ce take wanki ita kuma ta kwace kuɗin, to yanxun ta daina wanki saboda asibiti ance ta rage yawan amfani da ruwan sanyi dan inganta lafiyarta,


Fiddausi ta gaji da wannan zaman ita ba zawara ba ita ba mai aure ba, saboda haka yau ta ɗauki alwashin komawa gidan mijinta, gwaggo tayi juyin duniya karta koma amma fur fiddausi tace tafiyarta zata, saboda haka ita ta tattara yanata yanata tayi gidan ta..................,

Lallai itama raihana abun duniya ya dameta saboda haka tayo ɗamarar duk wanda yazo zata aureshi dan gaskiya ta gaji da wannan wahalar,

Yanxun an hanata wanki, dama dashi takd samu ta ɗan rage zafi, kuma girman kai ya hanata aiki gidaje, kuma ita babu ilimin boko mai zurfi bare ta fara aiki,


Sallama badiyya tayi ta shigo gidan nasu, kallo ɗaya zakai mata kasan tana cikin fushi, fankam fankam haka ta nufo ɗakin su raihana, babu ko sallama ta yaye labuƙen ƙofar ɗakinsu, ta fara cewa,

Ai dama duk abinda zakai da marar amana sai yaci amanarka, dan kutumar uwarki ina tausaya maki amma ashe ke ƙoƙarinki ki auri mijina?"" to daga yau na karajin labarin kinyi magana da mijina ko kinzo man gidan sai naci durin uwarki, kafin raihana tayi magana tuni badiyya ta fita dag gidan,

Baki raihana ta saki tana kallon umma, umma tace ai dama haka ne, idan dai baka da aure duk yanda kake da abokiyarki dole sai tayi nisa dake sabida kada ki aure mata miji, raihana tace ko waye yaje kuma ta haɗa wannan faɗan?"" umma tace Allah dai ya sawaƙe,

Bayan badiyya ta fita haka ta shiga gidan maƙotansu tana cewa ayi hankali da raihana aure take so, kuma duk mijin wanda ta riƙe tofa lallai yayi ta kanshi, saboda haka yanxun kowa ya fita harkarta,

***

Raihana ko fita tayi idan taga mace tayi mata magana bata ko kallon inda take, danma kada taga fuska tace zata zo gidanta, suma matan yusufa sunji labari, saboda haka sun shiga sun fita sun raba mijinsu da ita, dan ance idan har ta auri yusufa duk waje za"ayi dasu, to babu wanda take san *zawarci* duk wanda ta kama riƙewa take bata yanda ta sauka saboda rayuwa ,,,,

Raihana abun duk ya isheta saboda yanxun babu maiyi harkarta,

Ga baba ya kunno mata wuta ta fiddo miji tayi aure,

Kuka raihana takeyi gaban umma tace ita wallahi tama rasa ina zata saka rayuwarta, umma tace haƙuri zaki kawai ki fitar da miji kiyi aure, raihana tace umma ai babu mai sona, kuma a unguwa haka ake cewa wai bana aure sai nai kuɗi, jiya naje shagin shamau a gabana ake gulmana wai naƙi aure sai karuwanci nake a boye, inba ina iskanci ba, wai zan zauna har yanxun banyi aure ba, umma tace masu maganar suda Allah,

Kafin raihana tayi magana taji anacewa sallama alaikun raihan tana nan?"" raihana tace muryar waye nake ji kamar farida?""" tace nice, da sauri ta fito ta rungumeta sannan sukayo ɗakin umma,

Farida suka gaisa da umma sannan umma ta tashi ta fita daga ɗakin, tana fita farida ta fashe da kuka, raihana tace mi aka maki ke?""" tace ƙawata yaji nayo, amma gida har na fara fuskantar matsala kannena iskanci suke man idan nayi magana sai mamana tace ai rashin haƙurina yaja man gani nayo yaji har yanxun miji baizo biko ba, wallahi ko sabulun wanka mama ɗauke abinta take, amma lokacin ina gidan aurena baki ga yanda ake baki girma ba a gidanmu, raihana tace to duk miye yayi zafi haka?"" farida tace bari in faɗa maki abinda ya haɗani da mijina...........................

Raihana tace ina saurarenki,👂🏻

Kafin farida ta fara bada labari tace wallahi mata kuyi haƙuri ku zauna gidan mazajen ku dan *zawarci* ba ƙaramar fitina bane,

Sai yasa ka faɗa da mutane sannan kuma duk wanda yake ganinka da mutumci idan kana zaune gida saiya rainaka, Allah ya kara mana haƙuri ya uma ƙara mana ƙauna tsakaninmu da mazajenmu,
💦💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦

*Page* 1⃣6⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

````Meelat```

*Ƙawata Asmeenat Xeeyan Allah yasa damuwarki ubangiji ya yaye maki abinda yake damunki*

*Allah ya baki lafiya Halima Yahya Allah ubangiji yasa zakar jiki ne, Allah kuma ya baki ladar jinya*

*R*aihana tace inajinki,

Farida ta fara:• ke aure zaiyi ni kuma na tambayeshi dalilinshi na aure yace man saboda yana ra"ayi, tun lokacin daya faɗi man zaiyi aure na daina kwanciya ɗaki ɗaya dashi kuma na daina girki, na daina shara, duk abinda nasan baya so, shi nakeyi wanda nasan yana so kuma na daina,

Haka na shiga keta ma danginsa rashin mutumci, bana jin sauƙi a raina, kullum kamar ana balbala man wutar rashin mutumci a raina,

Irin abinda nake yasa ya zaunar dani yayi man nasiha, amma yanda kika san yana ƙara hayaƙani haka nakeji, dan nasihar kwata kwata bata shiga cikin jikina,

Idan kuma ya nemeni zaiyi kwanciyar aure dani sai ince yaje can wurin wanda zai auro tayi mashi tunda ni banda rana, da ina da amfani da baice zai sake aure ba,

Wannan abun yasa ya shiga maƙota gidan wata mata da muke gaisawa da ita, ya faɗa mata taxo taman nasiha,

Tazo tace man in rufa ma kaina asiri inyi haƙuri, wai miyasa mu mata bamu da adalci, duk wanda ta samu ta auri namiji bata yadda ya sake aure wannan wace irin rayuwace?"" idan ba"a aure ni an auro ni?"" ni banma gamsi da abinda take cewa ba, saboda haka na rufe idanuwa na, na cancara mata rashin mutumci, tunda ta tafi banma sake ganin ƙeyarta ba,

Muna cikin haka wata rana *safara'u* taxo, wata ƙawarsu ce, da taxo gidana na ganta ta zama "yar gayu ga makullin mota a hannunta ga ɓarka ɓarkan wayoyi, nace mata ƙawata ina kike aure yanxun?""

Dariya tayi safara,u sannan tace haba idan ina aure kin ganni haka?" aini nayi ban kwana da baƙin cikin namiji, jin wannan maganar da safara"u tayi yasa farida ta zayyano mata matsalar da take ciki,

Koda na gama gaya mata tace ni naso, in tattara inyi tafiya, idan yazo biki ince bazan koma ba, idan na rabu dashi zan su wanda yafi shi, ni kuma ina cikin wutar kishi, saboda haka shawarar da ta bani naga daidai ce, ta kuma ɗora da cewa ita gata babu aure amma tanajin daɗinta, ga motar ta kuma komai tace tana so za"a mata, tace yanda nike da kyau ina rabuwa dashi zan samu wanda yafi shi, wannan shawarar itace taman daidai, bayan safara,u ta tafi, na fara parking kayana, mai gida yana dawowa nace saiya sakeni,

Yace bazai sakeni ba, haka nayi ta bala"i ina masifa, amma ko inda nake bai kalla ba, dana ga haka kawai na tattara abinda zan nema a gida nayi tafiya na,

Tace raihana lokacin dana koma gida, har daɗi naji yanda aka nuna man ƙauna,

Hmmm ina yin sati ɗaya na fara ganin canji, wulaƙancin dai iri iri, wallahi wata rana ma idan ina buƙatar abu saidai inyi haƙuri, na gaji, kuma idan na kirashi a waya baya ɗauka, raihana tayi ajiyar zuciya tace gaskiya daɗi ya maki yawa, ina ruwanki da matar da zai auro?"" kima gode ma Allah bai sakeki ba, farida tace yanxun miye abinyi?"""

Raihana tace murje idanuwanki zaki kawai ki koma ɗakin mijinki, tace haba raihana ai babu aji kuma?"" raihana tace aji tun yaushe kika barshi a baya?"" farida tace kuma kinsan Allah har cewa nayi idan na tafi sai yaxo gidanmu yana haɗani da Allah bazan koma ba,

Raihana tace to kuma kin faɗa mashi wannan maganar miye dalilin da yasa kika kirashi?"" tace wallahi rashin tunani ne, tsaki raihana tayi sannan tace to ita safara"un ta san kin dawo gida?""

Farida tace ta sani mana, tunda data zo na faɗa mata halin da nake ciki sai tace zata haɗani da wani babban alhaji dama ai ba"a zama haka dole sai an ɗan nemi maza dan sune marufar asiri, wai har dubu ɗari zai bani, nace mata toni mijina na sunna ma na hanashi haƙƙinshi sai wani ƙaton banza, dariya tayi sannan tace man ai dama ɗan banzan wayanmu yake hanamu mu more rayuwarmu,

Bayan wani lokaci kuma na kirata nace mata nifa har yanxun mai gida baizo biko ba, tace man wai in shirya ta rakani wurin wani malami , haka na shirya mukaje wallahi raihana na kashe kuɗaɗe da yawa yace man zai kirani, bai kirani ba, saini na gaji na kirashi amma bai ɗauka ba ,

Raihana tace kinji wata matsalar kuma?"" nidai shawarar da zan baki kawai ki koma, idan ma yaxo ya taddaki a gidan kice mashi kawai kin dawo, farida tace gaskiya babu aji,

Raihana tace ai dama abinda yake ƙwararmu kenan matan malam bahaushe, wai ke girman kai kike ji, amma kinje kin kare kuɗinki wajen malamai amma basui maki komai ba,

Farida tayi shiru, raihana tace kixo gobe ni zan raka tunda har kikaga bai sakeki ba yana sanki, sannan kuma abinda yasa baizo biko ba, kila yana ganin kamar zaki mashi wulaƙanci tunda a haka kuka rabu,

Amma idan muka je Office ɗin nasu gobe idan Allah ya kaimu, abinda zakice mashi ,muna zuwa kawai kice ya baki makullin gida, kila zaice mi zakiyi?"" idan ya tambaya kice akwai wasu kayanki da zaki ɗauka ne, daga nan sai mu saurara muji abinda zaice, idan ya bada makullin sai muje gidan daga nan sai mu samu mafita,

Farida tace to Allah ya kaimu, raihana tace ai dole idan kina san zaman lafiya dole ki aje girman kai, idan ba haka ba, zakisha baƙar wahala, ni miye yaja man?"" gani nan ina zaune na rasa mai sona, ameenu kuma yana can ya samu tafi da gidanka, baki ga yanda akace take kula dashi ba, ina nan ina haukan banza, ni yanxun ma banda ubanda yake so na,

Wata rana ma hodar shafawa wahala take man, saboda haka ina baki haƙuri kawai kiyi haƙuri kixo ki koma ɗakinki tunda baizo ba bai aiko wani ba, duk maganar malamai ki barta duk ɓace hanya ce,

Farida tace babu damuwa Allah ya kaimu lafiya, haka sukai ɗan fira daga baya kuma farida ta ce zata tafi sai Allah ya kaimu raihana tayi mata rakiya sannan ta dawo gida,


***

Da daddare gwaggo tace ma raihana tazo takai ma ladi kuɗin adashen ta, raihana ta karɓa ta tafi,

Lokacin da ta isa gidan ta tadda ɗiyar ladi wanda take auren ameenu tsohon mijinta, bayan sun gaisa da ladi ta bata kuɗin, ita kuma ɗiyar ladin lokacin ta fito, ta ɗauki ɗanta ta fita saboda Ameenu yazo ɗaukarta,

Ita kuma lokacin raihana ta miƙe, tayi ma ladi saida safe, tana fitowa waje taga ameenu yana cikin motar zaune, ta matsa kusa dashi tace ranka ya daɗe ana ganin ka?""" kallon sama da ƙasa yayi mata, sannan ya kalli inda matarshi take, ita kuma taɓe baki tayi sannann tace malama ya akayi ne?"" abun yayi ma raihana ciwo saboda haka bata sake magana ba taja saɓa tabar wurin,

Tana tafiya sukazo suka wuce ta fuuuuuiiiii a mota, raihana ta matsa da sauri saboda ji tayi kamar aminu zai bigeta, lokacin da suka wuce raihana tace ikon Allah ashe aminu ba sona yake ba?"" har in ganshi in zuwabar da ajina inyi mashi magana amma ya basar dani,

Uhum Allah ka zaɓa mana alkairi haka kawai raihana ta faɗa a bayyane,

Lokacin da raihana ta iso gida, ta tadda an dawo da baba babu lafiya, duk su umma suna kusa dashi suna mashi sannu, itama raihana wurin taje tana mashi sannu,

Gwaggo tace raihana anshi maza kije ki sawo mashi maganin ciwon kai da masassara, tace to, gwaggo tace kada ki daɗe, raihana tace to, haka ta tafi taje ta siyo maganin ta dawo, baba yasha ya kwanta bacci,


****

Da safe baba yaji jiki da sauƙi abinka da ciwon talaka yace bara ya lallaɓa yaje kasuwa, haka ya lallaɓa ya tafi...............,,,,


Da rana misalin 1:34pm farida taxo, raihana itama taci shirin ta , tayi kyau sosai, saboda haka suna shirin tafiya *Office* ɗin mijin farida, niko nace lallai *zawarci* yayi zawarci tunda har mata zasu biko!!!




*A* madadin *AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* ni ```meelat``` nake cewa ku kasance tare dani,
📚✍🏻
💦💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦

*Page* 1⃣7⃣

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELART* 🌹

*T*are suka fito daga ɗaki farida da raihana Umma tana zaune a tsakar gida, raihana tace Umma sai mun dawo, umma tace to Allah yasa ku dawo lafiya ita dai umma bata san inda

Please Login or Register in order to submit comment