Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi a bayyane a ranta tace wancan ne cimarshi?""" tsaki tayi a ranta,,,,,,, sannan tace nifa bana cin komai,,,,,,,,, zainaba tace to....,,, fita tayi tabar ɗakin,,,,,

Faruk dake kwance yayi murmushi yace momysco kenan,,,,, hankalinki kwance kinsa hankalin "yan maza ya tashi,,,,, cije leɓonshi na ƙasa yayi tare da yin murmushin baƙin ciki,,, a gogon hannunshi ya kalla 1:02am,,,,, miƙewa yayi ya shiga toilet alwallah yayo, yaxo ya fara sallah,,,,,,,

***
*M*omy dake zaune farlo, ta kalli agogon dake maƙale jikin bangon farlon tayi murmushi sannan tace zainab kinga irin zuciyar ko?""",,,,,,, umar bazai zo ba,,,, zainab tace to momy ai yaji da ita,,,, momy tace idan shi taƙamarsa girman kai sainayi maganin taurin kai,,,,,, zainab tace momy shifa hali a ƙarƙashin rai yake,,,, tunda kinsan halinsa sai kiyi haƙuri ki tayashi da addu,a,,, momy tace duk taurin kansa sai yaxo ya sameni, zainab tace to shikenan,,,,,,

***

*K*wanci tashi babu wuya a wurin Allah, raihana yanxun tayi wata ɗaya da satika a gidan momy amma faruk baizo ba, kuma baiyi waya da kowa ba,,,,, yace idan momy ta dawo da raihana to, idan bata dawo da ita ba, can matsalarsu,,,, danshi baiga wanda ya isa yaja shi ƙasa ba saboda mace ba,,,,,, kuma duk wanda ya kirashi baya ɗauka, dan gaba ɗaya ya tattarasu ya zubar ,,,,,,

Raihana kuma tunda taje gidan momy bata yawo babu hijabi dan ita wata irin kunya gareta,,, kuma duk yanda takejin wani abu bata yadda wani ya gane,,,,, ita addu,arta ɗaya a barta ta koma gidansu da zama amma momy tace A, a, tayi zamanta anan tayi haƙuri,,, bata da yanda zatayi ta haƙura,,,, amma zainab tace ta barta ta koma ɗakinta wannan ba hukunci bane ,,,, momy tace idan bai zo ba, dole ta barta ta tafi,,,,

faruk kuwa harkar gabansa kawai yakeyi, idan sun haɗu da sadiq zaice mashi yaje gida momy tace yaje,,,, zaice kawai to,,,,,,,

Momy ce da bataliyarta zaune a farlo,,,,, hafsat zainab, amina , raihana, hafsat tace momy wai miye dalilin da yasa kika maido matar yaya a gidan nan,,,, momy tace haƙiƙa mai halinsa daban ne,,,, kuma duk wanda yabar hali haƙiƙa dama can ba nashi bane,,,,,

wato kana haihuwar ɗa amma kuma halinshi saiya banbanta da naka,,,, idan kana da halin kirki yayi mara kyau idan kana da halin banza zaiyi halin kirki, nidai banda zuciya, amma faruk bansan baƙar zuciyarshi inda ya sameta ba,,,,,, ga wani hali da gareshi nako Oho,,,, wato abinda ya faru shine,,,,,,

maganin nan dana ba raihana hafsat ban bada shi dan wani abu ba,,,, kunsan duk matar da umar yake aure?"",,,,, saiya sa anyi mata allurar planing?"",,, sukace A, a,, momy tace ni nayi bincike na gano, saboda duk matan da yake aure ace babu wanda ta taɓayin ciki?"",,,,,, da kaina naje asibitin da yake zuwa nayi bincike na gano hakan,,,,,,,

Dan haka na hana nace kada ayi ma raihana,,, nazo na sayi magani na bata dan kada yana kaita asibiti, ya ganta da ciki,,,, shiko magani nasan dole wata rana zata kuskure wurin shanshi,,,,,,,

Abinda yace man daya gano raihana tana mafani da magani, yace man ita kuma wannan da wannan salon tazo,,,,, nayi mashi faɗa shine yace shi idan ma abun yaxo da haka gaba ɗaya zaiyi haƙuri da aure,,,,,,

amma nidai abinda ya faɗa man game da matanshi daya rabu dasu shine,,,,,,,,,,,,
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦

*Page* 4⃣9⃣

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA*

***

*S*hi aure rayuwa gareshi idan kuma Allah ya ƙare zamanka da mutum sai kayi haƙuri,,,, nace to wane zalinci yasa kke wa mata allura?"",,,,, sai yace man a lokacin ya daina kai mace allura shi yana amfani da wani cream ne,

Aure auren da yayi yace duk abinda ya rabasu a yanda ya faɗi man, yace daga mai sata, sai mai kawo maza a gida, sai mai ƙoƙarin kasheshi dadai sauransu,,,,,

Nidai abunda na lura, shi aure aure ƙaddara ne, idan ubangiji ya ɗora maka jarabi a rayuwa baka da yanda zakayi, dan ko wane bawa yana da tashi ƙaddarar rayuwar,,,,

To daya ce raihana taxo da wannan salon , akwai matarshi umma daya aura , ta samu ciki lokacin daya saketa, ta tafi,,, bayan wani lokaci tazo tace man na zubar da ciki dani daku ko a lahira bamu da halaƙa,,,,,,,

To inajin shine yake tunanin cewa tazo da wani salon,,,,,,, amma shiya zauna dasu kuma shine yasan yanda yake jaraba mace,,,,,,, hafsat tace to kedai tunda an samu wannan ta zauna,,,,,, kafin itama yace baya auren nata momy ta koma,,,,,

Momy tace ƙarya yake bazai rabu da ita ba,,,, abu nawa nace kada yayiwa raihanar sai yayi,,,, hafsat tace kinsan garin wannan yaji yajin sai a samu matsala garin neman gira a rasa ido, tunda ta iyashi sai taje tayi ta haƙuri,,,,

Momy tace to,,,,, hafsat tace matar yaya kiyi haƙuri wata rana sai labari duk abinda yayi farko zaiyi ƙarshe, tunda mijinki yana sanki kiyi haƙuri kada ki wani damu da zuciyarshi,,,,,

Kedai zauna dashi tsakaninki da Allah,,, kiyi biyayya da zuciya ɗaya,, Allah yana kallonki wallahi ko ya taso zaiyi maki wani abu Allah bai zai bashi iko yayi maki ba,,,,,, raihana tace to,,,,,

Haka dai suka ɗanyi mata nasiha sosai,,,,, momy tace abinda yasa yake fushi dani wata yarinya ce, zaije ya jajibo kuma, wai dan nace mashi kada yayi aure shine yake fushi dani,,,, hafsat tace kedai Allah ya sawaƙe ai ban taɓa ganin hali irin na yaya ba,,,,,

Amina tace gara kowa ta koma ɗakinta momy a barki kema ki sararaaaaaa,,,,, haka dai suka yini suna fira,,, saida daddare kowa ya fara shirin tafiya gidanta,,,, dan haka momy da kanta kamar yanda taje ta taho da raihana taje ta maidata gidan faruk, ta ƙara mata nasiha,,,, sannan ta tafi,,,,,,

Momy tana tafiya,,,,,, raihana tace kai Allah ya sawaƙe, wannan wane irin haline don Allah?"",,,, wannan wane irin zuciya ne?"",,,,, to faruk wannan wane irin taurin kaine?""",,, Allah ya sawaƙe tace a daidai lokacin da take zamewa ta kwanta saman gado,,,,,

Da dariya ya nufi ɗakin tare da taɓa hannu,,,,, raihana dake kwance da sauri ta miƙe zaune,,, ɗaure fuskarshi yayi sannan yace kinga dama kin dawo?"",,,, raihana tayi shiru,,,, yace ai da kin sani kinyi zamanki,,,,,, ƙirjinsa yakai hannunsa ya taɓa sannan yace danni na soke ki a cikin lamarina yarinya,,,,,, dake za,a haɗa kai a wulaƙanta ni ko?" ya ɗan ɗaga girarsa murmushin takaici yayi sannan yace",,,, to ko anan, yaɗan ɗaga daidai ƙwalar rigar sa,,,,, sannan yaci gaba da cewa amma tunda kin dawo bani haƙuri,,,,,

Tsaki raihana tayi sannan ta kwanta,,,, faruk dake tsaye bakin ƙofa ya shiga cikin ɗakin wurin da raihana take kwance saman gado yaje ya jawota,,,, saida ya matso da ita bakin gado sannan ya ɗora guwarshi saman cinyarta tace ni kike ma tsaki?"",,,,,

kallonshi raihana tayi sannan tace da Allah ɗagani, wannan aicin zalin ne,,,, yace anci zalin ɗin , keba zalinci yasa kika tafi ba saboda tsabar iskanci da raini, tsaki raihana ta sakeyi tana ƙoƙarin tashi zaune,,,,, duƙawa yayi ya riƙe leɓonta na sama da ƙasa da hannunshi sannan yace idan kika sake man tsaki gaba ɗaya zanja su sai na ɓare maki baki,,,,,,, raihana cikin tsiwa tace aisai ka ɓare tunda bakinka ne,,,,, dariya yayi sannan ya ɗaga ta,,,,,

sannan yace bani haƙuri,,, raihana tace ai kaine zaka bani hakuri,,,, faruk ya riƙe ƙugu yace idan fa ana san zaman lafiya a bani haƙuri,,,,, raihana taɓe baki tayi sannan tace Allah ya baka haƙuri, baiyi magana ba ya fice daga ɗakin,,,,

tsaki raihana tayi a daidai lokacin da take kwanciya saman gado tana cewa gaskiya namiji mai zuciya baiyi ba,,,, niko nace komai sai an haɗa maki an baki,,,,,,

Faruk kuwa yana fita, kicin ya nufa, bawan Allah abinci ya ɗauko,,, ya nufi ɗakin raihana,,,,, bayan ya shiga ya ajiye abincin a ƙasa,,, sannan taje saman gado ya tasheta,,,,, yana cewa aciciya ga abinci, cikin yanayi na wanda ya fara bacci tace ta ƙoshi,,, yace tashi aciciya cinye manshi don Allah,,,, a daidai lokacin da yake jawota daga saman gado,,,

Raihana tace don Allah bana ci haba,,,, yace ke da Allah tashi,,, kwana da yawa banga ƙatuwar lomar aciciya ba, tsaki raihana tayi sannan tace don Allah ka daina ceman aciciya,,,,, dariya yayi sannan yace aciciya,,,,,,,

Dawowa yayi ya ɗauki abinci yaje saman gado ya tada ta zaune,,,, ya jawota jikinshi sannan yace bara a farayi maki lodi,,,,, haka dai ta haƙura yayi ta cusa mata , saida taci tasha mai sannan ya fitar da kayan ya mayar kicin,,,,,,,,

yana dawowa , yace mata taso muje,,,, tace ina zamu kuma?"",,,, baiyi magana ba, yayi waje,,,, tace Allah ya sawaƙe,,,, mutum komai sai yayi ta nuna isa da gadara,,,, dan gajeren tsaki tayi sannan ta tashi tabi bayanshi,,,,,

Farlo ta sameshi tsaye,,, tace wai ina zamu?"" ya kafeta da idanuwanshi, tace yiiiiiiiiiiiiiih kuka tayi ɗaki da gudu, tsaki yayi bai sake bi ta kanta ba, yayi ficewarsa daga farlo,,,,

yana fita mota ya hau yayi tafiyarsa,,,,,, ita kuma tana zuwa kwanciyarta tayi taci gaba da baccinta,,,,,

shi kuma lokacin daya dawo baije ɗakinta ba, ɗakinshi ya shige yaci gaba da ibadarshi.........

****

*T*o kowa dai yasan yau da gobe, kuma dole tsakanin harshe da haƙori ana samun saɓani,,,, to haka zaman faruk da raihana yake, danshi komao zuciya, sai yayi mata lafi wai kuma a dole shine zata bawa haƙuri,, a haka zata bashi dan tasan itace a ƙasanci,

raihana ce a toilet sai ihu take tana ƙarawa, tana kuka sosai,,, faruk dake kwance saman gado bacci yaɗan fara fizgarshi, ya tashi ya nufi toilet ɗin yana tambayar lafiya?"""",,,,,

amma raihana taƙi tayi magana, sai ihu take tana kallon cikinta,,,,,,, faruk sai magana yake amma bata ma san yanayi ba,,,,,,, riƙeta yayi sannan ta tsagaita da kukan tana kallonshi, yace miye?""" a hankali tayi magana tace cikina......,,, tare da sakin baki,,, faruk yace mi cikin naki yayi ne?""",,,,, raihana da hawaye suka sake gangarowa daga cikin idonta tayi kalar ban tausai , ta kalli faruk sannan ta sake magana cikin natsuwa, tace mutuwa zanyi,,,,,

Cikin damuwa faruk ya sake riƙeta sannan yace waye yace zaki mutu?"",,,,, har yanxun raihana kuka takeyi, yanda take abun ne yaji ta bashi tausayi , raihana tace kullum a cikina faɗa akeyi yau kuma naga cikin yayi wani ƙatoto,,,,,,,

tsaki faruk yayi baiyi magana ba, ya fita daga toilet ɗin, ganin ya fita raihana taci gaba da kuka tana diredire,,,,,, komawa yayi toilet ɗin baiyi magana ba, yaci gaba da kallonta,,,,, ita kuma tayi shiru,,, yace tunda bazakiyi wanka ba fito,,,,

yawo towel tayi ta ɗaura tabi bayanshi,,,,,, tana fitowa ya bar ɗakin, ita kuma ta matsa gaban madubi taci gaba da kallon cikin,,,,,,, tana kuka,,, saida tasha kukanta ta gaji dan kanta, shidai duk haukan da take bai sake bi ta kanta ba yana ɗakinshi,,,

kaya tasa ta nufi ɗakin,,,, tana shiga taci gaba da kuka,,, har ta kusa hawa saman gado ya sauko yaja hannunta ya fiddata waje ya rufe ɗakinshi,,,, da sauri ta tashi ta nufi wurin ƙofar tana kuka tana bubbugawa da ƙarfin tsiya,,, pillow ya ɗauka ya daɗe kunneshi yaci gaba da baccin shi,,,,,

ita kuma da ta gaji ta koma ɗaki ta kwanta amma taƙi bacci,,,, sai kuka take tana ayyano mutuwa,,,,,,,

***

*D*a safe bayan ya dawo sallah ɗakinta ya shiga, tana zaune saman gado ta zabga tagumi,,,,, ko tunanin mi takeyi?"",,,, faruk ya zauna a gefe raihana tayi kamar bata ganshi ba,,,,, dariya yayi sannan yace ashe haka kikeyi?""" idan bakiyi dariya ba kinfi kyau,,,, irin abinda take mashi idan yana fushi,,,, ƙara ɗaure fuska tayi sosai,,,, faruk ya sake sheƙewa da dariya sannan yace in sanii ni saina ma riƙa biya ana ɗaure fuskarnan amma na yau ai alakorone basai na biya ba,,, ɗan murmushi tayi , faruk yace nifa bana san dariya yau fuska nake so,, a daidai lokacin da yake kwanciya yana jawota jikinshi,,,,

yace ina kwana,,,, raihana tace lafiya qalau, yace kam lallao yarinyar nan wato nine zan gaishe ki ko?"",, batyi magana ba, yace miya sameki?"",,,,,, tace ban sani ba,,,, yace ai aiko ban sani ba babba ciwone ina kika samoshi?""",,,, tace kai bafa haka nake nufi ba,,,,, dariya yayi sosai sannan yace ai gani nayi za,a latsani nima na rama,,,,

Suna nan kwance yana ɗan janta da fira, yana bata labari wani tayi dariya wani kuma tayi shiru,,,,, yace aciciya yau tea kofi nawa kikasha ne?"",,, harararshi tayi cikin sigar wasa , sannan tace nace bana so , yace aciciyaaaaaaa,,,,,,, tace kaima acici, ni ta mace aciciya, kai namiji acici,,, dariya yayi sannan yace kuma kin iya bada suna fa,,,,,, haka dai yaci gaba da zaulayarta, yana ɗan sata nishaɗi,

saida rana tayi sosai sannan yace taje ta shirya su tafi asibiti,,, shima ɗakinshi yaje yayi wanka , ya shirya cikin shiga mai kyau da ɗaukar hankali,, ita raihana haka taci uban kyau ta haɗu,,,,, suka nufi asibiti,,,

Suna zuwa aka karɓesu cikin girmamawa , dan faruk yayi fice,, bayan "yan tambayoyi da "ya"yan gwaje gwaje, likita ya tabbatarwa faruk raihana tana ɗauke da ciki wata huɗu da sati ukku,,, jin daɗi wurin faruk ba,a magana, dan likitan da yayi mashi wannan babban albishir saida faruk ya zaneshi da bulallar kuɗi, ya barshi da jinya,,,,, kuma duk wanda yake asibitin wanda Allah yasa da rabonshi ya anshi hukunci oga, nima nan dai na samu 100k

Saida ya gama ɓarin kuɗi, likita kuma ya ƙara masu da shawarwari,,, kai tsaye gidan momy, suka nufa,,, a mota yabar raihana, dan yasan momy tana iya yaba mashi gaban raihana, dan tunda ta hanashi ƙara aure yake fushi da ita,,,,,,,,,,

Momyyyyyyyyyyyyyy adaidai lokacin da yake rungumeta, yana ɗan juyata,,,, momy tace ni zaka ma bariki ?""" faruk dariya yayi sannan yaɗan yi wata "yar rawa tare da kwaso shokiiii, yanda yayi abun ne yaba momy dariya,,,,, tace miye?"" yace da farko dai kiyi haƙuri ya duka ya riƙe ƙafatar yana cewa ta yafe mashi,,,,,,

Momy ta kamoshi ta miƙar dashi tsaye sannan tace na yafe maka, miye?""",,,,, murmushi faruk yayi sannan yace raihana keda ciki wata huɗu da sati ukku,,, yana maganar yana nunawa da hannunshi,,,,, momy tace Allah alhamdulillahi ubangiji ya raba lafiya, Allah ya bata lafiya, faruk yace amin,

juyawa yayi yana cewa saina dawo momy, momy tace zo nan,,,, komawa yayi momy tace to ita dai mai ciki ba,ayi mata zuciya, sai ka kiyaye da ɓata mata rai na faɗa maka,,,,,, yace to,,, da sauri yabar farlo, yana fita momy tace bawan Allah,

yana zuwa mota bayan ya shiga, ya kalli raihana yayi dariya, sannan yace aciciya,,,, batayi mashi magana ba,,,, yaci gaba janta, dan yasan bata san aciciya yake ce mata, tama gaji ta daina cewa ya bari,,,,,,,,,

Yinin ranar nan faruk haka yayi ta yawo da raihana a gari wai tayi farin ciki,,,,,,,

Kuma ko a gida ko wanka baya bari tayi da kanta, wai kada tayi fushi, ta samu matsala, kulawa sosai yake nuna mata,,,,,,, idan marece yayi haka zaijata su zagaya baya suyi wasa,,,,,, wannan ciki faruk jinshi yake kamar mi,,,,, abinci kuma baya bari ya tsinke saboda cikin wani irin cin abinci yake sata,,,,,,

Yanxun ma raihana ce kwance tana baccin rana,,, shine ya bashi damar fitowa waje,,,,, kafin ta tashi,,,, dan ita ganin yana wani ririta shi yasa take sheganta itama,,,,,,,,

yana zaune saman kujera a bakin ƙofar farlo ne,,,, yana karatun jarida,,,, ita kuma sai cewa takeyi barka da hutuwa "yar laɓai,,,, faruk ya ɗago kanshi ya kalleta,,,, murmushi yayi wanda yasa ta sauri durƙusawa ƙasa tana gaisheshi,,,,,,,

miƙewa tsaye yayi tare da cewa ku shigo mana,,,,, gwaggo da tawagar "ya"yanta suka bi bayan faruk,,,,,,,, ko wannensu ya riƙe haɓa yana mamakiyossss

Gwaggo taga sai wuce ƙattin parloli ake masu zubin indian parlour hankalin gwaggo ya tashi ba gwaggo ba harsu bushira haka sukayi ta bin bayan faruk har suka isa ciki......

Suna isa faruk yace su zauna,,,,, kowa ya kama kujera ya ɗare, faruk shima zama yayi saman kujera 1seater ya jirge, irin zaman nan na manya mutane,,,, wayarshi ya ɗauka yace mai aiki ya kawo masu lemu,,,,,

bayan an kawo masu faruk ya miƙe ya fita,,,,, dan yaɗan basu wuri suɗan ci susha,,, haka sukayi ta zuba ƙauyanaci komao saida suka cinye suka lashe kaff niko nace baku filako?""",,,,

Bayan ya dawo ne,,,, suka sake gaisawa,,,,,, haka sukayi ta fira,,,, gwaggo tace ina raihana ɗiyata?""" faruk yayi murmushi sannan yace bacci takeyi,,,, amma bara mu gani idan ta tashi,,,,, miƙewa yayi ya nufi ɗakin, raihana dage zaune gefen gado ta dafe cikinta,,,,, ta kalli faruk,,,,,

matsawa yayi da sauri wurin gadon yana cewa lafiya?""" taɓe baki raihana tayi sannan tace cikin nan ne fa kamar zai fito waje,,,, dariya faruk yayi sannan yace to swry a daidai lokacin daya zauna saman gadon ya rungumeta,,,,,, kwantar da kanta tayi saman jikinshi ya shafa kanta , sannan yace taso gasu gwaggos can a farlo sunxo,,,,,,,,,,

raihana ta ɗago kanta ta kalli faruk sannan tace waye gwaggos?""",,, yace wanda muka taɓa gaisawa da ita zamuje abuja a lokacin?""",,,,, raihana tace Allah sarki muje,,,, kamata yayi ya miƙar da ita tsaye , sannan ya riƙe hannunta suka fito farlo,

Saida suka shigo farlo sannan ya sakar mata hannu shi kuma ya fita,,, bushira tace in sani turawa,,,,, ku kuma haka kuke taku rayuwar auren ba kunya?""",,,,,, fiddausi tace keko ta nuna mana miji yna ƙaunarta,,,, raihana tayi dariya a daidai lokacin data zauna saman kujera,,,,,

dariya ta sakeyi, a ranta tace lalao faruk wai su wannan ne gwaggos?"" kila suma ya ɗauka duk gwaggona ne,,,,,kallon gwaggo raihana tayi sannan ta gaisheta,,, haka ta gaishe dasu fiddausi,,,,,,,

gwaggo tace dan kinyi aure a gidan soja wulaƙanci mu sai anyi mana tambayoyi kamar munxo waƙahi?""" ɗan kishingiɗawa raihana tayi saman kujera sannan ta ɗauki ƙafa ɗaya ta ɗora saman ɗaya,,,, sannan tace Allah ya baki haƙuri gwaggo,,,,,,,

gwaggo tace kina nan kin lutse abunki gidan soja , ga ƙatti suna gadinki ga manyan karnuka kamar a gida yare,,, ga bindigu masu sa birgici, mijinki yana sanki,,,, gaki kuma har kinyi ciki,,,,,

Cikin jin kunya raihana tace kaini gwaggo?"""",,, gwaggo tace to wallahi kidai bi ahankali mai yankar kaine mai gdan nan,,,,, dariya raihana tayi sannan tace ai idan ya cinyeni ya huta,,,,,

Bushira tace aike banza ce,,,, fiddausi tace da Allah ku barta ,,,, koma dai miye can ta matse mata,,,,,, tashi mu ki bamu kuɗi,,,,,, raihana tace kuɗi kuma?""",,,, fiddausi tace Eh,,,

Raihana tace to mi nake siyarwa?""" fiddausi tace wannan ƙaton gida?"",,,,har zakice kin rasa kuɗi?"",,, raihana tayi dariya sannan tace ai ga mai gdan a gabanku ya fita,,,,, bara in kira maku shi,,,,,,,,,

fiddausi tace ke , da Allah miye haka?"",, raihana tace in barshi?""" fiddausi tace Eh, dariya raihana tayi sannan ta zauna,,, gwaggo tace to bamu turamen atamfa,,,, raihana tace gwaggo nan fa ba kasuwa bace,,,,,,, gwaggo batayi magana ba, faruk ya shigo,,,, gaɓa ɗaya suka miƙe,,,,,, suna cewa zasu tafi,,,

faruk yace tun yanxu?"",,, tace Eh, yace to ku jirani,,,,,, ɗaki ya shiga bai daɗe da shiga ba ya fito,,,, wata "yar ƙaramar lader ya basu,,, suka ansa suna godiya,,, gwaggo saida ta buɗe taga ashe hatimin nasara ne kwance a ciki,,,, gwaggo an samu yanda akeso,,,,,

ta yashe baki taci gaba da zungurawa iyayen faruk addu,a,,, tana godiya kamar marokiya,,,,

Faruk yasa aka ɗaukesu aka mayar dasu gida,,,,, raihana kuwa bata basu komai ba, sukayo rakiya suka dawo,,,,

****
*K*wanci tashi babu wuya a wurin Allah su raihana an shiga wata aihuwa,,, dan haka tabi ta dami faruk lallai ita a gida zata koma ta aihu,,, wannan abun ne yasa shara"a, har wurin momy,,,,,,,

Ita kuma abinda tace raihana tayi haƙuri tayi zaman ta gdanta wannan duk bidi"a ne,,,, wannan wankan jego ɗin daga nan aure ake samun matsala,,,, dan haka tace tayi haƙuri idan ta aihu ko wata "yar uwarsu tazo ta zauna,,,,, ko kuma a samar mata wata tsohuwa ta zauna,,,,,, haka dai raihana tayi haƙuri,,,,,,

To kuma ana cikin haka zulaihat ta aihu,,,, raihana tace zataje,,, faruk yace babu fita harsai ta aihu,,,, dole ta haƙura,,,,,

Duk safiya haka yake jan raihana cikin gida yaɗan jijjjigata da wasanni,,,,, wanda zata ɗan motsa jiki,,,, sosai raihana tanajin daɗin kasancewa da faruk sosai matsala ɗaya zuciya,,,,,,,, amma a hankali tana fahimtarshi dan haka kuma tana ƙoƙari wurin ganin tana kiyayewa,,,,,,,,

***
*S*u raihana yau ba baka sai kunne,,,,,, tunda safe take kuka wai mararta na mata ciwo,,,,, faruk dake ta shirin tafiya,,,, yace babu wani nan dan kada in tafi,,,,, raihana tace Allah da gaske nake,,,, yace to Allah ya sawaƙe,,,,, zaki samu sauƙi,,,,,,, haka yaci gaba da shirinshi,,,, lokacin daya fito zai tafi raihana tayi ta kuka ta riƙeshi wai saidai su tafi tare,,,,,,, murmushi faruk yayi sannan yace to ta shirya,,,,,, maza ta tattaro kayanta,,,, da sauri ta nufi ɗaki dan haɗa kaya,,,,,,,,

tana shiga ɗaki shi kuma ya sulala yabar farlon kafin ta fito tuni faruk sun bar gidannnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnn...........
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦

*Page* 5⃣0⃣

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

🔚🔚

****

*R*aihana kuwa jin fitar motoci, da gudu ta fito kafin ta ida isowa tuni sunbar gidan,, wayarta dake hannunta ta fara kiran wayar faruk,,,,,,,,,,

Wayar tana shiga ya ɗauka tare da cewa aciciya abincinki?""" raihana tace da Allah malam wane abinci?"" dariya yayi sannan yace Allah ya baki haƙuri, miye?""" raihana tace wallahi banda lafiya sosai,,,,, murmushi yayi sannan yace ina maki addu"a sannu,, daga haka bai sake magana ba ya kashe wayarshi,,,,,

Ita kuma jin ya kashe wayar yasa ta fara kiran wayar ummanta,,, bayan umma ta ɗauka suka gaisa, raihana tace mata umma banda lafiya , umma tace miya sameki?""",,,,, raihana tace kawai dai wani iri nake ji,,,, dariya umma tayi sannan tace to sannu,,,,, ko asibiti zaki?"" raihana tace Eh,,, umma tace to ki faɗawa maman faruk ɗin mana,,, raihana tace ita dai A,a, umma tace kedai faɗa masu ki fita haƙƙinsu idan basu da hali ki kirani, raihana tace to sannan ta kashe wayarta,,,

Da sauri ta sauko daga saman gado ta durƙushe ƙasa,,,, tana innalillahi wa"inna ilaihir raji"un,,,,, tana ci gaba da maimatawa, zufa kusa sai keto mata take saboda azaba,,,,,,, kwanciya tayi daƙel ta iya ɗaga wayarta ta fara kiran zainab, dan kiran momy ya mata nauhi,,,,

Zainab tana ɗauka babu gaisuwa cikin murya jigata da wahaltuwa raihana tace ban lafi.......,,,,,, ai bata ƙarasa maganar ba, wayar ta faɗi ƙasa,, zainab taci gaba da cewa hello hello da sauri ta fito tana kiran momy,,,, momy dake farlo zaune tace miye?""" zainab tace gdan yaya babu lafiya fa,,,,,,

Momy tace wani abu ya faru ne?""",,,,, zainab tace naji tana cewa bata lafiya,,,, amma ta kashe wayar kuma na sake kiran wayar bata ɗauka ba,,,,,, momy cikin damuwa tace muje mu gani,,,,,,,,,, zainab ta koa ɗaki ta ɗauko gyalenta,,,, momy kuma akwai hijabi a jikinta, don haka da sauri zainab ta ɗauki makullin motar tayi gaba momy tabi bayanta .....

Ita kuma raihana,,,,, tana kwance har yanxun a wurin,,, ga wayarta a gefe sai kira yake shigowa tanaji amma bata iya ɗauka,,,,,, da momy da zainab tare suka shigo,,, da sauri momy ta ƙarasa inda raihana take kwance tana tambayar lafiya?""",,,

Raihana dai ta kasa magana,,,, zainab tace sannu matar yaya,,,,, momy tace wane sannu matar yaya, kamata asibiti zamu,,,,, zainab tace to,,, haka suka kama raihana, sukaje suka sakata mota, sai asibiti.....

Kafin suje tuni raihana tayi lugufff saboda jagalgalar mota,,,,, suna zuwa aka anshi raihana sai ɗakin ido ya raina fata,,, raihana sai salati take tana ƙarawa, momy kuwa sai addu,a take,,,,, zainab kuma sai kuka taketana kiran number hafsat, ta sheda mata , itama tace gata nan zuwa yanxun insha Allah,

Umma kuma ta kira wayar raihana harta gaji don haka ta haƙura, shi kuma faruk kiran wayar raihana bata ɗauka ba yasa shi dawowa,,,, a asibiti kuma momy tace zainab tunda an kawo raihana ta koma gda ta ɗauko mata kayan da zata canja, idan ta aihu ,

Suna nan jigumjigum, suna sauraren ikon Allah har zainab taje ta ɗauko kaya ta dawo, dan tunda cikin raihana ya shiga wata haihuwa ta haɗa komai a akwati da kayan babies ɗinta,, komai da komai da za,a buƙata,,,

zainab bata daɗe da dawowa ba, 6ter ta fito tare da cewa an sauka lafiya,,,,,, momy tace mi aka samu?"" dariya tayi, bata faɗa ba , tace sai ta shiga ta gani,,,,, momy tace wannan wane irin abune?"" ai tun ana aihuwa ake sanin abinda aka samu,,,, tace yi haƙuri momy, haka aka samu ta nuna da hannunta,,,,,, momy sai dariya take tana Allah raya,,,,,,

Ɗaukar kayan tayi ta koma ciki, kulawa mai kyau raihana ta samu dan asibitin kuɗi tasha banban , saida ta

Please Login or Register in order to submit comment